NAKASA BA KASAWA BACE COMPLETE BY AYSHA ALIYU GARKUWA

 NAKASA BA KASAWA BACE COMPLETE BY AYSHA ALIYU GARKUWA  

BISMILLAHI ina farawa da sunan Allah mai yawan rahma da jink’ai.  Alhamdulillahi na godewa Allah mahaliccina daya bani rai da lfy da nitsuwa, da konciyar hankali ya kuma ƙaramin ya buɗa min tunani na ya haskamin nazarina har na samu daman fara wannan sabon littafi nawa mai suna NAKASA BA KASAWA BACE ya Allah ina riƙonka da ka tsare min Al’ƙalami na daga rubuta sharri da abinda zai zamewa bayinka guba ko fitina, ya rabbil izzati ka tsarkake min tunani na ka kame min hannu na daga rubuta wani abinda zai zame min da-na-sa-ni duk ƙanƙantarshi, ya Allah ka bani rai da lfyar gama littafin nan lfy-lfy,  dani da masu karatun baki ɗaya*

_Wannan shafin forkon nakine ƙanwata kuma mai babban suna Fatima Sardauna, ina tayaki farin cikin gama  littafinki SOORAJ  lafiya, Allah ƙaro miki basira da hazaƙa, Allah ya bada ladan faɗakarwa_

Nakasarsa bata zama kasawa a gareshi, domin hausawa kance Babu nakasasshe sai kasasshe!

ya kasamce mai zarrar da ko lafiyayye marar nakasa bashi da irinta, Rayuwarshi madubine ga dukkan nakasassu, kana abar birgawace ga dukkan lafiyayyu kana abin so da sha’awar ko wanne bawa mai imani a zuciyarshi yadda sunanshi yake haka zahirinshi da bad’irinshi yake *SAIFUDDEEN* Muhammad Ahmadu  managarci ne salihi mai yawan fasaha da tawakkali kekyawane irin ken da ke tsantsar haiba.

Ɓiggiren tushe da asalinsu Saifuddeen.

Asalin su FULANIN DUKKU NE NA JIHAR GOMBE.

*DUKKU* wani yankine daga yankunan Gombe wanda ya kasance yankin fulanine masu tsananin kyau uwa uba fulanine masu fafutukar neman ilimi na bankƙare biyu duka wato ilimin Arabic da kuma Boko.

 Al’ummar Dukku sunyi fice da zarra tako wanna sashin shiyasa, suke ko ina cikin mutane masu daraja masu kima da cikar kamala.

*DUKKU diyam sad’i na kosam*

Malam Ahmadu shine kaka gasu Saifuddeen,

 Malamu Ahmadu asalin bafullatanin Dukku ne gaba da baya, 

nannen tushensa iyaye da kakanni, 

babban Malami da babu kamarshi a fad’in Dukku a waccan lokacin.

 Mafi akasari yaran garin a gunshi suke karatu, dan yanada tsankgaya mai girma , sai dai shi baya tara al’majirai, kowa yazo yayi  karatu kana in an tashi kowa ya koma gida, 

shiyasa yaran anguwannin nesama suke zuwa karatu, kamar yaran Sirinkiyo, Katafila,  Fada, da nan Dugge, kai wasu daga shabewa ma suna zuwa makarantar, wanna yasa ya shahara a cikin Dukku domin masarautar Dukku da kanta tanaji dashi, domin shine limamin masallacin fada. 

Allah ya azirta shi da kadararorin filayen cikin garin Dukku da tarin gonaki wanda yawan cinsu ya gajesu ne a wurin mahaifinshi wanda sune suka sari dajuka da tsaunikan  Dukku da kewaye kasan cewar wancan lokacin ba’a saida gonaki saida ka shiga daji ka sari fili ka gyarashi shike nan ya zama naka wahalakar ya mallaka maka shi. 

Malam Ahmadu yanada matarsa d’aya  mai suna Bintu Allah ya azurtasu  da yara uku.

Babban d’ansu sunanshi Muhammad Bella shine mahaifinsu Saifuddeen,  sai mai binshi Aliyu sai autarsu Aisha suna kiranta Dada.

Sun taso cikin had’in kai da tausayin juna, babu raini ko kad’an sai girmamawa da tausayawa. 

 Yayiwa  yaranshi maza aure.

Bello mahaifinsu Saifuddeen kenan mutun ne mai mutunci da kamala yanada nitsuwa shiyasa aka had’ashi aure da d’iyar goggonshi mai suna Fatima amman ana kiranta da Bisije, yaranta ku su Saifuddeen suna kiranta  Ummi.

Ummi kenan, wacce mahaifiyarta k’anwar Malam Ahmadu ne, Ummi marainiyace dan rana d’aya ta rasa iyayenta saka makon gobara da ya cisu dere d’aya, ita kuma lokacin an kaita yaye gidan kakunsu, shiyasa ta tsira, ba nisa tsakaninmu kakanin nasu suka rasu, shiyasa rik’onta ya dawo gidan Malam Ahmadun kawunta kenan.

Bello ya rayu da matsalar makarai tattare dashi, 

wanda yakan tashi time to time yana matuk’ar wahal dashi shiyasa, 

iyayenshi suka zab’i a had’ashi da Bisije Ummin kenan anaga tunda yar uwarshi ce zatayi hak’urin zama dashi, 

bayan an gama yin komai  na buk’atun hidimar aure, 

sannan akayi auren Bisije da Bello, 

anyi biki lfy an watse lfy. 

Ranar da aka watse abokan Bello na shirin rekoshi gidanshi inda yayi gina cikin asalin family house in nasu.

kawai sai suka sameshi ya toni rami mai zurfi kana ya had’a k’irarai ya shirga itatuwa ya hura wuta, 

wai zai fad’a ciki, 

nan abokanshi Ashiru da Hamisu sukayi kanshi da gudu suka kamashi, sai fizgewa yakeyi wai su barshi zai fad’a cikin wutar yana me ce musu. 

Wai a k’asan wutan al’jannace su barshi ya fad’a ciki.

Wannan abu ya tada hankali yan uwa da abokan arzi a daren ranar dole Hamisu da Ashiru,

a gidanshi suka kwana don in an barshin zai kashe kansa, sabida makaranshi ne suka motso, k’aninshi Aliyu da Dada kuwa sai rarrashin Amarya suke,

wacce taketa kuka. 

To mafarin bak’in cikin Ummi kenan tun randa aka watse bikinta ta fara shiga toskun rayuwa sabida, 

daga ranar duk bayan wata biyar sai cutar Bello ta tashi wani lokacinma yakan tashi sau uku a shekara, sai dai Alhamdulillahi abun baya sashi duka ko fad’a sai dai yakan tashi tsakiyar dare yayita  yawo yana zagaye cikin garin Dukku, 

kana duk inda ya samu masallaci sai ya tsaya yayi sallah raka’a biyu. 

Sannan yana tafiya yana karatun qura’an da k’arfi.

 Kafin gari ya waye sai muryarshi ta disashe, kana sawunshi su kumbura.

Mahaifinshi Malam Ahmadu dama yan uwanshi kab suna nema mishi mgn amman Allah baisa anyi dace ba. 

Haka shekaru sukayi taja Ummi tana ta hak’uri da d’an uwanta mijinta, koda kawunta yayi yunk’urin raba auren sai tayi ta kuka tace ita kam a barta dashi, acewarta in ita ma ‘yar uwarshi ta gujeshi wa zai zauna dashi, dole Malam Ahmadu ya barsu yana mai ci gaba da yiwa d’anshin addu’ar samun lfy.

Har tsawon shekaru da dama, 

inda Allah ya azurtasu da yara shida uku maza uku mata. 

Nuruddeen shine babba sai Rahma, kana Saifuddeen sannan Raihana sai Raliyya sannan Auta Hayatuddeen sakalin Ummi da Hamma Saifuddeen. 

k’anin Bello Kuma Aliyu har yau matarsa bata tab’a koda b’ariba.

su Nuruddeen na kiranshi Bappa Ali, kana Dada ma tayi aure suna kiranta Goggo Dada.

Ita kuma tunda tayi haihuwar fari bata kumaba, Ahmad shine sunan d’an nata kuma sa’an Saifuddeen ne.

Ana cikin haka ne kuma Allah yayiwa Malam Ahmadu rasuwa. 

mahaifinsu  Abba kenan daga ranar kula da d’aliban ya dawo hannun bappa Ali, da kuma Abban in yana cikin haiyacinshi. 

kafin bintu ta fita takaba ne itama Allah ya mata rasuwa sakamakon cutar murd’a na dare d’aya.

Daga nan Abba da bappa Ali da goggo Dada suka k’ara ruggume juna bisa amana da gsky da tausayawa d’an uwan nasu.

Yara kuwa sun fara girma ciwon mahaifinsu na ci musu tuwo a kwarya musamman Nuruddeen da Raihana sai Saifuddeen wanda a lokacin yakeda shekara goma sha uku kana ya gama primary school inshi, har  yaci gaba da secondary school inda yake JSS 1

shi kuwa Nurruddeen tuni yayi nisa yana Ss 3 Raihana Ss 2 da yake tsakaninsu da Saifuddeen akwai ‘yar tazara,

a gefen Arabic kuwa tun sunada shekara goma sha bbbiyu sukayin sauk’an alƙur’an mai girma.

So tuni Saifuddeen ya sauk’e Qur’an tun shekarar data gabata lokacin kanninsu na raye dan yanada 12 years yayi sauk’a kamar sauran yayunshi  tuni  ya meda hankalin kan hadda da sauran littafai da ake musu a isilamiyarsu. 

Saifuddeen yana ta murnar zai tafi JSS two wata rana kwatsam ya tashi da wani irin azabebben zazzabi mai tsananin zafi, 

kwana yayi yana firgita, 

da safe kuwa yana tashi sai mura ba tari amman  yanzu yanzu hancinshi na zubda ruwa kana hancin yayi jazazir hakama idanunshi, 

ganin haka Ummi ta kama hannunshi taje ta nunawa wata makociyarsu tsohuwa iya shatu kakar Salisu abokin Saifuddeen, 

tana nuna mata jikin Saifuddeen d’in.

 Tana gani tace k’end’ace bak’on daurane zata fito mishi ga kuma azabebben zazzab’in sank’arau daya rufeshi,

haka yasa ta nemi tsink’aro da gero ta barzasu ta jik’ashi da ruwa sannan ta kurba sai ta fesa mishi a jikinshi, 

cikin ikon Allah kafin dare duk Sun feso sun fito birjink a jikinshi har cikin tafin k’afafunshi zazzabin sank’arau kuma tamkar zai hallakashi.

Koda dare yayi Ummi ta d’aukeshi suka koma side inta, 

abu kamar mafarki koda gari ya waye sai aka samu jikin Saifuddeen yayi sumut duk bak’on dauran nan ya b’ace ya koma cikin jikinshi ya k’ume yaro sai karkarwa yakeyi dan zafin zazzabi ga kuma sank’arau da ya hanashi sukuni wanda har cikin kunnenshi yakeji yana bada sautin dummmm, 

ba irin mgnanin da ba’a bashi amman sunk’i su kuma fitowa a lokacin kuma ba’a wani damu da batun asibitiba ko riga kafinshi ba’a fiye yiba a garin. 

haka dai Saifuddeen yayi ta shan wahalar sheretuwannan da zazzafan zazzab’in sank’arau  daga k’arshe yayi sanadin kuram tashi.

Wannan al’amari ba k’aramin girgiza family ensu yayiba don Saifuddeen yarone mai shiga rai, gashi da nitsuwa da al’kunya 

iyaye da da ‘yam suna matuk’ar sonshi ran da aka gane Saifuddeen ya zama kurma a ranar anga tashin hankalin Bello Abba kenan hakama Nuruddeen daya dawo makaranta aka gaya mishi, kuka yayi tayi dan duk k’annenshi yafi k’aunar Saifuddeen Hayatuddeen kuwa lokacin shekaranshi 4 so baisan meke faruwa ba

yakan dai yi kuka in yaga suna kuka.

A Daren ranar jikin Abba ya tashi a wannan ranar ne karo na forko da ya rink’a ihu tamkar yaro k’arami.

K’arfe biyu dai-dai na dere  ya kama hannun Saifuddeen dake bacci ya mik’ar dashi, kana ya jashi suka fito haka ya rink’a janshi koro-koro duk inda suka samu masallaci sai ya sashi suyi Al’wala suyi nafila raka biyu kana suci gaba da tafiya. 

Saida akayi sallan asuba sannan suka dawo gida, nanma dan yaga Saifuddeen  d’in yanata kuka. 

Suna dawowa Ummi ta jawo d’anta ta ruggumeshi cikin kuka take tambayarshi ina sukaje, 

baki ya bud’e da nufin ya kuma gwada yin mgna amman ina ya kasa, hakan ya sashi kife kanshi jikin gini yana wani irin gurnanin azabebben kukan da duk mai imani sai ya tausaya mishi babu mai sanin zafi da kun’an da yakeji a ranshi sai wanda ya tab’a shiga irin wannan halin ace an haifeka lfy ranatsaka nakasa ta sameka, so yake ya bud’i baki ya yiwa Umminshi bayanin yadda yakeji amman ina Allah bai bashi damar hakanba ganin ya kuma kife kanshi jikin ginin ya sake zazzafan shesshek’an kukane yasa Yayanshi mik’ewa ya nufi inda yake.

Da Sauri Nuruddeen ya kamoshi,

 hannu yasa ya tallabe kanshi cikin tsananin kuka da tausayawa k’anin nashi murya na rawa yace.

“Saifuddeen…!!! 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *