NAYI GUDUN GARA CHAPTER 35

NAYI GUDUN GARA 







CHAPTER 35




Laila kuwa tana komawa shashinta ta saka CD ta shiga turkar rawa, saboda tsabar Jin dadin da takeji na fasa auren nan. Jin kida ya sanya ladifa ta fito ta shiga shashenta tace “laila kinajin dadi kam.” 
“Yo ba dole nai rawa ba da murna, da tuni an kwaso mana yar aiki matsayin kishiya oh! Ni laila da ina zan sanya kaina.” 
Dariya ladifa tai tace “to Allah ya kara farinciki. Ai ba don wani abuba da nazo na taya rawa.” 
“Aiko dai ga fili nan.” Ta fada tana ci gaba da rawar. 
Haka dai al’amuran rayuwar gidan ramadan taci gaba da gudana kowa ya fuskanci abinda ke gabansa. Ogan kuwa ya maida dukkan lamuransa ga harkokinsa. 

BA YAN SHEKARA DA YA 

Laila ta saki jiki, domin tasan cewa ramadan ita yake shayi shiisa ya saduda. Don taga bai kara batun sako wata macen ba. Duk da hakan ta sanya mai ido saboda kar ya kuma jajubo wata a cewarta. 
Shi kuwa ta bagarensa Tsoron ma ya tunkari mace yake, saboda ‘yan kananun matsalolin da ya fuskanta, kawai ya rigada ya maida hankalinsa kan matansa ya daina tunanin komai. Wata ranar laraba. 
Tuki ramadan yake a hankali ya shiga unguwarda yake san shiga, fakawa yayi a daidai kofar gidansu abokinsa. Ya dau waya yayi kira, ba adade ba sai ga wani abokinsa nan yana dan dingisa k’afa ya fito, yana zuwa suka cafe ya ce “Alhaji ramadan, ashe haka ka zama bigi.” 
Dariya ramadan yayi yace “har na kaika? ashe ba kaji dadi ba, ciwon k’afa k0? ai jiya abdallah ke gayamin” 
Mahmood yace “wallahi ka ganni nan na auna arziki, lokacin da b’arayin suka shiga gidana, Allah ne kadai ya kare basu kashe ni ba, tsautsayin ya fad’a akafar, Allah ya so iyalaina basa nan a lokacin.” Ramadan yace “Allah ya kare gaba, yanzu a gida kake jinya ko?.” 
“E fa, gida nakejinya, hajiya na kula dani. Saboda uwargida na jego a gida. Haka dai sukai ta jajantawa. Fita ya yi daga gaban motar ramadan din ya yace mai bari ya d’auko wayarsa. 
Yana nan zaune cikin motar, kamar daga sama yana d’aga idonta ya sauka kan wata budurwa nan, ta fito daga gidansu, wanda ke daura da gidansu mahmood, sanye take da wani kalar hijabi ruwan kwai ajikinta. Irin hijabin nan ne me mannewa ajiki, dukya fito da surarta kota’ina, tafiya take kamar tana kada jiki, tafiyar tata ma abin kalloce, wanda kallo daya za kai mata ka dauka ko da gayya take,tunda ramadan ya kyellaro kanta ya kasa d’auke idonsa akanta. Har tazo dafda shi idonsa na kanta, dan d’agowa tai a fakaice ta kalli motar sai ta danjuya, shanyayyun kananun idanuwanta ne suka dada burgeshi, har ta wuce ya sai ta mudubi yana dubanta, duk kyanjikin da yake ganin hansatu na dashi to wannan a idonsa ta doketa, har ta bacewa ganinsa bai dauke ido ba. Wani wawan numfashi yaja. a 
A daidai lokacin mahmood ya dawo ya bude motar ya zauna, kafar sa d’aya me ciwon na waje, yace “ai ramadan akwai wani busineesl,” 
Ramadan kuwa hankalinsa sam! Baya ga mahmood. Sai da yajuyo ya kalleshi yaga sam! Hakankalinsa naga mirrow yana shafa sajensa kwata miliyan. Mahmood yace “ya dai?.” Ramadan yayi wani murmushi ya kalleshi yace ” inajinka.” 
Nan suka ci gaba da hira irin ta maza wanda a daidai lokacin budurwarta kuma zuwa ta shige za ta koma gida. 
Shiru ramadan yayi ramadan ya bita da ido, musamman ganin yandajikinta kejuyawa, nan ya kuma sakin ajiyar zuciya. Mahmood ya tabo yace “Wannan yarinyar da tazo ta wuce 
please a ina take ne?“. Dariya mahmood ya sanya yace “kana nan da halinka dai ramadan na son mata.” “Bana son shakiyanci, ni dai ka gaya min wani abu akanta dan agaskiya tayi.” 
“Okey safna sunanta, a inda ka gata shiga nan ne gidansu, ai dama nasan yanda kake dan san mata ramadan da wuya kaga yarinyar nan baka kyasa ba.” 
“Kaima kasan ba kowacce kalar mace ce ke burgeni ba, kuma ba kowacce nake kulawa din ba, sai wacce naga ta dace da kalar macen da nake buri. Kuma kasan bana kula mace idan ba aurenta zan ba.” 
“Ni mai gayawa wasu ne ramadan. Amma kai da kake har da mata biyu basu isheka ba sai ka kara.” 
“Ba ruwanka kaidai kawai ka gayamin idan za kai bana san sanya ido.” Dariya mahmood ya sanya yace “amma sai dai wani hanzari ba gudu ba bazawara ce.” Da sauri ya kalleshi “ita din?.” 
“Zan maka karya ne? Yarinyar irin sakin wawa ce, dan auren baifi wata uku ba ya mutu.” ” 
Sumar kansa ya shafa yace “lalle kuwa sakin waws. Gaskiya yayi asarar dakwalwa.” 
Mahmood yace “amma ko da Zaka sota yaci ace kasan mai yasa aurenta ya mutu. Duk da 
cewa ni ko a gida banji dalilin mutuwar auren ba daga farko sai kwanaki ne. Naji wai mijin madoki ne shiisa auren ya mutu.” 
amma kasan ni babu wani abu da ya dameni da ita wai  bazawara ce amman fa komi yaji babu makusa fa, ko tafiyarta abin kalloce kamar tarwada. 
Dariya mahood ya sanya cike da tsokanar ramadan yace “koni nan ba don kubra da kishinta har da na sayarwa ba, ta kasa ta tsare ai dana fasa kai gurin safna.” 
Tsaki ramadan yayi “yanzu ma ai bata baci ba, well ni bana son na bar nan ba tare da wani contact nata ba.” Kafadarsa mahmood ya dafa “karka damu zan amso maka lambarta sai ka karasa ladanka. 
Tafawa sukai ramadan ya ce “godiya fa nake,” nan sukai sallama ya tafi. 
K’arfe uku na yamma ramadan ya k’arasa gida yana shiga ya zauna afalo ya daga kai sama, sai ya saki murmushi, laila ya shiga kira ba jimawa ba sai gata nan ta fito sanye da riga da siket na atamfa kalarja da bak’i, da kwalliya rad’au afuskarta tana rike da hannun najwa da take yar shekara daya da wata biyu, an sanya mata riga pink mai kyau, da wani takalmi na yara blue, an sanya mata riborm kalar pink da blue da aka daddaure mata 
gashinta da shi daya ke tana da suma mai yawa. 
Murmushi ramadan yayi ya mikawa najwa hannu ya d’auketa, yana son yarinyar musamman da yake ta ci sunan mamansa. “My baby cute kinyi kyau.” Sai ta sanya dariya ya zaro alawa ya bata. 
Laila kuwa wani yauki da yanga ta tsiri yi saboda dama abinda take so arayuwarta kenan ta ganta ita kad’ai da mijinta sai ‘yarsu. Ayauta dada burin dama ace ita kadaice matar ramadan. 
Zama gefensa tai tana mai sannu da zauwa sai iyayi take, iyayin nan dai na nan dai ba ta fasa ba, dan ma watannin baya kazanta ta so dakusar da ita, ta so ta kassara zamanta da ramadan wanda har k’ararta ya kai gidansu na kazantar, saboda yace baya son kazanta.Amma yaga kamar ba ta ji. Alokacin mamanta ta zo tayi mata fata -fata take cewaa ba ta santa da kazanta ba, ita da ta santa ’yar kwalliya, amma duk ta maida kanta buzuzu daga haihuwa d’aya, karshe ta ce mata wallahi idan ba ta daina ba za ta saba mata. 
Ta kuma tsora tata da cewar muddin miji ya nuna bai san abu wajen matarsa to indai ba ta 
daina ba. To kuwa zai samawa kansa mafita indai yana da dama. 
Wannnna dalilin ne yasanya ta rage taiwa kanta fad’a, musamman ma ganin yanda ya canja mata, kwata-kwata, hakan ya sanya taiwa kanta karatun ta nutsu ta fara ragewa ta fara dawowa da tsaftarta.Tare da rage san jiki da k’yiwa. 
Murmushi tai ta ce “abban najwa annashuwar me kake ne?.” 
Kallonta yayi yace “na ganinki ne mana,” wanda akasan ransa kawai na tunanin haduwa da  ne.
Suna cikin magana sai ga sallamar ladifa nan ta shigo cikin shigar wata doguwar riga ta 
material d’inkin buba. Mai zanen fari da baki da jaka ahannunta. Fuskarta cikin simple 
make up, da murmushi ta karasa inda suke, ramadan ya kalleta “baby sai yanzu ko kalli agogo. Ba fa banasan dad’ewa a waje.
Dan alamar shagwaba tai tace “am so sorry zaujina motar ce mai ya kare, sai da kamalu ya sayo. Kuma dad’ewa duk fuad ne ya dad’ar dani, saboda yau ma yace ba zai tawo ba.” 
“To shi ke nan naji.” 
Laila ta dan tabe baki ganin yanda ramadan ya wani kafe Lad’ifa da ido. Wanda acikin shekara D’ayan data wuce ta riga ta gane cewar ladifa itace matar da ramadan ya fiso, dan ba irin haukan da fushin da batai ba, amma shi k0 ajikinsa, komai yace Lad’ifa kaza, ladifa kaza, ko shawarace da ladifa yake farayi kafin ita, gashi ko a gabanwa sai ya nuna yayi missing d’inta, wannan dalilin ne ya ke raunata d’an zaman lafiyar da suka samu, dan duk ranar da kishin ya motsa laila saita nuna cikin habaici, idan kuma abin baya kanta sai su zauna kamar ba kishiyoyiba. 
Gyara zama ladifa tai tace “da alama dai yanzu ka dawo ko?.” Kaiya d’aga mata yana ma najwa wasa, 
Mik’ewa tai tace “bari na mik’o maka ma zobo drink da nai kafln na fita nasan ka shawo rana. 
Murmushi yayi ya bita da kallo, abinda ya sanya kenan take gaba adukkan komai nasa, wannna halin nata ne ya sanya ta samu wani irin matsayi aransa, shi ya dad’a sanyawa sonta ke hanashi nutsuwa, yarinyar tasan ta kansa tasan me yake so, da wanda baya so, wanda ko farin cikin ya keko bakin-ciki yake, to haka zata taya shi, idan a makwancinsu ne ta karbeshi hannu biyu, ba musu da raki, wannan dalilin ya sanya k0 yaso yi mata wani abun yakan hakurewa. Musamman wasu lokutan yakan tuno lokutan daya ringa sa ta a kunci, sai ya ji duk bai kyauta ba. 
Sab’anin laila da yanzu za tai abin arziki kamar ba ita ba, dan inta so ta kanyi abinda ke dada d’a ransa. Amma baza ajima ba za ta zobe ladan, ko tai mai gori akan wani abun, tayi rashin mutunci, gashi ita bata fiya damuwa da wai damuwarsa sosai ba, indai ba ta shafeta ba, ita dai damuwarta kawai ta sani data yarta. Gashi idan ya dawo bata fiya ta tarbarshi ba, har sai anci sa’a, dan wani abin ma da zai sanya yaji sanyi a makoshinsa ba zata bashi ba, wala Allah ko ya kwaso rana ko makamantan haka, ah wataran ma yana dawowa zata fara korafin abu kaza, baby najwa ba lafiya, ko yayi mata laifl kaza, yaki yin 
kaza, ratarta da Ladifa na da yawa. ‘ 
Dawowa tai rik’e da cup glass ta mika mai yasha yana santi, ya bawa najwa ta sha, laila ko tab’e baki kawai take dan haushin lad’ifar kawai ta ke, ita ta tsani gulmar nan ta Lad’ifa wai duk dan ta samu shiga wurin miji. Tsaki tai ta d’an gyara zama. 
Ta kalli Lad’ifar da d’an yak’e afuskarta hmm yanzu shi fuad ya ma manta da kanwartasa, ya ki dawowa.” 
Lad’ifa tai murmushi tace “kinsan shi da hajiya, (hajiyar ramadan) tunda dai tai mai yayen nan, shi kenan ya makale mata. Yau ma ai ina shiga gidan ya shige bayan hajiya da gudu yana cewa “ni Aa. Ya dauka tafiya zan dashi.” 
Dariya laila ta sanya ta ce “kai duk kulaficinsa da ke? amma kinga ya makalewa hajiya.” Ramadan ya ce “ai ita shagwabashi take ne dole yafi san can.” “Ni ai na wuta da fashe -fashen kayan falo na da yake min.“ Suka fasa dariya. Mik’ewa laila tai da sauri dan duba girkinta najwa ta bita abaya. Ganin haka ya sanya ramadan ya ce muje sama baby kiciyar da ni yunwa nakeji.” 
Murmuahi kawai tai sukai saman. 
Washegari 
Lambar safna mahmood ya turo mai sai ya samu kansa da murmushi.Buga mata waya yayi tana ta ring ba a d’auka ba, sai daga can aka d’auka, amon muryarta ne ya daki kunnesa ya 
ce “ramadan ne, hope zan samu ganinki inna zo gidanku yau?.” Dan daburcewa tai na nuna alamar rashin sani “daga ina please?!‘ “Ki bani dama kawai, ba sace ki zan ba, da alama za kiyi tsoro.” Sai tayi dan murmushi, “okey sai kazo.” 
Nan ya kashe karfe takwas na dare ya fece, lokacin girkin laila ne ganin yanda yake ta farfesa turare yana gyara zaman hular zanna dinsa, ta kalleshi ta ce “abban najwa ina kuma za ka?.” 
“Inda kika aikeni.” 
Zuciyarta ce ta shiga raya mata cewa lalle fa da inda za shi. Gabanta ne ya fadi ‘kardai wajen budurwa za shi,sai ta kuma kallonsa. “Amma da daren nan kake wani kashe kwalliya.“ 
Dariya yayi yace “ki ka sani koke nake yiwa? Kefa kin fiya kishi. To wurin abokina zani, zan rakashi wani guri.” 
Dan murmushi tai tace to a dawo lafiya, ba wai dan zuciyarta ta aminta ba. 
Karfe takwas da rabi ya faka a kofar gidansu safna, nan yayi ma safnar waya dan ita tama manta dashi, saida ya sake bayanin kansa, sannan ta gane gayawa mamanta tai ta fice. 
Da yake akwai hasken kwai a kofar gidan, ya haskaka safna, hakan ya bawa ramadan damar dada kare mata kallo, tana sanye cikin doguwar riga ta atamfa, da farin mayafi, komai ya fito das! duk abinda ramadan keso da mace ya riga ya gama ganosu jikin safna, nan ya bud’e ya fito ya tsaya ajikin motarsa, kallonsa tai ta dan maida kanta kan wayar tana dan nata. 
Gyara tsayuwa ya yi ya kuma balance da jikin motar, ya ce “aduk lokacin da mutum ya ga abinda ya narkar da ruhinsa ba zai kasa agwiwa ba, har sai ya shigar da kansa.” 
Sai ta dago ta kalleshi dan ta fahimci inda ya sanya gaba. 
Nan yaci gaba “wato na ganki kuma na yaba dake, ina da burin ki zamo mallakata. 
Murmushi tai ta dan sunkwi da kai “to godiya nake. Amma kasan ni bazawara ce.” 
