QADDARAR SUMAYYA
CHAPTER 18
Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajiyeta gefansa
yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun ake daf da
kammalashi
“Sai da na gaya miki kada ki daga” ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata iriyar
mutuwar iki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da kallonta,saidai
sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi ne ya shiga taso
maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film din ta koma dakin
gadonta.
Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar din ga gama
abinda zaya yi ya cimmata akan gadon.jikinsa ya janyota sannan cikin taushin murya yace
“Meke faruwa ne sumy uhmmm?”
“Babu komai” ta furta can qasan maqoshinta
“Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na siyayya
ita da ‘yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani lokaci,tun
daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na kuma ja mata
kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani” shiru sumayyan tayi taba nazarin
maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata
“Allah ya kyauta” ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi
“Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya” ya fada yana matse
mata yatsu har sai da taji zafi ta saki ‘yar qaramar qaara,sai ya hade bakinsa da nata cikin
wani irin salo da ya mantar da su komai
**
***
Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata yita jelan tura
1
masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni yake zuba su.
Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka sauke
farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka ba,ko babu
komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar ma’aiki ta farko nana
khadijatul kubra ta nemi ma’aiki da ya aureta,amma bata irin wannan sigar bace,ta siga ce
mai tsafta, mai ban sha’awa mai cike da hankali nutsuwa da kuma KARAMCI,sa’an nan ta
nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da kulawa,a ‘inda ko babu qauna akwai
tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.
Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna yayita
sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi shi kuma ya bita
da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da wanzuwa har tsawon
watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi.
Wace ce zainab?
Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe, suna da rufin asiri
dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da sabanin
mabanbantan ra’ayi ga jama’ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan yayin da
zainab ta kasance ‘yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya mahaifiyar
zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda ke da fada a ji
cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci karenta babu babbaka har
zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba musu gado kowa ya kama
gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin mijin da take so zainab din ta
aura ba kenan, miji take so ta samu koda ba mai kudi ba amma yana da abun
hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun duniya,talaka ne bashir
futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata idanu har ta aureshi,tayi aurenta
ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a federal college of education kano wato
FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin karatunta ne tare suke daukan lactures course
dinsu daya,bayan kammala karatu kuma aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake
kasuwa yake zuwa yana masa jira ana biyansa.
STORY CONTINUES BELOw
Duk iya yadda mama amaryan taso ta fahimtar da zainab din taqi fahimta,duk da
kusan cewa babu abinda ta baro na daga halayen uwarta,bata cimma nasara ba sai bayan
da akayi auren, su kaci soyayyarsu suka cinye,a lokacin da gishiri ya fara fita daga kan kaza
ne zainab din ta fahimci bashir bai dace da ita ba,daya bayan daya ta dinga bin sawun duk
wata dabi’a da huduba da uwar ke azata kai.
Cikin watanni biyar kacal suka balle auren, a lokacin tana dauke da ciki na watanni
uku,duk yadda suja zo zubar da cikin abin ya gagara,a cewar mama amaryan baya da wani
amfani tunda ubansa bai mallaki komai ba bare su saka ran samun wani alfanu tattare da
shi.
Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa, bayan wata
bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai lasisi, a
lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya sosai har
fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai, hakan ya so tsorata maman har ta soma
shirin hanata wasu abubuwan, am ma ina…maqeri ya riga mabada hali,tuni zainab din
tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu da zata aiwatar bata laifi a
idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.
Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba wajen bada
sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo mata,mukhtar din
yayi dai dai da ra’ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala zarratin, amma da ta samu
labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar ba matsala bace a gunta,aiki
guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga gidan,duk da tana diyar malamai ai bata
da maganin kirsa ko?.
****
Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba sai
data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa
zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d’a namiji ma,nan zainab din ta zube
mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da
taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.
Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci wayarsa,dama ya
tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata cikin
layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya riga da ya
sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa ba har zuwa
wannan lokaci.
“Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba” ya sanar da ita kai tsaye.
“La’ilaha illallahu, mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo zan
bugaci ganinka kaqi mukhtar” sai ta sa kuka
“Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da d’an
uwa” sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana zagi
aibata ko zargin sunayyarsa, hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.
Wayar ya sauke yana duban sumayya
“Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu”ya fada idanunsa na sauya launi da
alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada
“Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba cutarka
tana sane ba ko?” Shiru ya danyi sannan yace
“Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil
azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da
rayuwarmu” duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da
matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga dakinsa
ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajiye motarsa a inda
take kwana ya fice daga gidan.
Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude, a hankali ta dinga
ambaton
“Ya rabbi yassir wala ta’asir” sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.
Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo dariya da hirarsu
ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya katse hirar tasu,da daya
da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya yahanasun.
Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta dire
masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace
“Gani” sai ta dan murmusa
“Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?” Sai yaga rashin dacewar
yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya rusuna ya
3
tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya aijiye kofin.
Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta, har ya shigo da shi ya kulle gidan ya
qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya sameta a tsayen.
Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin da ta
shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,yar qaramar dariya ya
saki yana fadin
“Me ya tsorataki haka?” Qwayar idanunta ta juya
“Kaine mana, hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita”
“To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi” duk da bata ji farinciki ko kadan ba yadda ta
tsammata sai tace
“To Allah ya lamunce ya shige mana gaba” tayi maganar tana zama.
Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har bayan
kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi rayuwar
wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na daban
saidai idan shi yaga dama don rad’in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama bata
tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da ‘yar uwar tasa.
Bayan kwana biyu
a hankali ta shigo dakin ganin tunda ya kammala wanka ya shiga bai fito ba bayan ta
kammala shirya abincin dare sa zasu ci,turus ta tsaya tana dubansa.
Tsaye yake gaban mudubi sanye da sabuwar shaddarsa ruwan qwaiduwar qwai
dinkin boda,taje sumar kansa yake, sosai kayan suka masa kyau,sai ta jingina da bango ta
harde hannayenta tana dubansa,da alama ma baisan ta shigo ba.
“Da kyau,irin wannan kwalliya haka da akemin?” Juyowa yayi ya dubeta yana
murmushi
“Girmanki ne ai,amma zan danje unguwa tukunna” sai ta danyi jim gabanta na
faduwa,take ranta ya darsa mata wani abu,batasan sanda bakinta ya subuce ba
“Zance zaka kenan” juyowa ya sakeyi yana ajjuye cumb din tare da takowa gabanta
“Ya akayi kika canka?,naso ace da kaina na gaya miki my sumy” wani irin abu taji yana
ratsata tun daga kanta har qafafunta.yanayin fuskarta ya sauya
“Wai don Allah da gaske kake ko wasa?”
“Da gaske nake mana sumayya,na taba miki irin wannan wasan” ya fada yana qoqarin
janyota jikinsa,sai ta zame jikin ta kana ta ja da baya.jikinta ya soma rawa hawaye na shirin
zubo mata,hakan ya sanya ta tallafi kanta ta hanyar zama gefan gado,baiyi qasa a gwiwa ba
ya bita ya zauna gefanta
“Yi a hankali mana sumayya,me na daga hankali kuma,koma wace zata zo ai kema kinsan a
bayanki take ko?” Idanunta ta dago wadanda suka cika da qwalla har sun fara gangarowa
ta dubeshi
“Meye na tada hankali kuma,shin ban cancanci nayi kishinka bane ya mukhtar?”
“Kin cancanci fiye da haka ma sumayya, amma kiyi haquri,in sha Allahu ina saka ran
wannan karon alkhairi ne auren da zanyi”.
Cike da mamaki ta watsa masa wani kallon
wanne alkhairi ya mukhtar?,har ka manta wuyar da mukaci cikin shekara guda kacal?.
“No…ki kyautata zato sumayya ba haka na sanki ba… qarar wayar sa ce ta katse abinda
yake shirin gaya mata,ya sanya hannu ya daga wayar bayan ya hade fuska kamar yana
gaban mai kiran
‘nace miki gani nan ko?”daga haka ya datse kiran ya maida hankalinsa kanta.
Hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan ya miqe
“Ki bari na dawo zamuyi magana,ki kwantar da hankalinki sumayya kinji” bata iya amsa
masa ba har ya sanya hularsa ya fice
Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin faruwa?,mukhtar ne yau ya
tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana kuka,mukhtar din da baison bacin
ranta balle har yaga hawayenta?
“Ya rabbi yassir amrih” ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana digar
hawaye.
Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota ma,a dakin
nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar yana duban
idanunta da suka kumbura
“Subhanallahi..sumayya meye haka?” Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka,tsawon
mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da suka kammala
sannan ya nemi magana da ita.
“Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya, babu yadda za’ayi na iya bijirewa
maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba kamar auren
fa’iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA Cce zainab” yayi shiru yana jin quna can
qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin kamar dole ake masa ya
auri zainab.
Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa
“Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki daya,idan
da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu naki” maganar sai tayi
mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba
“Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai” tayi maganar
tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun.yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin
“Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa maka
yara,na yarda nikam juya ce” ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata shide,da
azama ya riqotan ya rungumeta yana lalashi,sam sai kalmominsa suka gaza yin tasiri cikin
zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri
“Nace ma ka sakeni kaji ko?!” Ta fada cikin gunjin kuka.
“Naqi na sakekin!” Ya fada a tsawace
“Yaushe kika koma haka sumayya?.yaushe kika koyi shegen kishi haka?” Ya fada yana
kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan
karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa daga
kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan gado ya
zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace
“Kiyvi haquri sumayya, baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har
ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi auren
nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya, ki yafewa mukhtar dinki mai qaunarki
kinji sumayyata” ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin kuka,abinda bata taba ji
daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya tabbatar maka da gaskiyarsa,take
tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta rungumeshi tana fadin
“Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi
adalci”
“In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu’a” ya fada yana kuma qanqameta.
***
Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din ya hada
kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai ganinsa tayi
da kayansa.yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya alkhairi, haka ya janyesu ya
miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke
Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta gamu da mai qarfin kurwa, kuma in sha
Allahu zama daram tazo.
Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin mace ta
zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din tayi,don tasan
komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin maganarsu,ta lura mutane
ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun da wjri,din ba zata lamunci
abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama zatayi ta zubawa sumayyan idanu
ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin ba.
Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar din
yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da lissafe
lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na ginin sabon
6:37 PM O
gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta bayar zai sauya mata
komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai wani lokaci sai ya hau qunci
shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin tamkar ya fasa,bata san meye matsalar
ba,data gaza gano haka sai taci gaba da addu’a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi
da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke
cinta,batasan dadin mijinta ba sai yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.
Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi mamaki
ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.
Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi yadda ta
saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar da suka
saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata nasihar da ta
sake kwantar mata da hankali.ya jaddada mata ta riqi addu’o inta,sosai taji dadi ta kuma
gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi dama mukhtar din yazo nema kuma bai
taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab.
Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta samu mai bata
shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni tayi mata sur ta
kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka sake kwantar mata
da hankali.
Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom
gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin
hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama
wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su dinma
kusan rabinsu sababbi ne.
Ana ya gobe za’a kawo amarya ta tare,tare da ‘yan rakiyarta suka je, sosai gidan ya
burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai gwargwado.da
fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din daban,sai qofar
da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d’aya,daga hagu da dama corridor ne
guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai daki falle biyu da
toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai yalwa wanda ka masa tsarin
tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma idan ka bude baya ne inda aka
yiwa yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka.
Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama
gabansu,hakan ga sanya randa za’a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi
zamanta saboda falon nasu cike yake da ‘yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta
karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu
aji guda ta sanya su.
Bata fito ba sai da taji motsin ‘yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko
amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake
binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin
jama’a.yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta
faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.
Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan
da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din
da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon
nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da
golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada
gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga
humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare
data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma ‘yan
danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.
Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi
ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi
din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.
A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba
mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa.wanu qaunarta ke taso masa ta wani
lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da
abinda yake ji din.ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga
ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki.ya jima cikin wannan
yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya
shagala,tunanin ya qwace masa.
Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube
ledojin hannunshi a qasa
“My sumy..yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba” ya fada cikin
marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata
fargaba da kamashi.yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga.yasha askin
saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.
Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi.yau nukhtar dinta zai
sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su huta,me yasa ba
zata gane iin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka haihu ba?,shine lawai
dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta a lokuta mabanbanta, ina ma ace ana siyar da
haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin daurawa,koda zata rasa lomar abincin da
zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta da mukhtar suyi rayuwar farinciki.
So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da zuciyarta ke
maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban haka, miqewa tayi gudu
gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike
da muradin cimmata,saidai tuni ta afka toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.
Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa kwashe minti
ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya sanyata cikin muryar
kuka tace
“Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni”
“Yau nine sumayya baki son gani?…yau..Bai kamamala maganar ba wayarsa dake
aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya sanyashi dagawa
“Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan naji shigowarka”,bazai iya tantance mai yaji ba,so yake
ya rufeta da masifa amma sai ya kasa, maimakon haka sai ya bige da cewa
“ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi”gabanta ha fadi haushi ta turniqeta,kada fa
ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu komai saura qiris tayi
maganin abun
“Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata kishiya,ka
taho ko nazo da kaina na tafi da kai”
“Ok gani nan” ya fadi da sauri tare da katse kiran, maida idanunsa yayi ga qofar toilet din,ya
tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya marairaice
“Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi” ya fada yana
juyawa.
Zamewa tayi tayi zaman dirshan saman tiles din bandakin sabon kuka na kubce mata
wanda ta sanya tafin hannunta ta toshe bakinta don kada su jiyota,duk da cewa ita tace ya
tafin bata yi tsammanin tafiyar tasa da gaggawa ba haka.
Ta jima tana kuka a ciki kafin ta lallashi kanta bayan tayi tilawar wasiyyoyin
mahaifiyarta tun daga auren da aka qara mata na fari zuwa wannan da ya kasance na biyu.
Bata bar bayin ba sai da cikakkiyar alwala,ta koma daki ta sauya kayan bacci,doguwar
riga ce har qasa mai taushi da kauri,hijabi ta dora saman riga ta shimfida abun sallaha ta
tayar da sallah hawaye na layi kan kumatunta.
Yana shiga ta miqe ta taroshi cikin karairaya da yauqi,ta amshi ledar hannunsa ta ajye
kana ta rungumeshi.yaqe haqora kawai yake,ko daya bata burgeshi ba,alamu sun nuna
babu kunya ko qwaya daya cikin idanunta,ko daya baiji dadin kasancewarta cikin jikinsa ba
amma sai ya kasa cewa da ita komai,sai ya dinga dauko daren farkon sumayya da na fa’iza
da nata yana hadawa,tuni lissafin ya wargaje don tako ina sun sha banban.
Biye yake da ita kawai sai ido da yake binta da shi,ita ta hada musu ruwa sukayi
wanka sannan ta samo plate ta juye kazar a ciki,kusan ita ta dinga ciyar da shi ta kuma ci
da kanta har suka kammala ta janyeshi gado don tuni ta dokanta,kusan ita ta gabatar da
komai a maimakonshi, mamaki da haushi ke tuqeshi,.gefe guda wani irin takaici wanda idan
ya yunqura zaiyi magana sai yaji ya kasa cewa komai,data dubeshi kuma sai yaji komai ya
wuce ya bar tasiri cikin ransa.
6.39 PM O
.
Kwana tayi zaune bayan ta gaji da yin sallolin,abinda bata taba zata zata iya ba,yaushe
mukhtar ya sake zame mata wani na daban haka,ita kanta tana mamakin yadda ta koyi
kishinsa har haka, sai da ta gabatar da sallar asuba taji idanunta sun soma nauyi da
zugi,duk yadda taso ta yakice baccin amma bata samu nasara ba,haka yazo ya saceta cikin
gaggawa ya kuma mata nauyi wanda hakan ya sanya ta gaza sanin meke wakana cikin
gidan har misalin qarfe goma da rabi ma safe wanda ta farka a firgice.
Bandakin cikin dakinta ta shiga da yake bayan na corridor akwai cikin daki,wanka tayi
bayan ta wanke bakinta ta dawo cikin dakin,jikinta babu qwari ta shirya cikin atamfa
doguwar riga wadda ta mata kyau,duk da batajin qwarin jikinta amma tayi lite make up
wadda ta dace da yanayinta,babu dauda ko qura a rea dinta sai dan kakkabe kakkabe
kawai da tayi sannan ta fito don samawa kanta abinda zata ci koda ruwan zafi ne,don jinta
take iska na yawo da ita tsabar babu komai a cikinta, ledar jiya mukhtar din ya bata ta
dauka ta fice da ita.
Bata kula da su ba sai data shigo cikin falon sosai,mukhyat sanye da yadi mai taushi
fari tas wanda ka yiwa aiki da zare ash,sai wandda idanunta suka sake sauka kanta wanda
bata tantama itace zainab din.
Macace wadda kallo daya ta yi mata ta fuskanci ta girmesu ita da fa’iza baki daya,A
qalla tayi shekaru ashirin ta takwas wanda hakan ke nuna ta girmi sumayyan da shekara
goma tunda sai yanzu taje cikin shekararta ta goma sha tara,baqa ce zainab din amma ba
baqi can ba,tana da cika wadda za’a iya kiranta qiba kai tsaye duk da wata mai yawa
bace,bata daga cikin sahun kyawawa ko kadan amma zaiyi wuya kai tsaye ka kirata da
mummuna saboda yanayin iya gogayya da iya salo,saidai tako ina sumayyan ta mata
fintikau,abu daya zata iya nuna mata qwala qwalan idanu da suke zagayayyu suka fi na
sumayya girma,sakamakon natan lumsassu ne ba kowanne lokaci kake iya gane girmansu
ba,sanye take da material mai santsi wanda aka yiwa dinkin riga da skert,breakfast sukeyi
wanda ya qunshi tea da soyayyen qwai da bread,sai kaji wanda ba tantama na jiya ne aka
sake gasa su.
Shi ya soma ganinta lokacin da zainab ke qoqarin bashi naman a baki,sai ya goce
wanda hakan ya janyo hankalin zainab din ta ankara da fitowar sumayyan, murmushi ya
sakar mata yayin da itama tayi qoqarin maida masa martani
“Kin tashi kenan,na leqaki na taras kina bacci”
“Eh,ban jima ai da tashi ba” ta fada tana takowa gabansu
“Kinyi kyau sumy ta” ya fada yana sake dubanta wanda kalmar ba qaramin dukan qirjin
zainab tayi ba,lokaci daya ranta yayi baqi,sumayyan ta yaga mata tako ina,kyau da
quruciya,akwai alamun nutsuwa tattare da ita sosai, hakan ta kwana da sanin lamba daya
ce ita cikin zuciyar mukhtar din,don ko darensu na jiya ya bata amsa,duk yadda taso
rikitashi ban manta sumayyan ba ita yake kira.
“Na gode ango mijin amarya,da fatan kun tashi lafiya” ta fada wajen kaiwa matuqa gurin
boye kishi da damuwarta,sai ta dubi zainab
“Amarya ina kwana ya kwanan baqunta”
“Lafiya ya kike”ta fada tana yatsina tare da qoqarin baiwa mukhtar tea
“Qalau” itama sumayyan ta fada cikin yanayin data amsa mata tare da motsa kafada kana
ta nufi kitchen don kaucewa ci gaba da kallon abinda ke faruwa.
Alamu sun nuna iyaka na cikinsu ne abincin,batasan waye yayi ba,amaryar ko mijin
amaryar,koma waye dama bata da buqata,sai ta dora tea kan gas da a yanzu shi mukhtar
ya siya mata take amfani da shi,ta bude kazar ta sake mata sabon hadi na spices,ta duba
dan madaidaicin ovean dinta ta soma kici kicin hadawa tare da duba hanyoyin da ake
hadawar.
Cikin haka mukhtar din ya shigi kitchen din dauke da kwanukan da suka ci abincin
zainab din na biye da shi,bata bi takan sumayyan ba ta nufi side dinta ta dire
kayan,mukhtar ya dubu sumayyan
“Me za’a girka mana ne naga ana hada ovean”
“Ai baka da buqatar abinci na malam” ta fada cikin gatse,murmushi yayi yana
kallonta,lallai sumayyan ta fara zama babbar mace,tunda har tafara banbance tsakanin aya
da tsakuwa.
Kafin ya furta komai muryar zainab ta ratsa kunnuwansu tana qwala masa kira cikin
wani irin salo,tamkar an soketa a qirji amma saita basarya juya yana cewa da ita
“Ina zuwa”
“Banda buqatar dawowarka ma” ta fada kishi na cinta tana qoqarin danneshi.
Har ta kammala babu shi babu alamarsa,ta juye ta koma daki da abincinta zuciyarta na
raunana,saboda wannan ne karo na farko data taba ganin sauyi daga gareshi har irin haka.
**
****
Cikin kwanakin wani amarci ta dinga gani cikin gidan wanda bata tsammata ba,baki
daya kamar daukar mukhtar din akayi aka sauya mata shi,hutu ya dauka na fita kasuwa har
na kwanaki bakwai,ko yaushe suna daki idan kaga fitowarsa salla ce zaya yi,saita wuni sur
bata sanyashi cikin idanunta ba,abun na taba ranta saidai bata yarda ta fiya zurfafa lamarin
cikin ranta,runda anty dije ta gaya mata dole zata iya ganin wasu sauye sauye duk son da
yake mata,amarya kota buzuz ce sai an mata rawar qafa,to bare baya ga wannan babu wani
sauyi da ta gani cikin ma’amalarsu shi da ita.
KUNDIN QADDARA TA”
Kwanaki uku take zaton zaya yiwa zainab din tunda bazawara ce,sai gashi ya shiga
cikin kwana na hudu biyar shida har zuwa bakwai.
Ranar kwana na bakwai din a ranar zaya soma fita kasuwa,tana kwance dakinta bayan
sha daya na safe taji sallamarsa,sai ta miqe ta zauna tana amsa masa,fuskarta babu yabo
babu fallasa,gefanta ya samu ya zauna yana fadin
“Ranki ya dade kinyi wuyar gani” ido ta daga ta dubeshi,lallai ne wai ita za’a yiwa halin
maza,magana yake gaya mata a fakaice koko yaya,duk da hakan sai ta dake ta kuma basar
ta kaufa zancan ta hanyar fadin
“Ina kwana”
“Lafiya sumy ta,kinga na qarawa zainab kwana ko,kinga baquwace tace kuma tan tsorom
zama ita daya” wani haushi ya taso ya turniqeta,budurwa ce zainab din ko yau ta fara
zaman gidan aure,ko ko tsabagen rainin wayo ne,wadan nan kalaman takeson gayawa
mukhtar din amma girmansa da take gani yasa ta gaza furtasu ta hadiye kayanta sai ta bige
da cewa
“Ko,Allah sarki” daga yanayin da tayi maganar kawai ya tabbatar masa cewa ta inda
zancansa ya shiga ta nan ya fice.
Kafin su sake cewa wani abu zainab din ta daga labulen dakin ta danno tana fadin
“Dear fito mana na rakaka,ina ta jira fa”
“Ai gani nan” ya fada yana fiddo kudin cefane daga aljihunsa,wani banzan kallo da
sumayyan batasan ta iyashi ba sai yau ta jefawa zainab sannan ta miqe zata fice ta bar
musu dakin, mukhtar yace
“Ina kuma zaki sumayya bamu gama magana ba”
“Baka shirya yin maganar da ni bane” ta fada tana shigewa toilet abinta ta soma daura
alwalar sallar walhar da dama ita take shirib tashi tayi.
Tana jiyosu daga nan zainab din na gaya masa ya qyaleta yazo su tafi.yace a’a taje falo
ta jirashi zaya fito yanzu,a bandakin ya cimmata ta gama alwalar tana gyara daurin
kallabinta,fuska a hade cikin kakkaurar murya yace mata
“Wai wane irin hali kika koya sumayya wanda ban sanki da shi ba,wannan wannw irin
wulaqanci ne ina miki magana kina tafiya gaban zainab salon ki koya mata yadda zata
raina ni”, tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,lallai a daki mutum a kuma hanashi kuka.
“ai tare muka siyi foam din makarantar koyon sabbin halaye ni da kai muka cike,muka
kuma fara daukar darasi a ciki”‘sarai yaso ya fahimceta amma sai ya waske
“Wai duka sumayya don na qarawa zainab kwanaki kike wannan abun.yanzun ban isa da
gidana ba kenan?”
“Isa kai,tunda gashi ka nuna salon taka isar” ta fada tana kashe famfo tare da qoqarin
rabeshi ta wuce,sai ya janyota jikinsa ya matse gam.yasan kan abarsa take ya fara sauke
mata fushinta.yayi nasara kam don itama bata bijire masa ba,don babu qarya tayi kewar
mijinta sosai.
Ita ta fara zame jikinta sannan tace
“Ka gayawa matarka kada ta sake shigo kin daki kanta tsaye,sabida hakan ya sabawa dokar
addinin musulunci idan ita din bata sani ba” sai ya lumshe ido ya dafe kai
“Oh sumayya harda mita ma sai da kika koya,to ayi haquri” daga nan sukayi sallama ya
ajiye mata kudin cefane duk da suna da komai.
Sosai zainab din ta qulu,ta fara lura sumayyan ta shalle zatonta,amma daga yau zata
fara dasa bamabamanta cikin gidan,shanye komai tayi ta masa rakiya kamar ta
hadeshu,duk yadda ya nuna jin dadinsa a fili amma zuciyarsa ta gaza karbar hakan,a boye
ma Allah Allah yake ta koma ya samu ya fice daga gidan.
Da azahar ta shiga kitchen ta musu girkin rana,tana fitowa ta samu zainab din a falon
zaune tana kallo,qafarta daya kan daya tana amsa waya,har sumayyan ta gifata ta taji ance
“Ke!” Da fari tayi zatan cikin wayarta ne sai taji ta sake cewa
“Ke dake nake magana sumayyata” waiwayowa tayi tana tsaye daga inda take
“Wai da ni kike?”
“Akwai wata mai sunan ne bayanke a gidan nan,koma ki dauko min abinci na”.
Baki ta sake tana kallonta cikin mamaki,ita kuma nata salon kenan,sai ta kada kai
kawai tace
idan kin damu ki shiga da kanki ki dauko”
“Ni kike gayawa wannan maganar, lallai yau zaki gane niba irin sauran kishiyoyinki
bane,wallahi yau sai kin gane matsayina gun mukhtar” bata tsaya bi ta kanta ba tayi
6-40 PM o
.
komawarta daki don tana da abunyi.
Lambar mukhtar ta soma laluba tana huci.yana tsaka da sallamar custumer yaga kiran
nata,sai da yaji wani dumm cikin kansa da yaga sunar,ko kadan baiyi farinciki ba amma sai
ya gaza share kiran
“Amarya bakya laifiya gidan”
Gida ba lafiya ba,mukhtar na fuskanci ka auroni ne don matarka ta rainani”
“Ya salam,me ya faru me tayi miki?”
“Bazan hanaka sana’a ba kabari idan ka dawo kaji koma mene ne,amma wallahi idan baka
dauki mataki ba bazan ci gaba da zama cikin gidan nan ba” sai yaji wata faduwar gaba da
sauri yace
“Haba zainab ki daina fadar wannan maganar mana,mai rabu mu ai sai Allah,bari na kira
ita sumayyan naji” da sauri ta katseshi don bata son ya mata fadan tun yanzu lamarin ya
wuce ba tare data iza wutar tafi haka ba
“A’ah nidai ban saka ba,nace ka bari kawai ka dawo”
“To shikenan sai na dawo din” ya fadi yana sauke wayar,sam jikinsa bai bashi sumayyan
zata aikata wani abu na rashin mutunci ga zaina din ba,amma sai ya samu kansa da yarda
da duka magan ganun zainab din.
Tun shuda saura ta gama fesa kwalliya tare da bade jikinta da turarenta data tanada
na musamman wanda ke hargitsa tunani da lissafin mukhtar ya dinga maida su ba dai dai
ba.
Cikin izza da isa ta fito daga dakin nata hannunta dauke da jug na kwalba wanda ta
cikashi da lemin zobo da cups dinsa,tana tafe tana murmushin tarkon data d’ana ta ratso
ta falo don fita harabar gidan,so take mukhtar din ya fara karo da ita kafin kowa saboda
abinda ta tsara ya tafi dai dai ba tare da mishkila ba,idanunta ne suka sauka kan sumayya
tada tsume cikin tata kwaliyar.wani irin material ne mai santsi kamar yanayin shufom
saidai ya fishi kauri da aka matsawa dinkin wata shegiyar gown wadda ta fidda duk wata
qira tata,kalar pink(ruwan hoda) ne mai turuwa,tayi amfani da dankunne da siririyar sarqa
fashion baqaqe,hakanan abun hannunta zuwa zobe,take farincikin dake ranta ya ja baya ta
raina tata kwalliyar data hasko farar fata ta hadu da pink da baqi,kishi ya sake taso mata,ya
zama lallai kota halin qaqa tayi rugu rugu da gwamnatin sumayyan cikin zuciyar mukhtar
ya zama tata ke wannan tashen,ta yadda zata yaga yarinyar yadda taga dama,yarinyar na
neman fin qarfin zatonta,don ba’a rufe awa ba taga yadda ta tashi hankalin gidan da
qamshin girkin abincin dare,ranta na suya ta fuce fuuu wanda sumayya bata ma lura da ita ba sai ficewarta ta gani kamar guguwa.
tofa.yanzu ake yinta, muje zuwa