NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
“Kayan lefen da za’a kai wa Husna, shin ke zamu bawa kudin ki siyo ko kuma shawartar Alhaji zamu yi? Mun so zuwa mu siyo sai muka ga in mukayi hakan Kila ba zaku ji dadi ba”Hajiya na bayewa tana matsar hawaye na dalilin rashin sanin inda suka samo kudin, ta amsa Masa, gara da kuka yi azancin kawowaba ni banida matsala, amma su Sa,a Kila ransu ba zai so. ba, alhalin Kan harkokinmu, saita ga kamar dalilin _ Salma ake baya da ita”tunda dai ta ambaci Sa’a daga Adamu_ har * Salmanu suka Kule, don haka cikinsu babu wanda ya – ’ sake tankawa kan maganar lefen har suka yi sallama da ita suka tafi gidan Alhaji… . A hanya Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu yake cewa,“Adamu akwai yiwuwar fa mu fasa bayar ‘da_ kudin nan, in dai akwai Sa’a cikin manunar nan to ni kam hankalina bai kwanta ba” Adamu yayi shiru yana nazari, shi ma dai ya _tsani Sa’a Kila fiye da yadda Salmanun ya tsaneta, don dai kawai bai kai Salmanu nuna zara bane. Ai kuwa, suna kawo wa Alhaji maganar ya gyara muryarsa yace – ku bayar da kudin sai a bawa Sa’a ta siyo, na Salma ma ita ta siyo komai
ZAMU TASHI
Da kyar a cikinsu aka samu Salmanu ya dan yi nishi
“Himn!”.Alhaji da yake zaton sun kawo masa maganar lefe ne don suna son yayi musu ciko, ya sake gyara zama yace musu,
“Amma dai don Allah kar ku yi mata Kwauron kudi, in baku shirya ba kawai a daga..Salmanu da yafi Adamu wutar ciki sai ya tare Alhaji, .Dubu dari biyu ne da mu, a tambaye ta idan basu isa ba za mu Karo ko hamsin ne…”.
Numfashin Alhaji ya so ya dauke, yayi saKare yana kallonsu baki bude,
‘ “Dubu dari biyu kace? Har ma in sun yi kadan za ku Karo wasu, haka kace ko?”
Salmanu ya kada kai, Adamu kuma yayi Kasa da nasa kan yana saKa ta inda zai daki Kalubalen Alhaji idan ya jefo, shi dai ya san ko ta ina ba zai yarda da wata dakatarwar Alhaji mai taba rai ba. ‘ Alhaji ya dubi tsakiya idon Adamu yace, Adamu a sana’ar hakar Www.bankinhausanovels.com.ng Kasar ka na nufin kake samun wannan makudan kudin?”Salmanu da Tanimu suka dorawa Adamu ido suna jiran ganin yadda zai yi da wannan gizagon na Alhaji. Amma ga mamamkinsu sai suka ga Adamu yayi fuska yace, “Amma dai na fada maka ina hadawa da harka saida gidaje.Au ai na zaci kai ne Ministry of works and Housing”. . _ Inji Alhaji cikin muguwar Kufula. . ‘Adamu yayi Kasa da kai cikin tasa Kufular. Alhaji yace, “Ko baka ji bane?” Adamu ya sake yin fuska, ~ . , “Ni ba ni da ta cewa Haushi ke ta shake Alhaji, amma dai ya matse ya bar kansa cikin tunani da lissafi, har dai daga. Karshe yace, rf “Babu laifi, ku ajiye kudin zan bawa Sa’ar, saita hada mata da na Salma wadda har yanzu Shagon ke ciyar da ita ya shayar kai kana can ‘yawon gantalinka babu wanda ya san duniyar da kake_ Buya… Adamu ya muskuta cikin Kuncin da ya saba tafiyar da Alhaji yace . “Ni Www.bankinhausanovels.com.ng bata taba sanar da ni cewa bata Koshi ba ma’ana shagon ba ya Kosar da ita.. – “Magana zaka fada min kenan?”. Adamu ya cigaba da cije-cije “Kawai ni dan ba ni da gata sai ayi ta yimi ‘gori, ni wallahi sai na Kirga abinda naci a shago nan amma kullum kowa da kowa dangi sai ya kwaso gori ya afka a kaina, an min aure an min shago, Kila wataran ma na sami me cewa rayuwar tawa shi ya dorar da ita…Sai Alhaji ya rasa ma abinda zai ce, don tsakani da Allah ya zaci da gaske dangin na yi masa — gorin, don haka shi ya ji takaicin kansa na gorin da — yayi masa wanda bai taso dalilin Kiba Ya kada kai kawai cikin basarwa ya ceKai matsalarka mayar da bamo dawaki – Adamu, ni ba na son janjanin magana, ku kawo . kudin ku tashi sannan in da hali ko dan yaya ne ka bawa ita Salma a dan, siyo mata wani abun, duk hanyar samar da zaman lafiyane” Adamu ya dubi Salmanu da inkiyar ya bayar da kudi, amma sai Salmanu yayi fuska ya sake rusuna murya yana bayani,Eh to, sai dai gobe mu kawo” Alhaji ya ce,
“Allah ya kai mu, kai Adamu ka kawo min akan kari, dama ina son ganawa da kai”.Suna fitowa waje Adamu ya dunkule hannu ya kai wa Salmanu naushi, Ka ga zaka janyo min matsala ko? Da ka bashi kudin ina zai gan ni goben bare har ya wani gana da ni.. Salmanu ya tare shi, Kai banza ne, yaushe zamu ba kura ajiyar nama, Sa’ar zamu dauki kudinmu mu bawa?, Kana ji. ma ana wata maganar mu bayar da na wata Salma” Adamu yayi shiru sai Tanimu ne ya shiga maganar, “Amma jiya dana cewa’Salma kunduba ai haushina kaji Salmanu, gashi yanzu kai da kanka kake fadar aibunta“Zaka fara ko Tanimu?”. inji Salmanu, Tanimu yayi saurin basarwa yana shafa kai yana kallon Adamu wanda ya ke dan nuna alamar Www.bankinhausanovels.com.ng muzanta, yace “Tonayi shiru”.Adamu ya kori tsarguwar zuciyarsa yace “In ba mu bata ba menene mafitar?” Kai tsaye Salmanu ya amsa, “Muje mu kai wa Husna kudin-nan, ai naga . -ana hakan ma”A sanyaye Tanimu da Adamu suka ce, Kana ganin babu matsala Salmanu?” “To sau nawa ana’hakan, ba mu da mafita bayan wannan in ba so.muke mu bawa Sa’a ta siyo”. mana kaya mara kyau ba, ko. ma kai tsaye in ta siyo. ta kai wa munafukin bokanta ya tsafe mana kayan” + ‘Hujjarsa‘ta Karshe ita ta nutsar da Adamu ya ga babu mafitar da ta fi zuwa a kai wa Husna kudin kayan lefenta. Saboda haka yayi na’am suka je suka kai mata dubu dari biyu da hamsin cif, ta rasa inda zata sa kanta don dadi sannan suka yi mata bankwana.
************
Ba Karamin rudu Sa’a ta shiga ba da ta ji maganar lefen Adamu da kuma adadin kudin da zai_bayar asai masa kayan lefen, kamar ta janyo safiya – don ta yi waya da Salma ko kuma ta ga Adamu yayi sallama ya kawo wannan kudin, ta ci alwashin sai abinda ya gani, ai dai ba zai kwada ta yaci ba, wallahi biyu zata raba kudi ta yo siyayyar da Salma. . Kwana ta yi tana faman yi wa Alhaji mita, Amma dai shi kuwa Adamu yana samun ‘wannan kudin amma zamansa’da .Salma_ ko dankunne bai taba sai mata ba bayan wanda ka sai mata?” Alhaji dai sai yayi shiru, wani karon kuma ya ce mata, . “In dai ya zo kar ki yi masa maganar, don na fahimci yana dan jin zafin kai, sannan ni kaina nace masa ya zo da dan wani abu na farantawa da zai bayar a yo wa ita ma Salma tata siyayyar”. Har Sa’a ta yi shiru sai kuma ta cigaba da mitarta da masifarta, lallai Adamu na shiga hakKin Salma, in dai yana da irin wannan kudin da zaiyyi
irin wannan auren ita yake barinta da cin -taliya da kifin gwagwanin shago hade da barbade madara… Alhaji ya sake gajiya da jarabar tata ya sake tare ta, “Wai ke Sa’a ba ma kya zama lissafin inda yaron nan ke samo kudi? Ni hankalina a tashe yake, — gara kullum safiya Adamu ya zo yayi Sallama na bashi abin kashewa ko kuma ita Salman in yi ta -samun labarin garin rogo kullum yake jika mata tana sha da suga, da dai na gan shi da maKudan kudaden . da ban san daga inda yake samo su ba, ni wannan ne tashin hankalin da yake neman zuba min zazza6i tun jiya’. – Wannan maganar tasa ta sanya jikinta sanyi, ta yi shiru dai ba don ta saduda ba, don ita a wajenta ko dai kudin jini yake samowa in ya ba Salma ita halak zata ci, shine da zunubinsa, saboda haka bata ga kyan wuri a kunne ba da zai dinga mayar da Husna sarauniyar duniya Salma ya
**************
Sai Karfe sha daya Adamu ya shigo gidan da Shirin ko ta kwana a fuskarsa.. Kowa ya lura da yadda yake gintsewa. Sa’a ta dinga kallonsa bacin ransa nayi mata wani irin tururi a Kirji, shi dai ya fiye taurin Www.bankinhausanovels.com.ng kai, asirin suke masa amma kadan ke bi ta kansa sai ma Kara habakar gagarar mutane da yake Ta nace sai da ta shiga ganawar tasa da dan uwansa, abinda ya sanya shi Kara kullatarta kenan. “Ina kudin?” Alhaji ya fara da tambayarsa. Dama tuni ya gama atisayensa na yadda zai yi maganar kudin, kansa tsaye babu alamun shakku ya amsa da cewa, .
Jiya muka yi waya da ita Husnan tace tafi — son na kai mata kudin ta siyo da kanta, shine yanzu da zan taho na biya na bata kudinta’ Sa’a ta dafe Kirji tamkar ya yanki naman. jikinta, tace“Ka kai mata kudin fa kace Adamu?”, – Ya kalle ta da kyau cikin-cin magani ya amsa,. oko akwai wata matsalar ne?” Ta kasa sarrafa kanta saboda tsabar rudewa, “Kayi hauka ne Adamu, kuma nawa ka kai . mata?”Ya amsa a gajarce, -“Dari biyu da hamsin”“Inna lillahi wainna ilaihiraji’’un”In ji Sa’a, dole duk suka tsaya suna kallonta, shi kansa Alhaji bai ga dalilin wannan hayakin kan nata ba, to ma wai me ya shafeta?. “Ka yi ganganci Adamu, yaya za’a yi ka wani kai mata kudin, budurwa ai allura cikin ruwa ce, in Allah bai yi da kai ba ta ina kake tunanin kudin zasu fito?”
Wannan maganar tata ta fi batawa Adamu rai, amma dai ya nuna jarumta inda ya kawar da kai’ cikin basarwa yace mata, .
“Baki sani ba Sa’a, Husna ko wani zata aura ba ni ba zan iya kai mata abinda ya fi haka cikin ruwan sanyi a matsayin gudunmowa, sannan ko ba ta aure ni ba zan iya mallaka mata duk abinda nake da shi, wanda bai sani ba ya sani na shiga neman kudi ne saboda ita, kuma duk abinda na samo saboda ita,natane Www.bankinhausanovels.com.ng
Sa’a ta kame kai saboda kan nata na juyawa ta rasa bakin magana,Alhaji kuma kallon Adamu kawai yake nasa hankalin na can tunanin inda Adamu yaje nemo kudi saboda mace. Da Kyar ta sa wa numfashinta Karfi ya bata — damar furuci, To shikenan, bayar da kudin Salman” Yayi fuska yace, ‘“Zan duba”Ta yi sukuki tana kallonsa tamkar ta tashi ta shake shi, Alhaji na lura da haka amma dai bai tanka ba, sai da falon yayi tsit.sannan ya sami damar magana, “To shikenan, ko ma dai meye mu ba kudin ko lefen ne a gabanmu ba, Allah ya sanya wa iyalin
da auren albarka”Wannan karon har cikin zuciyar Adamu ya amsa da, “Amin” Sa’a kuwa ta nuna wutar ciki ta Ki amsawa, Alhaji bai damu ba ya gyara zama ya sako maganar da ta dame shi“Akwai wani fili da na-siya a nan Tudurr Yola, shi ne nake neman ko kai da abokan aikinka za ku je yi min gininsa?”Bayan Alhaji yayi maganar. sai da ya dorawa Adamu ido don ganin yanayinsa, dama tarko ne ya dana masa don ya sami kama shi. Kan Adamu na Kasa, dama kuma tuni ya shiryawa iri-iren wannan Kalubalcn na Alhaji, babu abinda bai saKa ya warwarce ba don haka sai bai basa wuyar amsa masaba.. Nayi.maka murna Alhaji, sai dai an sami akasi, yanzu ba mu cika aiki a nan ba, mun fara fita Kasashen waje yin aiki, kwanan nan ma zanje Saudiyya, amma idan mun dawo za’a duba yadda zaayi.