Dake da budurwa baku da maraba,  banida damuwa fa, ya fad’a yanajifanta da mayen kallonsa, nan da nan taji ya burgeta ba taja aji ba ta karbi tayinsa. Tun daga rananar suka dinke. 
Kashe mata kudi kawai yake,danshi ramadan irin mazan nan ne da ke sakarwa macen da suke neman aure kudi, a ranar daya farai mata kyautar farko ta shiga gidan mamanta ba karamin murna tai ba. Ta kalli safna tace “da alama zamu bawa marada kunya a gidan 
nan. Safna tace “kwarai ma baki ganin yanda ‘yan can d’akin su saudat ke wani iyayi wai dan murja na auren mai kud’i ba.” 
Uwar tai murmushi tace “to gashi kema Allah ya baki, kuma karki sake ya kufce miki.” 
‘Safna yace a zidan malam karami. Wanda ke d’an kasuwa ne. matansa uku .maman safna 
ita ce ta biyu, gidane da suke da yawa sosai! kuma komansu a hade, ma’ana gidane mai 
fllin tsakargida, mai d’auke da bandaki a tsakar gida da kitchen da rijiya a can gefe. Sai 
kofofln d’akunan matan, wanda yake ciki da runfa runfa da bandaki, sai d’akin maigidan acan gefe daura da tsakar gida. 
Sai d’aya gefen d’aki biyu falle guda 2 na yaran gida ne,wanda akalla yaran gidan za suyi goma sha biyar. 
Adakinsu safna ita ce ta biyu, tana da yaya namiji sai k’annena mata biyu maza biyu. 
Ana taba kishi agidan nan, dan hatta yaran sun san makamar yanda ake zaman kishi kala kala kusfa -kusfa. D’an wancen dakin karya yake ya taba abinda bai danganci nasu ba. Ana yawaitar fad’a agidan. Ga gasa abinda wancen dakin sukai sai wancen ma sunyi, musamman ga ‘yan matan gidan idan wata na da saurayi mai kud’i waccen nata takala ne, sai ai ta mata dan habaici. 
Aduk cikin matan gidan kuwa, mamman safna tafi kowa son mayatar kudi, kamar taci babu, shiisa da yake safna na samun masoya tunkan tai auren suke ci da kudin samari burinta kawai ace yaranta sunfi na kowa a gidan. Haka ace mazajen yaranta sunfi na 
sauran kudi. 
Safna wankan tarwada ce, kalarfatarta mai kyau ce, sannan Kokadan safna bata da kyau a fuska, hancinta dan gajerene mai dan fadi . Sannan bata da cikar gira. Sai ta zana jagira take kyau. Ga idonta mitsi mitsi ne sosai sai dai masu kyau ne dai a Iumshe suke, sai ka dauka ita take Iumshe su, wanda kawai halittarta ce haka. Hakan ma na dada sanyawa ta dan fito tai kyau. Gashi kwaikwido ce, sam! bata da gashi da yawa, in akai mata kitso jelar ‘yar mitsil za ka ganta. 
Amma fa Allah yayi mata halitta ajiki, dan in ka sanya mata dari kafin kaga mai irinjikin safna da wuya sosai. Wanda ‘yan matan gidansu na hassada ma sosai da irin jikin safnar, ganin cewa duk tafi ‘yan matan kyan jiki mai d’aukan hankali, sai dai sauran wasu duk sun fita kyau a fuska, akwai lukutaye a yan matan gidan sosai,akwai kuma sirara, ita safna bawai lukuta bace can, amma komai na jikinta acike suke tsam! musamman hips nata da kirjinta, babu rama ko kadan ajikinta, ita ba lukuta bace kuma ba ramamiya ba, amma tafi kusanci da ‘yan dumadumai, fuskarta round face ce, gashi duk kayan da ta sanya sai sun amshe‘ta sun mata kyau sun zauna das! kamar ajikinta ake d’inkawa. 
Hakanjikinta keda kyau, Kirjinta tantsam yake acike taf! dan ko bata sanya bra ba, haka suke car dasu dam! Tana da fadin kugu sosai! kuma mai tudu wanda ko yaya ta taka sai hips nata ya motsa haka kirjinta. Sannan kuma bata da tumbi. Sannan akwai kyawun tafiya mai d’aukan hankali. Ko acikin kawayenta, safna na alfahri da kyawun jikinta, idan ana mata kurin kyau na fuska ko rashin gashi, sai tai dariya ta ce “diri iya diri muna da shi, kyan taflya kuwa babu mai kere mu, baiwar mu ce haka, dan haka mun wuce gori, ko ba mu da wancen muna da jikin cikakkiyar mace.” 
Ramadan hankalinsa kacokam! yankoma kan safna bunnsa kawai ya sanya ldO akanta sosai yarinyar ke tifiya da shi, musamman idanuwabta duk da suke mitsi mitsi ne amma yanda suke alumshe kamar tana jin bacci ne ke dada sanyawa yaji d’ari-bisa dari safna ta yi. Duk da cewa kokadan ba ta kai matansa kyau ba afuska, dan ko laila tafi safna kyau a fuska, ladifa kuwa dukka ta kere su a kyau, zubinta kamarzubin ba indiyawa ne. Amma fa ajiki kam sai dai duk su koma baya dan safna karshece. 
Ramadan sai ya kai goma a wirin safna suna hira,musamman da take da zakin murya mai dad’in sauraro, kuma magaanr ma a hankali take yinsa kuma cikin san burgewa. Hakan ke 
dada sanyawa ramadan yace lallai tsohon mijin safna yayi asarar mata. 
Lamarin daya fara damun matansa kenan, musamman laila, dan ta kula ma sai ranar girkinta ya fi ma yin hakan. 
Wata rana ya dawo da yake a dakinta ya ke, bai ma shiga d’akinta ba, direct sama ya zarce kawai ya watsa ruwa yana fitowa wayarsa ta hau kara, sunan safna ya gani, wanda ya sanyawa suna saminu saboda tsaro, murmushi yayi yace “ranki ya dade, da alama yau missing dina kike da yawa.” 
Murmushi tai ta lumshe idanuwan nan nata, ta bude su tace “ba wani abu bane kawai dai kewarka ke damuna, shiisa na bugo, yanzu ma haka ina dan waje ne ina neman wani kanina yazo na aikeshi. 
Zama yayi kan gefen gado ya ce “keda kanki? me zakiyi?.” 
“Cikin zakin muryarta wanda ramadan kejinta hartsakar kansa, tace “umma ce tai tuwo, 
shiisa zan bayar asayomin fulawa nai waina.” Murmushi yayi yace “aiko ni ma’abocin cin tuwo ne, sai ki daura damarar yi min” Dariya tai tace “ai ba damuwa.” “To ko dai nazo ne? sai nayo miki take away na kalar abinda kike san ci?.” “Danjim! tai a yi haka?.” “To meye ne yanzu takwas zaki ganni.” “Okey sai kazo” Ta katse ta koma tana tafiyarta mai kama da tana girgiza jiki. Wanda kalmar karshe ta ramadan akunnen laila taji, dam! gabanta ya fad’i, cikin wani irin sauri ta karasa kirjinta na sama yana kasa saboda tsabar kishi. Cikin wata iriyar muryar tace “da mace kake waya ko habiby.” 
Ta fad’a cikin sauri da fargaba. 
Yaso ya dan dabarbarce, sai ya kau da kai yace “ke babu dama kiji ana waya sai kice da macene, haba ki dinga bin abu a nutsuwa mana, haba dagaji ina waya, to da saminu ne abokina yanzu zanje mu had’u kan wata mastala. 
D’aukan wayar tai idonta ya kawo ruwa ta shiga bincika ba irin duban da batai ba, sam! bata ga ko sunan mace ba, sai saminu da sukai waya yanzu. 
Fusge wayar yayi yace “kar hannuki ya kara yimin bincike a waya na gaya miki.” 
“Dole nayi saboda hanyar lafiya a bita da shekara, dama gaya maka zan na gama dinner ka fito muci.” 
“Ba zan samu dama ba, kici naki kawai.” Tsai! ta tsaya tace “akan me?.” 
Tsaki yayi, yasan halinta da damuwa, sai yace “ki ajiye inna dawo zan ci,” 
ya juya fita, ita dai ta kasa gasgata komai daya fad’a mata aranta. 
Yana fita ya shiga wajen Lad’ifa tana kwance akan kujera kallon wani indian take ciikin shigarwata doguwar riga cotten bata da nauyi sosai mai gajeran hannu. Fuskarta d’auke da simple make up kwalli powder man leb’e. Kanta a tsefe ta tufkeshi. Ya zubo kafad’arta 
tare da d’aura d’an sirirn d’an kwali. 
Tayi mai bala’in kyau a ido. Peck ya bata a kimatu, yace “baby zan fita ki ajje min sweet mana.” Ya fada yana mata wani kallo. 
Murmushi tai ta kalleshi ba kyau zargi amma zaujin nata kwana biyu da alama wajen wata yake zuwa hira, dan ta riga da tasan shi ciki da bai, sai tai sauri ta kori shaid’an karya sanya ta zurfafa acikin tunanin data fara.” 
Cikin taushin murya tace “akan me zan ajje maka sweet bayan bani ce da girki ba..” 
“Please baby.” Dafe kanta tai ta ce “kayi hak’uri zauji, ni kam babu ruwana abinda ba zanso aimin ba ba zan ma wata ba, kaima kawai neman so ai rigima ne, d’aukan hakki ne ma ba kyau.” 
Hancinta ya danja yace ” Ina alfahri da ke my beauty, ina son tsarinki Allah yayi miki albarka i love you .” 
Fuska ta rufe ta ce “mee too.” Mik’ewa yayi tace “dan Allah ka d’auko mini fuad. Allah ina missing dinshi.” 
Dariya yayi yace “ba ruwana kinsan hajiya tace yaje kenan ta kwace shi. Kuma shima fuad ya ce sai hajiya.” 
D’an kuma takowa yayi ya shafi cikinta ya ce a“daure a k’ara haifo mana baby.“ 
Mirmushi tai tace “to Allah ya kawo.” 
Ameen yace ya fita 
Saida ya biya ya sayowa safna abinci a restuarant mai rai da lafiya da kayan sanyi sannan ya d’au hanyar gidansu, yana zuwa yayi mata waya ta fita, wanda ‘yan dakin su kaure sai lek’owa suke suna kallonta, lokacin da suke tsaye da ramadan. 
Kallonta yake suna hira, ya shiga tunani aransa, wani hanin ga Allah baiwa ne, bai samu hansatu ba, gashi nan yanzu ya samu wacce ta dokewa hansatu ta koina kuwa, ga ta yar cikin birni, kyan fuska kawai hansatu za ta d’ara safna, dan shi a idonsa ma bai ganin wani rashin kyanta afuska, dan sosai matuka halittar idonta ke mai kyau. 
Sun dade suna hira, wajen a yayi haramar tafiya, sanin cewa tana son taci abinci, motar ya koma dauko mata manyan ledodji biyu ta amsa. Tace “thank you sugar na.” Sukai sallama bai shiga ba, ya bita da ido musamman yanda take tafiya sosai tafiyarta ma ke matuk’ar burgeshi. Numfashi yaja yajuya ya tafi. 
Ana tsaka da haka watan azumin ramadan ya kama, nan kowa ya maida hankalinsa kan ibadar Allah. Da yake da zumi ne sai su Lad’ifa ke yin kosai da kunu na duka gidan wanda har almajirai uku ladifa ta samo ta ce suna zuwa suna amsar abinci na sadaka sabida azumi, wanda da laila tai magana ladifa tace “ahh abinda fa mutum ya bayar shine rabonsa. Kuma duk wanda ya ciyar da mai azumi ai ladansa nada yawa agurin rabbu,  baka ladan mai azumin, watan da kowa ke neman da cewa sai da hakan.Sosai ake san mace ta yawaita sadaka ko ba acikin azumi ba. Wannan dan jawabin ya sanya laila tace “to shike nan damani nai magana ne saboda kar abban fuad yayi magana.” 
Lad’ifa ta ce “shima ai hakan zaiso. Na yi mai magana ai.” 
Bayan kunun da suke yi sai kowacce tai na ta a b’angarenta abinda take san dafawa, wanda ramadan asha ruwan tsuntsaye ya kewa kayan dadin da sukeyi. Musamman duk ranarda Safna ta hada mai kayan shan ruwa wanda zata zagejiki tai mai abubuwa kala -kala, wanda bawai fin na gidansa yayi ba,asalima ma na gidansa yafi kayan dadi, da. Dandano Amma da yake ita yake yayi ya sanya yake kejin girkin nata har tsakar kanshi, haka yake zama yayi nak in zai tafi ya aje mata manyan kudi .Wanda ita da mamanta kejin matukar dad’i, nan fa habaici ya motsa, kaji uwar nace wa “bazawara mai farin-jini yau gashi za ta kuma shigewa tabarwasu tsaranta na zaman dabaro. Alhamdlh Allah ya kashe ya bawa yarinyata, maki gani ya kauda ido. 
ldan ta ciyo sauran matan gidan su tofa gida ya kaure ana haibaici -habaice da fada.‘ 
Yau laila ce da girki wanda daman duk wacce ke da girki da abincinta maigidan ke shan ruwa. Hakan ya sanya laila yau ta shirya yin delicious sosai da Ramadan zaiji dadinsa sosai! dan abinda babu ma haka ta dau mota bayan ta tambayeshi za ta dan fita taje ta sayo. Tun uku ta fara wasu abubuwan ga rigimar da baby najwa ke mata, duk ta hanata sakewa saida lad’ifa ta dan taimaka mata ta dauketa ta goya ta, sannan ta samu salama. Sai wajen shida ta samu kanta wanda abubuwan ba wai da yawa tayi su ba ‘yan caf cafta yisu kayan dad’i kala-kala daidai tabawa. 
Aranar kuma safna ta hadama ramadan girki itama.Tunda daya dauko hanyar gidansa, 
wanka zaije yayi ya kawai ya tafi gidansu safna lokacin safnar tai ta kiransa. Kan cewa ta hada mai kayan shan ruwa, duk da tasan cewa yana da matansa a gida kuma zasu tare shi da nasu, amma ita ba damuwarta bane, aganinta kyautata mai ne. Yanda za ta dada rike shi gam! Ajikinta. Sai daya biya ta masallaci yayi sallahr magrib. Sannan ya dau hanyar gida. Bayan ya karasa gidan yayi duk abinda ya saba na al’ada. Zama yayi ga kaya nan birjik na cima an jere mai kallon laila yayi yace “anya kuwa zan sha ruwa anan?.” Wani kallo laila tai mai tace “kamar yaya da ina kake shan ruwan?.” 
“kinga wani abokina ne ya hada mana shan ruwa agidansa, dalilin da ya sanya kenan, kuma shi keta kirana.” 
Da sauri ta dau wayar zata kashe, kiran ya kuma shigowa ta ga an sanya saminu. Sai ta saki tsaki “kai wannan saminun ya fara shiga hancina da kudundune wallahi zan mai rashin mutunci, akan me sai dare zai na kiranka, shi bai san kana da iyali bane. To wallahi babu 
inda za kaje su cinye. Next time kaje.” 
Kiran ne ya kuma zuwa kit ta danna wurin kashewa ta ajje wayar gefe tajuya. Dan idonta har ya kawo ruwa. 
D’an daburcewa yayi yace “yanzu saboda Allah meye na kashe min waya. Zan sabar miki 
fa laila ban fiya san irin haka ba fa.” Kuka ta sanya har da su shashsheka.Cikin kuka ta ce “kasan tun lokacin da nake aikin nan kuwa komai fa dan kai na yi amma zaka tulan kasa a ido.” 
Ganin yanda take kuka ya fara kokarin ci. Sai ta share hawayen ta zauna ganin yanda take ajiyar zuciyar yayi murmushi yace “laila rigima. Dan dariyar yake tai ta ce “ai kaine” A lokacin ladifa ta fito itama suka dada mantar da shi. 
Can wajen safna kuwa, jin an kashe wayar ya sanya taji haushi sosai, sai taga ko wulakanci ne ramadan yayi mata, ga shi ta kashe kudinta, ganin ba zuwa zai ba sai suka cinye abinsu wanda duk ba taji dadi ba. 


Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *