NI DA MIJINA PART 1 BY MAMAN NUR

Kallonta yayi cike da nuna ya isa da ita yace”ke zo nan”

Mikewa tayi jiki na rawa tace” k b waya fada maka ina nan?”

Yace”yaushe raini ya Shiga tsakanina dake da har kike tambaya ta?”

Tace”sorry my k b”

Hanun ta ya kama zai ja ta kawai ya ji khady ta rike hanun d’ayan tana jefa me kallon tsana

Wani mugun kallo ya jefa mata yace”zaki saketa ne ko sai ranki ya b’ace?”

Tace”bazan saketa ba yi abinda zaka yi”

Kokarin janyo mukram yayi sai ya kasa domin wani mugun riko khady tayi mata

Ganin ya kasa janta kuma babu alamun tsoronshi a idon khady

Hade rai yayi yace”ke zaki saketa ne ko sai na b’ula miki ciki?”

Kallon shi khady tayi tace”da rabon yau ka kwana bayan kanta”

Ai yana jin haka ya sake mukram dan ya tsane police station

Jakar hanun mukram ya kwace ya cire kudi ya kara gaba

Mukram ko kuka ta fashe dashi tace”zuciyata baka min adalci ba da ka kamu da soyyayar k b”

Rungumeta khady tayi tace”my friend you still have time wallahi kabir ba mijin aure bane”

Cikin kuka tace”iam trying my best”

Khady ta zaunar da ita itama ta zauna ta kalli kwayar idonta

Tace”the biggest mistake da mace zata yi is to marry a wrong man wallahi zaki rayu da nadama har karshen rayuwar ki,ki zauna kiyi tunani ki kuma duba ni’imar da Allah yayi miki,kina da iyaye masu sonki wallahi abban ki be cancaci haka daga gare ki ba,ya kamata rayuwata ya zame miki darasi kin fi kowa sanin ni marainiya ce kuma kin San irin kuncin rayuwa dana tsinci kaina tun rasuwar mahaifana a hanun kanin babana,wallahi ki daure kiyi wa iyayen ki biyyaya domin baza su cutar dake ba,ni yanzu ji nikeyi da mahaifina zai dawo duniya wallahi sai na kasance mai biyyaya a gare shi balle ke kina ganin su ki gode Allah”nasiha mai shiga jiki khady tayi mata wanda ya sanya jikin mukram mugun sanyi

Cikin kuka
Tace”inshaallah zan yi kokarin cire shi a raina wallahi ba laifina bane jarabta ce”

Murmushi khady tayi tace”ina mamakin ki mukram a ce da rashin kunyar ki da tsiwa ga rashin d’aukan raini shine kika bari wanan banza na juya ki”

Harararta tayi tace”karki kara ce me banza”

Khady tace”ai ni kullum in nayi sallah sai nayi addu’a Allah yasa Abba yayi miki aure da wanan Abdulsamad din dama na tab’a jin mami na cewa tun kina karama aka kama me”

Ai mikewa mukram tayi tace”me zanyi da tsohon nan?left over wata Allah ya kiyaye wanan mai mugun raini da ji da kanshi ai gomma in rayu ba aure”

Khady tace”ai ba a wasa da ikon Allah “

Tsaki tayi tace”yau nasan ba ki kauna ta me zanyi da wanda ya tab’a aure harda haihuwa biyu karki manta fa yar’shi ta fari ta kai shekara goma sai na biyu shekara shida amma dan cin fuskar zaki ce in aure shi nifa na fison namiji d’an shekara 25 zuwa 7 amma haka kawai zaki mun mugun fata nifa ko gaisuwa baya had’a ni dashi saboda shi bana son zuwa gidansu”

Murmushi kawai khady tayi domin ta ji mami na hiran auren da kawarta amma tasan mukram bata sani ba tace”tashi muje “

Tashi tayi tana ta mita khady ta share ta

Motar suka shiga khady ta ja suka tafi

Da misalin karfe 4:pm

Yace”ba sai kin ce komai ba naji duk maganar ku kuma na gani da idona domin yanzu na gan mukram tsaye da wanan d’an iskan yaron rike da hanun juna”

Mami ta kalleshi tace”Dan Allah alhaji kayi hakuri ka rufa min asiri zata daina”

Yace”babu komai domin ni ba wani abu zan mata ba amma kafin ta wulakanta ni a idon duniya zan tabbatar na mata sutura”

Ummi dai zama tayi bata ce komai ba amma a zuciyarta tana jinjina rashin ji irin na mukram”

Mami tace”me kake nufi alhaji?”

Yace”aure zan mata”

Mami tace”what?”

Yace”yes domin nisa ne ta zo kusa”

Wani sanyi ne ya rasa ummi tayi murmushi

Mami ko tamke fuska tayi tace”ai baby bata isa aure ba kuma da ake son had’ata da wanan tsohon ai ban taba ganin ya zo nan nimanta ba nidai a bamu lokaci mu fitar da wani “

Ko kulata beyi ba ya ciro waya a aljihu yayi dialling noban alhaji sunusi

Bugu biyu ya d’auka,Abba naji ya d’aga

Yace”alhaji akan maganar yaran nan ne bana son ya wuce nan da sati d’aya”

A can bangaren ko alhaji murmushi jin dadi yayi yace”ai yanzu zan sanar da hajiya rahama a fara shiri abu yayi kyau”

Sun d’an yi hira kafin su yanke waya

Mikewa mami tayi ta rike kugu tana karkada kafarta tace”wallahi babu Wanda zai auran mu da diya kamar akuya a ce ko shirye-shirye baza a bamu lokacin yi ba?”

Dariya ma ta so bashi amma sai ya gimtse domin shi kanshi yasan ya taro match domin mami akan mukram bata ji bata gani

Hade rai yayi yace”zan Baku ko nawa kuke bukata kuyi abinda kuke so ai in akwai kudi babu matsala”

Mami tace”saboda ba a son diyata shine ake niman kuntata mata za a yi mata auren dole ai dama na dade da sanin an tsane mu kawai fitowa fili ne ba za ayi a fadi ba”

Murmushi yayi yace”hajara ni kike cewa na tsane ku? “

Kau da kai tayi tace”kwarai kuwa Karya nayi gashi ka nuna mana a zahiri”

Yace”kome zakiyi kiyi amma aure ko babu fashi “

Ai wani kuka mami ta fashe dashi

Kallonta ummi tayi a ranta tace”ikon Allah ashe abin ya kai haka?”

Dafa ta tayi tace “yaya kiyi hakuri inshaallah akwai alheri tattare da auren nan”

Ture hanunta tayi cikin kuka tace”kyale ni domin na dade da sanin munafukai a nan gidan a ce ya’ta za ayi auren dole toh in ba munafurci ba meyasa ba ayiwa zahra ba?”

Sanin halinta yasa ummi yin murmushi tace”Allah ya baki hakuri”

A fusace tace”amin”

Abba ko cigaba yayi da rubuce-rubucen shi ko kulata beyi ba

Mukram ne ta shigo falon da sallama gaban Abba ta je ta durkusa har kasa

Tace”abban Dan Allah kayi hakuri na tuba daga yau bazan kara kulashi ba”

Kallonta yayi yace”mukram miye matsayina a gunki?”

Cikin sanyi jiki tace”kai mahaifina ne mai kaunata”

Yace”good,ina son in baki umurni ne kuma bana son ki min musu in har nine mahaifinki”

Ba tare da tayi wani tunani ba tace”nayi maka alkawarin zama mai biyyaya”

Yace”aure zan miki nan da sati d’aya ke da yayan ki Abdulsamad”

Ai zubewa tayi kasa tace”Abba na tuba kamin rai wallahi bana son shi”

Yace”wallahi mukram in na kara jin wani magana daga bakin ki zan muku sab’a miki”

Zuwa mami tayi ta d’aga ta ta rungumeta tace”yi shiru baby Allah na nan muje part din mu”

Kuka mukram keyi sosai tana birgima

Ummi ko sai harararta takeyi

Mami kuwa sai aikin lallashi

Mami tace”tashi muje baby”

Har sun kai kofa Abba yace”kuma ban yarda ki kara kula wanan d’an iska ba ko magana kika sakeyi dashi wallahi ban yafe miki ba”

Kuka ta kara fashewa dashi mami ta dinga kunkuni suka bar falo

Dariyar dramar mami ummi ta kece dashi

Shima abba dariya yayi yace”ai hajara akan mukram sai ta haukace”

Ummi tace” yau har munafukai aka kira mu”

Yace”ai hajara bata ganin laifin mukram amma kana ganin bikin baiyi kusa ba?”

Yace”ah’ah bari ayi zanfi samun kwanciyar hankali”

Ummi tace”toh Allah ya Sanya alkhairi”

Yace”amin”

Mami na shiga part dinta ta rufe mukram da fad’a

Tace”ai kin gan abinda kika jawo ai in banda iskanci da rashin wayau ina ke ina kabiru?”

Cikin kuka mukram ta rungumeta tace”mami na ki yi min rai wallahi bana son shi”

Mami tace”ai mukram aure kamar an d’aura ne domin ke kanki kin San alhaji baya magan so biyu kina ganin har kuka nayi me amma yaki kulani baby mu hakura kawai dama bamu da gaskiya nima dani ke d’aure miki gindi nasan baki kyauta ba”

Mukram tace”mami harda ke?”

Tace”ai gaskiya ce”

Ganin mami ma ta goyi bayan auren yasa ta rage sautin kukanta kuma ta kara yarda aure kamar an d’aurane

A ranta tace”lallai yaya zai gan ba dai-dai ba”

A wuni ranan ko fitowa basuyi ba ko abinci a part dinsu suka ci domin mami fushi take da kowa

Su Ahmad ko da Habib sai dariya suke musu

Bangaren Abdulsamad ko

DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️