NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


A JIYA MUN TSAYA 

Hankalin Adamu sam bai kwanta ba, tsoron ko kashe matar ubansa da Salmanu yake ta kirarin yi ya tafi cikawa ya kada cikin Adamu ainun, kawai sai yayi saurin rufe dakinsa ya tafi cikin gida wajen mahaifiyarsa _ hira, abinda ya jima bai yi ba musamman a lokaci? irin wannan, shi manufarsa, idan ma wata aika-aikar Salmanu ya je yayi ko an kama Salmanun idan aka hado da shi zai iya samun shaidar cewa ai dai-dai wanna lokacin yana’ cikin gidansu kusa da gyatumarsa, musamman dayake gidan nasu Kafa bata daukewa da masu siyen goro, ko wani bai gan shi ba wani zai gan shi tare da mahaifiyar — tasa. Salmanu na zaune a dakalin Kofar gidansu. Adamu cikin shigarsa ta Basaja_. wadda idan ba farin sani kayi masa ba daga kallo daya ba zaka shaida shi ba.
– Duk da ba aikin kirki yake shirin yi ba cikin nutsuwarsa yake, lokaci-lokaci yana kallon hanya har tsawon fiye da mintuna talatin. Allah ya taimake shi wadda yake jiran

ZAMU TASHI 

Karasowarta sai ga ta ya hango daidai lokacin da aka tayar da sallar Isha a masallacin unguwar.Da sauri ya mike ya shiga soron gidan wanda yake dundum da duhu ya labe. Yanzu

Kirjinsa na harbawa amma ba na tsoro bane face na fargabar kar Adamu da Sallar jam’! bata wucewa ya fito zuwa sallar Isha ya Bata _ masa shiri,

Salma cike da-doki da Kumajinta ta sako * Kafa soron gidan tana kokawar kunna fitilar wayarta, tun yamma ta sami aiken guntuwar wasika daga Adamu mai dauke da cewa,

Abin ‘yar haka ne? bani da lafiya amma kin kasa zuwa duba ni. To ina jiran zuwanki bayan sallar Isha in ban ga fuskarki ba zan -~ Iya runtsawa ba. ; .

’ Ita. da Anti Sa’a sun sha tsallen murnar hakkansu ya cimma ruwa, bayan sallar isha kuwa ta ci kwalabo ta dauko Kafa ta taho ba tare da sanin makircin Salmanu ta ratso ba, Adamu bai san da takardar ba kuma har zuwa_ . yau begenta bai yi masa yawan da zai kasa

Www.bankinhausanovels.com.ng runtsawa ba, yana kasa runtsawa_ tabbas amma kuka yake sharba yana tuhumar ta ” hanyar da ta bi ta shiga zuciyarsa.  Salmanu da ke labe bai bari ta kunna wayar tata ba ya fizge wayar, lokaci guda kuma ya fizgi hannunta cikin zafin nama. ’ ya jata ya makure a bango ya toshe mata baki – da hannunsa na hagu, na daman kuma ya zaro wuKkar da ke aljihunsa ya dora mata a wuya, ‘ yayi mata Magana cikin kaushin murya da tsoratarwa, . a . “Bari na kashe azzaluma kafin ta kashe wanda ta yi niyya” Salma ta sha kwatanta yadda ake mutuwar tsaye, amma bata taba tsammanin haka take ba sai yanzu da ta sami kanta cikin wannan wadin a ‘yan wadanann sakannin. Kirjinta sai bugwa yake fat-fat. Sai Salmanu ya sauke hannunsa da ya toshe bakinta cikin murya kasa-kasa yace mata, “Na rantse da Allah kika yi min ihu sai na Burma miki wuKar nan a ciki” ‘

Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta hadiye wani mugun yawu da Kyar, jikinta na Bari ta ce, . . “Wallahi ba zan yi ihu ba….. amma me kake nufi da ni?… don Allah kar ka bata min rayuwa…” Kafin ta rufe baki Salmanu ya kwaso wata uwar ashar ya rusa mata, ya dora da – ” cewa,  “Kun ci kaza-kazanku ke da abin naki, — . ke har kina da abinda za’a Kwata da Karfi? * Ko kyauta kika kawo min kanki zan kalle ki?”’…. ° . Salma ta ji raguwar fargaba da wannan kalaman nasa, don abinda ta fi tsoro kenan ‘ fyade, gara ma ya gurza mata wuKar da yake nuna ta da ita a-wuya da ace yayi mata fyaden. . , ‘“To…to…to, me nayi maka? Allah ya baka hakuri don Sayyidina Rasulullahi, _Ba tare da Salmanu ya janye wuKarsa ‘daga wuyanta ba ya ce, ‘ “Wanne tsubbun kika yi wa Adamu?” .

Www.bankinhausanovels.com.ng Hantar cikin Salma ta shiga kadawa kirrrrr! Har Salmanu na jiyo Kararta, bakinta na sassarfa ta ce, .

” “Ban gane ba wallahi” – Tana rufe baki Salmanu ya tare ta, “Zaki gane in kin ji kaifin wuKar, kin ga

in kin je lahira sai ki fadawa Allah dalilin dana turo ki can” . “Na rantse da Allah da gaske nake ban gane ba”.  Ta sake fada cikin kuka. _Salmanu ya amsa,  *Adamu ba ya sonki, kin kai shi gurin boka ya tsafe masa zuciya, shin kin san Kuncin da kika jefa shi kuwa? Za’a iya cutata na share mutum amma Karya ne a taba. rayuwar Adamu na Kyale”.” . Yanzu tsoron Salma ya nunka na da, tana fargabar ta inda aka ganta a gidan boka kuma – aka gane Adamu ta kai, sannan a daidai wannan lokacin ta dauki muryar mai gwada ta da wukKa, abokin Adamu ne Salmanu, ta san kuma da gaske Zai iya girba mata wukar.

Www.bankinhausanovels.com.ng Numfashinta sai kai komo yake tamkar. ta shide take jin kanta, sai du’a’I take Allah ya kubutar da ita. ‘Salmanu’ ya: dinga jero mata kwandon ashar yana saukewa, Karshe ya ci mata ’ alwashin in dai bata je ta karya asirin da tayi wa abokinsa ba to ta tabbatar kwananta Kalilan ne a duniya. Yana jin ya gama yi-mata kashedin ya , ‘tunkuda ta waje yana fadin,

“Bace min da gani, makira mai siffar dutsen guga, don zalinci kuma kin ga sambalelen yaro kin maKale masa”

. Kafar Salma rawa take tamkar ana kada mata gangi, amma a haka ta suri sauri, nan da nan sai ga ta ta Bace kamar walkiya.

Salmanu ya fito kan dakali ya zauna yana . kwasar dariya har da tuntsirawa. . . Ya san abinda. yayi kasada ce da zumuncin da ke tsakaninsa da gidansu _ Adamu, amma yana da yaKinin sai yayi _ tasirin samowa Adamu farin ciki ko KaKane. – “Barka da dare” . }

Www.bankinhausanovels.com.ng Ya ji wata zazzaKar murya ta farkar da shi lissafin dokin ranon da yake a tunanin makomar alakarsa da gidansu Adamu, don ba ya jin Adamu, ya san mai raba su sai mutuwa.

Ya dago da sauri ya kalli doguwar_. yarinyar da ke tsaye a gabansa wadda duhun dare bai hana shi gane ta ba, Husnan Adamu ce. ’

. Da hanzari cikin rawar murya ya amsa . Mata, = . ; “Barkanki dai” Cikin sakewa.ta sake ce masa, “Yauwa, ya harkoki ya. ayyuka?” A mamakance ya sake amsa mata, “A lhamdulillahi” -Ta dan yi jim, kafin da alamun Karfin hali tace, “Don Allah Adamu nake tambaya” Ya dan yi jim shi ma, har zai mike ya ce bari a kira miki shi, me ya tuna? Oho! Sai kuma ya fasa. A sanyaye ya kada kai, “Ya dan fita da nisa kuma, Kila ya kai , Karfe goma kafin ya shigo”

Www.bankinhausanovels.com.ng Husna ta gyara tsaiwar da a bayyane.ta nuna damuwar jin Adamu ba ya kusa ne, kamar ta rushe da kuka ta rarrashi kanta. A sanyaye ta miKa masa wasiKar da ta sherowa Adamu tana cewa, “Kai ne abokinsa dana gan ku tare rannan?” . ;

Salmanu ya karbi wasiKar yana amsawa’ “Eh nine, ban gane ki ba”.

Husna ta dan yi hucin hadiye damuwa da son nuna komai ba komai ba ne,

“Ka ba shi wannan takardar don Allah” Ta fada a takaice tare da share Korafinsa na bai gane ta ba.

Ya shiga juya takardar yana saKa abinda zai ce mata, bai Ankara ba sai jin muryarta yayi tana yi masa sai da safe tare da cewa,

“Na gode” “To sai anjima” Ya sami kansa da amsawa_ cikin dakusasshiyar murya yana hangenta har ta bace masa, a birkice ya sake mayar da  hankali ga kallon takardar amma azancinsa na

Www.bankinhausanovels.com.ng ga tunanin yadda soyayyar abokinsa ke zuwa a hagunce.

************

Salmanu ya jure boye takardar da Husna ta kawo wa Adamu har tsakiyar dare, kama akan ta ne ya zauna kwana a gidan, don da farko saboda aika-aikar da ya yi wa Salma yayi niyyar barin gidan don bai san abinda zata je gida ta fada ba, Kila kuma Alh. ya shiga maganar, a ZO nan a same shi atitsiye shi. ° Sai da ya bari dare ya raba, Adamu ya ’ hau buzunsa yana kuka yana rokon Allah. Raka’a biyu kacal yayi ya durKushe ya daga hannaye sama cikin kuka yana cewa, -‘ “Allah ka gan ta, sallar nan ‘yar faki ce ba yawa sai lada, gabobina sun yi rauni bisa abinda ka jarrabe ni da shi, Allah ka karkato da albarkarka da rahamarka gare ni da ‘ Zuciyata da kuma Husna da ka sa mana sonta, Allah kar ka Kwace mana sonta da ka ba mu,

Www.bankinhausanovels.com.ng kuma kar ka jarrabe mu da son abinda tun fil azal ba ma so” A cikin tausayi Salmanu yake amma addu’ar nan ta Adamu tayi mugun bashi dariya har ta tashe shi zaune, yace Kai dan iskan ina ne da kake son kashe_ ni da dariya?” Adamu bai kula ba ya cigaba da addu’arsa har sai da Salmanu ya furta cewa, “Kai ma ka tuna-min, dazu Husna ta ~ . kawo saKo a baka”  Da sauri Adamu ya shafa addu’ar ya – dube. shi cikin shakkun jin -abinda  ‘kunnuwansa suka ‘jiye masa, ya tsurawa – ” Salmanu ido a birkice,  . “Ka ce me! Husna?” me – Cike da jin alfahari Salmanu-ya mike ya dauko wasikar a aljihun wandonsa yana cewa, ~ . Meye na shakkun, menene Allah ba zai ‘ “ iya ba? Husna ceta kawo maka wasiKa, kuma daga jin yadda takardar ke tashin kamshi

Www.bankinhausanovels.com.ng kowa ya san saKon soyayya take dauke da shi Jikin Adamu na bari ya rarrafo daga shimfidar sallarsa ya zo ya riski Salmanu. ‘ Suka ware takarda dukkansu da dokin ganin abinda ta Kunsa, musamman Adamu, ga shi kuma Salmanu ya kankane takardar ya hana shi wai sai ya fara karantawa. Zuciyar Adamu sai bugawa take saboda ganin yadda Salmanu yayi duru-duru yana bin takardar da kallo cikin yatsine fuska, daga ganin abinda yake karantawa a takardar ba mai dadin ji da gani bane. Wai ya na ga kana ta faman tamushe fuska kamar wanda aka matsawa cin kashi?” –

Adamu ya kasa hakuri sai da ya tambaya.

A sanyaye Salmanu ya mika masa takardar yana sakin damarar da ya yi wa fuskarsa yana cewa,

“A’a babu komai, karatun takardar ne ya fi Karfina saboda da harshen Ingilishi ta rubuta. Sai dai kai ka karanta mana”

Www.bankinhausanovels.com.ng Kirjin Adamu ya barko wata shegiyar Kara saboda jin wannan samu da rashi, shi ma ba iya turancin yayi ba, karatun da yayi duk bige ne, kuma tun tuni ya sha rantsuwar ba zai bata lokacinsa a boko ba saboda babu abincinsa a ciki, ban da gaisuwa da Kananan kalmomin turancin yau da kullum da ake ji har a bakin wanda bai je makaranta ba ma bai san komai ba, saboda haka a kawo masamaganar ya karanta wasiKar turanci ma ya zama wani yarfa masa yaji a gyambo. Ya sauke wani irin gwauron numfashi ya ajiye takardar jiki a sanyaye ya koma ya hada kai da gwiwa. Salmanu ya shiga mamaki Kwarai, cikin ci-da-zuci ya dafa kafadar Adamu y ace, “Ina fatan ba zagi ta antayo maka ba?” Adamu ya hadiye Kunan ransa yace, “Ba na tsammanin zagin ne” “Yaya baka tsammmanin zagi ne, baka . karanta ba ne?” ; Salmanu ya sake tambaya a Kagauce, . Adamu ya daure dai ya fito da shi haske,

Www.bankinhausanovels.com.ng “Ni ma ban da gaisuwar sama ban gane komai a turancin nata ba”
Ba ta iya ba ko, amma dole sai ta yi mana fafa” ..

Salmanu ya fada iyakar gaskiyarsa, don shi kansa bai san Adamu bai iya turanci ba, musamman dayake in yana Magana yana jefa

‘ na Kare yawa. .

Haushin Salmanu duk. ya cika Adamu fiye ma da haushin yadda ya kasa sanin menene sakon da masoyiyarsa ta aiko masa. ~

. Salmanu ya sake daukan wasikar da – Adamu ya ajiye ya hau dabura karatunta . fili. Kawai sai Adamu ya ji kuka na neman ‘ kwace masa, amma ya daure ya hadiye shi ya fanshe dacewa, ~“Allah ka tsinewa wadanda suka kawo mana turanci suka ce mu dinga karatu da rubutu da shi, ko kowa ya yafe musu Allah ni . ba zan yafe musu ba” .

Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu ya saki takarda,-dariya da kuka-kuka na damunsa, cikin hadiye su duka ya dubi Adamu ya ce, “Au ko kai ne baka iya turancin ba ne?” ‘ “Eh mana!” _ Adamu ya amsa a fusace.  Kawai sai Salmanu ya saki dariyarsa son ransa. Ya dinga yi babu KakKautawa, tun tana Kular da Adamu har shi ma dariyar ta fara ‘ kama shi ya shiga taya Salmanu har suka ci suka Koshi sannan suka dawo neman mafita. _ Wai yanzu yayaza’ayine?” – — In ji Salmanu. |Adamu ya dan ja fasali sannan ya girgiza _ kai, ~ “Ni wallahi gaba daya kaina ya kulle sai dai zuwa gobe”’ – Salmanu ya fara gyara filonsa yana shirin ~ kwanciya ya ce, “Allah tashe mu Kalau, ko wani ne sai mu -nema ya karanta mana ya bayar mana da amsa” ; A Kufule Adamu ya tare shi, “Allah ya kiyaye, ai gara har in mutu ban san abinda ta rubuto ba…”

Www.bankinhausanovels.com.ng Shi ma Salmanu ya tare shi, . “In-haka ne babu wata mafita kenan” Adamu y ace, . +» “Mu dai jira goben mu gani”

Www.bankinhausanovels.com.ng

Hankalin Anti Sa’a yayi mugun tashi bisa labarin da Salma ta kawo mata; ta rasa inda * zata Bullowa lamarin ta wanke kanta idan dai. har da gaske ne wani basa’iden ya gan su a * gidan boka har ya fesa-labarin yadda ya koma . kunnensu, hukuncin da.za’ayi musu shi ne kisa__ da wuKa?‘ “‘Anya ba hasashe ba ne kawai Adamu da Salmanu suka yi Salma?” Data gama walankeluwar hasashenta ta yiwa Salma wanna tambayar da safe. ‘Salma har yanzu a tsorace take, don haka , bata iya tankawa ba face ta dinga ringima kai _ kamar Kadangare tana yarfe hannu, Anti Sa’a-ta sake girgizakai, «© < . “Ina shakkar hakan, amma dai zan yi . Kunar bakin wake in gwada wata dabara”’ |

Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta dago ta dube ta cikin zare ido, baki na rawa ta ce,
Me zaki yi?.A tsorace nake wannan maganar ta je kunnen Hajiya, ina da yaKinin ~ wani ne ya gan mu ya je ya fada. Ni dai na shiga uku, ban fara bin boka a sa’a ba….”

_ Kawai sai ta zarce da shassheKar kuka.

Wani mugun takaici ya tokare wa Anti Sa’a a maKoshi, ta kashe Salma da harara cikin mugun Kunan rai, Ke fa wallahi wata muguwar jaka ce, in an hada abin kirki da ke sai kin tankwabe – KoKarin mutum…”Salma ta katse ta cikin goge hawaye, ..

“Ni ba haka nake nufi ba Anti, kawai dai

_ abin ne ya firgita ni kuma dole ma kin san na –

_ yi ta hasashen ta inda suka gano mu, bugu da ; Kari ma ban sani ba maganin ya kama Adamu_ . ko bai kama shi ba tunda har suka sami damar —

‘tattauna na yi masa asiri shi da Abokinsa, kalli lamarin da kyau Anti dole ne ya firgita ‘irina” Anti Sa’a ta yi shiru tsawon lokaci, can sai
ta mike ta tafi Dakin maigidanta tana cewa

Salma,Www.bankinhausanovels.com.ng “Bari na gwada dabarar da na ce miki zar gwada mu gani’ Salma bata iya tankawa ba, illa ta bi Antin da kallo cikin shanye baki da bugawar zuciya. A mugun tsorace take, tana fargabar abinda zai . biyo baya idan Kwai ya fashe, akwai zallar kunya a ce wai ita ce budurwarta da ita kuma ‘yar uwar Adamu a ce ta kai kanta gurin boka neman soyayyar saurayi, saurayin ma dan . uwanta. Haba wannan abin kunyar har ina! Anti Sa’a ta sami Maigidanta kishingide yana hutawa, akwai alamun hankalinsa a. kwance yake, don haka ta Karawa fuskarta da. furucinta nutsuwa, amma fuskarta a Bace ta yi sallama, .hakan ya sanya ya karkato da hankalinsa gareta fuskarsa babu yabo babu fallasa, –  “Ke da wa na ga fuskarki da fishi?” _ Tanemi kyarar da ke fuskantarsa ta zauna tana ajiyar zuciya, . “Ba fishi ba ne bacin rai ne Alh. wani ta’addanci Abokin Adamu ya. kwaso ya kawo mana, wanda idan an bar shi ya sha gaskiya ba. akyautawakaiba” .

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *