NANNY CHAPTER C KARSHE
Riƙe ƙugu Tahir yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya, gefe Ɗaya kuma Zuciyarsa na Gudu Sosai Saboda Damuwa, Ashe ce Dake gefe Ta ƙarasa Kusa da Goggo Abu Ta Zauna Kusa da Ita Kafin Tace “Goggo…”+
Ta faɗa Tana kallonta Innaro Dake Tsaye Ta Ɗora Hannu Bisa Haɓa Tana Faɗin “Wai Hakimi meke Damunshi ne..?Tunda nake Dashi ban taɓa ganin yayi irin Wannan Fushin ba..” Tahir ya waigo ya Fara Taku Zuwa Kusa da Goggo Yana Faɗin “Ranshi yana ɓace…Dole a saurara mai Har ya Sauko Da kanshi..”
Ya faɗa yana Zama gefen Ashe, Dayan Hannun ya kama yana Faɗin “Goggo Don Allah Kiyi Haƙuri kibar kukan nan Haka nan Nayi miki alƙawarin Komai zai Daidaita Insha Allahu…” Ya faɗa yana Kallonta Goggo Ta Murmusa Tana kallon Tahir da Ashe kafin tace “Bakomai…Allah yayi muku albarka Ku Tashi ku Tafi kubi Umarnin Mahaifinku..” Ta faɗa Tana ƙoƙarin Ɓoye Hawayen Da Suka Taru acikin ƙwayan Idanuwanta.
Innaro ta saki Numfashi Tana Faɗin “Shine kawai magana Don Rashin Tafiyar Naku ma Matsala ne, ku Tashi ku Tafi Insha Allah komai zai zo da Sauƙi, maganar Mufeeda kuma Iya ta Dinga Kula da Ita Saboda yarinya ce..ko Goggo ya kika gani..?” Hannunta Ta zare cikin na Tahir kafin ta saka Hannun ta Share Ƙwallarta Tana Faɗin “Eh Hakan ma yayi Innaro, Allah ya Sauketa lafiya kabiya ka gaida Fuleran karka manta..”
Gyaɗa kai yayi kafin yace “Insha Allahu..” Har ya Miƙe Innaro Tace “Ya ita Faridan…? Ina Fatan ba Wata matsala…?” Jinjina kai Yayi kafin yace “Eh Innaro ba Wata Matsala…”
Sauke Numfashi Tayi kafin tace “Masha Allah…Ko jiya naji Mahaifinta suna Waya da Hakimi kan mganar ne, Allah Ubangiji ya kawo mana Komai Da Sauƙi…”..
Gaba ɗaya Suka amsa da Ameen Kafin Ashe da Tahir suyima su Goggo Sallama Suka Fice Suka barta Tana Share Ƙwallah Fita Sukayi Inda yabama Garzali Umarnin ya Shiga da kayan Abinci Zuwa Cikin Gidan Hakimi, A ƙasa Suka Taka Shida Ashe Har Zuwa Gidan Inna Fulera, Wanda Suna Tafe Tahir na Faɗama Ashe Abunda ya Faru da Wanda yake Faruwa yana gaya mata kamar ya Zubar mata Da Hawaye, Cikin Tausayin Ɗan’uwanta Take Lallashinsa Take bashi Shawaran karya Damu, kuma ya ƙyale Farida Duk inda Zataje Zata Dawo ne bayan Duniya ta koya mata Hankali ya yarda Da Shawaran Ashe Duk da A lokacin Farida bata da wani Fari Acikin Zuciyarsa.
A haka suka isa Gidan Inna Fulera, Ashe ce Ta fara shiga Suka Gaisa da Inna Fulera da Maman Lantana kafin tace musu Tahir zai Shigo Cikin Sauri Maman Lantana ta gyara Tabarma Tahir ya Shigo ganin Maman Lantana ne Awajen yasaka Daga Ashe Har Tahir ba Wanda ya Tada maganar Illah Sunkuyar da kai Da Tahir Yayi kunyar kansa na Ƙara kamashi ganin yadda Inna Fulera ta Rame Lokaci bayan Lokaci Tana Share Ƙwallah…
Basu Wani Daɗe ba Tahir ya Miƙe zai Tafi bayan ya bama Ashe 30k yace Tabama Inna Fulera, Ashe na Bata taƙi karɓa Sai Ta Fashe da Kuka Lokaci Ɗaya Ta Ɗago ido Tana kallon Tahir bayan ta Ɗago Daga Kwancen Datake Maman Lantana Tana gyara Mata Filon Kanta Saboda Taji Daɗin Zaman Sosai.
Cikin Muryan Ciwo da Kuka Inna Fulera tace “Alhaji…..”Ta faɗa Muryanta na Sarƙewa, cikin Sanyin Jiki Tahir ya Tsaya cak kafin ya Waigo Zuciyarsa na Tsinkewa Sosai Cikin Muryan Sanyi da Roƙo tace “Bana Buƙatar Kuɗinka Alhaji Abu Ɗaya Nake da Buƙata Awajenka..” jikinsa na Rawa ya Dawo ya Duƙe agaban Inna Fulera yana Faɗin “Ki Faɗi Abunda Kike Buƙata komai kike Buƙata matuƙar na Mallakeshi zan baki Shi Inna..” Ya faɗa Cikin Karaya..
STORY CONTINUES BELOW

Muskutawa Tayi kafin tace “Ba komai nake Bukata ba Illah ka Riƙe min Mufeeda Tsakani ga Allah…Ka zama gatanta..!kaji ƙanta..! Ka jibanci lamarinta…! Ka zama garkuwa a gareta Alhaji Domin Duk Duniya Mufeeda bata da Wani gata bayan kai..Don Allah kar ka barta tayi kukan maraici In kamin Wannan Abun Ka gamamin komai kuma Bana Buƙatar Wani kuɗi ko Kawan Duniya Farin cikin Mufeeda kaɗai Shine Burina Alhaji..” Ta faɗa Tana Rushewa da Kuka, Maman Lantana Dake gefe kanta ya Ɗaure amma bata kawo komai ba sai ta barshi a ƙila zafin Ciwo ne ke Damun Inna Fuleran.
Ƙuri Tahir yama Inna Fulera da Ido kafin ya maida kallonshi kan Ashe Wacce Idanuwanta Suka Cika da Ƙwallan Tausayin Inna Fulera Iska mai Zafi ya Furzar kafin yace “Girman alƙawari Inna Ba Abu bane mai Sauƙi, Amma Duk Da Haka Nayi miki Alƙawarin zama Gatan Mufeeda, Nayi miki alkawarin bazan bari Mufeeda Ta ƙara kukan Wani Abu ba…Sai na zama Silan Murmushinta anan gaba..” Ya faɗi Haka Idanuwansa Sun kawo Ruwa kafin ya miƙe da Sauri ya Fice Saboda Yadda Inna Fulera Ke kuka Tana Godiya sai yaga Kamar Bazata Tashi ba, Lokaci Ɗaya kuma Kunyar Abunda ya aikata ke Dawo mai Har Ashe ta Fito yana Tsaye yana Maida Hawayen Idanuwanshi Haka Suka Jero Har Zuwa gidan Hakimi ba Wanda ya ƙara magana, bai koma Cikin gidan ba Ashe ya umarta data cema su Basma Su Fito Tare Suka Fito Dasu Laila sama sama yayi ma Hakimi sallama suka Shiga mota Har da Ashe Har gidanta Suka kaita Kafin su Sauketa ita dasu Muda da Tsarabansu 20k yabama Muda da Laila ita kuma Ashe ya kara mata 10k ta ƙara Da Wanda ya bama Inna Fulera Taƙi karɓa Haka Motarsu Ta Ɗaga Ashe Ita da ‘ya’yanta Suna Daga maSu Hannu Har Suka ɓace ma ganinsu.
Sai yamma Suka Shigo Kaduna Tahir na Sauri Ko Gida bai Shiga ba Garzali ya Juya Dashi kamfani ya samu Kiran gaggawa bai Dawo ba sai Dare Lokacin kowa yayi barci iya kaɗai ya Tarar Farke, Mufeeda Ita da Naila Sun Daɗe da yin barci gaisawa sukayi sama sama, kafin ya Haura Zuwa Ɗakinsa Ransa Duk babu Daɗi ko yayi Wani Motsi sai ya Tuna da Alƙawarin Inna Fulera wanda Maganar da Suka gama Tattaunawa da Ishaq kenan kafin Su Rabu gaba daya Abubuwa sun mai yawa yanzu Farida bata gabanshi Matsala Goggo ce Sai Tausayin Mufeeda Daya ƙi barinshi Su sukafi Zama Cikin Ranshi Suka Hanashi Sukuni.
****
Farida kuwa Tana gidan Bilkisu Wajen Kwananta Uku amma basu ci karo da Mijin Bilkisu ba mai Suna Aliyu Saboda Tun Safe yake Fita kuma sai Dare yake Dawowa, Sai ya Fita Farida ke Fitowa Haka Kuma kafin ya Dawo Bilkisu zata san yadda Tayi Ta Hillaceta ta koma Ɗaki Abunda ke bama Farida Mamaki yadda Bilkisu ke Rawan Jiki da Abban su Walida in ya Dawo Haka zata Tsala Wanka, Taci Gayu Tana Kwakwarsa, In ko Ta mata sallama bata ƙara sakata a ido sai Washegari bayan ya Fita, Amma kuma Tana Daga Cikin masu bata Shawara ko Acikin group ɗinsu na makaranta Kan Mace ta Daina sakarma Namiji amma Ita gashi Bata Iya Haɗa komai da Mijinta.
Wani Abunda baima Farida Daɗi ba Shine yadda Bilkisu Ta Dinga yaɗa Abunda ya Faru Wajen Sauran Ƙawayensu Waɗanda basu san Meke Faruwa ba Haka Suka Haɗu agroup ɗinsu na Classic Ladies Sukayi Ta Tsinema Tahir Aciki Harda masu bata Shawaran Takaishi ƙara Kotu, yaƙe kawai Farida Keyi amma Bata jin Daɗin yadda Billy ta Fallasasu A duniya ba Ko ba komai Tana Son Tahir Kuma Har gobe yana Matsayin Uban ‘ya’yanta ne, Kuma Mijinta.
Ɓangaren su Umma kuwa basu san Abunda ke Faruwa ba Don Daga Faridan Har Tahir ɗin ba Wanda basa Waya Dashi amma ba Wanda yace ga wani Abu, Ita Farida Tsoron Su Umma ne Domin Tasan Ranta sai ya ɓaci Balle Abba dayayi Fushi da Ita don Musamman ya Kirata ya Zageta Tas, Balle kuma tace Ta Baro Gidan Tahir ai kila sai Abba ya Kusa Tsine mata, Shiko Tahir Faridan ne Kwata Kwata bata gabanshi Baya Fatan ya ƙara Buɗan baki ya Faɗi Wani Abu Daya Danganceta ya Ratayeta Gefe ne Domin Ahalin Da yake Ciki yafin Jin Tsananta da Haushinta Fiye da Kanshi Shiyasa Ko Umma ta tambayeshi Suna Zaune lafiya yake cema ta ba wata matsala Domin Kaucema Duk Abunda zai Dawo Da Farida Yamafi Jin Daɗi da bata nan Ko ba komai bayasan Abunda zai Dinga Takura Mufeeda.
Sai Ranar Data Kwana A cikin Gidan Kana Suka Ci karo da Abban su Walida, Ranar bai Fita ba Kwata kwata yana gida, Lokacin Daya ga Farida yayi Mamaki sosai nan yake Tambayanta Yaushe tazo..? Sai tace mai ta kwana biyu ma..Ido ya Zaro yana kallon Billy Wacce Tayi Fiƙi Fiƙi da Ido Zuciyarta na Tsananta Bugu Wani kallo yabi Farida Dashi bai dai yi magana ba Amma Acikin Ranshi yana Tunanin Wani Shirme kenan Mace da Gidan Mijinta Kuma Tazo Gidanshi Ta tare, Ina bazai Ɗauki Wannan Iskancin ba.
STORY CONTINUES BELOW

Bai mata magana ba sai da Suka Shiga Cikin Bedroom Ɗinsu kana ya Tsareta da Ido yana Faɗin “Da wani Dalili Farida Tazo nan gidan Harta kwana uku ban sani ba..? Ke dama wani Manufa Matar Da take da Mijinta..?”
Ya faɗa yana Hararanta Sanin Halinta na Shanshanci Shi bai Sake mata ba Shiyasa Duk yadda Billy taso tayi Iskanci bata samu Dama ba, Cikin Rawan Murya tace “Dama..Dama..Umh…” Tsawa Ya Daka mata yana Faɗin “Dama Menene..? Baki zaki Buɗe kiman magana Yadda zan Fahimceki kinsan bana son Raini ko….?”
Kai ta gyaɗa kafin tace “Matsala suka samu da Abban su Basma…” Kallonta yayi A ɗage kafin yace “Matsala..?” Ya maimata da Sigan Tambaya kai Ta gyaɗa mai alamar Hakane, Cikin Dariyan karki Raina min Wayau yace “Kuma Shikenan Don Sun samu Saɓani ita da Tahir sai kuma akace tazo gidan Aurenki ta tare ko..? Ke gaki Uwarta ko kuma Mai bata Shawaran karta koma gidan Mijinta ta cigaba da zama agidan naki Mijin..?” Ya faɗa yana kallonta Cikin ɓacin Rai..
Jikin Billy na Rawa Ta Riƙo Hannunshi Tana Faɗin “Don Allah ka Tsaya ka Saurare Abban Walida Wallahi Tahir ya chanchanci Farida Data barshi Amanarta fa yaci Shida yarinyar Datake mata Renon Naila..” Ta faɗa Lokaci Ɗaya Tana Zaunar Dashi gefe Ɗaya Kafin ta Fara Rattaba mai yadda Akayi Billy Saboda Sharri Harda ƙari kamar Agabanta Akayi
Haba Aliyu ya riƙe Kafin yace “Ke Bilkisu bana son Ƙarya fa..? Shi Tahir ɗin..? Haba Don Allah ya za’ayi mutum mai Daraja ya aikata Haka, Tahir fa Yana da Kima Sosai a idanuwan Waɗanda Suka sansa..” Ya faɗa yana Tantama Rantsuwa Billy Ta fara Jera mai, Domin ya yarda Da Ita, Bai yarda ba Miƙewa yayi yana Faɗin muje naga Faridan, Jiki na Rawa Tamai Jagora Zuwa Ɗakin data Sauke Farida, Cikin Tsare gida yake Tambayanta gaskiyan lamarin Cikin Kuka Farida ke labarta mai Hadda Hukuncin da Iyayenshi Da nata Suka bashi goyon Baya.
Tana Faɗa tana Share Ƙwallah, Jinjina kai Aliyu yayi kafin yace “Lallai ba Shakka In ko Hakane Tahir bai kyautama kanshi ba ya Cuci kanshi kuma ya Tozarta iyayensa Da kuma Zuri’arsa..Ya bani kunya Sosai, kuma sai na kirashi na mai magana..” Da Sauri Farida tace “Don Allah Abban Walida ka ƙyaleshi ko kayi mai magana bazai Saurareka ba baya ganin Abunda ya Aikata amatsayin laifi Tunda Haryana Ikirarin data bar gidan Gwara ni na Fita na bar mai gida..”
Miƙewa Aliyu yayi Daga kan Sofa yana Faɗin “maganar banza kenan Har office ɗinshi Zani Wallahi..Sai na gaya mai gaskiya sai dai ko karyaji Daɗi..” Daga Haka ya Fice Daga Ɗakin Cike da Mamakin Tahir ɗin Duk da ba wani Kusanci Suke da Juna sosai ba, amma Suna Taɓa Juna Lokaci bayan Lokaci Saboda ƙawancen Matansu Da ba yanzu yake ba, Yana Fita Farida Ta Miƙe zatama Billy magana tayi Saurin Dakatar da Ita tana Faɗin “Kinga Farida Bar maganar nan sai gobe..Yanzu lokacin Abban Walida ne kada mu Shiga Hakkinshi Nasan, Halin yan kaya na..” Daga Haka ta Fice Ta bar Farida Riƙe da baki Tana Binta da Kallo.
****
Washegari kuwa Da Misalin Ƙarfe 3:00pm na Rana Aliyu ya ƙwanƙwasa Ƙofar Office d’in Tahir inda ya bashi Umarnin Shigowa Suna Tare da Ishaq lokacin Suna Wani Lissafi ganin Aliyun sai da yayi mgana Cikin Fara’a Ya Tarbeshi yamai iso Zuwa Kujeran Dake office d’in Ruwa ya kawo mai Ya Zuba mai ya Mika mai ya karɓa yana Mai Godiya sai da yasha Ruwan ne ya Miƙawa Ishaq hannu suka gaisa Cikin Sakin Fuska ya kalli Tahir yana Faɗin “Alhaji Tahir Wajen ka nazo, Wata maganace mai Muhimmanci ke Tafe dani..”
Shiru Tahir yayi kafin yace “Allah Sarki ba komai ina Jinka..” Ya faɗa Cike da Mamaki Lokaci Ɗaya yana zama agefensa, Kallonsa Aliyu yayi kafin ya maida kallonshi kan Ishaq, Tun kafin yayi magana Tahir yace “Karka damu ka faɗi maganar Ishaq Tamkar Ɗan’uwa yake a gareni..” Zakuɗa kafaɗa Aliyu yayi kafin yace “Kana da Labarin Matarka Farida na gidana Tun Ranar data bar gidanka..?”
Tahir ya Ɗago ya kalli Ishaq shima ya kalleshi kafin Duka su maida Hankalinsu kan Aliyu Lokaci Ɗaya Tahir yace “Ah…Ina zan Sani kuwa Alhaji Aliyu..” Ya faɗa Cikin Halin Rashin Damuwa, Gyara zama yayi kafin yace “Toh Tana gidana nima bansani ba sai jiya na sani Shine na Turke Ita Bilkisun Shine Take Sanar dani Wani Labari mara Daɗin Ji ban yarda ba sai da Na Kira ita Faridan Na ƙarajin Ta bakinta Wai Alhaji Da gaske ne Maganar da Suka Faɗa min..?”
STORY CONTINUES BELOW

Miƙewa Tahir yayi yana Kallon Aliyu kafin yace “Wata magana kenan..?” Ya faɗa Jijiyoyin kansa Sun Fara Tashi Saboda Ɓacin Rai Cikin Jimami Aliyu yace “Na kama yarinyar Da kuka Ɗauko Daga Garinku tana muku Rainon Naila Ciki..” Ya faɗa yana Sakarma Tahir ido, Runtse ido Tahir yayi Zuciyarsa na Tafasa kamar tayi Bindiga Haka Shima Ishaq yana Tsinema Farida ne a Cikin Ranshi, shi Wallahi ko Zahra bai yarda ya bata wannan Labarin ba balle ke ace Mijinki amma baki da Buri sai na Tona mai Asiri ki tozartashi.
Taku Tahir yayi Zuwa bakin Window Office ɗinshi ya yaye labulen Wajen Cikin Juya baya yace “Eh Da gaske ne Aliyu..Nama Mufeeda Ciki, amma Duka Abunda ya Faru ba laifina bane Laifin Farida ne Ita ce Sanadiyar Jefani Cikin Halaka amma Wallahi bayan Matata Farida ban taɓa Keta Gonar da ba Tawa ba sai akan Mufeeda Wacce Ƙaddara ta Hau kanmu..” Ya ƙarashe Faɗa Cikin Muryan Kuka, Miƙewa Aliyu yayi yana Faɗin “Ashsha Kaji ko..? Abu baiyi Daɗi ba..”
Tahir bai bashi Zarafin ƙara magana ba, ya Shiga bashi Labarin irin zaman Wulaƙancin Dayayi da Farida da yadda ta banzatar da Rayuwarsa da Ƙoƙarinsa na ƙara Aure da yadda Goggo Take Dakatar dashi har Zuwa Faruwan komai Ya ƙarashe yana Faɗin “Wallahi Tallahi..Farida Ta Cutar dani Cutar da Allah ne kaɗai zai sakamin, Sai Farida tayi Wata Huɗu bata kalleni A shimfiɗa ba, Ku gayamin Ni Dutse ne ko Gunki da bazan Buƙaci mace ba..?” Ya faɗa lokaci Ɗaya yana Juyo da Fuskarsa Wacce Hawaye suka Wanke mishi ita.
Daga Ishaq Har Aliyu Jikinsu yayi Sanyi Sosai Aliyu ne ya ƙarasa Kusa Dashi ya Dafa Kafaɗarshi yana Faɗin “Cool Down Ka daina Kuka, Haƙiƙa Wannan Abun da ya faru ƙaddara ne ko Kuma nace Darasi ne ga Farida da Goggo, Amma fa maganar gaskiya kana da babban Laifi Tahir na yarda kabar Farida ta Rainaka take yarda taga Dama bayan Kai kake Aurenta aiko Min gatan da iyayenta Suka bata Tunda tabar Gabansu Ta Dawo ƙarƙashin Ikonka ya kamata ka Nuna mata ƙwanjinka na Mulkinka Amatsayinka na Namiji mai Cikakken Iko Agidanshi.. Maganar gaskiya kayi Kuskure..” Ya faɗa yana Murza Kafaɗarsa.
Numfashi Tahir ya Sauke kafin yace “Tabbas maganarka Hakane… Haƙurina da girman Iyayenta Danake gani Da kuma Nasihan Goggo Akaina da Kuma ‘ya’yan Dake Tsakanina da Farida yasanya Bana iya Mata Wani abu, In tayi ba Daidai ba Shine Kuskure na barta ta saba da Komai tayi Daidai ne Tabbas nima ina da Laifi ba komai Ake ma Haƙuri ba Gashi Haƙurina yajamin naje na Afkama Marainiyar Allah Daga Ƙarshe na zama Abun YaɗaWar Farida Kamar bamu Haɗa komai da Ita ba, ba komai…Haka Allah ya Tsara min..” Ya faɗa yana Share Hanci kamar Wani yaro.
Kafaɗarsa Aliyu ya Daka kafin yace “Kazama namiji Abokina ka ganni nan bana ma Bilkisu da Wasa Tunda na Lura tana da Rawar kai Ubanta Nakeci tasan Halina ko yanzu ɗin ma ina komawa zan Koro Faridan Dole ta Dawo Tunda bata da Wajen Zuwa…”
Da Sauri Tahir yace “No..no plz ka ƙyaleta Ka barta ta Zauna Da kanta zata Dawo ba sai kamata magana ba ai zataga Abunda saɓanin Shi Suke gaya mata zata ma kanta Faɗa Tun kafin Wani ya mata..” Ishaq yace “Shawara mai kyau Tahir…”
Aliyu ya Saki Hannu yana Faɗin “While Tunda kace Haka zan saka musu ido.. Amma True Tak, Yarinyar nan ta Haihu ka Aureta Wallahi Sweet Sixtyn suna da Daɗin Sha’ani, Tuni Farida zata Rena kanta Ta Dawo Tana begenka Lokacin Da ka mata Nisa..” Dariya Ishaq ya saka kafin yace “Shawara mai kyau..Dama Shi ya Chanchanta yayi Wuf da Ita..” Hararanshi Tahir yayi Bai yi Magana ba, Shima Aliyu Dariya yake kafin su Cigaba da Tattauna maganar Tare Suka Fito Sai da Sukayi sallar La’asar Cikin Jam’i kana suka Rako Aliyu ya Hau Motarsa Zuwa gida, su kuma suka koma Office d’in Tahir Ishaq bai Dawo da Maganar ba ganin Tahir ya basar da Zancen ya Ɗauko Lissafinsu suka cigaba dayi amma Cikin Ran Tahir Tsanar Farida ce ke ƙara Ninkuwa in ya Tuna Tana chan tana Yawo Dashi Acikin Duniya kamar babu Igiyan Aurenshi Akanta.
******
*BAYAN SATI ƊAYA*
Lokacin Tuni Har Su Basma Sun koma Makaranta Hadda Itama Mufeedan Don Da Tahir ya nuna kamar Ta Haƙura da Karatun Saboda Gujema idon Mutane sai Ta Fara Share Ƙwallah Shi kuma ƙwallar Mufeeda kamar dalma yake Acikin Ranshi, dole ya barta ta cigaba da Zuwa Makaranta amma bayan yaje yama Shugaban makarantan Bayanin Cewa Mufeeda matar Aure ce, Kuma tana Ɗauke da Juna biyu So School Authority Su kula da Ita, basu Tsaya Tambayan Waye Mijin Ba Illah Suka yarda da maganar Tahir Suka kuma Rubuta Cikin Record Book.
Hatta da Islamiyya ta koma Abunta kamar ba Ita ba, sai dai Tayi Kiɓa Sosai, Ta ƙara Fari ta Cika ta Ko’ina Saboda tana samun Abunda Take so Abincinta Dama Shine Faten Wake, sai ƙosai da Koko sai kayan kwaɗayi Irinsu Goriba, yalo Sai Ice cream Wanda In Mufeeda bata Sha ba kamar Cikin zai ɓare, Shiyasa Tahir kullum zai Dawo sai ya Shigo mata Dashi, Ba laifi Iya na Kula da Ita sosai su Basma ba’a barsu Abaya ba Lokaci kaɗan Mufeedan Ta Saki Ranta sai dai Tunanin Innarta Dayaki barin Ranta.
Ɓangaren Su Goggo Abu kuwa ba Wani Cigaba, Tahir Sau Ɗaya ya Kira Baba Hakimi Awaya Tunda yaji ya fara mai maganan Goggo Abu ya Datse Kiran, Tun daga Ranar ko ya Kirashi baya Ɗauka Dole ya Haƙura sai dai yana Kiran Goggo Akai akai Yana ƙara bata Haƙuri amma ya Ɓoye mata Shima Saboda Ita Baba Hakimi ya Daina ɗaga Wayarsa sai dai ya Dinga Nuna mata ta kwantar da Hankali komai xai Daidaita.
*******
Yana Toilet yana Wanka, Akayi ta Kiran Wayarsa bai ji ba sai da ya gama Wanka ya ɗauro Alwala ya Fito Ɗaure da Towel A ƙungunsa Ƙaramin na Saman kansa yana Tsane Ruwan Jikinsa, Yaji Kiran Wayarsa Cikin Sassarfa ya isa Kusa da Wayar, Abunda ya bashi tsoro ganin Kiran Baba Hakimi, Da Asuban Fari Domin Lokacin Wajen ƙarfe 4:43am ne.
Cikin Firgici Da Tsoro ya ɗaga Kiran yana Faɗin “Salamu Alaikum Baba..?” Ya faɗa Cikin Rawan Murya banji me akace ba Sai dai naji Tahir ya saki Salati yana Faɗin “Innalillahi Wa’inna Alaihirraju’un..Allah ya Jiƙanta da Rahma Allah yasa ta Huta…”
Ya faɗa kafin ya Ɗauke Wayar A kunnensa Cikin Mutuwar Jiki ya Faɗa gefen gado yana Dafe kanshi Ko’ina na Jikinsa na Rawa, lokaci ɗaya Yaji Hawaye Sun Cika mai ido Har Sun Fara gangarowa.
…Ya Daɗe Zaune a gefen Gado yana Dafe da kanshi yana Jimamin Abunda Baba Hakimi ya Sanar Dashi, Tausayin Mufeeda na Ƙara Cika masa Zuciya. Rashin Mahaifiya Akwai Ciwo balle Ita Daba Uwa ba uba..+
Ya daɗe Zaune Baisan Iya Adadin Lokacin Daya Ɗiba yana Tunani da Kuma Tausayin Mufeeda ba, Kiran Sallah ya ƙara Jiyowa Daga Masallatan Dake Kusa Dasu Zabura yayi ya Miƙe Lokaci Ɗaya yana Duba agogon Wayarsa yaga 5:10am Da Sauri Ya Nufi Wardrope ɗinshi ya Buɗe ya Ɗauko Wata Jallabiya mai Ruwan Toka ya Zura Hula ya sanya kafin ya Ɗauki Carbin sa ya Fice Daga Ɗakin.
Ƙasa ya Sauko Zuwa Ɗakin Bassam Shi ya kuma Tashi Su Basma, Iya kuma Koda ya Leƙa Ɗakinta Ta tashi sai yace Ta tashi Mufeeda Lokacin Sallah yayi, Daga nan Suka Wuce Masallaci Shida Bassam sai Wajen Bakwai Saura Suka Dawo Suna Shigowa Falon Suka Iske Basma Tsaye da Uniform A jikinta Cikin Girmamawa Ta Duƙa ta gaishe da Tahir, Cikin kallonta yake amsawa yana Faɗin “Ku Saka kayan gida ne Basma Gaba ɗayanmu yau Ɗanbatta zamu..” Tare da Bassam Suka Kalleshi Cikin Murna Suka ce “Da gaske Daddy..?” Kai ya gyaɗa musu alaman Hakane Tsalle Suka Farayi alamar Murna Cikin Dakewa yace “Ku ɗiba kayanku koda Kala Uku uku ne sai bayan Kwana Uku zaku Dawo..” Jin Haka yasa Suka Zura da Gudu Zuwa Ɗakunansu da Kallo ya bisu Acikin Ranshi yana Faɗin Kurucci Dangin Hauka.
Yana Shirin Haurawa Sama Iya ta Fito Daga Kichen ganinshi yasa Ta saki Fuska Tana Faɗin “Ah…Alhaji Barka da Safiya..” Cikin Sanyi ya waigo yana Faɗin “Ina kwana Iya..?” Ta amsa da lafiya lau bai bata Zarafin magana ba yace “Ahm Iya Ki Shirya kayanki ki kuma Saka Mufeeda Ta Shirya Kayanta Ɗanbatta zamu yanzu da Safen nan.” Iya ta Ji Zuciyarta ta Tsinke da Sauri Tace “Ɗanbatta kuma Alhaji..? Allah sa lafiya..?”
Shiru yayi kafin yace A hankali.. “Mahaifiyar Mufeeda ce Allah yama Rasuwa Jiya da Daddare yanzu Baba Hakimi ya Kirani yake Faɗa min..” Dafe Kirki Iya Tayi kafin tace “Innalillahi Wa’inna Alaihirraju’un…” Ciwo Tayi Alhaji..?”
Kai ya gyaɗa mata kafin yace “Eh har ta kwanta Asibiti ma, Ki Taimakama Mufeeda Don Allah Iya, Kuma karki Sanar da Ita Domin batasan Halin Da’ake Ciki ba..”Jinjina kai Iya Tayi Tana Faɗin “Allah Sarki Haƙiƙa Mufeeda Tayi Rashi babba..Allah Ya Jiƙan Inna Fulera, Insha Allahu Alhaji yanzu zamu Shirya..” Ta faɗa Cike da Tausayawa.
Gyaɗa mai kai yayi kafin ya Haura sama Ita kuma ta Koma Kichen Ta Cigaba da Soya Dankali, cikin Jimami da Tausayin Mufeeda sai da Ta kammalah Duka Abun karyawan Ta kwaso Zuwa Dininng kana Ta Shiga Ɗakin Mufeeda Ta Isketa Tayi Wanka Har ta shirya Cikin Uniform ɗinta Naila ma Ta mata Wanka Ta Shiryata Cikin Riga da Wando, Tana gefen Gadon Tana Riƙe da Hannun Naila wacce Ke Tata tan Tafiya, cike da Tausayin Mufeeda Iya ta Shigo Ɗakin Tana Faɗin “Mufeeda Ki Cire kayan Makarantar ki saka na gida kuma ki Haɗa kayanki Cikin Akwati Naki dana Naila yanzu Alhaji ke gayamin Ɗanbatta zamu Tafi Dukkanmu sai mun kwana Biyu A chan..”
Da Sauri Mufeeda Ta Ɗago Tana kallon Iya Cikin Fitar Magana tace “Ɗanbatta kuma iiya..? Na Shiga Uku ko Gida Daddy zai maidani..?” Ta faɗa Idanuwanta na Cikowa da Ƙwallah Saurin girgiza kai Iya Tayi Tana Faɗin “Ko Ɗaya inaga dai Hutu Alhaji ya samu yakeso muje chan Muyi Hutun..” Ta faɗa Tana Ƙara Jin Tausayin Mufeedan, jin Haka ya saka Mufeeda Ta Washe baki Tana Faɗin “Da gaske Iya..? Yau zan kwana A ƙirjin Innata..” Ta faɗa Cikin Farin ciki Lokaci Ɗaya Tana Ijiye Naila kan gado ta isa Wajen Akwatinta ta Ɗauko, Iya Fita tayi Tana Sharan Ƙwallar Tausayin Mufeeda.
STORY CONTINUES BELOW

Shiko Tahir kafin ya Shirya sai da ya Kira Ishaq ya Sanar Dashi Cikin Tausayawa Ishaq yace Ya Jirashi gashinan Zuwa Su Tafi Tare Haka ko Akayi, ƙarfe 8am da ‘yan Mintina Gaba daya Sun gama Shirinsu Sun karya Tahir ne ma bai Karya ba, Lokacin da Suka Fito sai ga Ishaq ya ƙaraso, musabaha Sukayi da Tahir Su Basma kuma Suka Ranƙwafa Suna gaisheshi ya amsa yana Shafa kansu, Nan da nan Suka Shiga Mota bayan Garzali ya Zuba kayansu Cikin Booth d’in Motar, Harda Tahir Shima da Jakar kayansa, Cikin gida kuwa Iya sai da ta kashe komai na Wuta Kana Suka Fito, Motar Garzali Su Iya da Basma da Bassam da Mufeeda Suka Shiga Tahir wanda ya ke Riƙe da Naila, da ishaq suka Shiga Motar Ishaq ɗin, Tara da Wani Abu na Safe Suka Ɗauki Hanya bayan Tahir ya Kira Baba Hakimi yace Atsahirta da Jana’izar Inna Fuleran Har su Iso ko Mufeeda ta samu ganin gawar Mahaifiyarta Suna Tafe Suna Janjanta Abun Shida Ishaq, Lokaci Ɗaya kuma suna Gudu ba Sosai ba.
******
Ƙarfe 11 da ‘yan Mintuna Motocinsu Suka Yada zango A ƙofar Gidan mai girma Hakimin Ɗanbatta Inda Suka Tarar da Al’umma Tsaye, wasu kuma Suna Zaune da alaman dai Isohuwarsu Ake jira, Mufeeda Kuwa Tunda Suka Shigo garin Ɗanbatta gabanta ke Faɗuwa Zuciyarta bata Tsinke ba Sai da Suka Tsaya A ƙofar Gidan Duk da Ƙofar Gidan Hakimi ba’a Rabashi da Jama’a amma na Yau Daban ne, Sukansu su Basma Sunyi Wani Iri balle da Suka Firfito Daga mota Sunji Ana gaisawa da Tahir Ana mai gaisuwa, Umarni ya basu kan Su Shiga Cikin Gida, Shi kuma Idanuwansa na kan Mufeeda bayan ya Miƙawa Iya Naila.
A cikin gidan ma Cike yake da Mata Tunda nan Aka kawo gawar Inna Fuleran Bayan ta cika Akayi mata Wanka da Suturu Tunda Suka Shiga gidan Mufeeda ke Jan Ƙafa, kamar Mara Lafiya, barinma yadda jama”a ke Binta da kallon Tausayi Basu Dai Tsaya ba sai da Suka Shiga Falon Goggo Abu Inda Suka Iske Goggo Abu zaune da Hijabi Da Carbi Ahannunta gefenta kuma Innaro ce sai Ashe da Maman Lantana Dake gafe Daga Tsakiyarsu kuma gawar Inna Fulera ce Lulluɓe Cikin Likkafani Tunda Suka Shigo Ɗakin Maman Lantana Ta ɗago Tana Kallon Mufeeda Idanuwanta na Zubar da Ƙwallah Tun daga Lokacin Jikin Mufeeda ya fara Rawa Saboda yadda gabanta ya fara Tsinkewa Lokaci Ɗaya.
Basma ganin gawa ne yasa Ta koma bayan iya Tana Rawar Jiki Ita ko Mufeeda Maman Lantana ta Nufa Tana Faɗin”Maman Lantana lafiya naga kina kuka..? Waye nan kwance ya Rasu..? Ina Innata naga banganta bane..” Ta ƙarashe Faɗa Cikin Fitan Hayyaci Hannunta Mama Lantana Ta Rik’e kafin Tajata har gaban gawan Inna Fulera ta saka Hannu ta yaye Farin likafanin Da’aka Lulluɓeta Dashi Dayake Tana Cikin Makara ne, Fuskar Inna Fulera Ta bayyana Kwance Bata Numfashi.
Daskarewa Mufeeda Tayi Tana bin gawar da kallo Cikin Rashin Hayyaci Kafin Ta Sulale ƙasa Ta Duƙe Gaban Gawar bakinta na Rawa Muryanta na Tsinkewa Take Faɗin “Inn… Innata..Ta..na barci ne ko..?” Ta faɗa Lokaci Ɗaya Ta Ɗago kai Suka Haɗa ido da Maman Lantana Hawaye Sun Fara Wanke mata Fuska Jikinta na Rawa ganin Tana Taɓa Inna Fulera ba motsi gashi Duk An Nannaɗeta Ciki Likafani Zuciyarta Ta Tabbatar mata da Sai Mutum ya Mutu Za’ayi mai Haka Kenan Innarta Ta Rasu..? Zuciyarta ce ta karye Ta Faɗa jikin Gawan Tana Faɗin “Innata ki Tashi…Nasan kina Jina..? Nice ‘Yarki Mufeeda ki Tashi ki ganni nasan Wasa Kike man baki Mutu ba..” Ta Faɗa Tana Kuka Wurjajan Su Goggo Abu Saboda Tausayi Sai Sharan Ƙwallah Suke na Tausayin Mufeeda Maman Lantana ne ta ƙaraso kusa Da Ita ta Riƙota Tana Kuka Take Faɗin “Bar Kuka Saman gawa Mufeeda Fulera ta tafi..Sai dai muyi mata Fatan Dacewa Ta Cika Da Kalmar Sunanki Abakinta bayan Ta Jaddada albarka agareki..” Ƙyam Mufeeda Ta Tsaya Da Kukanta Tana kallon Maman Lantana Cikin Fitan Hayyaci Take Faɗin “Da gaske ne dama Inna ba barci Take ba..? Innata fa Ta Rasu kika ce..?” Na Shiga uku ni Mufeeda ina zan Saka kaina..?” Ta faɗa Tana Sakin Wani Marayan Kuka, kamar zata Shiɗe Lokaci Ɗaya Tana ƙara Sulalewa kan gawar Iya da Basma na waje Ɗaya Suna Sharan Ƙwallah Hatta Naila Datake yarinya Ganin Mufeeda na Kuka Itama sai Ta Fashe da Kuka ganin Yadda Mufeeda ke ƙanƙame gawar Inna Fulera ne Tana Kuka Tana Faɗin Inna Ki Tashi ya sanya Innaro Tashi Ta Riƙota da Ƙarfi Cike da Tausayi amma sai Mufeeda Ta Turje domin Wani ƙarfi ne yazo mata ta ƙwace kanta ta koma ta ƙara kwanciya kan gawar Inna Fulera Tana Kuka Daidai lokaci kuma Su Tahir Suka Shigo Dashi da Ishaq da Wasu mutane su Shida Sunzo Daukan Gawar, Tun Shigowar su Mufeeda Cikin gidan Tahir ke Cikin Zullumi yanzu ma yana Shigowa Idanuwanshi na kanta Gaba ɗaya Jikinshi na ƙara Sanyi Kusa da Ita Suka Isa kafin ya Sanya Hannu ya Dafa kafaɗarta yana Faɗin “Mufeeda…” Ya faɗa Cike da Rauni.
STORY CONTINUES BELOW

Jin Muryansa yasa ta Ɗago da Sauri Ganinshi yasa Kawai Tayo Rimi ta afka mai Har sai da ya zauna kan Cafet ɗin bayan yayi Saurin Riƙeta Cikin Kuka Take Faɗin “Kagani Wai Daga Innata na barci suna cewa ta mutu, Zata Tashi ko Daddy kace mata Ta tashi gani nazo..” Ta faɗa Tana Zubar Hawaye Zuru yayi mata da Ido kamar ya Fashe mata da Kuka Cikin Fitar magana yace “Kinga Kwantar Da Hankalinki, kinji ko..? Kin Taɓa ganin Wanda ya Mutu ya Dawo..?” Girgiza kai tayi kafin ya cigaba da Faɗin “Toh ki saka Aranki Inna ta tafi bazata Taɓa Dawowa ba…Yanzu Addu’arki kaɗai Take buƙata ba Kukanki ba..” Tsuru tamai da Ido Hawaye na Zuba mata Shar kafin tace “Bani da Kowa…Inna itace gata na…Ya zanyi na Shiga Uku..” Baki ya Rufe mata yana Faɗin “A’ah kina damu…Mune gatanki Mufeeda nayi ma Inna Alƙawarin zan zamo garkuwarki Har Ƙarshen Rayuwarki ki daina Kuka Tashi ki bari Aɗauki gawarta Amata Sallah zamu kaita gidanta na gaskiya..” Ya faɗa yana Ɗagota Tsaye kafin yama Su Ishaq alama da Ido kan Su Ɗaga gawan Gaba ɗaya Falon ko Mamakin yadda Tahir ya Iya Shawo kan Mufeeda Akeyi, wacce Tun Taga Da Gaske za”a Fita da Gawan Inna Fulera sai ta ƙara Tuburewa Tana Kuka Tana Ƙoƙarin Ƙwace kanta Tana Faɗin “Wayyo ku Dawo min da Innata Ku Dawo min da Ita..” Take Faɗa Tana kuka Tana miƙa Hannu Har Aka Fice da Ita Agaban Idanuwanta Luu kawai Tayi Ajikin Tahir alamun Ta Sume, Fuskarta yake Shafawa yana Kiran Sunanta, Innaro da Ashe Suka Taso da Sauri Suka Riƙota Suka Shiga da Ita Uwar Ɗakin Goggo Abu Mama lantana kuma Ta bisu da Ruwa Shi kuma Tahir Da Sauri ya Fice yana Ji kamar Shima ya share Ƙwallar, Da kallon Tausayi Goggo Abu Ta Bishi Itama Ƙwallar Take Sharewa Domin Har yanzu bata Ishi Baba Hakimi kallo ba.
Har Aka kai Inna Fulera gidanta na Gaskiya Mufeeda bata ƙara magana ba Bayan Ta Farfaɗo Tana dai Zaune Zuru Hawaye na Zubar mata Kowa yazo ita yake Tausayi ba Uwa ba Uwa Gashi ba wani ƙwaƙƙwaran Dangi, Mutane sai magana Suke Wasu na Faɗin Ai Taimakonta Ma gidan su Hakimi, Sune gatanta, gida ya cika da ‘yan Zaman Makoki Hakama Ƙofar Gida Cike da Mutane Ciki Harda Su Tahir da Ishaq Harda Garzali Direba Wanda Tahir yace ya Koma gida yace ya barshi ya samu Jana’iza Mutane da Kuma alhinin Mutuwa ya saka ba Wanda Ya Lura ba Farida balle Har Ya Tambayeta Goggo Abu ne ke Damuwa Da Ita, Toh Itama Tana Ta kanta ne Ba wanda Ya Tuna Da Ita sai Washegari Da Umma Suka zo gaisuwa Ita da Abba,Tun Ajiya Ishaq ya koma Shida Garzali inda Tahir yace Ranar Uku ya Dawo ya Ɗaukesu.
Tahir ya Shiga Cikin Gida Da Rana gaida Umma Naila na Hannunsa bayan Tagama ma Tahir gaisuwa Shiko Rabin Hankalinsa naga Mufeeda Wadda Cikin Kwana Ɗaya Ta Fita Hayyacinta Kukan Zucci Take Wanda Sai dai Aga Hawaye na Zubo mata Ta fita Kamanninta Fuskarta Ta Kumbura Idanuwanta Sunyi Jawur Tana Kusa Da Goggo Zaune ta Tsurama Cafet Ɗinta ido Yana Nazarinta ne Umma Tace “Wai ni kam Ina Farida ne Tunda na Shigo ban Ganta bane ko Tana Shashen Innaro ne..?”
Gaba ɗaya wajen Aka Zuba ma Tahir Ido, dama Cikin Uwar Ɗakin Goggo Abu ne, Daga Umma sai Mufeeda sai Goggo Abu Innaro ma Tana Falo Ita Da Ashe da Sauran Jama’a Cikin Dakewa Da Rashin Damuwa Tahir yace “A’ah Umma bata zo ba..” Cikin mamaki Take Faɗin “Bangane bata zo ba? Tahir Mutuwa fa Akayi Shine ka ƙyaleta Taƙi Zuwa..?”
Murmushi yayi kafin Yace “Nifa Umma Tun Washegarin Tafiyarku Farida ta saka ƙafa Ta bar gidan Batare Dana san Inda Taje ba..” Salati Umma ta Saki Kafin Tace “Na shiga uku ni Aliya Farida Zata Kasheni Lokacina bai ƙare ba Haba Tahir Shine Duk Tsawon Wannan Lokacin Baka Taɓa Sanar damu ba..?” Kansa ya Sunkuyar batare Daya ce komai ba Mamakin Goggo Abu yake Yadda Ko ƙanzil batace ba Lalle Goggo Taga Rayuwa.
Cikin Ɓacin Rai Umma Ta Ciro Waya Ta Dokawa Farida Kira, lokacin da Kiran Umma ya Shigo Tana Zaune Afalon Na Billy Tana kallon Ikon Allah, domin Abban Su Walida ne yayi Tafiya yau zai Dawo Shine Billy Ta kasa Sukuni da Zama Tsakanin Kicthen da Falon ƙayataccen Girki Take mai Tana Rawan Jiki, Farida Abun na bata mamaki In Taga Abunda Billy ke Aikatawa kamar ba da ita Cikin masu Zugata kan ba’a Sakarma namiji Fuska Balle kai mai Rawan Jiki Itako Tunda Tazo Gidan Matuƙar Taga Billy Afalo Toh Abban Walida ya Fita ne In ko yana nan bata da Lokacin kowa bayan An Chaɓa Ado An Shiga Kichen Anyi Girki Ta Tuna Sanda Billy ke Bata Shawaran Ta Ɗauko mai aiki Kada ta zama baiwa mai abinci, Abun bai ƙara Ɗaure mata kai ba, sai da taga yadda Billy ke Rawan Jiki ko Muryan Abban Walida Taji, kenan Itace Suka Maida Sakarya da Suke Sanar Da Ita Tsakaninta da Namiji bawani Ragowa in Tanaso ta ƙwaci ‘Yancinta..?
Tana Cikin Wannan Tunanin Wayarta Ta Shiga Tsuwa, ganin Sunan Umma sai da gabanta ya amsa Tana Ɗagawa Umma tace “Kinci Ubanki Farida..” Cikin Mamaki Farida Tace “Kai Umma me nayi kuma..?” Umma tace “Ubanki kikayi Nace Ubanki kikayi..Ashe Farida Baki da Mutumci bansani ba? Kina gidan Uban waye Bayan kinbar gidan Mijinki…?” Tura Baki Farida Tayi kafin Tace “Umma ina gidan Billy….”
“Billyn ubanki Sakarya mara Tunani Wato ita Tana Gidan Aurenta Ke kuma Ta barki ki Zauna Tunda baki da mafaɗi, Toh maza ki Haɗo Yanaki yanaki Kizo Ɗanbatta yau ɗin nan muna Jiranki Nida Abbanki munzo Gaisuwar Rasuwar Mahafiyar Mufeeda..” Daga Haka Umma Ta Katse Kiran.
Sororo Farida Tayi Ranta na ƙuna da Sunan Mufeedan Da’a Aka Ambata Amma Haka Ta tashi ko kallon Ɓarayin da Billy Take bata yi ba Wacce ke Jera Kuloli bisa Dinning Ɗakin Da’a Aka Sauketa ta Shiga Tana Hawaye Ta Haɗa kayanta Tsab Ta Ɗauko Mayafinta da Akwatinta ta Fito, A falo Suka ci karo da Billy Cikin mamaki tace “Ah Farida Ina Zuwa naganki da Akwati Haka..?”
Kai Tsaye Farida tace “Ɗanbatta zani…” Sheƙeƙe Billy ke Binta da kallo kafin tace “Wai koma ma Tahir ɗin zakiyi Don Rashin Zuciya..?” Cike da Haushinta Farida Tace “Eh zan koma ma Mijina Tunda na lura masu bani Shawaran yadda zan Tafi da gida Su basu amfani da Shawaran ko Kaɗan..” Sororo Billy Tayi Domin Tagane magana Farida ta yaɓa Mata, Ɗaure Fuska Tayi kafin tace “Au Haka zaki ce…? Ke kika sani Ai ‘yanci Ake Neman ƙwatar miki Mutumin daya Tozartaki yama ‘Yar aikinki ciki ai magana ta ƙare..”
Farida Takama Hanyar Fita Take bama Billy Amsa Cikin Dakewa tace “Eh ‘Yanci Abarni na ƙwatarma kaina kamar yadda Kuma naga kuna Ƙwatarma kanku, kuma maganar yama ‘Yar Aikina ciki Gwarashi nashi ya bayyana Mijin Wata Fa.? Uban wa yasan Wani Ta’asan yake Aikatawa Adai yi Sha’ani..” Baki Billy Ta kama kafin tace “Kambu…! Amma kafin ta Sake Wata Magana Farida Ta Fice da Kallon Mamaki Ta Bita Kafin Ta taɓe baki tace A fili.. “banza.Allah sa Kin Fara Wayau kenan..”
Itako Farida Motar Ta ta Ta Shiga Taba ta Wuta sai da Ta Fahimci Lafiyarta kana Ta saki Hon Megadi ya Buɗe mata Ƙofa ta Fice da Gudu Cikin Lokaci kaɗan Ta Ɗauki Hanyar Ɗanbatta Zuciyarta Cike da Fargaban Wani Irin Hukunci Zata karɓa Wajen Umma da Abba.
Ƙarfe 2:40pm. Ta isa Ɗanbatta, Tahir da Hakimi da sauran mutane suna zaune a ƙofar gidan suna karɓar gaisuwa gurin jama’a masu zuwa musu ta’aziyya, haka ta ratsa tana sunne kai ta shige cikin gidan, tana shiga direct ɗakin Goggo Abu ta dosa.+
Tana shiga da Umma suka fara haɗa ido, rass taji gabanta ya faɗi tana turo baki ta ƙarasa ciki ta zauna a kusa da Goggo Abu ta duƙar da kai taƙi kallon kowa dake ɗakin, Mufeeda kuwa tana ganin Farida ta shigo tayi maza ta miƙe ta fita falon Goggo ta zauna, don bata son abinda zai haɗasu da Farida guri ɗaya, gani take zata iya rufeta da duka don haka take jin tsoronta.
Miƙewa Goggo Abu tayi itama ta fito falo gurin Mufeeda ta zauna akabar Umma da Farida kaɗai a cikin uwar ɗakin, ɗagowa Farida tayi tana kallon Umma tace “Umm…” Da sauri Umma ta dakatar da ita tana watsa mata harara take faɗin “Uban me ya kai ki gidan Bilkisu Farida…? Wato dai ke har yanzu bazaki natsu kiyi hankali da duniya kisan me take ciki ba ko Farida.? Yanzu da kika je gidan Bilkisun uban me kikaje tayi miki? Me ma yasa kika saka ƙafa wai kika bar gidan mijinki da ‘ya’yanki bayan duk irin faɗan da nayi miki ranar kafin mu tafi? Wato baki ji ba shine kika shure kika tafi gidan ƙawa har na tsawon kwanaki huɗu kina can a zaune saboda gaki ballagaza ko…? To uban me kika je yi gidan aurenta tayi miki..? Tana zaune da mijinta lafiya ke da baki san mutunci da darajar naki mijin ba shine kika kwashi jiki kika tafi gidanta tayi miki maganin taki matsalar ko?” Ta faɗa a hasale tana ji aranta kamar ta tashi ta rufeta da uban duka saboda takaicinta, ita ko Farida wani bala’in haushin Bilkisu ta ƙara ji a zuciyarta, take wasu hawaye suka fara zubowa daga cikin idanunta Umma na kallonta tace “Ai kuka kam yanzu kika farashi Farida..tunda dai kince ke ba mai hankali da tunani bace balle kisan ya kamata, na ɗauka zaki yi nadama ne saboda abinda sakacinki da toshewar tunaninki ya janyo muku ke da mijinki, ashe ba haka bane, ke inda tunaninki yake daban, abinda kika ɗaukarwa zuciyarki tun farko shi zaki ci gaba da yi. To kiyi Farida, bance ki fasa ba kici gaba…” Haka Umma tai tawa Farida faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Farida kuwa in banda kuka ba abinda take yi har da shassheƙa, sai yanzu ne ita da kanta take ganin aibun abunda tayi a rayuwarta, bata kyautawa kanta da ‘ya’yanta ba, uwa uba kuma mijinta, bata tashi sanin babban kuskuren data tafkawa rayuwarta ba, sai data je gidan Bilkisu taga yanda take yiwa mijinta take kaffa kaffa dashi, bata haɗa komai da mijinta ba. Ita yanzu wace riba zata ce taci na irin halayen dasu Bilkisu suka dinga zigata suna ɗorata akai kuma tana bi…?
Umma ce ta katse mata tunanin da take da faɗin “Yanzu a irin waɗannan abubuwan da kike yi wace riba kika samu? Me kuma zaki ɗorar? Miji ya gaji da halinki, har ya daina damuwa da duk wasu lamura da suka shafeki, kin kaisa bango halayenki sun gama isarsa, kin tafi kin bar gidan mijinki da ‘ya’yanki kin tafi gidan ƙawa kin zauna har tsawon kwanaki, kin gama fallasa kanki da zuri’arki a gaban ƙawayenki, sirrin gidanki da komu bai kamata mujishi ba kin gama tallatashi a titi ga wasu can kinyi terere da mijinki, don nasan sai kin gaya musu duk abinda yake faruwa, tunda tunaninki ya gama toshewa…” Ta faɗa tana murmushin takaici, wani kukan baƙin ciki Farida ta fashe dashi tana girgiza kanta, kafin ta ɗago hawaye na tsirarowa daga cikin idanunta tace “Umma don girman Allah…” Sake dakatar da ita Umma tayi da faɗin “Komai kika yi fa kanki kika yiwa, nidai zanci gaba da tayaki addu’a Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya. Don haka maza ki tashi kije ki yiwa Mufeeda gaisuwa…” Ta faɗa tare da miƙewa, itama Faridan tashi tayi tana share hawayen fuskarta tabi bayan Umma suka fito falo, inda Goggo Abu da Mufeeda suke sai Nailah da Iya da Maman Lantana, Umma zama tayi a kusa da Mufeeda tana kallon Farida da tayi tsaye tana kallon Mufeeda a sace tana turo baki alamar bazata iya ba an takura mata, wani kallo Umma ta watsa mata ba shiri ta dubi Mufeedan data sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da bakin hijabinta, sai data zabga mata uwar harara kafin ta ɗauke kai tana faɗin “Ya ƙarin haƙuri…Allah ya jiƙanta ya gafarta mata..” Ta faɗa a tare tana zama a kujerar dake falon.
STORY CONTINUES BELOW

A hankali Mufeeda ta ɗago ba tare da data kalli inda take ba tace “Alhamdulillahi…Momy mun gode Allah, Ameen na gode..” Ta faɗa ƙwalla na taruwa a cikin idanunta, janyota Goggo Abu tayi jikinta tana share mata hawaye, taɓe baki Farida tayi tana kallonsu kafin ta ɗauke kai tana sakin siririn tsaki.
Ranar a nan Umma ta kwana yayinda Abba kuma suka juya shida direba suka koma wanda sai ranar addu’an uku sannan zai dawo bayan anyi addu’an uku da safe sai su koma tare da Umma.
************
Yau akayi addu’an ukun Inna Fulera, bayan mutane duk sun watse yayi saura sai yasu yasu a gidan, suka taru dukkansu da Baba Hakimi da Goggo Abu da Innaro da Tahir da Ashe dasu Basma da Bassam sai Farida da Mufeeda da Umma da Abba.Sai Ishaq da Zahra da Suka zo Suma, Sai da suka haɗu gaba ɗayansu kafin Baba Hakimi yasa Tahir yayi addu’a aka shafa, sannan ya fuskanci Mufeeda wacce ke zaune a ƙasa ta duƙar da kanta ƙwalla na zubo mata, nan ya shiga yi mata nasiha sosai da nuna mata ta dinga yiwa mahaifiyarta addu’a ta daina mata kuka, kanta ta gyaɗa masa kafin ta ɗago tana share ƙwallar tausayin kanta.
Umma ce ta gyara zamanta tana kallon Abba take faɗin “Gata nan Alhaji ka tambayeta inda ta tafi tabar gidan mijinta da ‘ya’yanta tsawon kwanaki bata gidan aurenta…ba tare da tazo gida ba, ba kuma tazo nan Ɗanbatta ba…” Ta faɗa tare da nuna masa Farida da tayi tsuru tsuru tana raba idanu, wani kallo Abba yayi mata yana faɗin “Au wato bayan mun tafi shine tabar gidan tayi wani guri, saboda bata ji maganar da mukayi mata ba..?” Gyaɗa kai Umma tayi tace “Ai kuwa babu abinda ta ɗauka a faɗan da akayi mata..” Ta faɗa tana kallon Farida.
Gizgiza kai Baba Hakimi yayi yana faɗin “A’a bafa kusan dalilinta na barin gidan ba, ƙila dai akwai abinda shi Attahirun yayi mata ne…” Da sauri Abba ya katseshi da faɗin “A’a Mansur, karka ce haka, ai yana gaba da ita, kuma ko ba haka ba ai mijinta ne shi, kuma kome zaice mata ai bai kamata ace tayi fushi tabar gidan ta tafi wani guri daban inda ba’a sani ba…”
Baba Hakimi na kallon Abba yace “Ka bari muji abinda ya faru a bakinta tukunna..ke Farida faɗa mana abinda Attahiru yayi miki da yasa kika bar gida..?” Ya faɗa yana kallonta, ƙara sunkuyar da kai tayi ta shiga rattabo abinda ya faru ranar bayan tafiyarsu tana haɗawa har da sharri tana ƙullawa, tunda ta fara maganar kawai Tahir ya girgiza kai yana sakin murmushi bai ce komai ba, har ta dasa aya…
A harzuƙe Abba yace “Wato a ranar da muka gama magana akai miki faɗa a ranar kika sake shuka wata tsiyar ko Farida..? To ki sani wallahi tallahi babu inda Mufeeda zataje tana nan zaune daram a gidan anan zata zauna ta haihu, sai dai ke kibar gidan don ubanki kije duk gidan ubanda zaki amma banda gidana, kuma wallahi duk ranar da kika sake fita kika je wani waje bada yawun mijinki ba ko kika fita saboda nuna kinfi ƙarfinsa Allah ya isa bamu yafe miki ba, tunda ke bazaki taɓa yin hankali ba…” Ya faɗa a zafafe yana sauke numfashi, sake rushewa da kuka Farida tayi har tana jan numfashi kamar zata shiɗe saboda baƙin ciki, nan Umma ma ta ƙara dasawa sukayi mata tass, abin mamaki Goggo Abu na zaune tayi laƙwas sai bin kowa da kallo kawai take ta kasa magana.
Baba Hakimi ma yayi mata faɗa sosai sannan ya haɗa har da Tahir shima yayi musu faɗa kafin ya ɗora da faɗin “Kiyi haƙuri Farida ki rungumi Mufeeda ki tausayawa rayuwarta, ki zauna da ita lafiya kinga marainiyace, ki ƙara riƙeta kamar yanda kika fara riƙeta ada..idan cikinta ya isa haihuwa watan ya tsaya Innaro zata zo can gidan naku ta zauna don ta riƙa kula da ita har ta haihu..” Ya faɗa yana ƙara lallashin Farida kan ta zauna lafiya da mijinta ta kula da ‘ya’yanta.
Daga ƙarshe dai Baba Hakimi ya saka musu albarka tare da yi musu fatan alkhairi da gamawa lafiya dukkansu.
Nan Tahir ya matso gaban Abba ya duƙar da kai bai ce komai ba, lura da hakan da Abba yayi yasa yace “Me yake faruwa ne Tahir.? Ko akwai wata matsala ne kuma…?” Jinjina kai Tahir yayi alamar Eh.. Abba na gyara zama yace “Ka faɗa min ko mene ne Tahir insha Allahu indai inada dama Allah ya bani iko zanyi maka maganinsa…” Cikin jin daɗi Tahir ya ɗago yana faɗin “Dama Abba inaso ne ka roƙi Baba ya yafewa Goggo Abu..” Ya faɗa yana jin ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa, saurin ɗagowa Abba yayi yana kallon Baba Hakimi, kafin yayi magana Baba Hakimi ya rigasa yana murmushi yace “Na riga na yafe mata duniya da lahira, Allah kuma ya yafe mana baki ɗaya ya kiyaye gaba..” Da Ameen duk suka amsa, kafin Tahir ya fara miƙewa Shida Ishaq suka fita daga ɗakin suka nufi ƙofar gida gurin Sauran Jama”an Dake Wajen Wadanda Suka zo Addu”arku Uku ba Dadewa sai ga Su Abba Suma Sun Fito Suna Tattaunawa shida Baba Hakimi.
A ranar Umma da Abba suka koma Kano, da yamma suma su Tahir da Farida da Iya da Mufeeda da yara duk suka tattara suka yi shirin komawa Kaduna, mota biyu sukayi Tahir da Farida da Mufeeda suka shiga motar Ishaq, su kuma Basma da Bassam suka shiga motar Tahir da Garzali ya tuƙo suka ɗauki hanya, bayan sun bar motar Farida a nan gidan Baba Hakimi akan washegari Garzali zai dawo ya ɗauka.
******
A hankali abubuwa suka fara daidaita, sai dai Farida tana tsananin kishin Mufeeda, amma tana ƙoƙarin dannewa bata son a gane, don irin tsantsar kulawar da Tahir ke nuna mata kwata kwata bata so, amma tana yi tana dannewa, bata so a gane tana jin haushi.
Haka a ɓangaren Tahir shima kwata kwata baya ganin hasken Farida, don ta gama sire masa gaba ɗaya a ransa, daurewa kawai yake yana nuna kulawarsa a kanta, kuma yana ƙoƙarin sauke hakkinta dake rataye a wuyansa, amma duk ɓoyewarsa sai data gane, don a komai ya ƙara canza mata sosai, kusan rabin kulawarsa gabaki ɗaya yanzu duk ya ɗorata akan Mufeeda ne.
A lokacin ne kuma su Mufeeda suka shiga Jss2 suna ci gaba da karatunsu, bata da matsalar komai ta ƙara wani kyau da haske, sai dai kusan kullum kafin tayi barci sai ta tuna da Innarta, idan tai kuka sai ta share hawayenta kuma tayi mata addu’a.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya wani lokaci aji daɗi wani lokacin kuma aji akasin haka,Farida Bata Kaunar Ta Bude Ido Taga Mufeeda da Ciki Acikin gidannan Tsoronta Daya ne Abba da Umma Tasan yanzu Abu kadan Zatayi Suyi Fushi da Ita Sosai,Abunda kuma ke karamata Kishin Mufeeda Shine ganin yadda Tahir ya Watsar da al”amarinta bai Cika damuwa da Al”amarinta ba,gasu Bassam Sun ki marata baya Sun bi Bayan Mahaifinsu,Haka Suke Kafa kafa da Mudeeda kamar su lasheta komai take bukata tana samu Koda yaushe Cikin Tallalinta Sukeyi.
Tuni Farida ta Watsar Da Shawaran Kawayen banza,Tunda Agroup Dinsu Billy Taje Tana bada Lbrin Zata kwatar mata yanci Ta gayamata mgana Ranta ya baci,ta Shiga group din Ta maida mata martani Tamata Wankan Tsaki Billy Tasan bata da gaskiya Sai ta kama kame kame,anan Akayita bata Hakuri Daga karshe Fitama Farida Tayi Daga Group Wasu Dadama Sun Bita Suna bata Hakuri Suna Fadamata Kowa Data gani Anan yana lallaba Aurensa ne,ba wani mai Sakaci,sai Lokacin Farida Tagane tayi Wauta babba..Wato Duk Acikinsu itace Sakarya Tayi Kuka Sosai kamar Ranta zai Fita Tayi Nadama sanda bashi da amfani,Tadaina Fita kwata kwata Wanda Ta gyara Domin Shi ko kallo bata Isheshi Ba Domin yafi Nuna kalawarsa Akan Mufeeda Fiye Da Ita,Abunda yasa Farida Rama kenan Atsaye Duk tayi Wani Zuruzuru Da Ita.
***********
*BAYAN WATA SHIDA*
Cikin Mufeeda ya ƙara fitowa sosai yayi girma gwanin ban tausayi, Tun yana Wata Hufu Tafara Zuwa Awo Anan Iyali Hospital,kuma shi yake kaita watarana In yana da Lokaci Ranar dai bai samu Zuwa ba sai Garzali ya kaita ita da Innaro,tsufan cikin nata ne, yasa Tahir ya hanata zuwa islamiya yace ta riƙa zama a gida makarantar boko zata rinƙa zuwa kaɗai, duk ranar da ba makaranta tana zaune a gida, hakan yana ƙona ran Farida sosai ya baƙanta mata zuciya, don ta tsani ganin cikin bata ƙaunar tayi tozali dashi kwata kwata a rayuwarta, jira take kawai Mufeedan ta haihu Tahir ɗin yasan nayi da ita.
Baba Hakimi ya cika alƙawari Tahir na sanar Dashi Cikin Mufeeda ya Cika Wata Tara yace ya Aiko Garzali ya Ɗauketa, nan da nan kuwa ya aikashi sai ga Innaro Ta Iso Abunda ya ƙara baƙantama Farida rai ganin Ɗakin Mufeeda Tahir yace A sauketa Suna Murna kamar ba Ɗan Shege za’a Haifa ba, Haka Tazo da Jiƙe jiƙe Saboda Maganin sanyi, Take Ta bama Mufeedan Ita da Iya ba’a san Wanda yafi Wani kula da Mufeedan ba, Goggo Abu kuwa Batama ta Farida yanzu Domin Da ƙyar ta samu bayan Abba ya saka Baki Hakimi ke Kulata Ko a hakan ba kamar baya ba, Shiyasa Take ƙoƙarin gyara Kuskuranta ta kuma Ƙudirci Wani Abu A ranta Jira kawai Take Allah ya Sauke Mufeedan lafiya Ta Aiwartar da Ƙudirinta Domin yanzu Tausayin Mufeedan Take Kullum Cikin Kira Take awayar Innaro Ana bama Mufeeda Tana Tambayanta Me take ji..? Wani Lokacin Dariya kawai Mufeeda keyi bata cewa komai Domin Yawanci Tambayan Tahir kenan Inya Shigo Dubata da Safe da Kuma bayan Ya Dawo ko Shi bata bashi Amsa sai dai ta Sunkuyar Da kai Aranta Tana Jin Daɗin yadda Daddy ya fara maida Jikinshi ba kamar Farkon Al’amarin ba.
“”Ɓangaren Kayan Haihuwa Kuwa Babu Abunda Tahir bai gama Siya ba Kuɗi masu yawa ya Ware ya bama Matar Ishaq Zahra ta sayo komai da komai Kayan jariri kuwa komai Biyu ta Siyo na Mace Dana Namiji Tace Saboda Tahir bai yarda an mata Scanning ba, balle aga mai Zata Haifa.+
Kuma Zahran Da kanta ta kawo Kayan Gidan, Abunda Ya ƙarama Farida Ciwo yanzu Har Takai matsayin da Bata da Wani amfani Wajen Tahir, ya maida kanshi dashi da ‘yan’uwansa da Iyayensa Wajen Tattalin Mufeeda, Sai dai Tayi Wuni Cikin Ɗakinta Taita kuka bamai lallashinta Ita baga kulawan Miji ba Haka Zalika ma Su Bassam banda Gaisuwa babu Abunda Ke Haɗasu Koda yaushe Suna Ɗakin Mufeeda suda Iya da Innaro Wani Lokacin Tana Falo sai dai Tajiyo hirarsu Da Dariyansu Mufeeda kuwa Ko ta ganta ta gaisheta Farida bata amsawa Sai dai Ta bi Cikin Jikinta da kallo Cike Da Kishi ganin yadda yayi Girma yana Neman Rinjiyan Mufeedan, Burinta da Fatanta Allah Ya Sauke Mufeedan Lafiya ta ƙara gaba Allah barshi abunda Zata Haifa In Ta gama Shayarwa akaisa gidan Marayu Domin ba Wanda Zai Gurɓata mata ‘ya’ya dana Shege
******
Yau ɗin takama Jumma’atu Babban Rana ce, Misalin ƙarfe 9 na Safe Duka suna Zaune A falo Suna Hira Innaro, Iya da Basma sai Bassam Dake wasa da Naila Wacce Take Tafiyanta yanzu Sai Mufeeda dake Zaune kasan Cafet Ta Buɗe ƙafa Hannayenta na Baya ta Dafa ƙasa Ga Cikinta nan Wani Randa guda yayi girma sosai har yayi ƙasa, Ta kumbura Ko’ina na Jikinta ya Buɗe ya ƙara Girma, In ka kalleta Farat Ɗaya kamar ba Mufeeda ba Domin Ta Cika Ciki ya sakata tazama ƙatuwa, su Basma suna Hutun Ƙarshen Shekara in suka koma zasu Shiga jss3 hadda kawai Suke Zuwa yanzu da Islamiya.
Aya ce agabanta Tana ci Tana Dariyan Labarin da Iya ke basu na Matar ƙaninta da Ta faɗa masai, Basma Saboda Dariya Harda Riƙe Ciki, Mufeeda ma Dariyan Take lokaci Ɗaya tana Cin Ayanta, Farida Data Sauko Daga Sama ta bisu da kallon Takaichi Da ƙyar ta iya Buɗe baki Ta gaida Innaro, Iya ta gaidata Hakama Su Basma Duk ta amsa amma Mufeeda na Gaisheta tayi kamar bata jiba ta Shige Kichen Abunta Mufeeda bata damu ba Domin Inda Sabo ta Saba da Hallayar Farida.
Ruwa ta Ɗauko Kafin Ta sake Haurawa Sama Ƙofar Bedroom D’in Tahir Tabi da kallo, Tun Jiya Daya Dawo Daga Lagos bai sake Fitowa ba, Buɗe Ƙofar tayi Ta Shiga ta Iskeshi kwance Cikin Bargo yana barci Ƙyalesa Tayi Ta Fito Daga Ɗakin Tana Tunanin gajiyace Domin Wajen Satinsu Daya achan Shida Ishaq ne Suka Tafi Taran Sabbin Motocinsu da Zasu zo ta Jirgin Ƙasa, Toh basu iso ba Sai Shekaran jiya Da Daddare Su kuma jiya suka taho Zuwa Kaduna.
Ɗakinta ta koma ta Sha Ruwa kana Ta Koma ta kwanta Tana Tunanin Da Zarar Mufeeda Ta Haihu Ta bar mata gida Zata gyara Duka mu’amalanta da Mijinta Harda ‘ya’yanta Batasan Cewa Lokaci Tuni ya Ƙure mata ba.
Mufeeda Dake Dariya Ƙasa ƙasa, Taji kamar bayanta ya amsa Da Sauri ta gimtse Dariyan Tana jin Lokaci Ɗaya maranta ya Ƙulle, Cije baki tayi ganin ba Wanda ya lura da Halin Data ke ciki Ta Dafa Kujeran Ta Miƙe A hankali Tana Cije baki Lokaci Ɗaya Innaro da Iya Suka kalleta kafin Innaro taceb”Mufeeda lafiya..? Ina zaki Haka..?”
Saurin Sakin Murmushi Tayi kafin tace “Bakomai Innaro Toilet zan Shiga..” Innaro tace “Ayyah..Jeki Dawo..” Ta faɗa Tana kallonta da Sauri Mufeeda ta Fara Taku Zuwa Ɗakinta Tana Daurewa amma Fa Cijewa kawai take saboda yadda Ƙugunta ya Riƙe ga Maranta ta Ƙulle Waje Ɗaya,bHar ta Shige Ɗakinta Innaro na Binta da kallo kamar tana so Ta Ɗago Wani Abu…
STORY CONTINUES BELOW

Mufeeda Da ƙyar Ta iya kai kanta Tsakiyar Ɗakinta kafin ta Durƙushe Tana Riƙe gadon Hannu Biyu Jin Ƙugunta kamar zai Tsage gida Biyu, Zufa ce ke Keto mata kamar Wacce Ake Gasawa Salati Mufeeda ke Saki Cikin Ranta Lokaci Ɗaya Hawaye na Wanke mata Fuska ko Bata sani ba Wannan Azaban Data keji Ta Gane Naƙuda ce, Tun Abun na Ƙasa ƙasa Har ya gagari Tunanin Mufeeda Kuka Take Wurjajan da Majina Domin Tagama Yanke Kauna wallahi Mutuwa Zatayi domin Wannan Azaba Ta mutuwa ce.
Innaro ce Taga Shirun na Mufeeda Yayi yasa Ta kalli Basma Tana Faɗin “Ke Basma Maza Tashi ki Dubo min Mufeeda najita Shiru ne..” Da Hanzari Basma Ta Miƙe Ta Nufi Ɗakin Mufeeda Halin Data Tarar da ita ya bata Tsoro Cikin Firgici Tace “Innaro kuzo kuga Mufeeda..” Ta fada da Ƙarfi Jin Haka yasa Innaro da Iya Suka fara Rige Rigen Shiga Ɗakin Mufeeda Hankalinsu a Tashe, Bassam Dai Naila ya Ɗauka Wacce Ta Fashe da Kuka lokaci Ɗaya bai bisu Ɗakin ba ya dai Tsaya A falon yana Tunanin ko lafiya…
Kallo Ɗaya Innaro Tama Mufeeda Ta Fahimci Tana kan Gwiwa Basma Ta kallah Wacce Har Ta fara Hawayen Tausayin Mufeeda tace “Maza kije ki kira min Daddynki..” Da gudu Basma Ta Fita ta Haura sama Tahir na kwance Cikin Barci Yaji Basma na Faɗin “Daddy Daddy…Ka Tashi Innaro na Kira Mufeeda Zata Haihu Tana ta kuka..” Take Faɗa Tana Kuka Itama.
Zumbur ya Miƙe Daga Kwancen Yana Kallon Basma Ido ya Zaro yana Faɗin “Zata Haihu kika ce Basma..?” Kai ta gyaɗa mai tana Share Ƙwallah da Hanzari ya Dirko Daga kan gadon Da gashi sai Dogon Wando Jallabiyansa ya Laluba ya saka ya zari Key ɗin Mota ya Fita Da Sauri Basma Tabi Bayanshi Fitowarsu Da Hanzari ya Fito Da Farida Daga Ɗaki Ganin Tahir da gudu ya Sauka Ƙasa yasa Itama Tabi Bayansu da Sauri Tana mamakin Me ya Razana Tahir Lokaci Ɗaya Haka..?
Tahir ko na Shiga Ɗakin Mufeeda Yaga ba yarda Take Innaro na mai magana bai Saurareta ba kawai ya Cicciɓi Mufeeda Zuwa Waje yana Faɗin “Innaro ki Ɗauki Mayafi mutafi Asibiti..” Farida Dake Ƙoƙarin Shiga Ɗakin Mufeeda Tayi Baya ganin Tahir ya Ɗauko Mufeeda Tana Faman kuka tana Yarfa Hannu, suman Tsaye Tayi Cike Da Takaichi da Kishi Wai Tahir ne ya Ɗauki Mufeeda da Hannunsa Niko Nace Yamata Cikin ma balle Ɗauka.
Bata gama Mamaki ba Iya da Innaro Da Suka Rufa mai baya Da Gudu Mayafai A hannu Saboda Zullumi sai ga Basma Ita ma da Hijabi Ta Runtuma tabi Bayansu, baki ta Riƙe Cike da Baƙin ciki Lokaci Ɗaya kuma Falon ya ƙara Ɗaukan Kukan Naila, Daga Nailan Har Bassam D’in Da Harara Ta Bisu kafin Ta Saki Tsaki ta koma Sama Tana Ƙunƙuni Ita kaɗai.
Tahir ko Garzali bai Saurara ba ya Kai Mufeeda Bayan Mota, Ya Dawo Gidan Gaba Mazaunin Direba ko Su Innaro Dake Fitowa Haraban Gidan bai Jira ba ya Kunna Mota yayi Reverse da Ƙarfi lokaci Ɗaya ya saki Hon ya Fice Da Gudu, Su Innaro basu Tsaya ba Suka Faɗa Mota Basma Ta Shiga Gaba Innaro Tace “Garzali bi mana bayan Attahiru…” Cikin Bin Umarni Garzali yaja mota Yabi Bayan Tahir Daya Nufi Asibitin Iyali Hospital Dake Kusa Dasu.
****
Koda Tahir ya gama Faka Motarsa Cikin Haraban Asibitin Bai Jira Wani ba, Ya Fito Daga Mota ya Buɗe Baya ya Cicciɓo Mufeeda Dake kuka Wurjajan Lokaci Ɗaya Da Salati Domin Ji Take kamar Zata mutu da Gudu ya Nufi Cikin Asibitin Da Ita ganinshi Haka ne ya saka Nurses Da Gudu suka gungoro Gadon Ɗaukan Marasa Lafiya Zuwa Gareshi ganin kamar ya Fita Daga Hayyacinsa yana Kiran Likita.
Kan Gadon ya Ɗora ta da Hanzari Suka Shiga Turata yana Bin Bayansu cikin Tashin Hankali Labour Room Suka Shiga da Ita Suka Rufo ƙofa Dole Tahir ya Tsaya Awaje yana Safa da Marwa sai ga Su Innaro Sun Shigo Asibitin Hankalinsu Tashe Cikin Fargici Innaro Tace “Attahiru Ya Ake Ciki…?” Numfashi ya Sauke yana Faɗin “Bansani ba Innaro Sun Dai Shiga da Ita Ciki…” Gefe Suka Koma kowa na Addu’a Cikin Ransa Basma ko Hawaye Take Sharewa Suna nan Tsaye Wata Nurse Ta fito da Gudu Ta Wuce Office d’in Likita, Sai gashi Sun Fito A tare Cikin Hanzari Sun Koma Cikin Ɗakin Daga Wajen Suna Jin Salatin Mufeeda Da Kukanta Lokaci Ɗaya Tahir yaji Jikinsa ya Saki Ƙwalla Ta Cika mai ido yana Fatan Allah ya Sauki Yarinyar nan lafiya kada ta Mutu Da Cikin nan ya Shiga Uku.
STORY CONTINUES BELOW

Tsawon Awa Ɗaya Likitoci na Shige da Fice kan Mufeeda Haihuwa Shiru nan da nan Suka mata Scanning Nan Suka gano yan Biyu ne A cikinta amma Sun Galabaita, yunƙurin Fitowarsu da kansu Matsala ne, Nan da nan Wani Likita ya Fito Yana Faɗin “Ina Mijinta…?” Da Hanzari Tahir ya Isa Gabanshi yana Faɗin “Gani Dr..Hop ta Sauka lafiya..” Kai ya girgiza mai kafin yace “Biyoni Office da Sauri bamu da Lokaci..” Jin Haka yasa ya bishi da Hanzari, Zuwa Cikin Office Ɗinshi Suna Shiga Ciki ko zama baiyi ba ya Miƙa mai Wata Takarda yana Faɗin “Muna Buƙatar saka Hannunka anan, zamu Shiga da Ita Aiki ne yanzu Domin Ceto Rayuwarta data yaran Dake Cikinta..” Tahir na Zufa ya karɓa Takardan Haɗe da Biron ya Rattaba Hannu, kafin Likitan ya karɓa yana miƙa mai Wata ƙaramar Takarda yana Faɗin “Ka biya Kuɗin Aiki yanzu…” Tahir bai Tsaya ba ya Fito da Sauri su Innaro Dake Zaune Suka miƙe Suna kallonshi Kanshi ya Shafa yana Faɗin “Sun ce aiki zasu mata yanzu…Ku zauna anan Bari naje na Biya Kuɗin Aikin Na Dawo..” Innaro tace “Toh kana da Kuɗi A hannunka..?”
Yana Tafiya yake Faɗin “A’a Sai dai Atm ɗina zanyi Amfani Dashi..” Ya faɗa yana Ƙara Sauri Cikin Minti goma Sai gashi ya Dawo da Resit ya Riga ya Biya Kuɗin Aikin bai Daɗe da Isowa Wajen ba Sai ga Mufeeda An Gungurota Zuwa Ɗakin Tiyata an Chanza mata kaya, Kuka Take da Salati Lokaci Ɗaya Suna kallo Aka Shiga Da Ita Gefe Suka koma Kowa Da kalan Addu’an Dake Ranshi barin ma Tahir da Abun Duniya Suka Taru Suka mai yawa…
Shuɗewar Awa Biyu Kafin wasu Nurses Guda Biyu Su Fito Daga Ɗakin Tiyatan Ɗauke da Yara Guda Biyu Cikin Wasu Showels, da Hanzari Suka miƙe Suna kallonsu Cikin Fara’a Ɗaya Tace “Congratulation ta Sauka An Samu Twins, mace da Namiji…” Gaba ɗayansu Suka Haɗa baki Wajen Faɗin “Alhamdulillah.” Innaro Ta karɓi Namijin Iya kuma Ta karɓi Macen Dukkansu bakinsu yaƙi Rufuwa Shiko Tahir Hamdala yake Acikin Ranshi kafin yace “Ina ita Maman Yaran..?” hope tana lafiya..” Ɗayar tace “Eh ana gyarata ne da Zarar an kammalah zamu maidata Ɗakin Hutu..” Daga Haka Suka Wuce, Chan sai ga Likitocin Suma Sun Fito Suna Cire Safan Hannu, Musabaha sukayi da Tahir Suna mai Murna, Bakin kowa yaƙi Rufuwa, Bai Ɗauki yaran ba Domin Wani Tausayinsu ne ya Tsirga mai na Ya samar Dasu Ta Hanyar da bai dace ba, Ashe Dalilin Daya sa ya Afkama Mufeeda Kenan Rabon samun Waɗannan ne ya Kawo Haka.
Ba ɓata Lokaci aka Gunguro Mufeeda Zuwa Ɗaki na Mussaman Domin Hutu, Suka ce Kar wanda ya Shiga Inda Take Sai ta Farfaɗo bayan Awa biyu da wani Abu, Yanzu aje azo da kayan Jarirai da Kayan Tea d’in da Mai Jego zata Buƙata in ta Farfaɗo, Tahir ne ya barsu anan ya Koma gida, Farida na Jin Dirin Mota ta Zabura ta Fito Falo Suka Ci karo da Tahir Cikin Rawan Baki Tace “Ta Haihu..?”
Bai kalleta ba yace “Eh amma C.s Aka mata an Ciro ‘Yara Biyu mace da Namiji..” Dafe ƙirji Farida Tayi kafin Tace ” ‘Yan biyu fa kace…?” Ta faɗa Tana kallonsa Bai mata magana ba illah binta da Kallo Da yayi kafin yace “Eh Abunda Kunnenki ya jiye miki…” daga Haka ya Wuceta ya Barta sama ya Koma ya Ɗauko Wayarsa ya Sauko, Ɗakin Mufeeda ya Shiga Inda ya Tatarro Duka kayan Babies, Sai kuma Dogayen Riguna da Riga da Zani, ya Fito Nan ya Wuce Farida Tsakiyar Falon Tana Binshi da Kallo, Bassam ne ya Biyosa yana Tambayansa Mufeeda Ta Haihu Cike da Fara’a Tahir ya Ɗaga mai kai kafin yace “Kun samu ƙanne Bassam ‘Yan’uwanku ne Twince ne Suma..” Washe Baki Bassam yayi Harda Tsalle yana Faɗin “Daddy Zan Bika..” Bai ce mai komai ba sai ma Miƙa mai Jakar Kayan Mufeeda da yayi Suka Fice Daga Falon.
Sai da Tahir ya kawo Kayan Kana Aka maida Yaran Ciki aka Sake Gyarasu aka Shiryasu Cikin kayan Sanyi pick masu kyau Ɗakin da Mufeeda Suke Suka maidasu, suka ce suma abarsu Su Huta Haka nan, Bakin Basma da Bassam yaƙi Rufuwa saboda Murna Sai Lokacin Tahir ya samu Damar Kiran Baba Hakimi yake Sanar Dashi Baba Hakimi Dake Shirin Fita Sallar Azahar ya Washe Baki yana Faɗin “Kai Masha Allahu…Allah ya inganta..” Daga nan Abba ya Kira Shima ya Sanar Dashi, Shima ya Saka albarka, Daga Abba sai ya Kira Ishaq ya Sanar mai, Wanda ke Zuba kabbara Cikin Waya kafin Kace me Haihuwan Mufeeda Ta isa Kunnan Wanda ya kamata Farin ciki kamar bata Gurɓattaciyar Hanya aka samesu ba.
****
Baba Hakimi Na gama Waya da Tahir ya Shiga Cikin Turakarsa ya Ɗauko Huhun Goro da Dabino Cikin Wata Leda Waje ya Fita Zuwa Masallacin Kusa da gidan nashi Lokacin Har An Tada Sallar Jumma’a Domin Babban Masallaci ne Wanda ke Jikin Gidan nashi Inda Suke Gudanar da Sallar Jumma’a.
Bayan An idar da Sallah Baba Hakimi Ya bada Sanarwan Akwai ɗaurin Aure nan da nan ko Kowa ya Matso kuɗi ya Fito Dashi Duba 30k ya bama Liman yana Faɗin “Ina so kazama Wakilin Ɗana Tahir, ni kuma zan zama Wakilin Mufeeda A Ɗaura musu Aure..” Liman ya Washe baki ba tare Da bata Lokaci ba nan Take Shaidu Suka Shaida Ɗaurin Auren Tahir Mansur Ɗanbatta da Mufeeda Bello Ɗanbatta, Auren Daya bama Kowa Mamaki Domin Mutane Da dama Sun san Mufeeda A matsayin Wacce ke Reno A gidan Tahir, Cikin Fari ciki Taro ya Watse bayan an Raba Goro da Dabino Baba Hakimi ya ɗibi Wasu ya Shiga Dasu Cikin Gida Har Ɗakin Goggo Abu Wacce ke Cike da Murnan Wayar Da Tahir ya mata yanzu Yana sanar da Ita Haihuwan Mufeeda, goro da Minti ya miƙa mata yana Fadin “Na Ɗaura ma Tahir Aure da Mufeeda Yanzu bayan Mun Sauko Daga Sallar Jumma’a…” Baki Goggo Ta Washe kafin tace “Mallam kamar kasan Abunda Ke Raina kenan…Allah ya basu zaman lafiya..” Da Ameen ya amsa Cikin Jin Daɗin Haɗin kanta Duk Da yasan bazai Samu Matsala ba.
******
Har Yammah Su Innaro na Asibitin Sun cika Ɗakin da Mufeeda Take bayan ta Farfaɗo, Basma da Bassam Sun ƙanƙame yara Ko Tahir basu Bari ya Ɗauka ba, sai da Innaro ta karɓe Macen Ta Hannun Basma Ta Miƙa mai ya karɓa Cikin Jin kunya Lokaci Ɗaya yana Tsurama Jaririyar Ido Sak Basma Tana Jaririya, Lokaci Guda Idanuwansa Suka kawo kwallah yayi Saurin Mayar Dasu Mufeeda Dake Jingine da Gado Tana kallonshi yana Dagowa Suka Haɗa ido sai tayi Saurin Kauda kai Murmushi yayi ya ƙarasa Kusa da Ita yana Faɗin “Mufee ya Jikin..?” Kanta na Ƙasa Tace “Da Ɗauki Daddy…” Kai ya gyaɗa kafin yace “Masha Allah…Allah ya ƙara baki lafiya..” Da Ameen Ta amsa Ƙasa ƙasa, kan Jikinta ya Ɗora mata Jaririyan Yana Faɗin “Kina Sonta…?” Kallonsa Tayi kafin tace “Kaifa kana Sonsu…?” Kai ya Gyaɗa mata kafin yace “Ina sonsu Sosai kuma Zan Cigaba da Ƙaunarsu Har Ƙarshen rayuwata..” Murmushi Ta Saki kafin tace “Nima ina sonsu….” Dariya yayi yana kallonta kafin ya Miƙa Hannu ya karɓi na Hannun Bassam ya Ɗora mata Bisa Jikinta yana Ƙoƙarin Zama Kusa Da ita Wayarsa ta Shiga Ƙara Miƙewa yayi ya Zarota Ciki Aljihu sai yaga Hakimi ne Da Hanzari ya Fice Mufeeda ta Bisa da Kallo Cikin Wani yanayi.
Fita yayi Haraban Asibitin kana Ya Ɗaga Kiran Cikin Farin ciki Baba Hakimi yace “Ya Wajen Maijegon da Sabuwar Amarya don bazan Tambayi sabon Megidan Salamatu ba Tunkafin ya Fito Duniya Take Nuna min Son kai..” Dariya Tahir yayi kafin yace “Duk Suna lafiya Ranka ya Daɗe..” Baba Hakimi yace “Madallah kafin ya Zarce da Faɗin “Attahiru na yanke Wani Hukunci ba tare Da nayi Shawara Da kai ba Domin ina ganin Hakan Shine Daidai..” Tahir ya Jinjina kai yana Faɗin “Ka isa ne Ranka ya Daɗe kowani Hukunci ne zan karɓa Hannaye Bibbiyu..” Baba Hakimi ya saki Murmushin Jin Daɗi yana Faɗin “naji Daɗin Haka ba Komai Illah Ɗazu bayan sallar Jumma’a Na Ɗaura maka Aure da Mufeeda yanzu Haka tana Matsayin Matarka ne Attahiru..Bata da wanda ya fika ku Haɗu ku Rungumi ‘ya’yanku Karsu Tashi suga bakwa Tare Su Tuhume ku Wata rana..” Ajiyar Zuciya Tahir ya Sauke kafin yace “Hakane Baba…Allah ya bani ikon Adalci..” Da Ameen Baba Ya amsa kafin Su yanke Kiran Bayan Baba Hakimi ya tabbatar mai Suna Tafe ko yaushe.
Bai koma Cikin Asibitin ba yayi Tsaye yana Tunanin Wannan Al’amarin Guda Biyu Lokaci Ɗaya Haihuwa da Aure, Dafe kansa yayi yana Faɗin “Alhamdulillah…Allah ne Abun Godiya..” Yana Cikin Wannan Halin ya hangi motar Ishaq Ta Shigo Cikin Asibitin Bai Matsa daga Wajen Ba Har Suka ƙaraso Shida Zahra ta gaisheshi Bayan Ta mai barka, Shi ya musu Jagora zuwa cikin Ɗakin Suka Gaida Mufeeda Suka kuma Ɗauki Yaran Bayan Sun gaisa da su Innaro Nan Suka bar Zahra Tahir yaja Ishaq suka Fita Waje Cikin Damuwa ya labarta mai Abunda Baba Hakimi ya Kirasa ya gaya mai Baki Ishaq ya Washe kafin yace “Finally…Baba Hakimi ya gama maka Komai Friend…Mufeeda Ta Chanchanci Haka Domin Bata da Wani Gata Nan Duniya bayan kai…Gaskiya Allah sakama Baba Hakimi da alheri Yayi Abunda ya Dace..” Tahir dai Shiru yayi yana Jin Ishaq Shi kuma yana Cigaba da Bashi baki basu koma Cikin Ɗakin ba sai da Sukayi sallar Mangariba, suna komawa Tahir yace Su Basma Su Shirya su Koma gida, Harda Iya gobe da Safe sai su Dawo Innaro kaɗai Aka bari zata kwana da Mufeeda, Zahra tayi musu sallama Bayan ta ijiye musu kwandon Abincin Da tazo Dashi. Tare Suka Fita Bayan Tahir yayi musu Sai da Safe Mufeeda kuwa na Kwance Tana Binsu da kallo har Suka Fice Daga Ɗakin.
“””Suna Shigowa gidan da Farida Suka ci karo tana Zaune Afalo Tana Zare ido Domin gama wayarsu kenan da Umma tana Tambayanta ya Wajen masu jego tace suna lafiya tanama Asibitin ne Tafito amsa waya ne,Umma taji Dadi tace mata suna nan Zuwa Cikin Satin nan Ita da Abbanta……+
Daga Tahir har ya”yansa Babu Wanda ya Tankata Kowannensu Dakinsa ya Nufi Haka Shima Tahir ya Haura sama ya Fada Dakinsa A matukar gajiye yake Shiyasa yafada wanka,Iya ce kadai ta iya tsayawa tana gaida Faridan wacce Tabi su Basma da kallon Mamaki,Tahir ta Daina Damuwa dashi Domin baya Shiga Harkanta Tuni.
Bayan ta amsa gaisuwan Iya ne ta kalleta tana Fadin”Wai iya da gaske ne Mufeeda yan biyu ta Haifa…? Gyada mata kai Iya Tayi Lokaci Daya tana Washe baki tace”Eh Hajiya mace da Namiji yara nan kamar su Basma suna Jarirai inji innaro..”Harara Farida ta Zabgamata Lokaci Daya Tana Fadin”Kul kar na sake ji…Ni ya”yana na Sunnah ne karki kara Hadasu da Shegu wanda ba ya”yan Sunnah ba..”Cike da mamaki Iya ke kallonta bata samu Zarafin mgana sai ma gyada kai Datayi ta juya Zuwa Daki bayan ta kalli Naila dake barci kan kujera tagaji da kuka Barci ya kwasheta.
Da Harara Farida ta Bita kafin ta koma ta Zauna tana karkaɗa ƙafa, Iya tana Komawa ɗaki ta Fito ta Shiga kichen domin sama musu saukakkan Abinci da zasu ci Shiko Tahir Bayan ya Fito Wanka yayi sallar Isha’i da Shafa’i da Wuturi ya koma ya kwanta domin Haka kurum yaji Cikinsa ya Cika baya Sha’awan Cin komai kwance yake kawai yana Tunanin Wai shi yanzu mijin Mufeeda ne, Lalle Allah ne mai Tsara komai kuma ya aiwatar yana Fatan Allah yasanya alheri yabashi ikon kwatanta Adalci Domin baya ta Farida Ita yanzu bazai ƙara Ɗaukan Wani Iskancinta ba, Itama ta sani.
Da Iya ta gama Dafa musu macaroni da Kifi, Su Basma kaɗai Suka ci sai Iya ko Farida bata ci ba ɗaki ta koma tana kukan Bakin ciki da Takaichin Wai Mufeeda Ta haihu har ‘ya’ya biyu lalle ma wato zata Haɗa kafaɗa da ita, ba wanda yabi ta kanta Har Washegari da Safe Tahir ya Tafi Office Su kuma Iya da Basma da Bassam da Naila data saka Rigimar sai ta tafi Tahir baima sani ba Ya bari sai zuwa yammah su koma Tunda ya tafi musu da Abun karyawan da Iya tayi musu Ashe su kuma suna Gama Dafa na Rana suka tafi dashi Keke Napep Suka Shiga Zuwa Asibitin Suka bar Farida agida tana kallon ikon Allah.
Sanda suka isa asibitin ma Sun Iske Zahra matar Ishaq itama ta kawo Abinci Mufeeda na Zaune Innaro na bata Tea abaki Taji Sauƙi ba kamar jiya ba, Namijin ne ke Hannun Zahra Shine mai Rigima macen na kwance Tana barci Naila Haka ta saka Rigiman sai an bata Ta Ɗauka ganin Su Basma Sun Ɗauka harda kukanta Su Iya na mata Dariya, cikin ikon Allah Ruwan Nonon Mufeeda ya Fara Zuwa ba laifi Tunda Dukkansu suna samu Suna Sha Duk da baya isarsu Da Safe ma da Tahir yazo Likita yamai maganar za’a Haɗa musu da madara saboda kada yunwa ta kamasu.
Kumburin Jikin Mufeeda ya Ragu amma ba Sosai ba, Sunyi Waya da Baba Hakimi da Goggo Abu Awayar Innaro Kunya Mufeeda keyi Jin Suna Tambayanta Ya Jikinta bata magana sai dai Murmushi Suna nan har Dare nan Ishaq da Tahir suka samesa bayan Sun Dubata Suka Wuce gida Gaba ɗayansu bayan ya kawo musu Kayan marmari da Nama gashasshe saboda Mufeeda Ta maida Jikinta.
Haka Suka Din gayi Har Tsawon Kwana Biyar, amma Farida bata taka Asibiti ba sai Ranar da Mufeeda ta cika kwana Shida taji Sauki ma, har ta fara Zuwa Bayi da kanta aikin ya fara Bushewa, Farida kunya taji Yasa ta Shirya taje Asibitin Aikwai Tayi Nadama Sosai Domin ba wanda ma yabi Ta kanta Bata Raina kanta ba sai da Yammah Bayan Tahir ya Shigo Asibitin yana Shigowa Ɗakin Su Basma da Iya da Innaro Suka Fice Suka barshi amma ita sai ma gyara zama Datayi kuma Abun Haushi ko Yaran bata Ɗauka ba Daga Cikin gidansu ta leƙasu Idanuwanta na kawo ƙwallah ganin Tsabar kama da Tahir da yaran Suke ko Mufeeda Da ƙyar ta iya gaisheta ta amsa itama ta kauda kai saboda Nauyi Itako Hararanta kaɗai take Acikin Ranta tana Faɗin “Kin kusa bar min gida makira..”
STORY CONTINUES BELOW

Bata gama Jin Nadama ba sai Dataga Tahir ya Shigo ko ɓarayin Datake bai kallah Data gaisheshi ma Kansa na gefe ya amsa, amma yana isa kusa da Mufeeda ya saki Fuska yana tambayanta ya Jikinta ita kuma Munafukar tana Sunne kai Numfashinta bai kusa Ɗaukewa ba sai taga ya zauna gefen Gado ya Duƙa yana ma yaran Wasa Mufeeda kuma na kallonsa Tana Murmushi, macen ya Ɗauko yana Faɗin “Yarinyar taso ta ɗauke ki fa Mufee..? Ya faɗa yana kallonta.
Sunne kai tayi Tana Murmushi batace komai ba, sake kallonta yayi yana kallon Jinjiran kafin yace “Kila yau ko gobe ku koma gida, in kun koma sai mu Shawaran Wasu suna zasu saka musu..” Kan Mufeeda na ƙasa tace “Basai kayi Shawara dani ba Daddy Duk Sunan da ka saka musu Dai-dai ne..” Ta faɗa tana Wasa da Hannayenta Kallonta kawai yake yi Tausayinta na ƙara Shiganshi kaɗa kai yayi yana Faɗin “A’ah…zamu magana in kun koma gida kema kina da Hakki yaranki ne..” Bata sake magana ba illah Kallonsa Datake kasan Ido bataso ya Fahimci Tana kallonshi batasan kuwa yana Kallonta ta gefen ido sai dai yayi murmushi kaɗai
Farida Dake Zaune ba tasan Sanda Ta miƙe A fusace ba tana Faɗin “Asirin mutum ya Tonu yace Ƙaddara ne, Kuma ko kunya Yazo yana Abu goɗai goɗai, Wlh mutum bai isa ba Zuwa za’ayi abar min gida Nida Mijina da ‘ya’yana, bana son karuwancin Ƙauye..” Ta faɗa tana Ficewa Daga Ɗakin Daga Mufeedan Har Tahir da ido Suka bita Shiko Tahir ko Damuwa da kalamanta baiyi ba Mufeeda ce Idanuwanta Suka cika da Hawaye Tahir bai ce mata komai ba Cikin Ranshi Dariya ce Ke Cinsa na Tunanin yadda Farida zataji in Taji Mufeeda matarsa ce yanzu.
Haka ko akayi Washegari da Safe aka sallami Mufeeda suka koma gida kafin su Dawo Iya da Basma Sun riga sun gyara Ɗakin na Mufeeda suna Dawowa nan suka Sauketa ita da ‘ya’yanta Aranar kuma sai ga Ashe da Tawagarta ita da Laila da Muda tazo da kayan Wanka Goggo Abu ta bata Sakon ta kawo Itama Data Ɗauki yaran Sai da tayi ƙwallar Tausayi da Jinjina ma Rabo, Nan ta kwana Washegari kuwa sai ga Baba Hakimi ya iso gidan bai jima da Zuwa ba sai ga Abba da Umma suma sun iso Tunda Farida Taga Haka Jikinta bai bata ba illai kuwa Domin Taro Aka Sake zama kamar na Farko harda Mufeedan Shiko Baba Hakimi na Rike da Jaririn Namiji Abba na Riƙe da macen Tunda Farida Taga an Kirata Gabanta ke Faɗuwa Tana Addu’an Allah yasa Tafiya da Mufeeda Zasu yi ƙauye.
Bayan Buɗe Taro da sallama da Godiya Ga Allah Baba Hakimi ya Fara Magana yana Cewa “Kowa anan yasan Abunda ya Faru Har Aka samu Waɗannan yaran Munyi Tawassali da Sunayen Allah kuma mun yarda da Ƙaddara..Gashi Ashe Rabon bana Ɗaya bane Rabon Har na ‘ya’ya Biyu ne Hakan Kaɗai ya isa kowa yagane Ƙudurar Allah ne..” Kowa ya gyaɗa kai banda Farida dake kallon kowa ɗai ɗai.
Cikin Dattako Hakimi ya Cigaba da Faɗin “Magana Ɗaya zanyi Zuwa biyu dama Abunda Ya kawoni kenan, na Farko nazo ne naga Ƙaruwar Da aka samu na Biyu kuma na gabatar muku da Hukuncin Dana yanke ko nace Wanda na Zartar nasan Wasun ku sun sani kamar Kai Tahir da Ke Innaro Tare Da Aisha, toh ba wata Magana bace Illah Aranar da yarinyar ta sauka Attahiru na Kirana banyi ƙasa a Gwiwa ba na Biya Sadaki aka Ɗaura musu Aure…” Kowa maganar bata Razana Shi ba Umma da Abba da Iya Cikin Farin ciki Suke Faɗin “Masha Allah hakan yayi Dai dai.
Farida ko Kamar Saukan Aradu Haka Taji mganar Arzane ta miƙe Hannnunta Bisa Ƙirjinta tana Faɗin “Aure…? Mijin nawa kuka Aura mata kanbura uba…” Ta faɗa Tana girgiza jiki, Tahir Da yaji kamar Ta Tsikara mai allura na Zagin Data ƙunduma kafin ya Ɗauki mataki Umma ta miƙe ta Sharara mata mari tana Faɗin “Kinci Ubanki Farida Baban Mijin naki kike cema Kan Bura uba Saboda baki da Tarbiya..?” Kuka Farida ta Fashe Dashi Ta Duƙe tana Faɗin “Wayyo Allah na na Shiga uku ni Farida Ina zan saka kaina kowa baya sona.” Umma ta Ɗuma mata Dundu Tana Faɗin “Eh ɗin ba’a sonki ɗin Uban waye zai soki Kina da Mugun Hali Tir Dake Farida iliminki bai miki amfani ba..” Kuka Farida take kamar Ranta Zai Fita kowa A falon yaji Daɗin Hukuncin Umma Barin ma Ashe da Haushin Farida ya cika mata Ciki Abba ko Kunyace Ta Hanashi Magana Shiko Baba Hakimi mamakin Rashin ɗa’ar Farida ne ya kamashi.
STORY CONTINUES BELOW

Basma da Bassam Dake gefe ko Ajikinsu basu damu da Kukan Da Farida keyi ba sai ma murnan Da Suke Daddynsu ya auri Mufeeda Zasu Dinga ganin Twince dama Fargabansu kar a ɗauke musu su suna sonsu sosai kuma suna son zama da ita.
Mufeeda kuwa kanta na Duƙe Tana Share hawaye Wai Abun Mamaki itace matar Daddy, Lalle Allah mai yarda yaso amma Maganar gaskiya ba’ ajinta bane ya Fita komai da komai, Ta Daɗe tana Fatan Allah ya bata Miji Irin Daddy koda bai kaisa ba koda Rabinsa ne sai gashi shi ɗin Allah ya mallaka mata, Babu Abunda Zatama su Baba Hakimi sai godiya Domin Sun inganta Rayuwarta.
Hakimi ne ya Kaɗa kai yana Faɗin “Banzaci Haka Daga gareki ba Farida..Assha Abun bai min Daɗi ba..Karki manta Mufeeda yanzu amana take garemu, Tun mahaifiyarta na Raye take ƙarƙashin Ikon mu kuma in bai Aureta ba Alhalin Shi ya ɓata mata Rayuwa Wa kikeso ta Aura ga ‘ya’ya baki Tunanin Watarana agoranta musu..? Saboda Haka Tahir shine Rufin Asirin Mufeeda Itama Shine Rufin Asirinta ina Fatan zaku zauna lafiya da Junanku Ku Rungumi ƙaddaranku Tunda Haka Allah ya Tsara muku..” Ko ɗago kai Farida batayi ba sai Gunjin kuka take Baba Hakimi bai Damu ba Illah maida kallansa Da yayi kan Mufeeda yana Faɗin “Kiyi Haƙuri Mufeeda kiyi ma Mijinki biyayyah kuma ki kula da ‘ya’yanki na Tabbata Attahiru bazai barki kiyi Kukan Maraici ba..” Mufeeda kanta na ƙasa Tana Share Ƙwallah tace “Bakomai Ranka ya Daɗe…Bani da Bakin da zan mika godiyata zuwa gareku..Tun Mahaifiyata nada Rai kuke Jin ƙaina kuna Wahala dani, Daddy ya ingata Rayuwata ya Wahala dani ya Tarbiyantar dani kamar ‘yar daya Haifa na yarda Ƙaddara ne ya Faɗa mana Babu Abunda zan ce muku Sai Fatan Gamawa da Duniya lafiya, Allah ya saka muku da Gidan Aljannah Firdausi..” Ta faɗa tana kuka Sosai kowa Afalon sai da kalaman Mufeesda ya Sakashi kwallah Shi kanshi kafeta da Ido yayi yana Jinjina ma Kaifin Tunanin Mufeeda Kukan kuwa kara Narkamai da Zuciya yake.
Baba Hakimi ya Jinjina kai yana Faɗin “Ameen Ameen…Allah yayi muku albarka…Allah ya albarkaci Aurenku ya kuma baku zaman lafiya..” Yake Faɗa yana Share Siririyar ƙwallar Data Zubo mai, Abba ne yayi gyaran Murya yana Faɗin “Masha Allah…Allah ya bada zaman lafiya Haƙiƙa Mansur kayi Tunani mai kyau Allah ya sanya alheri..”
Kowa ya amsa da Ameen Baba Hakimi ne ya kalli Tahir yana Faɗin “Ka sanya musu suna..?” Kai ya gyaɗa kafin yace “Eh jiya da Daddare nayi ma Namijin Huɗuba da Sunanka macen kuma na mata Huɗuba da Sunan mahaifiyar Mufeeda..” Kowa ya Washe baki yana Faɗin Masha Allah Mufeeda kuwa Ɗagowa tayi tana kallon Tahir Lokaci Ɗaya Tana Kuka tana Dariyar Farin ciki Shima Murmushin ya sakar mata.
Baba Hakimi yace “Kai…kai Naji Daɗi sosai nagode..Allah ya Raya Mansur da Hulairatu..” Kowa ya karɓa da Ameen kafin ya cigaba da Faɗin “In zaku yi taron Sunanku Ku haɗashi duka da Tarewar Mufeeda Tunda Duka gida ne, Bana son Bidi’a Komai kuyi shi Lokaci Ɗaya..” Ashe tace “Insha Allahu Baba Dama munyi magana da Yaya Tahir In Sati ya Zagayo za’a Yi Taron Suna sai A haɗa da Tarewarsa Allah ya basu zaman lafiya..”
Ta faɗa tana makama Farida Harara Wacce tabar kuka sai ajiyar Zuciya, babu wanda ma ya ƙara bi takan Farida aka Rufe Taro da Addu’a Baba Hakimi ya miƙama Innaro Takawaranshi Shi kuma Abba ya miƙawa Iya mai sunan Inna Fulera suka Fita Waje, Farida kuwa Umma ta jata ɗaki ta Zaunar da Ita tana Faɗin “Farida..Farida.Farida..!
Ta faɗa tana kallonta Cikin Muryan Ɓacin Rai tace “Farida Sau nawa na kiraki..?” Ta faɗa tana Murɗe mata kunne Cikin Hawaye tace “Sau uku Umma..” Sakin mata kunne Tayi tana Faɗin “Kinga Duk Abunda ya Faru ko..? Kinji kuma kin gani yadda kika zama bora banza a idon Mijinki da ‘ya’yanki harda Dangin Mijinki…ko..?” Kai Farida Ta gyaɗa tana Kuka sosai Umma tace “Toh ya rage naki ki Zauna kima kanki karatun ta natsu In ba Haka ba Wlh Tallahi Tahir zai koreki Daga gidan nan Kina ji kina gani yarinya ƙarama ta ƙwace miki miji Tunda kin zama Sakarya Kina sane yanzu ba Da bane Wlh Tahir bazai ƙara Ɗaukan Abun da ya Ɗauka abaya ba, Ya Rage naki Farida Ki gyara Rayuwarki da Halayyarki in ba Haka ba Wlh Zaki Kwashi Nadaman Dayafi Wanda kike karɓa yanzu, Daga ƙarshe ina Fatan Allah ya Sausauta Zuciyarki ya Kori Sheɗan acikin Rayuwarki.” Ta faɗa tana miƙewa kafin tace “Zamu Tafi..Sai an kwana biyu ƙila nazo Ranar Tariyan, Don Allah Farida ki maida komai ba komai ba, ki nemi Gafaran Mijinki ki kuma Rungumi ‘ya’yanki Da Mufeeda Ko kimarki ta Dawo don Allah ba domin Halina ba…” Ta faɗa Tana Haɗa Hannuwanta Waje Ɗaya.
Farida ta miƙe ta Rungume Umma tana kuka take Faɗin “Insha Allahu Ummah naji maganarki…Nayi miki alƙawarin Zan Chanza Halina Umma zan Nemi gafaran Tahir dashi da Mufeeda Umma, Na gane kuma na Fahimta Duk Abunda ya Faru laifina ne..” Rungumeta Umma Tayi tana Bubbuga bayanta take Faɗin “Naji Daɗin Haka Allah yayi miki albarka..”
Ta faɗa tana Share mata ƙwallah, Har Falo ta Rakota Ta Shiga wajensu Innaro ta musu sallama ta Fice Haraban gidan inda Abba ke Jiranta Daga nan suka ma Tahir sallama suka Tafi, Baba Hakimi ko Tuni Garzali ya Miƙa Dashi Farida kuwa ɗaki ta koma tana kuka Cikin Zuciyarta tana Fatan Allah ya bata ƙarfin Gwiwan Gyara Rayuwarta.