Sa’a ta bude baki, Alhaji kuma yaji wani dunKulallen abu ya taso masa yana neman ‘sa shi _ amai, da gaske kenan zaton da yake wa Adamu na wata haramtacciyar sana’a ya tabbata, gashi ba kunya ba tsoron Allah yana neman ninke shi baibai.
“Aikin ginin zaka je Saudiyya duk maginan duniyar nan”.Adamu yayi fuska ya kada kai‘‘Saudiyya dai wadda na sani me dakin Allah Adamu?”’. Inji Sa’a. Adamu ya bata rai, – _ “Eh ita”.
Alhaji ya kai Kololuwa a razana da lamarin Adamu, don haka yayi tsai da zuciyarsa yana nema ta sigar da zai tare shi.. Ya yardar wa kansa hargaginsa da tashin hankalinsa ba zai taba samo’masa Adamu ba, don haka ya bullo da sigar rarrashi tamkar zai fashe masa da kuka, “Adamu ka fada min gaskiya, tsakaninka da Allah wacce sana’a kake?”. ; a Adamu yayi dum! Alhaji ya bashi tausayi bare ya yi masa gatsali, don haka a sanyaye ya daga kai ya dube shi, Alhaji ba ka yarda da ni bane? me kake zargina da shi?” Alhaji ya dan muttsuke kwallar da ta taru masa a ido, ya shiga girgiza kai ba tare da tankawa
ba. Sa’a ta fara mamaki da jin haushin dalilin Www.bankinhausanovels.com.ng
damuwar Alhaji, amma Adamu zahiri ya shiga taitayinsa, ya san damuwar Alhaji ta taso ne daga –
Kokkolin zuciya ta dalilin shakikiyar Kauna, shima sai yaji hawayen na son kubce masa, da kyar ya maze cikin raunin murya yace “Ka kwantar da hankalinka, ni babu. abin tsiyar.da nake”. Sa masa. ido kawai Alhaji yayi tsawon lokaci, . gannan daga bisani yayi murmushin yaKe ya nuna_ – masa Kofa, “Ba komai Allah ya tsare, tashi kaje. Salin alin ya tashi ko sallama bai musu ba ya fice, aka bar Sa’a da cizon yatsar ba a bata damar ta – nemi hakkin Salma na kayan fadar kishiya ba Bata iya hadiyewa ba sai da ta ajiyewa Alhaji magana, “Kai kake shagwaba Adamu wallahi, duk abin tsiya idan yayi baka gani, amma dai ai Salma marainiya ce bai kamata kana gani ya dinga danne hakKinta ba”Haushi ya cika Alhaji, amma ba halin ya yi_ fada, muryarsa a sanyaye yace’“To wai duka kike jiran kiga na tashi nasa — masa Sa’a?“ “Amma dai ai inka takura masa dole zai yi, kawai kayi shiru da zarar ya dasa maka baKar . Magana… Ya tare ta ya mike tsaye yana karkade riga Nar zai ficc ya bar mata pidan,
~~ “Qh na fahimee ki, so kike ki ga shi ya dakc ni tunda dai kin san ai daga baKar magana sai duka ya rage…” Yana dab da ficcwa ta daga murya, “Au ni shi nc ka gasa min baKar maganar?”, Bai sake cc mata komai ba ya fice. Ita kuma bata yi Kasa a gwiwa ba ta janyo waya ta shiga kiran Salma. SKECKKEKEKERKER . . Tun daga wa’azin tsakar dare da Adamu yayi wa Salma ta zama cikin rashin sukuni da tashin ‘ hankali, ta dai zaro jikakken goronta na fitsari ta ~ shaya a rana, zuciyarta cikin Kila wa Kalancin yin @ maganin ko barinsa, duk da dai son Adamu ya cigaba da ninKaya a doron zuciyarta yana ta shardanta mata abubuwa marasa dadi da zata dinga gamuwa da su. matuKar a zamanta da Adamu ta guji ‘sthirin. bokanta. Ba ta yaudari kanta ba tana da tabbacin wa’azin Adamu ba zai hana shi Ketare dokar Allah shi ya ci zalinta ba. Tun tum ta san Adamu malami ne mai kai kuka ga Allah, amma Karfin imaninsa bai kai matakin hana shi sabo ba, sannan ko yana cikin sabo in ya ga mai irinsa yana iya toshe kunya yayi masa wa’azi. . Tana ta harkokinta a cikin gida cikin sanyin – jiki har lokacin da ta dora girki.sai ga kiran Sa’a a
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG