NAGA RAYUWA COMPLETE

 NAGA RAYUWA COMPLETE

Yau ma kamar  Kullum muna xaune Ni da mahaifiyata a Cikin wata rumfa a kasuwa  yara sun baebaye mu suna ihu suna kiran 'ga kande mahaukaciya! Yar macukule', mahaifiyata ita ko sae xare ido take tana muxurae Ni kuwa in banda hawaye Ba abinda ke sintiri a fuskata, Inda sabo Na saba da irin rayuwa da muka tsinci kanmu ni da mahaifiyata.

Hannun ta Na kama ina hawaye nace 'inni taso mubar wurin nan kar yarannan su illata mu' ita kuwa tana ta tauna wata leda ko kallona batae ba sae gatsine2 take abinta, sae magana nake amma ina! taunar ta kawae take yi, hannu nasa da niyar cire ledar dake bakinta, ae kuwa caraf ta damqe hannuna 'ke wallahi xanci uwaki hehe😁,ke harma da ubanki, Yar iska! Kinsan albarkar dake jikin ledar nan kuwa , to dan ubanki itace babanki' nan kuma tasa shewa 'ye ubanki,sae kuma ta fito da ledar daga bakinta 'tasa dariya, kae wannan Leda ta iya haihuwa, sae kuma ta dubeni 'ke wae ke wace kike ta bina nace bana yi ko dole ne , ta nuna ledar hannunta, 'af toooww kice masoyina xaki qwace min to qwalelenki' kukana ya kuma qaruwa, da kyar Na lallashe ta muka bar wurin, Na tattare yan tsummokaran mu, muka tafi yaran suna binmu suna ihu mahaifiyata tana ta xunduma musu ashar!. Abin takaici ba me tsawatar wa.

Mun yi tafiya me nisa Inda muka sami wata bishiya dan mu huta, muna nan xaune har kusan  sallar magriba, muna nan a xaune  tana ta shirmenta, ni kam dae2 da rana daya ban taba Dana sanin kasancewarta mahaifiya ta ba, gyangyadi naga tana yi Na hada yan tsummokaran mu Na mata filo Na kwantar da ita, tashi nae Na shiga cikin anguwa dan yi baran abinda xamu ci.

Na Dade ina yawo gidaje ban sami komae ba sae can Na hango wata me tuyar qosae a bakin titi, da sauri Na nufi wurin ina xuwa Na tarar ga mutane masu siya nae sallama, amma cikinsu ba Wanda ya kalleni a xaton su ko mahaukaciya ce dan shigata kadae ta isa nuna hakan! Na qara yin sallama a karo Na biu, wani daga cikin masu siyan qosan ne Ya juyo ya dubeni ae kuwa ya buga wani uban tsaki 'ke dalla bar wurin nan sae kin sawa mutane datti, qaxama se wari kike ki wani xo kina maqe murya, wae ke a dole abar tausayi, gaba daya mutanen dake wurin suka sa dariya'.

Haka Na juya Na tafi ina ta yawo ba tare da Na samu abincin da xamu sa a cikin mu ni da mahaifiyata, Dana gaji da yawo Na yanke shawarar komawa Na ga halinda mahaifiyata ke ciki idan yaso daga baya Na sake fitowa nemar mana abinda xamu ci.

Ina tafe ina tunanin rayuwa yanda take juyi damu har Na iso Inda nabar mahaifiyata, tunanina ya tsaya cak! Sakamakon ganin da nae bata nan, hankali Na ya tashi Na Shiga nemanta duk inda nasan muna xuwa amma ban ganta ba,har bayan sallar isha ina yawon nemanta, haka Na haqura Na koma rumfa cikin kasuwa dama a can Muke kwana, kae Na hada da gwiwa Na fara xubar da xaxxafan hawaye, tashi nae Na fita saga cikin kasuwar duk Wanda Na gani sae Na kwatanta mishi mahaifiyata ina tambayar ko ya ganta amma  Kowa da Na doshe shi sae ya koreni😔.
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *