NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 29
Abban laila na dawowa da daddare, babu bata lokaci umma taje ta sanar mai da batun cikin laila, ta kara da cewar yaje ya sanar da mijinta. Sai daya gama jinta, ya ce “lkon Allah Allah ya sauketa lafiya, amma ba zanje ba, har sai sanda yaron yazo da kansa dan ya maida ta
“Haba alhaji ya za a ce hakan? ai hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, saboda Allah haka zaka zuba ido, muna kallon yarinya baka ganin dukyanda ta koma, dan Allah kai hakuri ka neme shi.”
“Zancen kike so saratu kome ya faru da yarinyar nan itace sila, ba wai ban damu da komawarta bane, so nake sai taji zaman gidan nan ya daMeta arai.”
“To Alhaji na nawa? kowacce mace indai an daura mata aure ai tafi san ta ganta agidanta.”
Bai kara cewa komai ba,ya karkade riga ya mike, cikin takaici umma tace “to anjima zamu asibiti a duba ta.”Yace “Sai kun dawo.”
Fuska atamke umma ta fito ta zauna adakinta tai tagumi, lamarin ya fara isarta gashi har an fara yadawa a unguwa ai auren laila ya mutu. Wasu ma har ganin kwakwaf suke zuwa.Akwai masu yada magana ma ai wai yanda laila ta fitsare yaushe zata iya zaman
aure.
Numfashi taja ta mike ta shiga daki laila ta shiga zauna, ta kalli umma tace “umma me yace?.”
Cikinjin haushi ta kalleta ai ga irinta nan laila, duk abubuwan da nake gaya miki kika share, sai da ta kwabe miki, ai wannan ma gwanda ace sakinki yayi asan cewa ba aure a kanki, gashi shi kuma baban naki ya hau dokin zuciya.”
Kuka ta sanya “umma wallahi na gane kurena dan Allah kuyi hakuri, yayi magana na koma,” haka ta shiga raira kuka kamar ba gobe, umma ta kalleta tace “karki damu insha Allahu zanje wurin ita mahaifiyar mijin naki, komai ayita ta kare. Yanzu ki shirya anjima
muje asibiti.”
Ladifa tagumi ta rafka, ita yaya za tai? haka kawai taje ta kuma samun wani cikin a kurkusa, gashi bata san yanda za tai da lamarinsa ba. Kiran sallahr magriba ne ya sanya ta mike, wanda adaidai lokacin msg ya shiga ta duba Ramadan ke gaya mata ta shirya gashi nan da anyi sallah.
Sai ta mike tana kaikawo ta shiga tunani, babu yanda za ai ta iya kin bashi kanta, har idan yazo amma tana jin babu dad’i.
Wanka taje tai tare da alwala ta zo tai sallah ta shirya cikin riga da wando ta dora abaya baka akai. Tare da yin simple make up, Zama tai tayi tagumi. Kamar rabin awa, saiga kiransa nan yace mata yana kofar gida.
Tashi tai ta shiga wajen hajiya da ke zaune tana jan carbi, ta tsugunna tace “hajiya baban fuad yace yana son muje akai fuad asibiti, saboda yar murar da ya fara.”
Kallonta hajiyar tai tace “dan kwasarwa yaro iska, to amma babu damuwa kuje.”
Cikin kasala ta mike ta shiga ta lullube fuad a tawul me kauri, ta sanyashi a kafada ta fita, yana motar yaga fitowarta sai ya murmusa. Ta bude gaban motar ta zauna wanda taki bari su hada ido.
Kallonta yayi yace “ya dai mum fuad?.”
sai ta juyar da kai tace “ni fa gaskiya ba zan iya ba.” Bai saurareta ba yaja motar, wanda direct sai da suka fara biyawa asibitin aka dan duba fuad sannan suka karasa gidansu.
Koda suka shiga fuskarta tamke ta shiga gidan, ya bita da kallo, alokacin akai kiran sallahr isha’i ta shige dakinsa, dan duk dakunanta tabar mukullinsu agida. Shimfide fuad tai tayi alwala ta tada sallah. Tana zaune sai gashi ya shigo. Sai ta juyar da kai, agefenta ya zauna ya ce “wai meye kike wani basarwa ne?.” Sai ta sanya kuka “ni wallahi ace ko arbain banba a takura min, wallahi ba zan iya ba.”
Haushi ne yaji ya kamashi yace “yanzu ladifa keda nake gani me hankali za kizo min da
wannnan maganar,” sai ta kuma fasa kuka, “ni Allah ban yarda ba ka maida ni gida.”
Tamke fuska yayi yace “ni mijinki ne ina bukatarki, dole ki bani hakkina, so kike sai naje ina bin matan waje, kinsan halin da nake ciki kuwa?.”
Sai ta mike cikin rawar murya ta ce ” to baga matarka laila can ba,haka kawai ni dana haihu ban arbin ba ace dole.”
Tsawa ya daka mata, wanda saida ya sanya fuad tashi ya fara kuka,da sauri ta fara jijjgashi harya koma bacci. ’
“Daga yau karna karajin kin ambaci wai ina da wata matar naje gunta mana, kinfini sanin inda take ne? ko an gaya miki idan ina bukatarta zanzo wajenki ne, yau da ita nake bukata wajenta zanje, wanda ko ayanzu naji bukatar hakan agareta zanje mata, dan haka last warning karna karajin kin min haka. Ke nake bukata dan haka kiji da wai.” Kwanciya tai a gefen gadon tace ni na ce ba zan iyaba ka mayar dani.”
Dafe goshi ramadan yayi ya shiga kallonta yace “please ladifa wai meye haka ne? bana son fa irin haka.”
Hade rai tai tajuya. Idan zaka bari muyi arbain to, dan ni gaskiya tsoro nakeji.”
Tsoron me kikeji.” “haka kawai na kuma samun ciki da wuri.”
Dariyar takaici yayi yace “problem,wai wake ba da cikin ne? ba Allah ba,sai aka ce miki jazaman ne in na kusanceki yau za ki kuma samun ciki? Wannan sai Allah. Karki sa raina ya baci na bata naki abanza.”
Yana fada ya zauna a gefenta ya kwanto da ita jikinsa ta fisge. Ta fice daga dakin.Dawowa tai ta dau fuad ta sauka kasa.
Ramadan wani irin takaici da haushi ne ya isheshi. Sai yayi kwafa ya sauka kasan, tana zaune kan kujera yace “ladifa karki sanya raina ya baci. Ranki zai mummunan baci. Muddin baki yarda ba wallahi ba zan komar dake gida ba kinzo kenan.”
Ya fada tare da hade rai ya bar wajen ya shareta.
Sai ta sanya kuka, ta dade a zaune bai waiwayota ba, sai da ya ga ta mike tana kuka zata fita, ya tashi “ya rikota, “ladifa mai kike son maida kanki ne? wannan abinda kike addine? Mai yasa zaki fifita al’ada akan addini, wanda ALLAH shi ya halastawa namji yaje wa matarsa aduk lokacin da yaso, indai ba tana al’ada ba,so kike Allah yayi fushi dake,ko so kike Allah ya tambayeki kin bani hakkina da kikai, ko so kike mala’iku su yi ta tsine miki.”
Idonsa na kanta yana fahimtar yanda maganarta shigeta. Sai ya rike hannunta ya shiga matsawa “plese ladifa.”
Ba tai magana ba, sai kawai ta dau fu’ad ta mike, ta mika mai dayan hannunta, shi kuma ya sanya nasa ya mike kamar rakumi da akala.Ya bita abaya
Suna komawa dakin ya kuma narke mata, sai lallashinta yake dada yi, yace “baby wallahi sonki ne yayi mini yawa, ji nake kawai ina bukatarjin duminki, shi,isa, ban son ki shiga fushin Allah.” Kallonsa tai ta sunkwi da kai, dan ita kanta tasan gaskiya ya fada,amma ita a al‘ada bata
ganin ana haka.Ta yaya ita zai zo ya dameta, tuno azabar Allah ya sanya jikinta yayi sanyi, tsoron Allah ya kamata ta kalleshi tace “kai hakuri zaujina.”
Murmushi yayi ya kwanto da itajikinsa,ya shiga rada mata kalamai masu dadi a kunnuwanta,a hankali taji a zuciyarta na narkewa, taji itama tana bukatarsa sosai, lumshe ido tai tana murmushi, fiskarta ya shafa yace “Are you ready.”
Kanta ta daga mai cikin wani salon kallon da ta watsa mai. Wanda daga wannan suka fada
duniyar ma,aurata.Sai wajen goma suka dawo daidai.
Alokacin da duk wani nutsuwarsu ta dawojikinsu, ladifa ta ankare da lokacin har goma tayi, zaro ido tai tace “wayyo dearna lokaci yaja kar arufe gida.”
Ramadan dake tsane ruwan kansa da towel yace “ba sai ki kwana ba, ai dama nan ne mazaunin ki. Kin ga sai kici gaba da faranta mini rai awannan dare.” Cikin shagwaba tace “Allah ni dai ka maidani.”
Murmushi yayi yana jin wani irin soyayyarta aransa, soyayar da yake mata tun farkon daya fara ganinta, ita ke dada taso mai, furzarda hucin iska yayi daga bakinsa yana tuno farincikin daya shiga wanda ta bashi. Kuma yaji zam -zam.
Sai goma da kwata ya daukesu ya tafi kaisu gida, yayi mata sayayyar kayan kwalam ya karasa dasu gida. Ladifa ta shiga hajiya na zaune a falo tace “ku kam ina kika tsaya ne ladifa?.”
Sai ta sunkwi dakai. Tace “hajiya mun dan biya ta gidane na gyara wasu abubuwan.” “To shikenan sai kije ki kwantar da fuad.”
Tana shiga daki ta kwanta ta shiga murmushi, sai doka murmushi take sakamakon tuno mutumin nata. Tashi tai ta sanya kayan bacci ta canjawa fuad kaya ta kwanta, a wannan lokacin kiransa ya shigo wayarta. Nan fa suka kuma lulawa cikin duniyar begen juna, sun dade akan layi suna waya, sai wajen 12 saura suka hakura. (hmm su ramadan wata sabuwar soyaya ta bude Allah yasa adore)
Da safe karfe goma umma da laila suka tafi asibiti. Sunje akai mata gwaje-gwaje aka tabbatar da cikinta dan wata uku da sati d’aya. Murna kamar me, laila ji take kawai ma ramadan ya maidata ma. Tun a hanya taita kiran lambarsa taki shiga har sukaje gida sai ta kyale.Suna komawa umman ta kuma yiwa baban laila maganar, kan ya nemi ramadan, ko bin maganarsu bai ba.
Amma azuciyarsa yana jin haushin lamarin, kuma yanajin haushin shurun da ramadan yayi, shi,isa shima yace sai sanda ya tako da kansa, ga kuma tunanin ita ta jawowa kanta shike sanyawa ya dada burus da maganar.
Zuba ido kawai umman ta yi, ta kuma cewa laila karta soma gayawa shi ramadan din da bakinta, ta bari manya suyi maganar. Za tai ta tausar mahaifinta har ya yarda. Ganin abin ya ci tura, kura takai bango ya sanya umman laila ta wanke kafafuwa ta tafi”! gidansu ramadan. Hajiyar ramadan na tsakargida ta shiga, lale marhabun tai mata suka shiga ciki suka gaisa. Umma laila tace “abinda dama ke tafe dani shine alamarin yaran nan ne yaci tura, ita gashi yanzu an tabbatar da tana da ciki na wata uku, gashi mahaifinta ya ki neman shi,
shi’isa nazo dan shi mijin nata ya sani saboda lamarin ciki dole babu boye-boye.
Hajiya cikin murmushi tace “ikon Allah ciki!! amma nayi murna.”
Umman laila ta kara da cewa, ” koda bai maidata ba, to yasan da Cikin.“
“Haba! haba maidata kuwa dole ne, shida ba sakinta yayi ba, insha Allahu zan mai magana.”
Nan hajiyarta mike dan tafiya, hajiya tace ai mata ya jiki kan tazo ta duba ta.
Tana tafiya hajiya ta kada kiran ramadan ta ce yazo tana nemansa. Lokacin yana gidansu ladifa yana cin lunch, suna hira yace mata zaizo yanzun nan.
Bayan barinsa nan, direct gidansu yaje ya zauna hajiya ta kalleshi ta ce. “Kasan da cikin matarka?”
Sai ya dago kai ya kalleta ya sunkwi da kai, ganin yayi shiru tace “to matarka laila nada ciki har na wata uku, dan haka ka maida ita dakinta, bana son wani dogon zance.
Yayi farin-cikin jin cikin sosai! sai ya dago yace. “to hajiya. ” Murmushi tai tace “ya masu wanka?.”
Ya amsa “lafiya kalau, sannan ta tambayeshi fuad, sun dade suna hira da mahaifiyar tasa, sannan ya tafi.
Inda yana tafe yana jin dad’i da mamaki. Kiran lailan yayi wanda sai yace tun daya kaita gida bai kara kiranta ba, tana zaune tana cin abinci kiran ya shiga, tana ganinsa tai wani yaken murmushi ta dauka cike da yanga tace “barka dai?.”
Yace “yakike?” Tace “lafiya.” Yayi mata yajikin, tace kalau take. “Ke ashe kina da ciiki shine baki gayamin ba,” Ya fada yana sauraren mai za tace.
Sai tai dan murmushi da alama adduarta ta karbu. Tace “nima ban sani ba, sai kwana uku da suka wuce.”
“To ki kula da kanki, zan turo miki kudi ta account, duk wani abin bukata kina amfani da shi. Zan yi tafiya ne wanda sai na dawo za ai maganar komawarki.”
Duk da ta danji dadi,amma jikinta a sanyayejin cewar ba yanzu zai maida ta ba, sai tace to muryarta kamar za tai kuka. Nan suka rabu shi ko yayi hakanne dan baison komawar laila gidansa yanzu, yafi so sai ladifa ta koma, sannan ta koma itama.
Laila sai ta tsame hannunta daga cikin abincin tai zuru, danji tai komai ya fice mata arai, sai ta sunkwi da kai ta shiga hawaye, alokacin umma ta fito ta ganta ahaka, tace “kukan me kike?.”
Sai ta kalleta tace “umma kinji abinda yace; nan ta gaya mata, umma tace ” sai hakuri fa, lamarin mazan nan fa sai du’ai , aduk lokacin da kai ke bid’arsu, su kuma alokacin suke shuka maka tsiya, kawai hakuri ne magani, ki ci gaba da addua, komaiya kusa zuwa k’arshe.Kuma kema ki na kama kanki kinji. Banda shashanci.”
Shiru tai kawai, domin ita lamarin ya dameta, duk yanzu batada kwarin ma wani fada Sai ta share.
Bayan sati days.
Yau ladifa ta koma gidanta. Ramadan sai zumudi yake, kamarwadda tai shekara ba ta gidan. Da yake da safe ta koma, kafin yamma gidan ya dau kamshi, ranar ramadan ko aiki bai fita ba, yana like da ladifarsa tare da fu’ad, wanda yini yayi a hannunsa, sai dai ya kaishi ta bashi abincinsa ya koma hannunsa. Ladifaji take dama ‘Iya ita kad’ai ce da mijinta babu wata. Wani irin kishi ma ta dinga jin tunowaryana da wata matar. Aranar ramadan bai saurarawa ladifa ba, saboda jinta yake kamar wata sabuwa, duk ya wani susuce.
Da asuba bayan sun tashi sallah, bini -bini idon ramadan akanta, tunani kawai yake gashi ta haihu amma kuma yajita zam~zam, koda ma haka matan ke komawa idan suka haihu? ya ayyana aransa, sai yayi murmushi, alokacin ta shigo dakin, ta zauna gefen gado ta gyarawa fuad kwanciyarsa dake can gefe, tsam! ramadan ya mik’e ya zauna gefenta yace “babyna wai canjaki akai ne? komai sweat,” sai tayi murmushi azuciyarta tana godewa iyayenta da yayarta da suka bata kulawa da suka gyarata, lallai ta dada gasgatawa cewar gyara shine mace. Dan ba zata taba manta wata kanwar kawaryayarta hadiza ba, bayan ta haihu mijinta ya yi ta wulakantata, wanda hakan ya zame mata gagarumar matsala, ba ta gano matsalar ba, har sai daga baya, dan bayan ta haihu haka ta koma gidan ta babu wani gyara da tayi, shi kuma miji yaji ba yanda ya saba ji ba, shine ya canja mata. Lalle ta yarda in kana gyara kanka cikin ingantantaun abubuwa zaka samu salama ta wani b’angaren agidanka.
Numfashi taja bayan ta dawo daga tunanin ta kalleshi “hmm! Nima ban sani ba.”
Rungumeta yayi ya shiga shakar kamshinta, tare da sanya fuskarsa gefen wuyanta yana lumshe ido. Nan suka kuma lulawa duniyarsu ta masoya, ramadan na cewa don’t leave me baby please.”
Ita kuwa wani irin dad’in kalamansa ta ringaji. Wanda hakan ya sanya ta kara kaimi wajen faranta ran zaujin nata.
Rayuwa suke cikin kwanciyar hankali hakan ya dada sanyawa sukai luf -luf ita da babynta. Duk da cewa har yanzu ba wani kina taiba, ‘yar k’ibar cikinma duk ta tafi, amma ta murje ta dan dada cika kadan, hakan ya dada sata fidda wani sihirtaccen kyau, wanda shi fuad kibarsa kawai yake kwasa, gashi kullum kara haske yake fau!! Ga fara’a da hakuri dan inta ajje shi, haka za tai ta aikinta, sai dai yayi ta kalle -kallensa indai yayi kuka to yunwa yakeji, wanda ta b’angarensa a yanzu suka fi samun sab’ani da ramadan, dan ba damar yaga an bar fuad shi kad’ai, sai ya hau mata fada ta bar yaro shikadai, me take ne? ba zata zo ta dauke shi ba.
Bayan kwana biyu Ramadan ne zaune a gaban hajiya, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.” yanzu kai ramadan ashe ba ka maida yarinyar nan ba, ai an gayamin, to wallahi tallahi muddin daga gobe zuwa jibi ba ka maidata ba, to sai na sabar maka, so kake ka dau alhakin ta, ko mai ma taimaka ai ta horu, yanzu so kake a sanyamu abakin duniya ko? to wallahi muddin baka maidata ba ayanda na gaya maka sai na sabar maka.”
Shiru yayi yana sauraronta, yace “kiyi hakuri hajiya zanyi yanda kikace wani dan aikine ya tsare ni.” Ba wani nan idan ka duba ka hanga yarinyar nan ta rigada ta zame maka kaddara. Allah ya riga ya hukunta sai kayi rayuwar aure da ita, ya riga ya qadarta matarkace, wanda kaine kaji ka gani, to akanme yanzu ba zakai hak’uri da lamarinta ba, kai ko tunani baka yi lokacinda ka saketa daga farko, kuma ta koma, to wallahi idan ba Allah ne ya qad’arta zamanku bai kare ba, wallahi komai za kuyi sai kun koma, yanzu ba gata nan da ciki ba, ba kasan yawan ‘ya’yan da Allah ya kaddara muku kai da ita ba, rayuwa fa kowa da yanda Allah ya tsara mai. Babu mai wuce kaddararsa.
Dan haka kad’au matarka bana son wani dogon magana, kuma da wai kar na k’ara jin wani makamancin haka ko saki bana so. Kai ko duba kanwarka zainab ba kai da keta galawura akan aurenta, da kyarfa mijinta ya maidata, to idan kaima kana so a kyautatawa naka, to kaima ka kyautatawa na wani, abinda bana so ai ma yarana, haka ban so aima na wani. Ka tsaya ka jajirce agidanka. Kowacce mace da halinta, ba wai dan ka samu lafiyayyar yarinyar irin lad’ifa ba, ka ce wai kowacce haka zaka sameta, ai yatsun hannunmu ma ba daya bane.”
Haka tai tayi mai fada, har yaji ba dadi, karshe yace mata zaije gidansu anjima.
Nan ya tashi ya tafi jiki asanyaye. Bai samu yaje gidan ba sai da magriba yaje ya samu mahaifin laila, sai yaji duk kunya ma ta kamashi musamman da suka hada ido da babanta, dan yasan zuru akai mai, wanda
hausawa ke cewa ta ishi da.
Nan dai yake gaya mai zancen komawar laila. Baba bai kasa agwiwa ba, ya yi wa ramadan nasiha sosai! wadda ta shiga jikinsa.
Bayan tafiyarsa, baba ya koma gidan, laila na tsakar gida tana wanke wasu kayanta marasa nauyi, ya kalleta yace “ke kishirya jibi zaki koma dakinki.” Sai ta tsugunna tace “to baba.”
Yana shiga dakinsa sai tajuya ta shige falonsu da gudu ta fada jikin hajiya tace “jibi zan koma.”
Cikin jin dadi hajiyar tace Allah abin godiya. Ki dinga dai kula yanzu bake kad’ai ba ce. Sai ki hau shirya kayanki.”
Washegari laila tun safe ta je gidan saloon akai mata saloon dasu gyaranjiki sharp -sharp, wanda acikin kudin da ramadan ya turo mata ne ta diba, sai wajen yamma ta dawo, babu laifi tayi kyau sosai. Nan duk ta faka kayanta kamar wacce zata wani garin, sai rawarjiki take. Umma tace “yakamata wannan rawarjiki ad’an daga mai kafa mana, mace ai ba
koyaushe ne take susucewa akan namiji ba, wani lokaci adinga dan jan aji amma bana shirme ba.”
Murmushi laila tai kawai tana sauraron uwar.
Washeagari ramadan karfe sha-biyu yana kofar gidansu laila. Wanda da umman laila tace ko wata daga cikin danginta za ta zo ta raka lailar, baba yace aa kawai tabi mijinta kamar yanda yazo ya ajjeta yazo ya tafi da ita.
Laila na zaune kanta asunkuye ta ci uwar kwalliya anfesa ta kamar babu gobe sai bulbula kamshi take. Umma da baba na gefe yace “laila amatsayina na mahaifinki, ina gargadinki da kar wani abu makamancin haka ya sake faruwa, kinga dai gwagwarmayarda kika sha ko. To ki hankalta. Sannan ina umartarki amatsayina na babanki da ki bi mijinki sauda kafa, yi nayi, bari na bari ba aibu ba ne. Ita biyayyar miji bata faduwa k’asa banza, ki girmamashi shi yake gaba dake, duk abinda yace kiyi kiyi ki bari ki bari, indai bai sabawa sharia ba. Abinda za ki min kenan ki biyani. Allah ya gani na baki tarbiya, na aurarda ke to ina rokonki da kiyi biyayya, kodan samun rahmar ubangiji ranar gobe k’iyama, idan wani abu ya shige miki duhu mikawa Allah kukanki. Allah yayi miki albarka ya kuma saukeki lafiya.
Tabbas! nasihohin baban nata sun shigeta, sai ta shiga kuka. Nan ya tashi ya fita, uwar tace “nidai abinda zan gaya miki kiyi amfani da abinda duk nake gwadamiki. Banda zazzafan kishin nan, ya kamata ki koyi rike shi aranki, banda nuna shi koyaushe, ki zauna da kishiyarki lafiya ki zauna da ita da zuciya daya. Allah ya bada zaman lafiya.”
Nan laila ta mike ta fita, wanda already kayanta na motar. Tana zuwa soro ta tsaya ta goge hawayenta ta fita, ramadan na gaban mota hular nan ya karo ta gaba, idonsa da glass yadan juya suka kalli juna cikin ido. Sai yajuya yana murmushin gefen baki.
Gaban motar ta shiga asanyaye ta gaida shi ya amsa, shiru tai tana wasa da gefen gyalenta tana satar kallonsa. Wanda shi ma yakan saci kallonta. Murmushi tai tajuya. Shi kuma ya juyar da kansa gefe yana nasa murmushin. A haka sukai ta tafiya kowanne da abinda yake sakawa aransa.
Hmm laila dai an dawo koya zaman zai kasance