NI DA AMARYATA COMPLETE
BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM
Da sunan ALLAH mai rahma mai jink’ai, ya ALLAH kabani ikon fad’in abinda zai amfani Al’ummarka, ka tsarkake harshena daga fad’ar abinda zai cutar da Al’ummarka. Amin ya “RABBI”.
Assalamu alaikum, ina mai farin cikin sake had’uwa daku asabon littafina, akaro na 4, ina godiya ga d’umbin masoyana aduk inda suke, “UBANGIJI ALLAH” yabar k’auna. Nagode🙏🏻
Zanyi amfani da wannan dama, domin taya d’umbin Al’ummar MUSILMI shiga sabuwar shekarar musulinci, ALLAH ya albarkacemu da rahamarsa.
🙋HAPPY NEW YEAR🙋
……….’Yammata biyune ke tafiya, cikin nutsuwa, jikinsu sanye da kayan makaranta, (uniform) pink d’in wando da farar riga, sai farin hijjab daya tsaya musu iya k’ugu, dan baikai d’uwawunsuba, bayansu goye da jakar makarantarsu (school bag).
“Sukaja birki abakin titin da d’umbin d’alibai ke tsaiy tsaye suna jiran motar makaranta,wash ALLAH!!!, d’aya daga cikin ‘yammatan ta fad’a.
D’ayar ta bita da kallon mamaki, kai fareeda badai gajiyaba???
“Wadda aka kira fareeda tad’anja tsaki wlhy kuwa sopy nagaji.
Sopy tai dariya nikam bansan randa zaki zama jarumaba fareeda, ke komai kin gaji sai kace mai yaron ciki??
“Fareeda ta harari sopy, “k” ki kaimin cikin ko??
Gaba d’aya suka tuntsure da dariya harda tafawa,, sopy tace”ina ni ina yimiki ciki rufani ki sayani,, suka kuma tuntsurewa da dariya.
Tsayuwar wata bak’ar motace ta tsayar musu da dariyar,suka k’urawa motar idanu, da alama sunsan mai ita, ko kuma suna son sani.
Wani farin saurayi mai d’an jiki yafito yana murmushi, idonsa akan ‘yammatan, yak’araso da sallama, suka amsa cikin sakin fuska, suka gaisheshi, sopy ta d’ora da fad’in habibina daga ina?? Da wannan farar safiyar ga sanyi??
Ya shafa sumar kansa, yana fad’in gimbiyatace ta fito dani ko fareeda??
Fareeda tai ‘yar dariya mai kama da yak’e,, tace”hakane.
Saurayin yayi d’an murmushi to kuzo mutafi karku makara, dan wannan motar makarantar taku saiku kai k’arfe takwas baku tafiba, yafad’a yana karb’ar school bag d’in sopy.
“Sopy ta tab’a fareeda K’AWATA tunanin mi kikeyi ne??
Fareeda taja ajiyar zuciya bakomai mikika gani???? Sopy tace”ban yardaba fad’a min gsky!!
Kunga kumuje sai ayi wannan magar a mota, saurayin yafad’a yana nufar motar.
Suka bishi abaya, bayan sun shiga motar, yaja suka tafi,, sopy tadage sai fareeda tafad’a mata damuwarta, ita kuma fareeda tadage akan babu abinda ke damunta.
Saurayin yay dariya nikam tunda nake arayuwata bantab’a ganin k’awance irin nakuba, mai cike da k’auna da yarda, dakuma aminci, wai idan kun tashi aure yaza ayine??
“Sopy ta kalli fareeda, my sister kinji wani zance,, aii mu insha ALLAH agari d’aya zamuyi aure ko?? Fareeda tace” insha ALLAH.
Tofa saurayin yafad’a, to ALLAH yacika muku burinku,, amma aii har yanzu bamusan gwanin K’AWAR tamuba??
Wlhy habibina nima kullum damuwata kenan,, bani da wani buri bayan naga mijin k’awata, tunda ni nakama nawa tafad’a tana kallon saurayin,, shima ya kalleta yay Murmushi, fareda yakamata ki tsaida gwani gashi har munkusa k’are makaranta.
Fareeda tad’an ja tsaki mara sauti, azuciyarta tace,, haba K’AWATA dama kin daina zumud’in ganin gwanina,, dan ganin mijin dazan aura bak’aramin tashin hankali bane agareki,, dan saurayin dakikeso da k’yauna shine wanda nake burin yazama mijina kota halin k’k’a😳😳 tofa.
Amma afili saitace karku damu gwanina yakusa bayyana insha ALLAHU.
“To ALLAH ya yarda cewar sopy”
A bakin get d’in makarantar ya ajiyesu, suka tsaya shida sopy suna sallam, yayinda fareeda tai gaba zuciyarta na zafi saboda kishi.
Bayan yatafi sopy tak’araso inda fareeda ke tsaye fuska a d’aure,, sopy tabita da kallo dan son gano matsalar K’AWARTATA,, amma sai fareeda tai gaba, tabar sopy a tsaye tana kallonta.
“Sopy tabita abaya, tana mai mamakin duk sanda suke tareda ABDUL sai fareeda taita fushi ko me yasa hakan???
Zuciyarta tace k’ila itama tana sonsane, kobatason tarayyarku,, tai saurin cewa kai A’a fareeda bahaka takeba,, domin na yarda da fareeda d’ari bisa d’ari,, nayarda da ita kamar yanda na yarda da kaina,, shaid’an bazan yarda da hud’ubarkaba, balle har ka haddasa rashin yarda tsakanina da K’AWATA, abin sona da k’aunata,, dan bayan iyayena da ‘yan uwana, babu wanda nake k’auna kamar fareeda da Abdul, mutanan nan biyu sunada matuk’ar muhimmanci arayuwata fiye da tunanin mai hankali.
Turk’ashi lallai akwai matsala,, shin yazata kasance ga fareeda da safiyya,, shin miyema dangar takar fareeda da safiyya ne?? mizai faru ga wad’annan k’awaye biyu?? ga fareeda taci burin auren saurayin k’awarta aminiyarta,, wanda kuma k’awartata tafi so da k’auna, gashi yakai kud’in aurenta,, shin burin fareeda zai cika?? Idan safiyya tagano fareeda nason ABDUL yaza ayine???
Nice kad’ai mai baku wannan amsar,, kubiyoni dominjin gundarin labarin “”NI DA K’AWATA”” yananan zuwa nan bada dad’ewaba, takuce dai mai sonku da k’aunarku BILLKISA IBRAHIM.. nagode🙏🏻…………..✍🏽
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕?
💕 I LOVE U MY FAN’s 💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 2~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸2⃣🔸🔶
ASALIN LABARIN …………WACECE SAFIYYA???? SAFIYYA IBRAHIM KABEER shine cikakken sunanta , malam ibrahim shine mahaifinta, cikakken haifaffen kano ne, a unguwar rijiyal lemo,, kowa dai yasan rijiyar lemo unguwar talakawace irinmu.
“Dan haka malam ibrahim talakane tib’is irin wanda sai annemo na gobe aci, sai dai malam ibrahim yanada wadatar zuci, dan mutumne mai taka tsantsan da tsantseni, matarsa d’aya hajara wadda suke kira da inna, itama mace mai hak’uri da kawaici, yaransu uku duk mata, Nafisa itace babba tayi aure harda yara biyu, dan daga aji uku na secondry aka cireta akai mata aure,, sai hauwa’u itamadai tayi aure kamar ‘yar uwarta itama tana aji uku akai mata aure, yanzu tanada yarinya d’aya dan ko tafiyama bata farayiba; suduka suna aure anan cikin garin kano, sai auta safiyya wadda yanzu take (s,s,3) a wata secondary ta ‘yammata, itamadai malam ibrahim yayi niyyar cireta yay mata aure amma sai uncle kabeer wani k’aninsa yahana, malam ibrahim yace” to shikam gsky bashida k’arfin rik’e ragamar karatunta, uncle kabeer yace” babu damuwa shizai d’auki nauyin karatunta dukda shima bawani k’arfine dashiba, amma yana aiki dan yayi karatu har zuwa degree.
Wanna nan shine dalilin cigaban karatun safiyya ‘yar gatan uncle kabeer.
” gidan malam ibrahim ana cikin hali na talauci da fatara,amma wannan baisa ‘ya’yansa sun lalaceba, saboda tarbiyyar dasuka samu a wajen inna da babansu, gasu ALLAH yabasu kwakwalwar karatu sunada k’ok’ari a makaranta, dan safiyya tuntana primary school take d’aukar na 1, har yanzu datake a secondary.
“” safiyya bak’ace saidai bak’inta mai k’yawune, irin wanda idan ka kalla saika sake kallo d’innan, tanada k’yau am ma bamai tsananiba, sai dai tanada manyan idanu dara dara wad’anda saudayawa susuke fara jan hankalin maza gareta,, gata tanada jiki mai k’yau irin wanda akecema karuwan jiki.
Fareeda ‘yar anguwar su sopy ce dan gida biyarne tsakaninsu, itamadai iyayenta talawane dan babanta abokin malam ibrahim ne, su hud’u iyayensu suka haifa maza biyu mata biyu itama itace auta,, fareeda k’yak’yk’awace fara tas, dan tanada k’yau na d’aukar hankali,, fareeda k’awar safiyyace tun suna yara, dan ayanda najima rana d’aya aka haifesu,, k’awancensu yanada matuk’ar dank’o, dan tare yake da tsantsar so da k’ auna dakuma yarda,, koda yaushe suna tare inbasa gidansu sopy to suna gidansu fareeda,, masu karatu amintakacefa mai tsantsar karfi ga wad’annan matasan ‘yammata.
“Koda yaushe suna tare, tare a ka sakasu makaranta, ko d’inki tare ake musu iri d’aya kuma,, sai dai halin fareeda dana safiyya sun bambanta, safiyya tana da hak’uri da zuciya dan idan tayi fushi fareeda ce kawai ke iya shawo kanta kokuma uncle kabeer, Dan shine ma yasa mata suna sopy,, takan dad’e batayi fushiba dan sai ankaita mak’ura sannan.
Fareeda kam tanada tsiywa dan bata barin saita kwana,, soda yawa itace ke jawo musu fad’a gata batada k’arfi sai dai safiyya tashigar mata fad’an, kunsan masu zuciya akwai k’arfin tsiya,, fareeda tanada son nuna ita watace dan tanada kwad’ayi damma sopy tana sakata a hanya.
Tafiyarsu tafara samun gar gada ne alokacin da Abdul yashigo rayuwar safiyya,, shima d’an anguwarsu ne,, amma abayan layinsu yake,,babanshi yanada rufin asiri dan gsky yafi iyayensu safiyya kud’i.
“Gidan su Abdul gidane na mata uku, da tarin yara dasuka kai adadin ashirin zuwa sama, Abdul shine na 6 a gidansu,, yayi karatu har zuwa (N,C,E)Sai dai Abdul irin samarinnan ne ‘yan k’arya dason nuna burga.
Sun had’u da safiyya awani yammacin ranar talata, lokacin sun dawo daga islamiyya itada fareeda,, tun aranar farko da fareeda taga Abdul takamu da sonsa,, sai dai kash daga baya sai ya nuna k’awarta yakeso safiyya,, dan danan kuma soyayya mai k’arfi tashiga tsakanin Abdul da safiyya, wannan yasa fareeda ta danne son Abdul azuciyarta, sai dai kuma yau da gobe sirrin nata yana nema fitowa fili.
“””” dan duk ranar da fareeda taga Abdul yazo wajen safiyya takanji wani bak’in ciki da kishi,, har yakansa ta nuna fushinta afili,, duk da tasan k’awarta tata tana tsananin son Abdul,, wanda a yanzun haka ankai kud’in auren Abdul gidansu safiyya, harda saka rana,, za ayi bikinsu bayan ta kammala secondry.
“Toko wannan aure zai yiwwu??ko fareeda zata hak’ura da k’udirinta kafin k’awar tata ta fargane??? kubiyoni dan tabba tarwa…………………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 3~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸3⃣🔸🔶
…………yau takama weekend babu school su sopy suna gida, sopy ce zaune tana wanke wanken kwanuka inna na gefenta tana tsintar shinkafa ‘yar hausa.
“Safiyya! Wai bazakiyi sauri ki tashi awajennan ba ko?? Nafad’a mikifa yau kece zaki mana abinci, amma kin zauna wanke2 bawani mai yawaba sai lank’andi kikeyi, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Sopy ta turo baki gaba ALLAH inna ni bana son yin girkin nan mutum yayta fama da iccen nan, ga azabar hayak’i idonka yayta hawaye kamar kana kuka.
Inna ta girgiza kai tana murmushi, nima d’in danake dafa miki kullum kizo kici haka nake fama, dan haka yau har girkin dare kezakiyi shi.
Sopy tazaro ido 😳kai inna da gsk kikeyi??
Na tab’ayimiki k’aryane?? Inna tabad’a tana mik’ewa tsaye,, Sopy tace”A’a.
inna tace” to yimaza ki gama ki tashi rana tanayi kinsan babanki kuma yakusa dawowa.
Sopy tai shiru tana wanke2n ta can kuma saitace inna!! Inna ta amsa da na’am.
Inna mizai hana ahad’e abincin harna dare?? A’a baza a had’eba kinsan dai babanku bason cin shinkarnan yakeba koda yaushe balle wannan fara da mai d’in, yana cine kawai dan bashida yanda zaiyi,, ayi shinkafar yanzu da daddare sai ayi tuwo.
Tuwo kuma inna!!!! Jiyafa shi mukaci nikam nagaji da cin tuwonnan wlhy.
Inna ta d’auki wani murfin roba dake gefenta ta jefi safiyya dashi,, dan k’aniyarki in bakici tuwonba mizakici?? Ko kin ajiye mana wani abincinne bayan tuwon?? Kudai yaran yanzu bakusan ku godema ALLAH ba yayin dayay muku ni’ima, da basai ki wuni ki kwana bamuci abinci agidannan ba, amma yanzu ALLAH yarufa mana asiri shine zakiyima mutane iyayi,, kul nasake jin wannan furicin abakinki.
“” Sopy tai kwal2 da idanu tana shirin yin kuka dan ganin ran innarta ya b’aci, tace” dan ALLAH inna kiyi hak’uri bazan sakeba ki gafarceni???
Inna tai murmushi to shikenan ya wuce share hawayenki kinji,, barma girkin nizanyi.
A’a inna kibari zanyi tafad’a tana nufar kichin d’in da hayakin wuta ya maida bangon bak’ik’k’irin, tafara k’ok’arin had’a wutar icce.
Sopy tana aiki suna hira da inna, inna tace waini lfy yau banga fareeda ba agidannan kuma kema banga kinje gidansuba????
Sopy tace”wlhy babu komai inna, tacemin ne zataje gidan k’anuwar mama a hotoro, nikuma kinsan ba shiri muke da’itaba shiyyasa nace bazanjeba,, to inaga tana can bata dawoba.
Hummm kudai kaiwai shirmenku ne ya motsa amma in banda haka miye nawani rashin shiri kema aii sadiya innar kice.
“Taf inna ALLAH yakiyaye sadiya tazama inna ta,, dan tunda nalura batasan abotarmu da fareeda nai alk’awarin na daina zuwa gidanta,, idan tazo nan anguwar ma gaisa, shima idan mun had’u kenan.
Inna ta shige d’aki tana fad’in kudai kuka sani.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::☆
Fareeda tana gidan innarta sadiya, k’anwar mamace mahaifiyar fareeda, itamadai bawata babba bace dan kusan sa’ar hauwa’u ce yayar safiyya.
Suna zaune afalon sadiyar gabansu tiren taliyane da yaji damai,, kunsan dai mu ‘yan kano mun iya k’wad’ayin mai da yaji, sadiya takalli fareeda ‘yar uwa ina jinki jamuje labari.
Fareeda ta harareta oh dama matsalar tawa labarice?? Sadiya tace yi hak’uri ina tsokanarkine. “””Fareeda taja ajiyar zuciya sannan takuma gyara zama tana fad’in wlhy anty da nayi niyyar bar mata Abdul amma yanzu bazan iyaba, idan nagansu tare jinake tamkar na had’iyi zuciya na mutu.
Dan ALLAH ki bani shawara miya kamata nayi???? Dan na mallaki Abdul.
“””Sadiya tayi murmushi aii wlhy koni ban goyi bayan ki bar mata shiba, Abdul k’yak’yk’awane dama dake yadace bawannan bak’ar yarin yarba,k’ilama asiri tai muku dan na lura tun farko ke yake so. Fareeda ta gir giza kai,, bana tunanin haka aunty sadiya nasan halin sopy nakuma san abinda zata iya,, inama tasan inda wasu malamai suke?? bare taje, kedai kawai bani shawara.
Sadiya ta tab’e baki dan ta lura fareeda bazata gane inda ta dosaba,, tace kawo kunnanki kiji!!!;!!
Fareeda ta mik’a kunnenta ga sadiya, can kuma sai suka tuntsire da dariya harda tafawa, fareeda tace”wlhy shawararki tayi auntyna ALLAH ya biyaki,, inada tabbacin samun ABDUL yanzu.
Tofa masu karatu wace irin shawar sadiya tabama fareeda ne??? dahar take murna haka, harma da tabbatar wa kanta samun ABDUL,, to kudai biyoni dan jin wannan bada k’ala………. ..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
4~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸4⃣🔸🔶
…………..koda yamma da fareeda tadawo bata shiga gidan su Sopy ba, Sopy tagama shirin islamiyya ta fito, inna bari nagani ko fareeda tadawo saimu wuce islamiyya idan kuma bata dawoba nisai na wuce.
“” to autar inna adawo lfy””
Tafita tana fad’in ALLAH yasa innata.
Da sallamarta tashiga gidan, mama dake zaune a k’ofar d’akinta tana linke kayan wanki, ta amsa da fara’arta,, Sopy ta tsugunna ta gaida mama.
“Mama tace” waini yau ina kika shiga safiyya?? Duk yau ban gankiba, ince dai lfy???
Sopy tayi murmushi wlhy lafiya lao mama ina gidane kawai.
Aii d’azu danaga fareeda ta shirya canake tare kuka tafi hotoron??
A’a mama batare mukajeba saboda zanyi wanki.
ALLAH sarki kishiga tana nan tun d’azu tadawo inagama barci takeyi;
Sopy tamik’e tana fad’in fareeda kasace aii,, amma barcin yamma.
Tad’aga labilen d’akin fareeda kwance d’ai d’ai akatifa tana kwasar barci, Sopy tak’arasa cikin d’akin tasa hannu ta daki bayan fareeda, ke uwar barci tashi.
“Fareeda ta taahi a firgice tana fad’in wayyo mama…….saitaga safiyya tsaye akanta,, Sopy tace sarkin tsoro kawai kin wani tashi afirgice kamar wadda aka firgita.
Fareeda ta harareta wlhy sopy ke ‘yar iskace miye na tashina ina barci??
To badole natashekiba tunda ke bak’ya duba agogo, kullum kece kikeja mu makara a islamiyya.
Fareeda ta yatsine fuska aini inagama yau bazani islamiyyar nanaba.
” saboda me??? Sopy ta tanbaya.
Babu komai kainane kawai keyimin ciwo.
Sopy tace” kinsha maganine?? A’a ban shaba amma yanzu zani nasiyo tunda kin tasheni,, tamik’e barima mufita tare.
Tare suka fito fareeda ta amshi kud’in magani awajen mama suka tafi,, dai2 zasu fita kwanar layinsu suka gamu da ABDUL dawani abokinsa Adam,, adam yace” ‘yan halak kunk’i ambato yanzu muke hirarku ashe kuna hanya.
“CIkin zolaya Sopy tace” kodai kuna gulmarmu???
Abdul yace” kajiko abokina shiyyasa nace kayi shiru karka fad’a,, wad’an nan baka iya musu.
Adam yay dariya gsky ne abokina,, wannan abotar mai k’arfice nadad’e banga k’awaye masu irin shak’uwarkuba, gaku nan tamkar ‘yan biyu.
“” fareeda tace” lah bakada labarin mu ‘yan biyune rana d’aya aka haifemu kaje ka tambaya.””
Adam ya jinjina kai aii bama saina tambayaba nayarda, dan abokina yatab’a fad’amin.
“Abdul yamatsa kusada sopy gimbiyata yayadai??
Tai murmushi lfy lao habibina saidai my sister ce kanta yake ciwo.
Ayya ALLAH yak’ara sauk’i shiyyasa naga d’aya da uniform d’aya babu???
Sopy tayi murmushi eh kusan hakane danni zanje islamiyya itakuma zata sayo magani ne.
“Ayya sorry fareeda ALLAH yak’ara sauk’i.”
Amin fareeda tafad’a tana fari da idanu.
Abdul yakalli agogon hannunsa gimbiyata yakamata ki wuce dan zaki makara karkisha bulalar makarafa.
Sopy tad’an murmusa gskyar ka habibina dan yasayyadi yananan abakin get, bari nawuce kasan idan ina tare dakai nakan manta kowa da komai.
” nima haka gimbiyata Abdul yafad”a yana kashe mata ido d’aya,,, Adam yace” kuna sha aninku masoyan zamani,, itakam fareeda tayi kicin kichin da rai kamar zata fasa ihu,, sopy ta tab’ata sister barina wuce saina dawo ALLAH yak’ara sauk’i.
“Amin tafad’a ranta a dagule”
Abdul yace” aii barima mu kaita k’yamis aduba miki ita.
Yawwa habibina nakwa gode maka,, bari nawuce sai da daddare mun had’u.
“To shikenan ALLAH ya kaimu my lovely wife.
Abdul yadawo da kallonsa kan fareeda bayan b’acewar sopy,, fareeda tad’anja k’aramin tsaki mara sauti,, Abdul yay saurin fad’in lfy?? Fareeda taid’an yak’e wlhy jinai kaina ya sara.
Okey sorry to muje ko??
Adam yace” aii ni inaga anan zamu rabu, dan wlhy abba ya aikeni amma sai yanzu natuna, kuje da daddare zamu had’u insha ALLAH fareeda ALLAH yak’ara sauk’i,, saida daddare idan munzo tad’i.
To Adam nagode ALLAH yakaimu daren.
“”Amin adam yafad’a,, sukai sallama yatafi suma suka tafi.
Tafiya suke cikin nutsuwa kowa da irin tunanin dayakeyi azuciyarsa, har suka isa k’yamis d’in sadiq amma k’yamis d’in arufe.
Abdul yace” inaga saimunje k’amis d’in Rufa’i fa,, kozaki iya??
Tai murmushi babu damuwa muje nida nake neman lfy.
Shima murmushin yayi,, to shikenan muje.
” sun isa k’yamis d’in Rufa’i aka bama fareeda magun guna,, Abdul yabiya suka fito,, saida sukaje bakin titi fareeda tace” Abdul idan bazaka damuba inason muyi wata magana.
“Abdul ya kalleta to ina saurarenki,,fad’a min.
A’a maganar bata tsaye bace,, indai ban takuraka ba musami gurin zama.
Abdul yace” to inaga kibari saida daddare idan nazo saimu zauna muyi maganar mu uku harda Sopy, inaga hakan zaifi ko???
“Fareeda ta had’iye wani kududun bak’in ciki daya tsaya mata a mak’oshi,, jikake k’uuuuuttt!!!
Abdul yace hakan yayi ko?? Fareeda ta girgiza kai,, Alamar A’a,, tacigaba da fad’in mubiyu nakeson muyi maganar dan banaso Sopy tasani,, kasaka mana lokaci muhad’u nida kai kaiwai.
Abdul yay shiru yana tunani, saikuma yaja numfashi, to amma miyasa baki son Sopy tasani?? Fareeda tayi d’an murmushi, babu komai wlhy amma bana son tasani saimun kammala komai sannan, inason nabata mamakine.
Abdul yay dariya to shikenan babu damuwa,, saimu bari zuwa kamar weekend ko???
Babu damuwa indai hakan yayi maka ni agareni babu matsala.
“” to amma kina ganin tayaya zamu kasance tare dake batareda sopy tasaniba?? Kinsan koda yaushe kuna tare.
Indai wannan ne babu matsala nasan yanda zan kauce mata.
To shikenan Abdul yafad’a yana kallon fareeda,, har gida yarakota sannan yajuya,, amma zuciyarsa tana tunanin mi fareeda keson fad’a masa wanda batason safiyya tasani ??? Hakadai yayta tunani har yak’arasa majalissarsu inda suke zama da abokansa da yamma bayan kowa yadawo aiki ko kasuwa.
To masu karatu kubiyo danjin mi fareeda zata fad’awa Abdul ne??? Shin idan ta fad’a masa zaya amince????? Kubiyo ni danjin amsar tan bayoyinku. ……………..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
5~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸5⃣🔸🔶
……………….fareeda tafito cikin sharin fita, mama tabita da kallo kekuma ina zakije da yamman nan???
Mama dan ALLAH kibarni naje gidan aunty sadiya gobe in ALLAH yakaimu da safe saina dawo tunda babu makaranta.
Mama ta harareta kinga fareeda kifita idanuna tunkafin na b’ata miki rai,, yaufa kwananki uku da zuwa gidan sadiyar shine yaukuma kice zaki koma,, to waima mizakije yine??
: : fareeda ta turo baki gaba nifa sak’o zan amso awajenta.
Sak’o kuma??? To sak’on mi?? Kuma waye yabada sak’o abaki??
Fareeda tayi shiru dan batasan abinda zata fad’awa mama tabarta zuwaba,, saikawai tacire gyalen ta ajiye saman igiyar shanya,, tana fad’in tunda dai kin hana shikenan.
Mama tai tsaki ke dai kika sani.
Sopy kwance atsakar gida jikin wata ‘yar bishiyar mangwaro dake tsakar gidansu,, hannunta rik’e da littafin English tana dubawa, dan exam tana gabatosu,, inna dake zirga zirga a tsakar gida dan k”ok’arin had’a abincin dare, ta kalli sopy safiyya ki tashi ki share tsakar gidannan kar magriba tayifa kina ganin rana tafara jaa.
To inna safiyya tafad’a tana mik’ewa, ta nannad’e tabarmar tafara sharar tsakar gidan,, tana cikin sharar malam ibrahim yay sallama da gudu sopy taje ta taryoshi,, baba sannu dazuwa.
Yauwa safiyan baba,, ya gidan?? Wlhy baba kafiya lao, to madalla.
Ta karb’i ledan hannunsa tana fad’in baba mika sayomin???
Yay dariya safiya way sai yaushe zakibar kwad’ayine kinfa girma,, inna tafito kichin tana masa sannu ya amsa cikin fara’a,, yaja kujera ‘yar tsugunno yazauna,, inna takawo masa ruwansha.
Sopy tagama shara ta wanke hannunta, sannan tanufo babanta, baba tunda kaki fad’a min nibari naduba dakaina,, baba yay dariya to duba ‘yar baba kankanace nasiyo miki saboda nasanki da son kankana,, ta d’auki ledar tana fad’in nagode babana mai sona.
Inna tace” malam ita kad’ai kasayoma kankarar Kenan? ?? Safiyya tace kai inna kina kishine???
Inna taimata 🖐🏻dak’uwa kinci gidanku nicema nake kishin dake ???
Malam ya mik’e yana musu dariya,, yad’au buta yayi alwala, ita kuma Sopy tazauna gyara kankana, dan tana fashin sallah.
Suna zaune atsakar gida suna cin abinci,, sopy tana gefe tana shan kankana,, inna tace” ni ina tawa kankanar?? Sopy tamik’e tana fad’in wlhy baba idan banbama inna kankanar nanba bazata barni nasha iskaba.
” inna tarik’e baki wayni yaushe safiyya ta rainani agidannan ne malam??? Malam ibrahim ya murmusa bawani raini,, aii ko kurama da ‘ya’yanta take wasa a dawa,, itama tana tsokanarkine kaway.
Inna tace” kaidai kana goya mata baya ne kaway,, safiyya tai dariya baba kabarta ai kwanannan zan tafiyata gidan aunty Nafisa hutu saita dad’e bata ganniba,, damma uncle kabeer bashida mata da gidansa zan koma………yaron dayay sallama yasa sopy yin shiru.
“” kai shamsu lfy ??sopy ta tanbaya,, shamsu yace wanine yace kizo awaje,, wani kuma?? Waye wani?? bashida suna ne??? Shamsu yace nibansan sunansaba amma agidan Alhaji Abubakar mai fata yake.
Baba yace”kaga yaro yitafiyar ka,, gata nan zuwa.
Sopy ta turo baki wlhy nikam baba banason fita tad’innan yau,, baba yace”” tobake kika zab’i mijinkiba da kanki maza tashi kije,, amma kar a zauna wannan doguwar hirar,, tun ana fad’ar gsky har akoma k’arya.
Sopy tace”to baba bari nak’are shan kankanata.
A’a tashikije idan kin dawo saikisha.
Dole tamik’e tatafi badan tasoba.
Inna ta kalli baba,, malam wlhy nidai dan kawai safiyya tanason yaron nan amma nikam bai kwanta min araiba,, banaso akai safiyya gidan nan mai tarin mata da ‘ya’ya.
Baba yaja ajiyar zuciya,, hajara babu abinda zamu iyayi face addu’a,, dan neman zab’in ALLAH, ALLAH yazab’a mana abinda yafi alkairi.
“To amin malam”
Awaje kuwa sopy tana fita saita tararda Abdul tare da fareeda suna hira,, lamarin yayi matuk’ar bawa sopy mamaki,, amma saita danne tak’arada wajensu da sallama.
Atare suka amsa mata,, takalli fareeda,, ke sister amma ke ‘yar rainin hankalice yanzu nan dama baki tafiba???? Fareeda tace” kibari kawai ‘yar uwa wlhy mamace ta kwafsa min tahanani zuwa,, fushi nakeyi shiyyasa kikaga ban shigoba,, yanzuma nazo na ari wayan Abdul ne nakira aunty sadiya nafad’a mata abinda yahanani zuwa.
Sopy taja ajiyar zuciya mai k’arfi,, Abdul yay saurin kallonta gimbiyata miye matsalarki???? Babu komai habibina ykk?? Lfy lau nake gimbiyata.
Nan dai suka dasa hira harda fareeda,, dan tak’i tafiya.
Hakan baisa sopy ta zargi komai ba, dan zuciyarta a tsarkake take,, ta yarda da fareeda da Abdul, d’ari bisa d’ari.
Washe gari saiga aunty sadiya tazo gidansu fareeda,, nanta wuni,, saida mama tashiga sallah sannan aunty sadiya tabama fareeda abinda takawo mata,, tai mata bayani dalla dalla sai dai nima bansan mita bataba masu karatu dan sunshige k’uryar d’akine.
” kukasance tare dani danjin yanda zata kasance…………………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 6~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸6⃣🔸🔶
…………….Yaud’in takasance asabar babu makaranta su sopy suna gida,, fareeda ce tadoso gidansu sopy hannunta rik’e da filet a rufe tashigo da sallama,, inna dake d’aki ta amsa mata,, tak’arasa d’akin inna ta gaisheta inna tace” yasu ladidin?? Lfy lao inna tamace na gaisheki wai anjima zata shigo kuje asibitin dubiyar nan.
“” A toshikenan babu damuwa saita zod’in,, kishiga safiyyan tana nan a d’akinta tana shirin tfy gidan hauwa’u,, nazatama tare zaku??? Eh dama tare zamuje to sai zanje gidan aunty sadiya nakai mata sak’o kinsan ita kuma bata zuwa gidan,, amma inna kai sak’on zan isketa acan d’in.
Ato shikenan ma,, itama d’in shirmene yake damunta kawai,, sadiya ba innarta bace??
Fareeda tayi murmushi bahaka bane inna laifin aunty sadiyarne aii,, tafad’a tana mik’ewa.
D’akin sopy ta shiga, sopy na zaune tana kwalliya fareeda ta zauna kusada ita ‘yammata wannan irin kwalliya haka’ saikace maishirin zuwa gasa??? Sopy ta harareta ke bakiga takibane??? Nitunda nake dake ma bantab’a ganin kinyi irin wannan gayunba wlhy????
“Fareeda ta tura mata filet d’in datazo dashi, tana fad’in shike nan kin rama.
Sopy ta bud’e filet d’in tana fad’in mikika kawo min??
Wlhy waynar filawace nayi dasafe,, to naga baki shigoba shiyyasa nabiyoki da ita.
Sopy tace” kin k’yauta kuwa dama tund’azu nakasa karyawa.
” saboda mi??
Wlhy bako mai kawai dai yaunatashi duk jikina babu dad’i ga gabana sai fad’uwa yakeyi. Fareeda tace tofa lfy dai””
Wlhy nima bansaniba ‘yar uwa.
To ALLAH yatabbatar mana da alkairinsa,,, fareeda tafad’a.
“” sopy tace” amin dai.
Tare suka fito kowacce tahau mota zuwa inda zata.
hauwa’u tatari ‘yar uwarta da murana,, sopy tace” aunty ina Arfat yake?? Yana wajen kareema yarinyar makwaftan mu d’azunnan tazo ta d’aukeshi suka tafi.
” kai aunty wanan d’an yaron kika bari aka fita dashi da wannan safiyar?? To yazanyi auta yariga yasaba dasu,, tashigo kawo min abune yamak’ale mata. Toni dai ki aika akawo min yarona! Karki damu zata kawoshi,, wai yana ganki ke kad’ai ina K’AWAR taki fareeda???
“Itama tana nan zuwa taje gidan sadiyane takai sak’o zuwa anjima zata zo.
To shikenan ALLAH yakawo ta nitashima ki d’ora mana abincin rana,, dama d’inki zanyi.
Kefa kinji matsalarki mutum baya zuwa gidanki ya huta dayazo saikin manna masa aiki, tafad’a tana kumbura baki.
Aunty hauwa’u tace” kekuma gashi baki son aiki ko?? Haka zamu kaiwa Abdul d’in ke,, inma zaki dage kidage wannan gidan nasu mai tarin ‘ya’ya da mata,, dan agidan za’a ajiyeki tunda dukkan matan yayyensa anan suke zaune.
Sopy ta tashi daga kwanciyar datayi,, to aishi yace” ba anan zamu zaunaba zai kama mana haya.
Aunty hauwa’u ta tab’e baki to ALLAH yasa hakane???
“Sopy tamik’e tana fad’in hakanema.
Miza’a dafa?? Aii inaga tuwon shinkafa za’ayi. Sopy tace” kai kukam kuda inna bakuda matsalar data wuce ta tuwo?? Aunty hauwa’u tai dariya,, toshi abban Arfat yakeson ci.
Nikam gsky bazanci tuwo daranaba,, zan dafa mana wani abu nida fareeda kafin tazo! Duk yanda kikayi cewar aunty hauwa’u.
Fareeda kam ta isa gidan aunty sadiya,, sadiya tabita da kallo lallai fareeda wannan irin kwalliya haka??? Duk ta tarar Abdul d’ince??? Fareeda tayi dariya auty sadiya ya rankine,?? kefa kikace na cake sosai.
” sadiya tace” gsk yane d’iyata, suka tafa nuna dariya.
Fareeda tace” yaya dai kin kammala girkin??
Aii komai ya kammala yanzu Abdul kawai zamu jira.
Fareeda tai wani ihu ALLAH yabar minke aunty na,, kina cikin aikina.
Sadiya tai dariya ALLAH yashir yaki fareeda,, yanzu dai ki kirashi dan muji yaushe zai iso??
“” to auntyna, fareeda takira Abdul yacemata aii gama shinan ahanyar zuwa,, tak’ara yimasa kwatancen layin?? Fareeda takuma yimasa kwatance sannan ta kashe wayar.
Sopy tagama abinci tazauna kusada aunty hauwa’u tana fad’in wash ALLAH yaudai saina sha maganin gajiya zan iya barci.
Aunty ta harareta way safiyya mikike son zamane?? Da dai keba raguwa bace wlhy.
Sopy tai dariya dama can dan ban gama sanin ciwon kaina baneba,, amma yanzu ina.
“” aunty tace” zaki gaya musu yarinya.
Kareema tai sallama hannunta d’auke da Arfat,, sopy ta karb’eshi da sauri tana fad’in oyoyo my son! Tai kissing d’in kumatunsa.
“” kareema ta gaisheta,, aunty hauwa’u tace kareema sannun ki! Kareema tai dariya kai aunty saikace wani aiki,, umma cema tace nakawoshi yasha nono amma ba kuka yakeba.
Aunty hauwa’u tace” aii nagode wlhy badankeba da Arfat bazai barni nayi d’inkin nanba,,, nibansan yanda zanyiba idan kinyi aure??? Kareema tafita da gudu wai kunya takeji,, su sopy sukasaka dariya…………………..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 7~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸7⃣🔸🔶
…………..Abdul ya iso yakira fareeda yay mata kwatancen inda yake,, suka aika wani yaro ya taho dashi zuwa k’ofar gidan,, amma sai yaja tunga yak’i shiga gidan,, fareeda tafito cikin dogon hijjab harda saka nik’af shi baima ganetaba dan haka yad’an ja gefe domin bata hanya,, tai masa sallama ya amsa yana binta da kallo,, tai dariya Abdul nicefa fareeda baka ganeniba ne??
Abdul yace”tofa wlhy ban ganekiba naga kinsaka nik’af nina zatama matar aurece!!
Fareeda tai dariya wlhy nice,, kashigo mana!!
A’a yaza ayi nashiga gidan mutane batareda izinin mai gidan ba???
Karka damu baya nan kuma yasan da zuwanka, kashigo kaway dan ALLAH.
sayda yay jim sannan yace” kina ganin babu matsala fareeda!
Babu wata matsala kamar yanda nagaya maka yasan da zuwanka,, kafinma katafi zai dawo gidan.
” to shike nan muje”
Har falon aunty sadiya suka kaishi yazauna yana shak’ar iskar fanka,, fareeda tafito zuwa tsakar gida ta iske aunty sadiya a kichin,, aunty sadiya tace” yaya dai yashigo?? Fareeda tace” yanama falonki zaune. Sukai dariya, sopy tacire nik’abi tad’au wata hoda a cikin leda ta kuma shafawa ta d’ au kwalli tashafa,, aunty sadiya tamik’o mata turare ta fesa,, sannan tace” nayi my aunty??? Sadiya ta jinjina kai kinyi d’iyata komai yaji,, d’auki abinci kitafi nima zanzo mugaisa.
To shikenan auntyna fareeda tafad’a tana d’aukar tiren da kulolo ke kai.
Tai sallama ak’ofar palon cikin irin wata murya wadda itama batasan tana da itaba,, Abdul ya amsa tareda mik’ewa yatarota tiren hannunta ya karb’a yana fad’in wannan tire haka aii yayi miki nauyi dayawa.
Fareeda tazauna tana murmushi Abdul yad’ago suka had’a ido,, jiyay wani abu yashige jikinsa tundaga kansa har zuwa yatsun k’afarsa,, yarintse ido yana fad’in yasalam!!
Fareeda tace”Abdul yaya dai???
Yasakar mata tsadadden murmushi babu komai ina cikin wani irin farin cikine dana kasance dake.
“Fareeda tace” tofa Abdul nikuma?? Ko ka manta ba gimbiyarka bace sopy??
Abdul ya b’ata rai kinga idan muna magarmu ki daina sako mana wata sopy.
Fareeda tayi murmushi to nabari my love kayi hak’uri kabar b’ata ranka.
“”Fareeda tazuba lemo akofi tabasa, yakarb’a yashanye,, takalleshi abincifa,, yay mata murmushi abani naci dama kamshinsa yanata cikamin hanci.
Fareeda tazuba masa farar shinkafa da miya yaci ya k’oshi suna hira,, saida yagama suka nutsu,, fareeda tace” Abdul yamaganar mune??? Abdul yay mata wani kallo na masoyi zuwa masoyiyarsa yace”ina saurarenki aii dama maganarce takawoni gareki my love!!
Fareeda tai wani murmushin mugunta tace” yayi k’yau,, tasowa tayi tadawo kujerar kusa dashi, takanne masa ido d’aya yay murmushi.
Shima yajuwyo sosai suna kallon juna,, suka k’urama juna ido kamar zasu cinye juna,, fareeda ce tafara janye nata idon tana murmushi,, cikin karsashi tace”my Abdul!!!!
Abdul ya amsa murya asark’e. Taja ajiyar zuciya Abdul ina matuk’ar k’aunarka fiye da mai buk’atar ruwa acikin sahara,, ina begenka fiyeda d’an da ke buk’atar nonon mahaifiyarsa alokacin dayake kuka, ina son kasancewa dakai tamkar bawan dake k’aunar bud’ar ido yagansa a aljanna, ina burin tara zuri’a dakai fiyeda talakan da ke burin tara dukiya, ina burin kozamu mutu mu mutu tare tamkar laila da majnun.
Hawaye suka zubo akuma tunta, Abdul yasa hannu yashare mata hawayen,, cikin sark’ewar murya yace” nima ina sonki fareeda ina k’aunarki, ina burin aurenki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAH kece uwar ‘ya’yana.
Fareeda tad’ago kai dasauri tana kallonsa dan ALLAH Abdul da gsk kake???
Abdul yay murmushi da gsk nakeyi fareeda insha ALLAHU zaki zama matata.
” fareeda tai dariyar farin ciki,, tace” to amma yanzu yaza muyi da sopy???
Abdul yace” zan fad’a mata bana ra’ayinta yanzu, kece ra’ayina!!
A’a Abdul bahaka za’ayiba kawo kunnanka kaji!! Abdul yamik’awa fareeda kunnansa tafad’a masa,, yay wani murmushi yace” (nice idear) hakanma yayi,, nandai sukaita hira suna zazzagema juna sirrin zuciyarsu.
Agidan aunty hauwa’u kuwa sopy nacan tana jiran fareeda kad’an kad’an saitayi tsak’i, aunty hauwa’u tace auta way miye matsalarki ne???
Sopy tai d’an tsaki wlhy aunty haka kawai yau sai gabana ke fad’uwa tunda safe,, ga fareeda daga kai sak’o amma shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu.
Aunty hauwa’u tace” k’ila gosulo ne yarik’e ta,, zatazo tunda tace miki zatazo,, fad’uwar gaba kuma kita addu’a insha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi.
Sopy tace” to ALLAH ya tabbatar mana da alkairin.
Kubiyoni masu karatu, danjin yanda zata kasance………………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 8~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸8⃣🔸🔶
…………….Sai wajan k’arfe 3:30 suka baro gidan aunty sadiya, Abdul ya kalli fareeda my love!! Yanzu “k” ina kika nufa??
Tai fari da idanu zanje wajen gimbiyarka ne a d’orayi, dan tana gidan aunty hauwa’u tana jirana.
Yad’an gintse fuska wato wannan gimbiyar bazai fita a bakinkiba ko??
Tai murmushi kayi hak’uri,, amma naga kaine kasaka mata gimbiyar aii?? Eh nine nasaka mata amma a da ba yanzuba,, yanzu kece gimbiyata! Dan haka karna sake jin wannan sunan wlhy natsaneshi.
Ta murmusa insha ALLAH wannan sunan ya goge har abada kamar yanda ALLAH ya shafe FIR’AUNA DA ABU LAHAB a doron k’asa.
“” Abdul yay murmushi harna k’ara sonki my love!!
Itama tai dariya to ALLAH yak’ara maka sona my love!! Amin Abdul yafad’a yana kallonta,, yacigaba toni bari nawuce gida dansu adam nacan suna jirana zamuje fagge.
Okey to saikun dawo,, nima bari nak’arasa dan nasan sopy nacan hankalinta atashe tana zura ido taga ta inda zan b’ullo.
Abdul yace” okey yazaro dubu d’aya yabata ga wannan kiyi k’ud’in mota,, tace to nagode,, saida yaga tashiga mota sannan yatafi shima.
Fareeda tanufi d’orayi cikin farinciki,, irin wanda daka ganta zaka shaida haka.
Ta isa gidan aunty hauwa’u sopy ta harareta aii dama kin koma saimu had’u agida.
Fareeda ta rungume sopy tana fad’in sorry my dear sister wlhy matsalar gosuloce kuma na tarar aunty sadiya bata nan nad’an dad’e kafin tadawo,, plz for giveme my sweet sister ayi hak’uri Amin azuri,, auntyna kisa baki a yafe min.
Aunty hauwa’u tayi dariya karki damu zaku daidaita nasani aii babu mai shiga tsakanin masoya.
” sopy ta tuntsire da dariya ALLAH dandai kawai na yarda dake,, amma da watace sainayi sati bamuyi magana ba.
Fareeda tace” to nagode my darling da kika yarda dani.
Sopy tace” to zauna nakawo miki abinci.
Nan sukaita hira abinsu,, sopy tace” way my sister miye yasaki farin cikine?? Naganki yau cikin irin wata walwala ta musamman; fareeda tayi dariya kibari kawai ‘yar uwa wlhy ina cikin farin ciki mai tarin yawa. Tofa k’awata miye sirrin???
“Fareeda tayi dariya nima ban saniba amma ki tayani da addu’a.
Sopy ta dafata to ALLAH ya tabbatar mana da alkairi my dear sister, nikuma kinga yau sai gabana keta yawan fad’uwa bansan daliliba??
Kema aikairine my sopy.
Nan dai sukaita hirarsu har saida mijin aunty hauwa’u yadawo yana tsokanarsu,, my jidda yaukuma mafarkinmu tagwayen inna sukayine?? Aunty hauwa’u tayi dariya kamar dai hakane abban Arfat nima nayi mamakin ganinsu, dan yauma girkinsu aka kaimaka kasuwa.
Haba shiyyasa naji girkin bai dad’iba yafad’a cikin tsokana.
“” sopy tace haba na robar kaidai fad’i gsky nasan yau kaci girki ba irin namatar kaba, zauna kabamu labarin santin dakayi akasuwa.
Gaba d’aya suka kwashe da dariya hauwa’u tace” autafa ya isheku kubarmin miji yasha iskar duniya,, abban Arfat yace” barni dasu my jidda aii duk zan iya dasu ba baki suka fini ba.
Haka sukaita hirarsu da wasa da dariya sai gab da magriba suka tafi gida.
“” kubiyoni masoyana,, ina k’yaunarku kamar yanda kuke son kasancewa dani a books d’ina, ina muku fatan alkairi akoda yaushe……………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 9~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸9⃣🔸🔶
……………Yau tsawon kwana hud’u kenan Sopy bataga Abdul ba, duk ta damu dan tunda suka had’u baitab’a kwana biyu baije gidansuba,, amma yanzu har tsawon kwana uku baizoba, gashi tana jin kunyar zuwa layinsu duboshi tagayawa fareeda tun jiya amma tace mata inkaji shiru to lfy ce,, itakam bata gamsu da wannan dalilinba,, wannan ne karo na farko dataji haushin rashin kasancewar waya a hannunta,, datanada waya saita kirashi kodan taji lfy?? Toko wayar baban ta zata amsa to saidai kuma batada nomber Abdul d’in tad’anja tsaki mara sauti,, kai bari uncle kabeer yazo zance masa ya saya min waya kodan irin wannan ranar,, ALLAH dai yasa ya amince kar yace saina gama makaranta.
Fareeda ta tab’ata,, tai firgigit alamar dawowa daga tunani,, sopy way mi kike tunanine inata magana tun d’azu amma kinyi shiriru miye matsalarki ne???
Sopy taja ajiyar zuciya matsalata dai d’ayace kamar yanda kika sani fareeda,, wace matsala kenan?? Fareeda ta tanbaya?? Sopy tace” matsalar Abdul mana,, yaufa tsawon kwana hud’u kenan baizo wajena ba!!
Fareeda tad’an tab’e baki,, aii nafad’a miki lfy itace ke b’uya amma ba ciwoba,, toki kwantar da hankalinki yanzu haka daga gidansu Abdul nake..
Da sauri sopy tace” dan ALLAH da gsk kikeyi?? Fareeda ta b’ata rai tunda mike dake natab’a miki k’aryane??? Sopy tace”A’a” tokuma fareeda ta fad’a, dama bawani abune ya hanashi zuwaba wani aikine abbansu yasakasu,, yace” nabaki hak’uri shima yayi missing d’inki amma zuwa gobe zaizo.
“” sopy ta sauke ajiyar zuciya kai wlhy harnaji dad’i, amma wlhy habibi yad’auki hakkina basai yasanar minba.
Fareeda tace” kedai ki masa uzuri tunda bai tab’a aikata miki maka mancin hakaba.
Sopy tace” hakane kuma na fahimce sa,, kema ngd miki abin k’aunata aminiyata mai sona da son farin cikina,, yau zanyi barci mai dad’i kenan tunda naji dalilin rashin zuwan rabin raina gareni.
Fareeda ta harareta amma bata ganiba, azuciyarta tace” ko ubanki neshi dole ki barshi.
Amma afili saitace lallai kam yau sai ayi barci harda munshari tunda anji labarin habibi.
” Sopy ta kai mata duka fareeda ta kauce tana dariya, itama sopyn dariya take, tace sister dan baki san so bane amma kibari inkin fara zaki san zafinsa dakuma dad’insa.
Fareeda ta tab’e baki tana fad’in naga lailah da majnun indai asoyayyane.
Nan dai sukata hirarsu.
Shikam Abdul kullum saiyazo wajan fareeda hira amma abayan layinsu suke hirar a soron gidan k’anin babanta” wannan yasa sopy bata tab’a ganinsuba, ko wani d’an anguwar bare akawo mata gulma.
Bayan tafiyar fareeda ma saita nufi inda suke had’uwa da Abdul, dan tasan yana can yana jiranta,, aiko kamar yanda tai tunani yana can zaune yana jiranta,,Tashiga soron da sallama, tazauna kusada Abdul ayya my love! Kayi hak’uri dan ALLAH nabarka kai kad’ai,, Abdul yay mata hararar wasa dama k’yace haka tunda kin barni ni kad’ai tun d’azu nake zaune anan yafad’a yana kallon agogon hannunsa.
“” kayi hak’uri dan ALLAH ina wajen mutuniyar ka, dan ta tada hankalinta saboda rashin ganinka,, ya yatsine fuska wacece kuma mutuniyata?? Fareeda tayi dariya kana da wata mutuni bayan sopy?? Ya harareta mutuniyar ki dai dan dama tare naganku, gashi kuma nabarku tare,, dan hakama kibar had’ani da ita.
Fareeda tad’an zaro ido waje tofa har lamarin yakai haka?? Abdul yace” aii yama wuce haka,, kinga nibama wannan ne agabanaba,, akwai abinda yakawoni.
“” fareeda tagyara zama to miye ketafe dakai my love!! Ya shafa sumar kansa fareeda akwai matsalafa! Matsala kuma wace irin matsala!!! Fareeda babana yak’i yarda da batun aurenmu dan yace bazai zama k’aramin murum ba,, bayan ankai kud’in aurena da safiyya yanzu kuma nace wata nakeso ba itaba,, wlhy nayi iya bakin k’ok’arina danya fahimta amma ina yamak’i saurarena.
Fareeda tai shiru tana tunani, zuwa can taja ajiyar zuciya, takuma gyara zama my love! to idan abba yak’i ita kuma ummafa??
Yaja ajiyar zuciya ita umma dama batada matsala, dan duk abinda nakeso itama tana sonshi kinsan ni d’an gatantane,, kodana fad’a mata catayi ALLAH ya zab’a mana abinda yafi alkairi.
Fareeda ta lankwasa yatsun hannunta sukai k’ara tace” karka damu my love! Shima abban zai yarda da buk’atarka.
Abdul yace” ta halin k’ak’a zai yarda abbana yanada taurin kai fareeda.
Fareeda tai murmushi karka damu kabar komai ahannuna wannan aikinane.
Yace” to shikenan,, fareeda tace” saidai matsala d’aya ke damuna,, yay saurin cewa wace matsala kuma?? Tace” matsalar sopy mana, tana cikin damuwar rashin ganinka yanzu haka saida nai mata k’arya sannan ta kwantar da hankalinta.
Banason dukkan al’amarin aurena yashafi gidansu sopy bare harta zargi wani abu, nafi son kozata san hakan to yazamto an d’aura aurenmu,, alokacin kome zai faru yafaru tunda an d’aura nasan daga baya kowa zai hak’ura yabarmu. Abdul yace” ke nifa ayanda nake jina bana tsoron kowa yasan sirrin zuciyata harda safiyya kuma aciki.
Fareeda ta girgiza kai A’a my love!! Nikam bana fatan faruwar hakan,, har yanzu zuciyata da ruhina suna k’aunar safiyya, bakuma nason abinda zai cutar da k’awancen mu,, kuma bana son ka k’ub’cemin yanzu,, dolene mu dai daita tafiyar mu domin kawcema b’acinran sopy.
Yace” to ta yaya?? Tace” kawo kunnanka kaji,, yamik’a mata kunne ta fad’a masa,, yad’aga kafad’a tareda tab’e baki idan kina ganin hakan zai kwantar miki da hankali sai nayi.
Tace” eh my love! Hakan zai sakani farin ciki,, ya murmisa to babu damuwa nibari na wuce sai da daddaren zaki ganni nazo.
To shikenan suka mik’e tare yanufi gida ita kuma tashiga gidan k’anin babanta domin gaishesu.
KIRA:- kai jama’a cin amana bashida k’yau yanzu idan kaine ko kece haka ta kasance dake kamar yanda take shirin kasan cewa da safiyya dan ALLAH yazakiji?? babu cin amana mai ciwo kamar irin ta wanda kafi k’auna ko ka amince dashi ka yarda dashi,, irin wannan cin amanar yafi zafi da ciwo,, yafi karya zuciya da bak’in ciki,, amana abune mai girma dan tana d’aya daga cikin alamomin MUNAFIKI, akwai irinsu fareeda da dama acikin al’umma,, samari da ‘yammata, k’awa da k’awa, aboki da aboki,, masu aikata cin amana,, wad’anda suka maida cin amana bakomaiba acikin laififfikan duniya,, to “UBANGIJI ALLAH” ya shirya zukatanmu ka ganar damu gsky. Amin ya “RABBI”
Ku biyoni danjin yanda zata kasance………………..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 10~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
🔶🔸🔟🔸🔶
……………Da daddare Abdul ya aiko kiran sopy,, cikin zumud’i tasaka hijjab tafita,, inna ta girgiza kai tana fad’in yaran zamani basu san kunyaba dai.
Inda suka saba zama ta iskeshi zaune, saidai fuskarsa babu walwala tak’arasa gareshi,, Assalamu alaika ya habibina,, yad’an kalleta batare daya amsaba, ya maida kansa kan waya.
” tazauna inda tasaba zama sai kuma jikinta yafara sanyi,, tace” habibina ina yini ?? Ykk? Ya kwana biyu?? Wlhy nayi missing d’inka.”
Yad’ago yana kallonta “k” irin wannan surutu haka bakinki baya gajiya?? Cikin mamaki sopy take kallonsa danjin furicin bakinsa,, ta daure tace” habibina miye matsalarka??
Yad’an yatsine fuska yana bin jikinsa da kallo,, sai kuma yakalleta “k” anaki tunanin minene matsalar ABDALLAHI ?? tad’anja numfashi habibina inda nasani aii bazan tanbayekaba sai kawai na fara maganinta.
“” yace to banida wata matsala nikam………kafin yarufe baki fareeda ta k’araso tana tafa hannaye,, suduka suka maida kallonsu gareta, dan danan fuskar Abdul ta sauya zuwa farinciki,, yace” sannu da zuwa m……. saikuma yayi shiru daya tuna gaban wadda yake, fareeda tak’araso tazauna kusada sopy tana fad’in yaudai sai abarmu muhuta ga habibi yazo.
Sopy tad’an rankwashi kanta ALLAH fareeda kinga gurin barcina,, Abdul ya tuntsure da dariya wadda shima kansa baisan tamiye ba,, suduka suka bishi da kallo,, sopy tace” my sister kinga habibi ko tunda yazofa yak’i wani sakin jiki dani tamkar surukarsa ko mak’iyyarsa,, saifa da kikazo yay dariya.
” fareeda ta tuntsure da dariya,, aidama tunda nazo dole film d’in ya k’are,, inba hakaba yasan zan tona,, dama yace” idan yazo gunki zai canja miki dan yaga ko kin damu dashi?? Sopy tad’an harari Abdul kai habibina ALLAH kad’auki hakkina,, yay murmushi wanda saida fareeda ta k’yafta masa ido yayishi,, yace” tokiyi hak’uri bazan sakeba kinji,, nan dai suka cigaba da hira,, mafi yawan hirar fareeda ce ke control d’in Abdul idan zai kauce hanya,, dan idan sopy tayi magana saikaga yaji haushi sai fareedan tayi saurin gyara masa,, da hakadai akai firar kowa ya kama gabansa,, badan hirar tayima sopy dad’iba.
Haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri,, su sopy suna zuwa makaranta,, kuma k’awancen su natafiya kamar da yanda yake,, sai dai fareeda tana cin dunduniyar sopy batareda sopyn ta fargaba,, domin tayarda da fareeda d’ari bisa d’ari.
Abdul kuwa yanzu ba kullum yake zuwa gidansu ba, saima ya had’a kwana hud’u biyar bai zoba,, sai idan fareeda ta matsa masa da magiya sannan yazo,, wannan lamarin ne yasaka sopy cikin matuk’ar damuwa, ga exam tana gabatosu, ga damuwa ta hanata maida hankali akan karatun,, duk k’arshen sati uncle kabeer saiyazo yayi musu bitar karatu amma ya lura kwata kwata sopy bata fahimta,, ya tsareta da tambayoyi tace masa babu abinda ke damunta,, daya kula bazata sanar dashi damuwartaba sai kawai yakoma lallashinta damata nasiha.
Ahankali inna tafara fahimtar matsalar sopy,, inna takira sopy ta tsareta saita fad’a mata abinda ke damunta,, harta rame haka sai tsawo kamar daren sallah,, sopy bata b’oyema inna komaiba ta fad’i damuwarta,, inna ta rarrasheta da alk’awarin tayata da addu’a.
“Ana cikin haka suka fara (S,S,C,E exam) d’insu saidai akwai matsala dan gsky sopy bata wani k’ok’ari,, gashi tasan abubuwa dayawa a exam d’in sai takan kasa rubuta komai akan takardar,, wani sa’in ma haka take fitowa bata rubuta komaiba,, dahaka suka gama rubuta (WAEC) suka fara (NECO) ba laifi Sopy tad’anyi k’ok’ari a neco amma bawani nakuzo ku ganiba,, to sopy ALLAH yabawa mai rabo sa’a dai kawai za’ace.
Suna cikin exam akakai kud’in auren Abdul gidansu fareeda,, sopy tayi matuk’ar farin ciki , dan bata san wa fareedan zata auraba,, dukda kullum tana nacin son ganin gwanin fareedar, amma sai tace” mata karta damu zata sansa aranar d’aurin aure,, danshi ba mazaunin kano bane,, ALLAH sarki safiyya itakam ta yarda mijin da fareedan zata aura bad’an kano bane.
“” dukda har yanzu matsalar rashin zuwan Abdul wajen sopy yana matuk’ar damunta,, amma yanzu takan d’an rage nuna damuwarta agaban mutane dan bata son inna tashiga damuwa akanta, sai idan tashiga d’akine takeshan kukanta, gashi kuma bata iya wani barcin kirki, ALLAH sarki sopy “SO” yanada zafi, musamman ma lokacin da wanda kakeso ke neman kufce maka.
To MASHA ALLAH su sopy sun gama exam, sun shiga kacaniyar shirin bikin fareeda daya rage saura sati biyu,, dan haka yanzu basuda wani lokacin kansu,, amma duk dahaka sopy bata harbo jirgin fareeda da Abdul ba,, dan tuna nintama baitab’a waigawa inda sukeba, bare harta zargesu.
Biki ya kankama sosai, dan jibi d’aurin aure yau kuma kamu,, agidan aunty zainab yayar fareeda suke zaune itama annan rijiyar lemon take, saidai akwai d’annisa tsakaninsu,, suna gidan anata hira da barkwanci irinna k’awaye,, sopy tamik’e tana fad’in kaini barinaje farkon layinnan na siyo gyad’a dafaffa, dan tunda zamu shigo naganta wlhy,, ko akwai mai zuwane???
Kowa yace A’a, fareeda ta mik’e kinga bar ‘yan iska K’AWATA muje narakaki, kuma wlhy ko munsiyo babu maicinta,, fareeda taja hannun sopy suka fita.
“Suna cikin tfy sopy tace” sister kinga habibina ko har yanzu baizoba tun wancan satin gashi nima inason muyi maganar aurenmu,, dan nasan kina tfy zan tsani anguwar wlhy.
Fareeda tadafata karki damu sister kibari yau idan munkoma gida saimuje wajensa.
” sopy tace” toshikenan sister amma wlhy lamarin nan na Abdul yafara isata…………tai shiru domin hango Abdul ya doso layin.
Fareeda tace” yaya dai naji kinyi shiru?? Da hannu sopy tanunama fareeda Abdul! Gaban fareeda yay matuk’ar fad’uwa shikuma wannan daga ina?? Fareeda ta fad’a a zuciyarta.
Tofa masu karatun k’a k’a rak’a k’ak’a kudai biyoni muji mizai farune??? …………………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 11~October ~2016
🔷🔹NI DA K’AWATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣1⃣🔸🔶
……………fareeda tai saurin cewa kinga sopy zoki b’uya naje wajansa Dan naji ina zaije ne???
” sopy tace” gsky ne K’AWATA shawararnan tayi jekiji mizai ce.
Fareeda ta nufi Abdul itakuma sopy ta b’uya.
Tunda ya hangota yake murmushi,, tak’arasa wajensa da sassarfa tamkar zata kifa,, yay saurin cewa my love! Daga ina??? Tace” A’a kaizan tanbaya daga ina Abdul?? Yace” ni wajenki nazomana.
Tad’an zaro ido waje Abdul miyasa bazaka kirani muhad’u a wani wajenba,, ko ka manta muna tareda sopy anan,, yanzu haka tare muke kuma itace tafara ganinka ma,, sai wayo naimata nace” bari na tanbayeka inazaka??
” yad’anja tsaki nikam gsky fareeda lamarin nan yafara isata yaza muyita b’oye b’oye akan abinda bashida muhimmanci bayan kuma miji da mata zamu zama,, way ko kina tsoron safiyyane??
Fareeda ta girgiza kai bawani tsoro Abdul inadai son kozata sani tofa sai bayan an d’aura aurenmu jibi,, yanzu kazo muje kace” mata wajenta kazo dan ALLAH karkayi abinda zaisa sopy ta fahimci wani abu plz kataima keni mijina abin sona!!!!;!! Tafad’a tana matse kwalla,, yay saurin cewa karkiyi kuka amaryata zanyi duk abinda kikeso plz karkiyi kuka.
“Fareeda tayi murmushi toshike nan muje.
Abdul yazagayo tabayan sopy yace” mai b’uya aii gani naganki.
Sopy tayi saurin juyowa danjin maganar habibinta,, tai murmushi to waya gayamaka ina nan?? Yay d’an murmushi aii basai anfad’a minba zuciyata ma zata iya ganoki,, barema ina kallonku keda fareeda kuna kullawa.
” sopy tai dariya sosai tace” to naji ina ka kaimin k’awata ne?? Yace” taje sayo muku gyad’a ne, yanzu zata dawo,, tace” okey tokai mike tafe dakaine?? Ya murmusa nazone kawai naganki gimbiyata,, ya d’akko kud’i har dubu goma ya mik’a mata ga wannan kiyi hidimar biki dasuko, saidai kiyi hak’uri babu yawa gashi kuma sunzo miki ak’ure.
Sopy tace” to ngd saidai karage domin kud’in sun yimin yawa, dan mun gama komai,,, Abdul ya girgiza kai kinsan bana son musu kuma babu k’yau maida hannun k’yauta baya.
Bayanda zatayi dole ta karb’a tai masa godiya.
Ya harareta batare data ganiba azuciyarsa yace” ‘ yar son banza.
“”kud’inda Abdul yabama sopy fareedace tabashi yabata tunda tasan kud’in zasu dawo hannunta ne.
Fareeda tak’araso sukad’an sake tattaunawa sannan Abdul yatafi,, bayan tfyr Abdul suma suka nufi gidan aunty zainab sopy tamik’awa fareeda kud’in my sis ga wannan habibine yabani ki ajiyesu awajenki ko wani abu zai taso mana.
Fareeda tace” ALLAH yasaka masa da alkairi.
RANA BATA K’ARYA SAIDAI UWAR D’IYA TAJI KUNYA:- yaune aka d’aura auren fareeda d’ahiru da Abdullahi Abubakar mai fata,, d’aurin auren dayabawa mutane mamaki, domin mutane dayawa sun san Abdul da k’awar fareeda yake soyayya,, amma gashi yanzu ya auri fareeda, dan danan surutu yafara yawa acikin anguwa.
Su sopy suna makwafta gidan wata saddik’a anan suke zaune,, sopy tagama shirinta cikin ankon dasukayi itada fareeda kawai,, saidai ta manta sark’arta agidansu dan haka tamik’e tana cema fareeda bari ta d’akko, sopy ta fito tana gaisawa da mutane,, amma sai mamki yakamata dataga anata nunata ana kus kus, bata kawo komai arantaba tayi wucewarta.
Da daddare aka kai fareeda d’akin mijinta dake cikin gidan su Abdul,, dukda darene lamarin yayi matuk’ar bama sopy mamaki,, saikuma gabanta yashiga yawan fad’uwa da sauti da sauri,, bayan raguwar mutane ‘yan kai amrya fareeda tacema sopy dan ALLAH ta samomata ruwa tasha,, sopy tace to amrsu ta ango mai dad’in suna aii dole naje neman ruwansha,, bayan fitar sopy fareeda ta d’auki wayarta takira Abdul,, dan dama shitakeson kita shiyyasa ta aiki sopy.
Sopy tana tsaye a k’ofar gidansu Abdul tanata kalle kalle zuciyarta cike da fargaba,, can saitaji muryar adam yana fad’in Abdul kana ganin hakan dakayi shine dai dai tun d’azu nakeson muyi magana kanata min hanya hanya,, yanzu kai kana ganin idan sopy tagano kaine ka auri fareeda mi kake ganin zai farune???
Abdu yay magana cikin tsawa kaga adam kafita hanyata wlhy to miye idan sopyn tagane nine na auri fareeda,, ita uwatace kokuwa zata tsirenine???
Bazata tsirekaba amma tabbas sai ALLAH ya saka mata kuma karubuta ka ajiye ranar nanan zuwa gareku daga kai har fareedar daka aura.
Tun sopy najin abinda suke fad’a harta dainaji,, garin yafara juya mata kafin kace me ta yanke jiki ta fad’e awajan,, dan dana hankalin mutane yadawo gurinta,, Aka fara fad’in “inna lillahi wa inna ilaihirraji un.” Wanine yay k’arfin halin fad’in ad’auketa mana atafi asibiti dan asume take……………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 12~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💕
Assalamu alaikum masu karatu,, ina mai baku hak’urin canja sunnan wannan book,, domin bansan an rubuta book d’in NI DA K’AWATA ba sai yanzu,,dan haka yanzu zai koma NI DA AMINIYATA,,, sannan ina k’ara bawa marubuciyar NI DA K’AWATA hak’uri. Ngd acigaba da gashi.
🔶🔸1⃣2⃣🔸🔶
…………..Asibiti mafi kusa aka nufa da sopy,, sannan labari yakai gidansu sopy,,, ALLAH ma yasa uncle kabeer yana nan,, shima yazo d’aurin auren fareeda,, babu b’ata lokaci suma suka nufi asibitin da aka kai sopy,, wadda likitoci suka rufu kanta,, amma ko motsi batayi kwance take tamkar gawa.
“Ganin dare yafarayi likitoci sukace su inna suje gida abarwa gobe,, aga abinda ALLAH zaiyi kuma,, inna tace” babu inda zataje tananan tareda sopy,, dak’ar aka lallasheta suka tafi akabar uncle kabeer awajenta.
Awannan lokacin kuwa amarya da angonta suna can ana ragargazar amarci,, dan ango bai d’agawa amaryar tasa k’afaba,, dukda yalura tana cikin damuwar abinda yafaru da AMINIYARTA,, itama dai tabada gudummawa dan tasan wannan shine zai k’ara kusanci tsakaninta da Abdul,, zai kuma k’ara zama dalilin da dole iyayensu su barta tazauna tareda mijinta,,, ba k’arya tasha wahala amma ta daure sosai dan tana son Abdul,, to fareeda saimuce ALLAH Yasanya alkairi yakuma shirya masu irin halinku nacin amana da yaudara. Amin
A asibiti kuwa har yanzu sopy bata farfad’oba kuma likitoci sun dage akan tanada rai bata mutuba,, to ALLAH yasa haka, dan gsky masu karatu indai sopy ta mutu to nimafa ‘yar rahoton taku bazan sake kawo muku rahotoba,, ALLAH dai yasa da ranta.
Shagalin biki yakoma zaman jigum jigum,, dan maman fareeda sai kuka takeyi tana fad’in wlhy saita kashe auren fareeda,, tunda har taci amanar safiyya,, in kuma ba hakaba zata tsinema fareeda inhar bata rabuda Abdul ba.
“”Tofa turkashi kunji wata sabuwa masu karatu.””
Har zuwa yamma sopy bata farfad’oba,, dayawa mutane sun fara yarda tama mutu,, dan ko mahaifinta ma cayayi likitoci suyi hak’uri subada gawar safiyya aje amata suttura.
“Wani likita yace” way baba wayace maka ta rasu?? Yarinyar nan tanada ranta dan ALLAH kubarmu muyi aikinmu.
Sai wajen k’arfe 4:46pm sopy ta farfad’o saidai sun hana kowa ganinta,, dansun yimata allurar barci,, saboda ta sami hutu,, dukkan ‘yan uwa suna asibitin kowa ka kalla baya cikin walwalarsa,,, labari kuwa sai k’ara baza anguwa yakeyi,, kunsan dai mutane da gulma,, dan yanzu gulma maza da mata kowa ya iyata,, ALLAH dai ya shiryar damu jama’a.
Mahaifin fareeda ya aika hargida aka kira masa Abdul da fareeda,, bayan d’an wani lokaci suka iso,, dukkan dangi sun had’u, mamar fareeda da babanta sai yayunta biyu yaya lawan, da yaya saminu, da zainab, sai k’anin babanta.
Sai baban sopy da inna, aunty Nafisa da hauwa’u,, sai uncle kabeer,, fareeda duk tabisu da kallo azuciyar ta tace” tofa wannan gangamin namiye?? Zuciyarta tace mata duk anyishine saboda “k”,, tai wani d ‘an guntun murmushi aiko sama tarwatsashi dan fad’ansu ko wani hargaginsu bazai tsorataniba,, tuni nashiryama fuskantar wannan matsalar.
Yaya lawan yadaka mata tsawa to mara kunya idan kin gama yimana kallon rainin arzik’in saiki zauna ko,, mara mutunci kawai.
Fareeda tad’an tab’e baki sannan ta zauna kusada mijinta,, babanta yay gyaran murya, yad’ora da fad’in assalamu alaikum!!! Kowa ya amsa,, yabi fuskokin kowa da kallo sanna yagyara zama yace” Abdullahi!!! Abdul ya amsa kansa ak’asa.
Baban fareeda yace” miyasa ka auri fareeda bayan kuma da safiyya kuke tare??? Kuma har munyi maganar aurenka da safiyya harda iyaye aciki???
Abdul yagyara zama, baba ku gafarceni dacan safiyya nakeso amma yanzu fareeda nakeso kuma gashima har kun auramin ita.
Baba ya k’ara d’aure fuska, to miyasa lokacin da maga batanka suka zo basu fad’i hakaba??? Saima sukace mana yayanka ne zai auri fareedan??
Abdul yace” nine nace sufad’i haka dan karka hanani auren fareeda.
Baba yaja tsaki to aii har yanzu bata sake zaniba domin dolene kasaki fareeda yanzu anan wurin,,, gaba d’aya wajen saida suka d’ago suna kallon baba banda mama da tace” wannan batu kam tilas ne dole kasaki fareeda ka auri safiyya.
Baban sopy yay saurin tareta amma dai ba haka mukayi dakaiba malam d’ahiru,, gsky karku raba musu aure………baban fareeda yay saurin katseshi, saidai kayi hak’uri malam ibrahim nariga nagama yanke hukunci.
Abdul yace” gsky baba saidai kuyi hak’uri wlhy bazan iya rabuwa da matataba ina sonta,, ina kuma burin kasancewa da ita har abada.
Fareeda ta karb’e wlhy nima baba inason mijina dan ALLAH karku rabamu,,,, aii kafin tarife baki yaya lawan yabata duka jikake taffff,, ta kwalla k’ara tana fad’in wlhy sai ALLAH yasaka min tunda ban yimimaka komai ba mugu azzalumi…….yako tashi yashiga dukanta tako ina,, Abdul yamik’e yashak’i wuyan yaya lawan yana fad’in kai bagidaje mahaukaci wlhy idan hannunka yak’ara sauka akan matata saina kasheka.
Uncle kabeer yadaka ma Abdul tsawa yace” sakeshi,, jikin Abdul yana rawa yasaki yaya lawan yakama hannun fareeda yana fad’in muje gida,,, baban fareeda yamik’e murya a sark’e yace” fareeda inhar kika koma gidan Abdullahi to babuni babuke, nacireki daga cikin ‘ya’yana kije nabar masa ke.
” fareeda tace” baba nasan rankane ab’ace amma wataran zaka gane hikimata ta auren Abdul, harma kayi alfahari da hakan,, mama tace lallai fareeda wuyanki ya isa yanka yanzunan mahaifinki kike fad’ama haka saboda d’a namiji,, fareeda ta tab’e baki mama kema nasan bazaki tab’a ganewaba sainan gaba,, kamar yanda kuka buk’ata zanyi nesa da ku da ‘ya’yanku har zuwa lokacin da zaku huce,, aunty zainab dake kusada ita ta wanka mata mari taka’ara mata nabiyu, Abdul yarik’e hannun cikin masiba zainab tace” kaid’an akuya sake min hannu ke kuma wlhy nan bada dad’ewaba zakiyi nadamar abinda kika aikata,, kuma saikinyi mamakin mijin da safiyya zata aura maci amana kawai.
Fareeda ta tab’e baki wannan kuma bai dameniba,, idan safiyya zata auri mazan duniya bai dameniba tunda nidai nasamu muradina,, taja hannun Abdul suka tafi,, mahaifin fareeda ya yanke jiki yafad’i agurin………………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 13~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣3⃣🔸🔶
………….gaba d’aya suka nufo kan baba,, uncle kabeer ne yay k’ok’arin yayyafa masa ruwa ya kawo numfashi,, yad’ago yana kallonsu dagaske fareeda tatafi ta zab’i yaron nan sama dani??
Aunty zainab tace” baba ta tafi kabarta kawai aii “DUNIYA MAKARANTA CE”” yace” shikenan ku shaida nacire fareeda acikin ‘ya’yana kuma duk wanda yay mu’amulla da ita acikin ku ban yafe masaba,, kamar yanda ta buk’ata nabarta da Abdullahi.
Baban safiyya yace” dan ALLAH malam d’ahiru kabar wannan furicin da fareeda da safiyya duk d’ayane agurinmu,, in akayi hak’uri itama safiyyan ALLAH zaibata wani, dama can ALLAH ya rubuta ABDULLAHI mijin fareedane ba safiyyaba……baban fareeda ya k’atseshi malam ibrahim kabarni kawai wlhy nariga na yanke hukunci dan haka kabarni ina ganin mutuncinka.
Dole kowa yay shiru,, dan sunsan ransa ab’ace yake,, daga nanma kowa yakama gabansa.
Agidan su sopy uncle kabeer yace” wlhy ni abunma ganinsa nake tamkar a mafarki,, dama akwai iyaye irinna Abdul??
Baban fareeda yay murmushi abba akwaima wad’anda suka fisu,, ni tun ranar da aka kawo kud’in auren fareeda na fahimci ko mai,, dan haka daga baya na yi bincike,, nagano Abdullahi fareeda zata aura.
aunty Nafisa tace” amma baba kayi shiru baka fad’awa kowaba??
Baba yace” hakane Nafisa fad’ar fashida wani amfani, tunda fareedar yakeson aure, dan haka ina mai gargad’inku kada kowa yad’auki wannan abin da zafi,, mutaya safiyya addu’ar samun lfy kawai, dakuma fatan ALLAH yabata miji nagari wanda yafi Abdullahi bawai dukiya nake nufiba,, A’a wanda yafishi k’yawawan halaye.
Kowa ya amsa da to,, yace” kukuma yakamata kushirya kutafi gida jenku,, tunda sunce yau zasu sallamo safiyyar daga asibiti.
“Suka amsa da to baba”
Da daddare aka sallamo safiyya, koda sukazo gida wanka kawai tayi tasha shayi da magani ta kwanta, dan akwai maganin barci aciki,, baba yace mai sunan baba!! miye likita yace gameda ciwon nata?? Uncle kabeer yaja numfashi,, yaya!! likita yace sopy tasamu matsala a zuciyarta,, dan tadad’e acikin damuwa da yawan fad’uwar gaba,, saikuma fad’uwar datayi shekaran jiya tayitane sakamakon jin abinda bata zataba,, amma yace” idan aka cigaba da lallashinta da yimata abinda zai sakata farinciki to zata dawo kamar yanda take,, inkuma bahakaba zuciyarta zata kamu sosai.
” inna tafashe da kuka,, ALLAH sarki safiyya kekuma taki jarabawar kenan?? Baba yace” hajara ba kuka zamuyiba addu’a safiyya kawai take buk’ata daga garemu.
Uncle kabeer yace”gsky ne wannan, nan dai suka cigaba da tattauna matsalar.
Yau da gobe ahankali jikin safiyya yafara sauk’i dan tana samun kulawa wajen baba da inna dakuma uncle kabeer,, yayyen tama suna bata kulawa,, haka mamar fareeda kullum saita shigo dubata itada baban dasu yaya lawan,, jikinta yana yin k’yau saidai yanzu bata son yawan magana,, ko hayaniya, ko fira ake akusada ita saidai kallo,, koda yaushe tana kwance, sallah ce kawai ketashinta abincima bata son ci,, sai uncle kabeer ya lallab’ata.
” lokuta da dama idan ta tuna cin amanar da AMINIYARTA tayi mata da SAURAYINTA wanda take matuk’ar SO sai kaga hawaye nazuba akumatunta,, takanyi bak’in cikin kub’ucewar mutane biyu masu muhimmanci agareta alokaci d’aya,, sun barta alokacin datake buk’atarsu fiye da kowa,, sun tafi lokacin datake buk’atar abokin shawara,, sun barta lokacin datake buk’atar mai d’ebe mata kewa,, sunyi nisa da ita alokacin datake buk’atar mai share mata hawaye,, tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi😭, nima bansan lokacin danawa hawayen suka fara zaryaba, dan nasan zafin rabuwa da masoyi,, saidai nawa mutuwace tarabamu, bakamar na safiyyaba da yana raye yayi nisane da’ita saka makon makircin AMINIYARTA.inna tashigo d’akin da sauri danjin kukan safiyya,, ta rungumeta ajikinta tana lallashinta,, haba safiyya kiyarda da k’addara mana alokacin data riskeki,, ki godema ALLAH mana alokacin daya jarabceki,, karki jahilci kanki kiyi hak’uri irin hak’urin manyan ANNABAWA mana ayayinda jarabawa ta riskesu,, inkikai hak’uri sai ALLAH yayi alfahari dake domin yana tare damasu hakuri,, indan kikayi hak’uri sai ALLAH ya musanya miki da mafi alkairi.
Sopy ta kuma rungume inna tana fad’in to inna zan daina,, kawai abinne yana bani mamaki,, wai fareeda da’ita aka had’a baki wajen cin amanata,, dama tuni tasan dukkan matsalata amma tarufeni,, duk halin k’unci da yawan damuwa dana shiga fareeda tanada masaniya akai,, shiyyasa kullum saitace zataje ta tanbayo miyasa Abdul yadaina zuwa wajena,, kullum da irin tsarin da zata yi min,,, ashe itace kecin dunduniyata ban saniba,, ashe fareedace tushen damuwata tafad’a tana rushewa da kuka,, haba AMINIYATA miyasa kika aikata?? Miyasa kika yimin haka?? Miyasa kika zama mai irin halin muna fukai??? Miyasa saida nayarda dake kikaci amanata??? Miyasa kika zab’i mu rabu akan saurayi????
Inna tace” kinga ya isa haka kiyi hak’uri. Sopy ta d’ago tana kallon inna, wlhy inna ba rabuwa da Abdul bane matsalata nafi jin ciwon rabuwa da fareeda,, domin zuciyata da ruhina suna matuk’ar k’aunar fareeda,, itace K’AWA tafarko da zuciyata ta yarda ta ita harta zama AMINIYA mafi soyuwa a zuciyata,, ashe zata rabuda ni akan saurayi,, zata raba tsantsar SO da k’auna da zumincin dake tsakaninmu,, ashe zata saka shakku da fargaba azukata guda biyu da tsantsar yarda ta cikasu?? Ashe duk so da k’aunar dana nunama Abdul da fareeda su babu abinda suka ajiye mini sai tari yaudara da cin amana??? Nikam nayi asarar AMINIYA da miji mafi soyuwa azuciyata,, inna banyi tunanin sake maye gurbin wad’annan mutanen biyuba arayuwata,, domin nayi asarsu alokacin danafi buk’atarsu.
Inna tace” kiyi hak’uri safiyya ki barma ALLAH shine mai kowa da komai,, inkinyi hak’uri zai musanya miki da wad’anda suka fisu,, kedai ki kasance mai gsky aduk inda kika tsinci kanki,, da ace kekika cutar gara ace ke aka cutar kinjiko???
Sopy tad’aga kai tana hawaye, insha ALLAHU inna karkiyi shakku akaina,, zan kasance kamar yanda kika buk’ata.
To shikenan yanzu dai ki kwantar da hankalinki kibar yawan damuwa kinga likita yahanki tunani saboda ciwonki,, muma bamu son mu rasaki.
” to inna zanyi k’ok’ari insha ALLAHU kodan hankalinku ya kwanta.
Inna tayi murmushi to shikenan auta ta.
Sopy tace” inna ina uncle yake??
Yaje siyo miki maganinki yanzu zai dawo,, wlhy inna bana son uncle yatafi yanzu dan ina jin dad’in zama dashi.
To aiko saidai hak’uri auta kinga dole ya koma wajen aikinsa,, dan kinga bikinsa shima yanata gaba towa.
Sopy tace” hakane kuma inna, ALLAH dai yakaimu lokacin.
Inna tamik’e tana fad’in amin autata……………..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 14~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣4⃣🔸🔶
………………Safiyya tasamu sauk’i Dan jikinta yayi k’yau saidai tayi matuk’ar rama,, fuskarta tayi wani fayau,, bata zuwa Ko ina koyaushe tana gida tareda innarta,, uncle kabeer yasaya mata waya mak’yau,, yabud’e mata watsapp da facebook duk dan surink’a d’ebe mata kewa,,, indan baya aiki saisuyita hirarsu a watsapp,, yabama budurwarsa nomber ta,, ta sakata a group’s 2 dayawa NA Novels dana hirar duniya dana addini irinsu HANYAR TSIRA dan wannan gidan bayin ALLAH suna k’aruwa dashi sosai ALLAH yabiya masu tunatar damu aduk inda suke.
“” irin wad’annan abubuwane sukan d’auke mata hankali bata samun lokacin tunani,, data ta wata 1 uncle kabeer ke siya mata,, shiyyasa batada matsalar MB, saidai takanyi kewar fareeda, Dan tunda suke basu tab’a yin kwana biyu basa tareba,, Dan haka duk kewarta ta addabeta, takan kwaso pictures d’insu taita kallo tana tuna baya,, duk abinda yashafi fareeda sopy ta maidashi wani madubinta,,sai dai idan inna taganta ta gurgiza kai kawai amma tana matuk’ar tausayin ‘yar tata.
Su fareeda anata shan amarci,, komai yanata tafiya yanda takeso,, Abdul yana tattalinta komai takeso shi yake mata,, inagama ansamu rabo dan naga tayi wani fari,, kokuwa duk amarcinne oho dai,, mudai ‘yan kallone.
Yau sopy anacikin farin cikin zuwan uncle kabeer,, sai hidimar girka masa abinci takeyi, inna taji dad’in yanda taga tasaki jikinta yau tana walwala, dan tunda abinnan yafaru basa ganin dariyar sopy,
Amma yau daka kalleta zaka gano farinciki a tareda ita.
“Sai wajen k’arfe biyu uncle kabeer ya iso, shima yayi farincikin ganin yanda jikin sopy yayi k’yau saidai kawai ramar datayine, tana zaune kusada uncle kabeer dake cin abincin data dafa masa,, takalle sa uncle kana ganin baba zaiyyarda da k’udirinmu kuwa? ?? Uncle kabeer ya ce, “aii dama tunda naga farincikinki ya yauta nasan akan maganar damukayine”, karki damu zanyi iya k’ok’arina tayanda zai fahimceni, insha ALLAHU zai amince.
Sopy ta ce, “danayi farinciki mai tarin yawa uncle, nasan hakan zaik’ara nisanta zuciyata daga damuwar data tsinci kanta.
Uncle kabeer yay murmushi hakane my daughter! Insha ALLAHU nan gaba kad’an komai zai zama labari, kedai kiyi k’ok’arin cika min burina,, dan yanzu zaki shirya muje makarantarku mu amso exam d’inki.
Cikin zumud’i ta ce, “angama my dear uncle! Inna dai tanajinsu bata tankaba, dan bata fahimci inda zancen nasu yadosaba.
Sun karb’o sakamakon jarabawar saidai sopy batayi k’ok’ari a WAEC nataba.
Uncle kabeer ya ce, “sopy ya akayi haka tafarune?? Sopy tad’an sosa gefen wuyanta, wlhy uncle! Sannan ina cikin wani yanayine!!
Uncle yay murmushi sannan kina cikin shauk’in son Abdul ko?? “Tasa hanu ta rufe fuskarta tana fad’in “kai uncle”.
Ya ce, “i, mana hakane”, amma babu damuwa saimuyi amfani da NECO kawai, dama mun gama magana da abokina,, shima malamine a “B,U,K”, nasan zai taimaka mana sosai.
To uncle nagode sosai ALLAH yabiya ka kaidai!! Yay murmushi to amin sopy na.
Sai dare uncle kabeer yasamu zama da baba, bayan sun gaisa ya ce, “yaya dama maganar yarinyar nan ne yakawoni.
Baba ya ce, “wace yarinya kenan??
Uncle yagyara zama, yaya yarinyar dazan aura!
Baba ya ce, “to miya faru da ita??
Babu komai yaya babanta ne , dama ya rok’eni akan dan ALLAH nabarta ta k’are karatunta, tunda saura shekara d’aya kacal, to nima sainaga hakan zai taimaka minma na k’arasa gidana, amma yaka gani??
Baba yaja numfashi, to idan haka yafi alkairi ALLAH ya tabbar abba, mudai kullum addu’ar fatan alkairi muke maka, da fatan gamawa lafiya, dan kai yaron kirkine, nak’agu naga ka ajiye iyali kaima.
Uncle kabeer yay murmushi karka damu yaya insha ALLAH zanyi adai k’ara tayamu da addu’a,, sai dai yaya bayannan inada wata buk’ata awajenka!! Inhar ban takuraka ba??
Baba ya murmusa karka damu mai sunan baba fad’amin buk’atarka indai batafi k’arfinaba zan yi maka ita.
Uncle ya ce, “batafi k’arfin kaba yaya! ” dama dan ALLAH ina son kayarje min namaida safiyya makaranta, dan wannan zaman nata bashida wani amfani, karatu zai matuk’ar taimaka mata wajen mance abubuwan dasuka faru abaya………………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 15~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣5⃣🔸🔶
……………Baba yaja numfashi, abba ban katse maka hanzariba, amma da dai anhak’ura da karatunnan hakanan, tunda ansamu na zaman duniya, sai kuma ayi aure.
Uncle ya ce, “hakane yaya, amma yanzu naga bawani tsayye bane ahannu, amma dazaman banzar gara ace karatu takeyi,, kotana karatun tasamu miji saitayi aurenta.
Baba ya kalli inna, to hajara kinji abinda abba ya ce, “amma ya kika gani??
Inna tai dariya, malam nikam banida shakku akan babnmu, dan haka kabashi dama, nima inaga hakan zai taimakawa safiyya wajen mance wasu abubuwan.
Baba ya ce, “to akira safiyya muji ta bakinta”
Uncle yay murmushi karka damu yaya indai safiyyace mungama magana da’ita.
To, to, kace dama saida kuka gama shawararku sannan aka tuna damu! Dariya sosai uncle yakeyi “cikin dariya ya ce, “A’a yaya mu mun isa; nan dai sukayita hirarsu da wasa da dariya.
TUNATARWA:- inaso naja hankalin iyaye akan ilimin ‘ya’yansu, mafi yawan iyaye sukan d’auki ilimin ‘ya’ya mata ba’abu mai muhimman ciba,, ni anawa ganin ilimin d’iya mace yafi na kowanne muhimmanci, karku manta uwa itake bada tarbiyya, kuma yara suna tashi ne da harshen mahaifiya, kunga kuwa ilimin d’iya mace yanada muhimmanci matuk’a,, dan zata zama foundetion na ilimin ‘ya’yanta,, wannanma kad’ai ya isa yazama abu mai muhimmanci ga bawa mace ilimi,, sannan ko a gidan aure zakaga mace mai ilimi tafi kowa iya rik’e miji da tattalinsa,, dan haka mubama ‘ya’yanmu mata ilim addini dana zamani,, ALLAH YASA MU GANE.
UNCLE kabeer yanata k’ok’ari wajen nemawa sopy Admission a (BUK ) da taimakon wani abokinsa aka dace,, dakansa yaymata komai.
To ALHAMDULILLAH komai dai ya kammala,, ranar monday sopy zata fara zuwa makaranta,, 😅dan haka tafi kowa fareenciki,, harta k’agara ranar tazo.
Su dai su inna sunata yima sopy nasiha, akan tazama mace tagari mai rik’e mutuncinta da darajarta,, idan ance ‘ya mace taje tayi ilimi, bawai ananufin taje tayi iskanciba,, dan dayawa ‘yan uwa mata idan suka samu saken zuwa nema ilimi,, sukan d’auka sun samu wayewa daganan sai afara iskanci,, kaiconmu wlhy ‘yan uwana mata, har yanzu wasunmu basu fahimci miye wayewaba dayawanmu muna jahiltar wayewa,, ballagar mace wadda ta maida kanta akuya ba ita bace wayayyiyaba,, wanna itace bagidajiya jahila,, mace mai kamunkai da girman kai awajen maza marasa tarbiyya,, mai adiini itace wayayyiyar mace, kuma suma mazan sunfi sonta,, zakaga duk iskancin namiji da mugun halinsa yana burin auren mace tagari, kodashi bai kasance miji nagariba, to ‘yan uwana ya kama ta mu gyara, kodan cin ribar rayuwarmu, ALLAH dai yasa mugane.
Su inna dai sunyima sopy nasihohi masu ratsa jiki da zuciya,, sunkuma yimata fatan alkairi da samun nasara arayuwa.
Saboda yanayin rayuwa,, sai uncle kabeer ya nema mata gurin zama a hostel, dan kar wataran kud’in mota ya gagareta,, itama hakan yayi mata dad’i, dan zaman anguwar yana d’an sata tayita tuna wasu abubuwan,, kuma idan tafita sai mutane suyita kallonta,
wasuma har nunata sukeyi, to, tasan idan tayi nisa da anguwar zata sake, ta kuma manta da abubuwan dasuka faru abaya.
Ku kasance dani akoda yaushe, ina muku fatan alkairi ……………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
16~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣6⃣🔸🔶
………….Sopy ana makaranta, komai yana tafiya yanda takeso, sai dai tak’i sakin jiki da kowacce k’awa, duk da ana nuna mata anabuk’atar yin k’awance da’ita, bakamar wata zaliha, itadai sopy tana burgeta, sai dai sopyn tak’i bata fuskar dazata kusanceta, itakam sopy tana tsoron makirci irin nad’an adam ne, dan wadda ta yarda da ita, ta amincewa ita tafara saka mata shakku game da halayen d’an adam, wannan yasa take nisantar ‘yammatan makarantar, sai dai tadage tana fahemtar abinda ake koya musu, kuma yanayin tasiri arayuwarta da kuma alk’awarin data d’aukarwa kanta da uncle kabeer.
Yau tanada lectures d’in safe, dan haka ta tashi tayi shirinta, cikin siket da riga na atanfa jaa da kore, tad’akko fareen hijjabi har k’asa tasaka, tad’an fesa turare mai sauk’in k’amshi, dukda bawata kwaliya tayiba tayi k’yau, dan sopy tanada k’yau irin wanda in kacika kallonta zai k’ara k’ayatar dakai, dukda bak’ace bak’inta yanada k’yawun kallo, gata da jiki maik’yau, irin wanda mutane sukan kirashi karuwan jiki, dolene idan kaga surar sopy komin ustazan cinka ka k’yasa, dan haka koda yaushe takan sance cikin hijjab, saboda idan har tasaka gyale tafita sai tasamu samari samada goma sunce suna sonta, wasukuma kwarjinin ta yake hanasu furtawa.
Tafito kafad’arta rataye da jar jakka, tafiya take cikin nutsuwa kanta ak’asa, tad’an kalli agogon hannunta mai sauk’in kud’i, tad’an tab’e bakinta, kai barima nazauna anan tunda munada sauran lokaci.
Tana nan zaune, saitaga d’alibai nata saurin shiga aji,wasuma harda d’an gudu, ita dai kallonsu takeyi, amma batayi wani yink’urin tashiba, zaliha tak’araso tana fad’in “lallai safiyya kina ganin kowa yana k’ok’arin shiga aji, amma ke kina zaune, yau munada lectures da “uncle G” kuma idan har yariga ki shiga aji tofa “k” bazai barki kishigaba……tak’arasa fad’a tana k’ok’arin tafiya, kafin sopy tace,”wani abu tuni zaliha takai k’ofar class.
Sopy tamik’e itama tanufi class d’in sai dai kash tana kaiwa ga k’ofar ajin shikuma malamin da zaliha takira uncle G yashiga.
Sopy ta tsaya cak abakin k’ofa, ta daure ta ce, “malam good morning!
Saida yay mata wani kallo na rainin hankali, sannan ya ce, “morning! da ganan yaja bakinsa yay shiru.
Sopy tai tsaye abakin k’ofa domin bai bata izinin shigaba, tana nan tsaye wasu ‘yammata suka k’araso suma, d’aya acikinsu ta ce, “A’isha yaukam munzo arashin sa’a uncle G!! yarigamu shiga, wadda aka kira A’isha ta tab’e baki, ki ce, “sarkin ‘yan girman kai yashiga, nikam wannan malami bansan miya d’auki kansaba???
Sopy dai tana tsaye tana jinsu, sai dai zuciyarta cike da tambayoyi, akan toshi wannan malamin wayeshi??? Ita dai yau kwananta hud’u a school d’innan, amma bai tab’a shiga a jinsu ba sai yau, to shikuma waye????
Ta maida kallonta gareshi, yana sanye da wani farin yadi mai laushi, rigar da kad’an ta wuce d’uwawunsa,k’afarsa sanye da bak’in takalmi,hakama hannunsa yana d’aure da bak’in agogo,, idanunsa cikin farin gilas siriri,, dukda dukannin kayan dake jikinsa bawasu masu tsada bane, amma shikam sun zauna dai dai da tsarin halittarsa.
Dogone amma ba canba, amma tabbas baza’a kirashi gajereba,bak’ine amma mai haske, yanada manyan idanu farare tas, wad’anda saboda haskensu har akan iya ganinsu tacikin kwalbar dake idonsa👓, dan har wani k’yalli sukeyi, kumatunsa zagaye yake da bak’in gashi sid’ik wanda ake kira saje, hakama bakinsa zuwa gemunsa shima zagaye yake da bak’in gashin, kansa babu suma mai yawa dan da’alama yanayin aski saidai ba irin tal tal d’innanba, domin akwai gashi kwance akansa bak’i sid’ik yasha mai sai k’yalli yakeyi, yanada d’an jiki dankuwa baza’a kirashi siririba,amma jikinsa yay masa k’yau.
Yad’an juyo yana kallon su sopy dake waje, yaji ajikinsa tabbas ana kallonsa, sopy tayi saurin d’auke idonta daga kallonsa, shima saiya d’an tab’e baki yacigaba da bawa d’alibai darasi akan English domin shi malamin turancine.
Yagama lecture d’insa, harda yin test, yazo fita sopy tamatsa gefe tabashi hanya, ko kallon inda suke baiyiba ya wuce abinsa, d’aya acikin ‘yammatan nan uku taja tsaki, kai wannan gay d’in akwai rainin hankali saikace d’an wani da wata.
Bayan fitarsa suka shiga, class suka cigaba da karb’ar sauran darasi.
Sopy zaune ajikin wata bishiya, tana duba books nata, dan bitar abubuwan da’akai musu, zaliha tazauna a kusada sopy tana fad’in ‘yar uwa dama kinanan?? Tun d’azu nake nemanki!!
Sopy tajuyo tana kallonta, e, ina nan, inad’an yin karatune.
Hakan yanada k’yau zaliha tafad’a tana murmushi.
Sopy ta maida kanta bisa karatunta, saikuma ta d’ago ta ce, “yauwa zaliha dan ALLAH bani labari gameda “uncle G” malamin d’azu da safe.
Zaliha ta gyara xama cikin zumud’i, dan ganin sopy yau takulata,, ta kaikaice tafara zabgo Zance tamkar ‘yar jarida.
Nidai ayanda nasani sunansa malam yuseef Husain Ahmad, Gurum amma anfi kiransa da uncle G, malamin English ne, mutum ne mai aji, baya son wasa, bakuma ya wasa da kowace d’aliba, dan baya sakarwa kowa fuska, inhar kayi sake yashiga aji kafin kashiga, tofa ranar bakada rabo amasu samun darasinsa.
Yanada ilimi fiye da tunanin mai hankali, dan ayanda naji, nan makarantar yayi, yafita da face class na Resold dan haka suka d’auke shi aiki, zan iya ce miki iya abinda nasani kenan gameda tarihinsa.
Tad’anyi dariya k’awata kar dai kema kin kamu da son sa?? dan wlhy rabin ‘yammatan makarantar nan duk son sa sukeyi,, harso suke yayi musu magana,, amma shi kam ko kallo basu isheshiba, shiyyasa suke cemasa mai girman kai.
Sopy ta harareta kekam na lura ke ‘yar rainin hankalice,, daga tanbayarki tarihin mutum saiki min fassara, to kuwa idan kinason mu shirya dake kidaina min irin wannan.
Ganin ran sopy yab’aci, zaliha tashiga bata hak’uri.
Fareeda zaune ta zabga uban tagumi babu abinda yake damunta sai tunanin sopy, ba k’arya tayi missing d’inta, sai dai haryanzu bata tab’aji azuyarta ta cutar da sopynba, bare tayi nadamar Hakan, Abdul yay kissing d’in kuma tunta, tai saurin juyowa tana kallonsa, ya ce, “miye damuwarki?? Tad’an yatsina fuska ta ce, “sopy nake tunani wlhy nayi missing d’inta my love!
Abdul yad’an tab’e baki, yana mik’ewa kinga wannan matsalarki ce, ni yanzuma tashi ki kawo min abinci dan yunwa nakeji wlhy,, fareeda ta harareshi oh hakama zakace matsalata ce???
To inada matsala da damuwarki ne?? Cikin jin haushi fareeda ta ce, “A’a.
Ya ce, “to, kuma, zakiji haushina??
Fareeda dai taimasa banza tafice domin kawo masa abinci………………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 17~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣7⃣🔸🔶
…………….yauma duk k’ok’arin sopy nagujema tarkon uncle G!, amma saida ta fad’a, dan kuwa harya shiga aji, tad’an cije leb’enta, dan bak’in ciki, tabishi da kallo yana tsaye gaban allo, yauma cikin manyan kaya sai dai yau shaddace mai ruwan k’asa, d’inkin dai tamkar na ranar, dan rigar itama bata wuce d’uwawun saba, amma yau babu glas.
Sai da yagama lecture d’insa sannan ya ce, “kowa yashirya yin test, kuma yau har nawaje su shigo.
Wannan magana tasa tabawa mafi yawan d’aliban mamaki, domin duk yanda kuke dashi inhar yarigaka shiga aji tofa bazaka shigoba, bare idan zayyi test, amma yau dakansa yabuk’aci su shigo.
Bayan shigowar su sopy da ragowar makararru, ya gabar musu da tanbayoyin.
A hankali yake takawa cikin class d’in bakajin motsin komai sai takunsa, kowane d’alibi ya duk’ufa wajen aikinsa, k’amshin turarensa duk ya gauraye class d’in, yak’araso dai dai inda sopy take zaune, yazuba mata idanu dan ganin batayi wani yunk’urin rubuta wani abubama.
Jin antsaya akanta yasata d’agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, sopy tai saurin janye nata idon dan baxata juri kallon saba, jikinta asanyaye tamaida kanta ga takarda.
Shikam wani abu yaji yasoki kansa harzuwa babban d’anyatsan kafarsa, yarintse ido yabud’e, ya salam yafad’a tare da jan ajiyar zuciya, ya wuce abinsa yana cigaba da zagaye d’alibai dan kar suyi satar amsa.
Lokacin daya basu yana cika yakarb’e, yafita abinsa.
Zaune yake a offece yana duba takardun jiya, dasu sopy sukayi teat, har yazo kan wata takarda danaga ya kurama ido, yajuyata yak’ara juyawa, sai kuma yak’ara maimaita sunan SAFIYYA IBRAHIM KABEER, tabbas yarinyar ce yafad’a afili, domin lokacin dayake zagaye sunan daya gani akan takardar gaban ta kenan, ya cire gilas d’in idonsa, yakuma murza idon dan tabbatar da abinda yagani shin gskne kokuwa idanunsane suke masa gizo??
Amma yasan ba gizo bane, domin sopy ita kad’ai tazauna, bare ya ce, “wajen wani ta kwafa”.
Yacigaba da juya takardar yana kallo,, aka kwan kwasa kofar domin neman izinin shigowa.
Ya ce, ” who is that?
Daga can akace nine.
Yay dariya come in, my gay!.
Abokinsane malam faruk, shima lecturer ne a makarantar, yabashi hannu suka gaisa, ya kalli takardar hannunsa, my man! lfy naga kanata juya takarda??, ko watace ta ce, “tana sonka??, dan na sanka akwai farin jini.”
Uncle G! Ya kalleshi aii idan wannan nema da sauk’i.
Malam faruk ya gyara zama to minene yafaru??
Kasan wani abu?? “A’a saika fad’a,, wato wata yarinya ce tabani mamaki wlhy, jiya namusu lecture, to sai takasance acikin makararru, yauma haka, amma abinda yabani mamaki nayi musu test , saikuma ta amsa mini komai dai dai, yamik’a masa takardar, karb’a kagani.
Malam faruk yakarb’a yana dubawa, ya jin jina kai , lallai wannan yakai ayi mamaki, dukda akwai mutane masu kwazo da kwakwalwa aduniya,, kai kankama abin misaline, dan haka karkai shakku.
Uncle G! Yad’an tab’e baki yana fad’in hakane abokina.
Sopy suna zaune itada zaliha a kofar wani class, saiga uncle G ! Yafito daga ajin, hannusa d’auke da littatafai, suka gaidashi sau d’aya ya amsa musu, har yad’an gotasu saikuma ya dawo, litta taffan hannunsa ya mik’awa sopy, cikin muryarsa mai dad’i ya ce, ” ki kaimin offece d’ina.
Cikin rawar murya sopy ta ce, “aii ni bansan offece d’inkaba, yad’an juyo ya kalleta, dan har ya fara tafiya, ki tambaya mana, taji yafad’a ya wuce abunsa.
Sopy takalli zaliha ta ce, “zaliha plz idan kin sani ki rakani mana? Zaliha ta rik’e hab’a rufani ki sayani sopy, sai dai na nuna miki, dan wlhy bakowa yake shiga wannan offece d’inba.
Kamar ya bakowaba ? To dan me??
Saboda maishi baya bari, kinga kina k’ara b’ata lokaci muje na nuna miki.
Sopy tabita tana mamakin yanda yawancin students a d’in makarantar suke shakkarsa,, dukda school d’in ta kasance university gidan ‘yanci.
Da wannan tunanin tak’arasa offece d’in da zaliha ta nuna mata,, a tunaninta baya nan dan haka ta dannakai kawai abinta batareda neman izinin shigaba,, tai sauri jada baya dan ga nin sa zaune akujerarsa ya d’ora k’afarsa saman tebir d’in gabansa, yana latsa waya.
Ya d’ago yana kallonta idanunsa sanye cikin glas, cikin rawar murya ta ce, “sorry ser bansan kana cikiba.
Baice mata komaiba , sai dai ya nuna mata tebir d’in dake gabansa, alamar ta ajiye.
Ta ajiye ta juya zata tafi,, sai taji ya ce, “waya baki izinin tafiya?? Ta juyo da sauri tana kallonsa, dan batai zaton da ita yakeba, amma saitaga shima ita yake kallo, tadawo ta tsaya, ya sauke k’afafunsa kasa, ya ce, “bismilla zauna”.
Jikin sopy a sanye ta zauna zuciyarta cike da mamakin wannan irin karfin hali haka.
Yakai tsawon minti biyar bai sake bi ta kanta ba yanata latsa wayarsa, saida ya mula Dan kansa, sannan yad’ago yana kallonta ya ce, “SAFIYYA IBRAHIM KABEER ko?
Dukda ba yau aka fara kiran cikakken sunantaba kamar haka , amma saitaji yau sunan yay mata daban tamkar banata ba, domin kuwa ya iya fad’ar sunan,, kamarma yafi kowa iyawa ………………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 18~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣8⃣🔸🔶
……………ya ce, “koba “k”!, baceba???
“Tai saurin fad’in nice ser.”
Ya jinjina kai tare da janyo wata takarda yamik’a mata, waye ya rubuta miki wannan????
Sopy takarb’a tana kallon takardar, test d’in ranarce aii, tad’an gyara zamanta, bawanda yarubuta min nice nayi da kaina.
Yad’an tsura mata idanu wannda yasa dole tayi k’asa da kanta domin kunya, shikuma ya murmusa, Karo na farko dana tab’a ganin murmushin sa, yacigaba da kallon takardar Kenan yanzu idan nace ki sake rubuta min zakiyi kamar haka??.
Sopy ta jin jina kai, ta ce, “insha ALLAHU ser”.
Ya ce, “good”, takarda da biro yabata, nabaki minti goma sha biyar.
Tad’an kalleshi saikuma ta kauda kai, azuciyarta ta ce, “idan kasaba rainawa d’alibanka hankali, to nikam bazan amince ba, taja takardar tana rubuta amsoshin tanbayoyinsa, tagama acikin minti goma.
Yad’an kalleta cike da mamaki, itama kallonsa take, ya danne mamkinsa dan karta kawo masa raini, ahankali ya furta zaki iya tafiya.
Sopy ta mik’e batare da ta tanka masaba, ta fice abinta.
Yabita da kallo afili yafurta miskilanci!!, humm kunji masu karatu shiya manta da nasa miskilancin, ahankali ya kwanta da bayansa ajikin kujerar, hannunsa rik’e da takardar data rubuta yanzu, yaja ajiyar zuciya, ya sumbaci takardar ya lumshe fararen ida nunsa masu suffar ganye.🍃
Narik’e hab’a dan mamaki, marak’isiyya ta zungureni aunty bily mikenan??? Naja numfashi wlhy nima bansaniba marak’isiyya, saidai musa ido akansa dan gano miye sirrin zuciyarsa,, amma wannan irin subba da yayma takardan nan aii abin tanbayane?? Marakisiyya ta ce, “lallaikam aunty bily.
Sopy na fitowa zaliha ta tareta, sopy miya faru?? naga kin dad’e, Sopy ta harareta to uwar ‘yan son gulma babu komai.
Plz dan ALLAH ki fad’a min nasan hakanan banza bazaki dad’e a offece d’in uncle G! ba, sopy tai d’an tsaki to bawani abubane test d’in jiya yasani na sake.
Ban ganeba??
Sopy tai gaba aii dama ke baki ganewa.
Zaliha tabiyota tana naci, dole sopy tagaya mata yanda sukayi,, zaliha ta ce, “lallai abin mamaki uncle G! kenan, kya k’ara gani indai shine.
:::::::::::::::::::::::::::::::♡ yau takasance alhamis sopy tana Zaune da ‘yar kazaginta zaliha suna duba wani book, gurin akwai yawaytar d’alibai suna shan iska, k’alilanne suke karatu, domin yawancinsu duk tare suke da samari suna hira, wani gay yak’araso inda suke, yay musu sallama zalihace kawai ta amsa amma sopy ko kallo bai ishetaba kanta yana ga littafai.
Saurayin ya zauna kusada zaliha, yayinda sopy ta mik’e ta canja gurin zama,, saurayin yabita da kallo, zaliha way yaushe k’awarki zata wayene??
Zaliha ta tab’e baki babu rana jamilu! dan ita ra’ayinta daban dana mutane.
Ya jinjina kai yana fad’in tofa, jami’a gidan bankashi.
Zaliha ta kalleshi ta k’yalk’yace da dariya suka tafa da gayen.
Sopy dake kallonsu taja tsak’i irin wannan abubuwanne yasa bata sakarma zaliha fuska dan ta kula ‘yar komai da ruwanka ce, tamai da kanta ga karatunta.
D’alibai sunata shan hirar soyayya agurin, sai sopy tazama saniyar ware, dan bata bama kowane saurayi fuskar kusantar taba,, batada abokin hira sai littafi ko waya, saikuma idan sun had’u da zaliha, ko kuma tayi tayin chatting abinta.
Uncle G! Yabi dukkan d’aliban da kallo cikin bak’in ciki, shikam irin wannan halayyar bata burgeshi, domin aganinsa rashin tarbiyya da kamunkai ne yake kai d’aliban maida makaranta wani lambun masoya, yad’anja tsaki tareda k’ara jingina a jikin motarsa, karaf idanunsa akan sopy dake gefe tana karatu, Yay d’an murmushi gsky tana k’ara burgeshi, dan yanason mace mai kamunkai, da rik’e mutuncin kai, ya lura yarinyar tanada tarbiyya dan baitab’a ganinta da wani saurayiba, ya dad’e yana saka mata ido amma haryanzu baiga wani abun aibu a tareda itaba,, saidai yakula muskilace tafad’a aji.
Yazo zai wuce duk yawancin d’aliban suka shiga gaidashi,, amma ita hankalinta nakan littatafai, ko kuma tanajinsu tadai sharesune oho.
Shima ya wuce batareda ya kuma kallontaba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, karatu yana tafiya yanda sopy ke buk’ata, domin tana fahimtar komai dallah dallah, daga ranar kuma bata k’ara yarda tamakara lecture d’in uncle G! Ba, da duk wani malami,, dan ta zauna ta tsarama kanta lokaci tayanda zai amfaneta harma ya amfani waninta,, matsala d’aya tafara fuskanta shine yanda samarin makarantar suke matsa mata, itakam ayanzu ta tsani halin maza dan tundaga abinda Abdul yay mata tayima maza k’ud’in Goro, tana matuk’ar bak’in cikin namiji ya ce, “yana sonta, amma tana iya bakin k’ok’arinta domin kaucewa dukkan wani namiji, ta maida hankalinta akan karatunta gaba d’aya,, tana kuma k’ok’arin mancewa da abinda ya faru a baya, dukda har yanzu zuciyarta tana k’aunar fareeda, idan tatunata takanji matuk’ar kewarta da begen ganinta, haka son Abdul yana nan azuciyarta amma tana addu’ar ALLAH ya yaye mata sonsa, yakuma mantar da ita shi.
Su fareeda amare, ana gidan Abdul ana shan amarci, sai dai tana fuskantar matsalar yanayin zaman takewar gidan, gidane mai matuk’ar yawa, wanda yatara iyaye da ‘ya’ya da jikoki, ga matan yayyensa suna shiga rayuwarta,, tagayawa Abdul amma yak’i d’aukar wani mataki, ga yaran gidan basuda wata cikakkiyar tarbiyya, dan kwata kwata yaran basa respert d’in na gaba dasu, sun raina yayyensu da matan yayyen.
Fareeda tafito daga kichin hannunta d’auke da kula, Abdul yashigo ransa ab’ace, tad’anja baya dan ganin yanda yafad’o babu ko sallama, ya wuceta batareda ya ko kalletaba, asanyaye tabishi zuwa d’aki, yana kwance akan gado yarufe fuskarsa da filo, tasa hannu tacire filon tana fad’in my love! bakada lafiya ne???
Cikin matuk’ar masifa ya ce, “asibiti ne ni.
Tad’anja baya tana fad’in ALLAH yabaka hak’uri.
Ya maida kansa yana fad’in kayane nad’e gammo na d’ora miki, yaja tsaki.
Fareeda ta zauna jagwab saman kujerar madubi, ta rintse idanu tana fad’in na shiga uku kardai ace Abdul zai fara juya min baya, lallai dolene na nemi zuwa gidan aunty sadiya………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 19~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸1⃣9⃣🔸🔶
…………..zaliha tak’araso dad’an gudunta, tana fad’in kai sopy shine kika taho kika barni?? Sopy tajuyo tana kallonta, ato naga ke kwalliyace damuwarki , bayan kinsan wannan d’an hayak’in shine zai farayi mana lecture yau.
Zaliha ta ce, “to muje aii akwaima sauran lokaci.
Jikin wata bishiya suka zauna kafin lokaci yayi.
Zaliha ta zunguri sopy, sopy! Sopy!! Ga mutuminki!!.
Sopy ta juyo, waye kuma mutumina? Karaf idanunsu suka had’u a karkashin inuwa d’aya,, tai saurin janye nata dan ganin wajensu ya nufo.
Wad’anda suke wajen suka shiga gaisheshi, yak’araso cikin tak’ama yana sanye da bak’in wando da jar riga, sai zabga k’amshi yakeyi, sajen nan ya kwanta luf luf akan k’yak’yk’yawar fuskarsa, azuciyar Sopy ta ce, “yaukuma k’ananun kaya aka saka”.
Jin zaliha tana gaidashi sai itama tadawo hayyacinta, ta gaidashi itama ya amsa da lfy, kowa yazuba musu ido, shima ganin haka sai kawai ya wayance da tambayarsu wacece sakina musa?? Zaliha ta ce, “uncle G! Muma bamu santaba, sopy ko bama ta tankaba, yajuya yana tambayar sauran d’aliban dake gurun, suma sukace basu santaba, yajuya yatafi, yana maijin haushin kansa, way sai yaushe yarinyar nan zata fahimci inda nadosa ne?? Ko sotake saina furta mata da bakina ne?? Yad’anja k’aramin tsaki, yarinyar nan miskilancin tafa yayi yawa, gashi sonta yay masa shigar sauri, batareda ya shiryaba, ya lumshe manyan idanunsa masu suffar ganye🍃, ya salam! Yafad’a tareda fitarda huci daga bakinsa.
Office yakoma yazauna, yajingina bayansa da kujera, idanunsa a lumshe tamkar mai barci.
K’ofar aka kwankwasa, ko motsawa baiyiba, saida aka buga sau uku sannan ya ce, “waye”?.
Wata zazzak’ar murya ta ce, “nice!!
Ya d’anja tsaki, ya ce, “kowaye ya shigo, ahankali aka turo k’ofar wata k’yak’yk’yawar yarinya fara tas tashigo.
Ya ce, “kowaye yafad’i abinda yakawoshi!, cikin rawar murya ta ce, “dama dadynane ya ce, “kazo ku gana idan kasamu lokaci.
Yabud’e fararen idanunsa wad’anda sukai d’anja ahanlin yanzu, sai dai har yanzu yana kwance a kujerar, yabita da kallon rainin hankali, miya faru yake nemana?
Ta gyara tsayuwa yanaso kuyi maganane.
Ya jinjina kai, toki sanar dashi yazo shi yasameni dan bana zuwa gidan kowa, kumama inada ayyukan yi masu yawan gaske.
Kuma indai akan maganar damukayi dakene, karma yafara zuwa wajena, ke kuma ina mai k’ara gargad’inki akan kifita hanyata, inko bahakaba zan cigaba da b’ata miki rai fiyeda yanda kike tsammani.
Yanuna mata hanyar fita, zaki iya tafiya dan inada aikin yi.
Ta marairaice fuska tamkar zatayi ihu, ta ce, “plz uncle G! ka daure muyi magana dan mu fahimci juna, wlhy ina tsananin k’aunarka, ka daure kasoni, nayimaka alk’awarin zan kasance yanda kake buk’ata, wlhy nayi maka alk’awari.
Uncle G! Yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad’an tsura mata idanuwa bahijja!! kamar yanda nafad’a miki tun farko, ba soyayya takawoni makarantar nan ba, bake kad’ai kika tab’a cewa kina sonaba, kuma suma amsar dana baki ita nake basu, ina mai baki shawara daki hak’ura kema kamar yanda suma sauran suka hak’ura,, kuduka bakwa cikin irin matar danake son aura, dan haka ina mai baki shawarar ki sama ranki hak’uri, daga yau kuma karki sake zuwa office d’ina, danni ba’a shigo min office saida dalili, kuma dalilin ma wanda yashafi karatu,musamman ma mata, ya nuna mata hanya zaki iya tafiya.
Taja numfashi idansu, har sun iya hakura da kai toni tabbas bazan iya rabuwa dakaiba, kaine mutum nafarko dana fara so kuma kaine na k’arshe, zan sanar da mahaifina yazo kamar yanda ka buk’ata, tunda kai kace bazakajeba, tana gama fad’a tafice abinta.
Shima tsaki yaja, yamik’e yana fad’ar ashe zaki mutu da son nawa kenan, dan har abada bazan sokiba, littatafai ya d’iba yafice shima, dan ya gudanar da lecture.
Ajinsu sopy yanufa, kamar yanda yasaba haka ya aikata, yahana makararru shiga, babu b’ata lokaci yashiga gudanar da lecture.
Sopy agaba take zaune, duk d’agowar datayi sai sun had’a ido da uncle G!, dan haka ma saita daina kallon inda yake, amma tanaji ajikinta har yanzu yana kallonta, kamar yanda yasaba yauma ya ce, “zaiyyi test.
bayan sun gama test yabisu yana karb’a, yazo karb’an na sopy, saida yafaki idon sauran d’aliban sannan ya ajiye mata wata takarda, ya karb’i ta hannunta, da ido ya nuna mata takardar daya ajiyemata, batace komaiba tad’auka kawai.
Bayan fitarsa kowa yafito, kafin ashiga wata lecture d’in.
Sopy batabi takan takardar uncle G! ba, dan bata d’auketa dawani muhimman ciba……………✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 20~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💕
🔶🔸2⃣0⃣🔸🔶
…………fareeda al’amura sun fara canja mata, dan yanzu Abdul yafara canja yanayin zaman nasu, ga masifar datake fuskanta wajan ummarsa, dan ummar Abdul masifafface, dukkan matan gidan tsoronta takeji, saboda masifarta.
Ta kula tunda likita ya ce, “tanada shigar ciki, tafara fuskantar matsala wajen Abdul, yafara nisantarta, Baya yin fira da ita yanzu, bakuma yadamuwa dasu kwana gado d’aya.
Lamarin yana damunta, gashi yahanata zuwa gidan aunty sadiya, ya karb’e wayarta tuni, yauma tana zaune ta yi tagumi, babu abinda take buk’ata sai nama,, tasan kuma Abdul bazai saya mataba, ga cikin nata mai shegen tsurfa da kwad’ayi, ta cije leb’e hawaye suka zubo mata akumatu, lallai idan har rayuwa tajuya mata baya to kuwa taga ta kanta, dan yanzu batada wanda zata tunkara tasamu sauk’i, aminiyarta tayi mata nisa, nisa kuma mai tarin yawa, tasan yanzu babu wadda sopy ta tsana kamar ita, garashin ‘yan uwa, ga rashin iyaye, tafashe da kuka, kuka take tamkar ranta zai fita, nikam na tab’e baki dan wlhy ko kad’an banji tausayin taba, na ce, “ni!, barima natafi wajen k’awata sopy, nagano muku takardar da uncle G! Yabata.
Sopy zaune akatifarta, gabanta kankanace yanke a filet, tad’akko littatafanta tana dubawa, hankalinta akwance, zuwa can tabud’e book d’in data saka takardar uncle G!, madina ta tab’ani yauwa aunty bily tad’akko book d’in data saka takardar nan, ALLAH dai yasa takaranta muji, na ce, “to amin deena!.
Tana bud’ewa takardar ta fad’o, ta d’auka tana jujjuyawa, dan ta manta kota miye, harta cigaba da karatunta saikuma ta d’akko takardar tana d’an tadubawa.
Ahankali tabud’e, takardar sai k’amshi takeyi, tad’an murmusa, sannan tafara karantawa kamar haka.
💞Assalamu alaikum. 💞
Gaisuwa dafatan alkairi, ina fatan wannan takardar zata sameki yayin da kike cikin nutsuwarki.
Ina buk’atar ganinki a office d’ina gobe idan ALLAH yakaimu, karkuma ki shanyani, ga kuma nomber na nanan, da daddare ki kirani ko kimin filashin, dan ina buk’atar ganin nomber d’inki.
💚kihuta lafiya💚
Youseef Hussain Ahmad Gurum. {Uncle G!!}.
Sopy ta d’an tab’e baki, lallai kam, saidai kayi hak’uri dan bazan iya aikata ko d’ayaba aciki, takai takardar wajen hancinta tashak’i k’amshi ta lumshe mayan idanunta.
Madina ta ce, “tofa kodai itama ta kamu ne??
Na ce, “to madina waye yasani, saidai mucigaba da kallon ikon ALLAH.
cigaba tayi da karatunta, amma lokaci2 takan kalli takardar tayi murmushi.
..yauma kamar yanda tasaba tashirya tsaf, cikin zani da riga na jan les, tasaka hijjabinta har k’asa, tad’auki jakkarta tafita, kai tsaye aji tanufa dan tanada lecture a dai dai wannan lokacin, bayan sungama karb’ar lecture d’in yawancin d’aliban suka firfito, itakam tana zaune abunta, saida taji zafi yafara isarta sannan ta tashi tafito, dan yau bataga ‘yar kazaginnataba wato zaliha, gurin data saba zama tazo tazauna, amma yau ba karatu takeba, waya tad’akko tafa chatin da uncle kabeer, sai faman murmushi takeyi wanda yake k’ara k’awatar da k’yawun fukarta.
Uncle G!, dake tsaye ajikin wata bishiya yaja ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, karfa yarinyar nan ta zautashi, dan wlhy jiya dak’yar ya iya barci, yadad’e yana jiran kiranta, amma har yay barci bata kiraba, yasan kuma takaranata letter d’insa amma tashareshi, tacigaba da harkokinta hankali kwance, shi gashi nan tabarsa cikin damuwa, dan wata irin soyayya yake mata mai tsanani, wadda yake ganin ‘yammatan!! dasuke cewa suna sonshi!! tasu soyayyar ta k’aryace, ya rintse ido yabud’esu akanta, wani k’ayataccen murmushi tasaki wannada yasa kumatunta lotsowa, shima saiya murmusa.
Gaba d’aya yinin yau zaman jiranta yazauna yi, amma batazoba, gashi yau bashida lecture dasu, duk sanda aka kwankwasa k’ofar office d’insa saiyayi tsammanin itace, amma sai anshigo yaga sab’anin hakan, har zuwa yamma batazoba, ya tattara yafita shima cikin damuwa, dan yaso sugana.
Itakam sopy tana sane, amma ta share tacigaba da sabgogin gabanta, tun wajen k’arfe 3:30pm tagama lectures nata, amma tayi tafiyarta d’aki batareda tabi takan uncle G! ba, duk da tasan yana office yana jiranta, dan duk yau bata gansaba ma.
Yau tsawo kwana biyu da uncle G!, yabama sopy letter domin buk’ar ganinta, dakuma bata izinin kiransa a waya, amma bata aikata ko d’ayaba, dukda abin yana cikin ranta, amma ta danne ta nuna baidameta ba, yauma data kasance juma’a kuma bai shigo musu lecture ba, gashi tana shirin zuwa gida weekend, dan haka tashirya bayan gama lecture karfe 11:15am tayi tafiyarta, lokacinma uncle G! Bai shigo school d’inba.
Bayan shigowarsa yayta baza idanu dan son ganinta, amma ko alamarta bai ganiba, baimaga k’awartataba zaliha,, shikam baya son tanbaya, dan kar akawo masa raini, dole yahak’ura yabarma monday, dan yaci alwashi ranar monday kobata nemeshiba tofa shi zai nemeta, dan bazai iya rik’e sonta azuciyarsaba, batareda ya sanar da itaba, domin sonta yayma zuciyarsa baban kamu wanda babu yanda za ayi ya iya hak’urin rik’eshi, shima mota yashiga yanufi gida……………….✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN’s💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 21~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣1⃣🔸🔶
………..safiyya ana gida anashan weekend, inna tayi farincikin ganin yanda sopy ta canja, tasaki jikinta sosai sai dai haryanzu tananan arame, dan bata k’ara k’ibaba.
Yanzu tarage yawan tunani, tafi maida hankali wajen karatunta, babama yaji dad’in ganinta sosai.
Taje tagaida maman su fareeda, harma tatayata wasu ayyukan, maman fareeda tanata k’ara lallashinta akan abinda yafaru, sopy ta ce, “wlhy mama ni yawuce awajena, dama can ALLAH yarubuta Abdul mijin fareeda ne, dan haka kudaina ganin laifinta, kud’auka wannan yana cikin k’addarar rayuwarmu ne kawai.
Mama ta ce, “hummm safiyya kenan ke dai mai hak’urice kawai!! Kuma insha ALLAH saikin sami miji nagari wanda yafi Abdullahi k’yawawan halaye, itakam mun barta da wayonta!!.
A’a mama dan ALLAH karkuce haka wlhy har yanzu ina k’aunar fareeda bana son iyayenmu suyi fushi da ita!!, dan ALLAH kuyafe mata!!.
Mama ta tsurama sopy idanu, tana matukar k’aunar yarinyar, saboda hak’urinta ga nutsuwa, lallai d’iyarta tayi asara, tunda har tarabuda safiyya bata koyi k’yawawan halaye daga garetaba.
Nan dai sukaita hirarsu har yamma.
Tayi k’ok’ari taje gidan aunty Nafisa da auty hauwa’u, har gidan aunty zainab yayar fareeda, nanama hak’uri tayita bata, sopy ta ce, ” bakomai yawuce”.
Ranar lahadi uncle kabeer yazo gidan dan shine zai maidata school, ya d’auketa sukaje yayo mata sayya ta kayan provision da Duk abunda zata buk’ata, ‘yar gatan uncle kabeer kenan, har d’unkuna yaymata yasaya mata takalma da hijja bai, da yamma tashirya suka tafi, harda kukan rabuwa da inna da baba.
Amota uncle kabeer! ke tambayarta taje gidan fareeda!? ta ce,:”haba uncle ALLAH ya kiyaeye aii har abada bazanje gidan fareeda ba, saidai idan tazo anguwar magaisa amma bazanje gidantaba!!.
Uncle kabeer yay murmushi saboda kishi??? Tai saurin fad’in uncle aii ni! Har abada bazanyi kishi da fareeda ba, koda d’imma ina bak’in cikin sub’ucewarta daga garenine, da kuma abunda ta aikata saboda son zuciya, amma ni yanzu haka na yafe mata, sai dai kuma bazamu tab’a komawa kamar daba, dan yanzu banida aminiyar data wuce inna da baba, sai uncle kabeer da my auntys d’ina.
Uncle kabeer yay dariya to shikenan kema ALLAH yabaki miji nagari.
Sopy tasa hannu tarufe fuskarta saboda kunya.
Adai dai wannan lokacinne kuma suka iso cikin makarantar, yasamu guri yay parking, ya zaro waya bari nakira abokina yazo yataremu.
Sopy ta ce, “waini waye wannan abokin nakane uncle?? Ni tunda nazo school d’innan ban sanshiba.
Ya ce, “zaki gansa yanzu nan.
Cikin ‘yan mintina ya iso, hankalin sopy yana kan waya tana chatin, uncle kabeer yabud’e motar yafito, suka rungume juna shida abokin nasa.
Kai abokina nazata makarantar nan zata zama gurin zuwanka fiye da haka, amma sainaga sab’anin haka, indai har bawani abu bane yakawoka ba, ba’a ganinka.
Uncle kabeer yay dariya karka damu indai nine yanzu zaka rink’a ganina sosai tunda my daughter d’ina tana school d’in!!.
Ya ce, “gsky ne, aii nima yakamata yau nasan wannan d’iyar tamu.
Uncle kabeer ya ce, “aii gata nan amota ma ita nakawo!!
Malamin yay dariya to ta fito, saimu k’arasa office ko?? Murnar ganinka tasa na manta a inda muke tsaye.
Uncle kabeer ya ce, “sopy tafito ga abokin nasa.
Da zumud’inta tafito kuwa, tayi turus tana kallon abokin na uncle kabeer,, ba wani bane illa uncle G!, shima kallonta yakeyi cikin wani yanayi mai wutar fassara,, uncle kabeer! Yay dariya to da alama kumma san juna kenan?.
Uncle G! Yay murmushi, ai d’aliba tace, kaga duk laifinkane kenan???. Uncle kabeer ya ce, “to, kayi hak’uri, ranar dana kawota ina sauri natafi wajen aikine wlhy.
Sopy ta daure ta ce, “uncle good evening!.
Ya ce, “ya weekend??
Ta ce, “ALHAMDULILLAHI.
MASHA ALLAH yafad’a yana kama hannun uncle kabeer!, abokina muje ciki ko.
Sopy ta ce, “uncle bari nakai kayan d’aki saina dawo muyi sallama, sannan kun gama.
Okey to shikenan babu damuwa, jeki kai, amma kisamu wasu sutayaki, dan kayan sunyi miki nauyi.
To uncle!.
Sopy takira zaliha awaya sukazo itada wata k’awar zalihar, suka tayata kwashe kayan, saidai gaba d’aya zuciyaryata cike take da tunanin dama uncle G! Shine abokin uncle kabeer??, k’in fita tayi har saida uncle kabeer ya kirata a waya sannan tafito.
Bayanda zatayi dole tanufi office d’in dan uncle kabeer ya ce, “tasameshi a can.
Ahankali ta tura k’ofar office d’in tashiga, office d’in sai tashin k’amshi yakeyi, uncle kabeer ya nuna mata kujerar dake kallonsa tazauna.
Ya ce, “kindai gama ko?? Ta d’aga kai alamar e, ya ce,”masha ALLAH, yagara zama to sopy! Ga abokina malam youseef tare mukai school d’innan dashi, amma dayake shi abincinsa anan yake, to gashi yana aiki anan, munsha gwagwarmayar rayuwa tare, komai namu tarene a school d’innan, gashinan duk abinda kike buk’ata to kizo wajensa ki karb’a, kokuma idan wani abu yashige miki duhu a b’angaren karatu, to kizo zai warware miki, domin wannan dakike gani kwarone, uncle yafad’a yana kallon uncle G!.
Uncle G! Yay dariya kaidai masherancine abokina har yanzu kana nan baka canjaba ko?
Uncle kabeer ya ce, “aii gsky ce, uncle kabeer yacigaba dafad’in abokina ga d’iyata wadda nafiji da ita acikin ‘ya’yana, batada damuwa kamar yada nasanar maka, itama tanada kwakwalwar karatu, dan haka ka taimaka mini wajan cika mini kwakwalwarta da karatu.
Uncle G! yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad’an tsurama sopy idanu tai saurin janye idanunta daga kallon datake masa, yay d’an murmushi, babu damuwa abokina nakarb’a, ainima d’iyatace.
Sopy tana mamakin yanda taga uncle G! yanata fara’a yau, domin yau itace rana tafarko dataga murmushinsa, sannan duk d’agowar datayi saita kamashi yana kallonta.
Sun d’an dad’e suna hira, kafin uncle kabeer ya tafi, saida suka rakashi har wajen motarsa bayan ficewarsa daga cikin makarantar uncle G! Ya juyo yana kallon sopy, tai kasa da kai dan tasan batada gsky………………..✍🏻
💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 22~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!! 🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣2⃣🔸🔶
……………yagara tsayuwar sa, aii dole kiji kunya, dan kinsan kinyi laifi.
Sopy tad’an d’ago ta kalleshi, ganin ita yake kallo yasata saurin yin k’asa da kai, ta daure ta ce, “laifin mi nayi??
Ya jin jina kai, okey tunda baki d’auki abinda kika aikata amatsayin laifiba shikena, ya kalli agogon hannunsa, yanzu inada wani aiki, amma zuwa gobe zan jiraki a office, kinada lecture d’in safene???
Sopy ta amsa da e, inadashi.
Okey to karfe nawa zaki fito??
Tayi d’an jim alamar tunani, karfe sha biyu.
Okey bada muwa, jan jiraki k’arfe hud’u, yajuya yana kallon yanda wasu tsurarin d’alibai masu dawowa weekend damasu harkokin gabansu, dayawansu su suke kallo, yad’an girgiza kai, kinga kije d’aki amma karki shanyani, inko bahakaba to zanzo har ajinku gaban kowa muyi magana.
Ta zaro ido😳 waje.
yay murmushi kina mamakine ?? To indai hakane kik’i zuwa kigani, saidai kawai ki ganni.
Ina saurarenki, yafad’a yana tafiya.
Sopy tabishi da kallon mamaki, wai mutum mai aji da nuna isa, mai ilimi wanda ‘yammatan! da samarin! university ke son yay musu magana, shine yau agabana, yake buk’atar naje wajensa, tad’anyi murmushi mai k’ayatarwa tanufi hostel.
D’aliban dasuka gansu aka d’auki gulma zuwa hostel, wasu kuma ganinsu harda uncle kabeer saiba su kawo komaiba aransu, to ALLAH yashiryi magulmata dai.
Washe gari sopy tanata harkokinta, dukda gargad’in da uncle G! yay mata baisa tayi yink’urin zuwa office d’insaba.
Shikam gaba d’aya hakalinsa yana kanta, karfe d’aya da ‘yan muntina yashigo musu lecture, saboda shi tak’i zama gaba, amma wannan bai hana idonsa lalibota ba.
Zaliha ta ce, “sopy wai kin kula da kallon da uncle G! Yake miki kuwa, wlhy tun d’azu hankalinsa yana kanki.
Sopy ta harareta, to uwar magul mata, ke bama karatun kike saurareba, wanda yake kallone agabanki, ni kibarni naji karatu, tana d’agowa suka had’a ido kuwa, tai surin kauda kai gefe.
Yagama lecture nasa yafita.
Har k’arfe hud’u tayi sopy batada niyyar zuwa office d’in uncle G!, tanata harkokinta abinta, suna zaune itada Nadiya, tana koya mata wani aiki.
Nadiya ta ce, “kai sopy kekam kin more wlhy, ina son mutum mai kwakwalwa arayuwata, wannan yana d’aya daga cikin abinda yasa kike matuk’ar birgeni.
Sopy tayi murmushi kekam Nadiya kinada yawan tsokana.
Nadiya ta ce, “wlhy babu wani tsokana gsky ce nake fad’a, kuma kema kin sani, saidai ki godema ALLAH.
Kafin sopy tayi magana wani saurayi ya k’araso wajen, ya ce, “waye safiyya ibrahim kabeer!!? Sopy ta amsa da nice, ALLAH yasa lafiya?? Saurayin ya ce, “lafiya k’alau, dama uncle G! ne ya ce, “kizo yana office d’insa, sopy tad’anja tsaki sannan ta ce,”to ina zuwa.
Aii kije kawai danni ba komawa zanyi office d’inba.
Nadiya ta ce, “kitashi kije bakisan miya faruba, badan tasoba ta mik’e tanufi office d’insa.
Saurayin ya kalli Nadiya, Nadiya dan ALLAH uncke G! Surayin yarinyar nan ne??
Nadiya ta girgiza kai, A’a, ba saurayinta bane, amma nima bansan dalilin dayasa yake nemanta ba, amma kai miyasa ka tanbaya?
Naje wajensane, shine ya ce, “nakira masa safiyya ibrahim, toni abunne yabani mamaki, danshi bai cika kula matan makarantar nan ba.
To babu abinda yake tsakaninsu, kuma maza dai kunzama magulmata.
A’a bawani gulma daga tambaya?.
To miye na tambayar, shin uncle G! Ba mutum bane, koko shi bazai iya yin soyayyaba ne?? Inma hakane wlhy nikam zanyi farinciki.
Saurayin yay dariya aii munga shi baya kula mata, gashi kuma kun mutu asonsa, kamar makarantar nan babu wani namiji sai uncle G!, bakuda wata hira sai tashi, komai uncle G!, tamkar wanda aka halitta da gold.
Nadiya ta ce, “yanada kamun kaine, ya iya rik’e mutuncin kansa fiyeda sauran malaman da d’alibai, baya wasa da kowa, gashi kuma mai aji da ilimi.
Saurayin yay gaba dan jin haushin furicinta.
Safiyya ta nufi office d’in uncle G!, saida taje k’ofar takasa shiga, tadad’e a tsaye, dan takasa kwankwasawa, ganin wasu d’alibai suna kallonta yasa ta daure ta kwankwasa ahankali batayi zaton zaijitaba ma, amma sai taji ya ce, “yes come in.
Ta d’auki tsawon minti biyu bata shigaba, ganin batada fafita yasa ta tura k’ofar office d’in tashiga, wani k’amshi ne yadaki hancinta, tashak’a tad’an lumshe idanu.
Cikin muryarsa mai dad’i ya ce, “shigo mana”.
Cikin sanyin jiki ta ida shigowa ta maida k’ofar ta rufe,, ta jingina da k’ofar.
Yana zaune a kujerarsa, gabansa da tarin takardu, yana dubawa inaga namasu test ne, dan ya kware wajen yima d’alibai test, jin anyi shiru yasashi d’agowa, azatonsa komawa tayi, amma saiya ganta atsaye, tana kallonsa, ya ce bismilla zoki zauna.
Ganin fuskarsa babu walwala yasa ta k’arasa ta zauna a d’aya daga kujerun dake gaban tebir d’in gabansa, yacigaba da duba takardun gabansa, batareda yakuma bi takan taba, yad’auki tsawon minti bakwai, kafin yad’an d’ago ya kalleta, tana zaune kanta ak’asa tana wasada wani zobe dake yatsanta na biyu, yad’anja numfashi sannan ya maida kansa ga aikinsa.
Cikin muryarsa mai amo da taushi ya ce, “yauma da bansa a nemomin keba da bazaki zoba ko?? Yacigaba da fad’in babu k’yau sab’a alk’awari dai.
Sopy ta ce, ” azuciyarta aii ni ban maka alk’awarin komaiba,, amma afili saita te ce, “aii dama zanzo.
Ya ce, “aii koma bakizoba ni zanje nemanki, dan na matsu muyi magana, tad’ago tana kallonsa, yana duba takardunne yana maganar.
Yad’ago zai mata magana, tayi saurin maida kanta k’asa, ya murmusa, tareda mik’ewa yanufi inda take, d’ayar kujerar dake kallonta ya zauna, k’amshinsa ya yawaita agurin, yay gyaran murya tare da fad’in kinsan abinda yasa nake nemanki??.
“Ta girgiza kai”
Yad’ora kafarsa d’aya saman d’aya, ya kwantar da bayansa ajikin kujerar,, saida yay mata kallon mintina uku sannan yaja numfashi, ina son na tambayeki samarinki nawa???.
Da sauri sopy tad’ago tana kallonsa, amma saiya gimtse fuska dan baya son raini.
Ta maida kanta k’asa tana cigaba da lankwasa yatsun hannunta suna k’ara.
Ya ce, “ina sararenki!!.
Sopy ta daure ta ce, “ni fa banida saurayi, cikin shagwab’a tayi maganar.
Yay murmushi tareda fad’in masha ALLAHU, yakuma ce wa,” to yaushe kika shirya yin Saurayin?, nanma saida ta kalleshi sannan ta ce, “banda lokacin aikata hakan.
Nanma saida ya murmusa, ya ce, “masha ALLAHU, yataso daga kwanciyar dayayi, ya ce, “toni na shirya yin auren safiyya, domin matata tarigaya ta iso, ba wasa nazo dashiba, domin inda buk’atar yin aure yanzu, yaya kenan??.
Sopy ta ce, “a zuciyarta, to ni ina ruwana da shirya yin aurenka ne??
Yaci gaba dafad’in nina shirya kefa?? Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkan soyayyata.
Sopy ta ce, “ban ganeba??
Ya murmusa zaki gane nan bada dad’ewaba, kije kiyi tunani akaina, kabeer yasanar dani komai daya shafi rayuwarki, dan haka bakida matsalar yimin bayanin kanki, nakuma yimiki alk’awarin mantar dake abinda yafaru dake abaya, sannan daga yau karna sake ganinki da zaliha, dan batada tarbiya, nasan bak’ya kula samarin makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina, ya mik’a mata wani littafi mai d’an girma, ga wannan ki karanta lokacin dakika samu dama, zaki samu dukkan abinda ya danganceni acikinsa, dukkan tarihina yana nan.
Tasa hannu biyu ta karb’a, ya d’akko lemon dake saman tebir d’in ya mik’a mata, sorry ga wannan kisha!.
Ta girgiza kai A’a nagode.
Ya ce, “kina nufin bazaki shaba, ko kina kyankyamin abin hannuna ne??.
Tai saurin girgiza kai, ya ce, “to karb’a kisha, ta ce, “aii ina azumine.
Ya ce, “wow nice, azumin me kenan??, ta ce, “na nafila.
Ya kuma cewa nice, aii haka akeso, to idan kinsha ruwa wace addu’a zakiyi akan aurenmu?.
Ta k’ara k’asa da kai, batareda tayi maganaba.
Ya ce, “kunyarki tayi yawa, amma zsn rage miki ita, dan dama haka nakeson matata ta kasance mai tarin kunya da nutsuwa, gashi ALLAH ya kawo min alokacin danake tsananin buk’ar hakan, wannan week d’in zanje gida nasanarda iyayena nasan zasuyi matuk’ar farinciki, dan kullum burinsu kenan, gashi dama sunsan kabeer, dan haka ki zauna da shirin zama matata nanda k’arshen shekara 2016.
Tayi saurin kallonsa, ya kashe mata ido d’aya, ina fatan kin shirya salo salo na soyayyar dazaki nuna min, danni mutumne mai buk’atar a soshi da nuna min tattali yak’arasa fad’a a hankali.
Itadai sopy takasa koda k’yak’yk’yawan motsi, dan ita mamaki ma yake bata, ko ina miskilancin da jan ajin nasa?? Dama yana magana haka??.
Kamar yasan tunanin datakeyi, ya ce, “kina mamakina ko? To daga yau kibari, domin ni mijinkine, ina fatan kwaykwayon {MANZON ALLAH S A W} ne, domin ya nunama mana yanda zamu so matanmu da kuma yanda zamu zauna dasu, dan haka kinada matuk’ar aiki agabanki,, ki shirya kuma.
Ya d’auki wayarta dake kan cinyarta, nomber d’insa yasa yakira wayarsa, sai kuma yacigaba da binciken wayar, babu wani abu mara k’yau aciki, saima hotu nanta masu k’yau, yagama gani ya mik’a mata.
Ta ce, “bari natafi kar mutane su zargi wani abu.
Ya gyara zama karki damu dasu, danni basu bane agabana, amma duk da haka na fahimceki, nima bana buk’atar kowa yasan wannan maganar sai an gama komai, kinji ko.
Ta jinjina kai alamar to.
Ya ce, “to tashi kije dan yamma tayi, sainazo barka da shan ruwa….
Aii kafin yarufe baki tayi waje.
Ya kwanta ajikin kujerar, ya lumshe idanu yana murmushi, ya ce, “ya ALLAH ka mallaka min wannan baiwa taka mai tarin nutsuwa da addini.
“muda muke a lab’e, ni da su pii pii mukace amin ya Rabbi…………………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 23~October ~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣3⃣🔸🔶
……….kwance take bayan ta gama shanruwa, tayi zugum dan kuwa tana duniyar tunanin abinda yafaru d’azu, tsakaninta da uncle G!, ta tuna yanda yake magana cikin gadara da bada umarni.
“Toni na shirya yin aure safiyya, domin matata tarigaya ta iso, bawasa nazo dashiba, domin inada buk’atar yin aure yanzu,”
Tayi murmushi, tareda sake tuno wata maganar tasa.
“Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkanin soyayyata”.
Taja numfashi tareda gyara kwanciya, wato shi baya lallashi, kai tsaye yake magana babu wani kwala kwala, to amma shi baisan ba’a umarni a soyayyaba ne?.
Ta tuna inda yake fad’in, daga yau karna sake ganinki da zaliha dan batada tarbiyya, nasan bakya kula samarin makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina”.
Ta murmusa, su uncle G! Masu kishi, to ina ruwana da kishinka, ni nan dakake gani maza duk d’aya na d’aukeku, a kan mizani d’aya nasakaku, taja ajiyar zuciya domin jin an kwala kiran sallar isha’i, tamik’e domin gabatar da sallah.
Saida ta kammala komai na al’adar rayuwarta, sannan tazauna domin duba book d’in da uncle G! Yabata, ga gajiyar azumi, tazauna tana fad’in wash ALLAH!! aii duk gajiyar danayi bazata hanani karanta book d’innan ba, tai saurin kallon wayarta datake wringing sabuwar nomber ce, dan haka ta share, saida aka k’ara kira sannan tad’auka tana mita, tai shiru batareda ta amsa ba, daga camma ank’iyin magana.
Ta daure ta ce, “kowaye idan bazaiyyi maganaba tofa zan kashe”.
jitai wata sassanyar murya ta ce, “assalamu aliki?.
Sopy taja ajiyar zuciya domin tagane mai maganar, ta amsa da wa’alaikassalam, ta d’ora da fad’in good evening sir.
Yay murmushi mai sauti, ya ce, ” evening, kinsha ruwa lafiya?
“Lafi law, sopy tafad’a”
Ya ce, “masha ALLAH”, Amma a canja min wannan sir!! D’in.
Tai d’an murmushi, to aii kai malaminane, in bance maka sir!! Ba mixan ce maka?
Ya ce, “hummm, ga sunaye nan masu yawa, darling, honey, dear, my love, prince, gasunan dai dayawa.
Hannu tasa ta rufe fuska tamkar yana gabanta.
Jin tayi shiru yasashi fad’in ya dai?
Nanma shiru tayi.
Ya ce, “okey, sarkin kunya, amma yakamata arage kunyarnan ko? Dan zata d’an cutar dani, in tambayeki mana??
Ta ce, “to, tambayeni?
Okey ince dai kinyi mana addu’a?? yayinda zaki sha ruwa, dan kinsan ana karb’ar addu’a a irin wannan lokacin.
Sopy ta gyara zama, ta ce, “e, nayi.
To, mikika rok’ar mana?.
“Komaima, na rok’a” sopy tafad’a, asanyaye.
Ya ce, “nice, “to d’an fad’amin mana naji.
Cikin shagwab’a ta ce, “ni dai basaina fad’aba.
Uncle G! Yay dariya, ya ce, “nice, my sopy karki damu wataran zaki fad’a, bari nabarki kiyi barci, goodnight.
Kafin ta ce, “wani abu ya sumbaci wayar, ya kashe, sopy ta rintse idanu tabud’e, ya salam ta fad’a tana kwanciya, dama maza basuda kunya, duk jan ajinsu dawani jijida kai, idan akazo fagen soyayya saisu canaja, duba dai kiga uncle G!, ni wlhy mamakima yake bani, ta lumshe ido tana murmushi, wanda itama batasan dalilin saba.
Ta dafe k’irjinta tana fad’in oh ni safiyya, waiy mike shirin faruwa dannine?? Miyasa nike shiga farinciki aduk lokacin da uncle G! Ya kasance danine?? Idan ban ganshiba nakanyi kewarsa? Shin miye dalilin hakan??.
Zuciyarta ta ce, “kin kamu da sonsa ne.
Ta girgiza kai tana fad’in ban yardaba, alokacin dana keson Abdul bahaka nakejiba aii, akwai dai dalili, to amma miye dalilin??
Uncle G! Yana burgenine kawai, amma bawai ina sonsa bane, zan iya cewama har yanzu ban amince da batunsa na d’azuba, domin kuwa Abdul yasa nayima dukkan maza kud’in goro a fannin yaudara, bana tunani zan sake shiga tarkon son wani namiji ahalin yanzu, nariga na shafe babin soyayyar wani namiji arayuwata, nasan ban isa nace, “bazanyi aureba, tunda nima saida akayi aure aka haifeni, amma koda nayi aure mijin dana aura bazai samu wata soyayya agareniba, sai dai kuma bazan iya nuna hakan ga uncle G! ba, saboda yanada girma a idona, malaminane abokin uncle d’inane, sannan koba komai ya girmeni, ta jawo book d’in domin karantawa.
Kubiyoni masu karatu, dominjin tarihin, youseef hussain Ahmad, wato uncle G!!!………………..✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 24~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣4⃣🔸🔶
………….TARIHIN UNCLE G!!!.
uncle G!, kona ce youseef hussain Ahmad, d’an asalin garin gurum ne, a k’aramar hukumar tsanyawa.
Malam hussain shine mahaifinsa, suna kiransa da baba, sahura itace mahaifiyarsa suna kiranta da gwaggo, su hud’u iyayensu suka haifa, hafsat itace babba tana aure anan cikin gurum harda yaranta, yusif shine nabiyu uncle G! Kenan, sai Libabatu itama tayi aure tanada yara, sai auta Aysha tana karatu yanzu tana (jss, a secondary ).
Gidan su uncle G! Talakawane sosai, saidai mahaifinsu yana son karatun boko sosai, wannan yasa ya tsayama ‘ya’yansa sukai karatu, duk da matan daga secondary ake musu aure, amma sun tsayama uncle G! Yayi karatu mai zurfi, dukda kwakwalwarsa ta taimaka masa wajen kaiwa ga matakin dayake a yanzu, bak’aramar gwagwar maya akashaba wajen karatun uncle G!, amma idan ALLAH ya ce, “kaine tofa kaine”.
Bayan ya kammala deploma d’insa ya samu aiki a primary school d’in Gurum, wannan ma ya taimaka masa wajen cigaban karatunsa, dan yana koyarwa ya rubuta takardar izinin komawa k’aro ilimi, da taimakon wani bawan ALLAH yasamu shiga (Ado bayaro university kano) anan ne ALLAH Yahad’ashi da uncle kabeer, duk talaucin gidansu sopy! Sunfi su uncle G! Arzik’i, dan haka uncle kabeer yataka rawa mai yawa arayuwar uncle G!, tab’angaren kud’i da wasu abubuwan, sun shaku da juna sosai shida uncle kabeer.
Uncle G! Bashida aure, dukda iyayensa suna damuwa da zamansa haka, akullum yana fad’a musu aure lokacine idan lokacin yayi zaiyi aure, yaso auren wata yarinya anan cikin garin gurum, amma sai ALLAH ya d’auke kayansa tarasu tunda ga nan bai sake yink’urin aureba sai yanzu dayaga sopy.
Uncle G! Yazama wani tauraro mai haskawa agarinsu, dan mutumne mai girmama manya, dakuma son cigaban matasa, har k’ungiyar taimakon matasa gareshi a k’auyensu, dukda bawani kud’ine dashiba saidai rufin asirin ALLAH,
Wannan shine tarihin uncle G!, atak’aice, nan gaba zaku rink’a jin sauran bayani akansa.
Sopy taja ajiyar zuciya, fuskarta d’auke da murmushi, lallai uncle G!, Ansha gwagwar mayar rayuwa, gsky yabata tausayi, dama ance babu maraya sai rago.
Tarungume littafin tashiga barci.
Dak’ar ta iya tashi da asuba tayi sallah, shed’an yaribace ta ta hau barci, wannan yasata makara gashi tanada lecture d’in safe, agurguje ta shirya tanufi aji.
Duk da haka saida ta makaro domin kuwa uncle G! Yarigata shiga, taja tunga ak’ofar class d’in, inda sauran d’alibai makararru suke irinta.
Tsaye yake yana gabatar da lecture, jikinsa sanye da blue d’in shadda d’inkin boda, bawata mai tsada bace, amma yayi k’yau, domin dama mai k’yawunne, babu abinda kakeji sai k’amshin turarensa, jiyay hancinsa yana shak’o masa kamshinta, yad’an juyo inda yake zatonta, kallon ido cikin ido sukayima juna, dukda idanunsa suna cikin gilas wannan bai hanata jin wani yarrrrrr! Ba, tai saurin kauda kai daga kallonsa, ya gyara tsayuwarsa yana wani d’an murmushin mugunta, yacigaba da gabatar da darasi.
Su sopy suna tsaye tareda suran maka rarrun d’alibai, har yagama lecture yafito, kallo d’aya sopy tai masa ta kauda kai, shikuma yawuce yana murmushin mugunta, wanda yabama sauran d’aliban mamaki, wasu kuma yabasu haushi dan aganinsu ya raina musu hankali, tunda akwai sa’aninsa agurin.
Ya k’arasa office d’insa amma saiyayi turus ak’ofa domin ganin kairat zaune, ya had’e rai ya ce, “lafiya dai??
Kairat tad’ago tana kallonsa, lafiyarce takawo hakan.
Yakuma tamke fuska ya ce, “miya kawoki office d’ina nace??.
Yanda yayi maganar cikin tsawa saita tsorata, dan tasan baya son wargi, cikin rawar murya ta ce, “dama nazo nasanar dakai dadyna zai maidani karatu AMERICA.
Uncle G! Ya tab’e baki, lallai yayi dabara, to ALLAH ya taimaka, zaki iya tafiya.
Kairat ta kalleshi cikin matuk’ar bak’in ciki, dan ganin yanda yake korarta, ta daure ta ce, “to ya maganarmu dan inaso nasan matsayina agurinka!!.
Saida yay mata kallon sama da k’asa sannan ya ce, “bakida wani matsayi agurina kamar yanda nasanar dake, sai dai ina miki fatan alkairi a rayuwarki”, ya nuna mata k’ofa akaro na biyu, zaki iya tafiya dan inada abinyi.
Wani bak’in cikine ya tokare mak’oshin kairat, tai waje cikin bak’in ciki, dan idan tayi magana kuka zai iya zuwa mata.
Uncle G! Yaja tsaki, yana fad’in ‘yar wahala, indai so nane kin d’akko abinda yafi k’arfinki, domin tuni wata ta karb’e zuciya ta, useless! Kawai.
Kairat d’iyar wani mai kud’ice, tunda aka kawota makarantar nana ta k’yalla ido akan uncle G! Taji takamu da sonsa mai tsanani, sai dai shid’in batai masaba, yafison ya auri d’iyar talakawa irinsa…………………✍🏻
💞bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 25~October~2016
🔷 🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣5⃣🔸🔶
…………Safiyya! kam tunda uncle G! Yafita tashiga aji tazauna zuciyarta cike da tunani iri iri, koda zaliha! ta zauna kusada ita tana mata surutun data saba bata kulataba, saima ta d’akko wayarta tana catin da uncle kabeer.
Wani sak’o yashigo amma saitayi burus dashi, dan azatonta wanine ya d’auki nomber d’inta a group dan haka wasu keyi, musamman ma samari.
Shigowar wani malami yasa ta daina catin d’in, tanatsu domin d’aukar lecture.
Bayan fitarsa batada wata lecture sai k’arfe uku, dan haka tanufi library domin wani bincike.
Ta shak’i wani k’amshi wanda tabbas tasan mai shi, amma saita share tacigaba da karatunta, jin k’amshin ya yawaita agurin yasata juyowa domin tabbatar da zarginta.
Uncle G! Ne tsaye yana binciken wasu books saidai da alama bai gantaba, dan haka tak’ara k’asa da kai, bata buk’atar yaganta.
sai dai ta makaro, domin kuwa tunda ya shigo da ita yafara tozali, ya basar ne kawai yanuna bai gantaba.
Cikin takunsa na masu aji da gayu yanufo inda take zaune, hannu biyu yasa yadafe tebir d’in gabanta, tareda fad’in Assalamu alaiki?.
Da sauri tad’ago dan batai tsammanin zuwansa ba.
Ya ce, “bakijin sallama ??.
Cikin rawar murya ta amsa, ta d’ora da gaisheshi.
Yaja kujera ya zauna yana fad’in ya ykk?
Sopy taja numfashi tana fad’in lfy law.
Ya ce, “good”.
Kafin yayi magana wayarsa ta hau k’ara alamun kira, ya cirota daga aljihun gaban rigarsa ya amsa.
Saida yagama wayarsa sannan yadawo da dubansa gareta, yayinda wasu d’alibai dake library d’in suke kallonsu.
Ya mik’e yana fad’in kisameni a office inaso muyi wata magana dake, domin inaso naje gida wannan week d’in akan maganar aurenmu!!.
Da sauri ta kalleshi, shima kallonta yakeyi, dan haka ta maida kanta k’asa, ya kwashi wasu takardunta data ajiye, ta daure ta ce, “uncle zanshiga lecture dasune fa.
Yatafi yana fad’in nasani idan kinzo saiki karb’a ina jiranki karki b’ata min lokaci.
Sopy ta dafe kai tana fad’in nashiga uku ni safiyya mutumin nan fa yafara shiga min hanci, yakamata na face shi, kanta ta maida ga karatu amma saita kasa karatun dole ta mik’e tafice, tadad’e tana tunanin zuwa office d’insa, dan gsky bataso azargeta akan yawan shiga office d’insa.
Wayarta ta hau wringing, tad’aga tana mita.
Muryar uncle G! Taji yana fad’in ina jiranki fa!!.
Kafin ta ce, “wani abu ya yanke wayar, ta dafe kai tana fad’in ya salam, dole ta daure ta nufi office d’in.
Ta kwankwasa, ya ce, “shigo mana, dan yasan ita ce!!.
Da sallama tashiga kanta ak’asa, yad’ago yana kallonta batareda ya ce komaiba.
Jin yayi shiru, ta ce, “gani!!.”
Ya ce, “aii naganki, ya maida kansa kan abinda yakeyi.
Sopy tabishi da kallo cikin takaici, takardunta yake dubawa, taja k’aramin tsaki amma baiji ba, a zuciyarta ta ce, “kaidai kana son sakani cikin matsala, banason wani yazargeni wlhy.
Ya d’ago yana fad’in wai bazaki zaunaba ne??.
Ta ce, “nanma ya isa.
Ya ce, “okey nima bari nataso tunda yau tsayuwar kike sha’awa.
Kafin ta ce wani abu yataso, ya k’araso inda take tsaye, jingina yayi ajikin bango ya hard’e hannayen sa a k’irji, ya dasa mata fararen idanunsa manya masu yalwar gashi.
Ta k’ara k’asa da kanta dan ganin irin kallon k’urullar dayake mata, ya murmusa dan ganin yanda taketa sinne kai kamar wadda tayi k’arya, ya gyara tsayuwarsa, sopy!! Wai sai yaushe zaki kalli cikin idanuna ne, kunyarki tayi yawa fa.
Hannu tasa ta rufe fuskarta.
Yay dariya tareda fad’in okey to shikenan, dama inason nasar dake jiya da daddare naje gidanku!!.
Ta zaro idanu, gidanmu kuma??
Ya jin jina kai, e, gidanku, aii dama na ce, “miki bada wasa nazoba, yacigaba da fad’in, munyi magana da baba, nasar dashi komai nida kabeer, yakuma karb’eni fiye da zatona, yanzu haka yabani izinin turo iyayena! Sai dai ya ce, “bikinmu zaikai nanda watanni dan yanzu suna shirin bikin kabeer, amma bayan bikin kabeer da wata uku zuwa hud’u sai ayi namu.
Sopy ta zame ta zauna a k’asa, bayanta jingine da k’ofa.
Ya bita da kallon mamaki, ya daure ya ce, “yaya dai? Ko hakan bai mikibane??.
Ta d’an kalleshi, ta girgiza kai.
Ya ce, “to miye matsalarki??.
Ta ce, “babu, ta cigaba da fad’in nasan iyayena bazasu cutar daniba, dan haka na amince da duk abinda suka yanke, kuma zan yimusu biyayya.
Uncle G! Yaja ajiyar zuciya yana fad’in ALHAMDULILLAH!!, ya tsugnna a gabanta, ya ce, “karki damu safiyya!, kabeer ya sanar dani abinda yafaru dake a baya, tsakaninki da AMINIYARKI da kuma SAURAYINKI, to inaso ki manta da abunda yafaru a baya, ki gogeshi a arayuwarki, kid’auka yanzu zaki sake sabuwar rayuwane, ki yarda ni ne!! Zab’in alkairin da ALLAH yay miki, zan baki mamaki insha ALLAHU, Zan rik’e amanar da baba yabani taki kinji.
Yaja numfashi, gobe idan ALLAH yakaimu kabeer zaizo, zai sanar dake sauran bayani, ni kuma jibi idan ALLAH ya kaimu zanje nasanar da iyayena, ya mik’a mata farin hankici daketa tashin k’amshi, karb’i ki goge hawayenki dan banason su zuba k’asa.
Sopy ta karb’a dan ita bama tasan tana kukaba, saidai batasan kukan na miyeba?? Farinciki ko bak’incikin rabuwa da Abdul, tasan tabbas uncle G! Yafi Abdul komai kyau, ilimi, aji, da sauran abubuwa masu yawan gske, kud’i kawai mahaifin Abdul zai nunawa uncle G!, itakam bata d’auki kud’i wani abu mai muhimmanciba arayuwarta, dan itama talakace tib’is, tanada tabbacin samun nutsuwa a gidan talaka d’an uwanta.
Jitai uncle G! Yana fad’in to kukan ya isa haka, inko bahakaba zan lashe hawayen dasuka sake zubowa.
Hannu tasa tasa tarufe fuska tana dariya.
Shima dariyar yayi, “wai yau miyasaki makara ne??
Cikin sanyin murya ta ce, “karatun tarihinka mana.
Ya ce, “nice, hakan yayi nasan yanzu kinsan ni kowaye, ni talakane tib’is, sai dai rufin asirin ALLAH kawai, ina fata wannan bazai shafi auren muba ko??, Dan kinji wayeni dakuma inda nafito, kinji su waye family nawa, zaki iya neman k’arin bayani a wajen kabeer, dan yasan komai a kaina.
Tai murmushi to aii nima talakace, nasan kuma kasani, tunda kana tareda uncle kabeer.
Yad’an murmusa yana fad’in to shikenan ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, amma daga yau idan kika k’ara makara a lecture d’ina tofa bayan horon hana shiga aji, akwai horo tsakanina dake, dan haka ki kiyaye, yafad’a yana mik’ewa.
Itama ta tashi tsaye, to bari na tafi.
Kai habadai tun yanzu, nifa ban gaji da ganinkiba!!.
Hannu tasa ta rufe fuska ta ce, “aii munkusa shiga lecture ne.
Yay dariya to sarkin kunya, ga kayanki can jeki d’auka.
Ahankali ta nufi tebir d’in sa, ta tattara takardunta ta kwaso zata juyo wayarsa ta hau wringing, ya ce, “taho min da phone d’ina!.
Saida ta d’an rissina sannan tabashi tay waje da sauri, dan batason yasake tsayar da ita.
Yay murmushi, yana binta da kallo……………[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 26~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣6⃣🔸🔶
………..Tunda tabar office d’in tazama wata shiru shiru, gaba d’aya abin mamaki yake bata jitake tamkar amafarki, wai itace zata zama matar uncle G!, kai wannan lamari tamkar ba gsk bane, lallai ko bata son uncle G! tofa dolene ta aureshi, kodan ta k’ara nisanta kanta da Abdul, da fareeda, wasu hawaye suka zubo akan kumatunta, wlhy tana son fareeda, amma gashi fareeda tajawo abinda yanisantasu da juna, tana matuk’ar kewarta da son ganinta, takifa kanta saman tebir tana kuka.
Zaliha ta tab’ata, sopy lfy dai ko? Sopy tad’ago tana kallon zaliha, fuska share share da hawaye, ta ce, “babu komai wlhy zazzab’i nakeji”.
Ayya sannu to kitashi na kaiki hostel mana.
Sopy ta girgiza kai ki bari mu gama lecture tunda saura d’aya.
Zaliha ta ce, “to shikenan”, amma fa wata magana najiyo yanzu akanki!!.
Sopy ta ce, “akaina kuma zaliha??, wace irin magana kenan?.
Zaliha sarkin gulma ta gyara zama, wlhy wasu samari naji suna fad’in way soyayya kukeyi keda uncle G! Wai shiyyasa kikema samari girman kai, dan anga wai yabiki library d’azu.
Sopy ta k’urama zaliha idanu, kamar zata cinyeta, saida zaliha ta tatab’ata, sannan taja ajiyar zuciya, zaliha ta ce, “mi kuma kike tunani?
Sopy ta girgiza kai babu komai, amma ni k’arya suke min, dan kawai sunga yashiga library sai suce wajena yaje.
To aii wai bayan fitowarsa ke kuma kinje office d’insa!.
Sopy taja tsaki, ta ce, “kai magulmaci madai yaji haushi wlhy, to uncle G! Abokin uncle d’inanane tare sukai karatu a wannan makarantar, wannan itace dangan takar dake tsakaninmu, sai a daina gulmarmu aii, ta maida kanta ta kwanta.
Zaliha uwar gulma aka jinjina kai, kinsan ba kowane yasan hakaba, dan nima dabaki fad’aba ban saniba, dan wlhy nima nazata soyayya kukeyi, to ammafa kallon dayake miki irin na masoyane, idan fa yana lecture to gaba d’aya hankalinsa yana kanki, to kinga aii masu fad’a basuda laifi.
Banza sopy tayi mata, dan tasan zaliha magul maciyace tafad’a aji, ita ba k’ok’ariba sai iyayi da gwalli.
Ganin sopy ta shareta sai tatashi ta fita, wajen samarin ta nufa tazauna, suka shiga tambayarta zaliha tagaya miki, zaliha ta rik’e baki tana fad’in kukam magulmatane wlhy, idan ance maxa sun iya gulma ku musa mana, to ta ce, “wai abokin uncle d’intane.
Wani acikin samarin ya ce, “kai wlhy ban yardaba, k’arya ta fad’a miki, amma kicigaba da saka mata ido zaki hano gskyr maganar, zaliha tamik’e tana fad’in aiko saina gano bari naje dan za’ayi mana lecture yanzu.
Samarin suka shek’e da dariya, suna fad’i zaliha dama ke kina fahimtar karatune.
Zaliha ta hararesu tai gaba, dan tasan magana suka gaya mata.
Koda sopy ta koma d”aki takasa aywatar da komai, tunani ya bai baye kwakwalwarta, ji tai yau son Abdul ya dawo mata sabo azuciya, jitai a yau zata iya auren Abdul suyi kishi da fareeda, ta rintse ido ta bud’e tana fad’in, ya ALLAH idan shaid’an ne yake k’awata mini hakan ALLAH ka dawo dani cikin hayyacina!, ta fashe da kuka tana girgiza kai, wlhy bazan iya zaman kishi NI DA AMINIYATA ba har abada, fareeda na hak’ura na bar miki Abdul har abada wlhy, nabar miki! Na bar miki!!! Ta k’arasa fad’a cikin kuka mai ban tausayi, masu karatu nimadai saida na matse hawaye dan sopy tabani tausayi.
Ta dad’e tana kuka daga k’arshe ta dangana, tayi shiru, sai shashsheka da takeyi, dahaka wani waha lallen barci ya d’auketa.
Da safe da ciwon kai mai tsanani ta tashi, dan haka bayan gama sallar asuba saita koma barci.
Wringing d’in wayartane ya tasheta, sunan uncle kabeer tagani akan wayar, ta tashi da sauri, tana amsa wayar, bansan miya fad’a mataba ta tashi da sauri tahau shirin fita.
Kai tsaye office d’in uncle G! Tanufa dan tasan uncle kabeer yanacan, ta kwankwasa aka bata izinin shiga, da sallama tashiga, suka amsa mata, ta rissina tana gaishesu.
Uncle kabeer ya d’ora da fad’in my daughter ya dai? Naganki kamar kina cikin damuwa?,
Sopy ta girgiza kai, ta ce, “uncle lafiyata k’alaw kainane kawai keyin ciwo.
Ayya sorry my daughter, yanuna mata kujera ta zauna, uncle G! Ya ce, “kinsha magani ko?.
Ta ce, “e nasha shine ma yasakani barci.
Okey ALLAH yabaki lfy.
“suka amsa da amin.”
Uncle G! Yamik’e yana fad’in bari naje nagabatar da lecture.
Okey lecturer!! Uncle kabeer yafad’a cikin tsokana.
Uncle G! Yafita yana fad’in kana nan baka canjaba kabeer.
Bayan fitar uncle G!, uncle kabeer yadawo da hankalinsa ga safiyya da kanta yake kasa tana wasa da zoben hannunta yay gyaran murya, sopy ta d’ago tana kallon sa, yay mata murmushi d’iyata yaya dai??.
Itama ta murmusa ta ce, “bakomai uncle.
Ya ce, “okey to shikenan, dama wata magana ce takawoni, duk da youseef yasanar dani kun fara maganar jiya ko??.
“E, uncle! Hakane”.
Uncle kabeer ya ce, “to ke yakika gani?? Kin amince??.
Sopy tay kasa da kai saboda kunya.
Karki damu d’iyata, karki bari kunya tahanaki fad’ar gskyar ki, inhar baki sonsa ki sanar dani.
Sopy ta rufe fuska da hannuta ta ce, “ina sonsa uncle!!.
Uncle kabeer yay dariya, “ALHAMDULILLAH”, yafad’a yana gyara zama, lallai ina tayaki murna d’iyata!!, da samun miji nagari mai addini da tarin ilimi, nasan watarana zakiyi alfaharin kasancewar youseef a matsayin mijinki, zakiji dad’in zama dashi domin kuwa mutumin kirkine shi, ALLAH ya kaimu lokacin musha biki.
Sopy taja hijjab ta rufe fuska.
Uncle kabeer yayi dariya, bazakice amin ba sopy.
Ta ce, “kai uncle wlhy kana bani kunya.
To bani kunyata uncle kabeer yafad’a.
Haka sukaita hirarsu, har uncle G! Yadawo, tunda ya shigo bakin sopy ya mutu, ta daina magana takuma sunkuyar da kai k’asa.
Uncle G! Ya nunawa uncle kabeer sopy da baki, uncle kabeer yay dariya ya ce, babu ruwana nidai, kunfi kusa.
Sopy ta d’ago karaf ta kama uncle G! Yana mata gwalo.
Batasan sanda ta harareshiba, ya ce, niko!!.
Saida taje bakin k’ofa sannan ta ce, “e, ta fita da gudu.
Dariya sosai sukeyi, uncle G! Ya ce, “kabeer dama haka safiyya take??.
Uncle G! Yay dariya ya ce, bazakaji mutuwar sarki abakinaba.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, sopy tana karatu yanda yakamata, takanje gida weekend lokaci2 idan tasamu dama, shak’uwa kuma tana k’ara shiga tsakaninta da uncle G!…………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 27~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸2⃣7⃣🔸🔶
……….BARI MU WAYWAYI FAREEDA….
Fareeda kam rayuwa ta canja mata, kwance take tana fidda numfashi da k’ar sakamakon zazzab’in dake jikinta, babu abinda ya haddasa mata zazzab’in sai uban aiki da umman Abdul tasakata, dak’yar tagama aikin tajawo jiki tazo ta kwanta.
Abdul yashigo ko sallama babu, ko kallo bata isheshiba ya wuce yana canja kaya, fareeda tabishi da kallo tana zubar da hawaye.
Ya gama yanufi hanyar k’ofa domin fita, ta daure ta ce, “Abdul!!.
Ya juyo yana kallonta awulak’ance batareda yayi maganaba,
Cikin kuka ta ce, “dan ALLAH Abdul inaso muyi magana, ka taimaka kazauna.
Ya gyara tsayuwa kinga malama idan zaki fad’a ki fad’a dan babu wani zama dazanyi, inada gurin zuwa.
Fareeda ta cije baki, cikin k’arfin hali ta tashi zaune.
Ta ce, “Abdul dan ALLAH miyasa ka juya mini baya, yakamata ka fahimceni, yanzu ka daina kula dani, kana ganin wahalhalu dana ke ciki agidannan ga gallazawar mahai fiyarka amma baka tab’a nuna rashin jin dad’in kaba, dan ALLAH karka barni Abdul, yanzune nafi buk’atar zama dakai Abdul, karka manta saboda kai nabar iyayena, nabar ‘yan uwana, nabar aminiyata mai sona dason ganin farincikina, amma danmi zaka barni bayan yanzu kai kad’ai gareni, saikuma wannan cikin dakake gani bai dace yazoba ayanzun.
Abdul yaja tsaki, yanuna ta da d’anyatsa yana fad’in, wlhy idan kina tare da wannan shegen cikin bazaki tab’a samunaba, zaki cigaba da rasa abubuwa arayuwarki kuwa, kamar yanda wad’ancan mutanan suka barki to nima haka zan barki, amma har yanzu kinada sauran dama, inhar kika yarda aka zubar da wannan cikin tofa zan dawo miki a matsayin Abdul d’inki nada, inko har kika cigaba da bijirewa buk’ata ta tofa zaki shiga k’angin rayuwa wanda yafi na yanzu, kuma bazaki raini d’an dake cikinkiba agidannan, dan nafad’a miki ban shirya haihuwaba yanzu, ban shirya zama uba ba yanzu, amma kikayi sakakin d’aukar ciki saikace wata akuya, acikin wata biyu da zuwanki, ke wlhy yanzuma dan abbana ya hanani sakinkine, amma kicigaba da zama akan taurin kanki kigani, idan ban yi waje dakeba, nabaki nanda sati biyu ki yanke wadda zata fisheki, ko ki yarda azubar da ciki, kicigaba da zama dani, ko kik’i yarda nayi waje dake.
Fareeda ta fasheda kuka ta ce, “haba Abdul kayimin adalci mana cikinnan fa d’an kane, ta hanyar aure muka sameshi, kuma namiji shike bada kwan haihuwa, miyasa bazaka gane ba laifina bane? Kuma wlhy ana mutuwa wajen zubar da ciki ko mutum yarasa mahaifarsa, baka gudun d’aya acikin wad’annan yafaru dani ne??.
Abdul yaja tsaki, yafice yana fad’in matsalarkice kuma wannan, nidai nafad’a miki buk’a tata, idan kin kiyaye kin tsira, idan kin cigaba da bijirewa zaki koma gidan tsohone.
Kuka sosai fareeda takeyi dan duk taji kalaman Abdul na k’arshe, ta tura kanta cikin filo tana gunjin kuka, yaune rana ta farko data tab’ajin wani abu mai kama da nadama ya ziyarci zuciyarta, saidai har yanzu tana son Abdul d’inta, tanaji kuma a zuciyarta tafi safiyya sonsa walhy, lallai dolene tabi hanyoyin dazata magance matsalar dake tsakanin ta da Abdul, koda kuwa zubar da cinne, tunda shine tushen faruwar matsalarsu,😳😳 lallai fareeda bakida hankali.
Agidansu sopy kuwa anata shirin bikin uncle kabeer, sopy duk tazama busy sakamakon duk abinda uncle kabeer zaiyi saida ita, ga makaranta damma cikin weekend za ayi bikin, batada wani lokacin kanta, yauma suna gama lecture uncle kabeer yakirata akan tashirya gashinan zuwa zai d’auketa suje wani waje, gudu2 tayi wanka bata tsaya yin wata kwlliyaba ta zura doguwar riga ta shadda tasaka hijjab sai dai yau iyakarsa guywa tad’ansaka turare ta fito.
Bata dad’e da fitowaba shikuma ya shigo cikin makarantar, bayan sun gaisa ta ce, “to uncle mutafi ko?.
Ya ce, “sai mun jira youseef dan hardashi zamuje.
Sopy tai saurin kallon uncle kabeer, uncle dammi sai da shi zamu?.
Uncle kabeer ya ce, “dan yanada muhimmanci atafiyar.
Sopy tayi shiru dan ita kam gsky bata son tafiya tare da shi, inhar yana guri bata sakewa, saboda tsananin kunyarsa datakeji……, muryarsa ce ta katse mata tunaninta, yak’araso yana fad’in sorry na b’ata muku lokaci ko?.
Uncle kabeer ya ce, “A’a, itama aii yanzu tazo.
Sopy ta daure ta ce, “ina yini sir! ?.
Ya ce, “lafya lau maa!.
Uncle kabeer ya tuntsure da dariya ya ce, “one one, kenan.
Suka shiga mota suna dariya banda sopy datad’an murmusa kawai, tunda suka shiga mota sopy tayi tsit, sai dai duk d’agowar dazatayi saitaga uncle G! Ita yake kallo ta madubin gaba, ganin yasaka mata ido saita daina d’agowa ma gaba d’aya.
Kasuwa sukaje, suka lodo kaya, na duk amfanin dazasuyi awajen biki, tundaga kayan abinci da drinks, da duk wani abunda zasu iya bukata, sun siyo dai dai k’arfinsu, suka zubo amota suka kai inda zasu ajiye.
Uncle kabeer ya ce, “auta saura d’inkinki ko?.
Sopy ta ce, “uncle aii telan ya ce, “sai gobe idan ALLAH yakaimu.
Okey to ALLAH yakaimu goben, yanzu bari mu kaiki makaranta ko?.
Ta ce, “dan ALLAH uncle ka kaini gida gobe sai nadawo.
Uncke G! ya harareta, saboda son yawo ko?? To makaranta zamu maida ke, dan goben da safe nine zan fara yi muku lecture, kuma harda test mai zafi, kinsan kuwa idan bak’ya nan hukuncin ki yafi nakowa.
Uncle kabeer ya juyo yana kallonta, to kinji fa, kinyarda na kaiki gidan??.
Sopy ta d’ago ta kalli uncle G!, daya tsura mata fararen ida nunsa masu haske, tai saurin maida kanta k’asa kamar xatai kuka.
Uncle kabeer ya ce, “sopy shagwab’arki tayi yawafa, ko kin manta kin girma, nafa kusa aurar dake.
Aii kamar jira take saita rushe da kuka.
Sukuma sai dariya ta kufce musu, suka fita daga motar suna dariya, uncle G! ya ce, “gsky kabeer bakada kirki, ya bud’e baya yashiga inda sopy take zaune, yakai hannu zai kama hannunta saita k’ank’ame jikinta, shima saiya fasa,.
Cikin taushin murya ya ce, “to kukan ya isa haka, ke dai abu kad’an sai kuka, kabeer ya shagwab’aki dayawa.
Ta turo baki gaba, ya ce, “hummm, ashe idan baki maida bakin nanba zan tsotseshi yanzunnan.
da sauri ta rufe fuskarta, ta kama k’ofa zata gudu, amma sai tajita gam arufe.
Ya murmusa da ina zakije??
Ta ce nidai kutafi na fasa zuwa gidan.
Uncke G! Ya ce, “aii dama dole ki fasa, tunda na hana, ya mik’a mata wata leda ga wanna kiyi kwalliyar biki ko,.
Ta ce, “uncle kabeer da babafa duk sunyimini d’inki.
Ya ce, “to aii nasu daban, nawa daban, su iyayene, nikuma mijine.
Tai k’asa dakai tana fad’in nagode ALLAH yak’ara bud’i.
Ya murmusa dan jin dad’in addu’arta gareshi, yad’ora da fad’in, kamar yanda nayi miki alk’awari gobe zan aika a d’akko miki Aysha.
Da sauri ta ce, “dan ALLAH dagaske sir!.
Uncle G! Ya harareta oh, bazaki daina cemin sir! D’innan ba ko?.
Ta ce, “to aii dai sunankane ko.
Ya ce, “humyim, zanyi maganin bakinki, nan bada dad’ewaba.
“Shiru tayi masa.”
Yayinda uncle kabeer yashigo motar yana fad’in kunga kumuje nifa inada aikin yi, dannaga ku soyayyace agabanku.
Sopy ta ce, “kai uncle nidai dan ALLAH kabari.
Uncle G! Ya koma gaba yana fad’in kaidai anyi uban banza, nikam ban more sirikiba.
Uncle kabeer yay dariya yace, “habawa kaidai kabini ahankali idan ba hakaba na hanaka d’iyar.
Taf, dakasha matsa kuwa, kaga aii kabayar da wuriko?? uncle G! Yafad’a yana tada motar……………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 28~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣8⃣🔸🔶
………..biki dai ya kankama, komai yana tafiya yanda akeso, Aysha k’anwar uncle G! Tazo, sopy tayi farincikin ganinta, itamadai Ayshar! sopy! ta burgeta, tana ganin kuma ida yayansu ya aureta bazasu samu matsalaba, dan suma talakawa ne kamarsu, kuma gidan mutunci.
Duk inda sopy tashiga Aysha na biye da ita, wannan yasa tasamu sauk’in wasu ayyukan, uncle G! Kam bata ganinsa domin suma suna can suna hidimominsu.
Yau aka d’aura auren KABEER MUKTHAR da ASIYA ALIYU d’aurin auren yasamu halartar mutane masu yawa, musamman abokan aikinsa da kuma wad’anda sukayi karatu tare, ga mutanen baba suma, to saimuce ALLAH yasanya alkairi uncle kabeer ALLAH yabada zuri’a d’ayyiba, nanda wata tara mu dawo suna.
Da daddare aka kai amarya d’akin mijinta, su sopy sun isa gidan tun kafin zuwan amarya, amarya da danginta suka iso, anyi musu tarba ta mutunci, bayan an kammala abubuwan al’ada, motoci suka kwashi mutane domin maidasu gidajensu, amma sopy da Aysha sunanan, uncle kabeer ya ce, “su tsaya su gyarama amrya inda aka b’ata, dan k’awayenta sun tafi dan gudun karsu rasa motar dazata maidasu gida, bayan tafiyar kowa suka k’uk’e suka gyara gidan suka bajeshi da k’amshi, wajan k’arfe tara abokan ango suka rako angon k’amshi.
Sudai su safiyya k’ofar gida suka koma domin jiran su, basufi minti talatinba suka fito, motar uncle G! Suka shiga ya maidasu gida, a k’ofar gidansu sopy uncle G! ya ce, “Aysha tashiga gida, Sopy ta ce, “to nima aii gidan zanje.
Ya ce, “A’a zamuyi magana ne.
Dole tayi shiru.Bayan fitar Aysha, uncle G! Ya kalli sopy, ita kuma tayi k’asa da kai, ya d’an murmusa yana fad’in Safiyya! sarkin kunya.
Yanda yakira sunan nata saida tsigar jikinta ya tashi, tabbas babu wanda ya iya fad’ar sunanta kamar uncle G!, yakan fad’i sunan dawani irin yanayi mai saka mamallakiyar sunan cikin wani irin yanayi.
Yay gyaran murya, tareda k’ara ambatar Safiyya!!
Itama cikin sanyin muryarta mai zak’i ta ce, “Na’am.
Yad’an gyara zamansa, ina ganin gobe idan ALLAH ya kaimu zan maida Aysha gida, daga nan kuma zan taho da magabatana domin kawo kud’in aurnmu!!.
Sopy tayi shiru tana tunani, yad’an buga yatsunsa biyu sukai k’ara, ta juyo tana kallonsa, yay murmushi tunanin mikikeyi ne?.
Ta ce, “bakomai, amma dan ALLAH kabar Aysha tad’an k’ara kwana biyu.
Ya ce, “bazai yuwuba Safiyya saboda Aysha tana makaranta kuma kinga gobe litinin, tamayi asarar karatun goben kenan.
Sopy ta ce, “hakane, amma dan ALLAH idan anyi musu hutu zaka kawota.
Karki damu, zatazo insha ALLAHU sannan ma kina gidanki!.
Tasa hannu tarufe fuska.
Humm sarkin kunya kenan, nikam kar kunyarnan ta cutar dani a abayan aure.
Bata ce, “komaiba tabud’e motar ta fita.
Yay murmushi to saida safe tunda babu sallama.
Washe gari uncle G! Yazo d’aukar Aysha, da kuka suka rabu da sopy, inna tanata lallashin Aysha, haba Aysha kukan ya isa haka mana, insha ALLAHU kwanannan ma zata dawo wajenku kinji, kiyi hak’uri kibar kuka ya isa haka.
Da haka dai sopy tarako Aysha wajen uncle G! Dake k’ofar gida, yabisu da kallon mamakin dan ganin idanunsu duk hawaye, ya jinjina kai yana fad’in sannunku da kuka, saikace wad’anda zasu mutu.
Sopy ta gaidashi ya amsa yana kumshe dariya.
Ahaka dai sukai sallama, uncle G! Yaja mota suka tafi, tunda suka tafi Aysha take kuka, saida uncle G! Yadaka mata tsawa sannan tayi shiru.
Cikin fad’a ya ce, “kinbi kin dameni da kuka, saikace har abada bazaku sake had’uwa ba? Inhar bakimin shiruba to wlhy zan tsaya na zaneki anan.
Tasan halinsa sarai dan haka tayi shiru, ta ce, “yaya dan ALLAH kayi hak’uri wlhy aunty safiyya tanada kirki, duk wanda ya zauna da’ita dole yayi bak’in cikin rabuwa da’ita, dan ALLAH yaya kuyi aure da wuri dan tadawo gidanmu gaba d’aya.
Uncle G! Yay murmushi oh Aysha kinda abin dariya wlhy, to wai mi auntyn nan taki tayi miki hakane kiketa yabonta??
ALLAH yaya sunada yawa, yanzu haka bakaga tsarabar datayo minba, ta gwaggo da ban ta baba daban hardasu aunty hafsat ma duk tayi musu suma.
Uncle G! Ya jinjina kai lalai aunty tana jidaku, kenan ni kad’aine batayima tsarabarba??. Aysha tayi dariya to yaya ai kai kuna tare kulum shiyyasa.
A’a bawani muna tare ita dai ta wareni kawai.
Haka sukaita hira har zuwa gida.
Itamadai sopy tunda suka tafi taiyi shiru dan tana k’aunar Aysha, yarinyar tanada shiga rai ga wayo da son aiki, zuwan su aunty NAFISA ne yasaka tad’an ware, suka shiga aikin gyaran gida, da kaiwa mak’ota kwanikansu da sauran abinda aka aro domin yin amfani, dayake duk danginsu anan cikin kano suke, sai yazama babu kowa a gidan sai isu isu, inna dakanta ta shirya karin kumallo sopy taje takaiwa su uncle kabeer…………………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 29~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸2⃣9⃣🔸🔶
……..Gwaggo ta tari autarta da murna, dan kwana biyunnan tayi kewarta, Aysha ta ce,”gwaggo wlhy nayi kewarki kwana biyu, sai dai naji dad’in zuwa kano.
Gwaggo ta ce, “kai auta fad’i gaskiya dai, kinga yanda kikai haske da k’iba a kwana biyunnan kuwa, mikike cine haka? .
Aysha tayi dariya, aii wlhy gwaggo bazasu lissafuba, kai matar da yaya zai aura tanada kirki gwaggo gata mai k’yau…….tayi shiru domin shigowar uncle G!.
Ya ce, “to uwar surutu ince har kin fara zubama gwaggo shi.
Gwaggo ta ce, “to badoleba tayi kewanane aii.
Uncle G! Yazauna a kan tabarmar dake shimfid’e ad’akin yashiga mik’a gaisuwa ga gwaggo.
Gwaggo ta amsa cikin fara’a, ta ce, “ya aikin? Da abokan zama?.
Wlhy lfy law gwaggo sunata gaisheku, da kuma godiya.
Kai haba saikace wani abu, mu abinda kabiru yay mana aii bazamu iya biyansaba.
Uncle G! Yay murmushi, ya ce, “gwaggo ina baba yake?.
Baban ku yana wajen zana idar malam haruna mai gari.
ALLAH sarki, gwaggo malam haruna yarasu?.
Wlhy kuwa d’annan yanzu badad’ewa aka fad’i mutuwarsa, inagama ba’a binnesaba.
To ALLAH yagafarta masa da dukkan musulmai baki d’aya, amma mutuminnan yasha wahalar jinya, ALLAH dai yasa kaffarane.
To amin gwaggo tafad’a tana mik’ewa, bari nakawo muku ruwa, munata surutu ko ruwa ba’a bakuba.
Uncle G! Ya ce, “bakomai gwaggo da kin barima Aysha saita d’ebo aii, gwaggo ta ce, bari nad’ebo tunda natashi, saima ahad’o da abinci, saidai kuma ban bayar ansiyo maka awarar taka ta famaba, wannan tararrabin rasuwar ya mantar dani,, Aysha taso ki siyo masa, ALLAH yasama bata k’areba kinsan Awarar uwaliya kamar nama take agarinnan.
Aysha ta ce, “to gwaggo kawo kud’in??, ki d’akko a k’ark’ashin filo, akwai d’ari biyu.
Uncle G! Ya ce, “karb’i barmata kud’inta, ya mik’a mata dubu d’aya, ta ce, “yaya daka bari na d’auki d’ari biyun dan wlhy sai kaga anata neman canji ak’isamu.
Ya ce, “to, kuma kiyi sauri, dan karki zauna neman zance.
Aysha tafita tana turo baki.
Gwaggo tashigo da ruwa a kofin silba, ta koma ta d’akko samira ta ajiye gaban uncle G!, ya ce, “yawwa gwggonmu sannunki da aiki.
Ta zauna tana fad’in aii kune da sannu, kuda kuka sha hanya, ya d’auki ruwan yasha, yana murmushi, suka cigaba da hira kafin Aysha tadawo.
Badad’ewa Aysha tadawo, sukaci suka k’oshi yafita danyin sallah da ta’aziyyar rasuwar da’akayi.
Baba yashigo, Aysha taje ta taroshi cikin farin ciki, A’a Ayshatu! saukar yaushe??, aysha tayi dariya baba tun d’azu mukazo harda yayama.
Ya ce, “madallah ina yusufan yake?, baba yanzu yafita sallah baku had’uba?, A’a bamu had’uba, k’ila masallaci juma’a yaje sallar dan sune naji sun tada sallah yanzu.
Saida yay gasuwar yadawo, ya tsugunna ya gaida baba, baba ya amsa cikin fara’a, yusufa! ya jama’ar birni?, dasu kabiru ango??.
Wlhy lfy law baba, yanata godiyar d’awainiya.
Kai haba in banda abin kabiru miye na godiya, abun nawa yake, tunda ALLAH bai nufa zamu d’aurin aurenba.
Aii bakomai baba hakanma angode ALLAH yasaka da alkairi, Aysha aii ta wakilceku.
Sun dad’e suna hira, anan nema uncle G! Yasanar da baba maganar tura manya gidansu safiyya, ckin jin kunya yake maganar.
Baba yayi dariya aii ko yusufa nayi farinciki da wannan magana, wlhy dama zamannan naka ya isheni haka, mutane sai surutu sukeyi wai dan kayi boko kak’i yin aure, sun manta aure lokacine.
Uncle G! Yay k’asa da kai yana fad’in gsky ne baba, amma kuyi hak’uri.
A’a aii bakomai yusufa tunda gashi lokaci yazo, aii mu sadai muce ALLAH ya kaimu lokaci, yasa kuma ayi da ranmu.
Akan leb’ensa ya ce, “amin.
Bayan sun gama tattaunawa yafita domin ganawa da matasan k’ungiyarsa kamar yanda yasaba, domin suma tuni sun hallara gurin dasuke had’uwa tunda sunsan da zuwansa.
Da dadadare aunty hafsat suka zo itada libabatu dan tuni Aysha taje gidajensu takai musu labarin matar da yaya zai aura, harda tsarabarsu, sannan ma shi bai dawoba yana waje.
Basu dad’e da zuwaba ya shigo shima, ya ce, “A’a ‘yan uwa kune da daddarennan??
“Sukace mune!!.
Yaja kujera ‘yar tsugunno yazauna, suka gaisa, sukai masa godiyar tsaraba, ya ce, “wace tsaraba kuma aii ni! banyima kowa tsaraba ba.
Aunty hafsat ta ce, “e, auta tace k’anwar muce tabamu ALLAH dai yasaka da alkairi yakuma kawo mana ita lfy.
Uncke G! Ya ce, “to amin, yakuke da yaranku da mazajen!! ku?
Suka ce, “duk muna nan lfy.
Ya ce, “aii haka akeso.
Baba yashigo yana fad’in tofa yau gidan biki akene?
Sukayi dariya, kowa ta gaidashi, sannan sukace munzo sannu da zuwane.
Baba yazauna yana fad’in ince ko har Aysha taje muku?.
Sukace aii baba tun d’azu ma kuwa.
Ya ce, “auta kenan sarkin hidima, nan dai sukayita hira, harma baba yay musu bayanin maganar auren yayansu.
Sunyi murna kwarai da gsk.
Washe gari uncle G! Yataho damasu kawo kud’in aure, anyi musu tarba ta mutunci, daganan komai ya gudana, atake kuma baba ya saka ranar aure nanda wata hud’u, iyayen uncle G! Sunji dad’i domin kuwa babu wani jan rai, bayan sun kammala uncle G! Yakaisu tasha suka hau mota domin komawa gida.
Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, sopy tana karatu, kuma sukan yi hira jefi jefi da uncle G!, Dan bai cika takurata ba, saboda Baya son tasamu matsla a karatunta, yakan taimaka mata akan abinda yashige mata duhu, dukda har yanzu tananan cikin jin kunyarsa bata cika sakin jikintaba idan yana guru, zuwa wannan lokacin kuma labari yabaza makaranta cewa uncle G! Zai auri safiyya.
Wasu har zuwa suke takanas domin ganin mai sa’ar data samu zuciyar tsadajjen namiji mai aji da ilimi irin uncle G!, dayawa sukanyi mamakin ganinta, dan azatonsu farace k’al kuma mai shegen k’yau👩🏻, wasu sukance dama masu k’yau basu cika zab’ar mace mai k’yauba, wasukuma sukanga safiyyan tadace da uncle G! D’in, domin itama tanada k’yau, sai dai k’yawunta mai b’oyuwane, irin wanda saika cika kallonta ko kana tareda ita kullum kake gani, to koma dai miye ‘yammata saiku saurara domin kuwa safiyya itace tauraruwar uncle G!, dan shiyyasan sirrikan daya gano agareta.
Magulmata dai anata aikin gulma, yayinda wasu ‘yammatan suke jin haushinta dan sunnunama uncle G! D’in so amma yay burus dasu, itakam ko kallo basu ishetaba dan bata shiga sabgar kowa, garama Nadiya sukan d’anyi hira amma itama bakomai tasani dangane da sopy ba.
Dan sopy ta daina k’awa bare AMINIYA, anriga anmata tabo azuciya akan AMINTAKA…………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YO[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 29~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣0⃣🔸🔶
……..Akwana atashi babu wuya gurun “UBANGIJI”, biki dai ya kankama, dukkan gidajen biyu sunata shiri, hakama uncle G! Yayi wuyar gani, ita kanta sopy baganinsa takeyiba, sai idan yaje musu lecture, ko kuma idan ya kirata a waya su gaisa.
Yau da yamma Sopy tashigo anguwarsu, tana shigowa layinsu tayi kicib’is da Abdul, suduka gabansu ya fad’i, yabita da kallon k’urullah, itako ta tamke fuska kamar bata tab’a dariyaba, ta ratseshi zata wuce, da sauri yasha gabanta, takauce zuwa gefensa nanma ya tareta.
Ta ce, “malam bani hanya nawuce.
Ya ce, “haba gimbiyata ninefa Abdul d’inki mai sonki da k’aunarki, wlhy ina kewar rashin ganinki, dan ALLAH ki tsaya muyi magana.
Ta balla masa harara tareda jan wani mugun tsaki ta ce, “kaga malam tunkafin na shuka maka rashin mutunci kabani hanya na wuce, wlhy Abdul natsaneka.
Ya rinyse ido ya bud’e dan tabbas kalmar tata ta daki zuciyarsa, ya marairaice murya yana fad’in, Sopy nasan baki tsaneniba haryanzu kina sona, kina cikin b’acin ran abinda yafaru abayane, dan ALLAH kibani dama namiki bayani yanda zaki fahimceni, kece kad’ai nakeso kuma ashirye nake dana aureki ahalin yanzu.
Sopy ta tuntsure da dariya, sannan ta tamke fuska tamkar ba ita tayi dariyarba, ta nunashi da d’anyatsa 👉🏻☹Abdul wai kaine! kake tunanin zama mijina!, tad’an murmusa, Abdul har abada bazan zama shashashar macen dazanyi miji irinkaba, ka d’auka SAFIYYA IBRAHIM KABEER ta sub’uce maka har gaba da abada, ta ciro kati daga jakarta ka karanta wannan shi kad’aima ya isa yabaka amsa, inama gayyatarka, dan nasamu miji mai tarin ilimi k’yau, aji mutunci, kai idan ina lissafa maka abinda ya dangan ceshi tofa sai mu kwana anan,kuma katashimin ahanya kafin natara maka mutane wlhy.
Jiki asanyaye yamatsa mata ta wuce, tunda yafara karanta katin yake fitar da numfashi mai kama da nishi, yajingina da bango gudun karya fad’i, cikin murya kamar mai kuka ya ce, “fareeda kin cuceni ALLAH ya isa tsakanina dake, kuma wlhy yau saikin gayawa aya zak’inta, yanufi gida kamar mayun wacin zaki.
Da sauri muka bishi dan muganewa idanmu abinda zai faru.
To bari mugani fareeda kota zubur da cikin??.
Tunda nagabato b’angarenta nakejin ihun kukanta, wanda inada tabbacin suma mutanen dake gidan sunajinta, amma babu wanda yay yink’urin zuwa yaga abinda yafaru.
Nak’arasa d’akin da sauri nida madina, Abdul ne ke lakad’awa fareeda dukan ‘yan danbe, duk yaji mata ciwo, amma wannan baisa ya daina d’irkartaba, dak’yar muka iya kwatarta, ya bimu da kallo yana huci kukuma daga ina??.
Madina ta ce, “tofa, Abdul maida wuk’ar mu bak’in fareeda ne, yaja tsaki tozaku iya tafiya aii ko.
Na ce, “kayi hak’uri Abdul kabari mu taimakawa fareeda kaga duk ciwone a jikinta, wata uwar harara yasakarmin, to aii ko uwar tace tazo gidannan saita fita, tunda sunce sun sallama mini ita, bareku gayyar sod’i, wlhy tun kafin nabud’e idanuna kubar gidannan idan kuwa bahakaba tokuwa jikinku zai fad’a muku.
Aii kafin yagama rufe baki madina uwar ‘yan tsoro taja hannuna munyi waje, ta ce, “humm aunty bily naga mutuminnan yafara haukacewa wlhy zai iya dukanmu, kekam gaki lutiya idan yasamu wannan tsokar aii kinga takanki.
Na balla mata harara ina fad’in ALLAH madi kin rainani, ni son k’ibar nan tawa nakeyi idan baki saniba.
Amma gsky Abdul bashida mutunci irin wannan duka dayake mata kamar wata karuwarsa, kuma muta nen gidan sunaji amma sunk’i cetonta.
Madina tayi dariya aii ni dad’i nakeji wlhy ALLAH yasa yay mata abinda yafi hakama, aii maganin maci amana kenan, kad’amma tagani.
To yaudai lefe ya iso na sopy, mota guda muta nen GURUM sukayo domin kawo lefen Safiyya.
Akwati uku da karami na sama, babu laifi uncle G! yataka rawar gani, dan lefennan saidai mak’iyi amma yayi atalauce ba a sarauceba, anyi musu tarba ta mutunci, irin wadda suka tabbatar da sunzo gidan karamci, sun kuma tabbatar d’ansu yasamu d’iyar gidan tarbiyya,agidansu fareeda aka amshi lefen dan babanta ne zai d’aurama Sopy aure, aka had’a musu shatara ta arzik’i sukatafi, suna yabon wad’annan muta nen kirki.
Sopy tagama shirinta tsaf, tafito tana fad’in inna nashirya bari natafi kafin su cinyeni da masifarsu, bakamar aunty Nafisa sai bala’i takemin ina b’ata musu lokaci.
Inna ta ce, “to adawo lfy, kuma aii sunfiki gsky tun yaushe suke jiranki amma kina d’aki kina lank’andi, aii mijinki yaga takansa, mutum yay ta abu kamar kwai yafashe masa aciki.
To yi hak’uri inna bari natafi ina k’ara b’ata lokaci.
To ki gaishesu, kicema yayar taku gobenfa sutaho da wuri dan ayi aikin cin-cin d’innan agama da wuri.
To inna zan fad’a mata, tatafi tana dariyar inna, tunda bikinnan yamatso kullum tana kan aikin abubuwa bata ko hutawa .
🔶🔸3⃣1⃣🔸🔶
…………..Da sallamarta tashiga gidan, suduka suka hauta da jaraba, aunty hauwa’u ta ce, ” ‘yarrainin wayo, kin zauna kinata yan kwana mu, saikace mu zai amfana, gwarama ki nutsu dan wannan mijin naki d’an kwalisa gara kije masa zam zam d’inki, ki rik’e abinki tunkafin wata takwace miki, irin wad’anna rubibinsu akeyi.
Sopy ta tab’e baki, nidai baruwana, dan tun wurima idan wannan zancen zakumin na koma, aunty asiya matar uncle kabeer ta tuntsure da dariya, barsu d’iyata wad’annan yayun banzane zoki zauna, aunty nafisa ta ce, “karma tazauna aii ita zai amfana bamuba, hakadai sukaita tsokanar sopy tana musu shagwab’a.
Gyarata suke kamar babu gobe, tundaga jikinta harzuwa inda ba’a fad’a🙈 sunsha gyara, zata zauna agidan auty Nafisa dan suci gaba da gyarata, tunda bawasu k’awaye garetaba wad’anda zasu takura mata.
Bata zuwa ko’ina daga d’aki sai tsakar gida, kunji ‘yar gatan auntys d’inta, wayartama ankarb’a ankashe, hankalin uncle G! Duk yatashi yanaso yaganta kodan su tattauna amma hakan tak’i samuwa.
Ya kira uncle kabeer ya tambaya?.
Uncle kabeer ya ce, “lafiyarta k’alau wlhy, nima haka nemanta nake amma tak’i yarda naganta, way tana wani gida b’oyo.
Tofa, uncle G! Yafad’a, to watake b’oyemawa??.
Uncle kabeer ya ce, “agonta mana.
Uncle G! Yay dariya to shikenan tunda dai lfy ai da sauk’i, amma yakamata kazo gobe mu had’ufa.
Okey to badamuwa, zuwa k’arfe hud’u zan shigo insha ALLAH.
TO ALLAH YAKAIMU.
yau k’unshi amma babu amarya, inna sai fad’a takeyi akan b’oye Sopy amma sunk’i fito da’ita saidai subata hak’uri, can gidan aka kai mai k’unshi tamata ta’iya sosai wlhy karkuga yanda Sopy tayi k’yau kamar ba’itaba, jikinnan yasha gyara, Nadiya kad’ai tasan inda take, dan ita take kula da abinda yashafi k’awayensu na makaranta da wanda sukayi secondary tare.
Sai a daren d’aurin aure aka dawo da sopy gidansu, inna ta rud’e daganin k’yawun da sopy tayi, sai latsa jikinta take tana fad’in kaga yara da dabara mikukaima auta na ne tayi haka?.
Su aunty asiya sai dariya suke ma inna.
Inna ta ce, “A lallai dole nabaku tukuyci dan gyaran dakukaima autata yayi.
MASU IYA MAGANA SUKANCE RANA BATA K’ARYA SADAI UWAR D’IYA TAJI KUNYA, to haka kuwa wannan ranar take ga uncle G! da Sopy.
Ayau dai and’ara auren Youseef Hussein Ahmad da Safiyya Ibrahim kabeer, karkuso kuga wankan shaddar da ango yayi, yayi kyau matuk’a, da yawan d’alibansa da malamai ‘yan uwansa sun halarci d’aurin auren, mutanen GURUM kuwa aii ba’a magana, matasan garinsu d’ai d’aine basu zoba, sai washe baki yake dan farin ciki wasuma bai sansuba, lallai naga taron gagarimin d’aurin aure, abin sai wanda yagani.
Dak’yar na iya nemo muku amarya sopy, itamadai taci gayu cikin wata atamfa mai k’yau, idan natsaya bayyana muku kwalliyarta sai nacika littafin, amma dai tabbas ta had’u tamkar zata gasar sarauniyar k’yau, tana zaune itada k’awaenta agidan su fareeda, dukkanin ‘yan professional writer da Zumunta sunje, sunkumayi rawar gani wajen mik’awa Sopy gudummawa, canna hango Hauwa lele😘 kusada amarya, to sopy saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Wajen k’arfe hud’u aka shirya amarya domin kaita garinsu uncle G!, dan sai ankaita can sun gama bikinsu, daga baya sai angonta yadawo da ita gidansu dake nan kano.
Sopy sai kuka take, dan iyayene suka zagayeta ana mata fad’a da nasiha, irin wadda akema amare, “sai dai wasu amaren basa d’aukar irin wannan fad’an saboda kunnen k’ashinsu”, to ita dai sopy da alama komai yana zama a kwakwalwarta.
Da haka dai aka d’ungunma da amarya zuwa GURUM dake acikin k’aramar hukumar Tsanyawa, tareda gayyar ‘yan uwa da abokan arzik’i, a k’awayenta Nadiya ce kawai taje, muma dai munbi ayari nida gayyar ‘yan group d’ina dan kar abamu labari……………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸3⃣2⃣🔸🔶
………A garin GURUM su Sopy sun sami tarba mai k’yau, daga dangin uncle G!, Suma sunada kirki, ananma biki aka d’ora, da daddare matasa suka warware kid’in daya bama dangin sopy sha’awa, atak’aice an dai sha shagali.
Washe gari bayan sallar azuhur dangin sopy sukayi haramar komawa kano, bayan an k’ara yima amarya nasiha da jan kunne akan sirikanta da dangin mijinta, suka tattaro suka taho, aka baro amarya tana kwasar kuka.
Da k’yar gwaggo ta lallasheta dan ad’akinta suka barota, daga k’arshe gwaggo ta lallab’ata tayi barici, kunga sirikan kwarai masu tattalin matan ‘ya’yansu.
Libabatu ta gyara b’angaren da su sopy zasu zauna kafin sutafi, wato b’angaren uncle G! Kenan, acan gefe yake akatange babu ruwanta da sirikanta saidai idan sun shiga, gyara sosai tayi ma b’angaren, ta amshi turaren wuta wajen gwaggo taje takunna, tak’ara da da wasu turarurrukan data gani ad’akin, azuciyarta ta ce, “oh ni liba, kaga d’akin yaya kamar na mace, nan dai tagama tafito.
Uncle G! Kuwa bayan yagama hidimar sallamar bak’i masu tfy, saikuma yashiga sabgogin sallamar ‘yan uwa da abokan arzik’i dake nan, dakuma mammaida kayayyakin da’aka aro na mutane.
Sai gab da magriba aka maida Sopy b’angarenta, aunty hafsa da kanta ta had’a mata ruwan wanka, Sopy ta ce, “nagode aunty!, aunty hafsat tayi murmushi bakomai k’anwata jekiyi wankan, dan muma tafiya zamuyi, lubabatu nacan tana jirana, sai da safe.
” Sopy ta ce, “to ALLAH yakaimu.
Bayan fitar aunty hafsa Sopy tashiga wanka zuciyarta cike da tunani iri-iri, tagama wanka tafito sukayi kicib’is da lubabatu, lubabatu ta ce, “to amarya muzamu gudu gida, sai gobe nazo cin kazar amarci, kifa ragemin.
Sopy tayi d’an murmushi ta ce, “to.
Libabatu tana tafiya sopy tashiga d’akin, tabi d’akin da kallo babu wani tarkace, katifa ce k’atuwa an lailayeta da zanin gado, sai wardrobe ta zuba kaya itama k’arama, sai kujera doguwa a gefenta akwai firij, saikuma wani tebir da kujera agefensa cike yake da littatafai, da alama library d’in uncle G! Ne, ba laifi d’akin yayi k’yau a talauce ba a sarauceba.
Ta zauna tashafa mai tayi kwalliya mai d’an sauk’i, wata atamfa tasaka siket da riga, sun kama jikinta sosai, ta ja k’aramin tsaki nikam bana son kaya su matseni, amma na lura duk haka aunty hauwa’u ta d’inka min kayana.
Haka ta zauna tana gyaran kai tana mitar d’inkunan, nace ashe Sopy tanada gashi ba laifi, dan dai tana b’oyeshine, tagama ta gyara gurin, sannan tahau sallah, bayan ta idar ta zauna agurin har aka kira sallar isha’i, ta tashi tayi.
Ta cire hijjabin kenan tanufi waje akwatin ta dan d’aukar k’aramin hijjabi wanda baikai girman wanda tayi sallarba.
Uncle G! Ya shigo d’akin da sallamarsa, Sopy tarikice tarasa inda zata dosa, wajen akwatin ko kuwa wajen hijjabin data gama sallah yanzu?.
Shima uncle G! Tsaye yake kam cikin farar shadda k’al yaukam harda hula, sai bulbula k’amshi yakeyi, fuskar nan tasa fayau da annurin angwanci, ya kasa koda motsi dan d’imautuwa da surar Sopy, ya tambayi kansa? wai dama haka sopy take da diri da cikakkiyar sura ta d’aukar han kali, lallai dolene ya godema ALLAHn daya halicci wannan k’ak’yk’yawar sura.
Ahankali ya k’arasa gareta, tasaka hanu tana kare k’irjinta🙅, ta rintse idanu danjin uncle G ya mannata da jikinsa, cak ya d’auketa ya dire saman kujera, shima ya zauna, kallonta yakeyi sama da k’asa kamar yau yafara ganinta.
Itako kanta yana k’asa tana wasa da zoben hannunta, ta daure ta ce, “ina yini?, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda kama hannunta ya r’intse anasa.
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrrrrrr, yaune rana ta farko da namiji ya tab’a kama hannunta, ta runtse manyan idanunta.
Uncle G! Yay murmushi, cikin muryarsa mai dad’i da amo ya ce, “kin wuni lafiya ??.
Cikin jin kunya ta ce, “lfy law.
Ya ce, “ya gajiyar biki??.
“Nanma saida tayi k’asa da kai sannan ta amsa.
Ya ce, “my Sopy aii kuma kunya ta k’are yau, domin kin zama tawa nazama naki har abada.
Ita dai tayi masa shiru, idonta arufe saboda tsananin kunyarsa datake ji, gashi kuma yak’i sakar mata hannu, ya matso da fuskarsa kusada tata, harsuna jin fitar numfashin juna, batayi aune ba taji ya manna mata wata k’yak’yk’awar sumba😘a kumatu. (Kiss)
Tayi wata ‘yar girgiza dan sumbar ta shigeta har cikin kwakwalwa………………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸3⃣3⃣🔸🔶
………..ya d’an murmusa dan ganin yanda taketa kare k’irjinta, yasak’ala hannunsa ta bayanta ya rungumota zuwa jikinsa, aii sai jikin mutuniyar taku ya hau rawa, cikin kunnanta ya ce, “tsawon kwana goma kina b’oyema ganina, yau kuma gani daga ni saike!!.
Ita dai jikinta sai rawa yakeyi, takuma kasa magana, ya hura mata iska a kunnenta, ta bud’e ido da sauri, yay murmushi, Sopy sarkin kunya yafad’a yana shafa jikinta, ya kuma matseta sosai ajikinsa, har saida tayi ‘yar k’ara sannan ya sassauta mata, ya ce, “haba sopy yau baza a yima uncle G!; magana bane? Ko har yanzu fushin tafiyar su uncle kabeer d’in akeyi?, dan ya ce, “min har kukayi sallama kuka kikeyi, kokuma garinmune babu dad’i??.
Sopy ta girgiza kai alamar A’a.
Ya ce, “to minene yasa aka k’iyimin magana??.
Ta daure ta ce, “ba komai kainane yake d’an ciwo.
Uncle G! Yay ‘yar dariya, to ALLAH yabaki lafiya Sopy na!, amma ko dai ana tsoron uncle G! ne??.
” nanma ta girgiza kai batare da tayi magana ba”
Ya mik’e yana fad’in shikenan idan anzo wajen kwanciya zamu gani.
Gaban Sopy yafad’i rasss, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba a kumatu, tayi saurin sharewa, itakam gsky tanada tsoro, ALLAH dai yasa karyay mata komai.
Ledar daya shigo da ita ya d’akko, wadda santin ganin surar sopy yasakashi yarda ta ak’ofar d’aki, ya zauna yana lallashinta akan taci kazar dake ciki, da k’yar yasamu taci akunya ce, yana mamakin kunya irinta sopy, gsky da haka kowace mace take, da ansamu sauk’in lalacewar ‘yammata kai harma zawarawa da matan aure, ALLAH dai ya shirya.
Bayan sun gama cin kazar wadda rabinta duk shi yaci kayansa, dan yana jin yunwa sosai, tunda aka fara bikinnan bai nutsu yaci abincin kirkiba, yaje yay brosh ya dawo, itama taje tayo.
Ya ce, “yana zuwa yanzu zai dawo.
Yana fita ta tashi tacanja kayan barci a gurguje, wani zani tasaka da riga tishet mara nauyi, tasaka k’aramin hijjabi, tayi kwanciyarta bisa kujera.
Ya kai tsawon minti talatin sannan yadawo, yarufe ko ina, yabi sopy da kallo yana d’an murmushi, ahankali ya furta safiyya sarkin tsoro, shima kayan barci yasaka, yad’an fesa turare.
Wajen kujerar datake kwance ya k’araso, ya shafa kuma tunta yana fad’in my sopy aii duk wayon amarya sai ansha manta.
Cak ya d’auketa yana fad’in kinga gurin barcinki nan ya nuna k’irjinsa da baki, saman katifar ya direta, tana jinsa amma tayi shiru, tak’iyin ko motsi dan tsoro da kunya.
Yashiga k’ok’arin cire mata hijjabin jikinta, sai asannan ta motsa ta rik’e hannunsa.
Yay murmushi mai sauti ya ce, “aii dama nasan idonki biyu.
“Tai masa shiru”
Ya ce, “okey aii nasan maganinki, bari kiga nasan yanda zanyi kiyi magana, batayi aune ba taji bakinsa cikin nata, duk iya k’ok’arinta na ta kwace kanta amma ta kasa, ta shiga tsungu ninsa, amma ina shikam baisan tanayiba, tsotsar bakinta yake cikin zafin nama, tamkar mafa raucin zaki🐅, ayayin dayaga abinci, Sopy tun tana tsungu ninsa harta hak’ura tabarma ALLAH.
sai da ya tsotse bakin tamkar zai rabata dashi sannan ya janye jikinsa yana maida numfashi.
Sai a sannan Sopy tasamu bakin yin kuka.
Ya rungumota tsam akan faffad’an k’irjinsa daketa tashin k’amshin turare, ahankali yashiga buga bayanta tamkar wata jaririya, cikin sark’ewar murya ya ce, “to kukan ya isa haka, kinga yi hak’uri ni babu abinda zan miki, yi barcinki kinji my sweet Sopy, cikin sigar lallaahi yake maganar, iska ya shiga hura mata a cikin kunne mai dad’i, ita kanta bata san sanda barci yay awon gaba da itaba, dama ga gajiyar biki.
Shikam ya dad’e baiyi barcin ba, dan kuwa hanka linsa yakai k’ololuwar tashi, anya zai iya cika alk’awarin daya d’auka na barin Sopy har sai sun koma gidansu, yaja wani gwauron numfashi tareda sake manneta a jikinsa, sanda bashida matarma baidamu ba haka, amma yau kodan yaganta a kusa dashine oho, ya tsurama fuskarta idonu, tanata barcinta, dukda yasan barcin cikin tsoro da fargaba ta yishi, ya shafa kanta tareda sumbatar ida nunta yana murmushi Sopy sarkin tsoro yafad’a yana gyar kwanciya.
Haka yayta sak’a wasik’ar jaki har barci yay awon gaba dashi.
Muma muka fito, dan komawa masaukinmu nida marak’isiyya, da madina, da aunty pii pii, da saratu, dan sunce ba inda zasu labari ya wucesu.
Na ce, “magulmata saiku tsaya, nasan kuna bak’in cikin d’an abinda uncle G! Zai banine, idan nagama yad’a labinsune, to kusani kad’an zan baku eheee😜😜😜 …………………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’sala💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 2~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣4⃣🔸🔶
……..Da asuba yatashi yay alwala sannan yatada ita ya ce, “nawuce masallaci, kanta ak’asa ta ce, “to adawo lfy.
Bayan fitarsa itama alwalar tayo tayi sallah, ta d’auki alkur’anin data gani a d’akin tayi karatu, zuwa sannan gari yafara haske, harzuwa sannan uncle G bai dawoba, ta tashi ta gyara d’akin fes, tashare d’an lungun nasu ta wanke bayin sannan tashiga wanka.
Uncle G yadawo motsin dayaji abayi ya tabbatar masada tana wanka, d’akin yashiga yashaki wani k’amshi mai dad’i ya lumshe idanu, yay murmushi mai k’ayatarwa ya ce, “lallai ina son mutum mai tsafta da rashin son jiki, gashi kuma ALLAH ya azurtani da samun mace, ALLAH nagodema da irin wannan tarin ni’imomi daka min.
Batayi zaton yana cikiba, dan haka tashigo d’akin kanta tsaye, gabanta yafad’a yayinda taga uncle G zaune, takalli jikinta daga ita sai zanifa, ta faki idonsa ta rarumi hijjabin sallah ta rufe jikinta.
Lamarin yayi matuk’ar bawa uncle G! dariya amma saiya gimtse ya ce, “yayadai ko kina jin sanyi ne?.
Ta ce, “A’a”.
Ya girgiza kai yana murmushi, taso wa yayi yanufo inda take, aii tunkafin yazo ta durk’ushe k’asa, ya tallafota zuwa jikinsa, saman kujera ya zauna ya d’orata saman cinyarsa ya ce, “haba autar inna aii komai na Sopy mallakin uncle G! ne, kokin manta baba da uncle kabeer sun bani har abada?.
Ta cusa kanta cikin hijjabi, tana mamakin uncle G wai dama haka yake?, wlhy da idan aka fad’a mata haka yake zata k’aryata, amma dan ALLAH jibi abinda yayi mata jiya da daddare, tamkar ba malamin taba.
Jin tayi shiru saiya d’an girgizata, yasa hannu yacire hijjabin daga fuskarta ya ce, “Safiyya! wannan kunyar takifa tayi yawa, nikam zata hanani shan sharafin amarci, amma bari nafara rageta, yafara k’ok’arin kwance zaninta.
Da sauri ta rik’e hannunsa tana fad’in plz uncle! kayi hak’uri na tuba.
Ya tsaya yana kallonta ya ce, “to kin yarda na shafa miki mai da kaina!.
Ta waro ido waje👀 tana kallonsa ta ce, “saikace wata jaririya?”, ya lumshe manyan ida nunsa yana murmushi, aii kema jaririya tace, kafin ki haifa mana wasu jariran.
Ta sinne kanta ak’irjinsa dan kunya.
Sallamar dasukajine yasa ta tashi daga jikinsa, ta d’auki hijjabin tasaka, uncle G ya ce, “kowa nene yashigo, Aysha! tashigo da tire a hannu ta, ta dire sannan ta gaishesu, harta mik’e uncle G ya ce, “Aysha akwai ruwan zafi kuwa agidannan?, zanyi wanka, ta ce, “e, yaya akwai wanda aka dafama baki na wanka, ya ce, “okey to d’auki botiki ki d’ebo min, ta ce, “to.
Babu dad’ewa Aysha takawo masa ruwan wankan, yaje yay wanka, kafin ya fito tayi sauri ta shirya, yashigo yana fad’in sopy kedai bak’ya gajiya da hijjab ko? Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba, ya shirya cikin k’ananun kaya, sannan sukayi karin kumallo.
Dole ya fita don muta nen daketa zuwa ganin amarya.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya a Gurum sopy tana ganin soyayya wajen dangin mijinta da iyayensa, kowa sonta ya ke da son faranta mata, sai abinda takeso zata ci, uncle G kam aii yafi kowa nuna mata kulawa, kuma yanzu baya shige mata, dan yaga tana matuk”ar jin kunyarsa, shima yakula idan yaci gaba da shigemata tofa zai cutu, dan haka ya shareta ko wajen kwanciyama kaida k’afa sukeyi.
Hakan yayima sopy dad’i kuwa, takan fita tsakar gida ta taya gwaggo aiki, da gwaggo tafara aiki ita kuma zataje ta karb’e, hakan yana k’arama gwaggo son sopy a zuciya, dan suna yabawa da halayen yarinyar itada baba.
Da haka sati guda yacika suka fara shirin dawowa kano, saidai nakula sopy bata son dawowa dan garin yayi mata dad’i……………..✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 2~November~ 2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM 💞
🔶🔸3⃣5⃣🔸🔶
………WASHE GARI suka tashi da shirin tfy, uncle G! Yana kula da sopy bata son a tafi.
Nasiha sosai baba da gwaggo sukai musu, dan sunce sopyma tazama d’aya daga cikin ‘ya’yansu.
” Haka yakamata surukai su rink’a d’aukar matan ‘ya’yansu, bawai ki zauna kina kishi da matar d’ankiba, wannan ba dai dai bane, idan kika d’auketa d’iyarkima wlhy saitafi girmamaki da baki daraja, amma daga lokacin dakika fara kishi da ita, tofa rainine zai shiga tsakaninku, shima d’an naki yazo yana jin haushinki a baza awofi, ALLAH yasa mugane”.
Sai bayan sallar azahar suka tafi sopy harda kuka, shi dariya ma take bashi, har sukazo tsanyawa tana kuka, daya kula idan ya k’yaleta ba bari zatayiba, sai ya fara janta da hira, tun tana amsawa ciki ciki harta ware tana kallon hanya da garuruwa, ya tsaya a bichi suka sha mai, sannan suka cigaba da tfy, ta ce, “to nan wane garine?, ya ce, “bichi kenan indai kinji ana fad’in bichi to itace wannan, A’a ni yauma natab’a jin sunan garin, yay murmushi kawai batareda ya ce komaiba.
Gab da la’asar suka shiga cikin kano, ya ce, “yanzu ina kikeso mu fara zuwa? Kona kaiki ki gaida su inna?.
Da sauri ta ce, “e, muje gidan su inna.
Yad’an murmusa batare da ya ce komaiba.
Ganin sun wuce titin layinsu ta ce, “munfa wuce uncle koka manta ne?, yad’an kalleta sannan ya maida kallonsa bida titi, na canja shawara ne aii.
Saboda mi? Sopy ta tanbaya.
Ya dafe sitiyari da hannu biyu saboda naga kamar bai daceba ne, sun kaiki gidan miji kuma kin zo musu yanda suka kaiki, yakamata a samu canji.
ALLAH sarki Sopy ita kam bata fahimci inda ya dosaba, amma ta lura kamar da wata fassara yay maganar, daga nan tayi shiru bata sake maganaba, shima dai bai kuma cewa komaiba, har suka isa anguwarsu.
Gidan ma daidaicine, ginin talaka mai wadatar zuci, da kansa yafita ya bud’e get d’in sannan suka shiga, inda motar ta tsaya nanne kawai fili, daga ita kuwa babu abinda zai k’ara shiga koda mashin ne, suka fito ya ce, “Safiyya ga gidanki to.
Sopy tayi ‘yar dariya ta ce, “naganshi kuma yayi k’yau.
Shima ma dariyar yayi yana bud’e but d’in motar ya sauke kayan duka, ya d’auki wasu yana fad’in namanta kefa makauniyace sai nayi miki jagora a gidan naki, itama d’auka tayi tabishi, yasa mukulli ya bud’e k’ofar falon, wani k’amshi ya daki hancinsu, suka ajiye kayan, ya ce, “zauna na k’arasa d’akkowa.
Sopy tabi falon da kallo tana jinjina kai, lallai iyayenta sunyi k’ok’ari, falon yayi k’yau, komai acikinsa jaa da farine, kujerune set guda sai santa rok (center rug) atsakkiya kujerun shima jaa anmasa kwalliya da fararen fula woyi, sai tebir a tsakkiyarsa shima dai tare suke da kujerun, falon zagaye yake da labulaye suma jaa da fari, sai tv sitan shima irin kujerun an d’ora filasma k’arama akai ta dai dai talaka.
Takai dubanta a dani (dinning) shima ank’awatashi da kujeru da firij, idan bata mantaba ta dad’e da ganin kujerun dani d’innan a gidan aunty Nafisa an lillib’esu da wani k’yalle ashe natane, hawaye suka gangaro a kumatunta na dad’i, bata san da bakin da zata godema iyayentaba da yayyenta musamman ma uncle kabeer dan yafi kowa taka rawar gani acikin rayuwarta, dama yayyenta sunsha gaya mata saboda aurenta suke sana’a tabbas yau ta shaida haka.
Uncle G! ya kamata ya zaunar saman kujera, dan tun d’azu yana kallonta, yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta, ya ce, “Safiyya ba kuka zakiyi ba addu’a yakamata kiyima ‘yan uwanki domin sun taka rawar gani a kanki, ko mak’iyi yaga kayannan saiya jin jina musa, hannunta yakama yanufi kichin da’ita aii sai sukaga abin kallo yana kichin, lallai kicin d’innan ya tsaru nanama komai jaa aka tsara, ya ce, “ga sito d’inki ya nuna mata wata ‘yar k’ofa, koda yake zomuje ki gani, suna bud’ewa kayan abinci suka bayyana uncle G! yasaki baki yana kallon ikon ALLAH harda su drinks yasan wannan tabas aikin uncle kabeer ne, uncle G ya rungume sopy cikin farinciki, ya ce sopy narasa bakin maga wlhy saidai muyita yima su baba addu’ar gamawa lfy, zomuje ki ida ganin ko ina.
Bedroom d’inta ya kai ta, sannan sukaje nasa nanma ya had’u saidai nasa komai ruwan ganyene (green) kenan, ya zaunar da ita a bakin gadoyana fad’in Safiyya kinga gidanki sai dai k’aramine dan na talakane, a hakama nakai tsawon shekara hud’u ina ginashi, dan cikin albashi ake cire wani abu ad’anyi aikin, amma mun godema ALLAH da baiwar da yayamana ta rai da lfy, ahakama munfi wasu, ina fata zakizo mu had’a kai mu zauna kfy, mukuma yarda da k’addara aduk lokacin data riskemu, muyi hak’uri a lokacin da babu ta waywayemu, muzama masu wadatar zuci akan abinda ALLAH ya azurtamu dashi, mukuma gode masa.
Arzik’i bashine rayuwa ba dan da wani arzik’in gara dawwama a talauci, nayi alk’awarin zan rik’eki amana, sannan ina rok’onki damuyi hak’uri da juna a yayin da muka samu sab’ani, mukuma fahimci juna alokacin da wani abu yashige mana duhu, na tabbata wannan zai taimaka mana wajen zaman aure.
Sopy ta ce, “insha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka.
Ya ce, “ALHAMDULILLAH.
yanzu tashi muje na rakaki d’akinki kid’an watsa ruwa ko?.
Ta ce, “to………………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣6⃣🔸🔶
………Har d’akinta yarakata, bayan fitarsa takuma k’arewa d’akin kallo, sannan tashiga wanka, tai murmushi dan ganin jininta yazo, lallai tayi farinci da faruwar hakan, tayi wanka tafito sai dai matsalarta d’aya batada always to yaya kenan zatayi?, tasan daga nan zuwa dare dole ta nemi mafita, inko ba hakaba zai rink’a b’ata mata jikine, tana nan zaune tana sak’a wasik’ar jakai saitaji sallama, ta fito da sauri tana amsawa, saitaga wata ‘yar matsakaiciyar budurwace hannunta rik’e da kwando.
“Yarinyar ta gaidata.”
“Ta amsa cikin sakin fuska”.
Yarinyar ta mik’o mata kwandon dake d’auke da kuloli ta ce, “gashi inji aunty Asiya.
Sopy ta ce, “aunty Asiya kuma?, wace aunty Asiya nasani anan anguwar?.
Uncle G yafito sanye da jallabiya fara, yarinyar ta gaidashi, saida ya amsa sannan ya ce, “Asiya matar kabeer fa, aii bamuda nisa gidansu na nan k’asanmu.
“Lah aii ban saniba”.
Ya ce, “na mantane nagaya miki, ni bari naje masallaci lokaci yana k’ara k’urewa, ta ce, “adawo lfy, yafita yana fad’in ALLAH yasa.
Yana fita Sopy ta Cema yarinyar ya sunanki?.
Ta ce, “sunana fatima amma anace mini ummy, nice name sopy tafad’a.
To ummy dan ALLAH ina zaki sayo mini always ?, ummy ta ce, “aii akwai shago nan bayanku kawo na siyo miki.
Yauwa ngd ummy ‘yar albarka, taje ta d’akko mata d’ari biyar tabata ta fad’a mata irin wanda takeso.
Babu dad’ewa uncle G yadawo, sannan sopy tana kicin tana d’auraye inda zasuci abinci.
A falo yazauna ya kunna tv dan anhad’a komai, wannan duk aikin uncle kabeer ne, ummy tayi sallama ta shigo, ya ce, “O, baki tafiba?, ta ce, “e, aunty ce ta aikeni.
Okey to kawo, ta mik’a masa ledar da canji ta ce, “bari natafi zanje islamiyyane, ya ce, “to ki gaishesu kice mun gode sosai ya mik’a mata naira d’ari, ta ce, “A’a, ngd, ya ce, “karb’i aii ni nabaki, ta amsa tana godiya ta tafi.
Ya bud’e ledar dan son ganin minene aciki, ya ce, “tofa, abinda kuma yafaru kenan, ya ajiye yana fad’in an rusa mini show d’ina kenan.
Sopy tafito da kayan filet, ta dire a saman tebirin dake tsakkiyar falon ta ce, “ga abinci ko akai dinning?, ya sakko k’asa yana fad’in aii ak’asama zanci, dan nagaji dayawa, saida tafara zuba masa abinci ya ce, “af, nama manta yarinyar ta ce, “tawuce gama sak’onki”.
Sopy ta ce, “to, ngd”.
Tagama zuba masa farar shinkafar da miya da lemon kwakwa, sai salat.
ya ce, “kefa?, ta ce, “sai anjima, harararta yayi, ya ce, “sa hannu muci kikuma cire wannan hijjab d’in kisha iska.
Ganin ya d’an d’aure fuska, yasata bin umarninsa, ta cire hijjabin tazauna sunacin abincin, dukda tsakura takeyi kuma a kunyace takeci, bai kuma ce mata komaiba yacigaba da kallonsa yana cin abinci.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Da daddare ya tarar da ita a d’akinta tagama shirin barci harma ta kwanta, ya ce, “taso muyi sallah, saida tayi k’asa da kai sannan ta ce, “ina fashin sallah.
Ya ce, “okey, dama ya tanbayane dan ya tabbatar.
A zatonta d’akinsa zai kwana amma saitaga ya hawo gadon ya kwanta kusada ita, ya jawota jikinsa ya rungume, to ba yadda zatayi tunda babu damar korarsa, saita maida kanta ta kwantar akan k’irjinsa ta hau barci.
♡♡♡♡♡♡♡♡
Rayuwa mai dad’i akeyi agidan uncle G dukda har yanzu babu abinda yashiga tsakaninsu, amma suna mutunta juna kuma uncle G yana nuna mata soyayya, danma kunyarsa datakeji tana sashi k’in yimata wasu abubuwan.
Kullum aunty Asiya saita turo mata kalar girkin daya dace tayi masa ta whatsapp, dan haka take girki mai dad’i da gamsarwa, ta kuma gyare gidan tsaf, uncle G yana jin dad’i dan yanason mutum mai tsafta, kullum sai tayi bak’i ‘yan anguwar suna shigowa ganin d’aki da kuma amaryar kanta, kunsan amarya da farinjini, har yara da ‘yammata ba a barsu abayaba, kuma duk wanda yazo saita kulla masa cin cin da dubulan, dan sopy bata da rowa, abokansama suna zuwa wasu harda matansu, su aunty Nafisane dai har yanzu babu wanda yazo acikinsu, har aunty Asiya datake kusa, garama uncle kabeer yazo sau d’aya shima da daddarene, kuma bai dad’eba yatafi……………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣7⃣🔸🔶
…………yau kwananta biyu da fara sallah, amma tak’i nunawa uncle G! hakan, batayin sallah saiya fita, kokuma ta kulle d’akin sannan tayi, to gashi gobe zai koma aiki, dan hutunsa ya k’are, suna zaune a falo suna kallon labarai sai sukaji ana kwan kwasa gida, uncle G! ya kalli agogon dake manne a bangon falon, ya ce, “to waye da darennan?, sopy ta ce, “bari naje na duba.
Ya ce, “A’a yizamanki barinaje.
Ta ce, “to.
Yaje ya bud’e wasu ‘yammatane su biyu suka gaisheshi, ya amsa fuskarsa babu walwala, dan kunsan uncle G! A gaban ‘yammata baya sakin fusaka, ya ce, “yaya dai?, ganin yanda ya had’e fuska sai suka daburce d’aya ta ce, “dama yarinyace tafita gida tun d’azu shine muke tunanin kota zo nan?.
Ya ce, “A’a, babu kowa nan gidan.
Sukace to mun gode saida safe.
ALLAH yakaimu yafad’a yamaida get d’in ya rufe, ya koma cikin gida, sopy ta ce, ” Suwaye? ALLAH yasa dai lafiya?.
Uncle G! yazauna yana fad’in wasu ‘yammatane wai yarinya suke nema, yarinya kuma anan gidan?, ya ce, “haka dai sukace.
Sopy ta ce, “sudai tasuce ta kawosu zasuce, nima na fahimci haka aii.
Wayarsa ta shiga k’ara alamar kira, ya d’auka, cikin zolaya ya ce, “surikina yagarinne?
Uncle kabeer ya ce, “haba malam daka d’aukeni sikin aii saika kwantar da murya.
Uncle G! yay dariya, aii dan baka kusane amma atsugunne nake yanzuma.
dariya sukayi gaba d’aya, uncle kabeer ya ce, “sonake nace maka yakamata gobe muje wajennan damukai magana ranar.
okey to babu damuwa saimuje, ina uwar biyu?, uncle G ya tanbaya.
Wlhy kaganta nan tana tayimin shagwab’a kasan mai ciki sai ahankali, ina my sweet Sopy?.
tana nan lfy gata nan kusadani.
To kagaishemin da ita saida safe, zataji ALLAH ya kaimu goben lfy.
Bayan ya ajiye wayar ya kalli sopy, kabeer yana gaisheki, ta turo baki cikin shagwab’a ta ce, “shine baice abaniba.
Yanda tayi maganar saita burgeshi, ya ce, “to bari nakira shi saiku gaisa, karkiyi kuka ‘yar gatan uncle kabeer, zoki karb’a wayan.
Azatonta da gsk yakeyi, saita tashi taje wajensa, tana k’ok’arin durk’usawa k’asa, ya jawota jikinsa, yana fad’in kinga wajen zamanki nan.
Ta ce, “to kira mini uncle d’in mu gaisa.
Yaja hancinta aikece uncle d’in, bawani kiranshi dazanyi, tashima na aikeki, ta tashi tsaye, saida yayi mata wani shu’umin kallo sannan ya ce, “yauwa je d’akina ki d’akko min ALKUR’ ANI yana nan gefen gado.
sofy ta ce, “to, shaf tamanta shirinta, bata kuma gane manufarsa ba, tanufi d’akinsa ta d’akko Alkur’ani, ya karb’a yana wani shu’umin murmushi mai kamada na mugunta, saman tebir ya ajiye Alkur’anin ya ce, “Sopy dama kin fara sallah?.
Gabanta ne ya fad’i rasss dan tanbayar tazo mata a bazata, ta daure ta ce, “e, ya kwanta a kujerar yana wata ‘yar dariya ta mugunta.
Sopy ta ce, “mugu d’an masa.
Daga nan kallo suka cigaba dayi, saidai kallo d’aya zakayima sopy kagane tana cikin wani hali mai kamada tsoro.
K’arfe goma dai dai ya mik’e yana fad’in tashi muje mu kwanta dare yayi, Sopy ta mik’e jiki a sanyaye tayi gaba yabita abaya yana mata gwalo😜.
Bayan sun shiga d’akinta ya ce, “ki sameni a d’akina yau acan zamu kwana, yafice abinsa batareda yajira amsartaba , tabishi da kallo kamar zata fasa ihu.
Ba yanda zatayi dole tayi sabon wanka tayi shirin barci, tad’an dad’e tana sak’a wasik’ar jakai, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, ya lek’o ya ce, “wai har yanzu baki gamabane?, ta mik’e kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Ad’akinsa ya ce, “tabiya shi suyi sallah, raka’a hud’u sukayi yayta kwararo musu addu’oi, iyakar sopy ta rink’a cewa amin, ya dafa kanta yay addu’a harda ‘yan kwallansa, a zuciyar sopy ta ce, “namiji da kuka?.
Bayan sun idar ta linke sallayar, ya canja jallabiyarsa zuwa kayan bari, yajuyo yana kallonta bazaki cire hijjabin bane?, ko bakijin zafi.
Ta d’aga kai alamar e, yay d’an murmushi a zuciyarsa ya ce, “duk dai wayon amrya sai ansha manta, yak’araso ya zauna kusada ita yakama hijjabin ya cire, tad’an takure jikinta kamar maijin sanyi.
Ya ce, “inga fuskarki kamar wani abu a saman idonki, ta d’ago fuska batare da wani tunaniba, ya kama fuskarta da hannu biyu yakai bakinsa kamar zai hure mata abun, bata ankaraba taji bakinsa a cikin nata, kissing d’inta yakeyi cikin kwarewa, ahankali ya kwantar da ita saman gadon, dahaka hannuwansa suka fara shiga inda baitab’a zuwaba, Sopy tafara hawaye, nidai ganin uncle G! yau dgske yake, yasa nayo waje abina, dan kar kallon kurullar yayi yawa🙈😜………………✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣8⃣🔸🔶
………..Safiyya yau anzama cikakkun mata, saidai tasha wahala sosai sai kuka takeyi, uncle G ya rugumeta yana lallashi da sa mata albarka, ya kwantar da’ita ahankali ya ce, “bari nayi wanka sai kema kiyi.
Bayi yashiga dominyin wanka zuciyarsa cike da farinciki irin wanda baitab’a shigaba a rayuwarsa, lallai aure rahamane kuma ni’ima ne.
Sopy taja bargo ta kudundune danjin sanyi yana shigarta, wani wahalallen barci ya d’auketa, uncle G! yafito yana fad’in my sopy tashi kiyi wankan, ganin tayi shiru saiya hawo gadon, ya yaye bargon saiyaji jikinta da zafi rau, gashi dukta jik’a filon da hawe da zufa, yad’agota zuwa jikinsa yana fad’in sorry Safiyyana, ALLAH yay miki albarka kinji, ya azurtamu da zuri’a tagari, zanin gadon yasa ya goge mata fuskarta, ya kwantar da’ita, yanufi kicin.
Shayi ya had’o mata mai kauri, yatada ita zaune, ta ce, “itafa ta k’oshi, ya ce, “daure kisha kinji, saikisha magani mukwanta, lallab’ata yaytayi tad’ansha kad’an, ya bata magungunan zazzab’i, sannan ya rungume matarsa suka shiga barci mai dad’i.
☆♡☆♡☆♡☆♡☆♡
Bai san yayi b’arnaba saida safe, dan sun makara, yatada ita dan tayi wanka tay sallah, amma takasa tafiya, tanayin taku d’aya taji wani azababben zafi ya ratsa har kwakwalwarta, cikin shagwab’a ta ce, “woyyo ALLAH na inna.
Uncle G ya k’araso da sauri ya tallafota zuwa jikinsa ya ce, “yaya dai?, cikin shagwab’a ta ce, “zafi.
D’aukarta yayi cak yakai bayi, ruwan zafi ya had’a yaymata gashi, tanata zuba masa shagwab’a, ya taimaka mata tayi wankan tsarki, sannan ya nad’ota a tawul kamar wata jaririya.
Tana idar da sallah ta kwanta akan sallayar dan barci takeji, uncle G! yashigo da tire a hannu ya dire agabanta, sopyna tashi kiyi break saiki kwanta gaba d’aya, da k’yar ya lallab’ata taci soyayyan kwan da shayi, bai takurataba dan lallab’ata yakeyi, bayan tagama ya kwashe kayan yazo ya canja zanin gadon, sannan ya d’auketa ya maidata saman gadon taci gaba da barcinta, shima ya kwanta yarungume kayarsa suka lula duniyar barci.
Sai k’arfe d’aya da wani abu suka tashi, sopy ce tafara tashi, ta lallab’a ahankali ta gudu d’akinta, uncle G! yana kallonta yay murmushi kawai dan ganin yanda take sand’a, shima tashi yayi yashiga wanka.
Itama sopy ad’akinta wankan tashiga, dan har yanzu jikinta ciwo yakeyi, tafito tayi kawlliya mai sauk’i tasaka doguwar riga ta atanfa, tana tsaye gaban madubi tana fesa turare uncle G! yashigo, ya rungumeta tabaya yana fad’in kingudo kin barni to gani na biyoki aii.
Tai kasa da kai dan kunya, ta ce, “ina kwana?, lafiya law sopyna, yaya kuka?, da kiransu inna da baba.
Hannu tasaka ta b’oye fuskarta🙈, dan takula zolayarta yakeyi, ya ce, “bari naje massalaci nadawo
Ta ce, “to adawo lfy, karfa ki dafa komai zanzo mana da abinci, dan yau ranarkice Autar inna.
Ita dai murmushi kawai take, amma kunya ta hanat yin magana.
Babu dad’ewa yadawo musu da abinci, lokacin sopy ta gyare gidan ta bad’eshi da k’amshi, da kansa yarink’a bata abincin, ita kuma tana zuba masa shagwab’ar datake k’ara masa sonta.
uncle kabeer yakirashi ya ce, “subar tafiyar sai gobe.
aii dama surikina dole abarta sai goben, dan dama zankiraka, yau babu mai ganina a waje.
Kai mutumina saboda mi? Uncle kabeer ya tanbaya.
A’a, basai kajiba kaidai abar kaza cikin gashinta kawai goben ma had’u.
ALLAH yashiryaka youseef kazama marakunya yanzu.
Uncle G yay dariya, idan yatashi ya shiryamu tare nida kai, suka tuntsure da dariya kowa yakashe wayar.
Haka uncle G yacigaba da tarairayar sopy awannan rana, komai shi yake mata, sopy ta ce, “a zuciyar wato su maza abinda suke so kenan?.😜………………..✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣9⃣🔸🔶
…………….JAMA’A!!! yakamata mu way wayi fareeda amaryar Abdul😜,
Saida na d’an lek’a saboda gudun jarabar ummar Abdul sannan nashiga, ba kowa atsakar gidan sai yara daketa wasa, ban kula kowa ba nashige abina, dan yaran gidan ba kunya suka cikaba, atsakar d’aki na tarar da fareeda tayi d’ai d’ai, sai dai kallo d’aya zaka mata kagano tana cikin damuwa, dan kuwa tarame tayi bak’ik’k’irin sai dogon hanci da idanuwa gwalo gwalo, sai ciki ritsitsi a gaba.
Ta tashi da sauri dan jin sallamata, tana ganina tasa kuka yauwa bily! wlhy nayi farincikin ganinki, dan ALLAH ki taimakeni wlhy Abdul zai kasheni a gidannan, ga kowa ya tsaneni bily! plx ki taimaka min.
Na zauna ina fad’in fareeda! wane irin taimako kikeso in miki, kindai san halin mijinki da surukarki.
Bily! wlhy idan baku taimakeniba kasheni zasuyi yanzu haka tun jiya cikina da bayana suke ciwo amma yak’i kaini asibiti, tunda akayi bikin Safiyya! al’amura suka k’ara lalacewa, ya ce, “yanda narabashi da Safiyya! to nima bazanyi farinciki ba a gidansa, ta rushe da kuka mai tsanani.
Kamar daga sama Abdul! yafad’o d’akin, yabini da kallon rainin hankali, wayke bily! kike kowa? Banace karna k’ara ganinki a gidannanba ne?.
Na ce, “haba Abdul, kaiwa “ALLAH DA MANZONSA”, kabari na taimakawa fareeda! kaga batada lafiya, kasan kuwa mai ciki saida kula.
Harara ya watsa mini, cikin fushi ya ce, “wlhy idan baki bar gidannanba zan karya miki k’afar dama.
Na zaro ido waje😳, A’a, Abdul name dazan zauna ka karya min k’afar dama, ka cuci mijina!!, kaga tafiyata, fareeda! ALLAH yabaki lafiya, nai waje.
Abdul! yaja tsaki yana fad’in bak’ar banza kawai, na ce, “oho nagodema “ALLAH” dayayini haka, aii fari bashine k’yauba.
Ina fita yashiga jibgar fareeda! Kamar ALLAH ya aikoshi, dan ubanki banace karna sake ganin wani naki a gidannanba, koda kud’in ubanki muka gina gidan?, dukanta yake kamar yasamu jaka, itako sai ihu takeyi, nanko jini yafara ambaliya, yau dai ansamu ummarsa tashigo wajen, ta ce, “Abdul mitayi makane?.
Umma kibari na kashe shegiyarnan tunda iyayenta ma ba sonta sukeyiba, dak’yar umma ta karb’eta.
Ina tsaye a k’ofar gida tausayin fareeda! duk ya cika min ciki, sainaga an kwasota kamar kayan wanki jini nata kwarara, ko numfashin kirki batayi.
Mai adai daita suka tare, suka tafi asibiti.
To fareeda tsuntsun d’ai da yaja ruwa shi ruwa kan doka,, kowa kuma yataka rawar wani tofa yarasa filin taka tasa,, ALLAH dai ya shirya.
☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆
Agidan uncle G! Kam Sopy sai shan tarairaya take, yanzuma suna falo zaune suna hira, kan sopy yana saman cinyar uncle G!, hannunsa na shafa gyararren gashinta daketa tashin k’amshi.
Cikin murya mai dad’i da taushi ta ce, “uncle G!!, ya ce, “Na’am Sopyna ya akayi?, tai shiru dan tana jin shakkar fad’ar abinda ke ranta, yad’an lek’a fuskarta ya ce, “miye damuwarki amaryata?.
Tasa hannu tarufe fuska dan jin kunya, yay ‘yar dariya sopyna ai kunya ta k’are kuma, yanzu an wuce wajen, dan Safiyya! tazama youseef!, youseef! yazama safiyya! koba hakaba?.
Ta ce, “hakane”
Ya ce, “ato.
Fad’imin kome kikeso indai baifi k’arfinaba zan mikishi.
Ta ce, “komiye?.
Ya ce, “e.
Dama maganar komawata makarntane dan ALLAH yaushe zan koma, kaga anata wuceni a karatu.
Sai da yad’an murmusa sannan ya ce, “to, kibari saikin warke, saiki koma, tunda nima jibi zan koma aiki, hutuna ya k’are.
Saida ta shagwb’e murya sannan ta ce, “ALLAH nifa lfy ta k’alau.
Kai sopyna fad’i gsky dai, kecefa d’azu kikace min jikinki duk ciwo yakeyi harda kuka kuma.
hannu tasa ta rufe fuska tana dariya, ya ce, “ato, kedai kika fad’a da kanki, dan haka kibari sai nestweek sannan mun k’ara shan amarci saiki koma.
b’oye fuskarta tayi acinyarsa, tana fad’in kai uncle ALLAH kana bani kunya.
Ya d’ago duskarta yana murmushi to bani kunyata sopyna.
Ta ce, “to, bayanzuba.
Ya ce, “nikam yanzu nakeso, yay kissing d’in goshinta, ta runtse ido kam dan kuwa sumbar ta shigeta.
Ya ce, “sopy matsoraciya mai kuka, dan ALLAH uncle kayi hakuri karka min da zafi, wayyo innata baba kazo ka taimakeni, yafad’a yana kwaikwayon muryarta.
D’aki ta nufa da gudu, dan taga zolayar tayi yawa.
Koda sukazo wajen kwanciya saitaita d’ari d’ari dashi, dan tsoron kar abinda yafaru jiya yasake faruwa, uncle G! ya rungumeta yana fad’in kwantar da hankalinki sopyna babu abinda zan miki barci zamuyi, ita dai tayi shiru amma zuciyarta cike da tsoro, ya cire mata rigar barcin dake jikinta way haka yakeso sukwana.
Bargo yaja ya lullub’esu ya cika hannuwa da🙈kundai gane, sukayi shiga barci mai dad’i……………….✍🏻
Assalamu alaikum, ina mik’o d’unbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke, da godiya mai tarin yawa, ngd da bibiyar books d’ina da kuke yi, harma wad’an da suka fara karantawa yanzu, luv u oll😂😂😂👍🏻.
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞U MY FAN’s💞💞…✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣0⃣🔸🔶
………….Yau tsawon kwanan fareeda uku a asibiti, ta haihu amma d’an baizo da raiba, kuma tun randa su umma suka kaita asibitin basu sake way wayarta ba, yau kuma tana tashi tayi gamo da takarda saki uku a gefen gadonta, kuka take rurus tana dana sanin hali irin nata, yau ga wanda ta fifita akan iyayenta ya gujeta, ta raba zuminci mai dank’o da kusancin dake tsakaninta da aminiyarta saboda Abdul, ta cutarda masoyiyarta saboda Abdul, ta yaudari abar k’aunarta saboda Abdul, taci amanar aminiyarta saboda Abdul, amma yau yarasa abinda zai saka mata dashi sai saki uku, sakin wula k’anci da toxarci, itakam ta shiga uku yanzu wazata dosa, tasan daga iyayenta har yayyenta babu mai saurarenta, tasan babu wadda suka tsana kamar ita ahalin yanzu, takuma rushewa da kuka mai tsuma rai, wata sister tashigo tana fad’in baiwar ALLAH lfy kiketa kuka haka?.
Fareeda ta ce, “babu komai.
Okey sister tafad’a, dama an sallamekine, dan wani mutumi yazo yabiya kud’in.
Fareeda ta ce, “to ngd, ta had’a inata inata tabar asibitin, zuciyarta cike da bak’in ciki, dan bata san inda zata nufaba, tasan ko giyar wake tasha bazata fara zuwa gidansuba, Dan mahaifinta ya gindaya mata sharad’i akan zuwan irin wannan ranar, takuma amince saboda lokacin giyar son Abdul tana kwasarta, lokacin da idanunta suka rufe ta manta da zuwan irin wannan rana, yauga ranar tazo mata batareda taci ribar abinda ta shukaba, saima asarori data tafka marasa adadi, wanda bazasu lussafuba, haka tacigaba da tafiya tana zubar da hawaye batarda tasan inda ta dosaba, ga jiri na d’ibarta saboda yunwa dan ta manta rabonta da cin abinci, ji kake wani kuwwwwwwww kacammmmm!!!!!, wani mai mota ya b’arar da ita a titin, da sauri mai motar yafito yana salati, kan kace mi mutane sun fara taruwa a wajen, mai motar ya ce, “a taimaka masa yasakata a mota, asibiti ya nufa da’ita cikin hanzari.
♡¤¤¤¤¤♡¤¤¤¤¤♡¤¤¤¤¤¤¤♡
Sopy tanata safa da marwa dan tun d’azu take kiran uncle G! Yak’i ya d’aga, ta kira uncle kabeer ya ce, “basa tare, aii saita k’ara rud’ewa, can taji ana kwan kwasa k’ofa tatafi da sauri ta bud’e, saitaga uncle G!, cikin matuk’ar rud’ewa ta ce, “uncle lafiya tun d’azun nake kiranka kak’i kad’aga?.
Yad’an rungumota zuwa jikinsa yana fad’in lafiyarnan da suk’i sopyna, amma mun godema ALLAH, yasaketa yana fad’in bafa ni kad’ai bane harda bak’uwa.
Ta ce, “bak’uwa kuma tana ina?.
Uncle G! yad’an lek’a ya ce, “shigo mana.
Bak’uwar ta ce, “to.
Tana shigowa sukayi arba da Sopy, cikin zaro ido😳 Sopy ta ce, “fa ree da!! Kece?.
Itama cikin matuk’ar razana da rud’ewa ta ce, “Safiyya!!, aisaita zube gurin asume……………..✍🏻
Tofa k’ak’ak’a k’ara, shin Sopy zata amince da fareeda kuwa?, ko ko itama zata koreta ne?, idan ta amince da ita zata yafemata kuwa?, shikanshi uncle G! Idan yasan wacece fareeda zai amince ta zauna dasu?, ni kad’aice mai baku wannan amsar dan haka kubiyoni………………….✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 6~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣1⃣🔸🔶
………..Uncle G! Ya kalli sopy da sauri dama kinsantane?.
Sopy ta juyar da kai gefe ta ce, “fareeda ce fa, kuma tunda naganku tare nasan ka san ko wacece, tana fad’ar haka tanufu d’aki tana hawaye.
Ran uncle G! Ya b’aci, amma saiya danne yashiga kiran sopy! Sopy!!.
Banza tai masa tashige d’aki cikin sauri, yarasa abinda zaiyi ga fareeda kwance a sume, gashi yakula ran sopy a b’ace yake, ruwa yad’akko ya yayyafama fareeda takawo numfashi.
Ya ce, “sannu”.
Ta ce, “yauwa, saikuma tasaki kuka yayinda tatuno abinda yafaru yanzunnan tamkar amafarki, cikin hawaye ta ce, “dan ALLAH kabarni natafi, nagode da taimakon daka min, amma ban cancanci zama gidannanba.
Ya ce, “saboda mi zakice haka?, taja hancinta kad’an tana dubansa ta ce, “saboda bazan iya zama a k’ar kashin inuwa d’aya da safiyya ba, ina matuk’ar jin kunyarta, sannan nasan safiyya tanada hak’uri, ammafa idan tayi fushi babu mai iya sauketa.
Ya ce, “A’a, bazan barki kitafiba, barema kunsan juna keda matata, karki damu nidai ki amince zaki zauna damu, nikuma nayi miki alk’awarin zan shawo kan safiyya harta fahimceki, yanzu tashi ki kwanta saman kujera.
Fareeda ta ce, “to, amma nasan sopy bazata tab’a fahimta ta ba, dan ban cancanci a fahimceni ba.
Ya ce, “karki damu ina zuwa, d’akin sopy yanufa saidai ta kulle d’akin da key, yabuga mata amma tayi burus dashi, fita yayi yazagaya wajen window d’inta yalek’a, tana zaune akan kujerar madubi, takifa kanta saman madubin tana kuka, uncle G ya ce, “ALLAH idan baki bud’e min k’ofarnanba zan matuk’ar b’ata miki rai😎, bai jira amsartaba ya zagayo, sai yatarar ta bud’e k’ofar.
D’akin yashiga, amma yanzu takoma saman gado, ya ce, “ki tashi ki had’a mata ruwan zafi tayi wanka, kibata wasu kayan tacanja najikinta.
Tashitai tana hawaye😭 tacika umarninsa.
Saida yaga ta had’a sannan yakira fareeda tashiga wanka, sannan ya fita.
Sopy ma fitowarta tayi falo tazauna, tana kuka.
Shikam uncle G wanka yashiga, amma tunaninsa yana kan sopy, ya kula tashiga cikin damuwa dayawa, to amma mi wannan matar tayi mata haka da zafi, kodayake yaji takirata da suna fareeda, kuma yasan fareeda a cikin tarihin rayuwarta, wannan yasa yad’an zargi wani abu, saidai kukan datakeyi yatab’a zuciyarsa, amma yasan dole saiya nuna b’acin ransa kafin tayi abinda yakeso, da wannan sake2n yagama wankan, yafito yay shirinsa cikin k’ananun kaya, yayi k’yau kamar matashin saurayi.
Falon yafito yanufi dinning ya zauna, sopy tana zaune tana kallonsa, shima ya juwyo ya kalleta ya ce, “yau baza’a bani abincin bane??.
Sopy ta mik’e tana zumb’ura baki😒, shidai binta kawai yake da kallo, dan dariya take bashi amma saiya gimtse, ta zuzzuba masa abincin sannan takoma falo abinta.
Baice komaiba yahau cin abincinsa, sai dai lokaci2 yakan kalli inda sopy take, yagama ya dawo falon shima, ya ce, “kije ki kaimata abinci itama, idan tagama saitasha magingunan ta kwanta.
Sopy tak’ara cika da haushi, amma takasa magana dan ganin yanda uncle G ya tsare gida😕, babu damar yin jayayya dashi, ta mik’e tanufi dinning tad’iba abinci tatafi d’aki.
Uncle G ya bita da kallo shi kam tana bashi dariya, Dan haka yad’an murmusa tareda fad’in ‘yarrigima.
Taje d’akin ta tarar fareeda tafito wankan tana zaune tana shafa mai, ko kallon inda take batayiba ta ce, “ga abincinan ya ce, “kici, idan kina kuma buk’ata ki kwanta, tai waje batarda tajira amsar fareedar ba.
Fareeda ta bita da kallo tana zubar da hawaye masu zafi, wai yau itace da sopynta suke zama doya da manja, sopyn dabata iya barci saita ganta, sopyn dabata walwala idan bana kusada ita, sopyn dake k’aunarta da sonta, takuma matso wasu hawaye kamar ruwan sama,😭bataga laifin sopy ba, dan ko itace abinda zatayi kenan, taja abincin ta hau ci, dan tana matuk’ar jin yunwa, cin yunwa tayi masa dan andad’e ba’a had’uba 😜😜.
A falo kuka zaman kurame aka cigaba dayi, har akan kira sallar magriba, yashirya yatafi masallaci, itama saita shiga d’akinsa domin yin sallahr, dama basu cin abu mai nauyi da daddare, dan haka ta d’akko alkur’ani tashiga karatu har akan kira sallahr isha’i…………✍🏻
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 6~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣2⃣🔸🔶
………….Uncle G yadawo daga masallacin, ganin sopy bata a palon sai yayi tunanin tana d’akinta, yanufi d’akin amma bata nan, fareeda ce kawai take barci, sai yaje kichin, nanma bata nan, dan haka yanufi d’akinsa, tana zaune a bakin gado ta rabga uban tagumi, uncle G yay wata sassanyar ajiyar zuciya tareda girgiza kai.
Kusada ita ya zauna, amma duk bata sani ba, ya jawota zuwa jikinsa, tai firgigit alamar dawowa.
Ya ce, “haba Safiyya wane irin tunanine haka??, ta fara mutsu2n kwace jikinta tana wani zumb’uro baki.
Ya kuma rungumeta tsam ajikonsa ya ce, “kinga yi hak’uri muyi magana ta fahimta.
Cikin shagwab’a ta ce, “ni dai ka k’yaleni, ba fareeda ta finiba!!.
Ya sumbaci bakinta ya ce, “ni na isa, aii youseef! sai Safiyya!, aurenmufa yafi auren zobe💍, yanzu dai tashi muyi magana.
Ta tatashi tana wani zuzzun b’uro baki😒, yanaso yayi dariya, amma yana tsoron karya sake tunzurata, dukda haka saida yad’an dara.
Ta ce, “O, dariyama kake min!.😏
Ya ce, “A’a, aii ke d’ince duk kin wani burkice min!.
Shiru tai masa, dan shima haushi yake bata😏.
Jawota yayi suka hau kan gadon sosai suna fuskantar juna, ta rintse ido kam, dan ganin yanda ya k’ura mata idanu, yay ‘yar dariya tareda had’e bakinsa da nata, soyayya mai tsafta yashiga nuna mata, yayinda lamura suka fara nisa sai tsoro yashigeta, ta tuna wahalar datasha kwana uku dasuka wuce, tafara mutsu2n kwace jikinta, amma ina tariga tazo hannu, dole ta hak’ura yaci gaba da sarrafata yanda yaso, har yakai ga zuwa inda yake kwad’ayi🙈.
Dukda yau batasha wahala kamar ranarba, amma tad’anji jiki, bayan komai yanatsa saiya shiga tsokanarta wai matsoraciya, tasa hannu ta rufe fuska🙈.
Yaudai tare sukai wanka, sopy tanata wani nok’e2 dan kunya, shiko gogan naku ko ajikinsa, d’akinta taje ta canja kaya, dan har yanzu fareeda barci takeyi.
A palo ta iske uncle G!, ya ce, “Sopyna yunwa nakejifa.
Ta ce, “yunwa kuma?.
Ya ce, “wlhy kuwa, bakin kwashe abincinba.
Tad’an zaro ido😳 tana fad’in yaushe naje cikinka na kwashe maka abinci?.
Ya ce, “zona gaya miki.
Sopy tayi dariya ta ce, “nak’i wayon”.
“Shima dariya yayi.”
Kichin taje ta had’o musu abinci mai d’an sauk’i, ya ce, “to bak’uwarmufa??.
Saida tad’an rage fara’a sannan ta ce, “to, aii barci takeyi.
Uncle G! ya ce, “saiki kai mata ki ajiye, idan tatashi zuwa anjima basai taciba, to, kawai ta ce, “masa”.
Bayan sun gama suka zauna kallon labarai, sai zuwa goma ya ce, “tashi muje mu kwanta kinga gobe idan ALLAH ya kaimu zan fara zuwa aiki, ta ce, “haka ne.”
♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡
Saida suka kwanta ta ce, “uncle!!.
Ya ce, “Na’am,
Wai dan ALLAH a ina ka ga fareeda ne?.
Saida ya rungumeta ajikinsa sannan ya ce, “kin daina fushin da nine?, ta ce, “nidama ba fushi nakeyi da kaiba aii, kawai dai rainane ya b’aci, amma kayi hak’uri bazan sakeba.
Yay mirmushi tareda sake rungumeta sosai yana shafa bayanta, ya ce, “na hakuta sopyna, amma kinsan ban tab’a ganin fareeda ba, nadai santa a labarine kawai.
Ta ce, “hakane”.
ya gyara kwanciyarsa zuwa rigingine, ya ce, “bayan fita ta daga gida, asibiti na nufa, dan dubo yayan faruk da baida lafiya, nafito kenan tsautsayi yasa na bige fareeda da mota akan titi, wannan yasa na d’auketa muka koma cikin asibiti, aka karb’eta da gaggawa dan a sume take, amma “”ALLAH gafurun rahimun”” sai ta farfad’o da wuri, kuma babu inda taji wani mummunan ciyo saidai d’an guggurjewa, dan haka aka sallamemu, to sainace tafad’amin gidansu na kaita, saita shiga kuka ta ce, “batada gurin zuwa, to nikuma saita bani tausayi shine nace tabani labarinta, amma saita kasa tanata kuka, nikuma ganin haka yasa nataho da’ita gida dan ta huta, sannan idan inada halin taimaka mata saina taimaka mata, kinji yanda akai muka had’u.
Sopy taja ajiyar zuciya ta ce, “tomiyasa baka d’aga wayataba?.
Saida ya kalleta sannan ya ce, “na barta a motane, shiyyasa banga kirankiba.
Ta ce, “to, yanzu yakake gani zamuyi da fareeda?, dan gsky bazan iya zama da itaba.
Ya d’an murmusa tareda jawota jikinsa ya ce, “haba sopyna nasanki mai tausayice, kiyi hak’uri mu zauna tare harta warke, sannan saimu san abinyi, ko muje mubama baba hak’uri amaida ita gidan mijinta, nasan har yanzu kina k’yaunar fareeda, ki yafe mata sopyna ALLAH yana tareda masu hak’uri.
Ta ce, “uncle amma kasan fareeda ta cutar dani ko?, ya ce, “nasan haka sopyna amma ki daure ki yafe mata, aii wani hanin ga ALLAH baiwane.
Ta rungumeshi itama tana ‘yar dariya ta ce, “gashima ALLAH yay min canji da samun gwarzon namiji mai ilimi da k’yau, ga nasaba.
Uncle G yad’ago fuskarta yana murmushi, ya ce, “sopyna nagode, amma taya nazama gwarzo? Tunda ban tab’a yin wani abu dazai nuna ni gwarzo bane.
Tayi murmushi tareda b’oye fuskarta a k’irjinsa ta ce, “kaima kasan kai gwarzone.
Cikin kunnenta ya ce, a wajen……. ya’arasa a hankali batareda najiba, ta kuma cusa kanta a kirjinsa tana fad’in nidai babu ruwana ga bily nan tana kallonmu.
Ya ce, “aii yanzu zan koreta, dan sa idonta yayi yawa.
🚶🏼nima sainayo waje tun kafin a koroni, nad’an lek’a fareeda naga har sannan barci takeyi, dan haka nima nataho wajen my sweet d’ina😜😜😎……………✍🏻
Kuyi hakuri jiya ba’ayi type ba.
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus’salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN’s💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 7~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣3⃣🔸🔶
…………Washe gari dak’yar sopy ta iya b’an b’are jikinta daga na uncle G!, dan tunda sukayi sallahr asuba suka koma suka kwanta, takula zaifara wani takale2, gashi yau zai koma aiki, tasamu dai dak’yar yabarta tashiga kichin ta had’a musu break, tana cikin gyaran falo fareeda ta fito, Sopy tayi burus da ita taci gaba da aikinta.
Fareeda ta daure ta ce, “mizan tayaki dashi sopy?.
Batareda ta kalletaba ta ce, “kibarshi kawai nama kusa gamawa.
Fareeda ta dage saita taya sopy aiki, Sopy ta ce, “kije ki kwanta kinsanfa bakida lafiya, fareeda tad’anyi murmushi mai ciwo ta ce, “Sopy kenan!!; karki damu da lafiyata dan nikaina batada amfani agareni, dan haka ki kawo natayaki kedai.
Sai asannan sopy ta kalli fareeda dake hawaye, saikuma jikin sopy yay sanyi, ta tabbata har yanzu tana k’yaunar fareeda, kawai b’acin raine yahana son tasiri dakuma danneshi datakeyi.
Fareeda ta surkushe agaban sopy tana zubar da hawaye, ta ce, “dan ALLAH Sopy ki yafe min, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, rud’in shaid’anne kawai ya kaini ga aikata kuskure mafi girma ga Aminiyata ‘yar uwata, dakuma iyayena, kuyimin kowanne irin hukunci, indai zaku huce, ki daina fushi dani plz, ta rushe da kuka mai ban tausayi.
Sopy ta kauda kai itama tana hawaye, sunkai tsawon minti uku kowa yana kuka, sannan sopy ta d’ago fareeda ta rungumeta suka cigaba da kuka ahaka, uncle G yana tsaye yana kallonsu cikin tausayi, lallai yasan gurinnan ana k’aunar juna, shaid’anne kawai yashiga tsakanin aminan juna, har yay tasirin b’ata tsakaninsu, ganin kukan nasu bamai k’arewa bane yasa shi yin tafi, da sauri suka juyo suna kallonsa, yay murmushi mai k’ayatarwa, tareda fad’in lallai yau ranace mai tarin farinciki da tarihi, na godema ALLAH dayasa muku hak’iri azukatanku.
Su duka murmushi suke, farida tai surin dafe kujera danjin jiri yana d’ibarta, da sauri sopy ta ruk’ota tana tambayar lfy??.
Fareeda ta ce, “kainane, uncle G ! Ya ce, “ki kaita d’aki ta kwanta, to sopy tafad’a tana rik’eda fareeda, uncle G! yabisu da kallo yana murmushi.
D’aki yakoma ya kwanta dan dasauran safiya, sopy kuma taci gaba da aikinta, bayan tagama tanufi d’aki danyin wanka, amma saita tarar fareeda ta gyara d’akin tsaf, sopy ta ce, “kai fareeda keda nace kizo ki kwanta ashe kina nan kina aiki.
Fareeda tad’anyi murmushi kawai, wanka sopy tashiga ta tsantsara kwalliya cikin siket da riga na material tayi k’yau sosai, ta ce, “fareeda kema yakamata kiyi wankan dan kiji k’arfin jikinki, saiki fito muyi break, fareeda ta ce, “to.
D’akin uncle G! tanufa, yana kwance d’ai d’ai yana barcinsa, sopy ta kalleshi tana murmushi, lallaima mutuminnan kamanta yau zakaje aiki ko?, saman gadon ta hau, tad’an jamasa hanci, ya d’an motsa, tashiga shafa kumatunsa da saje yakwanta luf luf na bak’in gashi, ahankali ya bud’e idanunsa, ta nuna masa agogonsa data d’aukko a durowar gefen gado, ya ware ido sosai dan ganin lokaci, ya mik’e yana fad’in sopyna nakusa makara fa.
Sopy tayi dariya tana fad’in ato hutun nan yasa kafara mantawa da makaranta, ya juyo yana kallonta, ya matso daf da ita murya kasa2 ya ce, “ba hutune yasani mantawa da makatantaba aii.
Sopy ta lumshe ido ta bud’e ta ce, “to, miye?, yad’an rungumota gefen jikinsa ya ce, “sopyna ce ta shayar dani zuma mai d’an d’ano, harna manta da kowa da komai.
Safiyya ta kwace jikinta tana dariya, ta ce, “uncle nidai babu ruwana ga ruwan wankanka can a bayi, bayi yanufa yana murmushi, saida yaje bakin k’ofar yajuyo yana kallonta.
Ta ce, “miya faru kuma??, ya d’an marairaice fuska ya ce, “baza’a taimaka amin wankanba.
Sopy ta zaro ido waje tana fad’in rufani kasayani, yanufota yana fad’in to bari na rufaki na sayaki, da gudu tafita tana dariya, shima bayin yashiga yana dariya.