NAMIJIN KISHI CHAPTER B KARSHE BY Taku Firdausi S Ahmad JannahJay
Www.bankinhausanovels.com.ng
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
26
Narkewa Jamila take sai tashen shagwaba ake, an zama masu ciki tun a asibiti fallinta ya tashi, suna zuwa gida ta d’au wayarta tafara fesawa mutane ba ko kunya, shikuwa sai murmushi yake, furar ma shi ya had’a masu sai yatsina take, ita lallai game ciki k’arnin nonon ne yake neman damunta…
Sai da tasami kwana biyu sannan takoma kan aikinta, baiyi k’ok’arin hanata ba don hawan jinin ya d’aga masa hankali, bai k’ara shiga fargaba ba sai da yaje gidansu yaji Mama nata nanata masa rike amanar matar tasa, sai yake ji kaman tasan komi abunka da mara gaskiya, daya dawo gida ranar sai ya tsiri magana akan sirri ga Khairi, ita da bata d’ago komi aranta ba sai ta biyeshi suke tattaunawa akan abun, tunda ita tasan bata tab’a fadawa kowa ba, iyakar kiyayewa Khairi tanayi don ganin wani abu bai k’ara gittawa ba, saboda haka suka koma rayuwarsu normal, abangaren Adam sai da Sabir yayi mashi hannunka mai sanda akan kishi sa don ranar da rashin lafiyarta ta faru sai da ya gano akwai wata ak’asa gashi dama sun san halinshi kafin auransu, sai yakeji kaman ba’a mashi adalcine sam bazasu gane son da yake matane yasa yake jin gara ya killaceta ba, ji yake kaman don shi akayita dariya ko akasuwa yaga tayi da masu shago haushi yake ji, kuma sai ka gane hakan afuskarsa…+
DUTSE
Sunje ziyara gidan iyayensa tunda sukaje k’anwarshi ta kawo masu drinks da abinci, take yatsina kuma azahiri cikinta bai zomata da wannan fi’ilinba, tana hakanne don ta tabbatarwa da zuriyar Ahmad tana da juna biyune, sai da yasha cup d’aya na kunun Ayar ya kalleta ” Sweety yanaga kin k’i shan komi?” shagwabe fuska tayi “Nasan in nasha amai zanyi, ne dama zobone haka mai d’an tsami” Naja’atu ya kira yace “Akwai zobo agidan nan?” tace “Eh akwai amma sai na duba can store don kwana biyu mun rage shansa agidannan” yace ” Jeki ki nemo ki hadama antynki, gatanan ki tambayeta yanda take so” fuska akebe na tab’ara tace “kisaka ginger sosai sai ki samin lemon tsamj kwaya d’aya, kuma kar asaka sugar ciki” murmushi tayi tace ” Shikenan anty yanzu kuwa zaki gani” bayan tafiyarta ne ya ware cikinshi yana aika tuwon fara shimkafa miyar egusi dayaji nama komi zam-zam, tanaso taci don d’aya daga cikin abinda takeso agidansu Ahmad kenan, amma sai tak’i motsi, ya kalleta yace “Kinsan anan zamu yini naga baki da niyyar cin abincin kuma naga favorite dinki ne” lokacin ne mahaifiyarss ta shigo ” A’a Jamila ya haka naga baki cin abincin? Ko bakison shine asama maki wani?” wani irin farin cikine ya kamata abunda take nema yasamu, sai ta sunkuyar da kanta kaman kunya tana A’a bahaka bane ba, nan ta k’walawa Naja kira lojacin tana shirin kawo zobon ne tace ” Ga antynki nan inaga bazata iya cin tuwonba, ki tambayeta ya takeso kimata banda shiririta kuma” ta fita tace aranta kunya taji shiyasa baza iya fada min ba, batasan har ya sanar minba, Allah dai ya inganta, ranar dai yinin su Jamila haka Naja’atu tasha jigila da ita.Sai da suka koma gida kawai 9 d’in dare tace sai ya karbo mata tuwon nan wai yanzu shi take buk’atar ci, shikuwa da baisan dabar garin ba sai ya tafi yana dariyar abun, don abokansa sunsha fad’a masa mata kanyi haka in suna da ciki, kuma ba laifinsu bane haka yake zuwa musu in ba’a samuba matsala ne, sanda ya shiga gidansu so yayi ya shiga kitchen ba tare da kowa yaganshiba ya duba in da akwai ya deba mata, don yana jin kunya Umma taji yayi ciki har ana zaben abinci, yaci sa’a har ya shiga kitchen d’in ba wanda yaganshi don ba kowa afalon gidan, sai dai to his suprise tana kitchen d’in duk da yawanci kannansa sunfiyin aiki, turus yayi kana kallonsa kaga mara gaskiya ” Tace mai sunan malam ya haka ka shigo da sand’a kamar wani barawo” shafa keyarsa ya fara yana inda-inda, juyawa tayi tacigaba da uzurinta dama tea ne take had’awa babansu tagama tayi ficewarta, tana fita ya fara bincike yaci sa’a akwai leda d’aya ya zuba mata aflask tare da miya ya fito, lokacin ta sake dawowa taganshi ta jijjiga kai, shikuwa yayi wuf ya fice, haka Jamila ta cigaba da fi’ilinta abu kad’an sai agantsare a cire mayafi azauna don kawai aga tafara girma, don cikinta ayanayinsa mai saurin fallasa ne…
STORY CONTINUES BELOW
“kai Khadija kodai ‘yan biyu zaki haifa mana? Wannan girma da kike” murmushi tayi ta ajiye mata tamarind juice tace ” Hmnn kin jiki da jan wahala ina ni ina yan biyu, ai bazan iya haifesuba d’ayane shima kuma k’arami” murmushi Khairi tayi tace “Aikuwa zaki iya haifar yan biyun, abunfa ba daga girmane ba” tabb ta furta tace ” Karkisa gabana ya fara fad’uwa mana, wallahi koya naji wata mata ta haihu sai na tambayeta ya taji” kyalkyalewa da dariya Khairi tayi tace ” Tab ashe kin gamu da aiki, kinsan kowa da kalar nak’udarshi, ki kwantar da hankalinki kawai” haka sukai ta hirarsu har yamma tayi Adam yazo d’aukarta, yana ganin yanayin fuskarta yasan tasami farin cikin da tadade bata samuba, sai dai ahanya tana nazarin magnar da Khadija tamata akan ramarta, batason yanda kowa ke tanka ramarta, abakin titi ya tsaya suka shiga wani Store zasu sayi shopping, anutse take d’aukar abubuwan da basu da shi cikin gidan, daga nesa ya hangota yana tare da k’anwarsa, sam hankalinta ya tafi ga spices da take dubawa, d’aga mata hannu yake amma da alama bata ganin, kallon k’anwar tasa yayi yace ina zuwa ya k’arasa ga Khairi ” Anty Ina yini? Ya jikinki?” ahankali ta juyo saurayin da ya bugetane rannan tace “Lafiya lou, kuma jiki tuni na warke” Yana tsaye daga farkon raw d’in yana kallonsu tace ” Kaga mijina can bari na k’arasa mu wuce” zuciya d’aya ya isa gareshi ya mik’a masa hannu, bakaramin kai zuciyarsa nesa yayiba ya amshi gaisuwar yace ” Naji dadi da naganka don in baka hakuri, tsautsayi yasa na bige matarka rannan” Yake yayi ” A’ah bakomi ya wuce ai” tana ganin suna magana ta ajiye ajiyar zuciya, saboda taga yanda da ya kule amma yanzu hirar da sukayi da saurayin ya wanke mata zargin, da yanda yagan sunnan ta karanci masifa afuskarsa, daga nan suka wuce gida, sai ya yaji tausayinta kan abunda yamata ranar, ita kuma ta nuna mishi ya wuce saboda haka kawai abunda takeso ya dinga kulawa da bincike kafin d’aukar mataki…
******* *******
Taje family house d’insu Adam ana ta shirin bikinsu Jidda da su Abdul, Jidda barene ita kuma Salma Khalifa zata aura don haka bikin ke musu dadi, cikinta daya girma kuwa har yafara fitowa don yanzu yakai 6 month harda dori, mai fulawa ce ke faman yiwa ‘yan mata, sanin halin Adam Khairi tace sai bayan biki sai amata saboda mijinta, kuma dama yawanci in tayi lalle in zata office da white handsocks take tafiya, yace baiga dalilin da zaisa wani ya kalle mata lalle ba bayan don shi akayi, amma haka su Jidda suka nace tabari ayi mata bakomi ai bayan biki week ne zai shiga kuma gata ma’aikaciya bata da time, shahada tayi tasa aka mata, akai mata shi yayi tas yayi maroon sannan bakinma dan kadan mai kyau aka yimata daga saman hannun, tad’an jima batayi lalle ba itama kanta hannun nata burgeta yake, lokacin la’asar ta kawo kai zata koma gida suka fito da yan matan, daidai lokacinne kuma su Abdul da Khalifa da wasuma haka kananun samari na danginsu suka iso wajan, suna tajansu da tsokana kallon hannayensu Khalifa yayi yace ” Kai Anty K gaskiya kunshinku yayi kyau sosai, kunyi ma angwaye wayo don na lura sai kunfimu kyau abikin nan” daidai lokacin Adam ya karaso, kuma yaji me yace ita kuwa Khairi tace ” A’a kaidai kawai kace Salma nata yayi kyau shine ka wayence, ka kwantar da hankalinka zaku hade gida in yaso kayita yabon nata” dariya Salma tayi tare da rufe idonta, shikuma yace ” La Anty ba haka bane bari ma na tafi tunda so ake ajuya maganar” tsaye yake kikam yayi folding hannunsa yana bin Khairi da kallo sai dariyarsu suke ” Ke! Ki sameni amota” ya nuna su Khalifa yace ” Da kukeson shewa da hira da yan mata sai ku jira Dinner ai ko” shiru sukai shiko Khalifa dake mai sanyi ne sai yake kunshe dariya Abdul kuwa haushi ya kamashi ba tun yau yalura Adam nason yi musu rashin M akan matarsa ba, yamutsa fuska Khairi tayi for d first time ta maida masa magana akan kishi tace “Haba yaya wane irin magana ce hakan kake akan wai in yanmata suke son shewa dasu, su din an musu shedar hakane?” bai kara magana ba yace ” To naji amma ke ba babba bace da zaki biye sauran yan matan amatsayinki na anty” turo bakinta gaba tayi tace ” Kajira naje na karbo masa sashen Kawu Bala” ta shiga bangarensu Abdul shikuma tuni yayi dakinsu na samari, jan tsaki Adam yayi ya wuce mota jiranta, su Salma kuwa suka komawa sashen kakar tasu sukayi, taga mood dinsu dai gashi nan tace ” A’a ya yanmata da haka, ni ba cewa kukai zakuje shago ba?” Salma ce ta bada labari harda na ranar da sukayi zuwa gaba dayansu gidan, dariya kakar tayi ta basu hakuri tace ” Dama haka kishin maza yake don dai shi wannan nasa yaso yin yawa, amma karku sashi kanku tunda kun san halin zai zo ya sameni”
Tun amota yake kunci ai yayi magana ta tankashi gabansu ta nuna bai isaba, itama kuwa yau bata shirya zama ya dametaba, suna hanya wayar Khadija ta shigo ta daga don son tura haushi sai shewa take tana tsokanarta, kure Radio yayi ta mata sallama ta k’ara maida kanta ga wayar ta fara buga Game, yasaba in taga yana ciccijewa take fama bashi hak’uri ko ta narke don ya sauko, amma wannan da suka je gida bayan magriba ta zuba masarta da miya taci ta mashi tayi yace baici, tace to ya fadi abunda yakeso yace baya jin yunwa, tace to shikenan, tayi shigewarta dakinta, da dare ta gama wankanta ta haye gado ta dora da Chat, shi duk jira yake tazo ta fara abunda ta saba na hakuri da lallashi yaji k’amas, haka yazo yayi wanka bayan yasha tea ya kwanta, bata nuna tasan ya shigo dakin ba, ya kashe bulb d’in, yayi minti goma akwance bacci bai d’aukeshiba, gashi gaskiya shariyar ta dameshi, ta gama chat ta kashe wayar ta ta ajiye ta kan bedside,Tana gama Addua ta shafe jikinta ta juya bayanta ta gyara duvet, ji yayi bazai iya kwana da haushintaba, ya matsa kusa da ita ya mata runguma kai karfi da sai da taji an kamata ta bud’e ido, sassauta rikon yayi tare da saka dayan hannunsa ya kunna side lamp yace ” Khairi me kike so ki koma ne wai, ace kin bagarar dani haka, kiyi laifi ki fini daukar zafi ko? ” asannu yake maganar ba fad’a ta dan yamutsa fuska tace ” Haba dai nike fushi kuma?” dungurum wasa yamata agoshi yace ” Kina acting as if bakisan me kikai ba, ni kike sharewa agidan nan ko? Har baki damu da naci abinci ba” yar dariya tayi ta duniyanci tace ” Ai kace bakasone nadauka ka koshine awaje, amma yanzu kana jin yunwa ne sai na sama maka abinda zaka ci” murmushi yayi ” Naji kedai ki huce don nasan da kina fushi da nine, don da bahaka kika saba yiminba, yanzu ina jin yunwa amma bata abinciba gaskiya” ta dago meyakeson yace amma sai tace “To wanne irin yunwace wannan bata abinciba? ” bai bata amsaba sai wani sak’o daya shiga aika mata, ta tsiri ture hannun shi ashagwabe shikuma yana lallabata da da wasa da da dariya suka gamsar da junansu, sai bayan sun fito awankane yake yaba hannunta, wai wallahi kaman ya tafi da hannu ya boye ya zama shi kadai zaike gani, kanta na kwance a kirjinshi bacci na dibarta yake fadar hakan, kawai murmushi tayi don Adam yayi nisa baya jin kira…
Gidan Jamila kuma sai abu ya fara tabarbarewa don yanzu motsi kadan ai ciki ya hanata son aiki, haka yake hakura in taga dama tayi girki ko kuma sai ta daidaici ya kusa dawowa sai ta sanar mashi awaya ya masu takeaway, ga gudun intercouse sai tace kar aje cikin ya fice, abun yashawa Ahmad kai….
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
27
Sati yafi biyu rabon da wani abu ta hadata dashi, iyakar bukatuwa yakai gashi at times sai kaga Students sunyi shigar banza, yar dauriyar da yake tanemi k’are masa, saboda shi ba mazinaci bane in ya dauko dakon bukatarsa ya kawowa Jamila ita gamai ciki sai ta tsiri ciwon baya ciwon kafa ciwon mara, haka zatayi ta lissafa masa su, yau da ya dawo ya samu abincin kan dinning shinkafa da miya ce da nama, duba fridge yayi yaga da cabbage da sauran vegetables, zama yayi ya yankasu fato- fato don bai saba ba, ya zauna ya ci abinci duk lokacin kuwa mai ciki tana kwance kan kujera wai bayanta ne ya rik’e, haka kawai taji sha’awar cin coleslow daya had’a, gashi dan kadan yayi don daidai shi yayi, tab’arewa tayi akan sai ya bata yace ” Bakisone shiyasa baki yankaba, yankan vegs ko akwance Wallahi kina iya yi, banson mai kike so kizamaba, kefa baki aman masu ciki kuma kina cin abinci so why the laziness? Haba” sai ta shiga ruwan hawaye ta shiga mitar baida tausayi ai kowa dakalar ciwon dayake experiencing during pregnancy, abunda bata saniba shine yanzu kwata-kwata yagaji da iya shegenta, da duk taurin kanta baya kaiwa sati bai samu hadin kantaba, jiki da jini da lafiyarsa kuma yana jin abinci mai kyau ace bazai ajiye bukatarshiba, yana tsaka da tunanin ne yakai hankalinshi ga floor na parlourn yaga tabbas ba shara, karo na hudu kenan bata shara, yanzu yakai bedroom shiyake gyarashi, amma wannan baya damunsa don dama yakamata yake tayata haushinsa dayane kawai rashin bashi hakkinsa, atleast ko wani abu da zaike sauke masa damuwane tayi, ranar haka ya kwana yana kunci in ta jashi da hira kan kayan babies sai ya kyaleta.+
KANO
Aranar da akai kamu haka Adam yakasa ya tsare 2 hours kawai tayi ya taso k’eyarta sai gida, dinner yace ta yan matace dole ta hak’ura sai bayan kai amare taje gidajen nasu, yasha kuwa mita daga dangi har kaka sai da ta wankeshi tace so yake ya rabata da mutane.
Yana zaune fuskarsa ba annuri ta fito da riga da zani na lace daya saya mata kwanaki kallonta yayi yace ” Gaskiya wannan ma baiyiba, ki sake” takoma ta dora mashi laffaya shima yace bai yarda ba,haka tasa kaya kala hudu karshe ta dauko Dubai abaya mai budewa da ta saya wajan Algazaru,tsarinta kaman za’ai bubu amma da different style sam bata kamataba, ta dora mayafinta, anan ne yaga tamasa gashi dama bata yi wani kwalliya sai dai tayi fresh tayi kyau, gashi tayi dumurmur saboda cikar da ciki yasata, ahaka yaje ya ajiyeta cikin Tahir guest palace nan ne taron zai wakana
Hall ne k’ato cike da manyan Doctor’s da manyan Lab officials da kananu as representers amma basu da yawa, ciki kuwa harda Khairi kansu ya d’au caji, don bakaramin programme akeyiba awurin abune daya had’a four states na na Northwest Kano, Katsina, Kaduna sai Jigawa, harda wasu turawa na wani organisations, harka ce ta boko tsantsa awajan, yanzu k’arfe hud’u da rabine dawowarsu kenan daga sallah, aka dora da jawabi, kana kallon Khairi kasan tana cikin wani yanayi, don wani message ya turo mata, akan lallai ta ji tsoron Allah ba ruwanta da cewa zatayi wani bayani, matuk’ar ba dolene sai tayiba, duk damuwarshi karta fita bayani aga hannayenta da lalle, sannan kuma bayan in bata fita ba ai wani bazai ma lura da zamantaba, shiru tayi ta k’ara bud’e message d’in, daga bangarensu harda Maryam Tafida H.O. D, da wani Mus’ab, cikin kulawa Maryam ta rada mata “meke damunta ko baby ne yakeson fara cin abinci” murmushi tayi ta ce A’a, batun yau ba Maryam take lura da Khairi na fama da matsala kan aikinta da kishi, duk da Khairi bata tab’a zama ta bata wani labariba, ana haka sai manyan cikinsu sun shirya tambayoyi wanda ya sani zasuke amsawa, abangaren Doctor’s Dr Kibiya ya amsa guda ukwu, inda su amatsayinsu na ma’aikatan asibiti d’aya sukaji dad’i, ana haka aka fara tambayoyi kan Lab, nan fa kake jin answers daga sauran states da wasu hospitals na cikin Kano, haka yasa H.O. D ya fara kallon team d’insa, har sai da ya rage saura 2 answers na bangaren Lab basu amsa ko d’ayaba har baturen dake jefa amsar yana cewa nasara nasara, shahada tayi ta mik’e ta isa ga stage ta shiga bayani, sosai ta burge especially in aka dubi qualification d’inta shine least, don koda akace zata sai da taga kamar wajan yafi k’arfinta duk masu degree afannin ne sai sama, kamar yanda akewa kowa tafi haka aka mata, baturen wajan ya kalleta yana ” Thank you young lady” shi yaganta karama baima lura da cikinta daya tashiba.
Bayan magriba suna zaune suna taba hira iya team dun asibitinsu, haka suna tattaunawa kowa sai yabonta yake, dama Khairi da son fannin nata taji dadi, kowa yana encouraging dinta akan kara karatun, sai dai aranta tana basu san wanda zai dakatar da itaba, amma saboda tana son abun tana yawan research kuma lokuta da dama in suna aiki cikin Lab in taga abunda bata saniba takan tambayi H.O. D, daga nan suka koma Hall inda zasuyi taking dinner, abincine kala-kala da drinks snacks wasu cimar ma ba irin namu bane, haka taronsu ya cigaba da gudana sai 8 suka tashi, suna tashi suka fito gaba d’aya, kusan kowa yana da mota ga gari ya had’e bak’in kirin, wayar Adam taki shiga saboda tsiyar network har Dr Kibiya ya wuce ya dawo don hanyar gidansu daya sai dai shi yana gabansu, anan sukayi deciding ya tafi da ita sai da suka shiga mota H.O. D ya shiga tashi, sannan su Maryam ma, sai yau take jin haushin kanta da Abbanta yaso bata karamar Vibe tak’i, wai har tana cewa Insha Allah da Salaryn ta zata saya
Abincin da ya karbo daga gidansune agabansa ya kasa ci, saboda tsabar bacin rai an nuna taron nasu a NTA ne, yaganta kan stage ” Wato tsabar taurin kai irin nata sai da taje tayi surutu ko, shikuma wannan mai jan kunnen uwar me yake gaya mata?”shi kad’ai yake sumbatu can kuma ya duba agogo yaga takwas harda yan mintuna, duk da yasan tace sai 8 amma sai da yaji haushi yaja tsaki ya fito kofar gida, anan ne yaga yanda hadari ya taso sosai da alama in ruwa ya b’alle za’ayi kaman da bakin kwarya, alokacinne suka isa k’ofar gida, cikin sand’a ta fito bataso yaganta dashi, saboda ta lura yafi tsanarsa da kowa amma ya zatayi bata da choice, kaman jira ake ta fito amotar ruwa yakece lokaci guda, ko godiya bata tsaya yi masa ba ta kwalwala zuwa gida, shikuma Adam banda ruwa ya balle wallahi sai ya isa ga motar ya zuba wa wanda ya kawota rashin mutumci, don duhun garij bai bari ya ga wayeba, sannan daga dan nesa da kofar gidan yayi parking ta opposite d’insu
Tana isa ga k’ofar gidan gabanta ya yanke yafadi, batayi tunanin zata ganshi awajeba kuma ga yanayin fushi dake kan fuskarsa, bai damu da ruwan dake jik’ashiba, ta rabeshi tayi cikin gidan don bataso yafara sauke fushinsa daga k’ofar gidan, cikin fushi ya d’oru abayanta zuwa falo, ita kuwa direct bedroom ta isa saboda jikewar da tayi, burinta d’aya ta ciresu tana kokarin daura towel ya isa bai yi wata-wataba ya sauke mata mari afuskarta, tsayawa tayi cak cike da tsoro mamaki hade da fargaba, hannunta dore kan kamatunta, abun Adam har yakai ya mareta to in ta tankashi tanaga rufeta da duka zaiyi, karkarwa kawai take tana ja da baya yana binta fuska d’auke da fushi, closet ne ya tokareta anan ta durkushe ta fashe da kuka ” Munafuka annami miya, wallahi kinyi asarar karatun ki, wai ke meye damuwarki da son fallasa kanki ga wasu mazan” duk da kukan da take mai sautine bai hanata jin kalamansa kantaba ” Wanne dan isakan ne ya ajiyeki amota?” yanzu idonsa har tsattsafo da hawaye yake saboda b’acin rai, bata yi maganaba sai tayi kokarin gyara zaman towel din, tayi wuf ta shige toilet, tsayawa yayi jikin toilet d’in yana cewa “In banda rashin gaskiya mai yasa bazaki kirani nazo na dauke kiba,nagaji da irin wannan abun Wallahi yazama dole ki zaba Khairi” cikin kuka tace ” Ai nayi kokarin kiranka taki shiga, kuma karka manta ruwa ke shirin zuwa don me zan tsaya, meye aciki don an rage min hanya ya kake so nayi” Haushi yaji ya bugi kofar ” Karya kike dama u set-up this kinsawa ranki ku taho kuna tadi, saboda ki nuna masa kwalliyarki ko, yinin da kukayi tare baiishekiba” durkushewa tayi atoilet din ta cigaba da kuka, don kanshi ya gaji ya fita daga dakin yana bak’in rai
K’ara kallonta yayi akaro na biyu, baccinta take hankali kwance, banda darajar cikin dake jikinta ba abunda zai hana ya sauk’e mata nauyinsa akanra yau, cike da jin haushi ya bubbuga mata kan pillow, cikin magagin bacci ta bud’e idonta yace “Jamila me kike nufine? Dama ciki ne ya had’ani dake ko me? Ba nan kike fama rokataba in kin karbo maganinki” yamutsa fuska tayi ” Na shiga uku da gori da tada maganganu, koma meye ai dai kasan bani da lafiya ne” kallonta yayi cike da bacin rai yace ” I dont care i need you right now” dafe kai tayi tace gaskiya nidai bazan yardaba, haka suka sha rikici in ya tabata ta botse ya tabs can ta tureshi karshe gudu tasa tabar masa d’akin, kwana yayi da ciwkn ciki dama yafi ssti yana fama dashi….
Da safe kuwa da ya fita school fuskarsa daure ba walwala, haka ya dinga fada cikin lecture hall kowa yakasa gane kansa, da yaji rashin murya ko motain da bai gamseshiba sai yace get out..
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
28
Sai da yagama lecture d’inshi sannan ne ya koma office d’insa ya dasa tunanin yanda zai shawo kan matsalarsa, sukuwa d’aliban daya dauka sai mamaki abun suke wasu suce kila matarshi ta kunnoshi, wasu suce babu ce tasa shi hakan, shikuwa anasa b’angaren kansa ne ya kama ciwo ko haduwa da Umar baiyiba ya koma gida, bai damu da ganin taba kawai direct d’akinsa ya wuce, wallahi banda Jamila nada juna biyu ba abunda zai hanashi kwata da k’arfi, amma bakomi inta k’ureshi zai bata mamaki.
Khairi kam kwanan bakin ciki tayi, masifar Adam ta isheta abun sai cinta yake azuciya, to wazata fad’awa k’awarta kanwarsa ce sannan iyayensu komi daya suke, karo na farko arayuwarta da tasan ta kwana tana nafilfili in tayi sallah sai ta huta ta k’ara d’orawa, b’arawon baccine ya saceta kan sallaya sai da tamakara a sallar asuba, tana gama sallar Asuba ta shiga ruwan zafi tayi wanka, shaf-shaf ta had’a breakfast ta ajiye duka lokacin bakwai da kwata tayi, ta sabi jakarta tayi Asibiti, don ba fashi tunda meye ya rage ya zabga wa fuskarta mutumcinta mari, yanzu yazama bata da saura gara ta cigaba da chasing dream d’inta she already lose Adam, shima dake kwana yayi kishi na Addabarsa shiyasa ya makara, bai fitoba sai bakawai da rabi da minti hudu yana fitowa ga komi ta ajiye amma bata gidan, wani mahaukacin haushintane ya taso masa, wato tayi laifi amma ko ta tsaya taji makomarta ta k’ara tafiyarta asibiti meaning she dont care, cije lips d’insa yayi tare da buga hannun shi kan dinning table d’in, ko shakka baya yi k’arfin alak’arta dasu Dr Kibiya ke ingizata ga son Asibiti, wallahi aka cigaba da haka sai yayi k’arar su, bai iya cin abincin ba sai zama da yayi yana cin alwashin wulk’ancin da zai cigaba da karta mata har sai ta ajiye aikinta infact sai ya mata kulle don zai hanata fitane cikin sumbatu yake fad’in ” Khairi tawace nikad’ai ba’ayita don kowaba sai ni Adam, dole na katangeki Khairi wallahi kika sake na rabaki da aiki fita sai ta gagareki, ni kadai nake da ikon kallon ki fiye da sau daya amma kash su Abba sun jamin kina yini cikin wasu k’atulan-mak’atulan”
Duka yau a Lab yazama rabin hirarsu kan jiyane, cikin farin ciki ake komi hakan kuwa bak’aramin taimaka wa damuwarta yayiba, duk da jefi-jefi takan shiga d’an tunani, bayan sun ragu kowa ya kama gabanshi, lokacin ne ta fito daga wajen staff ta tsiri waya da ‘yan uwanta musamman anties d’inta don wasu basu whatsapp irin sune zakaga ba’a fiya gaisawa ba sosai, magana take da Anty Murja sai kakarta dukansu na bangaren uwane, yan Jahun ne suna mata korafin aiki ya hanata zumunci, tafi awa d’aya awaje tana gaishe-gaishe, sai da tagama takoma ko minti biyu batayiba kiran oga ya shigo, k’in dagawa tayi bata shirya karbar shoutings dinsa a asibiti ba, shikuwa Adam ganin ya mata 3miss calls batai picking bane yasashi sending mata text ” Khair ya miki kyau, ni zan kiraki kik’i dagawa bayan tulin laifin da kikai ko? To ko’ina kike ina son ganinki yanzu agida, don kin fita bada izini naba” sai da ta maimaita text d’in sau uku, ta ajiye wayarta cike da damuwa kanta har ciwo yake, amma bata tashi ba sai da lokacin yayi, shikuwa yana can ya cika fam don ko office bai jeba knowing ya bata order ta dawo, tana shigowa ta ganshi gabanta ya fad’i seems like ya zame mata abun tsoro ko ganinsa tayi ji take taga tashin hankalinta don sai ya k’irkiri abu, tun daga yanayin hararar da yake mata tasan akwai tsiya, amma tasawa ranta yau ko kasheta zaiyi sai dai ya kasheta, sunkuyar da kanta tayi ta wuce kujerar da yake kai zata nufi bedroom d’inta bai jira komiba saboda tunzura ya tashi ya kwad’a mata maruka aduka side na chicks d’inta, wata iriyar tsanarsa ce ta shigeta alokaci guda ji take bata taba nadamar abu ba arayuwarta irin son Adam da auransa, bai tsaya daga nan ba ya fincikota ya mik’ar da ita don saida ta fad’i daya mareta, ya fara zuba mata zafafan kalamai masu dawwama arai ” Lallai kin tabbatar mun Dr yasha gabana, in banda kin raina ni kiyimin laifi wani shege ya kawoki k’ofar gida, amma ki iya tsallake gidana batare da umarni naba ki tafi wajan aiki saboda kinsan zaki ganshi, ohhoo wato ya rud’aki jiya ko? Khairi wallahi ni kad’ai nake da mallakin ki tunda kikai involving wani sai nasaki nadama” wani irin zugi zuciyarta take yau ko d’igon hawaye babu afuskarta sai kallon tsana da ta kureshi dashi, bai damu da rashin maganar ta taba yace”Khair gara nak’ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak’aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba…. Cikin Kuka tace ” Zargina kake? ” don yanzu hawaye ya fara zuba a idonta ” Oh zargi ne ma? Karki nemi raina min hankali, nima dan zamani ne kamarku, kalleni Khairi meya fini dashi?” yasan bazata amsa mishiba ” mena rageki dashi kin daina aikin nan, matan da sai sufi wata uku basu taka k’ofar gidaba amma ke kullum bisa titi, kina nunawa duniya ni’imar da Allah ya miki, look Khairi i had enough of this shit bazan k’araba, dole kidaina zuwa aiki ehe, rashin bin umarni na kuma bazai zame miki Alkhairi ba, im warning you karki ga munada alak’a wallahi bazata yi miki kyauba, mark my words” k’ura mishi ido tayi ya fuzgi car keys dinshi a dinning ya fice ya barta da tulin takaici…
STORY CONTINUES BELOW
Jamila ganin ai shike da hakkin ya duba lafiyarta amma ya shigo d’akin ya k’etare ta yasa ko takanshi bata bi ba. Al’amarin Ahmad kuwa tunda yashiga wahalallen ciwon mara dake addabarsa tsawin sati uku ke nuk’urkusarsa, yana juye-juye na ciwo amai ne ya taso masa dak’yar ya mike amma ina tuni ya kwace masa cikin d’akin, jin amansa ne ya sata shigowa lokacin tuni magariba ta sako kai, agigice ta isa gareshi tana masa sannu, kallo daya zaka masa kasan yana wahala. Bayan ta gyara wurin ya kwanta ciwon kai yace muje zuwa, haushinta ke nuk’urk’usar sa azuciya, dolenta ta gyara wurin ta had’o masa lipton da ta matsa lemon tsami ciki, da kyar yake sha fuskarsa kuwa ba annuri, yanzu ciwon cikin yad’an lafa “MyOne meya sameka ne? Meke damunka?” kallonta ya tsaya yi karta raina masa wayo mana, ai tasan irin matsuwar da yayi amma ta zauna take bashi wuya har yagaji da shan maganin kwantar da sha’awa, k’arin haushin ma bai wuci yanda da dare ita gata mai ciki take faman nanuk’arsa da narkewa ajikinsa da sunan ciwoba, tagama daka masa hankali karshe ta hanashi hakkinsa, tab’ashi tayi tace ” Ko bakaji tambayar da na maka bane?” jan tsaki yayi yace ” Pls leave this room” zaro ido tayi yace ” What!! anyway shikenan” ta ficewarta tana k’un-k’uni akan sai ta rama indai ita zai dizga tazo tana tambayershi abu amma ya koreta.
Da dare yad’an samu relief sai dai yana jinshi wani iri ne somehow, fitowa yayi saboda yunwa anan yasameta tana cin wainar fulawa(kalallaba), sunan ta ya kira ya tambayeta abincin sa tace ” Ai danaga fushi kake nad’auka bazaka iya ci abinci na ba shiyasa ban yiba” k’ura mata ido yayi cike da b’acin rai ” Jamila ki ganni ahalin rashin lafiya wadda kinsan kece sila, sannan baki bani wata kulawa ba kuma abincinma ya gagara” nuna kirjinta take ” Nice sila? Dawowa kai da abun ka fa” banda bai iya bugun mace ba da saiya zabga mata mari ” satinki nawa baki bani hakkina ba, kuma kinsan ni ba dutse bane ba ko? Wallahi ki kiyayi randa zan d’au mataki don sai kinyi nadama mara amfani” shiru tayi na wasu seconds tace ” Kayi hakuri yanzu dai kafadi me kake so kaci zan dafa maka?” zama yayi kan kujera yace ” Ki soyamin farar doya da egg sauce ya yi sai mint tea” bakinta acune tagama hada komi takawo masa, bin kirjinta yayi da kallo wanda ciki yasa sun kara cika, yaja tsaki ita kuwa ta dora da zuba yaji kan wainarta tana ci. Tun bayan ranar da ta gudu daga d’akinshi sai taga dama in tana jin tabarar ciwo take zuwa saboda kar ya tab’ata, yau ma saboda taji statement dinsa tayi gaggawar shiryawa ta shige d’akinta ta rufe, sai da yagama cin abincin ga zatonsa yau zata bari yayi kodan tankawar da yayi amma sai yaji k’ofarta arufe abun ya masifar b’ata masa rai, wato duk da taganshi awani hali ba tausayi bazata iya bashi ba, to gaskiya hak’urinsa yakai matuk’ar k’urewa amma bakomai zai d’au mataki akanta…
Kwana uku ajere bata fita wajan aiki, ta zauna tayi tunanin mafita amma sam brain dinta takasa bata hanya, gashi bata sharing da kowa balle taji opinion na wani, abu daya da take shine bata fasa yimasa komiba, amma fa ba sakewa tsakaninsu sai take masa abu tamkar master and maid, in yace ban abu zata tashi tace “to” takawo masa ba walwala ba wani sakewa irin na mata da miji, ba hira kawai zamane kurum, shikuma ason kansa sai yakeso ta ware ta ajiye komi gefe su koma daidai, in ya jata da hira bata tayashi sai ta bada amsar da zatayi making conversations din short, kuma bata dariya, yau ya dawo wanda yakama Friday complete week bata je aikiba kenan ya tarda ita zaune cikin falo, da waya ahannunta ta k’ura mata ido, saboda yanda tayi nisa atunani bataji shigowarsa ba, yaje ta baya cikin sanda ya rufe mata ido da sigar son wasa, cak tayi gabanta ya cigaba da bugu zuciyarta na fat-fat, tak’i magana sai da yaga bata da niyyar biyeshi ya saketa ya dawo ya zauna “Babyluv wai meke faruwane? Kin zama silent” dan yak’e tayi tace ” Bakomi bari na kawo maka abincin ka” ta tashi batare da taji amsarsa ba ta nufi kitchen ta kawosu dinning tayi serving dinsa, ta koma kan kujerun falon, kallonta yake kaman tana avoiding dinsa fa, haushi yaji ya kamashi ba duk don son da take mata ne yake hakan ba, sai da ya saita muryarsa yace ” Babyluv ke bazaki ci abincin ba? ” bata juyoba ta bashi amsa ” Nak’oshi ne tun d’azu naci” tana gama fad’a masa ta tashi tabar falon, sam bata son ganinsa ayanzu balle hira dashi, ba abunda ke b’ata mata rai irin zarginta da take takan zauna tayi kuka idan tana tuno kalamansa gareta, atunaninta shi mai iya fada da kowane idan yaji an jefeta da kalaman k’azafi, ta tabbata auranta dashi bazaije ko’inaba idan kuwa Auran bai mutuba to tabbas akwai randa za’azo atsinci gawarta….
Da week-end yana breakfast ya sanar mata zasuje gida su yini, duk aniyyar wai sata ta ware yasan dole sukaje gida zata ke biyeshi kodan kar agane komi, don yasan zai mata shedar sirri bata fadar komi na rayuwarsu, shiryawa tayi tayi k’ok’arin yin kwalliya tasa doguwar riga bak’a abaya tare da babban mayafi, bataso suga tulin k’ashin wuya da tayi na rama, sai janta yake da hira tana cijewa so take ta ware ta yafe masa amma ina zuciyarta ta rik’e abubuwa da yawa. Koda suka keb’e da mahaifiyarta taso taji koda matsala amma ta nuna mata bakomi haka yininsu ya wakana, zasu tafine sai Mama tace k’awarta zatazo asibiti amma tanaso Khairi ta mata hanya saboda yanayin layi, intazo zata nemeta ta bata No ta dake abunda zai kaita ya shafi Lab, lokacin tana cin abincine agidansu shi kuma ya tafi can gefen layinsu gidansu wani abokinsa…
Tunda takoma gida take tunanin dolene taje asibiti don kuwa rashin zuwanta yana nufin sugano bata zuwa, misali idan ita Antyn taje ta tambayi Khairi akace takwana biyu bata jeba fa? Shiru tayi tana tunani k’arshe ta yanke zataje sai tayi k’ok’arin dawowa kafin yazo tayi girkinta, da wannan shawarar ta kwanta adaren lahadi
Monday..
Bata nuna komiba ta tashi ta shirya tsaf sai da yatafi da awa d’aya sannan ta nufi asibiti, aikuwa tana zuwa bata gama daidaituwa kan kujeraba sai ga matar tazo ta rakata can k’ofar Lab da ake aiki, saboda Khairi ce takaita H. O. D dakansa yace shi zai mata gwaje-gwajen da tazo yi, Hajiya Mairo kuwa taji dadi sai da aka gama mata komi ta tafi inda Khairi ta rakata bakin titi tare da biya mata kud’in adaidaita..
Sister Khairi taji muryar Dr yana mata magana lokacin tana bakin gate, matsawa tayi daga kan hanya ya k’araso bayan sun gaisa yace “Don Allah ina son yin wata magana dake, ina fatan kaiki da nayi gidanki bai haddasa maki matsala ba” kirkirar murmushi tayi tace ” A’a bawata matsala da ta faru, namanta ko godiya ban maka ba” dama sun dan matsa gefene amma sai dai still suna daga bakin wajan ne, shi anashi tunanin saboda gudun zargi ne yasa bai nemi ganinta a office dinsaba, yace ” Kwana biyu naji ance bakizo ba ina fatan lafiya dai? Ko kuma baby ne ya matsa? ” tayi murmushi tace ” Lapia lou ba matsala” yafi minti talatin yana tsaye awajan gate din ta d’aya tsallaken sai dai kash yaso yazo ya tarda Dr kibiya awurin wallahi da sai sun kwashi ‘yan kallo, tana shiga office taga miss call d’insa, ta dauka cike da rawar jiki tabi ” Kizo kisameni k’ofar gate d’inku” Sallama tayiwa su Maryam ta tafi cike da tausayi Maryam ta bita da kallo, don tagama gane rikicin gidan Khairi, tana zuwa dakyar ya daure bai kai mata duka ba ya fizgi motar yayi gida da ita…
Tunda suka shiga yake masifa hawaye na sauka a idonsa, sai karkarwa take, jikinsa har tsuma da rawa yake saboda zuciya can ya kalleta yace “Khair bazan iya lamuntan wad’an nan agaskiya d’abi’ar ba don haka mafita guda d’ayace, yazama dole nai wa alak’armu katanga” cikin karkarwa tace ” me kake nufi? Kar kazo kai abunda zamuzo dukanmu muna dana sani kayi tunani” cikin zafin rai hawaye na fita a idonsa yace ” sai dai ke kiyi nadama baniba, amma bawani kalami da zakiyi da zai hanani daukar mataki” ya tureta ya fice…
Mota yaje yayi rubutu atakarda ya shiga d’aki ya mik’a mata, tunda takaranta abunda ya rubuta ta durk’ushe awurin take uban kuka, ina zata je? Da wanne ido zata kalli idon iyayenta, kamar mahaukaciya ta mik’e ta nufi d’akinta ta fara zuba kaya acikin trolley babba…
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
29
Tafe yake yana wasi-wasi akan zugar da shaid’an yake masa, tabbas amatse yake, yazo kan wata kwana kawai yaga wata yarinya da tadad’e tana bibiyar rayuwarsa, ya tuna ta tab’a cewa koda bazai aureta ba kawai su k’ulla alak’a ita hakan wani farin cikine arayuwarta, taka burki yayi ya tsaya daga shop dayaga ta shiga, aikuwa baifi minti biyar da tsayawa ba sai gata ta fito da leda sai ya samu kansa da fita da karba tare da kasheta da wani kallo, aikuwa Bubly taji wani masifar dad’i itama ta bishi da wani shu’umun murmushi, dama gata da dara-dara ido tuni hankalinsa ya fara tashi abunka da an dade ba’a had’u, cikin kisisina ta gogaggun ‘yan duniya, tana wani gantsare-gantsare burinta yau kawai su kebe in yaso ta bijiro da sharrin ciki ko zai aureta, sai da ta d’au minutes kafin ta juya ta fad’a masa unguwar da zai ajiyeta kallonta yayi yace “gidankine ko kuwa gidan ‘yan uwanki?” sai da ta lashi lips d’inta tace ” Gidana ne ko baka zuwa gidan mace” wani murmushi yayi batare da ya bata amsa ba…..2
Kayan ma tsabar rawar da jikinta yake yi batasan wasu iya d’ankwali take d’auka da zaniba wasu kuma iya riga da dankwali, fuzgosu take kawai duk ta hargitsa d’akin, sai da ta turo trolley d’in k’ofar falon, ta zube awurin tana kuka kamar zata mutu, kowa yasan yanda zafin saki take gun mace wadda ta nema ma hankalinta tashi yake balle baki nema ba, ba komine yake kara gigita Khairi ba irin yanda zata fuskanci gidansu, ga wani irin rad’ad’i da takeji azuciyarta, shafa cikinta tayi hmm ko Adam ya manta ba’ason sakin mace mai juna biyu, ko kuwa tsabar rashin tausayi da rashin sanin darajane? Lallai ta yarda maza sun iya yaudara, ina soyayyar dayake ik’irarin yana mata, shin ba inda soyayya ba tausayine? Duk da kasancewarta mai ciki ya iya runtse ido ya k’ullamata wannan masifar, tana jin yanda mararta ke nuk’urk’usarta banda ciwon kan da kuka yasa mata, tafi awa d’aya awajan rashin sanin inda ta nufa, wata zuciyar sai tace ta gudu Jahun, wata tace ta gudu Kura amma duk taga ba hanyace mai b’illewa ba, gadan-gadan ciwo yake cinta awurin,ga fargabar rashin cikan watan haihuwa na cikinta, bata da k’warin takawa ta fita saboda ciwon marar da ya had’e mata…
Sabeer yaja tsaki yace ” Ak kaga gaba d’aya numbers dinshi switchoff inaga kawai muje gidan nasa” sai da suka jira akai sallar magriba sannan suka nufi gidan Adam.
” Sabeer kalli can meye haka kaman mutum kaman kayan wanki?” ya nuna masa wajen da Adam ke parking motarshi, hanzari Sabeer yayi nufi wurin yana cewa ” Anya kuwa? mutum ne wannan” daidai lokacin nefa suka maido wuta, wani irin fad’uwar gaba ce ta ziyarcesu gaba d’ayansu, to yanzu ya zasuyi wazai tab’ata Adam yaji su hau sama su fad’o, amma ganin bata numfashi yasa Sabeer dagata sai alokacin AK ya kula da tun daga kan step na shiga falon jini ne zuwa inda take alamun jan jiki ta dungayi tazo nan, basu tsaya wani abu ba sukai Asubiti da ita…
Dukansu anrasa mai magana, suna ta tunanin abun, dole akwai abunda ya faru shi kwata-kwata numbers dinsa basu shiga, sannan ita ga yanayin da suka ganta ba daidai ba, sun kasa tantance wazasu kira karsu sanar agida kila abune da zasu iya taimakawa agamashi arufe, sai dai abunda ya d’aga masu hankali yanayinta ba dad’i ancire yaron wanda aka barshi abangaren kula da bakwaini, don he’s not normal, ita kuma uwar batasan waye akanta ba, har wajan k’arfe 10 na dare, dole suka nemi Hidaya tazo don itace bata da k’aramin baby…
Shikuwa Adam fita yayi yabar gidan yaje ya kama hotel ya shiga d’akin yadinga zunduma ihu shikad’ai, waishine matarsa take mu’amala da wani, kai lallai ba wata halitta adoran k’asa da takai mace cin amana, Khairinsa wanda kowa yakewa shaidar mutuniyar kirki itace take hakan, ashe duk sunkuyar dakanta da sanyinta na munafurcine, haka yakwana yana tunane-tunane, wallahi aure zai k’ara kwana kusa, sai ya k’untatawa rayuwarta, zata gani, kwata-kwata baiyi nadamar abunda ya aikataba asalima sai jinjinawa kansa da yayi da yaudararta batayi tasiri akansa ba, lallai shi ya cika Namijin Duniya.. Yayi wani murmushi na mugunta…
STORY CONTINUES BELOW
Tunda suka shiga gidan da kisisina sai da Bubly tasa ya sake wanka, sai da yafito ita kuma ta d’aura towel wanda koya ta sunkuya sai ukwunta ya fito, ta tafi tana jijjiga jiki dama gata da ukwu masu rawa, gabad’aya shaidan sai zuzutawa Ahmad feelings yake, so yake kawai tayi ta fito awuce wurin, dak’yar ya fita yayi sallar magriba kafin ya dawo Bubly tasha wani had’i tare da saka wata shegiyar short gown da sai da aka kwaye gun boobs dinta kawai nipples ne akasa wani net aka rufe, kalarta red tabbas sai wanda Allah ya tsare ne in yaganta baiji sha’awarshi ta motsaba, don ba abunda Allah ya rageta dashi na diri ga kuma kwanyar kisisina da take da, tunda ya shigo ya kasa d’auke idonsa akanta in yaso d’aukewa saboda tsoron Allah dayake bijiro masa, amma can feelings sai su tunzurashi don yafi sati baiyi romancing da Jamila ba ko hannunta bata bari ya tab’a, aikuwa ganin plan d’inta yana shiga ta k’araso gareshi ta rungumeshi as welcoming sai da ta tabbatar laushin boobs d’inta ya gogi jikinsa, bai mata musuba sai ma rik’on daya mata mai kyau ya shiga shan bakinta, ita ta kagu awuce babban harka don haka ta jashi cikin bedroom, suna shiga ta tanadi fruits d’inta d’auko grape tayi ta jefa abakinta da sigar jan hankali ta kamo bakinsu ta hadesu, ya fara enjoying sosai ayunwace yakai hannunsa kan boobs dinta sai dai me, yana tab’awa ya mik’e tsaye still hannunsa nakansu amma jikinsa rawa ya d’auka take ya fara wani mahaukacin shaking….
Sai da safe Khairi ta dawo cikin nutsuwarta amma bak’aramin fad’a Dr ta dingayi wa Sabeer ba, anata tunanin shine mijinta tana cewa sun barta tayi doguwar nak’uda banda Allah ya takaita da sai ta samu wani ciwon, yasha fad’a tace daga gani kai azzalumin mijine yarinya k’arama ace tana fama da hawan jini, kabarta ta wahala mazan arewa kuna ban mamaki fad’a tayi bana wasa ba,sudai kawai binta suke da “Afuwan Madam”..
K’arfe shida da rabi suka gwada number Adam sai gashi ya d’aga ” Cikin masifa Sabeer ya fara magana wai kai don Allah meya sameka? Kana da mace mai ciki ka tafi ka kashe waya wane irin rashin mutumci ne wannan” jan tsaki yayi yace “Naji inada d’a amma ai ba mata ta bace, yanzu ina kuka ganta? Nasan ai da saura kafin ta haife” wani irin haushin sane ya taso wa Sabeer yace ” To sai kazo asibiti d’an cikinta zai kashewa iyayenta diya, da kasan ciwon danka itama yar wani ce, wallahi da nasan aikin da kayi kenan da tun jiya zanje gidanku nabarsu susan halin da muka tsinci Khairi” sai dayaji gabansa ya fadi amma tsabar mugun kishi ya ce ai ita ta jawa kanta aransa, yace shikenan zaizo..
Kallon Ak yayi yace tashi muje gidansu dole suji kuma kaga ance sai an k’ara mata jini, tayi loosing jini duk da kaman tace guda d’aya za’a saka mata,anan ya fad’a masa Adam ya saketa, koda Hidaya taji sai da da ringa caccakar maza…
Tunda aka fad’a masu halin da take ciki Humaira take kuka ita da Hajiya Hassu, itakuwa Ummi irin abun nan da ake cewa hawaye yak’i zuwa ne, dole aka kira Muhsin don shine zai iya bata jini blood group d’insu iri d’ayane, aikuwa Safiyya biyoshi tayi tana kuka dole suka tafi tare…
Kowa ya hallara banda Adam yana can yana breakfast ahotel, anan ne iyayen suka tabbatar da matsala don su Sabeer kawai sunce bata lafiya ta haihu tana asibiti, an sakawa Khairi jini sai bayan awa biyu aka basu damar ganinta, don da safe jikinta kara rikicewa yayi, tunda ta d’ora idonta kan mahaifiyarta wani irin kuka ya kufce mata, yanzune ran Hajiya Hassu ya k’ara tunzura d’aukar waya tayi ta kira Adam tace yazo duk inda yake, shikuwa da har ya tafi Rano don yasan zuwa yanzu zance yaje kunnen gidansu so yayi sai yayi kwana uku zai dawo amma yanda ta dinga zuba masa miss calls yasashi karaya gashi ta ajiye masa message, karya bari dare yayi baizoba inba hakaba sai ta masa Allah ya isa nononta da yasha, bayama da Sabeer ya fad’a mata yanda suka ganta, hakin b’acin rai kawai take, sai da suka jima ana jajanta abunda ya faru sannan ne kuma Khairi tasan babyn yana k’ark’ashin kulawane, sai godiya Hajiya Hassu tayiwa su Ak sannan suka tafi, itakam Khairi bata bada labarin komi ammafa taki magana sai aikin hawaye take, basu san sakiba sudai anasu ya tafi ya barta ba kula sannan da alama sunyi rikicine…
B’acin ran dake fuskokinsu ya koma jimami tunda Dr tagaya masu cewa babyn ya koma, bakomai ke k’ara sasu damuwa irin tausayin Khairi in taji, amma dole ne agaya mata sai da Hajiya Hassu ta gama mata nasiha akan rashi da samu sannan ta gaya mata , abunda ya basu mamaki shine kawai sai tayi murmushi tace ” Alhamdulillah” amma hawaye sai da ya sauko a idonta, ita Safiyya kuka rake tigijim don tasa lrin yanda Khairi keson yara ga nafarkon bari ga wannan, ko kaffara bazatayiba tasan yayanta nada kamasho tunda doguwar nakuda kan kashe baby, haka suka tarkata gida can d’akin Safiyya nada Hajiya Hassu ta nemi a ajiye Khairi, haka kuwa akai an mata tanadin jego ta shiga ruwan zafi ta fito ta shirya tsaf, sai dai fuskarta ba walwala an tasa ta agaba da nono mai dumi tasha ga farfesu agefenta, lokacin ana kiran sallar Isha’i sai ga Adam ya shigo, bata kalleshiba ta shige d’akinta inda Ummi ke sallah itama ta tada, sai da aka fito daga sallah suka hallara gaba d’ayansu a babban falon gidan, har iyaye mazan don duka sun dawo daga inda suke, Khairi ce ke shigowa yanzu daga nesa taganshi agefe wani irin fad’uwar gaba tazo mata da wani irin tsanarsa dake cin ranta, ana iyayen suka nemi da suji bayanin meke faruwa takarda ta mik’awa Hajiya Hassu batare da tayi maganar, shiru yayi can kuma yafara bayani da in’ina yace ” Gaba d’aya ta canza haline atak’aicema ni yanzu ban yarda da itaba” zaro ido Ummi tayi take hawaye ya fara saukowa a idon Khairi, bud’e takardar tayi abunda tagani shine yasa ta tashi tsaye tace “Adam!!!” Kawai zuwa tayi ta fincikoshi wanda dolensa ya mik’e tsaye ta dinga d’ora masa mari hawaye na zuba a idonta sai da aka rik’e hannunta shikuma har bakinsa ya fashe baiyi k’ok’arin kaucewaba, komawa tayi ta zauna tare da fashewa da kuka tace ” Aisha maiyasa kika rik’eni baki bari na lahanta wannan shashashan ba dan iskan yaro wanda baisan rufin asiriba, so yake ya tozartamu a idon duniya ya zubar mana da mutumci” kodaga ganin abunda tayi sunsan meye atakaddar sakine meye banda shi, me ake rubutawa, fad’in tashin hankalin da suke ciki b’ata bakine, kuka Safiyya take ita da Humaira, Alhaji Aliyu kuwa bata baki ya fara yana cewa ” Shi dama Aure rai gareshi duk ranar daya ajakinsa yazo ba makawa sai ya mutu” Alhaji Abdullahi yayi shiru ya kasa magana saboda tsananin b’acin rai, kallon Adam yayi yace “Kace baka yarda da itaba bako? To ashe baka yarda da ubankaba don ni ni na aura maka Khairi wato ban iya zabi ba na baka mara tarbiyyako? To mungode kagama naka mukuma sai ka barmu muyi namu, tunda kai bakasan gata ba ka watsa mana k’asa a ido, kuma ni Alhaji Abdullahi sai na maka ka akotu na jifan d’iyata da sharri da kayi, na gaya maka ka saurari sammaci, tashi kabar min gida don bada kud’inka aka ginaba, ku sheda banason k’ara ganin k’afarsa acikin gidan nan, na yafewa.. ” cikin hanzari Alhaji Aliyu ya dakatar dashi baik’arasa ba, gaba d’aya daren baizowa zuriyarsu adadiba haka taro ya tashi zuciyar kowa ba d’adi, Adam ya dasa wani bacin rai ga iyayen nasu koda Safiyya tazo zata fita da falon sai da ta take masa k’afa tana kuka ta ja masa tsaki, Muhsin ya tashi yabi bayanta aikin rarrashi…
Tunda ya rik’esu bai iya sarrafasu sai wani irin shaking da jikinsa yake take yafara wani irin releasing da bai taba yiba arayuwarsa, yana tsayene amma yana jin yanda abu ke sauk’a akafarsa, take hawaye masu d’umi ke zuba a idonsa, idonta alumshe tana jira jin wasu bak’on yanayi amma taji shiru, bud’e idonta tayi don taga yanayin da yake ciki abunda tagani ya bata mamaki, durk’ushewa yayi awajan yana kuka kamar mace yana furta “Astagfirullah wa atubu ilaih” da k’arfi yake fad’a yana rusa uban kuka..
“Jakar uban nan ne Ahmad yake har irin wannan lokacin bai dawo ba, ashe yau za’ai bala’i agidan nan” hmnnn d’aukar wayarta tayo ta k’ara kiransa in kuwa tayi wannan kiran shine na takwas ba’a daga sauranba…
ila
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Jinjina ga masu comment da voting hak’ika kuna kara karfafamin gwuiwa. Nagode much luv😍
30
Tun da yafita daga gidan nasu yake b’acin rai, wane irin rashin Adalcine wannan ba’a bari ya fadi abubuwan da take masaba, amma shikenan yasan ko ba dad’e ko ba jima dole sugano alokacin ne zasu san bashi da laifi, kwata kwata baiyi nadama ba, abu d’ayane ya soki ransa shine rashin d’ansa da yayi, amma bakomi ai zai k’ara aure zai samu yara da yawa, shikad’ai ya koma gidan ak’ofar falon yaga jakarta da shatan wurin jinin nata sai da tausayinta ya sokeshi amma ya cije, ya shige daki ya watsa ruwa ya kwanta…+
Tashi tayi ta k’arasa inda yake yana kuka da sauri ya ja baya yana ” Karki sake ki tab’ani don wallahi sai nayi k’asa-k’asa dake” take hawaye ya fara zubowa a idonta, ita ba jahila bace tagano wani abun tabbas Ahmad bak’aramin kariya gareshi ajikiba, karfin Addua da imani ne yasa Allah ya kawo dalilin da ya dawo hankalinsa, don tasan shid’in kamiline baya zina gashi Allah ya kawo dalilin da yasa bazai aikata ba, yana durkushen nan yana jin yanda zazzab’i yake shigarsa don lokaci d’aya yaji wani irin sanyi na shigarsa har rawar zazzab’i yake, dakyar ya tashi ya nufi toilet d’inta yayi wankan tsarki ya fito yayi sallah, akasan tiles sannan ya zube awurin, nauyin takaicin abunda ya aikata ke cin k’irjinsa don haka numfashinsa ma fita yake dak’arfi, itama kokari tayi tayi yanda yayi ta, d’aukar bargo tayi ta rufa masa,lokacinne taga wayarsa na ta uban haske alamar kira na shigowa, ganin sunan namiji ajiki sai ta d’auka daga can b’angaren Umar yace “Oga ka rud’a hankalin uwargida fa, ina kashigane?” jikinta ne yayi sanyi tace ” Gashi nan bashi da lafiya, amma kazo gidana” ta sanar masa address d’inta, agigice Umar ya taho zuciyarsa cike da wasi-wasi, kafin fitarsa yanayin da matarsa tagani kan fuskarshi sai da tayi mamaki, yana tuk’i kiran Jamila na shigo masa tana so taji ko yasamu information kan Ahmad shikuwa yak’i d’agawa, don baisan me zai ce mata ba…
K’arasowa yayi cikin bedroom d’in inda Ahmad ke zube ak’asan tiles, jin muryar Umar yasashi bud’e fuskarsa cikin k’arfin hali yace ” Umar na cuci kaina, abunda banyiba ak’uruciyata ba shi na aikata” hawaye ya cigaba da zuba idonsa, gaban sane ya fad’i yace ” Ahmad me ya kaika haka? ” d’aure fuska yayi ya juya ga Bubly yace ” Wallahi nasan halin abokina sai dai wani abun kika zuba masa ko asiri, ki fadamin gaskiya ko kuma nasa arufeki” hawayenta ta share tace ” Wallahi ban mishi komiba, kuma maganar da ake yanzun ma hakan wallahi iyakar kiss ta shiga tsakaninmu” hayaniya ya cigaba da mata harda zaro belt zai zaneta, sai da Ahmad ya kamo shi yace ” Gaskiya take gaya maka, ba itace sanadi ba rashin juriyane irin nawa da kuma taimakon Jamila, wallahi nayi regretting Auran ta” kan Umar ya kulle shi bai san asalin meke faruwa gidan Ahmad ba duk da yanda suke, bak’arami tashin hankali Ahmad ya shiga ba sai da suka dangana dashi asibiti, sai da takai ansa mashi oxygen don birkicewa yayi ,tun kafin asibiti Umar yayi niyyar Jamila Ahmad ya hanashi, shiyasa batasan me akeyiba tana can tana tanadar wulakancin da zata mashi,ga kishi ya turata akan dole yana tare da mace ne….
Da safe ya dawo normal sai dai kallo d’aya zaka masa kasan yana cikin damuwa, shi tulin zunubin daya d’auka ne ke damunsa, kaishi gida Umar yayi sannan ne suka sanar mata baida lafiya, bin Umar tayi da harara kafin ta maida idonta ga Ahmad “Gaskiya bakamin adalciba, ayanayin da nake ciki ka fice ka kwana awani wurin sannan k’arshe ace baka da lafiya, to meyasa Umar bai fad’a minba tun jiya atleast nasan cewa You are safe” kallonta kawai yayi da ido ya shige toilet d’insa, kodaga yanayin da taganshi da mace ce mai nutsuwa ai yakamata ta adana korafinta, kana ganinsa kasan ba ciwone damuwarsa ba akwai abu azuciyarsa, sai da ya fito daga ciki ya shirya duka tana zaune tana kumbure-kumbure, duk da baijin k’arfin jikinsa haka ya wuce kitchen don shan tea shima bawai don yana soba sai don yasamu yasha magani da wani abu acikinsa….
STORY CONTINUES BELOW
Khairi hankalinta akwance yake duk da da damuwar Adam dank’are acikinta, shiyasa har yanzu zakaga tana yawan zama tayi shiru, tuni Safiyya taje asibiti ta sanar dole aka bata maternity leave, dakanta ta sanarwa Hajiya Hassu Adam ne ya zubarwa da Khairi cikin fari, abun ya b’ata musu rai, sai da aka kwana biyu da case d’in Khadija taji aikuwa take ta nemi mijinta ya bata dama, kuma ya bata ta nufi wurin Khairi, sai asannan ne ta d’an gaya mata wasu k’alubale da ta fuskanta awurinshi, sosai Khadija tayi kuka tace “Yanzu shikenan ya datse igiyar auranku, na tabbata zai ji ajikinsa amma kada ki bari koda wasa in yadawo kiki wanashi, ko zaki koma ki bari sai yaji ajikinsa wani abun harda sanyinki Khairi” Hajiya Hassu da ta dad’e abakin k’ofar d’akin tazo kawowa Khairi wani had’in zuma da akan yiwa masu jego azamanin da, taji harda mari da duka daya tab’a yi mata, komawa tayi d’akinta ta zauna don ji tayi k’afarta bazata iya d’aukartaba, cewa take ” Ina wannan yaron yaje ya dauko wannan halin, bayan hayaniya ma bai taba ji ubansa yamin ba ohh ni ‘yasu” tunani ne yamata yawa, lallai Khairi na buk’atar kulawa don tashiga matsala sannan kuma ta jure abu dayawa aranta, Adam yayi asarar rayuwarsa don yarasa mace mai rufa sirri miji, wanda ayanzu sunyi karanci amma bakomai insha Allah sai na wanzar da farin ciki arayuwarki, alwashin da Hajiya hassu ta d’auka kenan aranta..
Alhaji Abdullahi sai da su kaka suka saka baki ya janye k’arar da ya maka Adam, aka rufe maganar bataje ga zaman kotuba, kuma sukace abarshi ya cigaba da zuwa zai gane kuransa, idan yana zuwa yana ganinta karshe zaiji zai mayar da ita, wanda su anasu ganin ba’ason auran ace ya mutu gaba d’aya…
Ummin Khairi har rama tayi duk da batasan actual abunda ya dinga mata ba, amma ta kan danne abun saboda yanda iyayen Adam suka tsaya ganin sun kula da d’iyar tata, taso da akawota gida baza’a rasa abubuwan da take boyewa ba wanda tasan dole sai mahaifiya zata iya fad’awa
Safiyya ce ke dama wa Khairi fura don kullum sai ta biyo ta gidan in ta tashi daga aiki, kallon ta tayi tace ” Wallahi har kunyarku nakeji, baya HoneyB” murmushi Khairi tayi tace ” Meye na jin kunya kuma,karki manta kowa da kaddararsa sannan aure ai rai gareshi sai dai kawai muyi Addua Allah yasa hakane mafi alkhairi” kwalla ce ta taru a idonta tace ” Khairi bazaki gane ba Ya muhsin ya tare min duk wani abu da zaisa mace tace kash auren nan ya isheni, ga tarin kulawa duk rigima da neman fada da mace kanyi baya tankamin, sau tari har kunyar kaina nakeji in na masa laifi, wallahi ko tsawa bai tab’amin ba, k’arshe ace ni d’an uwana takai har duka yana iya miki banda tarin b’acin rai da ya dasawa zuciyarki, na tsani Ya Adam na tsaneshi” rufe mata baki Khairi tayi tace ” Kul kina cewa kin tsaneshi karki manta d’an uwankine na jini, kuma bawanda aduniya yake tsallake sharrin shaidan, dama iyakar zaman da Allah ya yanka mana kenan” sosai abun yake cin ranta amam dole ta nuna musu ya wuce awajanta, don asamu maslaha kowa yakoma rayuwarsa daidai, don akanta in ka shiga gidajensu kasan basu cikin walwala..
” AK ya kake ganin waccan yarinyar Abida ta bayan layinku? ina so ka shige min na nemi auranta nanda wata d’aya na angon ce” wata harara ya zuba masa yace “Ni bani da alak’a da ita, idan neman auranka zakai kaje kayi kai kad’ai karka irgamu aciki” hade rai yayi yace ” To meye ne wai hakan, ina kasan sau nawa na shanye irin shigewa Dr da takeyi, haba shikenan karkayi Sabeer zai shige min” jan tsaki Sabeer yayi yace ” Kowane mara tunani irinka? Wallahi Adam ina gujemaka ranar da zakai dana sani arayuwarka, kaida jin dadin aure hmnnn bari dai karna maka baki amma wallahi alhakin Khairi ya isheka dama batai deserving d’in kaba” cike da jin haushi ya tasowa Sabeer saura k’iris suyi fad’a haka suka rabu baran-baran…
Bayan Sati d’aya
Tun bayan abunda ya faru da Ahmad da Bubly Jamila takasa gane kansa, kwata-kwata baya bi takanta abinci ma baya neman tayi, in yazo yagani yaci in bai ganiba ya k’aleta, ya k’ara zama wani silent kullum haka yake, bawanda yasan meke damunsa sai Umar don sai bayan jinyarsane Umar yasan kalar tsiyar Jamila ya tausaya masa inda yace ” Tunda ta zabi haka gara ka k’ara aure, tunda Allah ya hore maka abunda zaka iya rike mace hud’u ma” kallonshi kawai Ahmad yayi yace ” Tashin hankali ne banaso, sannan tun bayan abunda Jamila takemin sai nakeji kamar kowacce mace ma zata iya hakan, yanzu tsoron zab’e nake ma” Umar yace ” Karka cire hope mata nagari basa karewa, kadage da Addua insha Allah zaka samu wadda zata kula dakai”
Tana zaune tana chatting taga an turo wasu kayan babies a bussiness group, kayan sun tafi da imaninta “Bari Ahmad yazo na nuna mishi gaskiya zamu sayi kayan matar nan koda set biyar ne” sallamarshi da taji yasata mikewa da fara’a yau ta tareshi, don da ta watsar dashi anata ganin yamata laifi kuma yafita daukar zafi, sai da takai mashi briefcase dinsa daki sannan ta zauna jiran ya fito daga wanka ta nuna masa kayan, bayan ya shirya ta shiga nuna masa pics din kawai binta da kallo yake, sai da tagama ruwan surutunta yace “shikenan nima sun min kyau, ki saya kawai” zaro ido tayi ” Kaman ya na saya? Wane irin abu kake ne? Nifa na lura tunda cikina ya fara girma kafara tsanata wato shape dina ya tafi sannan na fara muni ko? Dadinta ma ai bahaka da nake ba d’anka ne yasani yin hakan” nan tashiga maganganu harda kirkirar kuka, dafe kansa yayi yace ” Jamila walk out pls” ganin he’s serious yasa ta fice tana k’unk’uni, jan tsaki yayi ” meyasa ma zan kara aurene? Nak’arawa kaina wani tashin hankalin”
Soyayyar Adam da Abida tayi nisa don ranar dayaje mata da maganar tayi accepting d’insa, tunda taga yanayin motarsa kuma tasan Ak suna da kudi shida abokansa, don haka ita da mahaifiyar ta dad’i yakamasu, tuni ta saka Adam ya gaisa da mahaifinta acikin satin da suka had’u, mahaifinta yace ya turo, donshi dama ya k’agu ya aurar da ita tunda tayi shekara biyu dayin candy,bayan ya bar k’ofar gidansune ya fara tunanin yanda zai fuskanci gidansu da maganar auran lokacinne yayi tsuru-tsuru, sai da ya yini yana tunanin abun, daga baya yaje yasamu k’anin mahaifinsa wato baban su Jidda ya fad’a masa, shikuwa yace sai yaji daga bakin Abbansa, don dukansu sun san tsiyar daya k’ulla, takanas suka sashi bayan abun da kwana biyu sukace ya fad’i abunda tayi daya tabbatar suna da alak’a da Dr duk yagama bada labari, sukace to ya cancanci haddil k’azaf, wato hukuncin k’azafi yakamata amasa bulala tamanin, suka cimasa mutimci suka ce gashi ga duniya indai zina ce yake gayyatarta zai gani, shiyasa Kawu yace sai yaji ta bakin Abbansa.
Kama hab’a Alhaji Abdullahi yayi yace ” Shine yace aure zai k’ara ko? Hmnn to ba hannuna aciki, ban hanashiba amma kar a irgani aciki” dake lokacin suna tare da Abban Khairi sai ya shiga maganar yace ” Yakamata yayi saboda zamansa ba macen ma had’arine, kar aje abata goma biyar bata gyaruba” da Hajiya Hassu taji jirine ya d’ebeta ya kayar banda lokacin su Khairi na tare da ita da sai ta fad’a kan cooker gas, suka rik’ota suka kaita d’aki kuka take tana ” Wannan zamani ina zaka kaimu, yanzu Adam har takai yake abu kai tsaye ba ruwansa damu” Alhaji Abdullahi yace ” Ki kwantar da hankalinki dad’inta muna da wasu ‘ya’yan bashi kad’ai bane, yaje duniyace zata koya masa hankali, ki daina zubar da hawayenki sannan kidaina damuwa, kar wani ciwon ya kamaki” da Khairi taji bata ji damuwa canba amma kuma ta tuno rayuwar da sukai, hakan yasa ta tabbatar Adam ya shafe babinta arayuwa, yakamata itama ta ajiye damuwar baya da duk wani memories nashi ta fuskanci rayuwarta, domin shi bashi da asara in wani abu ya sameta…
Har su Kawu Bala da baban Khairi sunje sun nema masa auranta, sudai aransu basu ji dad’in yanayin gidanba, duk da ya lullubamusu akan ai yarinya ce nutsattsiya, shida wasu friends dinsa nagefe suka je suka had’o lefe abunsu, anan ne Ummi tayi magana tace aje ad’ebo kayan Khairi akaisu d’akin muhsin wasu kuma sitroom, tunda zaiyi aure abarwa amarya gidanta, haka kuwa akai aka d’ebe mata kayanta tsaf aka bar masa gidansa, abunda yadanganci bedsheet kwanuka Khairi tace bataso adauko don duk abunda zai tuna mata Adam bataso, sukansu kujerunta da aka debo ko kallonsu batayiba, auran da duka baiyi shekara biyu ba shiyasa kaya wasu kamar sabi, dardn ranar Khairi tayi kuka kamar ba gobe, duba yanda tun tana budurwa ya shiga rayuwar ta tadinga bin k’a’idojinsa tun awaje amma k’arshe ga yanda ta kaya, tabbas tanasonsa amma ya kafa tsanarsa aranta dakansa….
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
31
Ba kunya Adam ya kawo kayan lefe cikin gidansu akan za’akai gidansu Abida, duk abunda yake Hajiya Hassu bata masa magana iyakarta dashi in ya gaisheta ta k’ura masa ido, shikuwa ya sunkuyar dakai don har tsoron kallonta yake, haka aka nemo aunties dinshi suka kai, daga ganin rawar k’afar da Babar Abida keyi sukaji sun raina musu, dama dai yanayinsu talakawane don Abida har suyar awara tasha yi bakin layi kafin tayi Candy, bawannan ne damuwa ba illa zalamarsu da ta fito fili…
Fuska ad’aure ya shigo ya kalleta ” Khairi na rasa me kikayiwa zuriyar mu ne, kiji tsoron Allah ki gyara tsakani na da mahaifiyata, narasa karyar da kika gaya musu, don bana shakka akan dalilin ki take fushi dani” da yasan wutar tsanarsa dake ci azuciyarta da ya daina yarda suna had’uwa,ta ja wani mahaukacin tsaki ta kwanta ta bashi baya, juya bayan da tayi take wani abu ya bi jijiyoyinsa ya k’ura wa bayanta kallo, take yaji bazai iya sake magana ba ya shiga tuno soyayyar da suka zuba, yayi missing d’inta gashi bai isa ya had’a Abida da Khairi wajan diri da komiba, shiga yayi tunani da salon soyayya irin nata…+
Jira take taji ya rufeta da duka tunda yanzu bata da ciki ai bazai ji tausayinta ba, amma sai taji shiru ba masifa ba duka, juyowa tayi taga yanda ya kafe yana bin halittar ta da kallo,take taji haushi da sauri ta tashi tayi shigewarta toilet, cikin borin kunya ya d’aga murya yace ” Aikin banza meye bansaniba, kije kiji da matsalarki” koda yafita tunowa kawai yake da ita a idonsa, sai da shaidaniyar zuciyarsa ta tuno masa affairs da Dr sannan ya watsar da tunanin ta.
Labarin mutuwar auranta ya isa ga Maryam Tafida inda tazo ta sameta takanas, bayan jaje da ta mata sai asannan tacewa Khairi dama tariga tagano abubuwa na faruwa amma bata tab’a tunanin abun zai kai hakaba, sun jima suna hira inda Maryam ta nuna mata taja mutumcinta in yadawo ‘kome’, don tabbas yana sonta sosai amma kar tayi tunanin rabuwa dashi, murmushi Khairi tayi ta ce mata ita yanzu ba d’igon soyayyar Adam aranta don haka babinta dashi ya riga ya k’are, ita kuwa Maryam tace in kika huce zaki son soyayya d’ayace kuma kin damk’ata ga Adam…
Tuni Khairi jini ya tsaya mata hakan yana nufin tagama iddarta, tana iya aure koda kuwa aranar ne
Koda Dr yaji gulmar an saketa kuma harda maganarsa ciki, gaba d’aya hankalinsa ne ya tashi ya nemi number d’inta, domin da bashi da ita ya k’irata yace zasu zo shida H.O.D matsayin dubiyarta, taso hanasu amma sai tace gara suzo kila tasamu inma da wani zargin azuciyar iyayenta su wanketa…
A falon babansu Adam aka saukesu tunda har yanzu tana gidan, sun samu tarb’a mai kyau daga wajan Alhaji Abdullahi kafin shigowar Khairi saida suka nunawa Alhaji ba wata alak’a mai k’arfi tsakaninsu, asalima jarumtarta ne yasa sukan sakata acikin al’amura sosai, su anasu tunanin gidansu Khairin ne, kana ganin fuskar Dr Umar da H.O. D kasan mutane ne masu kamala don ga kwarjini nan kwance kan fuskarsu don haka ma shima Alhaji Abdullahi bai yi kokonton maganarsuba. …
Cikin mutumtawa suka gaisa sannan suka jajanta mata, inda suka nemi yafiyarta aganinsu harda laifinsu awajan zafafawar lamarin, nuna musu tayi bakomai dama k’addarartane, da zasu tafi suka ajiye mata 50k ta nuna bazata karba, kallonta Dr yayi yace ” Haba ai bawani abu bane tunda bamu zo da lemon dubiya ba” murmushi tayi ta rakasu tare da musu godiya sosai..
Daidai lokacin Adam zai shigo gidan, aikuwa cike da masifa ya nufi Dr zai cakumi wuyansa yaji muryar mahaifinsa ” Karka kuskura kace zakai masa hauka, dama irin abunda kake yi kenan k? fice min agida” sai alokacin ma suka gane gidansu Adam ne, da maganarsa suka isa hanya don bak’aramin mamaki ya basu gefe d’aya ya basu tausayi daga shi har Khairin..
STORY CONTINUES BELOW
Bikin Adam bawani shagali akayiba tunda na biyune ga kuma case dinshi da Khairi, amaryace ma dai ta had’a kamunta don tayi falli cikin k’awayenta, don haka kafin kace me har ta tare wasu abubuwan kayan d’akin shi ya zuba don basu da k’arfi sosai, yanda yad’au wata ba mace cike da zumud’insa ya shiga d’akin amarya bako kunya ta ware ta narki gasasshiyar kazarta, bayan duk wasu abubuwa da addini ya tanada Adam ya nufi sauke maitarsa sai dai yaji banbanci bakad’an ba, don zai iya cewa koda virgin ce gaskiga anmasa hanya duk dakuwa d’imbin gyaran da Abida tasha, had’in kan da ta bashi da taimakon tulin maganin da tasha yasa yaji k’ila don matsala da mata kan samune saboda wasu tsalle-tsalle, kuma yayi enjoying ba kad’an ba…
Bawanda ya kawo musu abinci shi yaje restaurant ya musu takeaway don amakircin abida harda d’iga jini a bedsheet bayan ya tashi kanta ya shiga toilet, don yace yajita zam-zam, shiyasa ta lafke tak’i moruwa wai ita lallai taji maza amatsayinta na cikakkiyar Virgin, washegari da ya zagayo tuni yaga yanda Abida ke sarrafashi koshi bai isa gaya mata komi ba abun har mamaki yabashi, amma fa yaji dad’in hakan duk da ko kusa bata isa kama Khairi taste ba d different is clear, sai dai shi jin dad’insa d’aya iyakarta secondary school to yasan ba batun aiki atsarinta.
*Hmm Adam kayi kuskure d’an isaka ba’a boko bane ko aiki, mutum ko bai tab’a zuwa School ba matuk’ar lalataccene zai aikata abunda yaso*
Bayan Sati yakaita dangi ta zaga kuma balaifi sun karb’eta hannu bibiyu, yanzu tafara girki babbar damuwarshi d’ayace Khairi ta sabar masa da abinci kala kala ita kuwa Abida daga shinkafa da wake sai kuwa taliya, hatta miya kala d’aya ta iya normal stew da ake bata iya sarrafa waba, wataran ma sai ta d’ana wainar fulawa as breakfast, gashi harsu oven ya kawo mata da toaster don yasan dama zai iya yiwuwa bata sansu agidansuba, in ta k’ure tayi masa d’anwake, haka yake jurewa, dankali da doya daya kawo sai da taga bayansu ta kyalesu, abunda bai saniba yanda kasan wankin ciki tazoyi gidansa, in ya fita aiki da tsakiyar rana sai atashi ahau soya irish da kwai, dama kawayenta kullum suna hanya da k’annanta guda biyu, da tagama za’ayiwa Inno mahaifiyarta zubi a flask su tafi dashi, kafin kace me wayam kayan break sun k’are, bai kawo komiba yace don batasan yanda ake handling gida bane, kafin yadawo suke watsewa shiyasa baisan ana tara masa gayyaba… …
Khairi kuwa ta nemi abarta taje Jahun tayi kwana biyu ko zata ware tadaina ganin Adam, saboda kullum ahanyar zuwa yake da faman kamun k’afa na ganin ya shirya da ‘yan gidansu, rana ta biyu daya kawo Abida sai da ta k’arewa Khairi kallo taga bata isa nuna mata komiba, gaba d’aya hankalinta ya tashi ta k’ara mik’ewa da shan maganin mata da k’aimi abed don kar yaji zai dawo da ita, shiyasa yanzu da taji Khairi ta tafi Jahun hankalinta ya kwanta. Tana zaune bayan ta gama yanka tumatir da albasa a bowl don yau da wake tayi da mai bata iya sarrafa attaruhu ko vegetables tayi masa miyar da zaiciba, wayar ta ta d’au k’ara tana dubawa taga sunan “ZMN (zumana)” cikin kisisina ta d’auka ” Haba hajiya Abee don kawai kin auri mai kud’i sai ki watsar dani, haba ai baikamata kimin hakaba” sai da tayi wani murmushi tace ” Haba Zumana kasan bazan yimaka hakaba, kawai so nake nayi kwana biyu na fara fita kasan nariga na saba da wasanka ai, kai d’in na dabanne” sun dad’e suna hira wadda rabi batsa ce da tuna kalar rayuwar da sukai..
Tunda ya shigo ta kawo masa abincin walwalarsa ta ragu amma dake ance amarya bata laifi sai yace mata “Queen ban fiya son cin mai hakaba next time pls in zaki dafamin ki soya min miya da sardines, in kuma ya k’arene ki fad’amin” jijjiga kai tayi tace ” Shikenan zan koya, dama inaso naje gidane kaga nayi 3weeks kuma mama batajin dad’i, yakamata naje dubiyarta” shiru yayi har sati uku yakai tace zata fita, ganin marairaicewar da yayi yasashi cewa ” Shikenan gobe sai na ajiyeki, kinga nima na dubata” cike da salo tace ” Ai kasan early kake fita inaga kawai kabarshi natafi, kaga bayan fitarka nake k’arasa gyaran gidan” yace mata shikenan , da dare bayan ya shirya tsaf ya kwanta yaga ta shigo d’akin ta cire gown da ta yini da ita ta zaro nightwear ta saka, ta zo ta kwanata har da damuk’ar k’irjinsa, yana lura tun bayan first week na amarcinsu yagane bata k’aunar wankan dare, abunda bai saniba itafa bata san yin wanka da dare ba so shes not use to it yanzu kuwa bai isa yace tayi adopting ba, haka ya kashe wutar gabansa hanci asama don gaskiya ta jima tana harkoki agidan so gumi yad’an taso ahammata dole ad’anji tashinta, atsawo sati ukun nasu yaga tulin ni’imar da Allah ya masa ada bai damuba, don ko ta abinci ya raina kansa dibga masa mai kawai take, kuma ba’a fiya son hakaba don hakan kan jawowa maza saurin releasing infact anason suma mazan suke cin abinci mai kara ni’ima saboda sperm dinsu dake bada kwan haihuwa, gashi wai har ya sake sabon refilling gas duk abunda yakan fi wata ita yanzu sun k’are sai da ya sayo, abun har mamaki yake bashi, amma yabarshi aransa
Kafin fitar Adam saida ya bata 10k ta yiwa mahaifiyarta sayayyar dubiya, saboda haka tana fita ta nufi arear su Zumanta, dama ta saka nik’ab d’inta, tsabar yanda ya karanceta tundaga yanayin tafiyarta ya gano itace aikuwa tuni ya washe baki, dake yana k’ofar gidan, gidane mai d’auke da d’akin samari guda uku, yau saura shikad’ai sauran duk sun tafi wajan sana’arsu, sai shi tana zuwa suka shige d’akinsa, tun daga k’ofa suke rik’e da bakin junansu har suka zub’e kan katifarsa dake d’akin, zuzutata yake yana shafe k’irjinta, itama batayi k’asa aguwiwaba ta cigaba da maida masa martani daga can naji yana cewa ” Abee wallahi har fushi nake dake, k’irikiri kika hanani yin sex dake gashi yanzu kin bawa wancan ya kwashe romon haba don Allah” cikin rad’a tace ” Haba karka manta tuntuni nace maka ni banason yin zina, kawai rage zafi nakeso kuma kamanta kai karigashi da senate duk sai da ka shanyesu fa yasamu, gashi kamin hanya da hannunka banda nasha magani dayawa wallahi da yakamani, kasan mai aure ba’a layance masa yasan komi” murmushi yayi tare da cakudar k’irjin nata yace ” Hakane na rigashi amma inaso wataran asammin nima, indai don kina gudun kar ajiki ba virgin ne yasa kika hanani to ai yanzu an wuce wurin, koda nayi bazai ganeba, kodan da alama gaulane tunda yakasa gane komi” haka suka gama shan mintinsu inda tamasa wasa da hannunta har yasamu relief sannan har azahar tayi, ta nufi gidansu dama sunyi da Adam zata koma bayan la’asar kafin ya dawo..
Tunda ta shiga gida suka dasa cafta ita da Inno da yanda zasuke wankar Adam, duk ana k’ara koya mata ta bata 5k ta coge sauran, don tanaso ta sayi wani tsumi awajan wata mata da ta saba da ita daga kaita a unguwarsu take, tana komawa gidan shaf-shaf ta dafa shinkafarta ta d’ora miya, tanayi tana murmushin iya shegen da sukai da Zumanta.
Tunda Khairi ta je Jahun take cikin farin ciki, gashi gidan da yanmata wad’anda baifi shekara d’aya ta basu ba, shiyasa ta ware sosai gefe d’aya Anty Asiya na bata abubuwa aranta tana cewa kila Adam ya dawo kwana kusa, d’iyar Anty Asiya Umaima tana zuwa Healthtech Jahun, hakanan Khairi ke joining d’insu tana zuwa duk da kuwa ta wuce wurin, in kaganta bazaka ce bazawara bace especially in tasa Unifoam, har ji take batason dawowa Kano
Kwance yake yana nazari akan tsarin rayuwar dayasa kansa, don kuwa yanzu Ahmad har rama yayi saboda abunda ya faru abaya ga k’arin miskilanci, koda Umma ta tasashi da tamabaya cewa yayi typhoid yake taita sawa ana kawo masa ganyayyaki, alhalin kuwa ciwon Damuwa ke damunsa, Jamila ganin yanda ya watsarta dakanta ta kawo masa kanta jiki da jini itama ai ba dutse bace, ranar yaso bagararta amma da fitina da komi sai da tasa yayi romancing d’inta k’arshe yana cikin yi ya tuno da Bubly, kawai ya tashi ya fad’a toilet yabar Jamila amatse don bak’aramin tada mata hankali yayi da wasanniba, ranar cikinta yayi ta murd’awa, tayi ta fushi dashi data tasa shi da mita, ya gaya mata gara taji yanda yakeji aduk sanda ya bijiro mata, daga baya dai in ta kawo kanta yakan biye mata amma fa yana da haushinta aransa, cikinta yakai wata bakwai yanzu so ya fito yayi turtsetse don haka ya fara bata kud’in sayan kayan babies, dalilin haka ne yad’an sassauta yake ware mata fuska saboda darajar babynshi
Suna zaune suna cin tuwon shinkafa miyar zogale, yaro yayi sallama yace ana sallama da maigidan, Alhaji Lawan mijin Anty Asiya ya fita bayan kaman minti talatin sai gashi yashigo cike da murmushi, sukuwa su Khairi da suke shan dariyar wani film da suke kalla basu ma kulaba, yayiwa Anty Asiya nuni da ta sameshi adakinsa, sai da suka gama cin abinci suka shirya bacci, har ta ja bargo zata fara bacci kawai Anty Asiya ta shigo d’akin tace ” Tashi Khairi Alkhairi ke bibiyar rayuwarki, nazo miki da Albishir mai dad’i” tashi tayi ta zauna tana facing d’inta Anty Asiya tacigaba ” Yanzu wannan kiran da akayiwa Alhaji akankine, Alhaji Yunus ne yazo akan yaganki kuma yana sonki da aure” Wani irin fad’uwar gaba taji tace ” Na bani Anty nikam yanzu ban shirya aureba, so nakema sai na dora degree dina sai nayi kar naje muke matsala da miji akan karatuna, kuma ma shi ba ajigawa yake aiki ba” dak’uwa ta mata tace” Kinji yarinya zuba miki ido za’ayi kuma, baruwanki da wani degree kyayi gidan miji, kuma aiki dayake ajigawa bazai hana ya aurekiba sai ya ajiyeki kano tunda yana da mata, karki manta yana da damarsa fa to meye zai gagareshi na yin gida biyu, mutumin kirkine na tabbata zakiji dad’in zama dashi, sai dai in ko yaro kikeso kaman Adamu” shiru tayi tace ” Nikam yanzu banason cunkuso azuciyata ban gama warkewa daga darasin maza ba” ta fada tare da share hawaye ganin haka yasa Anty Asiya ta shiga mata Nasiha da kwantar da hankali sannan ta fice..
Zaune suke a hall d’in kowa ya nutsu saboda sun san halin Dr Ahmad baya son hayaniya da makara, tun kafin cikar time dinsa da minti goma hall din yake cike, sai maganarshi ake har so take taga waye wannan ake tsoronshi, da sallama ya shigo cikin Hall d’in inda kowa ya bada attention gareshi, kallo ya bisu dashi d’aya bayan d’aya ya hangota Unifoam d’inta ya banbanta da nasu kad’an
Hello Fans inason jin ra’ayinku naga masu son Adam da Khairi, da masu son Khairi ta sake aure
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
32
Dedicated to Team Adam… 😍
Sai da yagama lecture d’insa sannan ya nuna Khairi yace kar ta sake zuwa da irin wannan unifoam d’in yasa kansa ya fita, bata wani damuba saboda tasan da zarar yayi magana da Director makarantar shikenan ya wuce, jan tsaki tayi bayan sun zauna suna break wayarta ta ta d’au k’ara, new number ce don haka tak’i dagawa, sam batason damuwa don kwana biyu da suka wuce wani a ma’aikatan asibitinsu ya dinga kiranta, lokacin taji takaicin zawarcinta in ba hakaba wasu basu isa da sumaka maganaba amma yanzu gani ake kazama atiti dole ka kula kowane banza…+
Yau sam daya tashi baya jin dad’i shiyasa k’arfe uku nayi ya fito daga office d’insu ya nufi gida, yana shiga bakinsa d’auke da sallama”salamu alaikum” agigice ta zabura ta amsa kamar taga abun tsoro, da mamaki yake binta da kallo “ke kuma meya sameki haka kika zabura? kuma ba kin fara baccine ba” cikin in’ina tace ” A’a ammm eh ban tsammaci ganin ka bane, sannu da zuwa” yace yawwa tuni tayi switching off wayarta, don dama suna tsaka da vedio call ne da Zumanta, wucewa yayi d’akinsa ya watsa ruwa ya zira jallabiya, itakuma tana can tayi tsuru don bata d’ora girki ba sanin wataran sai biyar da rabi ko shida yake dawowa ta sakankance, muryarshi taji yana k’iranta da hanzari ta nufi d’akin nasa, akwance yake yace ” Don Allah kawomin abinci haka kad’an, naci kafin nasha magani inajin kaman zazzabi keson rufeni” sunkuyar dakanta tayi dake ya rufe idonsa ya d’auka ta fita, k’ura masa ido tayi tarasa me zata ce jikinsa ne ya bashi ana kallonsa ya bud’e ido ” A’a ya naganki azaune, pls kiyi sauri” marairaice wa tayi ” ganin baka dawowa da wuri yasa banyi abincin ba, da yanzu nake jiran sallar la’asar nayi” dake yanajinshi somehow ga takaicin haukanta da take masa da store yace ” Wai meyake damunki duk tsawon zaman da kike acikin gidan nan me kike?” hak’uri ta shiga bashi sannan ta tafi kitchen d’in, indomie ta dafa masa ta kawo yace ” Abee ba k’wai ne agidan?” mutsu-mutsu tafara shejaranjiya ya shigo da robber crate wanda ke zuwa 18 each guda biyu ace har sun cinye, ganin tayi shiru yasan amsar ‘eh ce’ amma akwana uku ace sun cinye shi, jan tsaki yayi yace ” Abee bansan meye damuwarki ba, komi alokaci k’ank’ani yake k’arewa, ina kasa gane inda suke tafiya don bansan sanda mukaci k’wai ashirinba balle ace ya kare dukansa” tashi kije sum-sum ta tafi, abunda bai saniba ita duk wanda ya tako gidan daga unguwarsu sai an masa soye-soye ita lallai asan ta auri maikud’i, ko tsakiyar rana ne kodai asoya maka irish ko doya da k’wai dama abunda ta iya kenan, in indomie kakeso haka za’a dafamaka ita da kwai uku ko suya in mutum dayane, haka tsarinta ke tafiya, kaji kuwa bai isa sayosu da yawaba ya dauka zasuyi kwanaki, yini d’aya za’a cinye akwai randa ya shigo da kajinsa guda uku, ta soyesu kashegari ya zo da dare yace ta masa pepper chicken, baisan kaza d’aya tasawa mahaifiyarta a flask ba, tace ai saura fiffike da k’irji, kama bakinsa yayi ranar bai ce mata komiba, shiyasa yanzu ya tanka mata. Adam an gamu da tururuwa uwar jido ta d’iba sannan ta narki kayanta taci tayi nak…
Kaka ce ta kwanta jinya sosai wanda har sai da takai an cire rai, hakan yasa bayan an sallamota daga asibiti zuriyarta tururuwa wajan ganinta, yau yakasance gidan cike da ‘yaya da jikoki harda surukai, Adam ma yazo da Abida inda bayan 1 hour tace bari taje gidan auntynta dake kusa dasu, don gaba d’aya sai take jinta atakure duk yan uwan sunyi yawa, kuma tana zaunen ake sako hirar Khairi, tana fita tayi dialling number Zuma suka had’e don ya rage mata b’acin ran da ta shak’a, banda sharrin shaid’an meye basayi ita da mijinta, amma shaid’an ya raya mata kawai babu romance irin na Zumanta, shikansa daya ganta ranar sai da ya yabawa Adam don tayi b’ulb’ul tayi fresh komi nata ya cika, anci dadi an wartsake..
STORY CONTINUES BELOW
Dake jikokin kaka yawanci yini zasuyi su Jidda da sauran k’ananun mata suka yi girki awurinta, suka zuba a plate suna hira, kallonsu Safiyya tayi tace “Ya Adam ya kwafsa mana da tuni da Khairi awurin nan fa, amma yazo ya d’auko mana dumamusau yanzu har ta tafi yawonta, k’iri-kiri yake hana Khairi yawo gashi ita wannan ba aikin amma ko sati shida basu cikaba tana yawan raba kwalliyarta a titi” shewa Jidda tayi ta kalli Salma tace “Haba mu zamu baki labarin iskancin da muka tarar dasu sunayi, mukaje muka tarar k’awayenta su biyar gayyar bleaching fuska duk ta zama kalar kamfala nan fari nan bak’i, sun baje ta dire musu plates da soye-soye yanda kikasan garada goma za’a ciyar ita kuma an buga d’aurin kirji da wani lace na lefe dan dubu saba’in dinnan Royal blue, ita ga matar mai kudi sai zuba suke suna kurantata, wallahi na tausayawa Ya Adam don ya d’ebowa kansa” take ran Safiyya ya b’aci tace ” Shi yajawa kansa ai, yanzu ina amfanin ballagazar mace, wallahi tunda akai auran nan duk wanda yaje sai ya taho da maganarta abakinsa, kwanaki da Baba ta Kura taje kinsanta ba rufi, tazo tasamu Mama ta gaya mata taje tafi minti talatin wai Abida taje mak’ota yawo, da ta dawo sai gashi ta kawo mata plantain da rana tsaka da kwai itama ta zuba ta koma gefe tace wallahi plate da yarinyar nan ta share ko Adamun bai isa cinyeshiba” Take suka bushe da dariya sukace wayaga Madaka wato dakin take na abinci, cike da iskanci Sajida K’anwar Jidda tace ” Tada komad’a tazoyi ko wankin ciki, gidan father babu a unguwama babu dole yanzu an gani jiki ya matsa” kai iskancin Abida dai babu dadin fade, to shi kansa oga Adam duka auren baifi sati biyar ba amma har yafara shiga tunani, bakomine yafi damunsa ba irin yanda yanzu tunanin Khairi ya addabeshi, gashi batanan hakanan zaiyi hiding no yakirata yaki magana kawai yaji voice d’int, wani irin missing d’inta yake infact komi nata yake missing, tun daga sanyinta zuwa girkinta, dab’iunta kulawarta da kunyarta, uwa uba taste don ko kusa Abida bazata kamataba, abunda bai saniba basu da sana’a so fingering itada Zuma shiyasa taste d’inta ke raguwa, anayinshi akai-akai gashi bisa turbar shaid’an duk dan tudun ciki ya zaizaye..
B’angaren Ahmad kadaran-kadahan suke rayuwa, ita Jamila ta mik’e k’afa kishiya babu, tunda gashinan suna expecting baby ne, duk wani abu daya kamata Ahmad ya bata kud’in da zata tanada, shima anasa b’angaren akwai kayanda in ya shiga store yagani yakan sayo mata, iyakar fita hakki yana k’ok’arin yi, abunda ya rage shine walwalarsa amma dake Jamila ballagaza ce bata lura, domin macen da ta iya takunta koya taga sauyi a mijinta tana ganewa, kuma zatayi k’ok’arin ganin abunda yasa hakan, ganin yanayin da suke ciki ne yasa Ahmad karbar tayin da aka masa a B. U. K yana zuwa duk ranar Saturday yanawa yan PGD lecture, saboda bai fiya son zama ba, yana ganin yanda aka maidashi soko, bayan sau tari zaiga wasu abokan nasama basu kaishi kula da gida da tattalin mace ba amma hankalinsu akwance banda shi, aikuwa kamar ya bata lasisin yawone sai take ganin shirun da yake mata ai isar tane yasa tunda tazama uwar yaransa, bazaiso rabuwa da ita ba ko b’ata mata rai, ji take ita kakarta ta yanke sak’a, har kurari take cikin k’awaye isashiyar mace tilo a wurin Ahmad Jahun..
Gyara zaman mayafinta tayi tare da kai wata loman taliya ta kalli Suwaiba ” Kai k’awata zanso ki koyamin wannan dambun k’wan, don wallahi yamin dad’i” murmushi Suwaiba tayi tace “Aikuwa yau zan koya miki, da zarar kin iya kinsha kwana kenan” sallamar Bangis sukaji gaba d’aya suka had’a baki suka amsa masa, abunda zai baka mamaki Suwaiba ko tayi tunanin yafa mayafi akan rigarta da takasance mai karamin hannu ga kirji tankar abude kasancewar wuyan rigar yamata yawa, suka dasa hira har da Abida sai ka rantse Bangis macene don dukansu kusa-kusa suke, dama haka gidan Suwaiba yake maza kala-kala zakaga suna shigowa ana shan hira dasu, bazawarace da yaranta biyu, tazama k’awar Abida tundaga satin kawota da tashiga makota asunan gaisawa, gidan bedroom dayane da falo sai karamar baranda haka za’a cushe ayita tafka hira…
Yafi minti goma yana k’ofar gidan, gashi yayi k’iranta yafi sau biyar tak’i picking, ransa ya b’aci matuk’a yana tsaye sai ga wani saurayi da sukan zauna opposite din gidan nasa dake da shago awurin, sai yatambayeshi ko yaga mace tafita agidan, yace eh ga gidan da tashiga can ya nuna gida mafi k’ank’anta alayin, don duk yawanci manyan gidajene a unguwar ya nufi k’ofar gidan, Allah ya taimakeshi sai ga d’aya acikin yaran Suwaiba ya fito yace ” Kai jekace Abida tazo mijinta yana jiranta” yaro bai kai ga shiga gidanba sai ga Abida ta fito bayanta kuwa Bangis ne yana ” Haba wa ai wallahi mijinki ya godewa Allah ya samu mace mai dad’in kalami” turus tayi tana zare idanu, daga ganin yanayinta Bangis ya tabbatarwa kansa shine mijin nata tuni ya koma cikin gidan, ita kuwa Adam bai mata maganaba amma yanayin fuskarsa tasan rai zai b’aci, azuciyarsa yake raya yaso yaga fuskar Bangis dakyau wallahi da sai yasa an koyamar hankali, banda ma yayi wayon komawa cikin gidan da ba abun da zaisa bai cakumeshi ya kwad’a masa mariba..
Yana zaune kan kujera ya hard’e k’afa yana jijjigata cike da bakin ciki ” Abida yanzu k’imarkine ace har wani namiji yasan dadin kalamanki, tukunna ma gidan dakikaje ba gidan matar aure bane? Amma har take bari irin yan iskan unguwa ke shigar mata gida, ke kuma har kika ware baki yasamu damar yimiki magana kowacce” shiru tayi tana zunbura baki, tsawa yasa mata yace ” Bazan d’au haka agidanaba, ki fita bada izininaba sannan ina miki magana kina cika kina batsewa” Adam jira yake yaji ana bashi hak’uri yanda Khairi ta saba, sai yaji shiru asalima sai murgud’a baki take irin na tacac-cun marasa kunyarnan na k’auye, ji yayi kaman ya kifa mata mari amma ina yanaso karya sabawa kansa da dukan mace don yasan bai daceba cikin k’unk’uni tace ” In kagama maganar bari na kawo maka ruwa da abinci” binta da ido yayi yau shi akewa haka acikin gidansa, ehh lallai kuwa yasha yayi fadan da gamgan amma bai taba ganin Khairi tamasa hakaba asalima bata bari yayi dayawa batai calming dinsa da kalmar kayi hak’uriba, kuma takan daure taki nuna fushinta ayayin da yake fad’an, bai sha mamaki ba sai da dare yayi ya tab’ata ta hau tureshi ita lallai tana fushi dashi ya mata fad’a, har tana mitar ai d’azu yagama hayaniya da fada ita kuma gaskiya ko agidansu ba’a mata hakan, alallami ake binta in anaso tayi abu, sai asannan yace ” Amma koda nake miki fadan ai buntsurar baki kike, ba wani girmamawa amatsayina na mijinki” sai da yayi aikin rarrashi dakyar yasamu ta bashi kanta, shiyasa washegari ya yini yana tunane-tunane dama idonsane ya rufe dason yayi aure da wuri ya tusawa Khairi haushi yasa baima tsaya bi ta hankali da tarbiyya ba ya aurowa kansa jaraba.. Dama sautari maza basa gane ni’imar da Allah ya musu sai sun rasa, shine kalmar Allah karya kawo ranar yabo, kaga matarka na kokari ka raina sai batanan zakaga ashe ita yar aljannace
Alhaji Yunus kam ya hura wuta saida yazo zance wurin Khairi, haka bataso ta zira hijab zata fita anan Umaima tace ” Haba Anty haka zaki fita? Gaskiya ki canza shigar jikinki ga gown nan kiyi rolling” dariya tayi tace “Haba sai kace wata ‘yan mata, kawai kibarni na fita hakan wannan ai sai ku” fir Umaima ta hana ta fita sai da tasa ta canza ta murza hoda tasa gloss sannan, shikuwa Alhaji tuni ya mik’e a sitroom an kaimasa drinks yana jiran ta, da sallama ta shiga bayan nan ta gaisheshi, anan yamata bayani shi ba yaro bane da Aure yazo idan har yamata zaiso nanda wata d’aya ayi awuce wurin, tace masa zata yi tunani yace ba matsala, envelop ya ajiye mata yace ta sayi kayan kwalliya bai iya zab’e ba, ba magiyar da batayiba akan ya hak’ura yace sam sai ta karba, haka ya fita ya tafi…
Koda ta shiga falo da envelop ahannunta shewa Umaima tayi tace ” Kaga irin abunda ake so amma samarin yanzu sai rowar tsiya” rankwashinta Anty Asiya tayi tace “Ke kuma sai aukin san kudi, naga sanda zaki zab’i miji” basu labarin yanda akai tayi sannan suka bud’e envelop 30k ne aciki kaman had’i baki sukace “A’a gaskiya sunyi yawa daga zuwa kuma” Sai kuma Anty Asiya tace “Bazanyi mamakiba kwanan nan aka bashi muk’ami amma na manta kalarshi, ance dai suna manyan jiha, kuma kinga duka baifi shekara arba’in da biyuba” yamutsa fuska Khairi tayi tace ” Nidai gaskiya za’a mayar masa, don ni bazan iya auransaba, kinsan ban iya tashin hankaliba naje muke rikici da matarsa” tafa hannun Anty Asiya ta shigayi ” Kijimin yarinya ai bakyau maida kyauta baya, balle yakai yayi ba takura kansa yayiba, kuma ba rokarsa akayiba kudi dai kinci ko ada ai ana bada toshiya mazan yanzune suka zama marasa zuciya” da haka dai suka cigaba da zancen Alhaji Yunus amma fa sam ba sonshi a zuciyar Khairi haka kuma ba tsanarsa..
DUTSE
Sai da yasha rabin kunun gyadar da Umar yazo masu dashi sannan ya maida bayansa ya jingina da bango, idonsa lumshe yad’an fad’a kad’an hakanan in ka nazarceshi baya cikin nutsuwa sosai, shigowa Umar yayi d’auke da Tray wanda kanshi akwai flasks na abinci da plates da spoon, har ya ajiye gabansa bai saniba, sai da ya dafa kafad’arsa sannan ya bud’e idonsa da suka fara canzawa zuwa alamun ja kad’an Umar yace ” Ahmad har yanzu matsalar Jamilan ce ko kuwa watace daban?” yak’e yayi yace ” Banda tata wacce zaka gani, sam yanda kasan bataga canji atare daniba kawai shagalin gabanta take” Umar yace ” Haba abokina kaima fa kaika so ayi hakan, ga matanan kala-kala anemo maka tagari ka aura ka wuce wurin, in ba hakaba wallahi sai wani ciwon yakamaka iyayenka keda asara, tunda tana iya wasarere dakai bata da damuwa” ajiyar zuciya ya saki “Bazaka ganeba ni kawai ji nake kowacce zata iyamin hakan, amma kuma inason k’ara auren kwana kusa kasan kishinta jira nake kawai ta sauka lafiya ayi neman da auran kar ya d’ara wata biyu, yanda sai an kusa zataji labarin kaga shikenan” bushewa da dariya Umar yayi yace ” Wallahi koyaushe kazo da maganar aure kasa aranka za’ai rikici, don kishi dolene kawai ka zauna kana jin tsoro zaka kashe kanka, amma shikenan mujira ta haihun kafin nan zamuga wacce ta dace ka aura…
Naga comments ina jin dad’i, acigaba har sai mun kai gaci inayinku sosai
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Dedicated to Team Ahmad… 😍
33
Sai da akayi kwana uku sannan ne Khairi tabawa Alhaji Yunus amsa, hak’uri tabashi akan yayi hak’uri tanason komawa gidan mijinta, nuna mata yayi bakomi haka Allah ya k’addara shima zaizo hakan, amma idan bai yiwuba yanaso ta bashi dama akaro na biyu, tunda ta dawo ta fad’awa Anty Asiya suke zuba mata mita, ita da Umaima sai Nabila cike da takaici Umaima tace “Ni ba korarshine damuwa ta ba, aa fad’in zaki komawa Adam ne takaicina wai da gaske kike nufi ko kuwa don korar shine kika fad’a? ” Murmushi tayi tace ” Eh don na koreshine yasa nace zan koma, amma da zaki gane ba namiji yanzu a tsarina kawai so nake nakoma kan aikina, nayi requesting tafiya karatu, na nemi admission don naji an kusa fara sai dawa foam” Anty Asiya tace ” To sai ki zauna ai, ai kodan abunda Adam yayi yaci ace kin tattara nutsuwarki kinyi aure, shi yanzu ba gani yake yayi aureba so kece da zawarci gara kimaida kai kiyi auran, kar yayi tunanin jiransa kike” haka sukaita mata mita itakam taja tunga tace bawani namiji da zata k’ara yarda dashi, wani irin tarin Alk’awari da soyayya ne Adam bai mataba amma k’arshe saboda rashin imani har tana da juna biyu ya iya dukanta tare da saki,banda tulin zargi da jifanta da munanan kalamai, gani take shiga rayuwar wani kaman kasadace, tana iya auran wani shima taga yanada wani halin daban..+
Kamar koyaushe basa kwana biyu basu lek’a gidan kakar Khairi ba, yauma suna gida sun baza tabarma atsakar gida suna cin dafaffiyar gyada, kallonta Kaka tayi tace ” Wai ni Khairi yaron nan bai dawo Kome bane? Ko kuwa ke kika hanashi?” sunkuyar da kanta tayi don wannan shine karo na uku da Kaka ta mata wannan tambayar, ganin yanayin ta yasa Umaima magana tace ” Kaka ai tagama auran wannan D’an rainin hankalin, bai zoba kuma koda yazo yasan tafi k’arfinsa” murmushi Kaka tayi irin na manya tace “Umama kenan wato ke bazaki gane yanayin aureba, na tabbata har yau suna son juna kuma daga ita harshi bazasu so wani kaman junansu ba, ke tsiwa ke damunki inaga shiyasa kika kasa tsaida miji” Tabbas Umaima nada tsiwa shiyasa da tagama jin labarin abunda Adam yayi, gani tayi ba mai laifi irin Khairi gani take ya za’ai kabari namiji yake takaka yanda yakeso, Umaima tace ” Kaka nasan bansan tsakanin miji da mataba amma fa shi har ya samu yayi aure a wata d’aya, don ya nunawa duniya baya buk’atarta, don haka duk son shi da take ai dole taja gefe, don ba’a kome batare da had’in kan waniba” dukansu sunyi shiru can Kaka tace ” Hakane amma shikenan, ke kam Umama da k’uruciya akanki, ita kinga tayi shiru tanason mijinta har yanzu” jin haka yasa Khairi tace ” A’a Kaka ni mantawa nake da rayuwarsama, ni yanzu sai babba banda irinsu Ya Adam” daga Kaka har Umaima dariya sukai, don yanda take magana on top of her voice wai ta nuna she’s not into him anymore, sai da suka gama yini su sannan suka fito, daga nesa Umaima ta hango Ahmad ta tab’o Khairi tace kinga Dr Ahmad, ayatsine Khairi tace ” Waye hakan kuma” ganin har sunzo inda yake don yayi parking ne a opposite mak’otan gidan Kaka, suka gaisheshi ya amsa don hakan na faruwa indai yazo Jahun, wasu baya gane fuskarsu ma,amma yasan yawanci students d’insa ne…
Sai da suka isa gida sannan sai Umaima take ce mata ” Wanda rannan ya maki maganar Unifoam fa” Khairi tace ” Ohh nagane wannan visitor d’in kenan” anan Umaima ta bata labarinshi harda na matarshi, cikin mamaki Khairi tace ” Kai Student sun gamu da gulma ya akwai kuka san labarinsa?” Umaima tace ” D’an uwansu Nabila (Yarinyar mak’otansu) ne fa” Khairi tace ” Amma dai matar nan tasa tana ruwa, inda Adam ne ta isa mashi hakan, kodan kusan halinsu d’aya”
Yau Inno tazo gidan d’iyar ta kasancewar monday ne, shiyasa suka sakankance suke zuba hirar su, inda gwanar ta zage aka sami buhu irin na semovita ta zuba mata kayan abinci daga kan spaghetti da macroni cous-cous harda tin na peak milk, shirgi guda banda wanda aka dafa mata da tulin nama, kazace guda d’aya akai dambunt, tasan oga jiya ya kawota akan tamishi pepper soup, amma tayi musu dambunta yanda suna hira suna afawa abaki, ta ajiye masa drumstick guda biyu,nan gefe ga kwalin five alive dinsu, ko cup Inno batayi amfani dashiba, sai dai ta d’aga kwalin ta sha, ta kalli abida bagan ta ajiye kwalin tace ” Kai ikon Allah Abuda kinga yanda kikai shek’i ashe irin wannan dad’in kike ci, arzik’i yayi” cike dajin dad’i tace ” Haba ai dad’i ba’a magana Inno, shiyasa yanzu kema ki walwala d’iyarki ta auri mai arzik’i, kema ki wataya” barima yanzu na dafa mana shinkafa ahad’a salad (coleslow), aikuwa kafin kace me an dafa aka dafa kwai guda goma aka yanka zuwa k’arfe biyu tagama komi, sai da aka zuba mayonnaise da Salad cream duka ciki, aka zuba mata a uban plate Inno nakai Loma tace ” Kaii kice harda abun nan mai d’an tsami-tsami na shinkafar gidan biki, gashi wannan har yafi na gidan biki fitowa, ko cokali batayi amfani dashiba don haka hannunta gaje-gaje da farin mayonnaise, suka tsinkayi sallama daga bakin falon, sai da aka sake akaro na uku sannan cike da jin haushin an katse musu hira ta isa wajan tare da bud’e k’ofar, turus tayi tana k’irk’ira murmushi lokaci d’aya zuciyarya na bugu, har sai da suka karanci rashin nutsuwa atare da ita, asanyaye tace ” Mama ashe kune k’arar Tv ne ya hana muji, bismillah kushigo” suna shigowa Inno taji wata iriyar kunya takama ta, saboda tanda tayi jage-jage akan carpet hannu bakyan gani, ga tulin kwanuka gabanta, donkuwa duk wani abinci dayake gidan sai da aka zubo mata shi, samun wuri su Hajiya Hassu sukai, sannan aka gaisa sai sunk’ewa ‘ya da uwa suke, sukuwa basu nuna komiba, cikin yanayin dattako Hajiya Hassu tace ” Dama mun shigo unguwar takune shiyasa naga yakamata muzo mu duba lafiyarku” cikin sunkuyar dakai tace ” Aikuwa naji dad’i nagode” ta tashi zata nufi kitchen kawo musu drinks, anan Hajiya Hassu tace ” Abida ba sai kin wahala ba kinga sauri muke muna da gaishe-gaishe dayawa yau, mungode” suka nufi k’ofa
Sai da suka tafi sannan suka ajiye ajiyar zuciya Inno tace ” Gaskiya ni banji dad’in zuwansuba, bakya ganin bamuji kunya ba? Kinga had’amin abunda ya dace na tafi gida kar shi maigidan yazo” bataso ba haka ta had’a mata komi ta rakata bakin titi tare da bata dubu biyu bayan ta biya mata na Napep…
Tana tsaka da gyara wurin ya shigo, duka lokacin k’arfe uku da kad’an ta gota, kodaga yanayin wurin yasan anyi bak’ine kuma hardly ace familyn shine don ya lura tunda ya aureta daga ganin farko basa zuwa, sai nata gayyar da k’awayenta na lungu, sai da yadawo daga sallar la’asar sannan ya nufi dinning, tun daga kallan coleslow d’in yaga bazai iyaciba, mayonnaise tayi yawa, tana gefe tana firirita da farin yaudara yace “Ina pepper soup d’in” sosa kai tadinga yi tace ” Am nayi bak’ine shine na soya masu kazar” shiru yayi bayau aka faraba ya kawo abu akasa yimasa, wata sa’in ma baya ci gara wannan yasamu drumstick, aure gaba d’aya baiyi 2 month ba amma iyakar gajiya yai da Abida, haka ya tura white rice d’in ya tashi yabar table kotakan kazar baiyiba, tunda ya shiga d’aki yake jin missing d’in matarsa, k’aryane yace baya son Khairi kawai ta bada kantane ga wasu, shine abunda ke cimasa tuwo a kwarya, sau tari yakanji son ya koma mata amma ina duk da he’s not sure akan they have affair with Dr amma kawai ai ta sake musu da yawa, shikuma yanajin bazai iya d’aukar hakan ba, kwantawa yayi yana shafa gefen gadonsa yana tuna wani moments, bayanda za’ai yace Khairi tayi abu tak’iyi , bayan haka koya taga baici abinci yanda ya saba ba sai tasan yanda akai tasashi yayi, ko kuma idan taga mood d’inshi wani iri sai tasan yanda akai ya ware ya koma normal, har zolayarshi takanyi as aishi kaman baby yake awurinta ta kwantar da kansa ak’irjinta take shafa masa kai like a baby daya daga cikin salon kwantar masa da hankali kenan, ita kuwa Abida ba ruwanta fagen sauke buk’atane kam ana bashi had’in kai, duk da wata sa’in haka zaiji iska na fita agabanta, yana cikin tunanin ne ta shigo tana kumbure-kumbure, ta zauna tana ta hakan ganin bai kulataba tace ” Wai Adam meye haka akan na bawa bak’i abu zakamin haka, kadinga wani kumbure-kumbure? Shikenan basai kamin hakaba kayi hak’uri Insha Allah bazan k’ara bawa wani nawa abu ba in yazo gidan nan” kallonta yayi lallai ta raina masa hankali yaja tsaki ya tashi zaune yace ” Abida kinfi sanin kowa ni ba matsiyaci bane, domin kuwa ban gaji tsiyaba ina tsiya ina abinci? kinfi kowa sanin nafi arzikinsa, duk wacakar da kike da kayan store ina tanka maki? Kuma kinsan bakowanne namiji zai d’au shiritar da kikeyiba ko? Duk haukan da kike ina sane dashi, har kina da bakin wai ina miki wulakanci? Acikin satikan nan bazan irga crate nawa muka ciba, banda kayan tea sai kace mu muka fi kowa cikin zani, ace nakawo abu acikin gidan nan ban isa amin yanda nakesoba, to ki kiyayyeni banason banzanci wallahi” Kawai sai ta fashe da kuka ta fara magana ” Eh gara ka gayamin kace ina satan maka kaya, wato saboda ni d’iyar talakace saboda haka ina d’ibar maka ko? Basai ka gayamin maganaba, amma dai ai ba abanza aka auroniba nima ana morata” Abida ba kunya take sa’insa dashi, tunowa yayi da Khairi izza da isar da yake mata baisa tana masa hakan ba, sai Abida da tazo lokacin da yarage fada da hayaniya, ranar da tunanin abun ya kwanta.
Hajiya Hassu kuwa tun ahanya take mita ashe abunda yan uwansa suke zuwa suna fad’a ba k’arya bane, ba abincine damuwarta a’a haukan ne taga yayi yawa, an baza kaya sai kace ana biki, amma bakomi shi ya sayawa kansa ai, hak’uri Hajiya Aisha ta dinga bata tace ” Kinsan uwa mace bata fiya zuwa gidan diyarta ba, k’ila saboda tazone zumudi yasa aka karramata” itadai Hajiya Hassu sam abun bai mataba don labarai da yawa kanzo kunnenta…
D’aura links yake yana sauri zai nufi Jahun suna da meeting a school, don haka baison b’ata lokaci, tana tsaye ta hard’e hannunta akan k’irjinta da tulelen cikinta da bai wuci sati biyu ba EDD d’inta tace ” MyOne wannan kwalliya haka? Gashi kuma nasan ba’a fiya d’aurin aure ranar wednesday ba” Murmushi yayi halin kenan fa ya d’au perfumes ya fesa sannan ya d’au jakar System d’insa ya isa jikin k’ofar tace ” Wai ya nayi magana kabawa banza ajiyata, ko don zaka zancene yasa ka kasa amsamin tambayata” har idonta ya ciko da kwalla ya kwashe da dariya yace ” Sweety kenan karki damu zani Meeting ne, kuma ma waye zai ajiye mace kamarki yake zuwa zance ga iya kula ga tariraya” ji tayi kaman ya caka mata mashi don bazata yaudari kantaba, magana ya dab’a mata, tasan batayin abunda ya irga, dole taja bakinta tayi shiru ta bi bayansa domin rakiya, kafin ya tada mota yafad’a mata yanason tamasa alkubus miyar agushi sai cucumber juice, tace shikenan.. Sai da ya tada motar ya tafi sannan takoma ciki.
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Salam fans kwana biyu na shiga hayaniyar biki shiyasa baku jiniba, amma naso weekend dinnan nayi long chapter
34
Kwana biyu Adam ya kasa gane kansa, duk yanda yaso ya daure tunanin Khairi sai zuciyarsa ta masa taurin kai, har takai Abida ta fara complain rashin sakewa da yawan tunanin da yake, hatta Hajiya Hassu da take fushi dashi ta lura kuzarinsa ya ragu, kuma hasashenta yazama daidai tabbas Adam kewar matarsa ke damunsa, kamar yanda tunanin ya aureshi haka yau yake kwance kan kujera ya lumshe idonsa tamkar mai bacci, sai dai ba baccin yakeba abubuwa suka taru sukai masa yawa, tunowa yake da sanda Khairi ke ce masa kar yayi abunda zai zo yayi dana sani, gashi tun ba’aje ko’inaba ya fara, yanzu haka Abida bata gidan kuma baisan ina ta tafiba, don daga cewa zata mak’ota shikenan shiru yayi ta kiranta ta kasa d’agawa, hakanan ya aika yaro gidan Suwaiba ta bar gidan, jan tsaki yayi yana haka sai gata tayi sallama daga yanayinta kasan bata da gaskiya, bata tsaya ya k’are mata kalloba tayi sauri ta shige d’aki ta watsa ruwa bayan tayi sit bath da wani maganin mata da ta sayo, tsabar yanda ranshi ya b’aci yarasa ta ina zai fara mata fad’a, bayan ta kammala ta saka kayanta ta nufi falon tana cin magani (fushi), d’aya daga cikin d’abi’arta dake bashi haushi kenan, tayi laifi ta fika fushi cikin b’acin rai yace “Abida ina kikaje batare da izini naba?” cikin fitsara tace ” Dama tunda nace mak’ota ai makotan ba mutum daya bane, kuma karka manta sunnar matane kara unguwa akan wadda aka sani” Fada ya shiga mata yana jadda da mata bazai dau rashin kunyarta da gantaliba, ya hado da fadan zuwa da yake daga aiki ya tarar bata nan, kuma da shiga ta rashin kunya take fita mayafi ko wata budurwar albarka, aikuwa tuni ta mike azafafe tace ” Gaskiya idan gajiya kayi dani ka fadamin, kuma dama na gane kwana biyu hankalinka baya cikin gidan nan, baka tani to wallahi Allah zai bimin hakkina” kawai ta fashe da kuja ta ruga bedroom d’inta, sai da ya kaiwa bango duka saboda b’acin rai kafin nan ya koma ya kwanta asanyaye akan couch, ba’abunda ke damunsa irin tuno tarbiyyar Khairi da yanda yanzu ake nema amaidashi ba komiba acikin gidansa, shine duk kishinsa matarsa zatake sa gantalallen mayafi tana fita, kuma ace bai dau matakiba, hmnn ko quatern haka Khairi bata masa hakanba, ya runtse ido yadinga keta mata tsiya…+
Jamila an gama shirin haihuwa tsab, inda ta bijiro da komawa gida saboda haihuwar, bai musa mataba ya bata dama don dama suna sa ran acikin satin zata iya haihuwa, kayanta tsab da take buk’ata tayi parking inda ya kaita gida tare da ajiye mata 100k saboda shirgin wanka da kudin iccen wanka, da komi da za’a iya buk’ata, duk da cewa kuwa daidai da olive da akan sawa jarirai yasaya, duk wani abu daya dangancesu ya ajiye mata, sosai ranar take jin dadi ta dawo gida komai sai dai ayi mata, shikuma ya koma kan aikin sa..
Khairi zaune a office d’in director saboda yana so yayi Dr Ahmad maganarta don ya sake tankawa Unifoam d’intane, sai da Dr Ahmad ya shigo sannan yace mata ta fita, bayan fitarta Director yace wannan yarinyar da kaga ta fita ga dalilan dayasa kaga Unifoam d’inta is different dana sauran, saboda yanda suke dashi har d’an gutsura masa labarin Khairi yayi, take Ahmad yaji tausayinta ya dirar mashi arai don shima duk da matarshice ke haukan kishin ba dad’i yake jiba, kuma abun ya bashi mamaki yanzu wannan yarinyar ce bazawara gaskiya an cuceta ai tayi k’arama, dama Director sanin halin da Ahmad yake cikine yasashi fad’a masa hakan, don yanawa Khairi sha’awar shi amatsayinsa na Uncle d’inta..
Tunda ya fito daga office d’in yakeson yin magana da ita, amma sai yaji zuciya na hanashi yin hakan, ahaka yaje ya gabatar musu da Lectures d’in, kuma abunda ya fara burgeshi ga ita dama tun farkon zuwansa yaga tana da gogewa akaratun sosai, tana amsa tambayoyin sa akai-akai, gashi bata da baragada kana ganinta kasan shes gentle and cool, sai da suka fito yin sallah ya nemeta, anan yadan ja ta da magana yace shi matsayin Uncle dinta yake ai tunda kowa yasan yanda yake da Director, yaji labarinta yanaso in ba damuwa ya zama abokin shawarar ta domin shima yanda matsala makamancin ta ta, yana da kwarjinin da bazata ita hanashi komiba, don haka ta amsa tare da bashi number d’inta, yace taje ta shiga cikin yan uwanta Students, zasu dora maganar awaya…
STORY CONTINUES BELOW
Kamar wasa suka dinke ita da Ahmad awaya, tamkar yayanta ciki daya take jinsa Umaima kuwa kaman ta zuba ruwa ak’asa tasha don farin ciki, don dama tafiso taga hankalinta ya karkata ga wani yanda bazata komawa Adam ba
Yana cikin F. U. D aka kirashi kan Jamila na nak’uda sun kaita asibiti, agigice ya tafi yana tasbihi aransa, dama yana jiran ranar don kuwa EDD dinta ya dara da kwana uku ne, in kaga yanda Jamila ta zama kalar tausayi, sai ta kira sunan mamanta ajima ta kira sunan Ahmad, tun safe da aka kaita sai bayan k’arfe biyu ta sauka, kafin nan Jamila an kusa tafiya barzahu, tayi laushi lub’us muryarta duk ta dashe, gata da karad’i wayyo kaza wayyo can, haka dai Allah ya taimaketa ta haifi d’anta zankad’ed’e, karkaso kaga bakin su Umma da Ahmad, hatta su Maman Jamila kowa farin ciki yake, tsaf aka gyara Jamila bakace itace dazu take fadin wasiyya zatayi ba, ganin tsaf suke lafiya lou aka sallamesu, sukayi gida dasu daga ajiyesu da Ahmad yayi ya wuce ya hado shirgin kayan nama da su yaji, su Zuma duk don lafiyar matar tasa, suma bangaren gidansu duk abunda al’ada ta tanada sunyi, bakomine yake dad’awa Jamila farin ciki ba illa ganin Namiji ta haifa wato ita keda gida, kishiya bye-bye.. . .. Ahmad angon k’arni
Tana zaune tana waya da Maryam Tafida, Maryam tace ” Gaskiya baki da kirki shikenan don kin samu mutane, kin watsar damu ko? Ai dai zaki dawo ki samemu, kinsan hutunki ya kusa k’arewa” kyalkyalewa tayi da dariya ba k’arya sam ba sosai tafiya waya da mutaneba, hankalinta kwance yake anan tayi kiba ga fresh da tayi, sai ka rantse gyaran amare ake mata, tace ” Kai Adda Maryam kinsa dai ina nemanki, wani dadi zanji na manta dake, kuma soon zan dawo kafinma hutu na yakare su Ya Sayyid sun kusa dawowa, gashi ina missing Ummi, tun bayan abun nan bama samun zama nida ita” Sun dade suna shan hira kafin nan ta yanke, tana jiye wayar sai ga kiran Ahmad, bayan sun gaisa ya sanar mata an masa haihuwa, takuwa tayashi da farin ciki sosai..
Abida kam rashin mutumci sai dad’a k’aruwa yake, yanzu zuwa da take wajan zuma sosai, da ba sosai ba amma ganin tanayi ba’a kamata sai ta maidashi akai-akai, baya kwana biyu da Adam ya rage zama agida sosai don sai an tashi tsaf yake dawowa,wani sa’in ran weekend ma sai ya wuce PLAZA d’inshi, ita kuwa anan take samun dama satar fita, suje suyi ta shek’e ayarsu, Abida takasance mace mai son romance na fitar hankaki, ita bataki ayi awanni ana yi ba she don care atafi sex no just asha mata boobs da sauran tab’e-tab’e, shiyasa bata rabuwa da magungunan gyaran su amma ina dole su nuna, kafin kace me sun koma kamar guga, kuma tsabar iskanci sai ta deb’i drinks da meat pie da takanyi, ta tafi musu dashi sugama su cika cikinsu da dukiyar mijin nata, tsabar cin amana da rainin hankali, in fruits ne haka zata masu blending da madara ta zuba ajug ta tafi dashi,duk Adam bai saniba iyakar abunda zaice shine yagano tana satar fita don yasha zuwa yaga batanan, sai dai yayi fadan k’arshe ta fishi fushi, shiyasa saboda rashin jituwarsu bai fiya son zamaba agidan, k’arfi da yaji ya koyi zama awaje da dare sai 9 wataran 8 sannan zaka ga shi ya dawo, ita kuwa ko ajikinta don hakan zai bata damar yin chats dinta da Zuma
Yau tunda ya tashj ya shirya yiwa Khairi magana, so yake ya fara shirin dawo da ita ba gudu ba ja da baya, don yagama yin nadama yasan duk duniya bazai samu nutsuwa ba sai ya dawo da Khairi, tana zaune atsakar gida suna hira da Nabila suna shan rake, wayarta ta d’au k’ara gabanta ya yanke ya fad’i, yanayin da yake kan fuskarta yasa Umaima da ta fito daga toilet kallonta, tace ” Meya faru ne Sis” kafin nan wayar ta yanke tace ” Wallahi Ya Adam ke kirana” zaro ido Umaima tayi tace ” Hmnn kira kuma dama baji goge number sa ba kenan, ki kin gane through digits din ne?” tace ” Ban goge ba” wayar ce ta sake d’aukar k’ara Umaima tace ” D’auki ki nuna baki gane wayeba, nasan wallahi sai ranshi ya b’aci” aikiwa saura kiris wayar ta katse ta d’aga ” Salamu alaikum” daga can b’angaren sai da ajiyar zuciya ta kwacewa Adam ya amsa, ya kama inda-inda ya rasa mai zaice tace ” Pls wake magana ne?” wani irin tashin hankaline ya taso masa, haba ya za’ayi tace waye yanzu koda bata da number dinsa tace ta manta muryarshine, jan tsaki tayi ” Look idan bazaka fad’i wage ba i will cut d call dont waste my time” baisan sanda yace ” Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” ya kashe wayar dake wayar k’aramace china kiya volume na call yake kure kana ji kaman an sashi ahandsfree take su Umaima suka bushe da dariya tace ” Yawwa sis sai kin gasashi dan rainin sense” harararta Anth Asiya tayi da take gefe tana kwab’a cin-cin tace ” Wallahi Umaima ki kiyayu bakinji, tsakanin mata da miji kar Khairi takoma kizo kina jin kunya” take Khairi tace ” Subhanallah wayyo Anty kar mala’iku su amshi bakin kifa, nikam na sharr Adam arayuwata” suka cigaba da fadawa Khairi yanda zata ke gasawa Adam b’acin rai
Adam kwana yayi yana juye-juye, ya salam wani irin wutar sonta ke cin zuciyarsa, washegari yana tashi ya nufi wajan Kawu Bala ya sanar masa yana son ya shige masa amaida Khairi, sai da kawu yayi dariya yace jeka zan nemeka, bayan fitar Adam Kawu Bala ya kira Hajiya Hassu ya sanar mata, tace ka barshi sai yaji ajikinsa, hakanan shima Alhaji Abdullahi yace ka rabu dashi kowa ya tuba don wahala yayi abanza..
Hajiya maijego tana nan tayi rashe-rashe kullum k’awaye in sukazo anta cika baki kenan, idan kuwa kawar tana da kishiya sai Jamila ta shiga kuri da nuna su suka so aka musu kishiya, ai ita tafi k’arfin hakan bayama yanzu da ta haifi magaji….
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
35
Rashin Jamila agida bai damu Ahmad ba tunda dama koda tana nan wataran sai ahankali, sai dai zaman shiru ko bakomai wataran zakaji motsin mutum, kullum sai dai yaje gidansu ya karb’o abinci, ya dawo ya raba dare yana tad’i awaya, yawanci da mutum biyu zakaga ya d’au lokaci yana waya sai kuwa Umar, su Umar ‘yan taya b’era b’ari tunda Jamila ta haihu ya k’ira Ahmad yace ” To yanzu lokacinmu yayi zamu making move to that girl”
Ranar suna set na akwati aka wa Jamila daga gidansu Ahmad haka shima yaje algazaru ya samo mata mini set ita da yaransa, abun sai wanda yagani bikinsu atsare, sai da akai shagali kaman wani kamu da rabon robobi da mug mai sunan jariri Muhd Jahun, sunan baban Ahmad kenan bakinta har kunne sunan uban miji, take Chief of justice Muhd Jahun ya bawa takwaran nasa kyautar gida, nan danan Jamila takeji tayi karfi adangin Ahmad tunda gashi tayi uban miji…+
Kwance take suna waya da Sayyid, sai sako mata maganar Adam take tana kaucewa don kwata-kwata batason maganarshi ayanzu, dake su basusan wainar da ake soyawa ba, daga shi har Hafiz d’in dakyar take daurewa take bashi amsa, kiran Ya Ahmad ne ya shigo batasan sanda ta saki fara’a ba, hira sukai takai ta minti goma sha biyar rabi akan tafiyartane don nextweek end zata tafi, kwana biyu sai jadda mata tahowa Ummi keyi ita takasa gane dalilin hakan, dole tafara shirye-shiryen tafiya,sai da Adam ya zauna yamata typing long text akan bada hak’uri da neman yafiya, sannan yace ta k’ara bashi chance insha Allah bazatayi regretting ba, ko replying batayiba ta watsar dashi..
Wani sabon abu kuma kullum sai an kirata da new number ak’i magan haka zatayita hello-hello aki amsa wa, wanda wannan aikin Adam ne zuwa yayi shago ya sayo sims har mai shagon sai da yafara zarginsa, ganin kullum sai ya sayi guda biyu sai kace wani mara gaskiya, dalilin hakan kuwa shine in aka kirata aka ki magana to in aka jima taga kira da number sai tak’i dagawa shikuma sai ya sake saka wani new sim din ya k’irata, kawai yaji muryarta ma kwanciyar hankaline
Kullum Adam sai yaje gidansu ya gurfana gaban Mama akan tasa baki kan Komensu da Khairi, ta murshine idonta da toka ta yab’a masa maganganu masu ciwo, amma saboda shi yake so haka yake cijewa ya k’ara dawowa yanda kasan d’an maula haka yake zubewa kasan falo yana mata magiya, gwanin tausayi wataran ma tashi take ta shige bedroom d’inta ta rufe k’ofa tace masa in ya gaji ya tafi, ya faru yakai sau biyar rannan sai ga Jidda tazo gidan, agaban idonta yasha wulak’ancin nan har sai da ya bata tausayi, har cikin ranta duk da tasan bai kyautawa Khairiba amma tana ganin duk duniya bawanda zai sota kamarshi, kuma tunda yayi nadama ai shikenan, tana yin sallama da Mama ta shiga gidan su Khairi ta sanarwa Ummi abinda ake ciki, anan itama Ummi tace taji hakan na faruwa wanda baya mata dadi, don duk wanda yaga yanda Adam ayanzu ya koma sai yayi tunanin wani ciwon ne yakamashi, ya motse ya fita hayyacinsa ko tsabtar kirki baya iyawa saboda rashin nutsuwa, amma zataje suyi magana da Mama akan haka suka rabu da Jidda..
Adam yana tafe yana tsiyayar hawaye dawowarshi kenan daga gidansu, inda yake tuno kalamin Mama tana cewa ” Itafa tagama shiga lamarinsa aduniya, tunda ya runtse idonsa ya saki Khairi bayan tulin rashin kirkin da yamata ta rufe masa sirri, amman sai da yabankada mata rayuwa tunda ya saketa yamaidata bazawara, don haka yaje wahala yanzu ya fara yinta arayuwarsa amma kada ya kara tunanin ita Hafsatu zata kara shiga rayuwar auransa, babu hannunta yaje duk inda zaije ya nemo hanyar komensu” buga goshinsa yayi da hannunsa yana fad’in ” Adam ka cuci kanka gashi tun ba’aje ko’inaba soyayyarta na neman kaika ga halaka” shikad’ai yasan ciwon da zuciyarsa kany, lokuta da dama sai yaji kewayen zuciyarshi na kud’a especially idan yana tuno rashin yiwuwar dawowar Khairi arayuwarsa, a ahaka ya k’arasa gidansa ya ciro key ya bud’e, bai damu da knocking ba don tunda ya tsumduma kogin tunanin da rashin nutsuwa Abida ta sake samun lasisin yawo, yanzu ko takanta bayabi damuwarshi kawai Khairinsa, shiga yayi ya kwanata yana sak’e-sak’e aransa, yafi awa d’aya ahaka sai ga Abida ta shigo d’akin daga ganin yanayinta daga unguwa take, don kwalliya ce ajikinta sosai, ya fara zarginta tun kwanaki dayaga yanda take warewa wani guy da tace cousin d’intane, amma sai ya kawo na mujiya ya zuba mata shi kansa sai da yayi mamaki, bayajin haukar kishinta kaman na Khairi shiyasa ya tabbatar so shine silar Kishi, amma duk da hakan yana jin kishi sai dai irin wanda zai iya kawar dakai, bai mata maganaba sai ta hau ‘yan kame-kame ” Meyake damunka naganka wani iri?” bayason magana da kowa ayanzu saboda haka yace mata ” Bacci nake ji kawai ina son na hutane” daga haka ta kama bakinta tayi waje, dama daga wurin Zuma take don soyayya suke ba kama hannun yaro ko sanda suna saurayi da budurwa bai kai hakaba, kana ganinta kasan bata da damuwa har yar k’iba ta k’ara..
STORY CONTINUES BELOW
Kawu Bala tare da Kakar Adam suke zaune suna tad’i ciken nutsuwa tace masa ” Yanzu kuna zaune haka zaku kyale yaron nan yayi ta wahala? Bazaku nema masa Komen matarsa ba?” yace ” Nima dai yanzu nafara tunanin hakan don dukkan alamun nadama sun bayyana agareshi, gashi duk yabi ya lalace har mutane sun fara maganar abun, matsalar daga wajan Abban sa ne yace shi bazaice komiba don Adam ya cutar da yarinyar” Shiru tayi tana d’an nazari tace ” Wai irin kawaicin nan ne amma na tabbata suna jin abun aransu, ai badan shiba kodan su zasu so yarinyar takoma banaso muyi rashinta cikin zuriyarmu, ana jan k’afa haka sai dai aji wani ya fito neman auranta fa” Kawu Bala yace ” Hakane amma inaga zanyiwa shi Alhaji Aliyun magana, kila shi yaji ya hakura amma yaron nan jiya da naganshi sai da yaban tausayi, sai kiga yana tafiya kaman baya duban gabansa tsabar tunani, yanzu kinga ai yaga amfaninta tunda ance ita amaryar ballagazace, ya za’ayine kuskure yayi hakuri dolene, haka maza muke sai Addu’a”
Adam duk yanda yake tunanin abun zaizo da sauk’i yaki, shi kam Abbansa ko tsayawa sauraransa bayayi, akwai ranar da yazo yasameshi a falo dashi da Abban Khairi, bayan ya gaidasu ya gurfana ya shiga basu hak’uri akan ayafe masa kuskuren da yayi, ko tak Alhaji Abdullahi bai ceba balle yasa ran magana mai dad’i, sai Alhaji Aliyu ne yace ai an riga an yafe masa kuma dama haka aure ya gada wasu mazan ma kanyi fiye da nasa, kuma maganar ta wuce, bak’aramar kunya ce takama Adam ba ganin yanda ko afuska bai tab’a canza masa ba tun da akai abun har ya zuwa ranar, da alama shi zai iya sassauta masa amma kuma yana jin kunyar neman Komen daga gareshi zaiga kaman rashin kunyane, don kowa yasan mai yayiwa Khairin, haka ya d’ebi k’afafuwansa ya fice
Ganin tafiyarta tazo duk taje gidajen relatives nata sukai sallamah, wasu ta yini agidajensu kaman kakarta da Director, inda suka mata kyautuka sosai da tulin tsaraba. Ana gobe Khairi zata tafi sukai waya da Dr Ahmad yace mata daman ran saturday din zai shiga Daurin Aure kano, don haka in ba damuwa sai su tafi tare, da farko taki sai da su Umaima suka nuna mata ba komi ai tunda ansan halinshi, bai da wata matsala, da tulin tsaraba da komi aka cika boot din motar tasa, inda Khairi ta cakare da wata igbo wraffer da akai style da pattern dinta sannan an bi shi da stones, tayi kyau matuk’a sai kace wata budurwa, sai da suka rako ta bakin motar Umaima ta kalleta ta saci kallon Ahmad tace ” Sis wallahi yanda kikasan couples irin sabon auren nan” murmushi tayi tace ” Kyaji dashi zan fad’a masa tunda kin daina kunyarshi” kama bakinta tayi tace “Rufamin Asiri har yanzu fa bangama school ba” sunji ba d’adi tafiyarta ta itakam Nabila dake tana da saurin kuka har kwalla tayi, an saba ba kad’anba itama Khairi ji take kaman ta zauna, yanzu in takoma gida ba abokan hira nan kuwa akwai mutane haka suke raba dare suna chapter..
Hirar mai dad’i suke har sai da suka zo ajingi bacci ya kwasheta, dama gwanar baccin motace balle ta tashi da wuri ranar, ganin haka ya kira wata number awayarshi ya shiga hirarsa anutse, dake safiyane hanyar ba mutane sosai har sai da sukazo wajan Wudil shine ya ajiye wayar tasa..
Daga nesa yake hango mace gaban motar duk da bai gama tantance wace ceba, amma sai yake ga kamar Khairin sace da wani suna dariya, dariyar ma irin wanda ake tad’i mai dad’i, har zai shiga motarsa ya tsaya don ya tabbatar, cikin murmushi ta fito tana gyara zaman veil dinta a kafad’arta yasalam tayi masifan kyau bayama d’aurin dankwalinta daya kafu ta baya ga gashinta dayake cikin black ribborn, yana tsaye ya hard’e hannunsa don yaga wane ya kawota, fitowa yayi daga cikin motar yana nuna ta da key cikin dariya yana ” Haba hajiya kinji minsharin da kika dinga min amota, sai da na k’ure radio volume na samu nutsuwa” kyalkyalewa tayi da wata dariya dakan k’ara mata kyau sigar shewa haka take, aduk sanda Khairi tayi irin dariya katabbar hirar da ake na mata sugar tace ” Kai Ya Ahmad harda sharri” yace “To shikenan ai nayi recording zan sending miki awhatspp harma da Vedio” tare suka nufi boot don fito da kayanta, suna fito da kayan zuwa k’asa inda wasu yara yan layinsu suka shiga kaisu cikin gidan, shidai Adam yasan zuriyarsu Khairi sosai amma bai san wannan ba don haka take yaji wani mahaukacin kishi na dibarsa bayama da yaji hirar da suke, gashi Khairi taki kallon inda yake tana pretending as if batasan da shiba, don haka yaji gara yaje yayi magana da koma waye yaji shidin meye na ta.. Adam da k’arfin hali, ganin yaran sun kwashe komi sai ya zagaya baya ya bud’e ya d’auko wata leda babba fara irin na store cike da shirginmu na mata, ya rik’e ahannunsa, alokacinne Adam ya k’araso wurin, zuciya d’aya Ahmad ya mik’a masa hannu ” Assalamu alaikum” dakyar ya amshi hannun tare da amsa masa sai kuma ya jefa kallonsa ga khairi yace ” Wannan d’in waye kika tsaya kike yak’e masa hak’ori?” murgud’a baki tayi tace ” Bawan Allah lafiyarka kuwa? Meye dalilinka namin katsalandan arayuwa, bansankaba banda alak’a dakai don kawai zaman unguwa ya hadamu dakai zaka samin ido” cak yayi shi take cewa bata sanshiba? Cikin mamaki Ahmad yace ” Dama bakisanshiba yazo zai shigar mana magana, kai matsalar bahaushe kenan fa sa ido” ya maida kallonsa ga Adam yace ” Bawan Allah ubangiji ya hana irin wannan pls mind your bussiness” Adam ya zama statue awurin shi ake cewa hakan, lallai Khairi ta k’aro wulak’anci, matsawa sukai zuwa ga jikin get suka bar Adam atsaye k’ik’am yarasa tab’uka komi Ahmad yace ” Bari na tafi tare da mik’a mata ledar yace ” Ga nawa tsarabar ayi hak’uri bayawa” dauke da murmushi afuskarta tace ” Harda Hidima kuma, nagode amma nikam bazan iya karb’a ba” Had’e rai yayi yace ” Ashe baki d’aukeni yayankiba, in baki karba ba k’arshen friendship din mu yazo kenan” haka ta dan duk’a ta karba tare da mashi godiya, suka dinga daga ma juna hannu, har sai da ya shiga motar tana tsaye da zummar sai ya tafi zata shiga gida, aikuwa take Adam ya tare gaban motar cike dw mamaki Ahmad ke kallonsa ta glass “Malam wai meye hakane ka hanani tafiya” Ahmad ne yake fada ta window Adam ya tako ya tsaya jikin window yace ” Meye alak’arka da ita? Me ye na zak’alk’alewa mata ta?” murmushin rainin wayo Ahmad yayi yace ” Ahh point of correction mata ta dai, don kowa yasan nine masoyinta na hakika ka zuba ido kwana kusa zakaci goron daurin aurenmu” kamar an caka masa mashi azuciya yace “kuturun bala’i” ya zira hannunsa zai janyo rigar Ahmad Khairi da ta dawo ta kwad’a masa handbag d’inta tana hawaye tace ” Haba bawan Allah ko kai mayene ya kamata ka kyaleni, bani da alak’a dakai shine kake so ka shiga rayuwa ta da ta mijina, na rok’eka indai kud’i kakeso wallahi zan baka just leave my life, haba ko kazo na kaika gidanmu in taimako kake nema abaka, ba’a maula da wannan sigar don Allah kadaina” tana fad’a tana hawaye, Adam bai san sanda yayi wata dariya kaman wani boss ba irin ta yake ko kuwa ta ciwon rai wai shi Khairi take nunawa bata sanshiba harda jinginashi da maula wato so take ta nuna bata sanshiba kwata-kwata , dariyace ta kwacewa Ahmad sannan yace ” Babyna kidaina hawayen nan wallahi hankalina har yafara tashi, pls ki koma gidan i can handle him” hada ido sukai na seconds sannan ta juya ta nufi gida, Adam da yake jin kirjinsa na zafi haka ya dafe gefen zuciyarsa yana hailala, da haka Ahmad ya samu yaja motarsa yabar wajan..
2
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Dedicated to Team Khairi.. ❤
36
Da zumud’i ta shiga gida haka ta samu tarb’a mai kyau daga wajan Ummi, dad’i take ji ana sallar la’asar ta shiga gidansu Adam, sai daf da magriba ta baro Mama akan sai ta dawo, bayan sallar Magriba Abbanta ya dawo don haka taje falonsa suka d’au lokaci suna hira, don daya dawo daga sallar Isha’i a falonsa gaba d’aya sukaci abinci harda auta isma’il shi dake ba boarding yake ba, sai 9 saura suka koma cikin part dinsu itada Isma’il, bayan Ummi tagama da Abba ta dawo cikin gida, ta shiga d’akin Khairi taganta har tagama shirin bacci tana waya, alama ta mata da ido akan ta sameta bedroom d’inta, bata d’au lokaciba ta mishi sallama dama Ya Ahmad ne, ta zira jacket kan silk gown na jikinta tare da zira slippers wanda ya kasance na kayan bacci ta nufi d’akin, tana zuwa ta nuna mata alama ta zauna gefen gado dama ita tana zaune ne ak’arshen gadon, tun daga yanayin fuskar Umma tasan magana zasuyi mai muhimmanci s
don haka ta sake nutsuwa Ummi tace “Khairi ina son ki tattaro nutsuwarki nan, tsakanin ki da Allah kina nufin kin gama auran Adam ne ko kuwa kina son hirashine kawai? Don anzo an ban labari wanda yakawoki sun kusa rikici da Adamun har kina ik’irarin baki sanshiba” sunkuyar da kanta tayi kai yaron yanzu sun iya tsugudidi ta tabbatar a yaran unguwarne cikin masu shigar mata da kaya wani ya fad’a Ummi ta nisa tace ” Kimin magana ba wai ki sunkuyar dakai ba, wannan magana ce da take buk’atar furucinki” tarasa ta ina zata fara to me zatace tabbas takaranto tsananin sonta daga Adam da tarin Nadama, haka kuma k’aryane tace ba sonshi shima aranta, don da soyayyarsa ta tashi amma itakam da ta tuno rayuwar dayasata sai taji ko ganinsa ma batason yi Ummi tace ” Tunda kink’i magana shikenan zan baki lokaci zuwa Sati in kinki magana tabbas zan d’au matakin daya dace one more thing karki k’ara gigin nuna masa baki da alak’a dashi in ba so kike ki rusa zumuncin da aka dora tunkan haihuwarki ba… Ehe” ta nuna mata hanyar fita sumi-sumi ta tashi bayan ta furta ” Kiyi hak’uri” tana fita ta shige d’akinta hawaye ya balle mat, ko meye dalilin dayasa Ummi ta d’au zafi haka, kar dai Ummi bata ji zafin abunda Adam ya mata ba? To wanne mataki ne tace zata d’auka? Kanta ya kulle bata iya bin k’iran Ahmad ba kaman yanda ta fada masa in tagama da wuri she will call him back..+
Adam tunda ya je gidansa Abida takasa gane kansa don ganinta da yayi ta dawo daga mak’ota da wani firirin mayafi sai da ya dalla mata mari, wanda bawan nan karon ne ya fara ganintaba shiyasa abun ya bata mamaki, abunda bata saniba harda haushin kunnashi da Khairi tayi, yarasa inda zai tsoma ransa don ita kanta Abida kasa mashi rashin kunyar tayi, don ayanyinsa tasan hes not in his right sense, bacci sai b’arawone ya d’eb’eshi saboda fargaba don kuwa yaga Ahmad din yanada kamala da yake ganin in Khairi taki yarda su koma za’a iya bashi auranta, tabbas ya cuci kansa inba hakaba ya za’ayi wani ya tuk’o matarsa tun daga jigawa har zuwa Kano wayasan kalar tad’in da sukai, zuciyarshi ta cika da tsananin kishinta, sai da ya zubar da kwalla ya samu relief..
Safiya nayi Adam ya nad’i k’afa zuwa wurin Kawu Bala, lokacin 7:30 yana shirin fita unguwa, ko bai tambayaba yasan tuni ne don bayanda za’ayi ace ya doko sammako irin wannan, tsayawa yayi cikin sitroom d’insa suka tattaunawa inda Kawu Bala ya bashi hak’uri akan sai an shawo kan Abbansane dole, tunda shi din kaman matsayin Uba yake ga Khairi, in yace bazata komaba ta zauna inma bai nuna isa kan shi Adam d’inba, bawa Kawu bala labari yayi akan yaga wani yana sonta shi tsoronsa kar akwace masa ita, ya tausaya masa don amatsayinsa na namiji yasan irin feelings da Adam yake ji, bakin Adam duk a bushe ya isa ga Hajiya Inna kakarsu kenan, tunda ya shiga ta k’ureshi da ido har yasamu bakin sallaya da take kai tana lazimi, ajiye carbin tayi ta fuskanceshi sosai anan ya shiga gaidata, tana nazarinsa bayan sun gama gaisawa tace ” Adamu baka da lafiyane ko kuwa ita Abidan ce ba lafiya?” yak’e yayi tare da lashe busashen lips d’insa yace ” Ko d’aya babu duka lafiyarmu lou, magana ce akan jikarki nunawa take bata san niba balle nasa ran ina da wani matsayi, gashi Abba ya matsa lamba shi bazaisa baki ba, kinga yana da iko da ita” sai da ta b’alli goronta ta cinye batace komiba har saida yayi tunanin bazata ce komi sannan ta yi kwafa tace ” Ai kaima kaso amaka hakan Adam, matsalar mazan yanzu kenan saurin saki yanda banda abunka Khairi ko ba aure ai tazama jininka, yarinyar da tasan rufawa miji asiri awannan zamani banda k’uruciyar kanta ai itace macen kirki, babbar illa da ba d’a tsakaninku dama da akwai zuriya da tuni an maidata, amma me kayi silar zubar cikin” sai da ya runtse idonsa saboda tunowa da yayi cikinta da ya isa haihuwa korarta da yayi yayi silar mutuwar yaron, sakamankon doguwar nak’uda da tayi, sai hawaye shar kaman mace, abun ya tab’a zuciyar Kaka sosai tausayinsa ya taso mata, tasan shid’in ko ayarinta yana da taurin rai bai fiya kukaba, nasiha ta shiga masa da nuna masa ya dage da Addu’a insha Allah bamai auran masa mata zata dawo gareshi, ya jure horon da ake masa ta tabbata itama Khairi tana sonsa, yad’au duk maganganunta amma banda Khairi na sonsa don inba makancewa yayiba yaga kaman zallar tsana had’i da tsoronsa a idon Khairi, dalilin yar nutsuwar da yasamu daga Kaka ya iya shan rabin Cup na Koko da aka damo mata tare da kosai guda biyu..
STORY CONTINUES BELOW
Khairi kuwa da ta tashi da safe sukayi break da Ummi, takoma toilet tayi wanka tare da yin kwalliya cikin cotton material dayaji d’inki maikyau, ta zauna afalo ta kunna data tare da shiga chat abunta, kana ganinta kasan ba abunda yake damunta jefi-jefi zakaji ta saki dariya, tana tsaka da hakan sai ga Adam ya shigo cikin babban falon gidan nasu wanda aciki take, tana ganinsa ta mik’e tare da k’okarin yin sashen d’akinta, duk da rashin kuzari da yake ciki bai hanashi saurin bintaba tana isa ga k’ofar d’akinta yayi caraf ya rik’o hannunta, tare da jinginata jikin bangon corridor da d’akinta yake bayan ya rufe mata naki da d’ayan hannunsa, takaicin tab’ata da yayi yasa kwalla taruwa cikin idonta ” Khairi ni kike wulak’antawa agaban wani, ni Ya Adam d’inki? Har kina cewa baki da alak’a dani kin manta har yau akwai igiyata biyu akanki” yana magana yana bin jikinta da kallo bak’aramin kyau tamasa ba sakin bakin nata yayj inda ta furta ” Malam nace ni bansanja ba haba wane irin nacine wannan” tana mutsu-mutsun kwace hannunta, sake saka k’arfinsa yayi ya matseta har saida tace wash sannan ya cigaba da magana ” Wallahi k’arya kike har yau na tabbata da sona aranki, wai wace irin zuciya garekine shin bamuyi Allah laifi ya yafe mana, meyasa bazaki manta bayaba ki bani nadama na wanke kaina akaro na biyu, na gatalaki naji dake nasaki farin ciki” wata harara ta doka masa har cikin ransa sai da yajita tace ” Allah ya kyautamun ai dak’ik’i ke maimaita ajin baya, ni yanzu Khairin da kasani bace abaya waccan Khairi mn ta mutu da bak’in cikinka, wannan murucin kan dutse ce ashirye nake naganin na wanzar da farin ciki araina don haka nadaina tarayya da mutane masu tsananin son kansu, don haka pls let go off my hands i have in baka da abinyi inada dont spoil my mood” sakin hannun ta yayi sabo yaji muryar Ummi tana kiran Khairi da alamu ta kusa shiga falon sai da yasa hannu ya mari lips d’inta yace ” Im not selfish person stop saying it to me” jan tsaki tayi ta wuce zuwa falon, bin bayanta da kallo yayi tsan ya tsani tsaki shiyasa ta masa amma bakomai ai neman hanya yake, ko marinsa zatayi bazai damuba, ita da Ummi kitchen suka koma shiyasa ya samu daman fita batarr da tasan yana gidanba..
Yana shuga gidansu Mama da take yar fara’arta ta tsuke fuskarta, adak’ile ta dinga amsa gaisuwar da yake mata, syna gama gaisawa tacigaba da dama furarta Khairi ce tazo musu dashi, yafi 15 minutes gefenta bata nuna tasan da zamansa ba, din har ta sha furar da nonon bata masa tayiba duk da tasan yanaso, kuma ganin yaja gefe ya zauna tasan yana son magana da itane, yayi zuru abun tausayi ana haka sai ga Abbansa ya shigo ya kalleshi ya basar cikin sunkuya yashiga gaidashi ya amsa masa ba laifi shi bai d’aureba, Mama ta kalleshi tace ” Ashe ka dawo banjiba bari na kawo maka taka furar” ta mik’e ta nufi kitchen don dama ta maida masa nashi cikin fridge, kallon Adam yayi yace ” Kaikuma meye haka ka gurfana kamar kaje gaban sarki” sosa k’eyarsa yayi tare da murmushin yak’e wanda yake fidda zunzurutun ramar da yayi yace ” Eh dama naga Khairi ta dawone shine nakeso ko za’a shiga lamarin mukowa auranmu” lokacin ne ta dawo d’auke da tray da jug da cup kai sai containee sugar da spoon, Alhaji Abdullahi ya kalleta yace ” Gara da kika zo kinji abinda d’anki yace” murmushi tayi tace ” Inafa ai yasan tuni na sallamawa duniya shi, kai dashi amma ni d’iyata mai tsadace ai anshamu mun warke saj ta zabi wands ya dace don bazamu mata doleba” da Mama tassn ciwon da Adam yakeji aduk sanda ta nuna ta sallamashi ko kuma ta jingina Khairi da wani da ta tausaya masa, amma ya zaiyi shiya janyo don haka ya sunkuyar da kansa, yana jin tuk’uk’i ak’irjinsa, murmushi manya Alhji Abdullahi yayi yace ” Kwarai kuwa bamaj yimata dole, don kuwa tunda kamaidata bazawara kaman ka saya mata yancine, don yazo a addini iyaye subar bazawara ta furta da kanta bakamar budurwa ba da akace suna da ikon kawo mata miji, don haka ni anawa ganin kaje ka nemi had’in kanta in ta yafe ta amsa shikenan” wata irin fad’uwar gaba yaji don wallahi yassn halin mutane masu shiru-shiru in suka tara mutum basu iya yafiya da wuriba, balle Khairi nada saka abu arai kuma ga yanayin girman laifin da yamata, cigaba sukai da hirarsu kaman basu san da zaman Adam awurinba, tashi yayi zalau-zalau yayi falon bak’i nagidan don ya kwanta, kwanakin nan yakan yawaita ciwon kirji sai wata sa’in yaji zuciyarsa na fat-fat kaman zaiyi haki, sai ya kwanta rigingine yake jin sauk’i…
Ahmad ke zaune cikin dakin daya kama a bistol hotel, yana waya cike da nishad’i ” Haba kema kinsan nafi ji dake ai, sau tari nakayi kokonto ko kina sona” banji amsar da aka bashiba sai dai murmushi ya k’aru da alama amsar mai dad’i ce, yana haka yaji alamun wani k’iran ya sake shigowa Jamila ce don haka yace wa wadda suke wayar zai nemeta urgent call ya shigo masa, yana kashewa yabi Jamila “Haba Abban Aslam (Muhd) wai meyake faruwane kwanakin nan baka tamu, ko baby baka damu da ka nemeshiba sannan ayita k’iranka ana jinka busy” mai hali baya canzawa Hajiya Jamila uwar k’orafi kenan sai ka rantse ita din ta iya sauk’e hakkinsa yace ” Ina kwana? Don naga kin manta bamu gaisaba kin shiga wasu bayanai” dakyar ta amsa kana tace ” To ba doleba ace ba wani d’oki da kake, kodai don bana gidan ka samh saken soyayya da yan mata?” yace ” Aikuwa bazakice bana nemankuba, karki manta sau tari zan kiraki kice bacci zakiyi don ai sanda ciki ya tsufa baku fiya bacciba, sai bayan haihuwane kika ramawa, kuma waya da kike jin busy bani da mutane ne ko kuwa ya? keda bakya raina abun magana” hmm tayi kwafa tace ” Naji kana yi amma ai kwana biyu ba sosai kake kiranba, kuma maganar kanada jama’a meyasa da ban fiya jinka call waiting ba sai yanzu? Koma meye ai nakusa dawowa zan gani idanma munafurta na akeyi, sai anjima” kitt ta kashe wayar yaso ranshi ya b’aci amma sai ya basar daya tuno saura kad’an ya samu mai kwantar masa da hankali, atleast in wata ta had’a maka zafi wata zata wanke ka wannan shine gida biyu maganin gobara ya saki murmushi mai manufa sannan ya latso number ya dora da wayarshi.. ..
Khairi ta shaidawa Khadija ta dawo zatazo ganin cikinta da aka kusa haifewa so take taga girmansa, tayi ta tsokanarta tana cikin wayar sai ga k’iran Safiyya ya shigo, bayan tagama da Khadija ta bi k’iran nata cikin zumud’i tace ” Amma sis kin manna min hauka jiyafa kike fad’amin kina Jahun ashe ma already kin shigo kano” tace ” Ai suprise naso miki da sai dai ki ganni agidanki nazo yini yau d’innan, sai kuma da na shiga gaida Mama take cemin kunyi waya kince kin fito dubiyar wani collegue din Ya Muhsin, nasan kuwa sai kun k’arasa da gidan nan” hira sukai mai tsayi kaman ba anjimane zasu shigoba, aikuwa wurin k’arfe uku sai gasu sun shigo gidan side hug Khairi ta mata saboda ciki da yayi uban tsini, sannan ta maida kallonta ga Ya Muhsin daya samu kujera ya zauna, tagaidashi ta shiga dakin Ummi ta sameta bacci ya fara d’ibarta, amma bude kofar Khairi ya tasheta sai ta sanar mata da zuwan nasu, ta dubi agogo tace “Ashe uku har ta d’an gota gara da aka tasheni da sai na makara ai” ta fito falon suka gaggaisa ta koma shi kuma Ya muhsin ya shige falon Abba, su Khairi suka koma d’akinta suka shiga hirarsu Safiyya ce ta kama ankle din Khairi tace ” Kinga k’ibar da kikayi kuwa, gaskiya Jahun ta karb’eki ga wani fresh da kikayi, meye sirrin don nasan Jahun da zafi baici kiyi hakaba” fari tayi tace ” Hmnn wani sirrine namu na fulani, da fresh milk aka dingamin gyaran jiki hajiya nasha kuma agyara ni bakiji fatan na santsi ba” ba k’arya tayi tsaf abunta Safiyya tace ” Aikuwa bari na haihu zan je Anty Asiya tamin ko a fad’amin yanda ake nasa ake kawomin fresh milk daga ruga” kiran sallar la’asar ne ya tada su, suna gama yi suka fito falon don cin abinci tare suka shiga kitchen safiyya ta had’owa mijinta a tray itakuma Khairi takai musu nasu cikin d’akinta, Ya muhsin yana falo tana ajiyewa ya jefa mata hararar wasa ” Wato kin shareni saboda kin had’u da k’awarki ko?” cikin kisisina ta narke idonta tace ” HoneyB kasan bayanda za’ayi na shareka muna hira rabin hankalina na tare da kai” dariya yayi yace ” Kwarai kam shiyasa naji shewarki na fitowa daga d’akin” fitowar Ummi ce ta daka tarsu inda ta shiga d’aukowa Abba nashi, tuni Safiyya takoma d’akin Khairi don gaskiya tanason su zanta Sosai, suna gama ci Khairi ta gyara fuskarta ta sake kwalliya tare da fesa turare, da mamaki Safiyya ta kalleta tace ” Amma dai wannan gayun bawai don zaki gidan Mama bane kodai kinyi sabon catch ne” Dariya tayi tace “Ya Ahmad zaizo muyi sallama zai wuce dutse, yanzu haka text yamin yana k’ofar gida” kama baki Safiyya tace tace ” Gaskiya ne” sun fito da zummar ita Safiyya zata wuce gida in Khairi tagama sallama zata taho daga baya, suna fita Ahmad na tsaye suka gaisa da Safiyya ta wuce, Khairi tace Ahmad ya shigo daga cikin gate, Adam ashe yini yayi a unguwa ya kasa ya tsare don yaga shegen da zaizo gun matarsa, atsaye suka tsaya sukayi sallama akan nextweek in yazo zai shiga su gaisa da su Ummi, tare suka fito ta rakoshi jikin motarshi ya bud’e k’ofar kenan Adam ya iso gareshi, a daidai lokacinne kuma Safiyya ta dawo da niyyar d’aukar sakon da ta manta agidan wanda na Mama ne, tana tsaye tana ganin ikon Allah, Adam ya rik’e murfin motar Ahmad yana kora mishi warning akan ya rabu da matarsa, kasancewar ba’ajima da fitowa daga sallar la’asar ba akwai matasa a opossite na gidan nasu dake masallacin yana kusa dasu, aikuwa tuni ido yayi kansu, Ahmad bai tanka Adam ba sai murmushi da yake wanda yake k’ara tunzura Adam, take kuka ya kwacewa Khairi cikin masifa da muryar kuka tace ” Haba!! Wannan wace iriyar masiface ka kyale rayuwata” ta tsugunna awurin tare da fashewa da kuka, lokacinne Muhsin ya fito inda ya k’arasa inda Adam yake ya janyeshi, take Ahmad ya k’arawa motarsa wuta, ita kuma Safiyya taja Khairi suka nufi gidansu, don bataso Ummi taga halinda Khairi take, shima Muhsin d’in can sukayi da Adam….
1
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
37
Tunda suka nufi gida bawanda yake magana acikinsu, sai sheshshekar Khairi ke tashi, su Muhsin kansu ya kulle gaba d’ayansu suna zaune acikin falo ne, sa’arsu d’aya Mama tana part din Abbansu, sai kaga yanda Adam ke kumbure-kumbure Safiyya ce tace ” Don Allah Sis ki daina kukan nan, kar wani abu ya sameki na tabbata shima Ahmad bazai d’au abun da zafiba, tunda yasan kowane namiji zai iya hakan” yamutsa fuska tayi tace ” Haba ya bazan tada hankalina ba mutumin nan yana mutumtani, kuma don ni yazo kofar gidannan ace yasamu wannan humiliatons d’in, gaban jama’a for godsake this is not fair” dafa kafad’arta tayi tace ” Yeah i can feel your pain amma ki share hawayenki, mu fuskanci yanda za’a warware abun nan saboda abun idan ya cigaba gaskiya za’a iya samun matsala” still Adam bai magana ba sai ma rawa da jikinsa keyi na b’acin rai, cikin had’e rai Muhsin yace ” Ke Khairi meyesa da girmanki zaki ke tsayawa da saurayi awaje, koma wanne irin wulak’anci aka masa ai ke kika jawo masa, kuma ki adana hawayenki kukan ya isa haka” Adam cikin ranshi baya jin dad’in kukan da take amma he had no choice dole ya fito yamata zabu-zabu, don tasan he won’t let her go dole takoma masa gida yace ” Muhsin kaga yanda tamin jiya wai har tana ik’irarin bata sanniba, agaban wancan wawan take fad’in haka wai ni d’an maula nake bibiyarta” cije lips Safiyya tayi saboda yanda Adam ya tak’ark’are yana magana duk gumi ke tsatssafo masa ga ramar da yayi duk yakoma wani kala sai yabata dariya da tausayi, jan tsaki Muhsin yayi yace “Baki da hankali zakice bakisan shiba? Wanne irin hali kike so ki d’auka da ba nakiba, komi Adam yamiki yafi karfin ki dizgashi gaban wani har kice baki da alak’a dashi, ko ba aure Adam yafi k’arfin haka don ya isa dake, karki sake don wallahi ranki zai b’aci” cikin ranta take ayyanawa wato ita ake so aga laifi duk abunda yayi sai ta zuba masa ido ya hana ta farin ciki ko, tashi tayi ta sake fasa wani kukan mai murya ta na nuna kirjinta da yatsa tace ” Wai shin ni ba zuciya ak’irjina ne?Da ake son tauyeni nace bana son alak’a dashi ya fita rayuwata!! Ya fita arayuwata!!! jikinta har rawa yake hawaye yana ambaliya a fuskarta , tashi Safiyya tayi zata ruk’ota ta goce tace ” Ki barni na zubar da takaicin dake raina, wallahi banason ko ganins, ya daina shigewa lamurana in ba hakaba zan b’ace arayawarku ko na had’iye zuciya na huta” gaba d’ayansu kalamanta sun kad’asu, abun har ya kai haka awajanta? sun san tana da hak’uri kuma ko maida martanin da tayi bayan maganar Muhsin da mamaki, don kowa yasan tana da tsananin biyayya, daga fad’in haka ta juya da niyyar fita daga gidan, ba wanda ya iya yunk’urin hanata sai shi Adam da yake jin zafin kalamanta na bin zuciyarsa, ya tashi yana binta yana fad’in ” Da baki sona sai dai ki dau wuka ki kasheni, inba hakaba wallahi bazan daina bibiyarkiba ke d’in tawace bawanda ya isa ya aureki muddin ina numfashi” batason kalamansa don haka da gudu ta fice daga gate d’in gidan, agun ya durk’ushe yana haki don bugun zuciyarsa na ya k’aru da yawa lokaci d’aya yaji k’afarsa bazata iya d’aukar saba, yafi minti biyar a hakan kafin ya koma cikin gida inda sukuma su Safiyya suka rasa me zasuce, azuciyoyinsu akwai tulin wasuwasi, gaba d’aya su biyun abun tausayine, don Adam yana cikin wani yanayi da kowaye yagani yasan yayi nadama ba abunda yakeso sai dawowar Khairi, ita kuma ayanayinta tana nuna batason sake rayuwa dashi in aka matsa mata nan ma matsala ne, yana shiga yaga tagumi a fuskar Safiyya ya samu ya kwanta akan kujera, cike da tausayi Muhsin yake kallonsa yace ” Tashi kije ciki ki kawo masa abinci daga yanayinsa nasan baici komiba duk bakinsa abushe yake” tashi tayi ta nufi kitchen kafin ta dawo yake wa Adam magana ” Ka kwantar da hankalinka nasan bawanda zai bi bayanta akan ta ki komawa gareka, kana bukatar nutsuwa karka sa wani ciwon ya kamaka” sai da ya ajiye numfashi yace ” Bazaka ganeba irin kalaman da take su suke sage mun zuciya, naji tamkar bazata komaba jadda dawa take bata sona kallo yanda take kuka, wallahi ina sonta bazan kara daga mata hankali ba, sontane yake sakani kishi naji sam bana son naga tana alak’a da kowa” daidai lokacin Safiyya ta shigo dauke da babban tray da tahado abinci da ruwa kai, ta ajiye da kalamai masu dad’i Muhsin ya samu yaci, ita kuma Safiyya shiga d’aki tayi ta shiga tunani, gaskiya tafara jin tausayin sa gefe daya kuma bazata bi bayan a takurawa Khairi ba, sai bayan sallar magriba Mama ta shigo part d’in tagansu inda suka mata sallama sannan suka fito tare da Adam suna k’ara kwantar masa da hankali, yad’an ji sauk’i amma yana son yasan halin da take ciki….+
STORY CONTINUES BELOW
Khairi da ta isa gida a falo ta tarar da Ummin ta, k’ura mata ido tayi tace “ke tsaya anan wacce iriyar d’abi’a kikeso ki kawo mana, ace kina tafe cikin layi kina kuka daga nan gidan zuwa gidan Mama, saboda ki nunawa duniya wata b’araka ta shiga tsakaninmu dasu, ki fita a idona na rufe bana son bankad’a” sumi-sumi ta wuce d’akin ta bata fasa kukanta ba, tabbas yakamata take adana kukanta saboda kar agano da wata tsakanin su, mutane sunsha yabon alak’arsu don wasu har yanzu a unguwar su dauka suke iyayensu ciki d’aya suka fito, amma ita da zarar za’a maida magana tsakanin ta da Adam ko yana waje sai taji k’irjinta na tasowa dole sai ta zubar da hawaye take jin dad’i.
Ko k’afarta Ummi bata ganiba afalo har k’arfe tara na dare, sannan ne ta bita d’akin lokacinne ta tararta ta fito daga toilet tana fesa perfumes, tana jin shigowarta ta maida hankalinta inda Ummin take tsaye, tana takowa izuwa gareta Ummi tace ” Samu wuri ki zauna” zama tayi ita ta zauna kusa da ita ta kawo fuska sakakkiya tare da muryar nasiha tace ” Ummulkhairi yana da kyau a duk sanda zuciyarki take raya miki abubuwa ki dinga d’orasu a mizani, ba kowanne lokaci zuciya kemana sak’a mai kyauba , tabbas kinyi namijin k’ok’ari da kike rufe sirrinki da biyayya batare da kin raina mijinkiba, duk abunda ya miki kin jure kinyi hak’uri na jinjina miki, to yanzu ki duba baga ribar hak’urin kina ganiba, yau ya rabu dake amma hankalinsa yak’i kwantawa so yake yau ko magana mai dad’i ta shiga tsakaninku, kinga d’aya daga cikin ribar hak’uri ko” jijjiga kai tayi sannan tace ” ki kalleni ni mahaifiyarkice ban taba baki lokaci don naji meye takamaimai abunda yasa kika dawo daga rakiyarsa har hakaba, bayan kowa yasan shak’uwar dake tsakaninku” ana ta fad’a mata wasu abubuwan da da bata jiba, shiru tayi nawasu minutes tana nazari tace ” Nagama fuskarta inda matsalar ku take, tabbas wauta da saurin hawa suka kaishi suka baroshi, amma Adam ba wai zargin yake miki har cikin ransa ba, kawai yana rasa inda zai dora maganar ne don da ya na zarginki dasu babu yanda za’ayi ya dawo gareki a kishi irin na d’a namiji, ke kuma inda kika bada gudummawarki rashin tsayayyarki na wasu abubuwa baki dan yin digir-gir shiyasa yasamu yake komi yanda yakeso, zai muki abu baki nuna bakiso don ya kiyaye gaba, bakuma ina nufin kizama uwar mita da korafiba, amma akwai sanda akai abu yakamata amatsayinki na mace mai aji ki tauna tsakuwa” ta numfasa tace ” Ina fata kin gane, bayan haka har yau Adam yana sonki, bance ki koma masaba don ko da kika aureshi yardace azuciyarki idan babu ita yanzu baza’a tursasakiba, amma kisani shi wanda kike tunanin aura bakisan kalar halinshiba shima sabon darasi zaki dora, sannan kuma bakison kalar matarshiba zuwa zakiyi gidan wata da tagama tsara komi nata, so dole kibi yarima asha kid’a don zaki tarar da rayuwa daban da taki sanda kina ke kad’ai, don haka ki tattara nutsuwarki idan har ranki ba Adam ciki to karkice zaki koma don zaki sabawa mahaliccine, don dazarar bakimarsa a idonki zakike take iyakokinsa hakan na nufin shiga fushin ubangiji da tsinuwar mala’iku” Khairi kam tayi shiru don maganganun Ummi gaskiyane, ganin yanda diyar tata ta nutsu take sauraronta yasa ta kara mata nasihu da dabarun zama da miji ta siga maikyau, tak’aru sosai karshe tamata godiya sukai sallamar bacci..
Tunda Ummi ta fita ta ke d’aukar kowane statement take nazarinsa, amma fa ita Adam ya sire mata ayanzu duk da yanzu ya fara bata tausayi, sai dai takan tuna rashin tausayi da ya gwada mata, tana da juna biyu ya iya rufe idonsa ya dinga sakata bacin rai karshe harda saki ga mari da kaiwa bugu, idan kuma tayi duba da other side dinshi banda rikicin kishi da aikinta yana kula da ita, don sun yi soyayya anutse acikin gidansu yakanyi kaffa-kaffa da ita bak’wara agado, ko tauyewa na ciyarwa da tufatarwa don koda take aiki baya ido kan kud’inta, tsabar ta shiga rud’ani bata iya kiran Ahmad taji ko ya sauka lafiya ba sai shine yakirata, bayan sun gaisa tace ” Kayi hak’uri na sha’afa ban tambayeka hanyaba, i was busy ne d’azu” murmushi yayi yace “Bakomi nagane komi, d’azu munyi magana da mutuniyarki tace na gaisheki” dariya tayi tace ” Allah sarki ina amsawa, kace nima ina gaidata” jin voice dinta sai a hankali yasa yace mata “it seems you are sleepy, Goodnyt” bata musaba tace masa ” Night” yana kashewa ya kalli phone din full of thoughts sai da yayi jima yana nazari, don yagama gane yanayin muryata kaman tayi kuka, balle yasan abunda ya faru akwana biyun nan, shi amatsayinsa na namiji gaba d’ayansu zaice sun bashi tausayi, don mutuwar aure bata da da’di gashi saki d’ayane dole Adam yaji yana da damar mai data, yana haka wayarshi ta fara ringing dole ya daidaita nutsuwarshi don baiso yadaga ajishi ba daidaiba, yasan bazata ji dadiba zatayi ta tamyarshine akan meke damunsa….. .
Adam tunda ya shiga gida ya tarar da Abida na chats dinta, amma ganin shi haje-haje yasata bashi kulawa, amma baibi takan abinciba, ita kuwa Abida gaba d’aya bata jin dad’in rashin bata lokacinsa da yakeyi, shiyasa ma take so yau ta bijiro masa da maganar, da misalin k’arfe goma na dare ta sameshi yana kwance yayi nisa a tunani har sai da ta d’ora kanta akan k’irjinsa sannan yasan da zuwanta, cikin muryar shagwaba tace ” Habibi wai me namaka kadaina shiga al’amurana, bakasan zama acikin gidan nan baka zama tare dani duk kasa ina mussing d’inka” yasan baya zama yanzu agidan sosai yakusa wata baya zama sosai suyi hira dashi, balle tasamu wani kulawa na soyayya, dakyar yake sauke hakkinsa bayan kwana hudu-hudu wannan week din daya k’are kuwa banda peck in zai fita dayake daurewa yake mata zaice ko dogon kiss bai had’asu ba, saboda ita sha’awa bata wanzuwa acikin damuwa da rashin nutsuwa sam sai tayi k’aura, shafa kanta yayi yace ” Abubuwan shagone suka cushemin shiyasa, ba ‘a nutse nakeba amma kiyi hak’uri zan kokarin dawowa kan lokaci, sannan please kidaina yawon nan in ina zuwa na tarar bakyanan shike sani jin haushinki” dake abun yasha mata kai tana son mijin nata, kuma tana tsoron wata ta shigo rayuwarsa tace ” Insha Allah zan kiyaye kaji, amma kake dawowa gaba d’aya inaji kaman baka sona” rufe mata baki yayi yace ” Ki daina cewa bana sonki haba, kece naga baki damuwa da lamurana” da kilibibi sai da Abida ta samu kansa..
Tunda akai wannan rikicin sai da Muhsin yace kar ya zo kwana biyu inda Khairi zata ganshi, yabata iska zasu san yanda za’a bullowa lamuran…
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
38
Adam da shawarar Muhsin yayi amfani duk da yana son ganinta haka ya hak’ura, baya zuwa sai dai ya je gaishe da Mama, shima in ya shiga yaji tashin muryar Khairi sai ya juya sai bata nan ya sake dawowa, sai a waya da kullum sai ya ajiye mata text na ban hak’uri da yakan bata tausayi, wataran ko kuma ya tura mata morning message tareda wani piece of hadith ko verse da yake nuna ribar hak’uri da falalarsa, bata replying kwata-kwata+
Gobe ne dawowarsu Hafiz da Sayyid saboda haka gaba d’aya gidajen nasu gyara akamasu, aka gyara d’akunan su da komi, bangaren snacks da wasu abubuwan duka anyi ansa afridge sai washegari za’a soya, duk da Safiyya tayi nauyi sai da tazo, alokacin ne ta k’ara keb’ewa da Khairi tana shan cikinta taji ko tana da niyyar komawa gidan Adam, amma sam ta kasa gane alk’iblarta saima yini da taga tayi tana waya da Ahmad duk da dai bawani hirane na soyayya ba amma da alama akwai understanding da respect tsakaninsu is obvious Khairi na enjoying company d’insa, take sai taji tausayin dan uwan nata amma ko daya bata ga laifin Khairin ba, sai dare suka koma gida
Ranar da suka dawo zo kaga farin ciki afuskokin iyalan gidan, gaba d’ayansu sun canza sunyi tas ga girma da sukai dukansu, had’uwa sukai gidansu Khairi ana hirar yaushe gamo, hakan yasa Adam ya yini yana ganin Khairin tasa duk da bata bari abu ya had’asu ko kuma in ana magana ta had’o dashi sai tak’i magana ta fake da fake smiles, da la’asar jam’i sukai a falon nasu, ana gamawa aka fara serving abinci Khairi ke zubawa kowa, tana zuwa kusa da Adam ta had’e ranta ta zuba masa tare da cika masa wani sauce da tayi mai yaji, sosai ta zubashi kan nashi abincin ta yanda dole ya fito sosai, yana ankare da hakan amma sai ya basar, ya daure yake turawa ahakan dakya, komawa tayi ta zauna bayan tagama take shan banana shake, shikuwa duk motsinta yana kansa k’warewa yayi ya dinga tari sai da hankalin kowa ya dawo kansa, don kaman zai shid’e yana neman fad’uwa, cak ta tsaya da shan abun da take ta zuba masa ido cike da fargaba, su Sayyid na rik’e dashi idonsa na bud’ewa dakyar a haka yasamu yad’an lafa still tari yana taso masa kad’an-kad’an, sai sannu suke jera masa, Safiyya da Ummi idonsu yakai ga yanda tayi reacting abu biyu yazo zuciyarsu k’ila tana da hannu ahakan sannan kuma akwai alamun damuwa sosai, hakan yana nufin har yanzu tana sonsa kenan adake Ummi ta kalleta tace ” Khairi je ki samo mashi peak guda d’aya ki kawo masa” tashi tayi ta d’auko bayan ta bud’eta ta kawo masa, kasa kallon sa tayi shikuma sai neman saka idonsa yake anata tare da karya wuya da salon ruwan abun tausayi, luckily ya samu idonsu ya had’u hakan yasa ta karanto marairaice wa aciki, kallon ya shigeta don taji tausayinsa ya taso mata amma sai ta dake ta juya takoma wurinta ta k’irk’iri dariya tare da jefawa Ya sayyid tambaya akan tafiyar tasu..
Wurin k’arfe goma su Muhsin suka tafi gidansu, haka Adam ya d’ebi kafarsa ya tafi cike da kewarta, don zaman yinin da sukai yatuna masa good memories dinsa da ita, dake dare yayi har ya shige bedroom Abida batasan ya dawoba, sai jin mutum tayi akanta saboda yayi sallamar ma batajiba, a zabure ta tura wayar ta ta under pillow ta shiga masa sannu da zuwa, k’ureta da ido yayi yana son yin nazari yagama gane al’adar tane hakan natukar ta ganshi sai ta tsorata indai da waya ahannunta, yanzu yafara rashin yarda da uzurinta da wayar, shirin wanka yayi sai da taga ya shige ta janyo wayar sukai sallama da Zumanta dama vedio call suke na fitsara duk tayi rashe-rashe da dan iskan rigar baccin jikinta, shiyasa ma tabar bulb akunne yanda zai ganta dakyau suna zuba dirty talk duk sun tada hankalin juna, gashi yanzu Adam yazo ya katse musu jin dad’insu, sai da yafito ta iya mik’ewa ta kawo mishi kayan bacci, yana sakawa ya kwanta sai wani kisisina ta take saboda bai bari ta sauke jarabar da suka kunnowa kansuba ita da Zumanta, don haka takeso ya bata dama amma ina sam baya jin hakan, yanzu ba wadda yake gani illa Khairi, baya jin sha’awarta ko kad’an sai ma yawaita mafarkin Khairin da yake, ganin tana takura masa yace mata tayi hak’uri baya jin dad’i, bata nuna fushiba tace shikenan, baifi minti uku ba yayi bacci ita kuwa ta fice zuwa d’ayan bedroom d’in ta nemo Zuma su k’arasa, shikuwa shegen kaya dama abunda yake so kenan tuni suka d’ora daga inda aka tsaya..
STORY CONTINUES BELOW
Jamila ta gama shirinta tsaf na dawo wa daga hutun haihuwa, saboda haka suka turo kannanta azo agyara gida agoge, dake ranar aikine Ahmad baya nan suka zo sukayi gyaransu anutse da zummar gobe zata dawo da safe.
Washegari haka gidan nasu ya k’ara cika da yan zuwa sannu da zuwa daga familyn kwaru, shiyasa gidan nasu ya cika da mutane har Hajiya Inna sai da tazo, hakan yasa Khairi tazama very busy daga kitchen zuwa falo, don Safiyya anyi nauyi sai d’an abunda ba’a rasaba take daga zaune, tana cikin kitchen Salma ta biyota da waya ana kiranta Umaima ce, tasaka wayar tsakanin dankwalinta dake karamace ta na cigaba da had’a abinci, bayan sun gaisa Umaima take tambayarta ya Ahmad dariya tayi tace “Sau nawa zan gaya miki babu wannan atsakanin mu fa” daga can b’angaren Umaima tace “nikuwa ban yardaba, amma indai ta tabbata gaskiya ni banji dad’i ba, ina Ya sayyid? Naso munyi hutu da sai nazo cikin week d’in nan” tace ” Eh wlh koni na matsu kiyi hutu kizo mana, don gidan duk shiru yake min ba abokin hira” da haka sukai sallama bayan tace ta gaida Anty Asiya, dake agidansu Adam ne suke ganinshi tayi ya shigo kitchen d’in ta k’ofar baya unexpected, sai jin buruntu tayi aikuwa tuni ta zabura zata fice daga kitchen d’in mistakely ta taka bawon ayaba sai gata ta tafi suuuuu zata fad’i, ahanzarce ya rik’ota idon gam ta runtseshi tsabar tsoro tana jiran tajita ak’asa, sai dai jinta da tayi bainas samawati wal ardi sai ta d’an ware idonta taganta rik’e ahannunsa tuni ta tureshi da d’ayan hannunta da ba ludayi, don tsabar tsoron ludayin miyarma bata ajiyeba ta saka gudunn take ta had’e rai ” To sakeni kuma kawani damuk”emun jiki, wannan ai haramun ne” binta da ido yake yana ganin k’arfin halinta, sai yayi murmushi ta gefen baki yace ” Ayi hak’uri, nima banso hakan ta faruba” ta k’ankance ido tace ” Eh zakace hakan mana, kai ka tsora tani ai da duk hakan bata faruba sannan ka cukukuyemin riga kasa tayi squeezing, sau aukin bada hak’uri kaman bakasani kayi” ba isashiyar lafiyace dashi ba shiyasa ya koma gefe ya zauna kan plastic chair dake can jikin kofar store ya na d’an murmushi, komawa tayi kan girkin nata tana muzurai sai da ta juyo zata nemo warmers ta kwashe taganshi ya k’ure bayanta da kallo ” Wallahi an kalli na Allah ya isa” tafad’a tare da murgud’a baki dariya ce mai sauti ta kwace masa yace “Nan d’in kin manta har tsarki nasha miki kina yarinya, to wane darene jemage bai ganiba” bata da abin cewa kawai ta fice don nemo wasu yan matan su tayata fita da abincin, ai dai dole ya kyaleta in yagansu har Abida kuwa suka taso don ranar itama ta zo duk da zata koma da wuri, batayi mamakin ganinsa akitchen d’inba don ta lura da sauyinsa so yake ya dawo da matarsa, take wani kishi ya taso mata sai da ta fakaici ido ta watsa masa harara, tsare fuskarsa yayi tare da mata warning ta ido which means dont dare misbehave, ta cuno baki tare da fuzgar flask a hannun Khairi ta fice. Haka kwana uku suka shude na dawowarsu Sayyid a Hafiz kullum k’afar yan uwa na zuwa gidansu shima kuwa Adam yana ciki don yana more kallon matar tasa, kuma sai ya ja abunda zaisa ta tanka masa, koda tsiwane tayi yana jin dad’i..1
Jamila sai da akayi su lalle da kitso sannan ta dawo, ta samu tarb’a mai kyau daga maigidan nata bakinta har kunne, gashi dama yayi k’okarin ajiye duk wasu abu da suke buk’ata agidan, da dare dole Ahmad yayi k’ara’i yanda yakeso itama batayi k’okarin hanashiba, don tasha gyara a buk’ace take, sai wani sabon amarci suke ita dashi, washegarin ranar sai 11 ya shiga school, umar kuwa yayi ta zolayarshi shikuma yaki biyeshi sai yar dariya yake sai da yaga yana neman kureshi yace ” wallahi zan ma iskanci”..
Sai da ya shanye cup d’in green tea da ta had’a masa yace ” Wai ya naga kin mak’ale mana agidane, bazaki koma gidankiba shima Ya Adam shi yaso ya zuba maki ido, bagashi Safiyya kullum gidanta take komawa ba” jimm tayi kafin tace ” Ai ni yanzu kullum anan nake kwana” Ummi kuwa batace komiba sai ma tashi da tayi ta d’aukawa Abba jakarshi zai fita office, shima Abba bai nuna yaji maganarba suna fita ya kalleta yace “Bangane anan kike kwana ba wanne irin aure kuke hakan” tace ” Ai mun samu sab’ani nidashi yanzu hakama ba aurensa akaina” a zabure ya tashi yace ” What!!!! You mean u are divorcee, buttt how comes?” dole yayi mamaki in aka duba tulin so da shakuwar dake tsakaninsu, ga alak’a tasu ta iyaye kuma su Sayyid tunda sukazo basu ga wani canji tsakanin iyayen nasu ba, kama hannunta yayi ya ce ” what’s happening? meya yayi zafi har haka duk yanda kuke dashi? Ko ke kika nemi sakin?” duk ya wani dubulbule sama-sama ta fad’a masa main event da causes, shiru yayi gaskiya baiji dadiba kuma yaji haushin Adam d’in duk da gefe d’aya ya masa uzuri he’s a man yasan yanda kishin wasu mazan yake amma bai tab’a tunanin Adam can do this ba, amma bakomai kwantar mata da hankali yayi yace “What are your plans know” tace ” Ina so kawai na d’ora karatuna ne, ni da za’a barni i want to go far away koda acikin k’asar nan ne ya zamanto bazamuke had’uwa ba” murmushi yayi ” Kina nufin kin gama auransa kenan? Ko you dont like him anymore? Hmmnn dont decieve yourself har yanzu kina son shine shiyasa kike kara jin zafin abunda yamiki thinking of how could someone u cherish do this to you” had’e rai tayi tace ” Nidai bana sonshi yanzu just na tafi karatu in nadawo nagani if i can marry someone again, infact na tsani harka da maza yanzu fa, ba aure agabana shiyasa ma nake son na gudu don naga Ummi bazata kyaleniba” kallonta yake yace ” Shikenan Allah ya taimaka but Aure wajibine kanki bayama da kika taba yi, bawanda zai kyaleki sai dai baki samu manemiba”…
Yana tsaye yana waya a parking lot ta hangoshi ta window na kitchen d’inta, jan tsaki tayi tace ” Na lura fa Abban Aslam baida aiki sai jarabar waya, haba tunda na dawo hakane ke faruwa” fitowa tayi ta nufi parking lot sai kuma gashi shima zai shigo falon, tayi turus tana kallonsa shima kallon ta yake da mamaki yace ” Sweety ina zaki kuma? Ko wani abun kike so asayo zaki nemi d’an aike?” inda-inda ta shiga yi sai kuma ta koma, dariya yayi yana da yak’inin ganin yak’i shigowa yayi wayarne yasata zargi yace ” shure-shure baya hana mutuwa my Jam-jam” yayi dariya yana zama kan kujera text ya shigo masa ya bud’e take ya shiga wani murmushi, tsaf akan idon Jamila tace ” Abban Aslam ko kud’ine suka shigo akeso ab’oyemin” yayi dariya yace ” Ai kinsan haka akeso maza sukeyi, don halin matane da zarar kunji kud’i sai ku fara fito da kala-kalan needs don ku kunfi gane kashewa ba saving ba” dariya tayi tace ” Haba Abban Aslam kudai maza kemana wannan kallon, amma ai kud’i abun kashewa ne”
Wannan satin Khairi takoma wajan aikinta , cikin shiga maikyau ta fito da niyyar tafiya asibitin, tana tsaye cikin Layinsu wani mai napep zai ajiye wata mata gaba dasu akan zai dawo ya dauketa, sai ga Adam a mota zai shiga gidansu, ganinta atsaye yasa yayi parking ya mata magana ” In bazaki damuba kizo na saukeki” dauke kanta tayi shikuwa baiyi k’asa agwuiwaba ya shiga rok’arta akan ta shigo, don take yaji haushi tayi kyau ta tsaya a titi akalle masa ita, jan tsaki tayi tace ” Wai Malam ana dolene? Nace bazan shiga ba haba kaima in ba so kake araba zunubin dakaiba kayi gaba, karka manta iskanci nake zuwa asibitinfa kaga in ka kaini kaima kabi sahun yan taya b’era b’ari kenan” zugum yayi yakasa magana yace ” Shikenan na yarda araba dani, sannan kuma kidaina jinginawa kanki kalmar iskanci da wasu ina jin zafinta a raina” wani karamar shewa tayi ta ce ” Wata sabuwa, yaushe kenan? Ina kaike fadi bakaji zafiba sai yau, kaga don Allah ja kara mai kayi gaba kaje inda kake da kwarjini ba nan ba” daidai lokacin mai napep din ya tsaya bata jira komiba ta shige tabar Adam da sakakken baki don bai da tacewa
1
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Jinjina ga amsu comment da Addu’a ina jin dad’i sosai, jazakhumullah bilkhair
39
Tarb’a maikyau tasamu bayan dawowarta ga aikin nata, shiyasa hankalinta ya k’ara kwanciya take aikinta yanda ya dace, ta kowanne bangare tana samun support especially mutum biyun nan H. O. D da Dr Aliyu tunda yanzu da sauk’i ba aure, tana k’ara gogewa ta fannin aikin nata, ga Yayan ta Ahmad daya zama uban shawara da kuma rage mata kewa..
Dake yau yakama weekend d’an wajan Maryam Tafida ta tafi dubawa baida lafiya Taufiq d’an shekara uku, tunda taje suka shiga hirar duniya bayan ta ajiye mashi carton na bobo da packs na chocolates da chesse, yaron kuwa dake yafara samun sauk’i har ya shiga kallon catoon, don haka suke hirar su hankali kwance sai da lokacin girkinta yayi suka shiga tare suna hirarsu suna aiki, yau mijin Maryam zai zo mata kaman yanda ya saba saboda haka aikin da d’an yawa, suna tsaka da girkin nasu ne Maryam tace ” Nikuwa k’awata yaushe kika shirya komawa Adam, inaga kin wanashi iyakar yanda yakamata, saboda haka ki koma kawai ai ya shiga taitayinsa yasan muhimmancinki yanzu” yatsina fuska tayi tace ” Oh ni meyasa sai ina cikin good mood sai ki sakomin maganar wannan mutumin, har ma cewa nake dashi banda kwana biyu da mukaita had’uwa a dawowarsu Ya Sayyid” murmushi Maryam tayi tace ” Wallahi nasan har yau kina sonsa, don sonsa ke tura zuciyarki ga jin zafinsa, kin manta tarin soyayyarsa da kike fad’amin” shiru tayi ta cigaba da juya miyar ugwu, har suka k’are girkin bata yarda sun cigaba da maganar Adam ba, sun gama da abincikan sai had’a kaza da Khairi tace zata mata ita taje tayi wanka tunda sunyi waya yana daf da shigowa kanon, tanayi tana tunane-tunane tana marinating chicken d’in tana tuna wani lokaci da take hakan cikin Kitchen d’inta, Adam ya shigo tagama Marinating yazo jan tsokana don yasan batason ana tab’a mata girki bata gamaba, don majority mata na da halin haka anashi tunanin ta kammala kenan zubawa ne batayiba cikin flask, ya d’au cinya tare da saurin sakata abaki bayan ya kashe mata ido, maimakon yaga ta cuno baki ko ta nuna masa bataso as usual sai yaga ta kwashe da dariya lokacinne kuma ya gatsa cinyar yaji taki ciwuwa ga yajin masifa da yaji, take yayi sink da gudu yana tara bakinshi k’asan sin, wani murmushi ne ya k’wace mata da ta tuna yanda yayi saboda sai da ya jike rigarsa da ruwa yana shishitu duk ya ci d’anyen spices da ta had’a jiki, bata ankara taji har Maryam ta fito taganta awannan yanayin, sai da tayi tapping kafad’arta sannan ta dawo nutsuwarta Maryam ta kwashe da dariya tace ” Yarinya gidanki kike missing im sure inda zakai girki bayan albarka abika da romance da romantic gifts” tak’arasa tare da kashe mata ido sannan tace ” Wallahi iyakar aji fa kinma Adam so kawai ki bada had’in kai kodan farin cikin iyayenku, kisa hope akan bazai k’ara maimaita na baya dama zaman aure ai dole da k’alubale, don wasu matan in kikaji files na zaman aurensu sai kinsan kukan ciwo kike bakisan gyambo ba” bata iya tanka mata ba sai hararar wasa da ta watsa mata..+
Sai Yamma bayan ta gama shiryawa ta fito da zummar tafiya, mijin Maryam tuni sun shigo farfajiyar gidan tare da wani abokinsa, suna had’uwa ya fad’ada fara’arsa tare da gaisawa da ita yana cewa ” Yanaga kina shirin fita don nazo, wato gulmar tamu da kukene bakwaso muji ko?” dariya tayi tace “Ai tuni wannan mungamata duk wasu matakan tsaro mungama tsarasu, shiyasa ma zan tafi” yai dariya yace ” Ina fatan dai za’a sassautamin don naga kwana biyu k’awarki ta gama dani” tace ” Yanzu aka fara ai ba’aje ko’inaba” Maryam dake tsaye cikin kwalliya da kamala sai murmushi take, saboda dama mijin nata akwai barkwanci yasaba jan Khairi tun tana nauyi har ta saba tace ” K’awa rabu dashi wai fa ko Plan A bamu gamaba ya karaya haka” kallon Maryam d’in yayi cike da soyayya da kewa kana ganin yanda idonsu ya harde kasan sunyi missing juna kuma kana ganin yanayinsu suna cikin zaman lafiya, da wasa da barkwanci tayi sallama dasu duk da yaso takoma amma sai ta kawo uzuri mai k’arfi, zata tafi sai Abokinsa Alhaji Jamilu da tunda suke wasan yake d’an murmushi yace shima zai k’arasa nasa gidan, don haka zai kai Khairi gidansu, sun gaisa bayan ta shiga motar ta fad’a masa unguwarsu, lokacin ne zuciyarta ta tafi sha’awar rayuwar tasu don itama sunyi fiye da ita ma itada Adam, tana cikin Napep tana tunane-tunane gaskiya Adam bai kyauta mata ba saboda ya maida ita bazawara..
STORY CONTINUES BELOW
Daidai k’ofar gidansu yayi parking ta fito da ledar snacks da Maryam tayi insisting kan sai ta taho dasu, ta masa godiya bayan ta rufe k’ofar motar sannan ta shiga gidansu, yana tsaye a k’ofar gidansu yaga wani ya sauketa lokacin suna magana akantane tare da Muhsin da Hafiz, wani irin haushine yake cimai zuciya bazata game takaicin da yake jiba, kallon Muhsin yayi yace ” Kagani abunda banaso kenan, sai naga kaman bata planning sake aurena bana jindadi wallahi” kwantar masa da hankali suka shiga yi amma ina wani zazzabi ke taso masa, ahaka yayi sallama dasu ya nufi gidansa..
Adam yana zuwa gidansa ya tarar batanan, don haka zuciyarsa ta k’ara hasala wanne irin abune wannan wai, ya k’ira wayar Inno don yaji ko tana can daga yanayin amsarta yasan batanan, amma sai yayi dabarar da bata gane bai san inda ta tafi bane ya kashe wayar..
Jamila tun dawowarta daga gida Ahmad yake taka tsan-tsan wajan yawan waya da budurwar tashi don baiso tasani har sai anyi engagement d’insu, yaci sa’a kuwa hankalinta yakau akan hakan.
Yau shida Umar tare da wasu kamar yanda suka tsara tafiyar tasu ta mutum biyar suka nufi Adamawa, shiyasa ma Jamila tayi tafiyarta yini kuma shi yabata damar hakan, dake tun dawowarta bata sake fitaba, tayi yawo sosai don sai da ta dangana ga sahibartata Samira, sai da taga yanda Jamila take shek’i ta shiga zuzuta ” Uwagida kuma amarya agidan Adam Maman chief of justice” murmushi tayi tace ” Kwarai kuwa, kinsan na yarda da maganar haihuwa da ake don yanzu tinda akai haihuwar nan lallabata da Ahmad yake ta k’aru”nidai nace ta neman aurece.. Shewa Samira tayi tace ” Dama ai hakane yanzu ya kike ganinki awajan surukanki” tace ” Star balle na haifi maigidan bani da matsala ko kad’an yanzu, sai abunda raina yaso nake ko makarar girki nayi bai cemin uffan, haka da nayi demanding k’udi bai fiya damuwa yaji na maye ba sai kiga ya bani” cika baki dai Jamila bata barshiba tana ganin haihuwa da soyayyarta tayi nisa gun Ahmad da bazama yayi tunanin k’ara aure ba..
Tunda ta shiga office take ganin Maryam na nuna tanason yin magana da ita in private, bata samu damar hakan ba sai da time d’in sallah yayi sannan suka keb’e tace “K’awata kinyi kasuwafa duk da dai kinsan ina sonki da Adam” zaro ido tayi tace ” Kaman ya fa?” Maryam tace ” Eh Alhaji Jamilu wanda ya saukeki rannan shine yace min yana so ya aureki” gabanta ne ya fad’i tace ” Kai how comes haba amma banga alaman komi ba fa” tace ” Dama bazaki ganiba kinsan manyan mutane, amma yana da kirki ga hali nagari wallahi” Khairi tace “Nidai gaskiya kibari sam banson jin maganar nan, kibashi hak’uri” gatsininta Maryam tayi tace ” Wallahi bazan fad’iba, akan me yarinya ki saurari kira yau don har na bashi number dinki, kink’i Adam kink’ishi to zuba miki ido zamuyi kina juya mana diri a titi kawai” dariya kawai tayi tace ” Sai kiyi naga alama zuwan Abban Taufiq yasaki wannan tashen maganar” suka fita suka cigaba da aikin nasu…
Sai da Adam ya murza yatsunsa guri d’aya yace “Kawu wallahi gaba d’aya hankali na yakasa kwanciya domin kuwa Khairi manemanta k’aruwa suke, gashi sam bata bani fuska na ganin ta koma d’in, kuma su Abba sunce had’in kanta zan nema su bazasuce komiba” shiru yayi yace ” Amma kuwa Yaya yakamata ya sauko mana, aduba shi mutuwar aure ba sonta ake ba yanzu ka k’ara ban lokaci zanje na tuntubi iyayen naka, ita kanta Khairin zanyi magana da ita” akan haka ya baro gun Kawu Bala
Kamar yanda tun bayan faruwar abubuwan nasu ya dage wajan bibiyar Mama tasa baki, hakan yau takasance yana zaune yana aikin da ya saba wato magiya da Mama tagaji tashi tayi tace ” Kaga fa auran ka da Khairi ya gama k’arewa tunda ka iya saka hannu ka datse igiyarka, batare da shawarar muba saboda ka nunawa duniya kai ka isa da kanka to ba shikenan ba yanzu ma kayi da kanka, kuma fitsarar ka har tasa baka jin kunyar had’a ido da Babanka Aliyu wallahi kaban kunya, ina nan saina aura mata miji mai hankali wanda yasan darajar mace” kamar ta burma masa harsashi haka yaji don sai da ya dafe k’irjinsa, har tana cewa zata aurawa Khairi wani abun tamkar sukan kibiya yake aransa, ko Hafiz dake niyyar shigowa sai da yaji ba dad’i, tayi shigewarta d’aki tabarshi awurin, sai da Hafiz yazo yayi saurin shiga kitchen ya d’auko masa ruwa mai sanyi, don take tari ya sark’emasa sosai dakyar ya kafa idonsa har yayi ja, itama kanta Hajiya Hassu dakewa take amma tanajin ba dadi tasan yaron nata ya wahala, amma ina batason ya sake don tanaji da zuriyar Aliyu ya musu halacci arayuwa alokacin da mutane suka juyawa Abdullahi baya lokacin siyasa..
Tana zaune a kasan carpet yana maida numfashi Hafiz yace ” Yaya tabbas kayi kuskure amma abunda nakeso dakai shine, ka jure abunda Khairi zata maka domun kuwa bamai kawo karshen abun nan sai ita” daga haka ya fice ya nufi gidansu Khairi yana zuwa ya tarar tana zaune tana cin aya mai sugar, da fara’a ta tareshi tace ” Ya Hafiz sannu da zuwa” ya amsa tare da zama yace ” Ina Ummi?” tace ” Taje gidan kaninta na zoo road” ya kalleta anutse yace ” In bazaki damuba inason yin important magana dake” dama ta tashi ne tana shirin kawo mashi drink cak ta tsaya tare da ajiye plate da ayar ke ciki tace ” Bari na kawo maka drink tukun na” Yace ” A’a dama kin barshi don yanzu haka daga gida nake” takoma ta zauna tare da tattaro nutsuwarta tace ” Ina jinka” yace ” Maganarku da Ya Adam ne, nasan ya miki laifi amma don Allah ki dubi girman yafiya da taimako ki yafe masa, ki koma kodan farin cikin iyayenmu wallahi Khairi kaf zuriyar Baba ba wanda yakeso ki fita acikinmu, sanin kanki ne zuriyarmu na muki so fiye da wasu jikokin nasuma, don Allah ki dubi wannan lamarin, da zaki ga yanzu akalar halin da na baroshi zakisan yayi nadama yanaso ya gyara kurakuransa, bason kai bane sai dai iyakar gatan da za’a masa shine samun mace tagari kamanki, za’a zauna ki gindaya sharadi akan abunda bakiso duk ranar da ya sab’a dakanmu zamuje mu taho dake, kinsan dukanmu daya muke ba banbanci” duk kalamansa gaskiyane tasan kalar kaunar da suke nuna mata shiyasa yanzu har kunyar zuwa family house dinsu take tace ” Ya Hafiz ai ni tuni na yafe masa, kawai dai zuciyata ce ke tsoron abunda zai faru ko na yanzu da ya faru kasan kaf cikinmu bawanda ya zaci hakan” yasan da hakan sai yace ” Kwarai hakane, kuma naji dadi da kika yafe masa atleast baida alhakinki yanzu, bazan kuma daureki da kalamina ba saboda bansan kalar bacin ran da kika sha ba, don haka karki damu kanki ki tauye kanki kawai dai ina son shima ki duba lamarinsa” tace ” Shikenan nagode zan duba” murmushi yayi yace bari ya fita
Sai da ya cusa hannunsa cikin gashinsa da ya taru akai sannan yaja tsaki yace ” Haba don Allah ni idan kinsan iyakar haka zakimin karma kisa nayi kasadar takowa gidanki” cikin kashe murya tace ” Haba don Allah kai dai basai kajiba, kasani ko suprise zan maka wallahi na k’agu kazo ni abuk’ace nake dakai”ta fad’a tare da shafar saman kirjinta dake vedio call suke yace “Shikenan gani nan zanzo, kin tabbatar dai ai bazai dawo ba” tace “Eh yace min zai biya ta Plaza inaga sai bayan isha’i zai dawo” jin haka yasa shi katse wayar ya buga fito yace ” Yau dai saina shiga k’oramarki hajiya” ya shiga wanka cikin sauri yayi wanka tare da zira kaya sai gidan Abida, tun daga k’ofa ya fuskanci shegiyar shiga tayi don katon hijab din da tasa iska ta d’aga kafarta yaga alamun kaya baizo wajan ba, suna shiga tun daga falo suka fara gigita kansu da romance daga nan tsabar sun gigice suka zarce bedroom adaddafe, gaba d’ayansu hannayensu sai job yake zubawa ajikin d’an uwansa, gaba d’aya hankalinsu ya gama fita ajikinsu don ya gigita ta yanda bata da k’arfin hanashi shigarta, daga falo ya ga white trouser ak’asa abun ya bashi mamaki don bana shi bane sannan idanna ganewane baiyiba ai baida dabi’ar zubar da kaya a falo, nufar bedroom d’insa yayi don baijin dad’i tun maganganun Mama suka had’e da ciwon da yake atafe suka dagula masa lissafi, don haka ba abunda yake buk’ata illa ya kwanta, yana tura k’ofar d’akin ya tsaya yana wata mahaukaciyar karkarwa, Zuma yana cikin jikinta… Imagine mutum yaga matarsa turmi da tab’arya da wani balle Adam da kishinsa
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
40
Yana tsaye yana karkarwa Zumah yayi juyi da zummar sauya style yaganshi, take a gigice Zuma ya d’ago ya fuzgi rigarsa dake gefen pillow ya nufo jikin k’ofar, Adam shaking jikinsa yake shiyasa bai iya masa kyakkwan rik’oba, tuni yasamu damar fuzge daga jikinsa ya nufi waje, cikin kukan kura ya nufeta ya cakumota a tsirararta ya shiga gwara kanta da jikin bangon dakin zuwa jikin mirror yana ture kayan kai da kanta, tuni kuwa jini ya b’alle mata yayi wurgi da ita ta fad’a agicciye akan bedside ya nufi k’ofar gidan nasa, shi kuma Zumah cikin tsautsayi kofar ta mak’ale yanata fama yakasa bud’ewa wandon ko gama maidashi baiyiba kaman yayi ass down, kamoshi yayi ya shiga bugashi ga gate d’in, sai ihu yake mai shagon opposite dinsune sukaji ihu tare da wasu samari su biyu suka taho gidan, mai shago ya saka karfi ya bugo k’ofar ta bud’e kafin nan fuskar zuma taji ajikinta, suna bud’ewa Zumah ya niyyar guduwa caraf mai shago ya rik’eshi duk da baisan meke faruwaba, shiga rok’onsa yayi don Allah ka sakeni kasheni zaiyi wallahi, shi mai shago ya maida kai ga Adam da yakeson rik’eshi kuma lokaci guda yana tambayarsa akan mi ya faru, hakan yabawa Zuma damar zillewa ya buge sauran samarin ya samu ya ranta ana kare, Adam yana tsaye sai huci yake kuma kafarshi na rawa yace ” lawwali wannan shegennn na kama acikin gida na” take suka had’a sallallami, har yanzu numfashinsa fuzga yake ga wani irin rawa da jikinsa yake, sun rasa me zasuyi, baisan me zaiyiba haka kuma juwa yake ji kawai ya juya da niyyar komawa cikin gida sai dai ina k’irjinsa yayi nauyi hade da kansa, taku uku yayi ya dafe k’irjinsa yana jan numfashi lawwali ya ce ” Subhanallah” tare da daya saurayin suka nufeshi tare da rik’eshi yana jan numfashi dak’ar anan ya sume, gaba d’ayansu ba wanda ya iya mota lawwali ya kalli d’aya acikinsu yace Hassan d’an rik’eshi mu shiga mu sanarwa matar tasa, bai sake shiba wayar jikinsa ta shiga kuwwa, Muhsin ya gani ajiki kuma da pic dinsa da yasa as contact pic, lawwali take yagane fuskar don yasan yana ganinsa yana zuwa infact yasan ana cewa k’aninsa ne tuni ya d’auka ya irga masa komi yace mashi gashinan, baifi minti hudu ba sai gashi don dama yana hanyar zuwa gidan ne, halin daya ganshi yabashi mamaki don har da ciwo ahannunsa da yayi alamun kwalaba sai jini ke tststsafowa, take ya rarumeshi yasa amota tare da taimakon lawwalin, su Hassan suka koma don kula da shagon, da gudu sukai asibitin da yasan suna zuwa sosai, sai da aka shiga da shi emergency sannan ya tuna yakamata a nemi Abida, duk anyi komi ace ba ita wai meke faruwa ne? Ya tambayi Lawwali shikuma ya fada masa yanda suka ganshi, suna bakin wajan sai ga Dr Kibiya agigice sun kawo wani saurayi da ya buge shima aka shige dashi don yaji ciwo matuk’a..+
Ita kuwa Abida tuni ta rufe kofar dakin ta ciki don gudun kar Adam ya dawo ya cigaba da bugunta, taji jiki sai jini ke d’ibarta saboda duk taji ciwo da kwalaban Perfumes na kan madubi ga rad’adin da hannunta ke, da alama ma hannun ya goce, wayar ta ce tad’au k’ara dak’yar taja jikinta ta janyo wayar, sunan Muhsin da tagani ne jikinta ya k’ara sab’a rawa sai da ya kira ana uku ta d’aga daga yanayin yanda ta amsa sallamar yaji alamun bata da lafiya amma ya dake yace ” Abida kina gida ko kin fita?” rasa me zatace tayi ga murya a dashe na kuka lokacin ne taji radadin ya taso mata sai da tayi nishi, take zargin da yafara ya shiga gasgatashi don daga labarin Lawwali ya gano akwai rikici, kashewa yayi ya ce bari sukoma gidan, take suka dinguma shida Lawwali sai gidan, tun afalo yaga belt wadda ta Zuma ce yayi knocking bedroom d’in amma jin tashin nishi yasashi turawa Allah yasa Abida taja bedsheet daga yanayinta yak’ara tabbatarwa, dama abinda ya zata shiyasa yace bari ya taho tunda yaji ance yace wani ya shigo gidansa yasan zai yi kokarin illatasu, runtse idonsa yayi don jini ya wanke mata gaban fuska ga yanayinta, wazai k’ira? Safiyya tayi nauyi da yawa iyayensu kuma baikamata ya fara sakosu yanzu ba until he know what actually happen Khairi ce kurum cikin k’arfin hali yace ” Ki daure kisa koda doguwar rigane zamu fita dake asibiti” dakyar taja kafarta zuwa closet ta janyo arabian gown tare da dankwalinta tasaka, dolensa ya tayata suka kaita asibitin to ita d’inma kafin aje jini ya fita sosai ta fara fita hayyacinta, sai dai me yanayin halin da Adam yake ciki ya wuce tunanin sa dole ya sanarwa iyayensu don yanzu haka oxygen ne jikinsa bai isa numfashi dakansa ba…
STORY CONTINUES BELOW
Daga yanayin sa Mama gabanta ya fad’i don tasan kwana biyu Adam kaman baida lafiya, sai mutsu-mutsu bakinsa yake dakewa tayi tace ” Muhsin me yake faruwane? Don na lura bakinka akwai magana” idonsa ne ya tara kwalla amma ya fuske yanda bazata gane ba yace “Mama dama Adam ne baya jin dad’i nakaishi asibiti, to yanzu sun bashi gado ita kanta Abidan bata da lafiya balle ta kula dashi she was admited too” bata ji maganar har kantaba kila yana boye wani abun, don jinya ai an saba yinta a rayuwa kodai abun babbane ko kuma ya mutu, tasbihi tashiga yiwa ubangiji tana maimaita hasbunallahu wani’imal wakeel, yace zai jirata ta kimtsa ya shiga gidansu yasa Khairi shiryawar dole don lokacin bata jima da idar da sallar magriba ba, ganinta kam dadduma yasashi tunawa yayi missing jam’i, shine ya shiga masallaci yi kafin nan sun gama shiryawa
Gaba d’aya sun hallara daga ganin yanda yake matan duka suka shiga kuka har Khairi, tayi magana da Dr yace kawai su tayashi da Addu’a zuciyarsa taga wani abu da ya d’aga mata hankalin wanda tayi barazanar bugawa, jin haka Mama ta rafka salati tace ” Adam na yafe maka duniya da lahira Allah ya jik’anka” Ummi ta toshe mata baki tana ” Haba cuta ba mutuwa ba bi’iznillahi sai ya tashi kan k’afafunsa” lokacin mazan suka zo tare da su Sayyid kowa yayi zuru-zuru, basu ga Abida ba don haka basu zargi komiba, Muhsin jan su Sayyid yayi ya karanta musu abunda ya sani yanayin reaction d’insu ne ya fad’arwa da Khairi gaba don ta lura, su kuwa su Mama suna gefe basu saniba, take kukanta ya k’aru wani irin tausayinsa ya taso mata aranta cewa take “inaga an fada masa he cant making it shiyasa yaki fada mana” tuni kukanta ya k’aru tana ji aranta harda matsin da ta masane suka jefashi awannan yanayin..
Sai da aka d’au kwana biyu Adam bai san wanda yake kansaba, ita kuwa Abida da aka mata dressing na ciwonta ta kwana biyu, alokacinne wata Nurse tace tana jin wari daga gareta da alama ruwa na fita ak’asanta don haka ana buk’atar d’iba agwada a Lab, kasancewar Asibitin su Khairi ne ita ta d’au wannan al’amarin, abunda ta zarga shine Abida na d’auke da matsanancin infection dole aka d’orata kan drugs kuma shima Adam dole abashi incase koya d’auka, maidata gida sukayi aka sanarwa Inno, duk da su basu san kan lamarinba tambayar duniya sun mata tak’i fad’a shikuma Adam bai dawo nutsuwarshi ba balle suji, bayan sun kaita gida lallab’awa tayi ta had’a kayanta na sawa da wad’anda take buk’ata har da kud’ad’e alokar Adam dubu saba’in da uku ta nufi gidansu, bata b’oyewa Inno komiba ta gaya mata, anan tace ta nemo Zuma susan matakin da zasu d’auka don tabbas Adam ya mik’e zasuci k’aniyarsu..
A asibiti kuwa Khairi ke kula da komi, gashi sanin ita staff ce Dr Kibiya ko bai da duty ranar yakan tsaya kan lamarinsa, tunba sanda suka maidashi ICU ba, yanzu Alhmdlh yakan ci abinci batare da taimakon komiba sai dai baya magana sai dai yake bin mutane da ido. Sai da akai sati da case d’in sannan Adam ya ware tunda yagama dawowa nutsuwarsa yake hawaye,ya kama neman yafiyar iyayen da Khairi yana cewa ” Narasa komi arayuwata, rayuwata ta tab’arb’are tunda na rabu da Khairi masifu suke bina don Allah ku dawo min da ita cikin rayuwata” gaba d’aya ya basu tausayi yacigaba da magiya ganin sunyi shiru suna binsa da kallo, take ya shiga tari numfashinsa ya kwacemar, cikin azama Hafiz ya nemo Dr, Mama sai kuka take gaba d’aya ta fita hayyacinta, tausayinta duk ya shigesu abunka da uwa dama daurewa take take nuna masa bazata goyi bayansaba, Ummi kuwa harda watsawa khairi harara. Koda ya dawo nutsuwarsa yakasa fad’ar yanda abun yake suna d’akin da akan ajiye marasa lafiya daga gefen gadonshi ta d’aya raw din Adam ya hango Zumah, wani irin tunzurace ta taso masa duk da halin da Zuma yake ciki sai da ya isa gareshi ya dak’umi kafad’unsa, aikuwa cike da ciwo yake magana dak’yar yana cewa ” Inna ki bashi hak’uri kar ya k’ara sani” itakuwa ta fara kuka tana cewa ” Dafta kuzo ku kama wannan mahaukacine kuka had’ashi da mutane zai k’arasamin d’a” lokacinne wasu nurses da Dr Kibiya da ya shigo alokacin hankalin su ya kawo kai ya kamo Adam Zuma yace ” Kayi hak’uri wallahi sharrin shaid’anne wannan ne karo na farko da hakan ta faru ka yafemin, inaji ajikina ajalina ya sauka” Dr Kibiya dai yayi kokari ya kai Adam gadonsa tare da dialling number Khairi yace ” Ina sauran yan gidankune? Inaga yakamata ku tafi dashi gida yanzu, tunda an sallameku” ya kashe wayar Adam sai tsuma yake na b’acin rai Dr ya sake komawa wajan Zuma yana dudduba ciwukan nasa da karayar da yayi ak’afa, domin shine patient da ya kawo ranar da akazo da Adam tsautsauyine yasa ya bugeshi, sakamakon gudun tsira da Zuma yayi daga gidan Adam, sai dai Dr gaba d’aya yana mamakin abunda Adam yayi tabbas akwai wata ak’asa, hak’uri ya bawa Innarsa ya fita mahaifiyar Zuma ta kalleshi tace ” Mujittafa kai kuma meye had’inka da wannan mutumin?” bai iya cemata komi sai hawayen nadama daya balle masa..
STORY CONTINUES BELOW
Bayan sun koma da Adam gida d’akinsa nada a kasa aka gyara masa, sannan ne yayi wanka da ruwan dumi ya fito inda kowa yake jiransa don jin kanin labari, gaba d’aya sun k’agu suji abunda yasa ska gansu kare jini biri jini, kafin ya soma basu labari ma yanayin fuskarsa ya canza ya dubi Khairi yace ” Don Allah don Annabi ki yafemin, nasan na zargeki na gaya maki maganganu na b’atanci na jingina maki zina batare da wata hujja da ta yi nasaba da itaba, ki yafemin nasan alhakinki ke bina, nakira zina a gidana lokacinda ba tushenta ashe na kirata cikin dakina ne, gashi takai anyi nina jawowa kaina” da mamaki suke kallonsa kamar ya anyi zina agidansa, take ya basu labarin komi wani irin tashin hankaline ya bayyana afuskokinsu tabbas dole atausaya masa, matarka ta sunna ta k’etara alfarmar mutumcinka har cikin bedroom dinka da wani k’ato, lallashinsa suka cigaba dayi ita kuwa Khairi sarkin tausayi sai hawaye take ganin yandw yake kuka haik’am kamar wani yaro tace ” Tuntuni na dad’e da yafe maka Allah ya yafe mana baki d’aya” Safiyya sai ranar tasan me ake ciki, don boye mata Muhsin yayi saboda yanayinta, ita d’inma share hawayenta tayi tace ” ashe abunda ake tayi kenan aka lullubeni, sai naga kullum ina neman yan gida ake min excuse da cewar busy ake” nasiha sosai iyayen maza sukai masa gami da nuna masa illar abunda yayi abaya, da nuna masa aiki bashike nuna lalacewaba ga Abida ko bokon batayi na kuzo muganiba ta kasance mara tarbiyya, gashi yasan koda bata aiki girki ma wataran sai ya dawo take d’orawa, sukace dama tundaga kaita washegari suka koma suka tarar batanan, sai suka dauka don bakowa ga jinyane yasata tafiya ashe gudun dukansa take, Adam yace ” Bazan iya komawa gidan nan ba yanzu tamkar maidamin da b’acin raina bayane, kuma zan aika mata da takardarta” bawanda ya ce masa k’ala
Adam yazama bakowa ba mata ga ba Khairi ga tulin b’acin rai arayuwarsa, don haka yazama abun tausayi, kullum sai ka ganshi gurum amasallaci ko dak’i, bai fiya maganaba sai zikiri kurum, a office ma daya koma sunga bai fiye walwala ba, da Ak da Sabeer sukaji zancen sukace ” Dama ko bincike bakayiba aka nuna maka ba’ason auren anan kaki gashinan ai” ganin yanda yake dole suka ware masa suka koma normal kullum suna jansa ajiki..
Ahmad yana zaune tare da mabiyarsa Anty Hujra dake aure a lagos tazo ganin gida, suna tsara maganar lefe da za’a had’o masa, sai list ake na abubuwa idan kaga yanda yake surutu dole kasan ba k’aramin jin dadin kusantowar auran nasa yakeba, kuma abunda ke k’ara masa jin dad’i bai wuce rashin sanin Sweetyn nasa ba, kowa yaja bakinsa yayi shiru daga b’angarensa hakanan ya sanarwa wasu a relatives d’inta harda iyayenta don kar ace bai gaya mataba sai suka sama wakilai, ita kuwa Jamila sai sha’aninta take yau in tai fari gobe tayi bak’i ita alallai isashiyace bakuwa ko kad’an ya nuna mata fushi ko fad’a, shiyasa tak’ara sakankancewa batasan tsiya tana nan ana shirin k’ulla mataba, kamar koyaushe yanda ya saba dawowa da yamma haka yau takasance yana shigowa ya tarar bata falon tana kitchen yin girki kallon agogon hannunsa yayi saura baifi minti bakwai a kira sallah ba gashi tasan yana azumi kasacewar ranar alhamis ne, yaronsu Aslam yad’auka ya shiga masa wasa, sai gata ta fito sakamakon wayarta dake ringing ” A’ah my one dawowar yaushe kenan?” yace ” banjima da shigowa ba” sannu tamasa ta cigaba da wayarta kana ta koma kitchen, koda ya dawo daga sallar abunda yace ayi ba shi bane amma bai ce komiba yaci abuncinsa sannan ya fita bashi ya dawoba sai bayan k’arfe tara, tana kwance ad’akinta ta fara bacci dama tunda tazama mother sai taga dama in ya yi magana tace ai saboda baby aslam, koyaji haushi daurewa yake saboda gudun fitina, yau dinma haka tayi bai ce komiba ya koma d’akinsa yayi dialling number Khairi suka gaisa ya mata ya mai jiki don yasan case din Adam yayi 20 minutes yana mata nasiha, dabansan kalartaba na daiga daga can tayi sanyi har kwalla ta share kana sukai sallama tare da mashi godiya, sai ya kira sahibar tasa suka tsunduma soyayya in kaga yanda Ahmad yake soyewa sai ka rantse saurayine gani har 11 ta gota yace ” Baby bari na kyaleki Kiyi bacci, badan nagaji da jin sweet voice dinkiba” cikin shagwaba tace ” Nima ban gaji da jin sweet talks d’inkaba, amma banaso gobe ka kasa fita aiki on time good night take care” shima haka yace mata sannan yace ” Karki manta da Addu’a kinji Babyna Take care” daga can ta bashi Muahhhhh, take Ahmad ya lumshe ido bayan ya ajiye wayar ya shiga tunanin ta Allah ya kai damo ga harawa. Sai kuma ya saki dariya ya ruk’unk’ume pillow ya shiga tunanin Fatiman tashi..
Da safe da nishad’i ya tashi ya shirya ya nufi school inda suka had’u da Umar bayan sallar a zahar suka nufi gidanshi da yake yi awajan manpower k’ato, don ganin yanayin ginin nashi luckly ma’aikatan sunji an sakar masu kudi ba k’aramin sauri sukeba, gidan yana da girma sosai wajan 3 parts ne da garden, dama yayi part d’aya tuni shirin aure yasa ya k’ara kaimi don har anzo ana sa interlocks na compound, kashewa sukai da Umar bayan sunje wajan Hut da aka gama had’ata ansa dan lilo mai shillawa gefen kuwa different flowers ne da sukai girma masu kyau, harda metal table mai four chairs a wajan Umar ya kalleshi yace ” wato nan wajan tea d’in masoyane kenan” Ahmad yace ” K’warai kasan ni im very romantic gashi itama diyar taka haka take so ba koyaushe zaka ke zuwan min gidaba yanzu” Umar dariya yayi yace ” Allah ko? Sai na debo kaya na tare naga ta duniyancin” da wasa da dariya suka dawo, Jamila tasan kwana biyu ya dagema gini amma duk ranta bai kawo komiba saboda dama tasan kwanaki yanayi daga bayane ya watsar, batasan duk wofantar dashi da take shiyasa yake k’ara samun damar soyewa ba, in Fatima ta samu damar kafa soyayyar ta akansa, infact ko Jamila da suke gida daya baijin addiction da ita kaman Fatima, koya aiki yamasa yawa ya yini baijitaba sai yaji ya takura har kaguwa yake ya kirata, ga shi daga yanyin kalmanta za’ayi show da ita what hes dreaming kenan, yanason harkan wise da soyewa, itakuwa Jamila ba wannan ne gabantaba don har karatu yaso ta dora so that ta goge cikin mutane tace bataso, don mingling cikin mutane kana samun exposure da many experiance, to tana can tana aikin raino miji yana shan pamparing da spoiling daga budurwa, don Fatima irin duniyayun nan ne na Addini bana iskanciba, tarairaya da nuna mashi ya isa da take yasa koya suna magana yaga ranta ya b’aci zakaga ya shiga lallab’ata nan ne take fanshewa ta shiga shawgaaba da bori cikin aji ba fitsara ba, in yana biye mata wata sa’in har mamakin kansa yake.. Wannan kenan
Mama tana zaune tayi nisa cikin tunani, tausayin Adam ya isheta Ummi ta sameta awannan yanayi tashiga mata nasiha, share kwalla tayi tace ” Wannan zamani da rud’u yake” tace “Mugodewa Allah da aka gane da wuri da saita kwasa masa ciwo” sai da tajima tana kwantar mata da hankali, bawannan ne karo na farko da ta tararta ahakan ba ko Khairi taje ta sameta a irin wannan yanayin, shi kansa Alhaji Abdullahi yakan shiga damuwa saboda Adam, duk sun sauko sun huce, itama Khairi takan gaisheshi in sun had’u duk da basa tsayawa wata magana.
Zumah ya warke sai sauran karayar an maidashi gida tare da masa d’orin hannu, inda yasha fad’a daga Innarsa don taji zancen komi, Abida taga takardarta kuma taje ta kwashe furnitures dinta, tana nan tana fama da yoyon ruwan infection har yanzu bata warkeba, ga habaicin kawaye da yan unguwa, sau tari takan zauna tayi kuka don wasu sune yan zuwa gidanta suyi kwalama amma sune yan yada labarinta da zaginta.
Abban Khairi ganin yanayin abokinsa da yanayin damuwar da Family suka shiga yasa dakansa yayi fixing date na d’aura auren nasu batare da sanin kowaba sai Ummi da Muhsin, ranar Jumma’a ana saukowa daga masallaci Kawu bala ya wakilci auran aka maida auran Khairi da Adam.
Ayi hak’uri Team Ahmad, don Adam ya k’wace matarsa
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
41
Yana masallacin yaji ana fadar suna kamar nasa, yayi zuru yanaji kaman a mafarkine, ganin yanayinsa Hafiz da Muhsin ya fad’a masa mintina biyu da suka wuce awaya yace ” Yaya ba ka da bakin godewa Abban Khairi” yana jin haka ya fara Alhamdulillah Alhamdulillah da k’arfi kurum ya juya yayi sujudud shukura sai kuma yaji masallacin ya gagareshi zama ji yake kaman ya tashi ya taka rawa, kawai ya fito ya shiga rabawa mutane kudi da almajirai yana abu kaman ya zautu…
Su Khairi ana can Asibiti don aranar aka kai Safiyya da ita da Ummi suna can da Muhsin, sai bayan k’arfe 3 suka dawo da ita ta haifi santaleliyar ‘yarta, kuma gata cikin k’oshin lafiya ita da d’iyarta, sai da suka shiga gida Mama taji sannan tazo, duk abunda ake buk’ata na jego an tanada sai wanka da aka mata, yarinyar mai kyau bata da maraba da Muhsin shiyasa take d’ibar kama da Ummi, shikuwa Adam dama tun bayan d’aurin aure bai bar unguwarba yanzu kuma yaji labarin haihuwa, duk suka shigo gidan tare da sauran samarin suka mata sannu, baby tana hannun Khairi ta kane-kane sai dai akarb’a awajanta in kagama gani ka maidota wajenta, batasan da d’aurin aureba saboda yanzu hankali ya koma kan haihuwar, shikuma Adam burinsa yaga ya d’an keb’e da ita yajata da magana sai shishshigin magana yake mata, ita abunda yabata mamaki meye yasashi farin ciki haka don tamanta rabon da taga irin yanayin a wajansa, sai washegari da ‘yan k’ofar k’waru sukazo sannan ne su Jidda suka fara tsokanarta a zatonsu tasani, cak ta tsaya tana kallonsu zuciyarta na harbawa take kuma taji wani irin hawaye yana zubo mata da batasan kalarsaba don bazatace bakin ciki bane kuma ba farin ciki ba, ganin haka yasa sukasan ta bayan gida aka biyo mata, aikuwa suka cigaba da tsokanarta da kafa Adam, b’at ta b’acewa ganinsu kuwa don guduwa tayi daga unguwar ta tafi gidan Khadija, tana zuwa bayan sun gaisa ta irga mata komi, shewa Khadija tayi tace ” Allah ya k’arawa annabi daraja, da sai a kyaleki kidinga yanda kikeso?” jan tsaki tayi tace ” Haba nafara sauraran Alhaji Jamilufa, sai yayi tunanin kamar nasan da komen na tsaya bata masa time” kwantar mata da hankali Khadija tayi tace ” Ai zaiji labarinki wurin Maryam baki da matsala, kedai kawai ki hak’ura kuyi welcome back da mijinki” ganin Khadija ba abunda zata mata ta shareta ta kama waya da Ahmad shid’inma supporting abun yayi, kashe wayar tayi ta rabu dashi, sai dare ta dawo gida kafin nan duk su Jidda sun watse kowacce ta tafi gidanta, sai da ta shiga ta d’auki baby sannan kuma ta shirya shiga wanka, maman baby ana matse baccin gajiya, bayan ta fito daga wanka ta shirya ta shiga chat ko zai rage mata haushin bazata da aka mata, kodan tasan k’ila kowa na gidan yasani sun zuba mata idone tana cikin haka kiran Adam ya shigo, jan tsaki tayi ta saka wayar a silence don batasan maganganun da zata masaba, a bangaren Adam yayi tunanin by now ta sakko tunda satin daya wuce suna gaisawa yanaso yaji sanda ta shirya tarewa don ya d’anyi kwaskwarima a gidan nasa, ganin tak’i picking yaji gwuiwarshi tayi sanyi zumud’insa kuma ya koma ciki, baiyi zuciyaba ya mata sending message na goodnyt, tana ganin message d’in tace ” Iska na wahalar da mai kayan kara” lokacinne Safiyya ta farka tace ” Kedawa kike magana haka” tace ” kya sani wai dake za’a had’u a munafunce ni ko?” tuni Safiyya tagano inda maganar ta nufa sai dariya ce taso kwace mata amma ta dake tace ” Aiya yar uwa haba dai kin manta wace ni, don a farko banbi bayansa ba balle yanzu, yanda kika tsinci maganar nan haka na tsinceta fatan mudai Allah ya baku zaman lafiya ya kiyaye gaba” hmmn Khairi ta ja k’wafa saboda ta lura Safiyya taji dad’in abun, bata ce mata komiba sai wata yar harara da ta mata dariyar da ta danne ce ta fito tace ” Nidai ban kashe zomon ba kuma zomon masoya ma bana karb’ar ratayarsa” jan tsaki Khairi tayi tare da cilla mata ledar biscuit da ta cinye tace ” Kyaji dashi”+
STORY CONTINUES BELOW
DUTSE
Ahmad duk iyakar k’ok’arin da zaiyi na toshe kafa don kada Jamila tasani yayi, hakan ne yasa yake takatsantsan nayin wayarsa, bakuma ya fasa had’a lefensa ba hatta kayan fad’ar kishiya sun tsarashi shida Hujra, kuma har ya ajiye yan kud’ad’e da zai bata na gyaran funitures saboda tarewa a sabon gidansa.
Yanzu k’arfe bakwai da minti hamsin dawowarshi kenan daga sallar Isha’i, uwargida Jamila takawo masa abinci ya tasa a gabansa zai fara ci ya tuna d’azu suna magana da Fatiman sa yayi cutting call d’in saboda wata magana da Kabir yake masa, take ya ajiye spoon d’insa tare da dialling number ta lokaci d’aya kuma ya mik’e don fita zuwa parking lot, yayi sa’a tana kusa da wayar duk da dai saida ta kusa tsinkewa ta d’aga, cikin yauk’i da kwarewa a salon sarrafa voice take gaisheshi ” Baby yau jan ajin ya motsa kenan ko?” cikin salonta na shagwaba tace ” Laaa ni kuma a suwa kawai dai ka kira ina cikin yin azkhar ne” ya yarda da hakan amma yakanso salonta yace ” kedai ki fad’amin gaskiya irin efizy d’in nan ne naku na mata akeso amin” yar dariya tayi wadda duk sanda tayi sai yayi imagining gatacan ta tufe fuskarta na salon kunya, don hakan takeyi indai yaje zance, shiri-ricewa yayi suka cigaba da hirarsu, ita kuma Jamila taga ta kawo masa furar da ta dama masa bayanan, sai tayi tunanin ko ya shiga toilet ne shiru-shiru yak’i dawowa, tashi tayi ta shiga d’akinsa bai nan gashi toilet d’inma babu shi, take tashiga tunanin wane abu zaisashi fita haka da gaggawa yabar abincinshi cikin plate wanda gashi ya jiya gabansa da alama ko loma d’aya baiyiba, fitowa tayi ta hangeshi jikin motarsa ya jingina yana ta murmushi, wani irin fad’uwar gaba taji , take ta shiga takowa zuwa gareshi, wata dariya yayi mai d’an sauti yace ” Haka kika ce ko hmmn zaki shigo hannu sai kin fara pleading zan tuna maki irin cika bakin da kikayi” cak yayi yana kallonta ta k’ureshi da ido tana muzurai, don ta mashi bazata sai da ya tattaro dauriyarsa ya saita yanayinsa ta yanda bazata gane kad’uwar da yayi ba ta kalleshi ta jefa masa tambaya ” Waini nakasa gane kanka kwanakin nan kana yawan fitowa waya bakin gate, ko meye dalilin hakan?” Dariya yayi yace ” Kai Sweety kina dabawa kai tunani, duka sau nawa kika ga nayi hakan i think usually it happens in ace shigowata gida kenan aka kira na tsaya nayi kafin na shiga falo ko? Yaune kawai ai” kallon karka raina min wayo ta bishi dashi tace ” Allah ko? To amma meye yau na barin abinci bud’e kaman ka tafi ceton yan gobara, bayan hakama wace hakan kake ce mata zata shigo hannu har kana washe baki” tuni yaji dabara ta fad’o masa ya ce ” Yanzu dai da kika ga na fito wata maganace ta dangi da banso kiji, kuma kina nufin zaki fara samin idone nida yar uwata da Hujra nefa muke wasa, haba karki sakemin irin wannan!” ya tsiri yan fad’a kan zata fara shiga tsakanin sa da yan uwansa, cikin ransa yake jan istigfari, take ta shiga bashi hak’uri don sosai Ahmad ya fik’ik’ice mata, can b’angaren da Babyn tashi taji ya kashe tasan k’ila yayarta ce tazo take taji kishi ya taso mata sai kuma wata zuciyar tace mata ” Ke kuwa keda zaki sameta kin shigar mata gida ai kishi ba naki bane” matse pillow tayi inda best friend d’in ta da ta k’ura mata ido da sigar tsokana tace ” Ikon Allah gaskiya Malamin nan yana wuta kinga yanda idonki ke juyewa” murmushi tayi tace ” Baki rabo da sherri, bari kiga na fara editing chapter d’in nan don naga wasu har cover sunyi” ta tashi ta janyo system d’inta ta shiga folder ta project d’inta…
Haka Ahmad ya cigaba da zageyensa duk randa yake wata wayar tajishi sai ya samu dabarar samfewa, har lokacin bikin nasu ya cigaba da k’aratowa, yau yana zaune cikin site d’in nasa yana ganin ana paint na gidan inda d’ayan part d’in masu saka wall wallpaper ke sakawa, wayarshi ce tayi k’ara ya d’aga ” Umar dama kai nake nema don naga wancan bq d’in nawa inaso nasa mashi wasu kayan irin na shagon yaya Mukhtar” bansan amsar da yabashi yace ” To saika k’araso dai”
Adam ya daure yaje gidan nasa domin tunda akai abun sai Muhsin ne ya d’ebo masa kayan sawa kin zuwa yayi, amma ganin yanzu zasu koma da Khairi yaji wasai duk da dai yana shiga falon gidan abun ya dinga dawo masa akansa, sosai yaji b’acin rai ya shiga d’akinsa inda ya k’i dubam kan gadon yana bud’e drawer yaga ba kud’i, yasan bai wuce aikin Abida ba, amma yaga rashin kunyarta don ko jiya sai da ta k’irashi magiya akan kuskurenta ya maidata tunda saki d’ayane, blacklist yasata tare da blocking d’inta a watsapp, abunda yaga zai iya buk’ata ya d’auko inda complete kayan d’akin nasa ya shirya bayarsu shi bedsheet d’in parking lot ya kawoshi ya banka masa wuta, yana gidan engineer d’in da yakeson yayi taking care na renovating gidan yazo suka d’an duduba suka ce gobe zasu fara aikin, sannan ya fita tare dasu sukayi bank don basu wasu kud’aden..
Bangaren Abida da Zuma babu kyau, don dukansu sun fita hayyacinsu shikam Zuma k’afa ta mik’e bayan kwana biyu da mik’ewarta ya fito bakin layi zai tsallaka kwata ya samu gocewa, haka aka k’ara yayimarsa gun d’ori, tunda aka dawo dashi daga d’orin nan ya samu damar k’iran Abida yana tsine mata kan ita taja masa, inda itama take tsine masa tana ganin shine ya watsata har ya janyo mata kisan aure tana cikin daula yasa ta dawo gidan jiya, ga b’akin cikin yanda mahifinta har hawaye yayi kanta yace kuma bashi ba ita, har yanzu dak’yar yake amsa gaisuwarta, ga jarabar infection d’an kud’in da ta sato ta k’ararshi anan don ma wata sa’in in suka had’e da Khairi a asibiti takan biya mata na drugs, ta buga da Adam baya bata dama don yanzu bata iya samun number dinsa, ita kanta Inno ta fara kyararta don har wari-wari take, abun kamar na aljanu don duk yawacin maganin da mutane kance ya musu aiki in tayi da zarar ya fara tafiya sai ya dawo, shima Zuman hakan take awajansa yana fama da kaikayi da sab’ewarta da rad’ad’i, dukansu sunyi nadama suna kaicon rayuwarsu, yanzu haka tana nan yan kayan ta masu tsada take saidawa a sayesu a wulak’ance ta samu na rufawa kai asiri.
Khairi tabawa Maryam labarin komi inda ta nuna mata bakomi, aka bawa Alhaji Jamilu hak’uri, dake mutum ne mai fahimta bai nuna komiba yace ” Allah ya basu zaman lafiya” Cikin Sauri take had’a kayanta zata fita daga office ta riga ta nemi permission, kuma sun bata dan gobene sunan Safiyya, tana da niyyar shigowa kasuwa don k’arasa sayo wasu abubuwa, tana gamawa da kasuwa tayi gida Humaira ta dawo hutu a wata yarinya Mami yar k’anwar Mama da tazo mata hutu, yarinyar batafi tsarar Humaira ba don haka suka shiga yin snacks, sai bayan magriba ta samu ta d’an kishingida tana hutawa, tana kuma tunanin makamarta da Adam har batason kwanakin da Mama tace abarta su cika don zai gama shan maganin infection sannan Mama tace za’a mata gyara don har an fara bata wasu abubuwan, kuma an canzo mata wasu funitures din, shiri su Maman suke mata ba kad’an ba har kunya taji na yanda bata musu karaba ta nuna tana k’in Adam d’in, k’arfe bakwai da rabi ana fitowa daga sallar Isha’i sai ga k’iran mijin Khadija ya shaida mata Khadijan ta sauk’a cikin mamaki tace ” Tun yaushe kenan” yace ” Tun la’asar dai sukaje asibiti sai yanzune ta haihu amma duka suna lafiya ita da babyn nata namiji” ba shiri tace sai ta tafi tayo tsokana Ummi tace ” Amma dai adaren nan bakya fita napep ba sai dai ki nemi wani cikin yayyanki” suna maganar sai ga d’an ana cen nata yazo aikuwa Ummi tace ” Ga yayanki Adam nan sai ya kaiki” haka tana zumb’ure-zumbure ta bishi, duk shishiginsa ahanya bata bashi amsar da ya wuce unmm da A’a, haka ya daure, sai da tagama cin lokacinta ta fito sannan ya tashi ya bud’e mata k’ofa ta shiga sannan ya rufe, ta gaji matuk’a dama don yau bata zauna sosai ba, basufi minti biyu da tahowaba bacci ya kwasheta kafin su isa gida, har yayi parking cikin gidansu bata saniba, shikuma baison tashinta don haka kawai gyara mata kujera yayi ya kwantar da tasa shima ya k’urawa fuskarta ido tare da mik’a hannunsa ya kamo nata ya rik’e, can kuma yasa d’aya hannun nasa ya shafi lips d’inta wanda sauran lip gloss ke kai ji yake kaman ya kama lips din nata, yayi missing d’insu ba kad’an ba, bacci yayiwa Khairi dad’i don sunyi minti goma ahakan can yaga tayi luu zata bugi wajan A. C ya tallafo goshinta tare da k’ok’arin gyara mata zaman, take ta bud’e idonta inda ya sauka akan k’irjinta da ya rik’o wani irin zabura tayi ta hankad’eshi tace ” Gaskiya bansan shishshigi fa” tafad’a tare da bangajeshi ta bud’e k’ofar asukwane ta shige cikin gida, sororo yayi don baida k’warin motsi gaba d’aya jikinsa ya mutu saboda yanda ta d’aga masa hankali..
Tunda taji mummunan labari mn k’ara Aure da Ahmad zaiyi tayi faduwar yan bori, tafi minti biyar bata kwakwaran motsi kaman statue, hawayene ke zuba a idonta tana zaune daram ak’asa kamar zaman ‘yan bori ” Ni za’aci amana? Wallahi ba’a sayi zaman lafiya ba Allah ya tsinewa zuriyar Muhd Jahun Albarka” ta dafe k’irjinta dake mata suya, Samira tace “Yanzu dai daurewa zakiyi ki nutsu kije kiji asalin zancen, don musan yanda zamu b’ullowa lamarin” cikin muryar kuka da haki tace ” Kamani na mik’e, za’ayi kwalabar uba kuwa wallahi sai na nuna musu kalar haukana”
K’arshen alewa k’asa taji yau, ko waye ya fad’a mata?
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
42
Hawaye ne ke malalala kawai a idonta tana sumbatu, mai Napep da ya d’auketa sai da ya tanka mata yace ” Haba baiwar Allah komi yayi zafi maganinsa Allah, ki fawwalawa ubangiji lamuranki mana” cike da jin haushi tace ” Dallah malam kamin shiru, bakasan me akamin ba zaka nemi cikani da surutu” jin haka yace ” Allah ya baki hak’uri” a haka suka isa gida ta zaro d’ari biyu ta mik’a masa ta shige gidan a sukwane, dama tasan Ahmad yana nan kasancewar ranar Asabar ne, sai dai tana shiga ta tarar baya cikin falo yana cikin bedroom d’insa gefe guda ga akwatina nan guda biyar na fad’ar kishiya masu kyau, tun d’azu Anty Hujra ta kawosu inda kuma aka ce ya sanar mata don gudun kar taji a wani wurin ranta zaifi b’aci, sai dai kash an rigashi, banko k’ofar d’akin tai daga yanayin ta ya gano abunda ya faru, binshi take da kallon tsana cikin dusashen muryar kuka tace ” Yayi kyau Ahmad Jahun, anci moriyar ganga shine za’a yada koranta ko? To wallahi ba kaiba duk zuriyar kuma sunyi kad’an a tozartani naga shegen da zai d’aura maka auren” kallonta yake gaba d’aya ya dubulbule shi tashin hankaline baya so shiyasa ya gagara fad’a mata tuntuni, amma ganin ba fashi sai yayi kuma yazama dole ya tsaya kyam kodon wadda zai kawo yakamata ya zama isashen namiji avgidansa yace ” Jamila ki samu wuri mu zauna nayi miki bayani, sannan inaso ki bani aron hankalinki da nutsuwarki don kema ki rage rad’ad’in dake ranki” jan tsaki tayi tace ” Hankali! Nutsuwa! Ai dukansu ba’a so su samuba cikin gidan nan, kace zaka had’a soyayya ta da wata kace nutsuwa Ahmad Wallahi sainaci abu takazar uban duk mahalukin daya had’a abun nan, kai bari kaji nadad’e da sanin kana munafintata shine yanzu barikin ta isheku kaida ita shine zaka kawota cikin gidana to Wallahi ba’a isa ba” murmushi yayi ya zaci fiye da hakama shiyasa ko d’ar baijiba yace ” Aure dai sai dai kiyi hak’uri don babu fashi matsawar ina da rai, ga kuma kayan fad’ar kishiya nan ki duba in akwai buk’atar gyarawa, ga kud’i kiyi wasu hidindumin da d’inki” ya ajiye bandir na yan dubu guda biyu 200k, wajan akwatinan tayi tayi wurgi da d’an kit d’in tace ” Wallahi baka isaba har da wani kayan fad’ar kishiya, Ahmad Allah wadaran auranka Allah wadaran saninka da nayi arayuwata” tana fad’a tana wancakali da akwatinan shikuwa kud’in yana kan gado, Ahmad yayi folding hannunsa tare da jingina jikin closet yana kallonta, sai k’ok’arin lalata boxes d’in take sunki daga baya ta bud’e guda d’aya ta shiga fito da kayan tana watsasu tana waresu, murmushi kawai yake yace ” Jamila nasan kowacce mace najin zafin idan za’a mata abokiyar zama, amma inaso kibi abun asannu bani da niyyar wulk’antaki bakuma don nadaina sonki bane zan k’ara auren, inason k’arin sunna cikin gidana sannan inason nazama cikake kaman kowa, nasha maki magana akan kurakuranki na zamantakewarmu sai kikai watsi dasu burinki kawai ke kiyi abunda ya dameki, kinsha nuna min baki damu da buk’atunaba akanki saura kiris na aikata alfasha, duk na jure Jamila nifa ba dutse bane dazan ke ci kuma nazo buk’ata da dare ki watsamin k’asa a ido kuma nazauna ina cutuwa, kinga tunda Allah ya horemin inada arziki dole naje nakawo abunda zaike d’aukemin lalurata, ko ba komai kinga kema kya huta da jarabata ko? Koba haka kike cewa ba?” kukan kura tayi ta yi kansa , da hannu d’aya ya ruk’eta tana kai masa yakushi, tana fad’in ” Wallahi bazan iya had’a jikinka dana wataba, kasake ka ce zaka had’a jikinka da na wata sai dai ayi biyu babu wallahi, kamai dani rijiya kasa guga acan ka dawo ka saka ajikina wallahi bazai yiwuba” sai mutsu-mutsu take anan Allah ya bata sa’a ta gantsara masa uban cizo wanda sai da yayi k’ara ya saketa yana yarfe hannunsa har jini sai da ya tsatstsafo awajan, ga shatin hak’oranta nan ya fito b’aro-b’aro, ta nufi kan gado ta janyo wayarsa ” Wallahi sai naga wata shegiyar ce wannan har gidan iyayenta zanje na mata warning shigowarta gidana tamkar saka rayuwarta cikin uk’ubane” Ahmad kam yana can yana fama da hannu ya ciju matuk’a, sauri yayi ya nufi kitchen ya d’auko ice block yana d’orawa akan wajan amma ba sauk’i, ita kuma Jamila tayi ta gwada password wayar tak’i bud’uwa don ya canza wanda ta sani abaya, kwantawa tayi ak’asa tana malangari tana zunduma ihu kamar ance babanta ya mutu…+
STORY CONTINUES BELOW
Bayan Sallar magriba har yaje chemist an wanke wurin, dake mai chemist d’in abokinsane yasan zancen k’ara auren, ya shiga tsokanar sa ” Oga kaje ka nemi maganin k’arfe don yanzu wasan ya fara, badai yau tajiba” dariya yayi yace ” aikuwa na shiryawa komi, ba gudu ba ja da baya” daga nan gidansu ya wuce ya taho da Hujra da Yaya dan azo a d’an taushi Jamila..
Suna shigowa falon suka sameta ajingine ajikin bango ta gefen k’ofa da tab’arya na turmin k’arfe jira take ya shigo ta rabza masa a kai, sallamar mata taji had’e da tasa har ta d’aga ta tsaya tana k’urawa Hujra kallo wadda itama kallon mamaki take mata, amsa sallamar tayi a dak’ile ta matsa suka shigo binta da kallo Yaya tayi tare da jijjiga kai, zama Hujra sukayi gaba d’ayansu akan kujera inda ita kuma ta tsaya k’ik’am asaitinsa tana kuma jifan Hujra da kallon haushi, ita kuma Hujra tana kallonta da sigar ” Kin ban tausayi don kuwa ba fashi, ai an daina kishin hauka yanzu” Yaya ce tayi gyaran murya ta shiga yiwa Jamila nasiha akan duk wannan tada zaune tsaye da shirim dukan miji bazai hana aureba, don maza halinsu gudane matuk’ar sukace zasu k’ara aure to duk wani hauka da zakiyi bazai hanasuba, garama ki samawa kanji lafiya azauna lafiya , kija girmaki inda idan yagama rawar kan amarya sai kiga ya dawo wajanki, har kina mamaki sai kiga sabon mutumtaki zaike da kuma ganin darajarki” itadai hmm kawai take don ba daukar nasihar take ba, gani take duk sune munafukan da suka had’a komi, can Hujra ta amsa tace ” Sister an daina yayin wannan kishin, don akan d’a namiji bazakaje ka janyo wa kanka fushin Allah ba yazamanto ga mari ga tsinka jaka don zaki jimasa ciwo abaki haki, sannan kuma shi ba fasa auren yayiba kinga kinyi tantal badam’alu, ai an waye wayake haka ai nice ke nunawa zanyi bansan yanayiba, kishi halittace dole zakaji don bawanda yakesonta amma in tazo haka zaki hak’ura hannu bibiyu ki karba in kika ja girmanki wallahi dagashi har ita sai sunzo suna jin kunyarki, balle nayi bincike kan Salima yarinyace wadda bata da hayaniya kuma kin girmemata, ina fata zaki kama girmanki ta yanda raini ma bazai samu damar shiga tsakanin kuba” wata harara ta watsa mata tace ” To azagwaiwai uwar zuba tsari, naji munafuka ai nasan labarin komi kece kika shiga kika fita akai komi dake saboda tun farko daman bakya k’aunata da Ahmad, insha Allahu yanda kikai silar k’ara auransa wallahi sai mijinki ya kawo mata uku gaban ki” gaba d’aya kallonta suke da mamaki Ahmad zai shiga mata fad’a Yaya ta dakatarshi ta kallu Hujra tace ” Kiyi hak’uri ina fatan kinsan zafin kishine yake damunta, ita yanzu abar alallab’ace, ki tashi mutafi” Ahmad harara ya shiga watsawa Jamila ita kuwa ta cigaba da jifan Hujra da zuriyarsu da mugayen kalamai wanda banda Hujra takai zuciya nesa wallahi da sai ta mareta, don gani take a banza k’anwarta ta nawa tana gaya mata maganganun banza, haka ya rakasu bakin gate inda Yaya ta k’ara nanata masa sai ya k’ara hakuri ya jure, kuma kada yayi kokarin saki ko dukanta duk haukar da zata masa, suka fita suna tu’ajjabin abun Jamila, dama can jininsu bai had’u dana Hujra ba saboda tasha zuwa tana ganin rashin kulawa irin nata, shiyasa yanzu take k’aimi wajan ganin ya samu farin cikinsa, bayama da ta binciko halayyar Fatima (Saleema) da dabi’unta har a hostel sai da ta dubo, kuma da ita akaje Adamawa kaiwa kayan al’ada da lefe, ta yaba da tsarin gidan nasu..
Cikin dare Jamila tana zaune sai kad’a k’afa take duk tayi haje-haje saboda kuka da tashin hankali, ajima sai ta d’ebo munanan kalamai ta watsa masa ko uffan baya cemata, tayi tagaji ana haka wayarshi ta hau ringing Saleema na kiransa lokacin ya shiga toilet d’auro alwala, cikin hanzari ta d’auki wayar ga k’aramin contact pic yayi appearing inda ta gane fuskar yarinyar batasan sanda tace ” Jar uban can, dama nasan za’ayi hakan ashe wannan matsiyaciyar dagaske soyayya suke, hasashena gaskiyane ” dagawa tayi sallama Saleema tayi inda Jamila ta bata amsa da wata iriyar ashar tace ” Buri ya cika ko? Na samu kan mijina shine tsabar tambad’ewa da salon karuwanci kika kirashi alhalin yana cikin gida, to anyi walk’iya naganki, kin dade kina bibiyarsa shine kika je kika masa asiri har kina shirin shigowa gidana to wallahi ina baki shawara tun wuri ki janye kudurinki akansa, in ba hakaba Wallahi zuriyarki kaf sai na hanasu jin dadin duniya sai nasa rayuwa tamiki muni.. Fuzge wayar taji anyi, ya kanga wayar akunnensa yace ” Baby kiyi hak’uri i hope bata batamin rankiba” wani irin b’acin raine ya tasowa Jamila ta shiga rawar jiki tana nuna k’irjinta tana ” Ahmad ni kakewa haka agabana! Agabana! Wallahi sai kayi nadamar hakan” da gudu tayi kitchen ta d’auko tab’aryarta, kafin ta dawo awaya Saleema da tagama jin hayaniyar Jamila tace ” Banji dad’in abunda kamataba, kasan cin fuska bakyau, laifina ne dana kiraka yanzu, yanzu ka rarrasheta mayi magana gobe” bata jira amsar shiba ta kashe wayar, shi gaskiya baiji dad’iba ai miss call yamata ta biyo bai shirya daina jin muryarta ba, yana wannan tunanin sai ga Jamila da tab’arya ta kawo masa duka ak’irji don tsayinta baiyi nasa ba gashi ya d’aga kai sama yanayin tunani, aikuwa tuni ya murd’e hannunta ya wullata kan gado kafin ta mik’e yayi sauri ya bar d’akin ya rufoshi ta waje tare da saka key, sai ihu take ta ciki tana ” Eh gara ka kulleni ai kaje kacigaba da cin amanata, dama kun dade kunayi kaida ita ka saba lalatarka da ita, Allah ya isa wallahi sai Allah yasakamin amanata da akaci” anan falo ya kwanta ita kuma ta cigaba da bugun k’ofa tana yi tana zage-zage ta zageshi ta zagi Saleema har tagaji sai wajan Uku dukansu bacci ya d’ebesu..
A b’angaren Saleema kuwa taji ba d’ad’i, tanason Ahmad don bazata iya rabuwa dashiba amma at times takanji kamar bazata iya da masifar Jamila ba.
Mafarin Soyayyar Ahmad da Saleema ya samo asaline daga sanda yace yanason k’ara aure, inda yacewa Umar yarinyar da ke kawo masa abinci in bata da tsayayye yanasonta, cikin jin dadi Umar yace ” Gaskiya naji dad’i kuma ina mai tabbatar ma Saleema irin matan da kowanne namiji ke buk’tace, ko cikin nieces d’ina da cousins d’ina na school d’in nan nafi ware mata, saboda batada rawar kai da zak’ewa ko Madina (Matarsa) bata damuwa da alakarmu” kafin zuwan Ahmad Umar ya k’irata yamata bayani, inda afarko tace gaskiya bazata iyaba saboda abubuwan da suka shiga tsakanin ta da matarsa, sai asannan ne Umar yasan ita akaiwa don shi Ahmad baisan alak’arsa da Saleeman ba, bayan wasu time tayi shawara da Nucy da gidansu akace ta amsa batasan mai Allah yake nufiba, balle kuma shi Ahmad din yakai namijin aure don kowa yamasa shedar halin kirki, daga haka Ahmad yafara soyayya da ita basu d’au time ba suka tsunduma son juna, lokacin da ya had’u da Khairi yabata labarinsa haka itama shi yacigaba da k’arfafa mata gwuiwa akan Adam shiyasa, randa yakaita gida yad’inga abunda zai tunzura Adam don yayi proving mata how much Adam loves her, kafin kace me Ahmad yaje yola time din tayi hutu, Ahmad ya had’a Khairi da Saleema k’awance cikin ikon Allah jininsu ya had’u sosai, yanzu haka jira ake tak’are final exam d’inta da one month sai asha shagalin Biki, sukuwa Students da sukaji labarin sai murna suke mata wasu kuma hassada, su Tsumagiya sukace ai bikin dole arak’ashe dasu, kafin kace me labari ya watsu a school ahaka Samira taji zancen wajan wata yarinya yar unguwarsu dake karatu a F. U. D.
Da safe daya bud’e d’akin tana yashe ak’asan floor tana bacci da kanta daya baje dama atsefe yake, tashinta yayi don tayi sallah yayi hanzarin fita zuwa masallaci, bayan ya dawo ya shige d’akin ya rufe tana d’ayan bedroom d’in wanda yake matsayin nata, kaman jira ake ya kwanta zazzabi ya rufeshi saboda cizon Jamila, ita kuwa Jamila daga hakan shiri tayi tayi ficewarta zuwa gidansu.
Adam yana nan yana shan magani akan ka’ida kuma bai fasa cusa kai ga Khairi ba, itama Khairin sai tsuma ta ake bayama yanzu da ya rage saura sati takoma gidan nata, awajan aiki tayi requesting leave na komawa karatu yana kan process inda H.O. D yace insha Allah zai tsaya mata don ta tafi, Adam dakansa yaje B.U.K yayi magana da wani friend dinsa akan samun Admission nata, don yasan hakan zai faranta mata rai…
Anyi sunan Khadija lafiya lou kuma sun sha shagali, da dare Adam ne yaje ya d’aukota, agabansa ta tsaya suka gaisa da abokan mijin Khadija sannan ta shigo motar, yaji kishi amma ina bazai iya mata haukaba, gashi mayafin dake jikinta ya bashi haushi don shape dinta bai boyuba, haka ta zauna tana basarwa tana yauk’i, jira take taji yayi fad’an shigarta taji shiru, dama tana sane tayi hakan don taga gudun ruwansa.
Ahmad da zazzab’i ya yini sai bayan sallar la’asar yajishi wasai, sannan ne yaji tunwa ta takura masa ya fito yaga gidan kaman yanda yake jiya, take gabansa ya fad’i kardai yaji Jamila tayi? Ya tambayi kansa, amma bari dai ya duba d’akinta shiga yayi ya duba yaga ko’ina na gidan alamun bata nan, komawa yayi d’aki ya shiga k’iranta tak’i dagawa, take ransa ya b’aci shiryawa yayi ya nufi gidansu inda a hanya ya sai yoghurt yasha roba d’aya saboda yunwar da yake ji, bayan yaje gidan nasu yayi sallama yayi dace mahaifinta yana cikin sitroom d’insa nan ya shiga suka gaisa, inda yayi wa Ahmad nasiha tare da nuna masa sai hak’uri lamarin mata, kuma kada ya bari koda wasa hargagi ko fitinarta yasa yaji shakkar komi, zata daina nan gaba, har kunyar sa yaji don mahaifinta nada dattako bai taba bin bayanta in wani abu ya taso, yana zaune afalon ya k’ira mahaifiyarta awaya yace su shigo da ita, ya mata fad’a bakad’anba sannan yacewa Ahmad in tamasa wani haukan ya sanar masa dakansa zaizo har gida ya hukunta ta, dama kafin nan suma su Anty sun mata nasiha, don haka daga nan dauko jakarta tayi suka taho gidansu.. Zamuji ko ta huce
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
43
Ranar da su Jamila suka koma sauk’i daya Ahmad ya samu shine batai k’ok’arin yin komiba, illa bak’ak’en maganganu wanda agunsa bai daukesu komiba, hatta baby Aslam yasan gidansu ba sauk’i don nono gagarar bashi tayi sai cikin dare da taga yana kuka yana neman shid’e mata, acikin daren ta lalubi number Samira ta gaya mata tasan wace ce wane mataki take ganin zasu d’auka? Alokacin mijinta ya farka ya daka matsa tsawa yace ta kashe ba shiri ta kashe wayar..+
Jibine tariyar Khairi hakan yasa akaje har gida aka mata sabon jere tamkar na sabuwar amarya, shikansa Adam kwaskwarimar da yayiwa gidan tayi kyau sosai, sai rawar jiki yake. Da misalin k’arfe hud’u na yamma suka hallara gaban iyayen nasu inda suka musu nasiha mai tab’a zuciya, sun nunawa Adam illar fushi da zargi da tsananin kishi, itama sun mata nasiha akan k’ara kiyaye martabar Auranta, dama wasu abubuwan da suka shafi zamantakewa, daga bisani har k’walla sai da Adam ya share don bak’aramin shigarsa abun yayi ba, a ransa yake ayyanawa ba abunda zaisa ya maimaita kuskurensa na baya don shikad’ai yasan wahalar da yasha, ana gama musu ya durk’usa yayiwa su Abban Khairi godiya da Ummi, ita Khairi sai share hawaye take dabatasan na mene ne ba, suna tashi daga wurin dama magriba tayi shiga tayi toilet ta d’auro alwala bayan ta idar da sallah Ummi ta aiko Humaira k’iranta, bata wani b’ata lokaciba ta nufi d’akinta, sabon darasi ta d’ora mata had’e da jan kunne, anan ne tace mata tabata mamaki da sun zuba mata ido haka zata cigaba da nuna k’inta ga Adam ko kara bazata iyayiwa Hajiya Hassu ba, sunkuyar da kanta tayi cikin kunya don wallahi shaf kanta ya kulle, sosai ta mata nasiha da k’arin dabarun gidan miji, sai da jikinta yayi sanyi sai kace lokacin ne take amarya, da dare Adam ya k’irata a waya ta d’aga yad’inga janta da hira tana Un da un’um, batason ta sake masa da wuri so take taja mutumcinta kosan gaba duk da tasan ya wani kuma tana da hope akan ya shiryu, yanda tad’inga gwada hak’urinsa akwanakin taga yana iya daurewa koda yaganta da wasu. Dama an jima ana mata gyaran jiki don haka tsaf take hatta skin d’inta shek’i take, koda sukai waya da Umaima ce mata tayi nanda Sati zata zo musu hutu tace sai Allah ya kawota..1
Jamila tunda akai abun nan ta bud’en shika-shikan rashin mutumci , bata shara sai ta ga dama girki kuwa daidai cikinta take haka zaiji k’amshi ta hanashi, shikuwa a nasa b’angaren bai fasa ajiye mata komiba da duk wani hak’kinta, sau tari in ya zauna afalo ko d’aki yana hutawa kawai ta tsiri k’ure volume d’in tv ta kamo channel d’in wak’a ta k’ure, haka zai yi kaman baya ji don yasan neman magana ne kurum, in yaga ranar bazai iya hak’ura da baccin ba sai ya fice ya bar mata gidan yaje gidan Umar, a bangaren soyayyarsa da Saleema sai muce sai shukra don k’ara mannewa suke da juna, a duk sanda Jamila ta k’ureshi da haukarta daya kira Saleema zaiji kwanciyar hankali
Daga b’angaren gidansu Saleema kasancewarta mace diya tal awajan iyayenta bak’aramin shiri suke mataba, duk wasu kayan gyare-gyare an tanada don yimata, haka kayan d’aki ba’a magana don Alhaji Ibrahim Moddibo yana da kud’i bakad’anba, mahaifiyarta yar maidugurice Yagana an dad’e ana tsumin k’amshi don Saleema don haka jira ake tayi grad ta dawo a mata gyaranta balle da akaji gidan kishiya zata shiga.
Khairi takoma gidanta da rakiyar Anty Asiya da matar Kawu bala, tunda suka tafi ta tashi ta zagaya gidan abunda taga yakamata ta gyara ta gyara shi, shikuwa Adam sai d’ari-d’arin fuskantar gidan yake saboda yaga kaman har yanzu bata sauko ba, su Ak sai zolayarsa suke suna cewa kar ya bada maza, a haka dai ya daure takwas da rabi ya shiga gidansa tare da parking, yana fitowa ya bud’e bayan motar ya fito da ledodin kayan ciye-ciyensa ya dan tattaro dauriya ya shiga falon bakinsa d’auke da sallama, tana can cikin bedroom d’inta fitowarta daga wanka kenan tana sanye da bathrob silver colour, amsawa tayi tare da zira hijab k’ato ta fito falo bata kalleshiba ta amshi kedodin tana furta sannu da zuwa, so yake ya had’a ido da ita amma tak’i bashi dama, takai ledodin kitchen tare da dauko masa ruwa da cup ta kawo masa, tayi shigewarta d’akinta tacigaba da shiryawa sai da tad’au 30 minutes tana shafe-shafe daga kan creams zuwa oil perfumes, tuni tad’au k’amshi koda can gwanar turarece balle yanzu an k’ara shiryo makaman kama miji, ta d’auko wani kayan bacci k’irar jumpsuit saidai su iyakarsu gwuiwa ta maida hijab d’in nata kai ta tada sallar shafa’i da Wutri, a can Adam shima yayi wanka yasa pyjamas cream colour ya nufi d’akin nata, sai ya tarar tana sallah cewa yayi ” In kin idar kisameni a falo please”
STORY CONTINUES BELOW
Bayan wasu minutes ta fito ta sameshi a zaune inda ya umarceta da ta kawo masu abinci suci, batayi musu ba ta nufi kitchen d’in ta bude ledar kaza tasa a unbreakable tare da dorawa kan tray ta d’ora sauran drinks kama da fresh milk da smoothie na Hajaj, ta kawo falon ta ajiye masa agabansa bayan ta zuba masa milk d’in acikin cup, ta koma kan kujera ta hakimce tare da canza channel daga aljazeera zuwa Mbc bollywood, k’ura mata ido yayi yace ” Babyluv ke bazaki ci bane?” jijjiga kai tayi tace “Nak’oshi” ji yayi shima bazai iya ciba lallashinta yacigaba da yi da bata hak’uri akan laifinsa na baya, take taji ta tuno abubuwan da suka faru a baya yana magana tana kallon falon, yaza’ayi ta manta ranar daya koreta da tsohon ciki kawai sai ta fashe da kuka ta tashi da gudu tayi d’akinta ta fad’a kan gado, kuka take mai sauti tuni ya biyo bayanta Allah yaso bata rufe k’ofar ba ya isa bakin gadon yace ” batun yauba nasan har yanzu baki yafeminba, duk da agida kin furta nasan ganin idon iyayenmune” cikin kukan tace ” Nariga na yafe maka, nakasa mantawa ne wannan shine illar furuci ka jingina min zina, don Allah kafita a d’akin nan” ganin haik’am kukan take yasa yace “Shikenan zan fita amma don kidaina kuka har cikin raina nake jinsa , karki sa kanki yai maki ciwo” gyada masa kai kawai tayi sabin hawaye na zubowa a idonta, komawa yayi ya tattara kayan yakai kitchen kwana yayi yana juye-juye, yasan yayi nadama yarasa me zaiyi ta huce da alama ta rik’eshi matuk’a, ita kam Khairi sai da tayi kuka ba na wasa ba cikin ikon Allah tana gama kukan tajita sakayau kaman an ciremata kaya masu nauyi ak’irjin nata, har taji duk wani haushi da cunkushewa sun bar ranta, a haka b’arawon bacci ya d’auketa..
Da Asuba shi ya tadata ta hanyar mata knocking, bayan tayi sallar ta dad’e tana musu Addu’a akan Allah ya basu zaman lafiya ya rage masa fitinar dake k’irjinsa, shikam sai bayan ya dawo daga sallar ne ya samu isashen bacci bashine ya farkaba sai goma da ‘yan mintina, kafin nan har tagama duk abunda ya dace ta ci kwalliya da riga da skirt na atamfa wanda yamata d’as ajikinta sai k’amshi take, tana mik’e akan kujera tana kallo, sai da yayi wanka ya fito ya ganta kan kujera kasa janye idonsa yayi akanta suka k’ure juna da kallo wanda zallar Soyayyar da sukewa juna bata b’uya ba, ita ta fara janye idonta kana ta tashi ta russuna ta gaidashi, yaji dad’in warewarta ta kalleshi tace “Breakfast is ready” suna zuwa dinning dama tayi warming kazar juya ne sai ta soya masu chips kad’an ta dafa tea mai spices, sunci abincin su a nutse sannan suka dawo cikin falon yana zaune kan doguwar sitter ita kuma ta d’auki kayan ta kaisu kitchen, bayan ta dawo kafin ta zauna ya mata alama da ta isa gareshi batayi musuba ta taka zuwa gareshi tare da mik’a mashi hannunta yanda ya buk’ata, take Adam ya janyota ta fad’a jikinta ya shiga mata magana k’asa-k’asa da sukad’ai sukasan me yake cewa, sai d’an murmushi take nan ne wasan ya fara canza salo don da ya lalubi bakinta taso hanashi aman ina itama sama-sama take jin kanta saboda kayan da akaita bata tasha, take ta bashi had’in kai suka shiga shan bakin junansu kaman ba gobe, duk ya birkice mata da tayi k’ok’arin janye jikinta zai k’ank’ameta sai sunsunar wuyarta yake, daga baya ma sai ya zira hannunsa cikin rigarta ta baya yana shafarta ahankali, ita kuma tuni ta lumshe ido so take tad’an masa bore amma ko’ina najikinta na amsar sak’on abunka da an dad’e ba’a had’uba, tana cikin wannan yanayin taji hannunsa akan k’irjinta take suka ajiye numfashi gaba d’ayansu, tuni ya b’alle mata bra sukuwa sun sauko ta saman d’inkin rigar sai neman hanyar yanda zai jisu abakinsa yake, dak’yar ta kwace daga jikinsa ta hau gyara rigarta , awahallce cike da buk’atuwa yace ” Babyluv.. Ya haka please dont stop me im really hungry” sai da ta mak’alk’aleshi ta shiga masa magana da wani salo akunne tace ” kamanta muna falone fa” yace ” Duk da falon ne wazai shigo mana yanzu” duk ya marairaice mata ya k’ara janyota abuk’ace tana d’an tuttureshi da salon shagwaba haka ya samu ya cire mata riga yagama budurinsa da jikinta, banda ma kar ya zak’e da sai ya k’ure chapter amma yabarwa dare wannan, sai da yasamu nutsuwa ya rungumeta ya k’ara bata hak’uri da sake mata alk’awarin kula da ita, koda tayi yunk’urin tashi hanata yayi ya kwak’umeta acewarsa yayi missing d’umin jikinta sosai, koda rana tayi tanason masu girki k’i yayi sam da bacci ya nemi d’aukarshi sai ya tashi tare da ita sukai kwanciyarsu, sai daf da k’arfe biyu suka tashi inda ya jasu salla, bawani yunwa suke jiba kuma suna da ragowar kazarsu harda snacks don haka shine ya d’an cima itakam kawai smoothie ta k’ara sha..
Sabon angwanci kawai ake zubawa agidan da dare bayan sun gama ciye-ciyensu, wanda ita komi k’adan ta tab’a har yana zolayarta akan ko tak’i ci sai ya fanshe fa,shi ya fita sallar Isha’i ita kuma ta shiga d’aki tana idarwa ta fad’a wanka, wanka tayi na tarar maigida don tasan yau daga ganin rawar kan Adam ba saurara mata zaiyiba yajima bai had’u da maceba, balle shi koda baida jarabar naci to kuma baida juriyar dad’ewa ba’a ganaba, kayan baccin da ta d’auko d’aya daga cikin dozen da ta sayone dukansu na fitina ne natada hankali, wannan basu da maraba da net sai dai har k’asa suke black ne, tasaka hijab tayi shafa’i da wutri, kafin nan gogan ya shigo har ya wuce room d’insa shima ya shirya tsaf abunsa, har wani rawar k’afa yake basu suka had’eba sai 9,dakansa ya biyota d’aki ya d’auko amaryar tasa ya kaita d’akinsa sukayi nafila da Addu’o’i, Allah -Allah yake ya cire hijab d’in don k’amshinta sallama yake doka masa, Ya salam ya furta sanda yayi arba da ita wato bad dressing yayi ga matar da tayiwa mijinta, awani irin slow motion suka jone suka shiga romancing juna cikin nuna k’warewa kai wasu salon da ta masa bata yi masa su abayaba, take ya shiga mata koken dad’i sunsha amarci ranar ba kad’an ba, har kwalla sai da ya share sai yanzu yasan yaso ya janyowa kansa asarar mace tagari mai ni’ima da tsafta, don duk inda yakai kansa jikin Khairi k’amshine shiyasa baya jin wahalar lashe jikinta ta ko’ina, gashi bata cika hanashi k’irjintaba yanda wasu kanyi wai kar su tsofe ko kahau tsarawa miji dokoki nakarka tab’amin can, da sun kai zasu k’ara gigita kansu da wasanni is like he cant get enough of her ranar ganin karya k’waretane yasa ya kyaleta, don ji yayi tasake masa taste da wani laushi, motsi kad’an sai ya rik’o ta jikinsa shidai yajisu manne, sai da suka gama tsaf ta shiga shagwaba akan ita bazata iya mikewa tayi wankaba nan ya lalace yashiga rarrashi sannan ne sukayi wanka kowa yayi na tsarki, suka shirya sai bacci anan ma ruk’unk’umeta yayi yana shakar k’amshin gashinta.. Allah dai ya bada zaman lafia A. K
Ahmad tuni ya sanarwa iyayensa komawarsu sabon gida bayan ya kai Jamila inda zata zabi furnitures anan kano, taso fulako amma dake yan gulma sun zuzuta mata kudinsu Saleema sai ta ware ta zab’a, aka shirya gidan tsaf dake akwai main falo dazaike had’asu sai kowacce nada falo da 2 bedrooms, da d’akin yara guda biyu, sai guest rooms guda biyu da d’aya ta baya na yar aiki, shikuma ogan yana da falo da bedroom d’insa, akwai kitchen na kowacce sai traditional one daga baya inda anan akayi k’aton wajen wanke-wanke, akwai bq agidan amma shi baigama had’ashiba, haka aka d’an taru da yan uwansa sai k’awayenta suka tare agidansu nasu ko’ina da kayansa kuma kodaga windows da chandlies kasan an kashe kud’i ba kad’an ba agidan, hatta d’akunan yan aiki ya musu gadaje, filine k’aton gaske don haka ko gun shuke-shuke yanada girma banda wajan parking dazaici mota kamar takwas, duk da Jamila taji dad’in gidan da sauye-sauye daya mata da ta tuno saboda kishiyane sai ranta yayi masifar baci dan fara’ar da ta fara sai ta daina, ahaka tayi dabara ta samu number Saleema tashiga tura mata sak’o tsoratarwa da wulk’anci, sa taso takawa har Adamawa taci mutumcinta amma ina ya mata warning akan muddin ta zubar masa da mutumci kamar haka abakin auranta, to bazataso hakan ba shiyasa takoma yin hargagi kurum irin na matsorata, itakuwa Saleema aduk sanda Jamila ta tura mata text na hauka sai ta mata reply da kalaman da zata k’ara tunzurata don ita Jamilar ma dariya take bata, sau tari takan nuna mata itafa in akan Ahmad ne ashirye take da komi don bak’aramin so take masaba k’arshe tasha zagi daga Jamilan, bata taba fad’a masa ba don aganinta rashin dacewane kai k’arar, hankali kwance tagama karatunta takoma gida inda anan ne suka d’ora da mata tsumin kamshi da yan gyare-gyarr na gida, son yawan sayen maganin matan nan baida amfani sosai kai bakasan yanda akai ba ka kama sha…
Gidansu Khairi soyayya kurum akesha sai kace sabon aure, kowa yana takatsan-tsan da d’an uwansa, a haka ta k’are satinta ta fara zuwa aiki kafin fara attending lectures, don admision ya fito tasamu, Adam dakansa yaje yamata registration dakomi, kaman koyaushe shine yake kaita yaje ya d’aukota, dake ya je yak’ara sanin yanda zaike controlling kishinsa a opera news sai da yayi following handle daya shafi such issues don haka ya ke j’ara fuskantar komi, yanzu haka suna gaisawa sosai da su H. O. D, shiyasa take jinta complete kaman bata da matsalar komi, su Hafiz da Sayyid sai yanzu suna can Camp shi Hafiz an kaishi nasarawa state shi kuma Sayyid Abuja yanzu haka sauran kwanaki su dawo don basanan ma Khairi ta tare, Humaira ana can zaman Candy sai isma’il dake Ss1 yanzu, rayuwarsu na tafiya daidai.
Tana kitchen tana had’a masa lunch wayarya ta shiga ringing etana dubawa taga Umaima ce take murmushi ya k’wace mata anan take sanar mata jibi zata shigo kano, abun yamata dad’i sun jima suna waya sannan takashe ta k’arasa tare da saurin shiga wanka don gyara jikinta kafin dawowar maigidan nata daga unguwa.
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
44
Bikin Saleema sai dad’a k’aratowa yake, a bangare biyun shiri ake sosai don Ahmad rawar jiki yake ba kad’anba, ya riga yasan taste na abincin ta don haka yasa aransa da zarar tazo wannan maganar takau, Jamila har lab’e take masa idan yana waya, bayama yanzu daya zamanto ga k’ofar falonta ga nasa dukan nasu asama yake sauran d’akunan ne ak’asa,dayaga haka sai ya tsiri tafiya BQ yana yin wayarsa, da taga duk tsorotarwar da takewa Saleema ta nuna mata ba gudu ba ja da baya, abun sai ya dameta takanas ta tafi gidansu Ahmad bada hak’uri akan don Allah su rok’eshi ya janye zata sauya halinta, su kuwa suka k’ara kwantar mata da hankali sukace tunda magana tayi k’arfi ai ba zancen a soketa babu dalilin, haka ta dawo zuciyarta na mata suya, da ya dawo daga office ranar yaga tashin hankali don hanashi hutawa tayi tayi kuka tayi cizo duk yana k’yaleta, don yasa aransa duk haukan da zatayi ba zai tankataba, duk don ta b’ata masa rai tabar Aslma a falon k’asa yayita kuka shikuma yana sama yana juyowa, da ya sauko yaganshi yashe ba ko riga ajikinsa sai shan yatsa yake alamun yunwa, nan ne ransa ya b’aci donshi bai yarda abawa d’ansa wahalaba, ya d’aukoshi yaje yayi ta bugun d’akin ta tak’i bud’ewa sai da yaje d’akinsa ya binciko spare keys ya bud’e, yana shiga bedroom d’inta ya ganta akwance kaca-kaca tana d’aure da zani sai yanzu yaga tsananin fita hayyacinta da tayi ga uwar rama, yaji tausayinta ya kamashi don yasan son shine sila, amma saboda yaronsa ya dake yace ta tashi ta bashi nono ko ranta yayi masifar b’aci, a gadarance tace ” Bazan bayarba sai ka jira waccan shegiyar tazo ta bashi, tunda ta saba bawa uban nasan yanzu ma baza’a rasa ruwan da zata bawa yaronba” yaji haushin furucinta don ko hannun Saleema bai tab’a rik’ewaba, yace ” Ke karki raina min hankali mana maza ki tashi kafin na tsinka miki mari” juyawa tayi tana hawaye ta kwanta tare da cewa ” Sai mu gani ai in nakane” Aikuwa tagani don a jiye Aslam gefe yayi ya saka k’arfinsa ya falle zani daman ba bra ajikinta take suka bayyana, ya janyo yaronsa yasa masa a baki tana mutsu-mutsu ya saukar mata da nauyinsa inda har nishi ta fara, tuni Aslma ya kama sha abun tausayi don kwana biyu haka take masa har yankwanewa yafara da kuwa bul dashi abun sha’awa, taji uwar wahala tashiga cewa ” Ahmad ka d’agani tunda yafara sha ai zan k’arasa bashi” yace ” Inafa in kinga na d’agaki ya k’oshi” saka hannunsa yayi ya k’ara gyara masa zaman nonon abakinsa ya rikeshi yana d’an matsashi kad’an kad’an, iyakar wuya Jamila tazo sai kace wata akuya kara saka kuka tayi mai sauti tana cewa ” Wannan wane irin wulak’ancine haka, nace zan bashi don Allah ka daga ni kar ka sa nayi amai”saida yaja seconds sannan ya tashi yana muzurai yaron kuwa sai da yayi nak bacci ya kwasheshi atake, ya d’aukeshi ya d’auko riga da wando ya saka masa sannan ya maidashi gefe, tana zaune tana d’acin rai don tagama hawayen nata ya kalleta yace ” Jamila akan zan miki kishiya shine kikeson illata yaronki, meye laifinsa? Kinsan kuwa yara amanace Allah ya bamu, ina miki gargadi duk iskancin ki ya tsaya akaina amma wallahi akan Aslam zan miki abunda bakya tunani” sai turo baki take tana ” Aini ma amanace awajanka shine kaje kaci amanata da wata” bai bari ta k’arasa maganar da ta d’eboba yasa hannunsa ya matse bakinta har saida tayi k’ara ya shiga yamutsata azafafe don dukansu sunyi kwanaki wani abu bai shiga tsakaninsuba, daurewa kawai yake to ita kanta da ta fara mutsu-mutsu tana cewa “Kaje gun waccan ta baka” sai gashi da ya kamo tasharta tayi luff suka raya sunna, suna gamawa ta fashe da kuka domin zuciyarta ce ta tafi tunanin yanzu da zarar ya kawo wata haka zasuke sharing d’insa duk irin touches daya ke mata zaije ya mata kankat sai dai wataran taganta da cikinsa, sai kuka shikuwa da yariga ya gano musabbabi shiga lallashinta yayi inda ta yanko masa wata maganar b’acin rai dole ya bar mata d’akin…+
Khairi taje tayiwa collegues d’inta sallama don yanzu zata fara zuwa B.U.K zasu fara lectures, motar da Abbanta yayi niyyar bata ita ya aiko mata da ita vibe maroon colour su biyu ya sayawa itada Safiyya, takanas sukaje masa godiya har Alhaji Abdullahi yake cewa Abban nata dama ya bari mazajensu sun saya masu, sukai dariya, haka ranar suka yini cikin farin ciki a gidan iyayen nasu, balle ma da Umaima ta dawo sai dak’yar Adam ya tattaro ta, bayan tafiyarsune Umaima tayi waya da Anty Asiya tace ” Wallahi mama bakiji kunyar da najiba da Adam yazo, ashe yana sonta haka nadinga dagewa akan su rabu” daga can Anty Asiya tayi dariya tace ” Shiyasa ake cewa tsakanin mata da miji sai Allah” tun a hanyar tace ya tsaya wurin masu sai da fruits, ta fad’i quantity da takeso ta zaro kud’i zata biya ya hana itakuwa ta dage, k’arshe dai ita ta biya suka nufi gida, tana zuwa tayi masu smothie na pineapple sukasha bayan sun yi wanka, dake lokacin misalin k’arfe tara da yan mintina bayan ta saka night gown d’inta wanda bak’aramin fitar da shape d’inta tayiba ga k’irjin V Shape ne hakan yasa komi nata a bayyane yake tana cikin fesa turare yazo ya d’auketa suka dawo falo, acikin yanayin shagwaba tace ” Handsome na d’auka bacci zamuyi yanzu fa” hannunshi na shafar cikinta zuwa k’irjinta yace ” A’a bacci kuma yau anan falo zamuyi bacci, bayan kin tayani kallon show d’innan” ya fad’a yana nuna mata Tv, waro ido tayi tace ” Bacci afalo? Ko meyasa?” rad’a ya mata akunne da saida ta rufe idonta tace ” Kaga ni yarinyace ban iya wannan ba” tashi yayi daga kishingidar da yayi yace ” Koba yarinya ba bari nagani in itace” ya fad’a yana kai hannunsa k’asan ta ita kuma cike da shagwaba tadan gantsare tare da ruk’o wuyansa tana bashi hak’uri, tuni ya k’ara rikicewa yayi saurin juyata zuwa k’asansa lokaci d’aya ya kaima tongue d’inta chafka..
STORY CONTINUES BELOW
Adam yakan gaisa da Ahmad don tunda yaji yanda ya dinga bata shawara akan takoma masa yace ta bashi number d’insa, don haka ita yanzu Khairi zaiyi wuya tayi waya da Ahmad saboda mutumcin auranta, shiyasa friendship d’inta ya koma da Saleema, daman kusan sa’annine da shekara d’aya Khairi ta fita, kuma komi Adam ya sani don har alk’awari ya mata zai barta ta je gidan koda bayan bikin ne.
Su Sayyid sun dawo shida Hafiz, tare suka zo da Umaima gidan nata suka yini, dake weekend ne Adam yaje d’aurin aure garko, hira sosai sukai dasu inda a take-taken Hafiz tagane son Umaima yake, da lokacin Sallah yayi suka fita, bayan sun idar take tambayarta bata mata boye-boyeba ta fad’a mata komi, tace zata bashi dama tagani domin Abdul saurayintamunyi breakup last month, har hutun Umaima ya k’are duk bayan kwana biyu sai tazo gidan Khairi , da ta matsa mata akan tazo ta kwana tace ” Bazan iya zamaba kuna fallin amarci ku kashemin ido” da Umaima zata koma sha tara ta arziki suka had’a mata, inda Khairi tabata materials guda biyu da kayan shafa masu kyau, su a cikin sabon lefen da Adam ya matane akwatina guda biyar, shikuma Adam ya bata 10k, hatta gidansu Hajiya Hassu sun mata kyautuka, zaman da tayi idan ta shiga gidan takan tayata wasu aikin hakan yasa ta shiga ranta sosai, sai bayan tafiyartane Hafiz yake sanarwa Hajiya Hassu tace ” Masha Allah in hakane bazamuyi k’asa agwuiwaba, duk da dai ba’a tabbatar da fara aikinku ba amma munada hope kwana kusa zaku samu” yaji dad’i sosai suma iyayensu maza da sukaji sunyi na’am da abun.
Biki ya kankama duk da dai ita Saleema tace banda Kamu ba abunda zatayi, yan sa’ido daga hostel kuwa takanas suka taho kano, don komi su Saleema anan zasuyi gidan yayanta Fahad, saboda a samawa mutan Jahun sauk’in komi, tunda akace an fara shagalin Biki Jamila haukarta ya k’ara yawa kullum cikin iface-iface take, abunda yasa Ahmad baya damuwa bata tab’a nuna zata yi kisan kai ba shiyasa yake daga nata k’afa, amma batun rashin kunya ba’a magana da rashin gyara da k’in girki, watsa masa abu in yana kwance da hanashi bacci duk tanayi, shiyasa ma yan aiki dattawa biyu yasamo suke kula da gidan da Aslam.
An zo an mata kafin kaya, anci sa’a Jamila bata musu haukaba duk da dai bawani sakewa tayiba, sai su Samira da yan uwantane suka tarbesu dakyau, Ahmad lokacin da zulumi ya yini don ya zaci Jamila zata masa haukan da ta saba, da batayiba abun ya masa dad’i har k’ara zuwa yayi takanas d’akinta ya k’ara lallashinta, tare da mata kai akan ba wata mace da zata gaya mata komi.
Su acan sun fara shagalinsu inda wasu a abokansa sukace yakamata ayi dinner anan Kano , hakan kuwa akayi ana gobe d’aurin aure aka yi dinner a Meena Event Centre cikin Kano , duk abunda ake sai da yan uwan Jamila sukace ta daure duk shagalin da za’ayi tayi attending, amma ina saboda yanayin zuru-zurun da tayi tace bazata ba don kunyata zataji, sai yan gidansune suka wakilceta a kamun da dinner, amma ita tana dutse ana can anayi Samira na watso mata update ta waya, bata tashi gigicewa ba sai da taga pics d’insu da vedios na wajan dinner sunyi kyau matuk’a, gashi sai tafi ake masu don sun burge mutane, yan school kam dayawa sunje wasu ma bata sansu ba don kawai su tabbatar Dr Ahmad dayake daurewane ya auri student, aikuwa sunga yanda yake binta da romeo type look, gurin yad’au mutane sai kace auren fari, su Khairi sunje ita da Adam inda suka sha kwalliya mai kyau, daman shi Adam yaje d’aurin aure, amma basu dad’e awajan Dinner ba saboda Khairi bata jin dad’in jikinta.
Washegari ana d’aura aure kuma ango ya tattaro ya dawo saboda tarb’ar yan kawo amarya anan Dutse, kuma don yazo ya taushi k’irjin uwargida sarautar mata, an bar wad’anda zasu d’auko amarya inda wad’anda basu suka taho da wad’anda sukaje bikin, sauran yan uwa aka kawo su gidansu Ahmad akan washegari yan Jahun zasu tafi bayan an kawo amarya..
Jamila tunda taji an shafa fatiha jikinta ya kama kyarma, sai alokacin tafara jin haushinta na rashin haukar da batayiba ta hana auran, yanzu shikenan daga gobe sun zama su biyu awajan Ahmad zata fara raba shimfid’a da wata, ina bazai yiwuba dole tad’au mataki anan ne shaid’an ya shiga mata zuga duk da agefe zuciyarta na kawo mata nasihun da ajiya mahaifiyarta tazo har gidan ta mata tare da wasu Anties d’inta, zuga zuciyarta take mata ba kad’an ba, tashi tayi ta d’auko wayarta ta dinga zuba masa miss calls, shikuma a lokacin yaje wajan amarsune an masu yan pictures sai a sannan ne ya rik’e hannunta yana kallon asalin lallen da aka mata, yanaji wayarshi na vibration sai da yagama mata maganar ya zaro wayar yaga sunan Jamila, take yaji gabansa ya fad’i ahaka ya daure ya d’aga itakuma Saleema kanta k’asa don bak’aramar kunyarshi take jiba, daga can bangaren Jamila ke tambayarsa ” Zaka dawo yau d’in ne ko kuwa tare da yan kawo amarya zaka zauna ku taho?” yace ” A’a yanzu haka nagama shirin tahowa insha Allah kafin magriba ma nazo gida ai” kashe wayar tayi ta zauna ta cigaba da uban kuka in tayi mai hawaye sai ajima tayi mai sauti wata sa’inma sai ta zunduma ihu tace ” Wayyo Allah na shiga ukuna” tayi k’ak’aji ta huta sai kuma ta nuna k’irjinta “Ni Jamila ni za’ayiwa kishiya Ahmad ka cuceni kaci amanata” daga yanayin maganar da yake tasan da Jamilane haka kurum taji wani kishi ya mintsini zuciyarta, take yar k’wallar da ta taho mata tayi gaggawar saka yatsarta ta share, sake mata sallama yayi sannan suka lula hanyar Dutse, yabar komi a hannun Umar.
Tare suke da wasu Friends d’in nasa da wasu Cousins d’insa, sai hira suke akan bikin shikuwa yanayin muryar Jamila ta masifar d’aga masa hankali, da alama zatayi wani haukarne ko kuma nemansa take ta zube masa wani wulk’ancin, wani cousin dinsane ya jefo masa tsokana dole ya ware suka cigaba da hirarsu, kafin shida suna Dutse direct gidansa suka kaishi inda wad’anda keda gida a dutse cikinsu suka wuce sauran yasa dama an kai katifu BQ su biyune ya nuna masu masauki, agajiye ya shiga bata nan tana d’akinta, don haka bai nemeta ba sai da yayi wanka yana fitowa yaji ana kiran sallar magriba, dake sanyine 6 nayi ake fara kiraye-kirayen sallah, yana sauka yaga suma sun fito da niyyar tafiya masallaci tare suka je daga nan suka dawo gida, sanda ya shigo tana falon k’asa ko kallon inda yake batayiba sai shine ya mata sannu da gida ya tambayi abinci, cewa tayi bata yiba amma an kawo daga gidansu na tarar amarya gasu can, direct ya shiga babban kitchen din dake ak’asa yake yaga manyan coolers da different abinci, zuba musu kala uku yayi ya had’a ababban tray da drinks yakai musu, sannan ya dawo shikam baijin cin abinci yanzu samun gado yayi ya kwanta yad’an matse baccin gajiya, Jamila ganin yanda ya basarta sai ta k’ara k’ulewa k’udurin da ta dad’e dashi aranta shine ya fad’o mata ahanzarce ta shiga k’aramin kitchen d’inta ta d’auko wuk’a sabuwa gal ta nufi d’akin nasa a sukwane, tana shiga kuwa ta tarar ko rufe k’ofar bedroom d’insa baiyiba, baccinsa yake hani’an dagashi sai boxer ya kwanta rigingine, har taje kansa bai saniba saboda azabar gajiya, tafi minti uku tana kallonsa tana ayyana abubuwa da yawa, kuma hawaye basu bar suntiri afuskartaba, sunkuyawa tayi ta shafi saman wandonsa tace ” Yanzu daga yau nasan wannan abun zai bar wurina ya koma wurinta, eh mana wurinta tunda kaji aranka sai ka yi sharing d’insa da ita” ita kad’ai take surutunta, sai kuma ta kwashe da wata dariya ta na kallon wuk’ar sai shek’in sabunta take, tana cikin dariyar sama-sama ya fara jinta ya d’anyi juyi tare da bud’e idonsa dakyar ganin mutum yayi kyam akansa, k’ok’arin tashi yake yi ta kalleshi tace “Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbatar ma Jamila ba’a mata barazana arayuwarta bakuma a had’a soyayyarta da ta kowacce ‘ya mace… Ahmad da kahad’a soyayyata da ta wata ‘ya mace gara na datse tak’amarka ta d’a namiji kowa ya huta” ta nufeshi da wuk’a tsirara ahannunta ganin wuk’ar yasa yake k’ok’arin tashi saboda baccin daya fara jikinshi ya yi nauyi tayi wuf ta hayo kan gadon tare da kai hannunta kan wandonsa zata cire, tuni wani irin k’arfi yazo masa ya bangajeta inda sai da tayi wutsil ta fad’a gefen gadon agicciye, da gudu ya nufo k’asa yana gyara wandonsa sai dai kafin yabar saman ma ta biyoshi da wuk’ar tana kuka ” Wallahi sai na cireta kowa ya huta, badai itace jarabar da tasa zaka k’ara aureba” yana dirowa k’asa a 360 yayi parking lot,yana ” Baba bud’emin” Allah yasa akwai car key a aljihun wandon tuni ya bud’e motar ya kunnata daidai lokacin da maigadi yake kan bud’e gate d’in, sukuma su Yunus suna can cikin bacci sukaji hargowarsa kafin su k’araso Ya take motar lokacin har takaiwa motar caka, tuni ya fice tsayawa sukai suna kallonta su da maigadi ita kuma da gudu ta koma cikin gida ta zube afalo tana kurma ihu, take Aslam shima ya d’ora da kuka yi take ba k’ak’kautawa, su kuma gajiya sukai da tsaiwa suka koma suna tunanin hauka irin na Jamila… Ko’ina Ahmad yayi1
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
45
Rasa inda zaisa ransa yayi ga tarin takaici, sai ya tafi gidansu ya shiga part d’in mazan gidan ya d’au kayan k’aninsa yasa, ya kira gidansu Jamila kan yan tafiya tayata tarb’ar amarya su hanzarta, akai dace suna hanyarsu na zuwa, gidan nasuma shiga yayi ya sanar musu, sannan ya koma cikin gidan, gara yaje ya mata gargadi karta d’auka tsoronta yakeji k’arshe ta badashi awajan dangin amarya, kafin zuwansa har ta gaji da kukanta ta koma part d’inta ta sauya kaya da alama tayi sallah, tana zaune tana jan zuciya ya shiga sai da ya k’ure d’aure fuskarsa ya isa gareta, daga yanayinsa tagane zai iya mata komi gashi hannunsa rik’e da belt tashi tayi tana jan baya da baya har takai jikin k’ofar band’aki tana cewa” Ahmad ni zaka daka? Akan wata don zaka kawo wata shine tun yau zaka nunamun iyakata” wani harara yake aikamata zuwa yayi ya shak’eta jikin bangon yace ” k’warai kuwa zan yi fiye da haka matuk’ar zaki cigaba da mini hauka agida, jamila ina hankalinki ya shiga ace kin nufeni da wuk’a da kin kasheni kina tunanin Allah zai k’yaleki ko kuwa Aslma in ya tashi zai yafemiki?wane irin rashin yarda da k’addarane haka, wallahi kika k’ara barazana da makami Wallahi sai na sakeki” tuni jikinta ya sab’i rawa ta shiga koke-koke da mitar dama ya daina sonta, daka matsa tsawa yayi yace ” Inaso komi ya tafi daidai inba hakaba Wallahi zakisha mamaki, nagaji dake wani irin lallashine ban mikiba” ya fad’i tare da ficewa daga d’aki ya d’auki abunda zai buk’ata ya fice, don yan kawo amarya suna gab da shigowa dutse, ta tsorata da yanayinsa don makamancin kalaman da yayi basu tab’a shiga tsakaninsu ba, dole ta tashi tad’an kintsa kanta tana cikin shiri taji sallamar su Samira da wasu yan familyn Ahmad kamar Hujra da gwaggonshi ta jahun, haka ta sauko suka zauna jiran yan kawo amarya..+
An kawo amarya inda aka damk’ata amana tare da musu nasiha daga Antties d’in amaryar da kuma dangin Ahmad, don dole tabi shawarar Samira ta dinga yak’e tare da amsa musu, da cewar Allah ya basu zaman lafiya insha Allah baza’aji kansuba, har d’akinta aka kaita tare da su Nucy da Tsumagiya, kamar yanda aka bada umarni su zasu kwana agidan tunda da dakuna kawai abarsu su kwana ak’asa ita kuwa amarya tana can sama d’akinta, sun shiga sun zagaye komi kaya tubarkalla an zuba matasu masu kyau da tsada, ga uban gara da aka mata b’angaren kitchen tasha kayan eloctronics damk’am don sun cika kitchen d’in, kasancewarshi k’arami ne sai da aka kai wasu central kitchen, da Saleema taji ance su su zauna k’asa taji ba dad’i aranta tayi ta mitar abun wannan ai rashin kunyane salon abashi dama ya tab’ata gobe ta kasa kallon Aunties d’in nata, don taga alama rawar k’afarshi tayi yawa akanta, an basu abinci da komi inda suka shirya saboda gajiya k’arfe tara duk sun kwanta, ita kuwa tuni ta lalubo number Nucy ta kirata, tana d’agawa tace ” Haba Nucy ya zakimin haka, don ance ku kwana k’asa gaba d’ayanku sai ki yarda kuzo ku tayani kwana mana, ai dai kunsan duk jarabarshi bai isa tab’ani su Aunty Fanna na nan ba ko?” Nucy ta tashi ta shige toilet tace ” Ke ki rufamin Asiri, result d’inmu har yanzu yana school fa bazakisa na kwafsa ba kwab’a ta tayi ruwaba, ballema ke da kanki jiya kike cewa a magungunan da aka d’inga baki har jin feelings kike to meye na damuwa kawai kibari ya kashe arna” cikin jin haushi taja tsaki “kefa namanta bakya rabo da iskanci, shikenan tunda bazakizo ba Tsumagiya ko Furera wani ya zo” Nucy tace ” Wallahi ba ruwana ya za’ayi mu shiga tsakanin sunna, a’a kinsan darajar wannan daran kuwa?” sam Nucy ta hana Saleema magana k’arshe jan tsaki tayi ta kashe wayar, sai da aka tabbatar duk abunda suke buk’ata an ajiye sannan Hujra tabar gidan, sai wurin 10:00 nadare Ahmad yazo kafin nan an tanadi duk mak’ulashen amarya kashi uku Umar ya sayo, tuni ya zaro waya ya k’ira Nucy ta lek’o ya bata babban ledar ciki, shikuwa Ango dagewa yayi akan bamai rakashi tunda ba na fari bane, kuma dare yayi gida da mutane ai basa k’etare su tafi yawan surutu ba don haka ya karb’i leda ya shige ciki, da d’akin Uwargida ya fara inda ya tararta a azaune sai jan zuciya take idonta ya kad’a yayi ja matuk’a, tana gainsa da leda ta mik’e tace ” Ka fice min ad’aki na yafe” kallonta yayi na wasu seconds kana ya ajiye mata ledar ya isa gareta ” Jamila ki kwantar da hankalinki, insha Allah bazaki sameni da rashin adalci tsakaninkuba, har yanzu ina sonki karki manta kece firstlove dina duk wani so da zanyi ko sabo da wani yazama abayanki, kin riga kinyi nisa, ki saka wannan aranki kina da matsayi mai girma a zuciyata” duk da taji dad’in rungumetan da yayi amma take hawaye ya fara suntirikishi na cinta , luff tayi tana sakin ajiyar zuciya, sai da ya d’anyi romancing d’inta sannan ya kaita gado ta kwanta ya kwanta gefenta ya tayata yin Addu’ar bacci ya jamata blanket, sannan ya mata hot peck agoshi ya fice, taji sauk’i kad’an don yana fita wani sabon kukan ya k’wace mata, shikuwa dama tuni acan gidan Umar ya sake wanka shirin bacci yayi tsaf kana ya shiga d’aki Saleema, tana jingine jikin gado har bacci ya fuzgeta taji sallamarsa, bayan ta amsa jikinta ya shiga rawa don muryarta har rawa take daya tambayeta ya zaman kad’aici ta bashi amsa dak’yar, duk wani abu da ake tunanin ango nayi hakan Ahmad yayi sunyi sallah sannan ya tilasta mata cin wani abu, tsorone fal a zuciyarta sai yace mata ” Ki kwantar da hankalinki ba abunda zan miki, ashe duk cika bakinki matsoraciya ce ke?” saboda Saleema awaya roi-roi suke hira bai zaci zatai tsoro kaman hakaba kasancewar wayewarta da yanayin sakewar da take dashi awaya, sai da ya koma falo ta iya shirin baccin ta azatonta ma ya koma site d’inshine, bayan tagama duk wasu goge-goge ta sa rigar baccinta da bata fi iya tsakiyar cinyartaba, dama wad’annan kayan ta saba da sasu a hostel, ta kawo wata net cap tasaka ta kwanta, tare da yin Addu’o’i, batafi minti biyu da fara bacci ba don baiyi nauyiba taji shigowarsa, sai alokacin taga haukarta don ya nuna mata bakomi meyasa ta yarda bata rufe k’ofarta ba atleast gobe ya fara don ita bama tsorone damuwarta ba karsu Aunty gobe su gane wani abu ya shiga tsakaninsu, tana cikin wannan tunani taji hannunsa sun zagayeta, take gabanta ya fara dukan uku-uku yana jin k’arar bugun zuciyarta, rad’a ya shiga mata akunne, ita dai ba abunda take iya yi sai numfashin tsoro, murya asark’e tace ” Hero don Allah karka min komi kaga su Anty Fanna suna nan” dariya yayi yace ” Naji don suna nan sai muk’i bin sunnar ma’aiki, suma zasuyi alfahari da hakan ai kuma kinga zasu san yarinyarsu ta kawo mutumcinta” rok’onshi ta shigayi shikuwa yayi biris, k’arshe ma mik’ewa yayi ya kunna bulb d’in d’akin don ya samu damar k’are mata kallo, aikuwa da sauri tayi k’ok’arin shigewa cikin blanket sai dai tuni yayi hanzarin rik’eshi yana binta da wani mayen kallo, kunya ta taso ta rufeta sai da ya kalleta son ranshi sannan ya kashe bulb din, hankali shi duk yabi ya tashi ya kunna sidelamp ya janyota jikinsa tare da rungumeta yana shak’ar k’amshinta, batayi auneba taji ya cafki bakinta ya shiga bata zafafa kissess harshenta sam yak’i sakinsa, tuni ta shiga rud’ani yana kissing d’inta hannunsa na yawo sai da ya zare nighty d’inta, tuni jikinsu ya had’e nan ne yayi maraba da k’irjinta wanda suke acike daidai tuni ya shiga yamutsa su iya son ransa, tsorone fal aranta tana Addu’a Allah yasa kar ya wuce babban wuri batayi auneba taji ya d’ora bakinsa yana sha a yunwace, tuni kuka ya k’wace mata ” Don Allah kayi hak’uri” baisan tanayiba sai da Ahmad ya d’au lokaci yana wasanni ajikinta kana ya kyaleta kafin nan tasha kukanta wanda shi ya k’ara tunzurashi, don Saleema Allah ya mata baiwar muryar shagwaba bakad’an ba ko amata tana cikin wad’anda suka iya sosai yazama jikinta, don an shagwabata agida ko ak’awaye haka zakaji most of times muryarta, darajar su Anty taci gashi ta nuna batason su gane da yau yunwar da ya dad’e da ita sai ya kaudata, don tun randa hatsaniya ta had’asu da Jamila kan Aslam bai k’ara kusantarta ba shikuma gashi mabuk’aci, aikin rarrashi ya shiga kana ya shiga zolayarta ” Ke da kikace min ke jarumace sai gashi ba’aje ko’inaba kin karaya” tace ” Aini ba akan wannan nake nufiba” kama fuskarta yayi yace “Akan meye kenan?” yana kallon bakinta da yakejin kamar ya k’ara kamasu, tana cikin nagana yayi caraf ya sake rik’esu wannan karon ta fara jin dad’in abun, sai da ya dau wasu minutes d’in kana ya kyaleta, sukai sake shirin bacci, sai da ta matsa kuryar gado ta iya bacci.
STORY CONTINUES BELOW
Jamila kam kasa rintsawa tayi har shaid’an sai da yasata ta fito tana safa da marwa a corridor tana ” Yanzu yana can yana nuk’urkusarta, hoo maza da jaraba suke”
Da safe tsaf ta shirya amma duk da ba abunda ya shiga tsakaninsu sai da taji kunyar saukowa k’asa, haka dai ta daure suna cikin gaisawa aka dinga shigo musu da breakfast, wanda daga gidansu Ahmad ne mai rai da lafiya, suna gama ci aka sallamesu nan ne kuka sabo ya kwacewa amarya dakyar aka cireta daga rikon da tayiwa Anty Fanna, sai da tayi kuka mai isarta sannan ta shige d’akinta..
Bayan sallar magriba Ahmad ya had’asu ya musu nasiha, sannan ya tambaye shawarar uwargida akan kwana, take Jamila aka shiga ciccijewa ana muzurai ita gata babba tace “Inaga kwana bibbiyun yayi” sai Ahmad yace “Amarya hakan yayi miki” bata samu bakin maganaba Jamila tace ” To da kasan zaka tambayeta ya mata ai da kasani kawai ka bari ta fad’a, ni bansan kinibibi” tsawa ya daka mata yace ” Jamila kishiga hankalin kifa, wai ke meyasa bakyasan kama girmanki”tace ” Yayi kyau gara ka nuna mata banda mutumci awurinka” itadai Saleema batace komiba, ganin ranshi ya b’aci tace ” Hero kayi hak’uri, kadaina damun kanka don Allah” kama hab’a Jamila tayi tace ” Ke kinji kisisina banason shishshigi a al’amurana, dake nake koda mijina?” kallonsu duka Saleema tayi tace ” Hero zan iya tafiya?” yace ” Eh shikenan kije” ta juya tayi tafiyart tabar Jamila na b’arin baki shima tafiyarsa yayi, sai da yayi sallar Isha’i ya shigo masu da kayan ciye-ciye, ya kaima Jamila nata sannan ya ajiye masu nasu a d’akinsa don yau Saleema zata fara shiga turakar miji, saboda tsabar fitina Jamila ta shigo don ta duba taga ya nasu yake ko an mata rashin Adalci, tana cikin dube-duben ledar ya fito daga toilet yana tsane jikinsa, dariyace ta kwace masa inda ita kuma tashiga inda-inda ” banga yaji bane a cikin nawa naman” bai cemata komiba ya nufi jikin dressing mirror, komawa tayi d’akinta tana shiga ta samu Aslam sai kuka yake ta d’aukeshi ta shiga bashi nono tanayi tana yagar kazarta don yini tayi tana k’unci ko abincin kirki bata ciba
Saleema shiri tayi tsaf ta gyara jikinta duk inda yakamata, sannan ta d’au waya ta k’ira family nata taji ko sun sauka lafiya, da sauran k’awayenta ta musu bangajiya daga haka ta koma kan gadonta tana tunanin yanda zasu kaya da Ahmad, bacci ya fara d’ibarta sai wayarta ta shiga k’ara Hero tagani arubuce take gabanta ya fad’i,yau za’ashiga other room kenan…
Ahmad ya samu ya raya darensa da Saleema, inda tasha jiki don kara’i yayi a hakama ya samu ya sassauta mata saboda sabon hannuce, kuka take ba kad’an ba sai shimata albarka yake yana aikin lallashinta, hakika Saleema ta shayar dashi mamaki matuk’a yanda wasu kewa ‘yan matan jami’a kallo ashe bahaka bane, gashi ita duk wayewarta bata banzatar da kanta ba don zai iya rantsuwa akan shi yafara hanya ajikinta ballanta na kuma budurcinta, kuma yaci sa’a bata masa taurin kaiba shiyasa a nutse ya mata batare da ya mata ciwoba, adaren ya gyara ta tsaf ji yake kaman ya sake, ba mita ba k’orafi banda tsoron da yagani wannan kuwa common ne ga budurwa.
KANO
Adam wasu lokutan shi yake kai ta makaranta don ita tana da tsoron tuk’in ne, yasha zuwa school ya tarar ana group discussion ya daure, kishi dolene yajishi amma baya hayaniya sai dai yaji ba dad’i aransa, akwai ranar da ya zo d’aukarta yaga ta fito daga office d’in level coordinator wani irin abu yaji aransa, take mood d’insa ya canza ya k’ura mata ido tana iya gano azababben kishin daya cika masa ido, take gabanta ya fara rawa tana cewa Ubangiji yasa ba ba gidan jiya za’a komaba, ab’angaren Adam kuwa kafin ta iso gareshi dake tana nesane ya shiga jan tasbihi da ta’auwuzi don ya kori shaid’anin da yakeson shiga rayuwarsa akaro na biyu, aikuwa tana zuwa jikin motar taga ya sake mata fara’a ya bud’e k’ofa yana cewa ” Babyluv oyoyo” take ta ajiye sanyayyen ajiyar zuciya tace ” Yawwa Handsome nabarka da jira ko?” yace ” No bawani jira bane, ballema kin wuce haka ai” hannunsu hard’e ana junansu suka tafi gida, bak’aramin kwanciyar hankali tasamuba, don bawani fad’a koya ransa ya b’aci daya tashi mata hayaniya zai tuno baya sai kaga in zai mata fad’a a nutse da sigar nasiha yake mata, hakan yasa kimarsa da girmasa suka k’aru a zuciyarta.
Tana idar da sallar Asuba taji bacci na cinta na masifa abun ba’a magana, dakyar tayi azkar dinta tana kwanciya sai ga Adam ya dawo daga yanayinsa yanda ya rungumeta tasan abuk’ace yake dakyar ta samu ta bashi had’in kai in 20 minutes ya samu nutsuwa, adaddafe ta tashi tayi alwala ta dawo takwanta don bacci takeji sosai, har yana cemata ” Yau kece da k’in yin wanka, ki tashi ni sai na miki” dakyar tayi dariya tace ” , Na yafe, kaje kayi nikam sai anjima.. ” shiga yayi toilet d’in yayi wanka yana fitowa ya tarar tayi nisa sosai don haka shima kwantawar yayi don bacci dama asabar ce ba zuwa aiki, baifi minti biyu da bacci ba ta tashe shi tace ” Handsome don Allah ka d’aukomin banana, yunwa nakeji” uhmm kawai yace ya d’auka tsokana ne sai da yaga ta zauna sosai tana rik’e cikinta tana kukan shagwaba tace ” Allah yunwa nakejin, wallahi cikina har yafara ciwon yunwa” bud’e idonsa yayi yake kallonta sannan ya tashi yaje ya d’auko mata guda biyu bayan ya bata yace ” Banda rigima nasan baki cin abu sassafe ai” tuni ta cinye tace ” More please” da mamakj ya fita ya d’auko mata sauran jikin bunch d’in guda biyar, gani yayi har taci hud’u yadda take cima da sauri-sauri kawai ya tsaya yana kallonta, haka kuma batace masa komiba da ta shida ahannunta bacci ya kwasheta bata k’arasa cinyetaba, tana baccin yasa hannu ya zame singlet na jikinta ya kalli kirjinta, sai yayi murmushi yace Allah yasa zarginsa ya tabbata, monday sai suje asibiti aduba masu. Aikuwa kafin monday cin ayaba da safe da tsakiyar dare haka Khairi keyi, ga cinta ya k’aru. Monday kafin ta shiga school sukaje, ana dubawa aka gano tana d’auke da ciki na wata biyu kenan satin da ta dawo da alama haduwarsu na farko tad’auka, bak’aramin farin ciki suka shiga ba sukai Addu’a Allah ya inganta musu.
Tsawon kwana biyar da Saleema tayI agidan soyayya kawai suke zubawa ita dashi, don dole Jamila ke girki duk da yawanci sai ta makara take yi, amma ta daure tanayi ita kuwa Saleema tuni ta fara ajiye kunya tana maidawa Ahmad martani, don wata sa’in in ta masa abu sai yake mamakin yanda ta sani uwa uba dauriyarta da rashin k’orafi, a fili zaka gane yana cikin nutsuwa da walwala, ita kuwa Jamila haka zata k’irk’iro tsokana don Saleema ta tanka mata ita kuwa bata biye mata.
Ana ranar da Ahmad zai fita d’akin Saleema da safe ta shirya tsaf tayi shiga mai matuk’ar d’aukar hankali na straight gown nude colour, tayi kyau matuk’a sannan shape d’inta yafito , Ahmad tunda ya dawo daga waje yaganta ya shiga eyeing din ta hakan kuwa a idon Jamila, take haushi ya taso mata, sai da Ahmad ya fita sallar Azahar ta biyo Saleema har d’aki ta shiga mata warning “Kedai wallahi anyi shegiya tsinanniya, in banda jaraba miji zai bar d’akinki shine don kalan masifa kika so ya k’are nauyinsa akanki, wato yazo dakina babu k’arfi yakasa komi ko? Kwana bakwai da kikai dashi bai ishekiba saboda ke jarababbiyace ” kallonta Saleema tayi tace ” Kwarai kuwa sai na had’a masa dana bye-bye kafin yamma don na kura kullum da yunwar hakan yake kwana” cikin masifa Jamila ta nufeta da zummar ciremata rigar tana fad’in ” Wallahi baki isaba sai kin cire rigar nan” sallamar Ahmad taji lokacin har ta isa ga Saleena ta rik’o mata bayan rigar wurin zip, cak Ahmad yayi yana kallonsu hannunsa rik’e da k’ofar d’akin…
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
46
Kallonsu yake don bai gane me ake cikiba, sakin Saleema tayi idonta kuwa yayi tsuru-tsuru Saleemace tayi k’arfin halin magana tace ” Hero sannu da zuwa” kallon meke faruwa yake mata tace ” Zip d’ina ne yak’i zuguwa take gyaramin” bai yardaba amma jin dabarar Saleema Jamila ta k’irk’iro yak’e tace ” Eh hakane, bari naje inaga Aslma ya tashi a bacci kar ya fad’o k’asa” da hanzari ta fita daga d’akin bayan ta makawa Saleema harara, sai da yaga ta rufo k’ofar ya rungumeta ta baya yana zira kansa ga wuyanta yace ” Ki fad’amin gaskiya meya faru? ” dariya tayi tace ” Wacce gaskiya kuma” kaga zo muje bedroom akwai abunda nakeson nuna maka” kallo mai shauk’i ya bita dashi aikuwa tuni ya bi bayanta yana kallon yanda take karkad’a jikinta, ita kuwa Jamila sai da ta lab’e don taji ko zata fad’a masa mai ya faru..+
Da dare kamar yanda Saleema tagama rud’ashi don haka da buk’ata ya isa ga madam d’in tasa, amma me? duk hargagin kishin da mitar za’a hanashi aiki wajanta da take bata iya juremasa ba, take kuwa ya fara tsaki jin tana ta mita tagaji bazata iya komawa second round ba kai tsaye ba wani salon ladabi balle ya mata uzuri, cikin fushi yace mata ” yanzu da da ba d’aya bane bazan zauna kina wahalar daniba, bazan d’aukaba garama ki sani” masifa ta shiga yi tana cewa ” Kace kurum zaka fara satan kwana kana kai mata, kunga sai ku haifi cikakken d’an haram” yace ” Bazanyi sataba amma kisani wallahi zan iya zare hannuna kanki, in kanwane ki jik’a kisha” ya kwanta rai ba dad’i, asatin nan kurum Saleema ta nuna masa zata iya komi don farin cikinsa he cant wait ranarta ya zagayo, tunowa yayi sun dandale da yar rigimar Jamila akan 15 minutes da safene na checkup akan wadda ba d’akinta ya kwanaba da dare ma haka, yasan she will come with something da zai sashi farin ciki, da tunanin romance na d’azu da sukai yayi bacci, ita kam tuni ta gyara kwanciyar ta ta shiga bacci.. .. Abun takaici miji na d’akinka yana tunanin wata
Saleema duk sai tajita ba d’adi don ta saba ajikinsa take bacci a yan kwanakin nan, ta yarda da body contact shiyasa take yawan manne mashi akai dace shima yanada interest akai, da safe kuwa kaman yanda suka saba afalon k’asane suke da Dinning nan suke cin abinci, don ba ranarta bane bai hanata kashe kala da kaya material lace dinkin na riga da skirt tayi normal make-up, Itama Jamila tayi kwalliyarta sai dai inda ta bada kanta had’e ranta da tayi, sukuwa maza nason ganin smile kan fuskar mace, ita kishi ke hanata cin riba, itakuwa Saleema bayan ta gaidashi suna cin abinci koya suka had’a ido sai ta bishi da naughty smile dake sakashi jin shocking na fuzgarshi, haka suka gama ya bi Saleema d’akinta as sallama don zai fara zuwa office ne, sai da ya sid’e mata nude lipstick d’inta bayan ta sake mashi jiki yaji duminta don a kisisinarta sai da tasa ya cire shirt na jikinsa as tayi missing skin d’inshi, jikinsu na had’uwa take idonsa ya fara ja yad’au caji, sai ta saki dariya ganin gaba d’aya yana neman sakankancewa tace ” Easy Hero kaida keda gida biyu, abunda hausawa sukacewa maganin gobara fa, kaga kar kaje office Uncle Umar ya maka dariya” yana samantane cikin d’an muryar nishi yace ” Ai da bazan damuba, kece gaba d’aya kika rud’ani fa” hannunta cikin sumarshi tace “Laa nid’in kuwa? Matsoraciyar nan fa ko kamanta mai kace” dariya sukai gaba daya sannan sukai last kiss ya fito, kafin nan Jamila na tsaye da briefcase dinsa ta cika fam tana duba agogon wayarta, sai yanzu take jin haushin kanta nasa 15,wanda tayi hakan ne alokacin don ganin week din amaryane tace hakan idan yazo wurinta, tamanta gaba tafi baya yawa, aikuwa taga kwayar idonsa tadan birkice gashi sai blushing yake daga falo ta mika masa ta fasa rakiyar saboda haushi, baiyi mamaki ba saboda yasan dama bata sabayiba sai tana da dalili, yanzuma yasan don da amaryane, yana k’ok’arin shiga mota ya hango Saleema ta saman balcony tana mashi bye-bye, har tana d’an masa inmitating mashi alamun kukan missing, shikuma yamata alama da kar tayi they would be in touch da phone yake d’aga mata, haka Ahmad ya tafi baki baya rufuwa, aikuwa kaman yanda tace Umar sai tsokanarsa yake ” Kaga bakinka kuwa, don Allah ka fara kintsashi kar d’alibai su d’agoka, sai wageshi kake kaman round about” kyaleshi yayi da ya isheshi yace ” Kaidai anyi uncle din banza” Sannan Umar yace ” Au na manta ashe ni surukine, to ya my daughter? ” bai bashi amsa ba sai ga k’ira tsam Ahmad yayi ya shige toilet, ta waje Umar yace ” Eyyyh ba shakka, nima bari nazo na k’ira madam ni za’ayiwa haka”
STORY CONTINUES BELOW
Haka rayuwarsu ta tafi Jamila bata k’aunar taga Saleema tayi gayu, sai haushi yakamata sai tayi ta habaici kaman kishiyar k’auye, ko kuma sai Saleema tad’an fito da k’awayenta sai ta kallesu ta kwashe da dariya tace ” Ana fama” don kawai ta bata haushi sau uku tana mata haka ranar ta friends dinta suka zo, ana nan sai ga su Tsumagiya sunzo dake suna da S.o sunzo gyaranta, aikuwa sun jima asama falon Saleema sai da ta sauko rakasu tare da leda na cosmetics sai ga Jamila bata kula da akwai Tsumagiya ba, ta kallesu tayi dariya tace “Wannan shine kwashi kwaraf d’in ai” juyowa Tsumagiya tayi suna had’a ido kawai Jamila ta shiga inda-inda ta shiga gaidasu, wata dariyace ta tasowa Saleema amma ta dake, to dalilin wannan ta rage mata yin hakan saboda kar ta sake maimaita wa..
Khairi tana karatunta cikin kwanciyar hankali, at times takan shiga Lab agaisa, cikinta kuwa taci sa’a bamai laulayi bane sai azabar ci da take, matuk’ar in ta tashi zatayi gaggawar shan lipton to bazatayi l amaiba kuma zata yini normal, sai dan ciwon kai da d’an zazzabi jefi-jefi, Adam bak’aramin kaffa-kaffa yake da itaba bayaso asake samun matsala da cikin, shiyasa duk neman maganar aikenshi kitchen dauko min banana ko pineapple duk baccin da yake sai kaga ya daure, su kuwa iyayensu ganin suna zaune lafiya abun bak’aramin d’adi yake musuba, gashi su Muhsin da wuya kaji ance sunyi matsalar da har takai wani ya shiga, baya wuce rikicin mata da miji da zasuyi solving dakansu, don haka yanzu Family d’insu ya k’ara dinkewa.
Yau Safiyya tazo mata yini tare da Babynta da suke kira Afnan, yarinyar kamarta k’ara bayyana yake dasu Khairi saboda ba inda ta baro Muhsin, hira suke sosai har suka sakankance basu d’ora girki da wuriba, Adam da Muhsin da sukaje Kura tare da su Abba da yunwa suka dawo, lokacin k’arfe uku harda minti ashirin da bakwai, daka gansu kasan yunwa na cinsu, sun taresu sannan suka zauna kallon Khairi Adam yayi yace ” Babyluv ba’a gama abinci bane?” lokacin ta kawo musu sauran cake da take dashi tace ” Handsome da saura mun sha’afa ne amma nasan kuna dawo wa daga sallar la’asar zaku tarar ya gamu” jan tsaki yayi yacewa Muhsin ” Matarka ta shafawa mata ta, don ni nasan halin Babyluv dina bata makaran abinci koda tafita kuwa” Muhsin yace ” A’a me kake nufi? Nima matata bata makarar abinci, balle ta koyawa matarka kawai dai surutun matar kane yayi yawa har tasa aka manta damu” dariya Safiyya tayi tace ” HoneyB ya za’ai mu manta daku, kawai stew ne bai k’arasa ba shima nepa ne da suka d’auke afarko yasa ba’ayi blending ba” Khairi sai murmushi take tana zaune jikinsu na gogar juna da Adam tace ” Handsome ina fatan yunwa bai maka yunwa ba kar ya illata min kai” murmushi yayi bayan ya gutsiri cake da ta bashi yace ” ganinki yasa rabin yunwar ya tafi, bari muje masallaci kar mu rasa jam’i” daga haka suka fice, kafin su dawo su Khairi sun tsara abincin ak’asa saboda suji dad’in ci, bawani abu bane white rice sukai sai stew gefe d’aya sun had’a musu macroni salad sai zobo da suka had’a dayasha cucumber da pineapple da kayan k’amshi, sannan sunyi dicing watermelon da paw-paw da banana a trasfarrent bowl, ya bada colour mai kyau, tare kowa yake ci da matarsa abun sha’awa, tabbas da Alhaji Aliyu da Abdullahi zasuga hakan zasu k’ara jin dadi saboda haduwar kan ‘ya’yansu, suna cikin ci Safiyya tace bari muyi pic din tarihi ta d’auki wayarta ta musu pics guda uku, nafarko normal one na biyun kuwa couple pose sukai, ahaka cikin jin d’ad’i suka gama ci Muhsin ya koma kan kujera inda Khairi ta kwashi kayan kan tray Adam ya tayata kaiwa kitchen a cewarsu bak’insu su huta, suna shiga kitchen d’in ta ajiye na hannunta Adam ya rik’ota yace ” Ya babyna?” ya fada yana shafar cikinta tare da d’an mintsinin cibiyarta ahankali, lumshe ido tayi ta rik’e hannun nasa da still yana kan cibiyarta tace ” Ur baby is very ok” peck ya mata agoshi suka fito, suna zama tayi already Safiyya ta zuba ma Muhsin diced fruits d’in acup yanasha, itama Khairi zuba wa tayi ta mik’a mashi, ta zuba nata ta ajiye gabanta Afnan da bata jima da tashiba ta shiga kuka, d’aukota tayi ta isa ga Safiyya tace ” Maman baby tunda kin koshi bismillah ki sallamemu” kicinkicin da fuska Safiyya tayi tace ” Haba daga ci ai baima fara zuwa ba, don Allah ki ajiyeta wallahi bansan feeding sosai, nasan bawani yunwa take jiba” tab Khairi tace ” Wallahi sai kin bata, haka Mama ta miki? wato kina sahun masu son wahalar da Baby ko” sai ta rage muryarta tace ” Ai kin saba bawa babanta kodan shi kema kina enjoying ne?” take mata k’afa Safiyya tayi Muhsin yasa baki yace ta bata sannan ta karb’eta, haka suka yini cikin walwala suna wasa da barkwanci suna fitowa daga magriba suka tafi gida..
STORY CONTINUES BELOW
DUTSE
Duk da Ahmad bai tab’a zama ya kushe Jamilaba, ko ya tona sirrin dake tsakaninsu ga Saleema amma ta fahimci Jamila nada sakaci kansa, sai ta alak’anta hakan da kishi ne yasa, aranta take mamakin wasu abubuwan especially kan girki nata kawai idone nata, shiyasa ta d’aura damarar yi da gayya don ta nunama Jamila atleast kozata koya.
Kasancewar yau ita keda girki bak’aramin shiri takewa Heron nataba, sai hidimarta take inda Jamila takaici ke cin ranta sai tsaki take ita kad’ai, ita kuwa Saleema zama tayi ta mashi friedrice tayi shredding liver ta had’ata mata sauce dayaji sweet paper, ta had’a coleslow tare da Pineapple and ginger juice, to me take jira tunda akwai kayan had’i, tsawon yini tana zaune agida ai zata iya komi balle abincin bawani yawa, tana gamawa ta jera komi a dinning ta haura sama don ta k’ara kimtsa kanta, tasan yace mata yana son ganinta da S gown saboda haka ta sami straight gown d’inta dark purple tasa wanda zip ne akayishi tun daga farko har k’asanta tagaba, yanayinta tana da d’an rubber ta saka hulan turban mai style mai kyau, k’arfe shida Saura ya shigo gidan bataji nauyin ganin Jamila takasa ta tsare a falon k’asa ba ta tafi da salonta ta tareshi hannunsu sark’ale dana juna suka shigo falon, wani kallon Jamila tabisu dashi ta tashi tana kallonsa tace ” Ahmad bakuwa zakuke mana fitsara a gidaba saboda Aslam sannan ka yiwa matarka warning ta rage mana tsirara banaso yarona ya bud’e idonsa da hakan” Ahmad yana da niyyar mata magana Saleema ta kalleshi ta rufe masa baki da fingers d’inta tace ” karka damu kanka kace zakai fad’a kga yanzu ka dawo, banaso kasawa kanka komi kar kanka yayi ciwo” ashagwaban ce kallonta yake yayi shirun kuwa suka haura sama suka ba banza ajiyarta, take ranta ya b’aci ita za’a mannawa hauka kawai sai ta fashe da kuka, a sama kuwa sam Saleema tak’i barima ya maida maganar ta bashi drink yasha ya shiga ya d’auro alwala ya nufi masallaci.
Bayan ya dawo duk da Jamila taci abincin da yamma sai ta sake hawa table don ta takura musu, yana cin abincin ita Saleema na gefe na tayashi k’ara wani abun, can Jamila takai loman shinkafa tace ” Ahmad zakai fama agidan nan, yarinya sai son almubazzaranci” kallonta yayi yace ” Jamila nasaba sauraran gulma daga garekine? ” Ita Saleema bud’e ido tayi tana mamaki to wanne almubazszaranci tayi? ranshi har ya fara b’aci bayason neman rigima ita kuma Jamila tace ” Ai ba gulma bane saboda tana wajan wadda tayi ai” zai bata amsa Saleema ta kalleshi irin kallon please leave her, ya kalleta yanaso yace allow me to stop her, ta tashi ta isa gareshi ta kamo kanshi tasaka ak’irjinta da sigar lallashi tana shafa bayansa ahankali, Jamila kuwa ajiye spoon tayi tana kallon ikon Allah ” Take it Easy Hero, please kar ka kware” ta fad’a sannan ta sakeshi ta koma kan kujerar ta Jamila bak’in ciki ne ya k’ureta ta tashi tabar musu table d’in, sukuwa suka cigaba da cin abincinsu sai da yayi nak ta gyara wurin suka haura sama, yana zaune akan gado ya had’a bayansa da allon gadon yace ” Baby ki fad’amin gaskiya ko akwai abunda yake faruwa idan bana nan” murmushi tayi tace ” Laa bawani abu dayake faruwa kawai dai maybe sai kana nan ne take irin maganganun kaga kuma ai agaban kane, don Allah kadaina biyeta don kowacce mace zata iya fiye da hakama, sai mujira har ta huce ko? ” ta fad’a tana kallonsa da sigar shagwabarta “Eh hakane yanda kikace za’ayi” had’ata da jikinsa yayi yana jin k’amshinta tana danna waya suna kallon pics na bikinsu tare, wani suyi dariya wani kuma ya mata bayani kan waye apic din ko ita tafad’a mashi ahaka aka kira Isha’i ya fita, koda dare yayo sai da ta rud’ashi fiye da tunanin sa sai da yajishi very weak kanshi ya d’ora akan k’ijinta yana mata godiya da yabo, ita kuma tana nuna masa ashirye take sannan burinta akullum tamasa biyayya, ya bata wuya amma gashi sai nuna mashi take bakomi amma yana iya gane hakan a yanayinta, ahaka sukai wanka suka dawo suka kwanta amma sai da ta sauya masu bedsheet kafin nan, tana kwanciya kuwa bacci ya shiga fizgarta, gyaramata kwanciya yayi ajikinsa yana d’an mammatsa mata hannunta, yasan sun gaji kodaga yanayin wasannin da tamasa ranar, bacci mai nauyine ya d’auketa shikuma ya k’ura mata ido yana jin k’aunarta na nunkuwa aransa, yafi minti talatin ahaka cikin bacci tayi juyi taganshi idonsa biyu a yanayin bacci take tambayarsa ” Meya faru ka kasa bacci ne? ” yace ” Yanzu na bude idona nima” tace “Ok mu koma ko” yayi murmushi yace ” Yass baby” suka rungume juna suka shiga baccinsu..
Koda wani weekend Ahmad ya kawosu gidansu suka yini, anan Jamila taga a salin kunya da biyayya awajan Saleema don sai da ta taya su Naja’atu aiki agidan, sannan tak’i hawa kujera saboda jin nauyinsu da take, daga nan bayan Sallar la’asar ya kaisu gidansu Jamila 5:30 suka baro gida suka nufi nasu, ranar ya kasance girkin Jamila tagama shirin ta tsaf saboda tanaso yau ta bashi dama sosai don ta lura har rawar k’afa yake kan ranar Saleema, kuma tana kyautata zaton jarabar tane yasa hakan don tasan ko ita basu tashi case sai akan wannan, a ranar kam tayi k’ok’ari don ta jure 3 round duk da na farko ne ta iya tayashi, sauran sakin jiki tayi ko kiss yake bata iya saka hannu ta rikeshi tayi lakwaf kamar wanda ake raping, amma duk da hakan kuma akarin kanta taga yanda ya bata kulawa da zasuyi bacci a ranta tace “g
“Gaskiya Ahmad akwai jaraba mata biyu amma kullum sai kaga kamar a buk’ace yake, washegari ta tashi tayi kwalliyarta cikin riga da zani tayi breakfast d’in ta tea da bread sai tayi frying egg, tagama jerashi ak’asa tamasa magana shikuma ya shiga duba lafiyar Saleema, inda sukai gaisuwarsu ta masoya sannan yace ta fito break, itama kaman had’in baki ranar wraffer skirt ne ajikinta na atamfa holland, don haka yau hausa ce acikin gidan nasa, koda suka zauna cin abinci sai yake kallonsu yana godewa Allah daya bashi mata kamarsu, da yazo zai fita unguwa yama Jamila alaman yar rakiyar atunaninsa ko itama zata keyi sai yaga akasin don yatsina fuska tayi tace ” Haba Ahmad kasan na gaji wlh duka jiya ba baccin kirki kasan kabari nayiba, gabadaya jikina ciwo yake” take wani abu yazo ya daki k’irjin Saleema, shima Ahmad sai yaji wani iri yasan da gayya Jamila tayi hakan don ta bawa Saleema kishi, cikin dauriya Saleema ta basar bata nuna komiba, sai wani felek’e take wai tabata haushi Saleema kuwa tace aranta wannan ai k’auyanci kenan, amma da ita ake zancen kowa yaci tuwo da ita miya yasha sai ta gumawa Jamila bak’in ciki soon nan gaba bazata kara shaawar tak’ularta da irin wannan abun ba..
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
47
Yau girki ya dawo ga amarsu salon ta na yau daban ne, tunda ta taro Ahmad take shishige masa gashi ranar wata net gown tasa taje k’asa amma har d’an tsinin nipples d’inta yana gani, don lace bra tasa kuma halfcup ce, gaba daya ya rikice sai kaima wajan hannu yake, tasan Jamila ta saba sa ido ta zauna afalo duk ranar girkin Saleema don ta hanasu rawar gaban hantsi, don haka tun daga farfajiya tasan yanda akai ta gigitar da shi, sanin yan aiki basu zama sosai da yamma a falo yasa daya kai hannunsa k’irjinta bata hanashiba saima turo masa su da tayi, sai sauke ajiyar zuciya yake na buk’ata Jamila na kame akan dinning tana kallon shigowarsu, cikin rad’a Ahmad yake cewa ” Oh my god baby anya zan iya jurewa har mukai sama” dan dariya tayi ashagwabe tace ” Zaka iya meye na k’aguwa, kaida abunka yau kaman baby zan baka sai ka gaji dan kanka” jin haka yaji ya k’ara kunnuwa dan shi dirty talks suna kunnashi sosai, jin haka kawai ya d’auketa gaba d’aya ya dora kan kujerar dake kusa da stairs ya shiga mutsu-mutsun zame mata riga ita kuma tana masa nishin shagwaba tana cewa ” Hero kabari mu k’ara sa d’aki i will let you suck ’em till u satisfy” Jamila kawai mik’ewa tayi tsaye tayi lokaci d’aya jikinta ya d’auki rawa hawaye na saukowa a idonta, ahaka Ahmad yayi nasarar zaro daya daga jikin bra ya saka abakinsa wani nishin iya shege Saleema ta saki, shima jinshi abakinsa ya saki ajiyar zuciya, ta gefen ido Saleema take kallon Jamila aikuwa taga yes ta rama iskancin da tamata har ta bata bashi, don ranar da Jamila ta fadi wai ta gaji bakaramin kishi ne ya turketaba tasan tana sanine ta fada, to ita kuwa ramako irin wannan bata sanya wajan yinsa, ya samu minti uku yana haka Jamila ta kasa daukar mataki don kafarta rawa take balle ta samu damar zuwa kusa dasu, minti biyar Ahmad yamanta inda suke sai da Jamila ta kusa isowa tsakiyar falon Saleema ta tureshi ahankali tana kirkirar kwalla makirci tace ” Hero nafada maka falone kar wani ya shigo yaganmu ko Aunty” a wahale ya mik’e yana kallon cikin falon zuwa k’ofa, wata iriyar Kunyace ta kamashi da yaga Jamila a tsaye take Saleema dama tai hanzarin maida rigarta don bataso kishiyarta tasan jikinta tun yanzu , Jamila da suka had’a ido da Ahmad kawai sai ta taka da gudu tayi sama d’akinta, kallon Saleema yayi ta gyada mashi kai alamun yaje ya rarrasheta, baiyi kasa agwuiwaba ya bita, yana tafiya Saleema tace ” Hmmn dani kike wasa, ai ke karamar mara kunya ce”…+
Tunda tashiga tak’i juyowa ta kalleshi sai ma isa da tayi jikin closet tana fito da kayanta, hak’uri ya shiga bata yana tare kayan da take watsowa zuwa k’asa tace “Ahmad wane irin cin fuskane wannan? Tunda kamanta da zamana agidan gara na koma gidan mu” Tabbas an mata laifi amma ya zaiyi shi sam ya fita nutsuwar shine , ya dage kai yana rik’eta tana tureshi dakyar ya samu ya matseta jikin closet din yai gaggawar saka bakinsa abakinta ya shiga janyo tongue dinta yana mata wani salo, tadan ladabtu sai dai hawaye bai daina fitowa daga idontaba, ganin tayi lak’was ya shiga bata baki ” Don Allah kiyi hakuri i wont repeat it again, i dont know when it started please Sweety bazan sakeba” kukanta ta cigaba dayi yasaka hannu ya share mata hawaye yace ” Don Allah ki daina kinga tsabar yawan kukan da kike kinsa fararen idon nan nawa sun fara canza kala and u know suna cikin abunda sukafi daukar hankalina ake ko” harararshi tayi kawai ta shige toilet, sai ji yayi an tada jam’i , sallar magribar nan sai da ya makara..
Da dare sai Saleema tafishi nuna damuwa kan abu, wai ita har kunyar fita take a yanda tace mashi, don haka bai gano da niyya tayi hakan ba, haka darensu ya kaya da yaje yiwa Jamila sallama sai da ya jima yana aikin lallab’ata har 15 minutes d’i ta wuce, koda ya dawo wajan Saleema tun kan ta tambaya ya shiga mata bayani tace ” A’a bakomai ai yakamata, don mun mata laifi im sorry i dont know it will grow like this bazan k’ara saka irin kayanba Hero kayi hak’uri” duk tayi kalan tausayi rungumeta yayi yace ” Bakomi Baby ba laifinki bane harda ni, insha Allah zamu kiyaye stop worrying yourself, ok?” ta gyada masa kai tace ” Okh.. .
STORY CONTINUES BELOW
Jamila kuwa bugawa Samira waya tayi ta fad’a mata, wata ashar Samira ta saki tace ” kuma ke wane mataki kike tunanin d’auka?” share hancinta tayi tace ” Har yanzu bansan me zan musu na huceba, komi na kawo a raina sai naji kaman ban d’auki mataki ba” Samira tace ” Kema ki rama mana, mezai hana kimata wanda yafi hakan inda dama ki cika mata gida da ihu ranar da yadawo wajanki, koda kuwa bakiji d’ad’in abun ba” Jamila ta kyalkyale da dariya tace “Kuma hakane fa nasan dole taji haushi, amma anya zan iya kuwa?” Samira na tsaka da bata muguwar shawara mijinta yazo ya daka mata tsawa yace ” Ya za’ai kibarni ina jiranki, don uwarki” take jikinta ya sab’i rawa ta tafi d’aki, haka mijin Samira yake ko kwatar halin Ahmad baiyiba amma tana nan tana zuga Jamila zata janyowa kanta mutuwar aure, don shi mijin Samira baya d’aukar wargi kuma haka zai tayi sai yayi sau 6 adare d’aya, shiyasa bata da aiki sai aukin maganin mata don kullum adirje take awajansa, ita kuwa Jamila taci sa’a mijinta baya wuce uku arana wataran biyu ko yayi fashi ma, amma take hanashi duk gani take shi jarababbene abinda takasa ganewa kowacce mace tana hakuri da buk’atar mijinta, domin idan kina ganin naki nada jaraba in kikaji labarin wata sai kisan naki baije ko’inaba, ko kuma kaga wani sai aukin sex baya romance balle dan aike ya isa ga macen har suyi enjoying gaba d’aya, to haka k’alubalen rayuwa ya gada.
Washegari Jamila bata nuna musu komiba, ita kuma Saleema sai batayi wata shigaba ta tsirara duk a sunan plan ne, sai tasa bubu na wani lace ta tareshi normal sukai lunching d’insu lafiya lou, batai tunanin komiba amma fa yini sukai ranar ana banka mata harara ko kuma kaji kawai Jamila tayi dariya tace ” zanyi tsiya a gidan nan” afili take fad’a ita kuwa Saleema ko ajikinta don tasan ashirye take, balle me zai dameta wanda ya kawota ya ajiye suna d’asawa dashi, haka danginsa in sunzo basa nuna basa yinta, itama kuma komi normal take musu b’angaren iyayenta tana waya dasu akai-akai, wata sa’in in tana waya da Ya fahad har wani iri Ahmad yakeji saboda shagwabarta.
KANO
Yau tunda ta tashi take jinta somehow daga school wucewa tayi gidan khadija zata duba babynta, k’ofar gida suka had’u da mijinta suka gaisa saidai taga kaman fuskarshi ba walwala, bayan sun gaisa da Khadija take nazarin ta tad’an fad’a kad’an da alama suna da matsala amma sai ta kawar, tasan in ta dameta zata mata maganar kar taje ta tambaya k’ila ko sirrine da bataso ta sani, sun d’an taba hira inda Khairi keta yiwa babyn wasa da d’an rawa a haka yayi bacci, itama ta kishingida tana kallon Khadija minti kad’an ko suna magana sai tayi zuru alamun tunani, bazata iya kyaleta a haka ba saboda Khadija duk sanda taganta adamuwa takan kokarin ganin ta san meye ke damunta ta bata shawara, tsabar ta shiga tunani har Khairi tabar kujerar da take ta isa gareta bata saniba ta dafa cinyarta ” meyake faruwa dake ne?” firgigit ta dawo daga tunanin, ta sake mata tambayar take k’walla ta fara cikowa daga idanunta tace ” Wallahi gaba d’aya na shiga damuwane, nida Ya Amin komi yana nema ya cakud’emin kinga munkusa wata yanzu muna rikici na rasa wazan fad’awa matsalata don abun ne da kunya” Subhanallah Khairi tace tace ” Wane irin abune haka, kodan in wani laifine kika masa ki je kibashi hakuri mana ki saukar dakai a wuce wurin” tace “Bazaki ganeba ba laifi bane kuma laifine, kwata-kwata yanzu bamu enjoying sexlife ne ni ban fiya son yawan yi da yakeba, bana iya jura kusan yanzu sai kiga yana fushi dani duk randa na hanashi yi sosai, gashi shikansa da wuri yake gajiya amma sai kiga in ya huta yana nuna yanaso sai yazama sai nafara bacci sai ya kara bijirowa in yagama in 15 minutes ajima sai yakara duk ya hanani sakewa da daren, taya zan jura ahaka ba bacci a nutse” shiru Khairi tayi tace “Idan hakane duka ku biyun kuna da matsala wadda kusan kece maganinta kurum, don duk da niba masaniya bace kan nan kuma ba aikin lafiya nakeba, ina tunanin sai kin gyara salon abincinku yanda zaku zama kuna da kuzari both kedashi, tayanda yin farkoma zaku d’au time so zakiga bazakuyi akai-akaiba inba yanada nacin bane sosai, kuma kema zakiji kina da karfin jurar haka” Khadija tace ” Kaman ya? Abincinmu?” tace ” Eh abincinku kila baki bawa fruits da vegtables hakki sosaiba, ko kuma kina saka mai dayawa a abincinku, da irin natural drinks da zakike muku ke kanki karkiyi sanya dasu, wannan yawan shan maganin matan ba shine gyaraba sai kiyi tayi in baka cima mai ma’ana kaga abun yak’i ci yaki cinyewa” tabbas biri zaiyi kama da mutum don tasan bata wani damu da suba, koshi mijin yafi sayan tarkacen lemuna roba da dai kayan kwalam don sukan fi 3 weeks basu sha fruit ba haka ganye sai jefi-jefi, dake yanada son shinkafa da wake iyakarshi in tayi ta soya titus da tumatir da albasa da take yankawa, kuma yana yawancinta bata saka ko lettuce zogale kuwa da zobo sai in wata a dangi ta kawo take amfani dasu, ko in taje gida tayi sha’awar daukowa hatta kunun aya sai dai wataran ta saya, sosai Khairi ta mata bayani ta ce zata bada number ta asakata wani group na girke-girke na masana ne na kafiya da manha haka zataga abu mai ma’ana sosai aciki, sannan ta kwantar mata da hankali tace ” Kafin komi yafara aiki don Allah kidaina masa korafi akan hakan, wazai je ya nema bandake ko so kike yafara bin matan banza? Kowa haka yake hak’uri da bukatar mijinsa wani yafika wani matarsa ta fishi kuma dole ka jure, don shine tarayya dole akwai differences between kaida spouce dinka hakkin sane ka jure hakan” hirar da sukai tasa ta jita d’an warware sai da tayi sallar la’asar ta tafi gidanta, sannan ta d’ora masa abinci, don ita tama ci wani gidan khadija yanda tazama acici ai bazata kai la’asar batai lunch ba.
****** *******
Yanda Samira ta bawa Jamila shawara hakan kuwa tayi don ranar haka tadinga zuba masa kwakwazo yana toshe mata baki yanda kasan cire mata rai yake, to ita ba iyawa tayi ba balle koda ta iya ta ware murya dayawa abun sai yazama kaman mutum ana masa gyaran targad’e, ihu kan gari Allah yaso ma gidan katone makoci ba jinsu zaiyiba, Aslam kuwa farkawa yayi yayi ta tsalla ihu dole taje ta d’aukoshi daga gadon shi ta shiga bashi nono, shikansa Ahmad mamaki yake yace mata ” Wai meye dalilin ki nayin hakan” yana gefen gado ransa duk ab’ace tace ” Ai kaine gaba d’aya ka rud’ani” had’e rai yayi shida yasan normal abune da suka saba kuma mai yasa da batayi, yagama ganota so take ta cusawa Salima haushi, kai Jamila mai kala-kala in tagama wannan ta b’ullo da wannan yace mata ” Naji inma ramawa kikai akan abunda yafaru shekaranjiya please nabaki hakuri don Allah karki sake mana ihun nan, in mutane suka jiyo fa kinsan dare da daukar magana” sai da Aslam yakoma bacci ta tashi zata shiga toilet ta kalleshi tace ” Naji shugaban masu adalci na kasa ai ita baka mata fadan ba saini, kuma inda itane tayi bazakace yayi yawaba naga kunsaba yi kaida ita, tunda hakane na yafe mata kaje kuyi tayi kaida ita, daga yau ba abunda zai sake shiga tsakaninmu” dafe goshinsa yayi wata sabuwa kenan, daga fadar gaskiya ihun is too much is beyond yanda aka saba, wai dama haka mata biyu suke? Yake tambayar kansa ace wai karin dadi ashe kullum a matsala kake, shi baida aiki sai rikici. Matsalar wasu matan kenan sai kaga sun rufe ido basa ganin laifinsu saboda kishi, har shaidan yake neman nuna musu kishiya ce tasa miji ke musu wani abun bayan suke da problem, tana shiga toilet ta kama kuka tana tsinewa Umar da wadanda suka bada gudummawa a auro Saleema.
Sai juye-juye take takaici na cinta don duk kwaroroton Jamila akunnenta, tasan ya wuce tunani don tun tanajin haushi da take jiyowa sai da ta bushe da dariya don kanaji kasan k’ak’aroshi akai, tayi dariya mai isarta tace “Bazan biyekiba don Wallahi wataran sai anyi abunda bakya tunani” da safe ko ta nuna taji abunda akai, ran Jamila yak’ara b’aci so tayi taga Saleema na fushi dashi ta yanda zata san taji haushi amma ina sai ma wani had’ewa da tayi cikin palazzo trouser da crop top tay rolling, aikuwa da ta gitta sai ya bita da ido, suna yin break yana shashimar k’afarta ta k’asa, da Jamila ta tafi rakashi tana kisisina wai duk don ta bata haushi sai Saleema ta d’auki Aslam daya fara rarrafawa zai kama mamanshi yana kuka tace ” Aslam rigima ko? Kabar Abba yayi sallama da mama kaji” tana jijjiga shi k’arshe sama tayi dashi, bayan Jamila ta dawo daga rakiyarsa taje daki tafi minti 15 tana yar fara’a zata cigaba da zak’e masa awaje don Saleema taji haushi amma a cikin room shi zatake garawa don Wallahi tayi zuciya sai ya sauko yana rokonta zata bashi, tana cikin chat sai ga Saleema tayi knocking bayan ta b’ude tace ” Anty a bani kayan Aslma na canza masa ban kulaba ya batasu da cream dana ajiye akasa” yatsina tayi ta d’auko mata wasu itakuwa sai da ta murmusa ta karb’a, bayan fitarta Jamila tace wannan anyi matsiyaciya wai ita bata fushine?. Ahmad yana tafe yana mamakin Jamila fada sukai amma da safe tana ta shigemasa wato dai dagaske so take take tunzura baby d’ad’in tama bata biyeta sai yayi dariya yace ” Mata! Mata hmm”
Adaren ranar sai ya k’ara bijiro mata don ya tabbatar da gaskene ta daina aikuwa halin da ta saba da shi ta nuna, sam ta cije shima dama bayanason yi bane kawai don yayi confirming ne, aikuwa ya mata maganganu inda yace “Taje ta rik’e zai kyaleta har sai tazo ta nemeshi ranar zata koyi hankali” tace ” Hum’un zan gani” yayi kwanciyarshi daga bayama fitowa yayi falonsa ya kwanta ya shiga chatting d’insa luckily yaga Baby online dake time d’in goma da rabi yace ” meya hanaki bacci kika kai dare haka online” tace “missing d’in mijina nayi, amma in bakaso nayi staying i would turnoff my data” yace ” Banaso kike fin goma online please , amma yanzu i want have gist with you” tace ” Hero bazakai bacciba? Kaga ba d’adi in mukaima Anty haka” bazataso kantaba don ko ita bazataji dadi in akai mata hakaba, duk da shes missing him deep down da tuni yanzu tana jikinsa tana tab’ararta yanda takeso yace “Nasan da hakan bata jin dadine har tasha magani bacci ya kwasheta” sai da yaji kunyar sharotan da yayi don in ba haka yayiba zata koreshine kuma gaskiya shi yana son magana da ita kodan ya sauko daga hurashi da Jamila tayi, sun d’au time suna chat inda rabi na tuna last nights din sune gabad’aya sun samu nutsuwa, sannan past 11 bacci ya fara d’aukarta sai gani yayi yamata message an dade batai replying ba yasan kuwa sai dai baccin ne, sai ya k’irata vibration na wayar ya tadata ta tashi ta kashe data bayan sunyi sallama ta bashi muahh ta wayar..
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
Slm fans kunjini kwana biyu shiru amma nagama typing waya ke ban matsala.
48
Abida tana nan rayuwa ta birkice mata gabad’aya, don yanzu bata isa taje inda ake taro a unguwarsu ba sai tasha habaici da dariya, ace ta lek’o-takoma tunda taje gidan daula ta kaso auranta gashi yanzu takoma gidan jiya, duk abun baya mata dadi, har yau bata daina son Adam ba, ga takurar rayuwa don d’an zaman da tayi da Adam tafara sabo da jin dadi yanzu kuwa harkace ta d’umamemn tuwon masara da kuka, anyi abinci mai zafi shine ayi masa da miya ko tuwon shinkafa, duk tabi tayi duhu yanzu ko sha’awar iskancinma batayi, ji take Zumah ya cuceta amma don baida kunya da suka had’u yana d’an dingisawa haka shima yake blaming dinta, sai da suka kusa fada aka rabasu, tadawo gida ranar tana kuka kamar ranta zai fita, Inno kuwa lallashinta ta shiga yi don kuskurene an riga anyishi, kaf cikin mutanenta sun watse sai kad’an mariya k’awarta ta amana itace har yau take jin tausayinta, yau tazo ta sameta a cikin gidan ta tasa shinkafa da wake gabanta tana juyawa sai hawaye take Mariyar ta shigo tace ” Abida mai yake damunki? Haba k’addara taringa fata yakamata ki daina damuwar idan ba so kike abun ya had’e miki da ciwo ba” share hawayenta tayi tace ” Wallahi har yau ina takaicin abunda yasa na ce Zuma yazo, kinsan ban taba bashi kainaba sai ranar saboda tsautsayi wai kuma nace yazo gida, in banda azal din tonon asiri nasan fa yana gari, ga zunubin hakkin mijina gana mahalicci, wallahi har yau inason komawa gidan Adam, bawan Allah nan ya mutuntani nata masa abubuwa baya cewa komi, na cuci kaina Mariya” takarasa fada tare da fashewa da kuka Mariya tace ” Hakane tabbas kun biyewa shaidan, sai dai ki godewa Allah da ta faru ranar farko don da yanzu kin cigaba dayi zunubinki na daduwa, yanzu shawarar da zan baki ki dage dayin Addua zai fi miki, sannan ki sake neman yafiyar Adam don kin cuceshi, abunda na dade ina nuna maki kidaina kenan saboda in kasaba sai kayi auran ma kazo kana bin na waje, gashi baka isa kace baka zinaba don baza’a yardaba, na tabba yanzu a idon Adam gani yake kin saba cin amanarsa bazaiyi tunanin ranar kika faraba” Sai da Mariya ta dade tana mata nasiha sannan tasa tad’an shirya suka tafi ziyara ko Abidan zata samu ta d’an ware.
Adam yana zaune a office dinsa yana chat da Babyluv masinjansa ya shigo yace masa yayi bak’uwa Adam yace ” Bak’uwa kuma? Amma da mamaki ba’a saba zuwa nemana ba, amma kace ta shigo” tana shigowa ya mik’e tsaye take annurin fuskarsa ya d’auke ya shiga nuna mata k’ofa take ta zube a gabansa tana kuka ” Don Allah kayi hak’uri ka saurareni” kuka take sosai ganin karta sa ajiyo awaje yace ” Tashi ki zauna ina jinki maza-maza ki fadi abunda yakawo ki kiyi ki tafi” jin haka taji dadi ya lullubeta da alama zata samu nasara ta tashi ta zauna tace ” Ina yini?” a dak’ile yace lafiya lou zata shiga wata gaisuwar yace ” Please ki fad’i meya kawoki in ba hakaba just get out from my office i dont have your time” jikintane ya sab’i rawa tace ” Don Allah don Annabi kayi hak’uri, sharrin shaid’anne amma har yau ina sonka” kama bakinsa yayi ransa na ci da wutar kishi da takaici tunowa yake an kai masa k’ato har gadonsa na sunna, runtse idonsa yayi ya tashi yace ” karki raina min hankaki naji kinasone what do you mean na maidaki bayan naganki kina lalata da wani? Goddamn” jikinsa sai tsuma yake har yanzu in ya tuna abun sai yaji ai bai d’au matakin daya daceba, ganin yanayinsa ta tashi ta fice da sauri don zai iya had’a mata na jaki ayanda yake jinsa, bata d’ad’e da fitaba ya shiga had’a kayansa zai bar office din she spoilt his mood, baya kaunar tuna abun don ko baka son matarka tamaka haka ta kure wulakantaka, har wani ajiyar zuciyar b’acin rai ce ke k’wace masa, gara yayi yaje gida ko Babyluv zata sauko dashi kasa, yaci sa’a ranar bata da lecture friday ce.. ..+
Yana shiga ya sameta taci wankan trouser da wani top da aka dan daure gefenta, sai dai bacci take hani’an don har ya shigo bataji shigowarsaba, k’ura mata ido yayi her innocent face is cute abunda yazo ransa kenan, yafi k’arfin minti uku yana kallonta had’e da tuno rayuwarsu na baya, juyi tuyi wanda saura k’iris ta fad’o k’asa yayi k’ok’arin gyara mata kwanciyar aikuwa ta cigaba da baccinta, d’aukarta yayi cancalak yayi bedroom da ita anan ya bud’e mini fridge dinsu ya dauko ruwa yasha, sannan ya koma kusa da ita akan gadon, cikin bacci taji ana shafa cikinta har zuwa kan marata sai kuma ayi sama zuwa k’irjinta, a hankali ta bud’e idonta suna had’a ido tayi yunk’uri tana k’ok’arin tashi ya maidata tare da k’irk’ira murmushi da take tagano fuskarshi ba walwala ya yafashi ne kawai da muryar Bacci tace ” Handsome meya faru naganka haka, kuma at this time?” sai da yaja seconds yace ” I was pissed up shiyasa na taho gida nasan zan ware da zarar naganki” murmushi tayi don taji dadin maganar tasa tace ” Who pissed you up? Who want play with my king?” ta d’aure fuska kaman irin zata iya wani abun kirki ne kama lips d’inta yayi da ta d’an turosu yace ” Dont mind na huce ai share kawai” kamo kanshi tayi da hannayenta biyu tace ” Are u sure?” gyada mata kai yayi tace ” No i dont thinks so let me check it myself” ta had’e bakinsu take kuwa ya shiga biyeta sun d’au time yana romancing d’inta inda rabi aikin tane don Khairi ta iya wasa dashi fiye da tunani shikansa a namiji bazaice ya fita iyawa ba, haka har ya ware sosai tare bacci ya kwashesu sai daf da la’asar suka tashi, shima shine yaji k’iran sallar farko ya tasheta tare da d’auko mata rigarta da suka yada ta suka yada ta gefen gado ya bata ta saka, sai bayan yadawo suka zauna cin abinci shine yayi serving d’inta aikuwa tuni ta had’e rai ” Tace Handsome wannan rowa haka, duka in na daure da 5 large help zai k’arefa pls i need more” kyalkyalewa yayi da dariya yace ” Haba Babyluv har kin raina da kin bari kin fara ci ai, in yaso anjima sai na k’ara maki” cikin turo baki ta kwace serving spoon din tace ” Daga yau na yafe maka serving kowa ya zuba ma kanshi don nima na daina zuba maka” dariya ya dingayi aikuwa ta kara sai gashi ta tashi dashi, yayi ta tsokanarta har sai da ta shiga kwallar shagwaba sannan ya kyaleta..
STORY CONTINUES BELOW
DUTSE
Jamila tun bayan ihunta tacigaba da rawar k’afa wa Ahmad agaban Saleema inda acikin dakin duk ranarta ta nuna bataso, shima kuwa ya tattara ta ya ajiye agefe don bai baro d’akin Saleema bai wareba, kuma takanyi k’okarin faranta masa koda da romance ne in yaje mata sallama abunda bata yarda shine su shiga hakkin Jamila, akwai ranar da dayazo sallamar ta lura he is in need don daga fara mashi butterfly kiss ya shige neman ta, dakyar ta samu ta banbareshi aikuwa fita yayi yana cushe don ranar rabin dare kasa bacci yayi sai salloli ya dingayi, ita kuwa Jamila ko ajikinta jira take kawai yazo wataran yana begging gwuiwa ak’asa nan tasamu ta dirza masa wulk’anci, yanzu haka anfi sati uku da hakan, yau ranar girkin tane gashi haka kurum kwana biyu takanji buk’ata sosai last kwanakinta har pretending tayi na mirginan bacci ta fad’a jikinsa amma sai ya gyara mata kwanciyar tayi hakan yafi sai hudu a daren tasan ya ganota amma ina sai ya gyara mata kwanciya ya basar da ita, sai ma ak’arshe ya jera pillows tsakaninsu yanda kota sake juyi bazata fad’o kansa ba, ranar taji takaici matuk’a dan har ciwon ciki sai da tayi, da safe tayi ta kumbure-kumbure tana tak’ular Saleema, anan Saleema take ganin ikon Allah don tunda taga haka tasamu matsala da oganne, d’aya daga cikin illar zafin kishi kenan da daukar mataki, don gashi tasa duk sanda take da matsala da mijin sai Saleema tagane saboda ranar zatayi ta janta da rigimane sai kace itace ta haddasa hakan.
Suna tafe cikin mota ita dashi sunje k’arbar result dinta bak’aramin farin ciki take ba saboda tasan zata samu kyautar Daddy d’inta, don yace matuk’ar tafita da Upper second class zai saya mata mota mai kyau, sun tsaya wani joint don sayan burger da ice cream, Ahmad yana waje ta d’auki wayarta ta bugawa Mummynta bata daga ba haka shima Daddy jan tsaki tayi, da ashagwaba ta kira ya Fahad take fad’a masa lokacinne Ahmad ya shigo ” Kaga na kira Mummy basu d’agaba duk sai naji raina ya b’aci im so eager to give them this news ashema sun manta dani” daga can yace ” Haba little taya zakice haka” tace ” In ba hakaba ya za’ai ace both of them bawanda yayi picking tunda nabar gidan aka daina sona ma” kallonta Ahmad yake yana dan dariya k’asa k’asa baisan mai Fahad yace mataba yaga kawai tayi dariya tace ” Bye.. Im missing you agaida Munib da Anty” kallonta Ahmad yayi yace ” Saleeman Daddy” ta turo baki karka k’ara tunzurani ya kyalkyale da dariya yace ” Na ja bakina nayi shiru kar a fashemin daga ratayar zomo, karshe a hanani my dinner” yak’ara sa fad’a tare da mata wani kallo itama ta narke nata idon tare da masa wani shu’umin kallo, haka suna hirar masoya sukaje gida kafinsu k’ara sa madam ta kumbura don gani tayi sun dad’e kuma har yanzu time dinta ai bai fitaba, daga yanayin ta Saleema ta karanceta so amma shes very happy yau bata da lokacin ta haurawa tayi sama, ta shiga bugawa yan uwanta na arzik’i..
Sai dare ta basu labari bayan sunsha k’orafi don tab’ara harda wani kuka “Daddy don nabar gidan duk kun daina sona ma” dake handsfree take Mummy naji ta saka dariya ” Kedai bakya girma wallahi ni da zan iyama wani zanyiwo amatsayin auta” kara ta saki “Daddy kana jin Mummy ko, aikuwa da na daina zuwa Yola kuwa, don kishine zai kasheni” ta dade suna hirarsu sun mata fatan Alkhairi sannan tasha Addua akace taje tayi shawarar model din motan da takeso in a week, aikuwa tayi ta zuba godiya, tana gama wayar Man d’in nata na gefe ya gama shigar da wasu takaddu a email, ita yake jira wani kallo ta bishi dashi ta juya takwanta yau yangar ta motsa kenan, har ya kashe komi yakwanta bata yi motsiba as in bacci take dariya yayi yace ” Baby yau kuma yanga ake sonmin” dif bata motsaba amma tana kunshe dariyarta dama rigar jikinta irin rigar baccin nan ne mai d’an fad’i kaman t-shirt dakadan ta hau kan jinyarta, saka hannunsa yayi ya shiga mata cakulkuli aciki ba shiri ta shiga zillewa tana dariya sosai don na corridor zai iya jiyowa har sai da takusa fad’owa agadon ya kyaleta cikin shagwaba tace ” Hero Zakasa ajimu awaje, kasan yau bakina is open so yanzu dariyata is too loud” yace ” Ai kece zaki d’aga min hankali while you know im in need of your.. ” bai k’arasaba ta sark’alo wuyanshi da hannunta tace ” And im very exited today, so you will have what you want plus bonus” ta kwashe da wata dariya in naugty way, wasanni suka shiga yi don tuni ya cire nightyn ta dama shi already ba riga jikinsa sai boxers dumin jikinsj na had’uwa suka shiga jin dad’in rayuwarsu sai da sukai satisfying kansu through romance, suka sake wanka sai bacci wanda kafin suyi sai da sukasha watsar da komi nakan gadon k’asa saboda fitinar Saleema at the end kan lazyman sukai baccin tana jikinshi, cikin dare ta tasheshi suka koma don kada hannunsa yayi tsami ga nauyinta, gashi yafi k’arfin lazy din zai takura.
Dama mai neman kukane aka jefeshi da kashi Ahmad irin rayuwar da yakeso kenan he want free and romantic life, donshi bai dauka zai zo yana wa mace muzurai ba he want be friends with his wife tahakane zaka ke enjoying life dinka, in kamaida matarka kamar kawarka wannan kunyar ta matan hausawa sanda zata ajiye ta gefe take faranta maka bata saniba.
Jamila tun daga kyalkyalar dariyar da Saleema tayi ta dime tashiga kuka, ta raba dare tana kuka a cewarta rashin Adalci Ahmad yake nunawa tsakaninsu, don ita kwanakin nan sai yazo yayi ta typing ko kuma yayi kwanciyarshi, ya dinga nuna baya bukata, kujifa ta manta halinta one thing da mata masu irin haukar nan kenan, kai bazaka duba mai kaiwa mutumba kai yana maka sai ka k’ule, da safe k’in saukowa tayi break dayaje sanar mata ma sai taki bud’e ido takallesa, daya isheta da tambaya sai tace kanta ke ciwo amma tasha magani anjima zata fito taci abincin, shikuwa Ahmad ganin shike da hakkin kula da ita sai daya koma sukai break ya taho mata dashi saman inda Salewma ta biyoshi dashi ababban Tray ta mata sannu, amma sai tak’i masawa take taje gano, Ahmad yace ” Sweety bakiji ana maki magana bane” Saleema tayi saurin katseshi tace ” Kasan mai ciwon kai bai fiya son maganaba, Anty Allah ya k’aro sauki” da zata fita ta d’auki Aslam don yabarta ta huta, da harara ta bita duk akan idonsa shima yagane sai ya basar, sai da ya tisa ta yaga ta fara ci yace “Na tafi school inaga late zan dawo yau, idan kina buk’atar wani abu just let me know, in kuma zuwa azahar kinji jikin yaki dadi ki kirani sai nazo nakaiki asibiti” gyada masa kai kawai tayi, yana fita ta ware ta narki abincinta
Da Azahar wasu familyn Ahmad sunzo don haka Saleema ak’asan ta yini sai k’arfe biyar suka tafi, suna tafiya Jamila da ta jima da komawa d’akinta ta sauko ta shiga yada wa Saleema bak’aken maganganu tace ” Idan ma baka kikaje kikaiwa mijina Wallahi kwanan nan kaikayi zai koma kan mashekiya” murmushi kawai tayi tacigaba da danne-danne awayarta suna magana da Khairi ne, ganin taki biyeta Jamila ta d’au waya ta shiga habaici as tana hira da watane dariyace ta kwacewa Saleema, kuma Jamilan ta bata tausayi saboda furucin da tayi kan baka yasa tagano tana nufin yanzu Ahmad bai nemanta wanda gaskiya bai daceba, yakamata ya sauke hakkinta, gashi har awayar tana maganar wata an hana mijinta kusantar ta bayan tasan da bai gajiya da ita, murmushi kurum tayi tana ayyanawa aranta ” Tabbas Jamila bata da wayo, koda asirin ake kya bari mutum yasan yayi aiki” haurawa Sama tayi ganin magriba takusa kuma sunyi waya dashi yace mata kila yayi sallar isha’i agida ko yashigo bayan yayita a masjid..
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad *@jannahjay8*
© 2019
49
Sai da tayi salla ta sake wanka ta shirya kanta cikin silver english gown tayi turban mai kyau, tana fitowa taga Aslam yana yawonshi a corridor da tsaiwarshi wadda batai k’arfiba yanayi yana fad’uwa, duk ya b’ata kayansa komawa tayi ta masa wankan dake lokuta da dama in ta daukoshi tamasa wanka wanda ta cire masa hadawa take da undies dinta ta wanke a washing machine dinta don haka akwai kayansa adakin, bata buk’atar zuwa balle yau taga matar akusa take, tasaka mashi ta hada masa tea ta bashi, bai jimaba yayi bacci tana zaune tana zikiri da counter taji shigowarsa lokacin ana kan kiran sallar Isha’i na farko, da hanzarinta ta sauka k’asa sai da ya shigo falo ta tareshi inda ya d’an saukar mata da nauyinsa ya furta wash da dariya afuskarsa tace ” Sanne Hero yau duk an wahalar min dakai baka ga yanda ka komaba” lokacinne yaga hakimar zaune ya kalleta yace ” Sweety ya k’arfin jikinki? Im sorry i was busy da rana shiyasa ban kara kiranki naji ya kike ba” dakyar ta amsa tace ” Da sauki” wai don ba ranar ta bane sannu da zuwan ma sai taga daman yi, suna k’okarin hawa stairs da Saleema yake cewa ” Ina jinki ya nakoma? ” ta kwashe da dariya tace ” Tab ai yanzu in ba nida maman Aslma ba bamai sayanka naira hamsin” kama baki yayi yace ” Eyye lallai zan kamakine yarinya” ta dinga dariya tace ” Zaka shiga toilet ka gani, duk shatan birone inaga akumatunka” ta had’a mashi ruwa yana shiga tana k’ok’arin fita ya ruk’ota ya sunkuya kan kafad’unta inda taji nauyinshi yace ” please na gaji sosai fa dak’yar nake daga hannuna can you wash me up” zaro ido tayi tace ” Sorry sir” ya dungure kanta yana dariya usually haka take masa in ranar tanso tanuna taji kunyarshi sai ta kirashi da sunan da suke fadamasa a school… +
Su Sayyid sun samu aiki a Norhwest lecturing tunda dama dukansu sunyi masters ne kafin dawowarsu, an musu hanya duk da suna kan service ne sai yazamanto suna service a Northwest din, Soyayyar Hafiz da Umaima sai habaka take don su Alhaji Abdullahi sun je nema masa kuma har anyi alk’awari, jira ake tak’arashe karatunta ad’aura in yaso ta d’ora degree din ad’akinta, Khairi taji dadi ko bakomi Umaiman zata dawo kano atleast ta samu wani a yan uwan Umminta akusa.
Bangaren Khadija Alhamdulillah tayi amfani da shawarar kuma yanzu tana samun sauki, takan jure shima kuma yanzu ya fara sauyawa don in taga hadi mai amfani agroup daya danganci kayan naturar ko herbals takan musu, don yaka yanzu Alhamdulillah sai da takira Khairi ta mata godiya tace mata bakomi ai haka shine zumunci.
Yau Saleema ta shirya tarar Ahmad da maganar Jamila, tun safe take nuk’u-nuk’u tazauna ta auna ta rasa ta ina zata fara, yanzu haka yana gabatane yana cin fried egg da mint tea, ta k’urawa k’asa ido ya dan zungreta yace ” Baby wai meke faruwa dakene yau? Duk kina ta tunani fadamin waye ya tab’a min ke?” ta nunashi da bakinta da ta turo yace ” Ni? lallai i must punish myself ya za’ai na batawa ruhie rai my oxygen and water” sai tayi yar dariya tace ” Ai daga yau in dai baka canzaba na daina kulaka ma, kuma ba ruwana munyi baran-baran” ta karasa da sigar da yara kanyi na shagwaba yace “Cewa zakiyi kinaso na koma mad man don in kika b’ata dani nabi ina naga haske” dariya tayi kawai yagama ci yanzu ta tashi ta kwashe komi, zuwa yayi ya wanke bakinsa kafin nan ita tadanyi chewing mentos bubble gum, zama yayi kan kujera dake suna falonta ya janyota yana cewa ” Tell me im ready to apologize” sunkuyar da kanta tayi tana murza yatsansa na d’ayan hannunshi dake ajiye ” Tace kayi hak’uri zan maka shishshigi tsakaninka da matarka, amma gani nayi wannan shine zaman tare, bazan so Allah ya kamaka da laifi ba kuma bazan ji dadi ka take hakkin taba don nima zan sawa raina wataran zakamin hakan ko fiye, kada kamata ba iya ci bane hakkinta kurum don me zaka daina had’a shimfida da ita? Duk girman laifin da tamaka kasan Allah bazai barkaba, domin zamanka take wazai dauke mata kewa?” ransa ne ya shiga baci kuma gefe daya yasan gaskiya ta fad’a amma ai batasan me ta masaba yace ” Waya ce miki hakan, ni nace maki bani yi? ” tace ” Please dont pretend wallahi bakayi, infact nagane bakwa shiri baka damuwa da ita kwana biyu shes too silent and she seems lose ka duba lamarin nan, bai kamata ka biyeta ba komi ta maka kasan matsayinta a wurinka, don Allah ka shirya don naga alamun nadamar komene ta maka tunda gashi tana shiga damuwa akan watsar da ita da kayi” duk ta marairaice shiru yayi yana nazari sai kuma ya tashi tsaye, addini ne ya bawa miji damar k’auracewa matarsa in ta fara masa hakan na wani lokaci, amma bakomi shikansa ya lura Jamilan tayi sanyi don ko jiya sai da yaji tausayin ta ganin yanda ta zama ba kuzari ba wani falli, ita kuma Saleema ganin haka sai tayi tunanin ransa ne ya b’ace, take taji wani iri na shiga abunda ba ruwanka tace ” Hero idan ranka ya b’aci don Allah ka yafemin” idonta har ya fara kawo k’walla, zuwa yayi ya zauna tare da had’ata da jikinsa ” Ko d’aya bawai raina ne ya b’aciba, ina nazarine akan maganganun ki kuma insha Allah zan duba zan san me zanyi nan gaba” murmushi tayi tace ” Yawwa nagode” kuka ne ya nemi k’wace mata da sauri ta ruga zuwa d’akinta ta fad’a gado tadinga kuka ” Yau itace sai wata ta saka baki tsakanin ta da mijinta? Lallai ta yi kuskure tabar damarta don gashi tana zaune wata tafita matsayi da sanin shawo kan Ahmad, wanda ta rigata saninshi da komi akansa, ji yanda take masa kalami da ladabi, ashe shiyasa kowa yanzu adangi yasan Ahmad yafison Saleema sai dai in baka mallaki hankalinka ba” ranar tayi kuka tayi nadamar abunda take bata k’ara shiga tunani ba sai da ta k’ira Samira tana d’agawa tace ” Kawa wannan kira haka da dare, gashi ina shirin zuwa wajan oga ne inaga sai gobe gaskiya mayi maganar dama ina son shigowa” bata jira amsarta ba ta kashe wayar, ashe itace sakarya takasa jure komi sabida son jikinta, ita kanta tasan tasha bak’antawa Ahmad yana jurewa don ba wadda batasan hana miji hakkinsa laifine mai girma, koda kuwa mutum baida ilmi addini sosai.. ..
STORY CONTINUES BELOW
Washegari k’alau suka fito cikin shigarsu mai kyau, bayan sun zauna kan Table sai gata ta fito suka gaisa a mutumce , don da Aslam yake mik’owa Saleema hannu dakanta ta mik’a matashi tana dan murmushi, hakan ya musu dadi sai dai Ahmad yana tamke yake kaman yanda ya ke mata a kwanakin, idan suna hira tasa baki sai yayi maganar da zaisa zancen ya k’are, haka yagama cin Abincin yazo fita tace ” Abban Aslma don Allah ina so naje gida” bai juyoba yace ” A’a ba yau ba” ya d’auka zata tsaya musu yaji tace ” Shikenan, adawo lafiya” Saleema tabishi zuwa parking lot..
Ranar har ‘yar hirace ta shiga tsakaninsu a falo, don ta lura Saleema bata da mugun nufi kanta tunda ta tabbata jiya badan ganin ido ba, don zata iya rantsewa basu san ta musu lab’e ba, gaskiya abun ya isheta ace kusan wata biyu kaida miji sai kallo don a falo yake kwana ranarta yabar mata d’akin, tayi rokom tun rannan ya basar dama yace zata gani gashi nan kuwa anzo ita ke nemansa, banda gaisuwa ba abunda yake had’asu sai dai in yaje dakinta yayi ta wasa da Aslma abunshi, ko abu zai saya masa sai dai taga yazo dashi, daga ranar tafara sassautawa Saleema shikuwa Ahamd yana lura da hakan sai asannan yafara shirin saukowa.. …
Har ta shirya zata school aka ce mata an d’aga lecture sai gobe aikuwa taji dadi matuk’a ta samu tad’an huta ma balle tayi nauyi yanzu sosai duka lokacin goma bata yiba, doguwar rigace bubu ajikinta na cotton material kishingida kurum tayi, ta turama Adam text yamata reply tana dariya taji ana knocking, bayan ta b’ude wazata gani Abida, ta k’oje ta k’orame bakyan gani, har falo ta kawota ta kawo mata abun motsa baki sannan suka shiga gaisawa, Abida ta fad’a mata tazo neman yafiyar Adam ne taje office bai saurareta ba, tace “Rayuwata taki fari jinake hakkinsa ke bina, don haka ko zaki saka baki nasan zaiji maganarki” takarasa tana kuka tace ” Karkiji komi insha Allah zan yi iyakar k’ok’arina kinji, ki share hawayenki” tashi tayi zata tafi Khairi tace ta tsaya, ta shiga kitchen tad’an had’o mata abubuwa sannan taje daki ta d’auko mata atamfa igbo wraffer haka da wata doguwar rigarta bak’a da mayafi, don kayan jikin Abidan duk a mace tana fitowa da leda a hannunta da kudi dubu 3 ta mik’a mata take ta zube tana godiya, Adam da yayi mantuwa ya dawo daukar wata folder a waje yayi parking motarshi kuma yana da key kawai bude gidan yayi, Sallama kurum sukaji ya kallesu gaba d’ayansu yace ” Ke!! Me kike min agida? Eyye!!! ” take jikinta ya sab’i rawa, da sauri ya shiga d’akinsa ya d’auko belt lokacin tana farfajiyar gidan takusa isa gate ya bita itama Khairi ta d’oru a bayansa, ta rikeshi tamau yana k’ok’arin tureta ta d’an saki nishi dole ya juya ya rik’eta a haka Abida ta ruga waje, tare suka koma ciki ransa a b’ace ya shige d’aki ta bishi ” please ki kyaleni, don me zaki bar ta ta shigomin gida bakisan tarwatsamin farin ciki takeba” cikin sigar lallami tace ” Dama ai tazo baka hak’urine, saboda tayi nadama” fad’a ya shigayi da alama bacin rai ya rufe masa ido duk ya birkice mata, zata iya cewa tyn bayan dawowarta bata taba gainsa a irin wannan yanayin ba kurum sai ta saki kuka ” Kayi hakuri don Allah gani take kaman ina da matsayi awurinka da zan fadi sakonta, tinda kaki sauraranta a office amma tunda duk d’aya muke shikenan” duk da ransa hauhawa yake dole ya fara kokarin saita kansa ya rungumota ” Babyluv kamar ya matsayinku daya? Ya zakike b’ata min ranki a kanta har kina kuka? Please kidaina” turo baki tayi ” Kaine kake ta fad’a kana hayaniya baby ma sai juyi yake bai saba ji ba duk ya tsorata” dariya yayi ya shafa cikinta ya sunkuya ” Baby daddy is sorry bazan karawa Mum dinka hayaniya ba kaji” ganin ya nutsu ta shiga lallaminsa adadi tana nuna masa irin nasihar da yamata kan yafiya da afuwa yace ” Shikenan na yafe mata banson tana zuwan min gidane, ina tuna abun ” tace ” Shikenan bazatake zuwaba, tana bukatar taimako zanje gidansu sai na sanar mata ka yafe mata, wallahi duk taban tausayi” shidai bason maganar yakeba da tagane hakan yace ” Shikenan zan barki kije amma, ku mata dake kun fiya tausayine” tace ” Nagode” ta masa kiss akan eyes d’inshi, yace ” Okk kin taro rigima kuwa” tana dariya tana zillewa shiko ya ruk’ota yace ” Ki k’arasa abunda kika fara” sai da ya yamutsata sannan ya gyaramata kwanciya kan gado ya dau folder ya fita..
An kawowa Saleema motarta Corolla L.E golden colour zokaga murna wurinta, duk su Nucy amaryar next month sun taya ta murna, Ahmad haka yayita tsokanarta wai basaban ba don ranar bakinta yaki rufuwa motsi kadan sai taje ta bude motar.Sai da Saleema tasamu week ta na lallamin Ahmad ya sauko yace ya yarda har sai da ta masa kuka akan hakan ta fara masa fushi harda kin biyeshi wani dare sannan ya yarda zasu shirya da Jam, yau dake ranar Jamilar ne sai ya fara waremata hakan yamata dad’i tayi komi d’inta anutse, da dare bayan sun gama shirin bacci ta tsugunna har k’asa ta nemi yafiyarsa, anan yamata nasiha tace ” Insha Allah bazata k’araba sharrin shaidan ne da son jiki da k’iwa” a ranar sunsha soyayya don Ahmad don kanshi ya kyaleta to itama kanta a bukace take..
Da safe tayi kwalliyarta da girki mai kyau, koda Ahmad zai fita ta rakashi bayan ta dawo ta samu Saleema suka shiga hirar series da suka gani jiya da dare tace ” Saleema nagode da taimakon da kikamin, inda ace kowa gaka yake samun kishiya da an zauna lafiya aduniyar nan” tace ” Taimako kuma Anty name?” murmushi Jamila tayi tace “Nasan ke kika shiryamu nida Ahmad, duk da inada yakinin bai gayamaki laifin da nama saba don namasa shedar hakan, kuma kema nasan ba bin diddigi bane, nagode sosai ” tace “Karkiji komi yiwa kaine don duk mai hankali basataso taga gemun yar uwarta na ci da wutaba, kai kanka kasan baka wuce abin yazo maka ba, lamarin maza sai hak’uri Anty dole kajure abubuwa da dama, duk yanda mace takai ga Salonta wataran sai an samu sab’ani bazakace wai iya sex ko girki ko biyayya zaisa wataran bazaku b’ata dashiba, sudai kawai abubuwane da zasusa ka shiga ran mutum sosai ta yanda ko rikicine yazo muku zai zo muku da sauk’i, kuma kinga maza ke saman mu dole wani lokacin ko bama son wani abu mu daure muyi masu kodan gudun fadawa fushin ubangiji” maganganun Saleema sun shigeta sun dade suna hirar duniya da halin maza da rayuwar auran ma kanta, koda ya dawo ya lura gidan nasa an fara shiri sosai yaji dad’i.
Cikin dare nak’uda ta turnuk’e Khairi don tun tana daurewa sai da takai ta tashi Adam tana kuka, agigice ya sauko ita already tana durk’ushe a k’asa ya rungumeta rik’eshi tayi gam tana kuka tana cewa ya yafemata mutuwa zatai, tuni ya gigice ya fita ya kunna mota ya bud’e gate, ya dawo ya zira mata hijab sai Asibiti, da alama bak’aramar wahala take shaba, suna zuwa akwai maternity da ita….
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 2019
50 🔚
Bak’aramar wahala tashaba sai dai Alhmdlh asbubar fari ta sauka tasamu d’a namiji sak mahaifinsa farine dai bai kai na Adam ba, fad’in farin cikin da family suka shiga kaman b’ata bakine, kafin gari ya waye har sunzo inda aka tafi da ita gidansu Adam nan dai inda tayi jegonta na farko, yan uwa da abokan arziki sai b’ulb’ulowa suke ga yan Asibiti, tana ganin tarairaya awajan ogan, alokacinne kuma ta dage da cin farfesu da su nono da zuma mai dumi, sam bata k’i gashin da ake yiba takan hau garwashi again shima don gyara, shikuwa Adam kusan kullum sai an koreshi ahakan ma cikin dare zai k’irata awaya sai bacci ya saceta yake k’yaleta, kullum sai yazo da safe kafin ya wuce office, soyayyar da Adam kewa babyn ko ita Khairi albarka don cewa yayi sai anyi suna special yanda yarasa baby sau biyun nan dole ya godewa Allah..+
Ahmad yayi alk’awarin kawo matansa suna aikuwa haka akai suna yakama ranar Asabar ya taho dasu da safe, inda aka tsara wuri mai kyau Khairi tafito tas acikin lace mai azabar kyau shima baby an masa kwalliya cikin kaya Navy blue masu kyau, yaci sunan baban Khairi Aliyu kenan, an ci ansha hatta su Safiyya da Khadija kwalliya sukai na kece raini, can na hango su Maryam tafida da matan su Sabeer da Ak don sune yan rabon suverniors, Jamila da Saleema kuwa bazakace kishiyoyi bane don Ankon wani paper lace sukai da Ahmad ya musu tare, sunyi tsaf abun dai ya k’ayatar sai wanda yagani, sai dare suka keb’e dasu Saleema inda zaman nasu rabi na karuwane daga Khairi, lokacinne kuma Jamila tak’ara ganin haukar da tayi abaya, adaren suka koma dutse don sai past 9 suka isa gida…
Duk wani gyara daya dace mace tayi wanda bana cushe-cushen haukaba Khairi nayi, yanzu tasamu kimanin Sati uku da haihuwa, Adam yagaji soyake ta dawo ya rasa yanda za’ayi ya tari Mama da maganar, in yazo yana mutsu-mutsu yanason mata magana sai ta kawar kuma tagane inda ya nufa, kamar yanda yanzu ya sabarwa kansa cikin dare in yakasa bacci haka zaisa Khairi ta tashi ta kunna data suyi ta vedio call, yauma hakan takasance tana baccinta mai dad’i taji vibration na wayarta dole ta tashi bata damu da taga waye ba don tasan oganne, muryarshi cike da damuwa yace ta kunna datar ta, bayan ta kunna ya ajiye wayar yana jingine yana kallonta yace “Wai Babyluv don Allah bakya tausayina ne? Nikad’ai nake haukana ma kenan baki damu kidawo gidaba”murmushi tayi tace ” Kaima kasan nima nayi missing dinka, ba yanda zanyine” jan tsaki yayi yace ” Ba yanda zakiyi fa kika ce? Haba sai dai in bakiyi niyyaba wallahi” tace ” To me kake so nace? Naje nace musu zan tafi ko ya?” yace ” To in kince hakan laifine ko sab’o?” tace ” Nidai gaskiya bazan iyaba” fushi yayi ya kashe wayarsa ita kuwa takoma baccinta, washegari da yazo yaje ya tunkari Mama tace sai tayi kwana talatin da biyar ko talatin duk yanda tagani, haka ya zungumi baki ko naiman Khairi baiyiba ya fice, ita kuwa da tana jinsu da Mama ta dinga dariya…
Bayan kwana biyu da hakan ya je yasanarwa iyayen mazan kan ko zasu bada baki bako kunya, aikuwa take Abban Khairi ya saka baki dan sawa yayi aka kira Mama, bayan wasu mintuna sai gata ta shigo d’akin da Khairi take tasan yana nan ta sa hannu harda masa dundu tace ” Rasa kunya harda kai k’arata ko? To jibi kazo ka kaita yawan dangi sannan washegari kuje Jahun da ita sai ku tattara ku kama hanya ku tafi gidanku” dariya ce ta tasowa Khairi na dundun da aka masa sai da Mama tafita ta kwashe da dariya harda rik’e ciki b’ata rai yayi yace ” Au dariya ma kike ko? Ai koma meye akanki akamin kuma sai na fanshe kayana” Hakan kuwa akai sai da suka zaga dangi taje Jahun tadan lalleka dakema wasu sunzo mata suna don haka sunje Dutse wajan Saleema, bayan dawowarsu daga Jahun an gama mata shirin komi sai komawa gidansu..
*DUTSE*
Ba laifi yanzu gidan Ahmad ana zaman lafiya, kuma yakan sakewa Jamila duk da bata isa kamo Saleema fagen kula dashiba da sanin makamar miji, don Saleema kilibibin ta ya isa da sanin salon jan ragamar miji, zaune suke gaba d’ayansu suna kallo Baby Aslam sai gwalangwalantun sa yake ak’asa su suna kallon wani movie, abun gwanin sha’awa dake yana d’akin Saleema ne tana daga gefenshi gefen cinyarta na jikinshi, sai da tasbihi Jamila tasamu kishin daya taso mata ya kwanta don bazaka raba mutum da kishi ba, ita kuwa Saleema bata daukar hakan a komiba saboda ai mijintane da dai bata dakinsane bazatayi hakan ba, yanayin rayuwar gidansune yasa bata jin komi dom Mummy ko agabansu tana iya yin haka akusa da Daddy tsarin turai ne su, shiyasa take da salon abu dayawa, sai anyi abun dariya zakaga da wani salo tayi lu jikinsa irin dariyar nan taci k’arfinta sai kaga shikuma yana d’an tuttureta da salon wasa yana cewa ” Kwanan nan za’aji kashina ya goce, duk kinvi kin takurawa jikina” da salonta ta kalleshi ashagwaba tace ” Yanzu kaman ni har na isa karya maka k’ashi Hero nikarka had’ani da Ummu gaskiya” itakam Jamila tashi tayi ta d’auki Aslam asunan zata je ta gyara masa jiki don dare ya fara yi ta musu sallama, kaman jira yake tabar wajan yad’an kishingida kan couch d’in ya birkitota samanshi gaba d’aya yace ” Kwana biyu so kike kidinga overact ko?” zaro ido tayi tace ” Kaman ya kenan? i thought this is normal things that each one of us can do” yana lasan gefen kunnanta yana cewa “No.. No kawai ki rage karki ballo mana rigima i know My Woman in ke kishinki baije kaman nata ba ita tanaji, beside in sona baida yawa aranki kaman nata baza kike jiba amma ita ina ganin kaman mood dinta na canzawa, kuma banga laifintaba arage please Baby in mukadai ne you can do morethan this” shiru tayi tana nazari sai kuma tayi dariya gaskiyar shine amma tani wani kishi ya taso mata har yana ikirarin Jamila tafisonshi wato ma yafi shaidanta kanta, amma sai ta dake (barikin iya takun rayuwa kenan) tace ” Insha Allah Hero zan kiyaye, dama hakane kowa da yanayinshi kaga” amma daga baya sai daga baya suna other room bayan sunagama shan love take mashi mitan ashagwaba ” Yanzu Hero baka yarda da son da nake maka ba ko?” yace ” Yaushe nafadi hakan? ” tace ” Dazu mana kace ma bana sonka fa” yace ” Niba haka nake nufiba, dama don naji me zakice ne amma nasan kina sona just nasan harda yanayin rayuwarki yasa kika dauka bakomi bane, kuma kinga so shine silar kishi kila nata yafi naki dats why bata iya controlling kaman ke” ya karasa da sigar zolaya sai tashiga kukan tab’ara tace ” Kawai nasan ni na sameta sannan nasan kuna shiga other room ma meyasa dan tana shige maka afalo zan damu kaina, amma kasan ina da kishi just ina mantaining ne” Dariya yayi yace ” Is that so? ” sai ta hau tureshi “Tunda baka yarda bama bari na tafi dakina” ta mik’e da gayya tayi hakan don kuwa tasan yakanso ganinta da bra and pant ta mik’e tsaye ta janyo rigarta dake gefe wai zata tafi dakinta adaren, aikuwa tuni ya sauko ya rungumota ta baya yana lallashi daga baya ta koma sukai baccinsu.
STORY CONTINUES BELOW
Adam a nasa tunanin dawowarta zaisa ta ware masa amma ina sai yan kame-kame take yau kwananta uku da dawowa ya kama tayo kwana 35 kenan, har tagama shirin baccinta ta kai baby gadon shi ta kwanta sai gashi ya fito daga toilet yazo ya sameta ya kira sunanta “Babyluv nasan kina jina kullum sai kiyi pretending din bacci ko? Nasan kinjima da fara sallah tun kina gida shine kika zabi kiyi ta wahalar dani” maganganu ya dinga mata masu shiga jiki tace ” Handsome kawai tausayin Asad nake ji, banaso musama mashi kani da wuri” yace ” Insha Allah ba abunda zai faru, kinsan wallahi na daure sosai kiduba ki gani man, kodan dama nikadai ke haukana” rufe mashi baki tayi tace ” Ko d’aya nikaina kasan nayi missing din ka ko? Just ina daurewa ne amma im really in need of you” tana fad’an haka yaga ta sauko tuni ya shiga shafata azafi zafi itama kuwa ta shiga maida masa martani sun jima suna ririta juna da romancing tako’ina jikinsu ke had’uwa sai da suka tabbatar kowannensu ya taho hanya sannan suka raya darensu, tun bayan daren dawowarta zai ce bai kara samun dare mai nutswa irin wannan ba don dayagama yana kwance jikinta tana shafa masa bayansa ahankali sai hirar soyayya suke, iyakar nutsuwa ya samu sai yajita ta sake zama ta daban, yayi zaton zaijita abud’e sosai amma ina taci abu masu ni’ima natural sai yaji tayi tastesosai.. Haka zamansu ya cigaba da wakana cikin farin ciki
Bayan wata d’aya suka shiga bikin Umaima da Hafiz, shikuwa Sayyid yasamu wata Nafisa yar wajan Kawunsa na kura suma ansaka rana saura watanni 6,anso hadawa amma ita yarinyar ana jiran takarasa wani course ne a Uni gwag.
Bayan Shekara Uku
Abubuwa da dama sun faru masu dad’i da marasa dadi, Yanzu Khairi takusa gama karatunta, Safiyya ta kara haihuwa Namiji ne Abdullah suna kiransa Fadal, sai Khadija ita ma namijin ne Umarfaruq, Umaima da Nafisa duk sun haihu suma, kowa ya samu cigaba daidai gwargwado aduk sanda matsala ta tasowa wani haka zakaga an had’a kai an masa maganinta
Yanzu yaran Jamila biyu bayan Aslam ta haifi Juwairiyya sunan mahaifiyarta ne suna kiranta Yasmin, abunda ya bawa Jamila mamaki yanda har yanzu Saleema bata da ciki amma darajarta nan nan wajan Ahmad, sai ta tuna sanda ta gigice tana ganin kaman haihuwane darajar, yanzu Jamila in taga wata na hauka ko nawa miji komi yanda taga dama sai kaga tana dariya karshe sai ta mata nasiha.
Abida ta auri wani mai mata biyu ba laifi tana cikin rufin asiri sai dai ina har yau tana kewar gidan Adam, shikuwa zuma k’auyensu ya koma aka aura masa wata cousin dinshi ya cigaba da sana’arsa na saida fruits.
Tagama komi na abinci da tarar maigida, nufar hut dinsu Saleema tayi ta tafi da Smothie dinta tana d’an jin music tana shan kayanta, shikuwa Ahmad dawowarshi kenan daga dubiyar wani collegue d’insa ya duba bata room shine ya taho, daga nesa yake hango bakinta na bin wak’ar wanda yasha gloss sai sheki yake, murmushi ne ya k’wace masa ya taho wajan har yazo inda take bata san yazoba, don kaman ta d’an tafi wani tunani ne, sai da ya shafa wuyanta sannan ta dawo hankalinta yace ” Baby meye yake damunki?” cikin salonta tace ” kwana biyun nan gaba d’aya bana jin dad’ine, lokuta da dama sai nagama cin abinci sai zuciyata ta tsiri tashi kuma most of time ina zama moody ne” hannunta cikin nasa yace ” Tabbas na lura da hakan, inaga yakamata muje asibiti a duba min ke, don bazan iya ganganci da lafiyarkiba” Murmushi tayi tace “Thanks” d’auke mata smothie d’in yayi ya shanye sauran ciki tuni tasaka rikici akan sai ya biyata da dan gudu ya fito daga Hut din ta biyoshi bai saniba yayi tuntub’e da interlock dake gefegefen grasses din wajan tuni ya fad’a cikin grass din dake kewaye da medium flowers, itama sai gata samanshi tana kama bakinshi wai sai ta cijeshi, yana dariya ganin tasa hannunta ta kamo lips dinshi yayi saurin juyata takoma k’asan sa ya k’ura mata ido, itama k’ureshi tayi da idon suna kallon juna cike da shauk’i had’e bakinsu yayi inda tuni ta cafke har sai dakyar ya kwace, ya kalleta yace ” You changed” tace ” Kaman ya? ” ya kai hannunsa saman kirjinta ya latsa yace ” Bakiga yanda kika kara girma bane kad’an, nikinsan zan gane don nasan kayana” ya k’arasa tare da manne mata ido kai mashi dukan wasa tayi ak’wanji tace ” Allah ni banganiba, kai dai kanaso kace na fara zama lukuta kaikuma bakaso” dariya yayi ya tasheta ya gyara mata zama ajikinsa yace ” Seriously amma shikenan ai gobe zamu Asibiti adubaki, kan nausea din nan zamuji komi” daga saman balcony tana ganinsu take taji wani iri amma dasauri tabar wajan, bataji haushinsuba sai ma jinjinawa Saleema da tayi, tace tasan tariga tayi nisa ta dade da gano Ahmad is romantic person anma tahanashi komi gashi anzo an maidata yar kallo, dole itama tadage Addua tayiwa kanta kan Allah yasa ta dage itama take kwatantawa..
An duba Saleema wanda sakamako ya nuna tana dauke da cikin wata uku ba sati d’aya, zokaga murna aikuwa sai ta shiga matso kwalla wai tsoron nakuda kuma gashi tanason cikin, motsi kadan sai ta shafa cikinta tayi murmushi, ranar ne Mummy ta tace an kusa arage shagwaba tunda kin kusa fara ajiye yaranki..
Bayan Shekara Biyu
Zumuncinsu Adam da Ahmad yayi k’arfi sosai, don haka Saleema sun kara shakuwa da Khairii, Su Saleema an haifi Baby Boy sunan Daddy d’in Ibraheem khaleel, Jamila nada yara uku kuma lafiya lou suke zamansu, sai dan abunda ba’a rasaba na zaman tare, shima Ahmad yana iyakar k’ok’arinshi na ganin ya yi Adalci tsakaninsu, ita yanzu Saleemabayan service tana aiki a Gunduma health system ne, Jamila na Online bussiness, har zuwa yanzu Saleema bata bar soyewarta ba don da ta sallami yaro zata tafi other room dinta, inda zata faranta masa karshe ta bude fagen shagwaba tana shigemasa jiki shikuma ya biya kudin wanka ya shiga tarairairayarta, kaman koyaushe yauma sai da tagama bajintarta don batama so bane dolene ta daure saboda ya kawo mata bukatarsa, sai da suka sake wanka suka kwanta ya shiga shi mata albarka yace yasan shes not in the mood amma ta fifita farin cikinsa, tace daman shine zama mace don ke din wurin jinginar mijinkice da yaranki dole kidau nauyin abubuwa dayawa, had’e bakinsu yayi sai da ya saki tace ” Wait ina da wani new update” cikin jin dadi yace meye tace ” kai dai in nace kayi abu kurum kayi, tace kwanta” ya kwanta.. Bangano update din meye ba….
Khairi tuni ta gama degree dinta don yanzu takoma kan aiki, ta haifi Nana hafsa bayan grad dinta, tana zaune tana reaserch a system dinta, Adam da baijima da fita k’ofar gidaba ya dawo ya kwanta yafi minti biyar yayi lamo yana jiran tazo don tasan ita yake jira amma shiru, zuwa yayi har d’akinta ya kalleta yace ” Babyluv yau ko kina strike ne?” dariya tayi tace ” Im coming Handsome just give me 3 minutes would join you My Zamzam” dariya yayi yace ” nak’i bazan tafi ba nasan sai kikai 10 minutes” aikuwa haka yajirata tagama ya d’aukota sai other room, tundaga k’ofa ya jinginata jikin bango ya shiga lalubarta adaddafe suka kai kan gado inda ya mintsini wuyarta kad’an ta saki karar shagwaba yace ” Wa kikewa yanga kwana biyun nan? Wai tun da kika dawo daga seminar kaman kwana ukun da kikai can cire maki sona akai kike jamin rai ko? ” tace ” Ayya bawani yanga fa Handsome”ya k’ara saka hannunsa da salon mintsini ya rik’e wuyar yace ” Zaki k’ara” tana wani gantsarewa kaman tana jin zafi ta shiga cewa” nadaina nadaina” kallon yanda k’irjinta keyi yake kawai, sannan ya saketa yana dariya suka shiga kissing junansu, sai da suka nutsu sannan ya rungumeta yana mata susa gashinta dake watse kan pillow tace ” Handsome Albishir” yace ” Goro” tace ” Im six weeks pregnant” tashi yayi yace ” Are you serious?” ta kama hannunshi ” Yes serious, yau an dubani a asibiti” take ya shiga hamdala ya rungumota ” Allah yamaki Albarka Babyluv Allah ya inganta ya raba lafiya” ya sake rungumeta hannun shi na shafar saman mararta akunnenta ya shiga mata rad’a yana mata wani salon licking… To sai dai muce Khairi Allah ya inganta…
Tammat bi hamdullah Allah yasa mu amfana daga darasin dake cikin littafin nan kuskuren da nayi Allah ya yafe mani… Kad’au mai amfani kawatsar da mara amfani
*Godiya ba iyaka ga masoyana da duk wanda ya bibiyi littafin namijin kishi, bazan manta da masu comment ba i really appriciate it don ko comment d’aya kayi wallahi yana kara sani jin yin typing, tabbas kun taka rawar gani don kun kara sawa dream dina yana yin gaba Nagode sosai Jazakumullah bilkhair, da masu voting da masu godiya duk kuna ciki, duk wanda yake comment yasa aransa Namijin kishi nakune don nayi dedicating dinsa ga masoya masu kara mana karfin gwuiwa, abunda wasu readers basu saniba Wallahi comment yana kara mana k’arfin gwuiwa ko tanx kikace in akai posting muna jin dadi, balle kuma in kikai comment kan page sai muji kawai mun cire kiwar typing saboda wani ya nuna farin cikinsa, nagode nagode masu Addua kuma nagode sosai Allah sadamu da Alkhairi*
*Taku Firdausi S Ahmad JannahJay*