NAYI GUDUN GARA CHAPTER 41

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 41

Ta dade tana kuka sannan ta tashi ta shiga hada kayanta. 
Ladifa ta dade a zaune sai da taji daidai sannan ta hau samanta, laila kuma ta shiga dakinta.. 
Duk wasu muhimman kayanta saida ta hada sannan ta tafi. 
Tana zuwa gida ta shiga dakin mamanta. Allah yaso babu kowa a tsakar gidan. Maman na zaune tana kulla wasu abubuwa a leda ta ce “safna daga ina haka?.” 
Safanar ta zauna ta fara hawaye “ya sakeni.‘ 
Wani irin zabura tayi, taja da baya tace “kalu innalillahi wa inna ilaihi rajuun,‘ yau naga ta kaina, shi kenan makiya sun sakoni a gaba, yanzu wannan ma sai da kika kashe shi ya mutu.‘ 
ta kalleta tace “mama kiyi kasa da muryarki karsu ji dan dariya za ai mana.” Zama tai tace “to ke meya hadaku?.” 
Ta gaya mata komai karya da gaskiya tace ‘cabdi yanzu akan matarsa ya sake ki? Ai da kin hakura kin zauna talaucinsa ai ba lalle ya dore ba.‘ 
“Mama ni ba zan iya zama ba wallahi na taso cikin talauci kuma na koma masa ba.Gaba gaba ma gidan sai mun barshi, dan fa baki ga yanda komai ya tsaya agidan ba.‘ 
“To amma ai yana da kudin ba kince an rike kayansa bane” Tace E! 
“To ai ko ba dade ba jima zai fito. Ko ba komai gwanda can anan, ni yanzu bansan yama zan da surutun jama’a ba gaskiya safna kin batan rai.” 
Koda washegari babanta ya ganta agidan yace kwanan me take sai ta kada baki tace “ai mijinta ne yayi tafiya shi,isa tazo ta zauna, kuma matansa duk sun haihu suna gida ta shirga karya wanda ‘yan gidan kawai sun sanya ido ne basu yadda ba. ’ 
Haka suka bagarar da mutan gidan. Suka ishi nuna isa da gadara agidan nasu yanzu sunfl karfin kowa na gidan. Kayan cima kuwa sai wanda suka ga damar dafawa. Wanda suna cine duk da kudaden satar da safna ta sato ne. 
Bangaren gidan ramadan kuwa yanzu zaman lafiya ya fara wadata agidan, shi kansa yanzu ramadan ya gane dubun mistake din da yayi, da ace akomai ya nemi zabin Allah da ba haka ba, kuma da ace tun farko da abokinsa ya ce yayi bincike akan mutuwar auren safna da yayi da yasan wasu matsalar basu faru ba, kawai alokacin idonsa arufe yake, wanda gani yake bukatar son zuciyarsa ne kawai maslaha ga rayuwarsa,
wanda aka ce daga son zuciya sai bata, babu inda son zuciya ke kai bawa sai mahallaka. 
Haka ya hade kan matansa dan kam shi daya kara wani aure kam sun ishehi, ya riga daya gane su neza su iya zama dashi a kowanne hali,tunda gashi a sanadin rashin kudin daya same shi, safna ta rabu da shi. Wanda ga shi su suna zaune da shi a haka. 
Kwana biyu basu ga safna ba, da suka tambayeshi yace tana gidansu dan koda hajiya ta tambayeshi ya gaya mata. Farko tace “agaskiya banji dadin sakin nan ba, bana son saki arayuwata. Sai da yayi mata bayanin cewa safna sace sace take mai, abubuwa dai kala 
kala, maman tajinjina kai ta ce “gaskiya mace mai sata kuwa ba abokiyar zama bace, dan ba zata
Zama uwa ta gari ba. Allah dai ya raka taki gona wannan ba matar arziki bace sai kuma kayi hankali. Ka hakura da wannan aure auren ka zauna da matanka atoh.’ Tun daga nan ya komar da hankalinsa kan gidansa da aikinsa. Kuma yana ta fafutukar yanda kayansa zasu futo. 
Wata ranar talata ladifa na gyara dakin ramadan, ta kalli cctv camera din dakin, sai taji tana son ganin meke da akwai, ta kunna babu wani abu sai lokaicn da ita zatai shara ko safna ko laila. Wajen karshe taga lokacin da ramadan ya shiga da jaka. Sai ta ga safna ta zugejaka,ta dibi kudin nan ta zuba adankwali da fita aguje, taga kuma lokacin da ya fito ya dauka ya tafi Sai ta dafe kai dama safna ce me sace-sacen nan! lailai biri yayi kama da mutum. Sai ta ajje da mamaki a ranta ta barwa zuciyarta lokacin ramadan baya nan. Ta fita ta sauka kasa. 
Da dare bayan ya dawo ta shiga dakin ta zauna gefensa yace ‘matata.‘ Tai mai sannu da hutawa tace “ina so kadan duba wannan CCTV camera dan kaga wani abu. 
Sai kuwa ya duba ya shiga, cike da mamaki yace “safna! safna! ashe itace sila, itace tai min sata, sai ya tashi yana kai kawo lalle mamakin safna yawa gare shi. Kallon ladifa yayi yace “safna ta bani wahala, nan ya ringa gaya mata duk irin abubuwan da tai mai, wani tai dariya wani taji takaici wani tace maganinsa kenan azuciyarsa. Da kudiri ya kwanta wanda washegari yaje police ya kai musu report nan suka ce karya damu za suje gidan. Ba yajin zai ragawa safna dan kowanne hukunci sai an mata wallahi. 
Cike tsakar gidan yake ana fada harda su zage zage, saboda yan
gidan sun gano auren safna ya mutu wanda anan sukai ta shewa ana yada magana, inda maman murja tace “yo dama aina fada ramin karya kurarrme yanda akai na farko haka akai na biyu.” 
Hakan data fada ne ya harzuka mamamn safna ta shiga surfa zagi kan wai sune sukai ma safna asiri aurenta ya mutu. 
Maman murja tace “ai wallahi indai ba zaki daina sharri ba to wallahi yarinyar nan ko 
tayi aure goma haka zata dawo, Idan ko aka kaita ta zauna agidan to karshenta ba zai kyau ba, duk munji labarin irin zaman da tai da irin mallake miji da akai da asiri ai.’ Maman safna tace ”karya kike wallahi sharrinku ne kuma wallahi yanda auren safna ya 
mutu sai na murja ma ya mutu, sai dai suyi biyu babu” maman murja tace “wallahi kome ya faru kece.‘ 
Suna cikin wannan badakalar ta bala’i motar ‘yan sanda ta tsaya a kofar gidan, wata murtukekiyar mata ce mai kirar masu karfi da ke sanye da kayansu na ‘yan sanda ta doshi gidan. Ta shiga. 
Tai sallama ba ajiba saboda hayaniya kuma sun cika wajen. Sai da ta karasa tace ‘salamu alakum da karfl’ 
sannan suka ganta, nan fa duk suka dare kowa ya koma gefen dakinsa suka zaro ido, “mun shiga uku hukuma agidan nan, maman murja ta fada. Ta hada hannunta biyu guri guda 
An rasa wa zai mata magana sai can maman safna ta fita tace “baiwar Allah wakike nema ne, ta ce Ramadan yayi karar safna ta mika takarda. Muna son tazo tabi mu idan anje can 
taji ko meye.‘ ‘ Me tayi wai haba ta yaya za ace za a tafi: da ita Maman murja tace “yo tunda kika ji ance Ramadan tsohon mijinta ai kinsan wani abun ta tafka.” ‘Ta Allah ba taki ba maman murja.” “Sorry ku fito mana da ita.” ‘Yar sanda ta fada. Dafe kirji safna tayi tana daga cikin daki, tace “shikenan ta faru ta kare.‘ 
‘Yar sanda tace malama ki fito da ita muna jira”, maman murja ce ta shiga falon ta turo safna tace “gata nan duk abinda akace tayi tofa tayi da wannan makirar uwar tata.” 
Nan fa matar ta tasa keyar safna sukai waje, take gida ya dada hargitsewa, mamanta na kuka, da sauri maman ta zari mayafi, suka bisu duuuu! sauran suka biyosu waje,yara sun tsaya kallo suka shiga maman safna tace “baiwar Allah inane police station din ta gaya mata, nan tai bakin titi cikin sauri tare da tura nazir ya kira babansu. 
Da akaje police station da ita. Ramadan yazo suka kallijuna ya kauda kai, sai ta fasa kuka nan ramadan ya kuma maimaita lefin da safna tai mai na satar kudi har miliyan uku. Da 
yake ya tawo da videon ya nuna musu suka rubuta statement. Itama aka tambayeta aka rubuta statement dinta. 
Lokacin da baban safna sukaje da mamanta da yaji yace daman ko ba dade ko bajima, sai kin girbi abinda kika shuka ya fada yana kallon maman safna ya ce gashi nan idan nai magana ban isa ba, kuma nasan duk kece da alhakin sanyata wani abu, dan haka ni banda komai ban san yanda zan ba. Ya tafi maman safna ta sanya kuka Lokacin da ramadan ya koma gida ya sanar da matansa abun sunji babu dadi lalle Allah yaso su da rahma da ya rabasu da safna, haka suka dada tsorata da duniya. 
Ranar da za a zauna maman safna ko tsakar gida ta kasa fitowa, dan tun abinda ya faru ta daina zaman tsakar gida, sabooda magana ake gaya mata, karara suke cemata uwar barauniya. Da tai magana suce ai yanzu ba ki da bakin magana, saboda mun san fari balle baki, shima mijinta na farko ai munji shima zuwa akai aka so a tatukeshi aka malakeshi da yake uwarsa atsaye take, ta sanya ya yanko yar wata uku da aure, maimakon a saduda aka kuma cin buri, ai gashi nan idan anki cin biri anci dila.”
Sai dai maman safna tai tsaki tace “waya wuce kaddara ne.?.” 
Dakyar ta fito da mayafi ita da muftahu babban danta, suka tafi kotun Iokacin already safna na can, da suka je har kuliya ya zauna safna na kan wajen tambaya . Nan aka fara shariar inda ake tuhumar safna da lefin satarma tsohon mijinta kudi har miliyan uku wanda ya shafi abubuwansa da yawa. 
An gabatar da video da safna ke satar. Wanda ita ce shaidar ramadan. shariar bata bada wahala ba saboda komai yazo cikin sauki,ta amsa lefinta inda kotu ta yanke mata hukunci cikin laifi biyu, akace ta biya kudin data sata k0 kuma tai shekara a gidan yari. Sannan ga lefin sata, shi kuma sai anci ta tara ta biya dubu ashirin k0 tai wata biyar agidan yari. 
Ana gama shariar alkali ya tafl, safna ta sanya kuka tana kallon ramadan, k0 ta kanta bai biba ya fice. Nan aka tafi da safna cell din kotun kafin agama setling. 
Muftahu ya kalli maman safna dake kuka, yace mama shi’isa nake gaya muku ku ringa komai a sannu gashi nan shi bai duba zaman auren da sukai ba yaki hakuri. 
Maman tace ina zai hakura yaci moriyar ganga, yanzu dai muje akwai ragowar kudin, ta gayan inda suke kaga idan aka kai wala Allah. Komai yazo da sauki. Sannan ina da wata sarka zan baka asiyar sai a bada dubu ashirin din na lefin satar, domin idan akace yarinyar nan ta zauna gidan yari ban san wanne irin zama zamuyi agidan nan ba. 
Sunje gida matan gidan suna Allah ya tsare gaba wanda duk da biyu suke, kudin taje ta dauko da sarkarsuka koma can kotun sukaje  bangaren masu karbar kudin nasu da aka yanke musu. Anan aka kirga dollarda kudin nigeria aka ga sunci dubu dari takwas ne saura milyan biyu da dari biyu. 
Muftahu yaje ya sayar da sarkar nan zuwa yamma ya dawo ya bada kudin na lefin satar. 
Dukda haka saida aka
sanya dole aka kintata iya ragowar kudin zaman da zatai a gidan yari sai dai in har sun ciko. 
Kuka maman safna ta sanya tana cewa “kaico’ Da yamma akazo aka tafi da safna da wasu gidan yari tana kuka wiwi. 
Maman safna da kuka ta koma gida tana, Allah ya isah tasan duk sharrin kishiyoyi ne kuma ba za ta taba yafewa ba. 
Sai kaji kishiyoyin na yada habaici kwadayi mubudin wahala, inda kwadayi da wulakanci sata da tsakar rana. Allah ya rabamu da saka a mugun zare. 
An bawa ramadan kudinsa bai kasa a gwiwa ba, ya maidawa shugabansa wasu daga cikin ragowar kudin da bai biya ba,anan yake sanar mai ta dalilin batan kudin. . 
Mamaki sosai yayi yace “mata! mata! ai wasu matan shaidanune. Ai idan ka dace da mace ta gari to karka taba bari ta kubce maka, koda kuwa ita ce karshen muni a mataye, domin macce ta gari itace silar zaman lafiya. 
Shugaba ya kara da cewa “farkon aurena na auri matata, amma ta zamemin jaraba, domin ta rabani da uwata da kowa nawa, makwabta abokai sai ita da danginta kawai. Hakuri‘ nake da ita kota’ina ba najin dadinta, kasan ance ramin karya kurarrene, Allah ya tonu 
asirinta muka rabu. Da Allah ya tashi sakamin sai ya bani mata ta gari alokacin nasan nai aure, mace nutsatstsiya ko tari nayi zata shiga damuwa ga ladabi da biyayya. Kai yanzu kake tasowa ina baka shawara muddin kana da nagartacciyar mace ka riketa da kyau. Domin sauda dama dan adam yakan butulcewa niemar da Allah yayi mai, ba zai gane ba har sai ya rasa ta.” Jinjina kai ramadan yayi koshi ya gasgata hakan. 
Ko akan matarsa ladifa, da da yake mata kallon hadarin kaji, ada bai duba nagartarta ta ba, bai duba tarin baiwarda Allah yayi mata ba, ya kasa godewa Allah. sai yake duba halitta, wanda wannan duk soye soyen zuciya ne, ashe itace mace gangariya. Gashi da Allah ya so saka mata sai gashi ya hadashi da irin matan da yake so, ta silarsu ya shiga matsala kalakala saboda bai nemi zabin Allah ba ya duba son zuciyarsa. Kuma bai godewa Allah ba, lalle duk wanda bai godewa Allah ba, ya godewa azabarsa. Lalle ya yarda hali nagari shine nagarta. Gashi ta sular Iadifar ma laila ta dawo mutuniyar kirki, nan yaji sonta na dada shiga ransa. Yaji dama bai mata abubuwan da ya faru a baya ba. Sai dai ya godewa Allah da 
bai gangancin rabuwa da ita ba. 
Sai da shugaba ya yi magana ya dago yace “to shikenan Allah ya kiyaye gaba ana kula ko gaba. Ramadan ya tashi ya tafi yana jin kamar an cire mai kaya, wani irin shaukin matarsa ne yakejin yana shigarsa. Allah Allah yake yaje gida ya ganta ko zuciyarta ta bar azalzala. 
ya amsa fuska asake, takowa yayi ya shafi kan arif yace “ya gida my dear.‘ tace ‘lafiyalau.” 
Nan ya hau sama ya tura dakinta bai ganta ba. Ya shiga nasa tana tsaye tana saka turaren wuta akasko a dakin, duk da nauyin cikinta da har yafi na fuad girma, baya hanata wasu abubuwan na hidimarsa. Rungumeta taji yayi ta baya yace “idan babu ke bansan yaya rayuwata zata kasance ba, ina sonki so mai yawa baby.” 
Juyo da ita yayi ya kuma rungumeta ‘kece rayuwata maman fuad.‘ ’ Lumshe ido tai tace “wata sabuwar soyayyace ta motsa.‘ 
“Hmm! idan banyi miki soyayya ba wa zanwa, nagartacciyar mata irinki burin kowanne mutum maisan zama nagartacce.“ 
Sai tai murmushi tana jin dadi aranta, nan yake gaya mata cewar an yankewa safna hukunci a kotu komai dai ya gayamata,jimami tai tace “Allah yayi mana me kyau.  Sauka kasan sukai suka zauna tare da laila ana hira ana cin abinci, yake ce musu hajiya dai ta rike fuad da najwa dariya ladifa tai tace ai sunfi son wajen nata.
“BAYAN” SATI BIYU 
Nadamar satar kudi sosai safna ta shiga yi duk ta fada. Wai yau ita ce A gidan yari. Sai kuma ta shiga dana-sanin cewa da tai ya saketa. Domin tabbats da da aurensa akanta tasan tabbas ba zai bari a kaita kotu ba. 
Mamanta kuwa ta rasa yaya zatai dan baban safna ko maganr baya son yi, ga jarfaryan gidansu duk sun sakota agaba, wanda saboda takaici har saida ta kwanta ciwo na kwana biyu wanda hawanjini ke san mata kwaf daya. 
Yau da daddare taje wajen baban safna tana kuka, kan ya taimaka yaje wajen ramadan ya rokeshi, ya yafewa safna a saketa. 
Baban safna yaCe “sai yanzu kika sanni? Ai baki maidani mai daraja ba, saboda ban da kudi, innai magana a hayayyako mini, yanzu kuma ribar me kuka samu?.” 
Share hawaye tai taCe ‘ka yi hakuri, nayi kuskure, kasan lamarin gidan nan wallahi har tsoro nake safiya tayi, irin habaici da tsangwama, wai mune irin sata, yanzu takai har kaffa -kaffa‘ suke a d’akunansu, komai ma wai dan karni da yarana muyi musu dan hali, dan Allah ka tsawatar ka tanka.” Numfashi yaja yace naji kije zan nemi shi tsohon mijin nata. 
Bayan sati daya baban safna yaje gidan ramadan. Ramadan yana girmamashi, nan yayi ta rokansa, kan yayi hakuri, idan kuma hakan ba zai samu ba sai ai yarjejeniya, ko biya ne sai su ringa yi, har a karasa biyan ragowar,ganin yanda baban ke cikin damuwa yana fadin irin halin da yake ciki na matansa, dan duk baiyi sa’ar mata na gari ba, babu wacce zai bugi kirji ya ce ta gari ce, sai dai wata tafi wata illa! wanda maman safna na daga ciki. Harya ke cemai maman safnar ita ce silar koyawa ‘yar mugwayen halaye. 
Yace kalleni duk rashin samun mata nagari ne ya sanya ni haka,jidalunsu ya komar dani haka. Duk da cewa Akwai kaddara amma komai da sila, dan akwai da dama wanda suke talakawa, da Allah ya basu mata na gari, ka gansu a nutse. Masu iya magana sunce macce ta gari itace silar zama lafiya. 
Anan ramadan ya kuma samun karin haske, tabbas shi kam yayi dace, kuma yaso tafka kuskure saidai Allah ya taimake shi. 
Yace “to shikenan baba insha Allahu zanje kan maganar, ba sai an biya ba, na yafe saboda koba komai kai tamkar mahaifina ne, na yafe.” 
Haka baban yayi ta mai godiya yana Addu’ar Allah ya bashi mace ta gari ba irin safna ba, idan kuma yana da ita ya riketa gam! 
Ramadan yaje kotun an sulhunta ya ce ya yafe ragowar kudin, nan aka fito da safna duk ta jigata ta rame a sati biyu. 
Dawowarta da kwana biyu babanta ya hadasu yayi musu nasiha mai ratsa zuciya kan zaman lafiya agidan, tabbas yasan yana da lefi, dan itace ma tun yana danye ake tankwara shi. 
Yau ladifa ta tashi da nakuda. Aka tafi kaita asibiti akace haihuwa ce, tun karfe uku na yamma suka tafi har dare bata haihuba, sai azaba da take sha Ramadan da laila sunyi jugum -jugum dukjikinsu asanyaye,wajen tara na dare likita yace dole saidai ai mata aiki saboda jininta ya hau, sabida tension din labour din nan, ramadan ya sanya hannu lokacin hajiyarta ta je, ladifa kuwa sai hawaye take na azaba ganin an shiga da ita tiyata suka shiga addua kan Allah yasa ayi lafia. 
Wajen rabun awa aka fito aka karbi rigunanjarirai mace da namiji twins sabodajin dadi har da hawaye ramadan, laila da hajiyar ladifa kuwa sai godewa Allah su ke,tun allurar da akaiwa ladifa ba ta motsa ba. Lokutan da aka diba na in allurar ta saketa za ta tashi, har 
lokutan da yakamata Allurar ta saketa yayi, amma bata farka ba, su kansu likitoci na mamaki rashin farkowarta, nan fa hankalinsu ya dan tashi, su ramadan hankali ya tashi yana bakin kofar, nan fa ramadan ya shiga dakin yana zaune ya kurawa ladifa ido. Likita ya shigo. Ramadan ya fita wajen mintuna sai gashi nan ya fito jiki a sanyaye. Ramadan ya mike 
Jikin ramadan ne ya fara rawa. Wani irin zubewa yayi ya sume, da sauri laila tayo kansa, nurses suka zo suka daukeshi aka kaishi wani daki. lnalilllahi waninna ilai rajuuuun kawai hajiya ke cewa, laila kuka ta sanya kasharban ta shiga raira shi, shi kuwa ramadan yana can ana kokarin ba shi taimakon gaggawa, suman da yayi ya farfado. “Da gaske nakeji ne ladifa ta mutu, innalillahi wa inna ilaihir raju’un. Matata ‘yar aljanna. Allah ya jikanki ladifa, wallah ke ‘yar aljanna ce indai aljannar mace tana karkashin kafar mijinta. To na daga miki tawa sau dari, ya kuma fasa kuka, ba zan iyajure rashinki ba.” 
Kuka yake hawaye na zirara kamar mace, mik’ewa yayi zai fita kawai ya kuma wani suman.Nurses suka kuma rufa akansa. 
Hajiya hawaye kawai take ta kasa kuka sai sunkwi dakai take tana Auta. ” 
Haka laila ma kuka kawai take ta kasa tsugum! babu wanda sukai kokarin gayawa a ‘yan uwa saboda basa cikin nutsuwa. Laila Sai zuwa take tana kallon babies din cike da tausayi 
sai kuka take kamar ranta zai fita.Dakin da ladifar take ne akwance ta shiga ta tsaya kanta tana kuka. Motsi ladifa ta fara yi ta bude idonta. Tana dan yatsine fuska. Tace “laila.” 
Da sauri ta kalleta. Sai ta sanya dariya ta fita aguje. Ta kira nurses suka shiga inda dakin da ladifar take. 
Da sauri laila ta shiga dakin da ramadan yake tana dariya “ba ta mutuba ta tashi.” 
Da sauri ya tashi jikinsa na rawa, yabi ita abaya. Suka shiga dakin idonta na kallon sili ta kallesu, ramadan ya zauna gefenta ya rike hannuta “sannu Allah nagode maka daka tashi kafadunta.” 
Lumshe ido tai ta koma bacci. 
Sai da tai sati daya sannan suka koma gida. Wanda wannan karan agidanta ta zauna, sai ‘yar uwar hajiya da ta zo ta zzuna mata,
twins masu farijini kyawawa da su farare kal kal dasu kamar ka sace su ka gudu da su ita kanga inta kallesu godiya takewa Allah. Ramadan binibini yana wajensu, har kunya matar ke yi saboda irin yanda ramadan ke ba kunya agaban kowa nuna son ladifa yake afili. Tun abin na damun laila taji haushi harta ke dannewa. 
Yauma wajejen yamma suna zaune ladifa na zaune tana cin romon kaza da akai mata irin ta masu jego sai tiriri take. Dakin sai kamshin turaren wuta yake ga twins na bacci a cikin net ya shiga. 
Ya zauna tai murmushi tace “sannu da zuwa?.” 
Mai jego ta lumshe ido ya ce “ya naga kanki rabi a tsefe rabi a kitse, sai ta ai dariya ce ta “laila ta fara ta min kuma sai arifya tsiri sai ta tafi.‘ 
Tsam ya mike “bari na taimaka miki.” 
Tai dariya, nan ya shiga yi mata tsifar sai ta kuma sakin dariya ta ce “so kake wasu ‘yan barka su shigo su ganka a haka?
“Na san dai cewa za suyi kin mallakeni ko? To babu damuwa dan kuwa kin mallekeni har zuciyata.” Sai tai dariya ta ce “Abu fuad nawa.” 
Alokacin laila ta shiga dakin sai ta sanya dariya, tare da rik’e hab’a, ta ce “namiji da suna hajara,” yayi murmushi. Duk da cewa farko ta yi dam ta nuna kishi sai ta kuma basar. Ta ce “lallai ka ragemin aiki bari naje na wanke fldar twins.” Yana flta ladifa ta ce “ni dai zauji.” 
“Yes! mom fuad ya dai.” 
Ta ce “Dan Allah kana rage nuna wani abun agaban laila, sai naji wani iri wallahi. Dole sai kana rufe wani abun saboda…me” “Itama matarka ce.‘ 
Katseta yayi “na san me nake yi kowa da muhallinsa. Karki damu ba wani abu bane.“ Sai tai shiru. Ya d‘an yi mata da yawa ya fita. 
Haka ranar suna, aka rad’ama twins suna, babu wani taro da akai saboda cewar maijegon ba lafiya take da ita ba sosai. Aka sanyawa macen sunan hajiyar ladifar da kuma sunan babanta wannan karar tayi mata dadi sosai! macen ake ce mata Hanan, namijin kuma 
hanif. ‘ 
Kan wata daya ladifa ta yi garau da ita kamar ba ita ce aka yiwa aiki aka dauko yara ba. Jikinta me kyau dan kamar ba ita ta haihu ba. 
Safna A yan kwanankin nan ta tsiri kiran ramadan a waya kan ya maidata dakinta. Ko ta yo mai text. Sai da yayi mata kashedi ya ce ta daina kiransa dan babu wani gurbi da zai iya ajjeta akaro na biyu.Allah ya bata miji tai aure. Tun daga ranar bata sake kiransa ba. 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *