NAYI GUDUN GARA CHAPTER 25

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 25
Yana zaune akan kujera su kuma kowacce na gefe ta Ciki na Clki. Kallonsu ya yi d’aya bayan d’aya daga bisani yaja numfashi yace. “Ladifa.” 
Ta amsa, ya kalli laila itama ta amsa. “Ina son ku fahimceni sosai da kunnen basira, na tara ku ne akan abunuwan da suke wakana a gidan nan, ba naso, ba sai mini dad’i, yanzu ku dan Allah ba abin kunya bane a taradda ku kuna fada kamaryara?.” 
Kallonsu ya kuma yi, ya kalli lad’ifa kanta a sunkuye, laila kuma na girgiza k’afa. 
“Wallahi karna kara ganin wata taimin fada agidan nan, ba ruwan wata da wata,ku zauna lafiya a mutunta kuma, na sanki laila kece ummul aba’isin komai, saboda kowa na san halinsa, to ki shiga hankalinki, dan zan sabar muku duk ranan dana kara ganin anyi fada 
da wani makamin.” 
Tabe baki laila tai ta ce “ai daman nasan ni ba kaunata kake ba, shi,isa za ka ce nice silar komai.” ‘ 
“Shut up!bana son irin halin nan. Duk wacce kiga gani to dan ina sonta na aurota, dan haka maganar ma wani so ki ajje shi gefe, fatan kin fahimta?.” 
Sai ta juyar da kai.Ba tace komai ba. Gyara zama lad’ifa tai tace “insha Allahu zaka sameni da bin abinda ka shimfida.“ 
Murmushi yayi ya lumshe ido dan yasan ba shi da matsala wajen ladifarsa. juyawa yayi ga laila sai ta yatsine fuska “naji amma kaiwa matarka kashedi, atoh! tana shigar min hanci da kudundune.” 
Girgiza kai yayi “nidai na fada idan kunne yaji tojiki ya tsira. Zaman lafiya nake so ba tashin hankali ba.Sannan ranar alhamis da daddare akwai dinner ta abokina da zamu, dan haka kowacce ta sani.” 
Wani dadi laila taji, domin dama ta dade ba taje dinner ba. “Yanzu naji magana ta fada.” 
Gyara zama lad’ifa tai ta ce “ni kam me zanje nai a dinner da ciki?.” Dariya yayi “na sanki dama can bakya so, to wannan ina bukata ajje, waye zaice ke mai ciki ce indai ba kura miki ido akai ba, ki kokarta kawai.” Sai tai murmushi tace “To.” 
Nan suka watse, shi ya fita,su kuma kowacce tai nata waje. nan. 
Da takalmin k’afarsa ya taka hardakin bai ko cire su ba ya haye gadon, sai da yayi balance, sannan fa ya tunani sai ya tashi ya rage kayanjikinsa su takalman da kayan duk ya watsar da su a tsakiyar d’akin, ya bashashshare tare da kunna fanka,duk ranar da ya kwaso 
bai sanya ya tashi da niyyar yin wanka ba. 
Tun lokacin da ya shigo gidan tana kitchen tana aiki, mata mai kimanin shekara ashirin da takwas 28, dan tsaki kawai tai, dan tasan duk gyaran d’akin da ta yi sai ya bata . Tashi tai ta shiga falon ta zarce hartsakiyar d’akin, sai ta tsaya turus! ganin yanda duk ya zame mata 
zanin gado. 
Cikin gajiya da halin mijin nata ta ce “haba baban shahid yanzu ka tsaya ka cire takalmin 
awaje shine ka tako har tsakiyar gado da shi?.” 
Tsaki yayi ya kalleta “ke dallah can matsa, wallahi jamila zan mangareki in kina min abinda bana so wai kece me gidan koni?.” 
“Haba baban shahid. Gaskiya fa na fada. To wallahi na gaji da kalar kazantarka haba? Yanzu ka dawo maimakon ka shiga ka watsa ruwa amma shine harda zuwa bayan gashi can na hada maka.” 
In tana yi mai wadannan nan maganganu bata ransa take, kamar shi mijinta, tace za ta nuna mai abinda ya dace da shi.Sai ya saki tsaki. Ya mike. Da sauri ya janyota tasan kwanan zancen dan sai yace zai biya bukatarsa da warin daudar da yake. Kiciniya suka fara yi amma da yake yafi karfinta, haka ya murkusheta sai da ya biya bukatarsa san ransa, ya tashi ya bar dakin. Cikin takaici ta shiga kuka, sai da ta sha kukanta sosai! sannan ta mik’e ta fita dan tai 
wanka, al’amuran gidan ya ta’azzara a wajenta. 
Bayan fitowa daga wanka, ta d’au wayarta ta latso layin lad’ifa, tana dauka ta shaida mata za tazo gidanta anjima, da murna ladifa tace tana jiranta. 
Jamila na ajje wayar ta goge hawaye tanajin kamarta kashe aurenta, ita saita ce sam! Ba tai sa ar aure ba.A yau tana jin gwanda aurenta na farko akan wannan, zata iya cewa ma ta wani fannin alhakin majinta na farko ne. Wanda alokacin wataran in tsiyarta ya tashi sai ya 
ajje mata kudi kafin ya sadu da ita.Amma gashi yau inda ta fado,miji ba tsafta cikin kazanta zai afka mata. Aduk kuma sanda yaso, ko bata so, In tace za tai magana ya narketa. Haka zai afka mata kamar dabba.Kuka ta sanya “wayyo Nayi gudun gara, ga shi na tadda zago.” Wajen Karfe daya ta fita daga gidan. 
Zuwa biyu 2 ta isah gidan Ladifa Sallama ta tsaya ta nai a falon kasa shiru. Ta jima, sai ga laila ta bude shashenta ta fitO da alamar bacci a idonta. Nan suka gaisa tace mata in Ladifa take nema tana sama.Ta koma. 
Nan jamaila ta mike tai saman wanda adaidai Iokacin ladifa ta fito da murna ta rungumeta ta ce “oyoyo anty jamila, ashe! da gaske kike? sai yau ai nayi fishi.Jamila Cosins ne ita da ladifa babanta da babanta wa da kani ne. A kalla zata bawa ladifa shekara takwas) 
Sai data zare mayafinta ta zauna sannan tace “hmm! ke dai bari kanwata, lamarin duniya ne sai a hankali.” 
Zama lad’ifa tai suka gaisa ta kawo mata kayan motsa baki. Sai da tai sallah, sannan ta zauna, taci abinci suna ci gaba da hira wadda ta kaisu har hirar zamantakewar Aure. 
Jamila ta kalleta tace “wallahi ladifa lamuran nan sai a hankali, kinga yau wallahi da yaji zan na tafi gida, dan na gaji da lamuran nasir, wallahi ban taba sanin nasir kazami bane sai bayan da mukai aure,lokacin kafinn muyi aure yana zuwa zance wajena wallahi tas-tas, amma yanzu in yayi wanka so daya shi ke nan duk uban ranar daya kwaso a jikina zai fanshe gashi ba ya daga min ka’fa. ‘ 
Babban matsalar ma, bai iya soyayya ba, wallahi ko mu’amala muke hakazai zo mun sandakai babu ruwansa. Ga kazanta kamar shi ya yanke mata cibi Bai damu da yayi su brush ba in zai kwanta, ke in yayi wanka daya da safen nan baya sakewa gashi haka zai barbazar min da kayan daya cire adaki, ko’ina, idan nai magana yace min na fiya masifa, kinsan ni dai da son tsafta amma yana neman ya sa na koyi kazanta. 
Wallahi tunda na aureshi d’an kiss d’in nan bai taba min ba.ldan ma aka samu na damu sai yayi min, to fa zaki ga sai a hankali, dan bai tsaftace bakin.ln nai magana yace shi ai mijina ne du abinda nake mai Allah na gani, zan kuma gani a kwaryar shana.” 
Shiru lad’ifa tai jikinta asanyaye tace “ni sai na ga ya jamila bai dace ki na fallasa sirrin maigidanki ba, babu kyau kuma ba dadi.Ko ba komai uban danki ne shahid, Kamata yayi kiyi kokarin saita shi. Mace na iya saita mijinta aduk yanda take so, duk yanda ta fahimce shi to sai ta samu ta yanda za tai ta gyara abinta cikin hikima.” 
“Ba zan iya ba ladifa, so nawa ina gwadawa. Kullum cikin nuna mai abinda ya dace nake amma yaki, wallahi ai na kusa rabuwa da shi ma, dan ina kwaruwa fa, kalli fa duk yanda na canja na dawo, Allahn da ya taimakeni ma akwai abinci sosai agidansa.” 
“Ni aganina kiyi hakuri abinda fa hakuri bai baka ba to rashinsa ba zai baka ba. Ko kin manta aurenki na farko anty jamila. Sai nace kinyi gudun gara ga shi kin tadda zago, alhakin jazuli ne sai ince, saboda kowa yasan alokacin kece ke wahalar da jazuli mutumin na iya kar kokarinsa,dan kawai bai da shi yana Auna miki abinci kika ka sa tsama dashi, aganinki takura ce, ai gashi nan kin had’u da finshi. ” 
Dariya jamila ta sanya “yau na ga ladifa,kamar irin kece yayar nan tawa kin zage kina gayan daidai! Dalilin daya sa kika ga na gaya miki saboda na san kina da nitsuwa ne wallahi, abinne yake cina, ba wai bayyana sirrinsa ba, shawara kawai nake san ki bani.” 
Lad’ifa tace “ni dai indai shawara ce ki bar zancen kashe aure, saboda kinga anty jamila kar a fara irga miki yawan aure -aure, kamata yayi ki jajirce kibi hanyoyin da zaki bi ki tabbatar ya saitu san ranki, ammafa sai kin yi hakuri,saboda kinga tun auren farkonki kika gaza hak’uri, wanda nasan jazuli baida wani illa tanan, illa auna miki abinci da yake, wanda gashi rashin hakurinki ya sanya kin fada gun wanda ya fshi.” 
Shiru jamila tai tace “zan gwada, amma wallahi ina cutuwa fa!” “Hmm ke dai kiyi hakuri kowa da kika ga yana zaune agidansa, hak’uri fa yake,wallahi wani matsalar da yake ciki tafi taki, ita kanta rayuwar nan “yar hakuri ce, idan kace ba zakai hak’uri a rayuwaba,to za kai ta shan wahala. Wallahi nasan da ace kinsan irin nasir zaki 
aura kafin ki kaso Aurenki, na san da kinyi zamanki a gidan jazuli.” 
“Wallahi kuwa kanwata, dan sai yanzu nake dana-sani dan jazuli akwai tsafta.Kuma daidai 
gwargwado baya zuwarmin kamar sunduk . 
“To kinga, da kinyi hak’uri ai da ba haka ba. kinga yanzu ma idan kika ce za ki kashe wannan auren ma, to baki san wanne irin miji zaki kuma aura ba, saboda mazan nan fa, ba wai kwarya bane da zaka kwankwasa su kaji wadda tafi karko, kowanne bawa fa da akwai yanayin kaddararsa.” 
“Hakane kanwata, that’s why i like you wallahi, you are very smart and interlligent girl, ta fada tana kurbar lemo. wayarta tai kara ta d’auka sai tai tsaki “kin ganshi ko, wallahi tallahi mutumin nan yana takuran, yanzu fa watakil wani abun yake nema yake wannan kiran.” 
Dariya lad’ifa tai kawai tana tunani aranta lalle ita a aljanna take, zata iya cewa ko lokacin da take nacin ya ringa nuna kulawarsa da soyayyarsa akanta baya zuwar mata irin haka, dan indai ta fannin gabatar da sunna ne to zata jinjinawa ramadan dan kwararrene wajen iya sarrafa mace da nuna soyayya a yayin gudanarwa, ga tsafta, gashi yanzu da tai hak’uri ta fara samun soyayarsa a fili da kulawa akowanne yanayi,tabbas babu abinda ya kai hakuri riba, lalle kowanne bawa tara yake bai cika goma ba, kuma kowanne akwai ta inda ya ke da nak’asu. ‘ 
“Nidai ki hak’uri karki kashe aurenki anty jamila, yanzu idan ni nayi irin haka, ai saiki min fad’a.” 
“Hmm lad’ifa ba zaki gane ba.”
“Ni ko zan gane, kowa fa da kika ganshi yana da tashi matsalar.” 
Haka dai sukai ta hira har wajen shida sannan ta tafi gida.
Kuka take rubza, ta shiga gidan nasu, hajiyarsu na alwala ta tsaya tace “ke kuma zainab me ye haka? sai taja gefe ta zauna. 
Tsam! Hajiya ta mike tace “muje daki.” Binta tai ta zauna, hajiyarta ce “hala rashin hak’urin naki, kika kuma bugawa Sai ta fasa kuka “wallahi hajiya, na gaji da auren nan, tun fa daya k’ara aure ya juyan baya, komai amarya, hatta girkin hajiyarsa ya koma shashinta, komai ya koma wajenta, dan gulma har zuwa take ta nai ma hajiya gyaran bangarenta, gashi k0 asibiti zasu da ita yake tafiya dan akai hajiyar, duk ya canjamin ba damar nai magana, sai ya ce dole ya mutunta mai mutunta uwarsa, wallahi duk ta mallakeshi sai abinda tace.” 
Hajiyar ta ce “Alhamdulillai, na gode Allah, dadina da gobe saurin zuwa, yau ko nice wannan yarinya abinda zan yi kenan, gashi nan ba boka ba malam ta samu saukakkiyar hanya ta mallake mijinki, nan nan, anan nake gaya miki kullum kibi mijinki, ki girmama uwarsa amma ke gani kike kamar takura ce, keba zaki iya zama da uwar miji ba, an takura miki da hidimarta, da yake shi d’an halak ne yace bai san zance ba, to tunda ke ba zaki iya ba, ai gashi ya samo wacce zata iya.” 
Kuka zainab ta fasa “na shiga uku yanzu hajiya shike nan sai na zauna na zuba ido ana cuta 
ta. “Wa ya cuceki ne zainaba? ai ke kika cuci kanki tun kina da dama, mijinki me hak’uri da kyautatawa, wallahi samun irinsa a maze sai an tona, gashi kin samu uwar miji mai kau da kai da hakuri kika sa k’afa kika ture ni’imar da Allah yayi miki, yau ga irinta nan, ai duk mace mai wayo kame abinda tasan mijinta na matukar so zatai, wallahi ba za tai mamaki ba, in taga yanda zaina girmamata. 
Nan nan ,yarinyar nan, ‘yar gidan mansura kina dai ganin yanda uwar miji ta sako ta agaba, tana kokarin hanata zaman aure da d’anta, kullum cikin yaji’ yarinyar nan take, amma ke kin samu kinyi dace da uwar miji me kirki kin sa k’afa kin shure. Ko duba ba kya yi da matar wanki ramadan, keda bakinki kinsha gayan irin cin kashin da yake mata agabanki wataran in kinje, amma haka yarinyar nan take biyayya da hakuri ,Ramadan dana ne amma 
nasan ba Shi da kirki ta nan bangaren. Amma ke kin samu miji me hak’uri kina tsiyataku. Maganinki wallahi duk macen da take da miji mai hak’uri take mai tsiya yana shanyewa,to duk ranar da yayi aure za ta gane kurenta, 
musamman inya samu mai yi mai abinda yake so.” Kuka zainab ta kuma kara volume nasa. “Wallahi mallake shi tai amaryar nan hajiya.” 
Ko kara bi takanta ba tai ba, ta fara sallah, kuka zainab ke yi wanda har sai da hajiyarta idar ta daka mata tsawa. 
“Za ki min shiru ko saina bibbige bakinki?.“ 
Shiru tai hajiyar taci gaba “wallahi indai ba zakiyi zaman aure da ladabi da biyayya ba kina tare da wahala, kuma yanzu -yanzu za ki koma gidanki ba sai gobe ba, ko kuma wallahi na bugawa yayanku ramadan yazo ya casan jikinki. ” Ko kuma yanzu na shiga shashen kawunki na sanar mai, Kinsan dai sarai kwaunki ya hanaki yajin nan” 
“Yanzu hajiya ba za kiyi wani abu akai ba?.” 
“Me kuwa zan yi? ai kin rigada kin yada damarki wallahi, indai zaki d’au shawarata to ki sarda kai ga megidanki, mijinki me fahimta ne atoh.” Haka tajuya ta shiga jan carbinta tabar zainab na kuka. 
Tsaye take agaban wardrobe tana kallon nunkakkun kayanta, ta rasa kayanda za ta zaba, can ta dauko wani bakin material, harta ajje, tunanita tsaya ta nai, sai ta maida shi, ta d’auko wani black cotton lace me wasu manyan zane wanda dukkansa bakine, da kwandala kwandalan stone fari ajikinsa, tare da wani kyalli-kyalli a gefe-gefen bakin lace din shima fari,wanda kallo daya zakai mai ka tabbatar yaji kudi. Da sauri tajuya ta dau wayarta ta kirawo ya kareema, tana dauka tace “ya karima karfa ki manta da turo min da mai makeup d’in.” Daga can kareema tace zata zo insha Allah.” Ajje wayar tai ta bude bangaren mayafaai ta dauko wani farin mayafi mai wasu tarin ado masu daukan ido, sannan ta zaro sarka fashion da awarwaro, zobe duk farare, tare da 
bakin dogon takalmi doga mai madauri daga sama -samansa. 
Karfe shida ramadan ya dawo ko hutawa bai ba, Wayar chairman ta sameshi, ya daga ya kejaddadamai fa yazo, tsaki yayi yace “kaifa ka fiya na ci Sai kace wata tsiyar zaka ban inna zo.” Ya fad’a da dariya. Shima dariya chairman ya yi yace “da k0 kaga rashin mutunci.” Nan ya kashe. Dakin laila ya leka yake sanar mata ta shirya zasu fita. 
Yayi sama ya gayawa lad’ifa ma. Karfe shida da rabi wacce ke makeup tazo, lad’ifa ta hau da ita samanta bayan tayo alwala saboda sallahr magrib da ta zauna aka farai mata. 
Abangaren laila ma shirinta take, dan ita ta iya fesa kwalliyarta da kanta ta kware. Itama ta dauko wata gown brown mai adon wasu manyar brown fulawas. Komai dai brown ne za tai shigarta. 
Kan takwas ramadan ya fito fes! wanda kallo daya zakai mai kasan zai yaki ‘yan mata awajen. Alokacin mai make up ta tafi. Laila ce ta fara futowa tayi kyau sosai! A kallo daya zakai mata kasan cewa ko ina ya saitu ya zauna dam! Wanda rigar a farko da ta sanya sai ba tacika taba, saboda lokacin da aka dinka anyi tane da dan wara-wara yanda kayan cuko zasu samu mazauni. ayau sai da tayi cikonta, sannan rigar ta zauna ajikinta, ta fito cif-cif, kallo d’aya ramadan yayi mata ya shiga ayyana anya! ba tai ciko ba, sai kawai ya basar. ‘ Wani yauki ta shiga yi tana wani tafiya sai kace za ta fadi. Musamman ganin Ramadan dake tsaye agefen mota. Gaban motar tai sauri ta shige wanda alokacin girkin lad’ifa ne.Dan kam ita ba zata iya zama a baya ba. 
Lad’ifa kawai’ sukejira ita kuma tana can tana neman wayarta saida ta ganta. 
Fita ramadan yayi dan yaga mai ta tsaya yayi, karo sukai a k’ofar shiga falon, sauka kadan ta fadi, ga dogon takalmin da ta sanya sai yayi sauri ya tareta, ta fada jikinsa, ahankali ya dagota ya kura mata ido, ganin yanda ta fito tayi masifar kyau wanda ta dad’e batai irinsa ba, da yake ita ba ma’abociyar irin kwalliyar nan bace, yau da a kai mata sai ta fito kamar wata d’awisu , ga fararfatarta ta kwanta akan bakin shigar da tai, wanda kallo daya zakai mata ka kasa dauke idonka. Ga kayan sunyi mata cif-cif sun mata dan dam-dam! saboda cikinjikinta da ya dan kara mata cika. 
“Lad’ifa ta” Ya fada a hankali yana dada mannata ajikinsa. Yana shakar kamshinta, wanda sai kaje dab da ita zaka ji daddadan kamshin. Fararen idonta da suka ji gazal yayiwa duba. Ya karasa da kallonsa zuwa lips d’inta da ya ke matukar so, sosai shape d’insa suka k’ara fitowa da jambakin da aka dadira mata, ga wani irin d’auri da aka yi mata yayi matuk’ar saituwa, hakan ya dad’a kawata fuskarta. Ya kalli girarta da ta zanu, sai ya lumshe ido, Sai yaji yana jin kishin taje dinner din nan, murmushi tai cikin sanyayyar 
murya tace “zauji wannan kallon fa?.” Wani murmushin yake  yace a hankali kamar me rad’a “ji nake kamar …… “Ji kake kamar me….
Sai yayi murmushi ya lakuce hancinta yace “muje.” 
ltama murmushin tai tana maijin yanda mijin nata ya burgeta. 
Gaba yayi yana Murmushi, tare da wasa da mukullin dake hannunsa, shi sai yace bai tab’a ganinta cikin irin kwalliyar nan ba, Sai yace tun lokacin bikinta.Duk da cewa yafi sonta a natural dinta. Amma yau da tai kwalliyar sai yaga ta karai mai wani irin kyau na daban. 
Tsayawa ladifa tai ganin laila a gaba tana basarwa, sai kawai tai murmushi tasan neman tsokana ne kawai irin na laila. Tunda tasan girkinta ne tasan ita ce agaban. 
lta kuma tai alkawarin ta daina biye mata, za ta dada hak’uri akan abinda tasan samunsa da rashinsa ba zasu kareta da komai ba. Bayan ta shiga, sai ta zauna a saitin Ramadan,tana zama ya juyo gaba daya ya kalleta tare da lumshe ido, ya saki wani kayataccen murmushi ya juya, dan ji yayi gaba d’aya ladifar ta saukar mai da kasala. Itama sunkwi da kai tai tana murmushi. 
Juyawa yayi ya kalli laila da ke gefensa, itama tai mai kyau sosai a ido, duk da cewa ko rabi -rabin kyan da ladifa tai ba tai ba, amma saboda gogewa da iya kwalliya, da sanin kusfakusfa na kwalliya da iya kyale-kyale itama ta haskaka sosai! Sai ya sanya hannu ya shafi gefen fuskarta. Ita kuma ta wani saki fari tanajin baya ita. Ahankali ya ja suka tafl. Sanda sukaje motoci ne birjik! wanda suka amsa sunansu, hadaddun ‘yan mata, da couples mata da miji, sai shigewaa ciki suke, agefe ramadan ya faka. Ga wani sanyayyan kida na tashi, nan fa jikin laila ya fara tsuma, dan an tuno ‘yan matanci. Nan duk suka firfita hasken filin wajen hall din ya haskaka su suka fito radau Jerawa sukai suka shige, ramadan na jin kansa asama dan ya tara kyawawan mata musamman lad’ifa. 
Wajen ya kawatu da kayan kawa masu kyau da walwali, hade da tsari, suka kama wajen su ka zauna, kowanne kujera mace da namiji ne hakan zai nuna maka mata da mazajensu ne, lad’ifa dai kanta na dan sunkuye tana latsa waya, dan karar kida ma yayi mata yawa, dan ita ko da tana budurwa ma bata saba zuwa dinner ba, duk sai taji ta takura. Laila ko sai wani basarwa ake. 
Sai Karfe tara ango da amarya suka karaso, sunyi kyau sosai nan aka fara gudanar da shagalin. 
Suna nan zaune bayan an diddire musu cup cakes kalakala da choculate agabansu kamin a kawo abinci sai ga wata budurwa nan kamar ta karye. Tana zuwa tace “laila laila.” Ihu laila taso tai wai ta ga kawarta, sai ta kalli ramadan da ya hade girar sama da kasa, yana wulla mata wani mugun kallo, ai sai ta fasa tace “shafcy ban zata zan ganki anan ba.” “Amaryar ai kawatace.” Tace “kinyi wuyar gani, tun bayan da muka gama school.” 
Samun gefe shafcy tai ta zauna a dayan gefen kujerar da ke saitin ramadan, sai satar kallonsa take tana hira da laila , dan kallo daya tai mai ya tafi da ita. Sai iyayi take tana dan rawa da kafadunta tana bin kidan dan ta burge. 
Sai alokacin ta juya ta kalli ladifa tace “sannu ko.” Ladifa tace “yawwa sannu.” 
Ganin yanda shafcy keta satar kallon Ramadan ya sanya laila ta ankare, musamman ganin yanda ya hade rai dan shi kallo daya yayi mata yasan bata cikin irin tsarin matan da ya keso. Shi,isa ya hade rai.
Tashi laila tai taja hannun shafcy tace “muje can da ba kowa mafi sakewa muyi hira, dan ta yiwa shafcy farin sani dan Kwararriyace wajen snatching don a school d’insu da taga saurayi yayi mata, sai ta san yanda tai ya dawo nata. 
Suna zama shafcy tace “laila kinga yanda kike wani shining, gaskiya aure ya karbe ki, amma wancen guy din yayi min kyau wallahi ya hadu kin sanshi ne?.” Hade rai laila tai tace “to ai shine mijina, wai ke har yau baki canja ba ne? to kinsan dai halina bana ragayya wallahi, mijna yafi Karfinki.” Tabe baki shafcy tai. “maida wukar. Ban manta koke wacece ba. Waccen kishiyarki ce? “E! “Wow she is very young and beautiful wallahi.” “Wait shafcy, wannan ai cin fuska ne, a gabana ki na wani koda kishiyata.” Kai! Laila, ba karya na fada ba, dan k0 rabinta a kyau ba kiyiba. Sai dai ki fita kyalekyale.” 
“Kya ji da shi dai.” Laila ta fad’a tana kallon wani shashi. 
Wani song aka sanya mai matukar dadi, wanda laila taji ma dole ta taka, nan suka mike ita da shafcy, dan ta manta da cewar tare suka zo da ramadan ma. Rawa suka je suna tika, wanda ramadan bai kula ba, saboda ladifa ta dauke mai hankalin, musamman ganin yanda ya kafe wasu ‘yan mata da suka zo wucewa da kallo. Har suka zauna yana yawaita kallon daya. Wanda har saida ladifa ta ankare sai tajanye mai hankali. .Daga kan dazai, sai ya gano laila na rawa ita da su shafcy da wasu yan mata, wani irin takaici da haushi ne ya isheshi, ganin yanda kowacce mace ta kame da mijinta azaune, amma banda laila sai ya mike. Cike da takun izza ya karasa wajen suka gaisa da chairman, yayi wa ramadan godiya zuwan da sukai. Juyowar da laila za tai ta ga idon ramadan na kanta, ya hade rai sai sum-sum ta matse ta fita ta koma wajensu, ladifa ta kalleta tai dan murmushi ta juyar da kai, dan itama ta ganota sanda take rawar. Ramadan na dawowa ya hade rai ya kalli laila, yace “karki kara motsawa in dai bani na baki izini ba, menene naki na rawa? Kowa na kallonki ba kya ganin da maza awajenne?.” Ta ce “afuwan habeeby..” Juyar da kai yayi. Yayi kwafa. Haka dai biki yayi ta gudana, wanda sai wajen sha d’aya su ramadan suka mik’e zasu tafi, wanda su kadai suka fara tafiya, sun fita harabar wajen zasu shiga mota sai ga murabus kamar an jefoshi. Sai ya shiga wani kobarewa ya tsaya gabansu, yace “laila amma naji 
dadin ganinki, dama ina ta bugo wayarki bakya dauka, ko ta whatsap, baki san tarin missing dinki da nake ba. 
Ya fada yana satar kallon ramadan, da ya harde hannaye biyu ya tamke fuska. 
“Please mana laila kiyi magana mana.Kuma yin magana zai murabus sai yaji saukar naushin 
ramadan a fuskarsa,wani irin kamewa yayi, ya daga idanuwansa ya kalli ramadan yana huci.” Cikin fushi yace “baka da hankali zaka ringa kula matar aure matata, baka da hankali ne?.” Magana zai Ramadan ya kuma naushinsa, ganin stars murabus ya fara yi, da sauri yayi baya da gudu ya shiga adaidaita sahunsa yaja ya fice ya tsaya a can waje, yana maida numfashi.Yana jin dole ya nunawa ramadan shi dan zara ne. Gogejinin da Ramadan ya fitar mai a hand yayi, yana jira mai video camera ya fito su tafi
In banda bari babu abindajikin laila keyi, musaman ganin irin kallon da ramadan ke mata. Ladifa kuwa cike da mamaki take kallon laila. 
Afusace ramadan ya zagaya, ganin hakan ladifa ta shige baya, wanda adarare laila ta shiga itama gaba, yaja motar suka bar wajen aguje. 
Koda suka koma gida, da sauri laila tai shashenta, dan kar Ramadan ya tsara ta, yana 
fitowa direct shashen laila yayi, ya tsaya abayanta yace “laila” Sai ta juyo ya kalleta yace “wanne dan iskan kato ne yayi miki magana dazu?, sannan waya baki izinin sanya kayan ciko.” Jikinta ne ya shiga rawa dan ta rasa tambayar da zata fara amsawa. Cikin tsawa yace ta gaya mai yana sauraronta. 
“Mm..mmm daman kayan da na sanya ne sunfi zama min ajiki in nai cikon, shi…shi kuma wannan wani ne a unguwarmuu ban san zan ganshi a wajenba.” Wani mari ya sakar mata “ni za ki maida banda hankali ko? har abada me ya sanya laila baki da tunani ne? dole ne aka ce sai kin sanya kayan, ina manyan kayanki ne? yanzu keba matar aure bace? Ba kiga yanda ladifa tai ba.” “Amma ai ba yanzu ya kamata kai magana ba, tun kafin mu tafi yakamata.” “Ban dauka kayan naki haka suka matsu ba, ai har sai da mukaje” 
Kuma ki tattara kayan cikon nan tunda ba ki da tunani na kwashe wancen saida kika kara siyowa. 
Sannan ni za kiyiwa karyar saurayin da yayi miki magana ko? to wallahi laila muddin na binciki gaskiya na gano hukuncin da zan yanke akanki ba zai miki dadi ba, dan cuko kuma karki fasa sawa.” 
Ya fita afusace, jikinta na rawa bayan fitarsa tace “masifaffe kawai.” 
Mu tara a next chapter mai dauke sa drama

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *