QADDARAR SUMAYYAH
CHAPTER 24
Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da
mamansu ne,ta dubi lukman
“Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam, kada a ja abun
yayi nisa don Allah,yaran na buqatar mamarsu” kai ya kada baison gaya
mata wani abu da zai daga mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura
ta bar gidan sai yake jin kamar an zare masa wata qaya data tsaya masa
a maqoshi
“To naji” kawai ya fada.
Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku
yace kada ta sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata
dawo,ai ta saba ba yau farau ba,hakan ya sanya ta tsuke
bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada hankali sosai
kan rashin dawowar mamansu ba.
Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan
yayi dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya
ta fara fuskantar matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke
da ita,amma sai ta jure tayi amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara
janye qananan,nuratu basma da syyada, islam ce kawai ta taqi biyuya,ta
soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta tattarata ta watsar
gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na annabawa
da sahabbai,suna bala’in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta
gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu
abubuwa da dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya
ba,kamar alwala,sallah,sallama idan zasu shiga guri,addu’ar sanya
kanya,addu’ar bacci da tashi daga bacci,addu’ar shiga bandaki data
fitowa,addu’ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da
hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi
sukeji,nuwaira tafi kowa murna takance
“Anty dama tuntuni kema ‘yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar
qur’ani ko?” Dariya takanyi tace
“To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah”tarbiyya
take basu sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi
fisabilillahi,don har ga Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da
kakarsu na gwada mata qauna.
A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan
kaga sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar
son yara,abun ya yiwa hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da
addu’ar kada Allah yasa karima dawo,don ita kanta yanzu anan
bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta suje su kwana tare da
ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin girmanta,ta
bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a
kwance,sau tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da
nutsuwa ya samu sosai irin wadda bai taba samun irinta ba tunda ya
fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai kuma yi fatan kasancewa
da ita har qarshen rayuwarsa, hatta da mai gadi da mai aikin gidan
sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu ‘yanci.
Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam
sun mance ma basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan
tada zancanta shikenan an wuce gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu
baki daya saboda haka nuwaira ta samu matsayinta na babba a gidan,a
yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da bata isa
ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau
zasu daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah
zai sashi a wuta,ta wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu
yadda zasu gane haka ma aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa
zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun san wuta.
Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk
wanu ilimi da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya
yarje mata kan ta nema musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar
dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin karatunsu saboda haka ta
yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka gama
musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna
suke da fara zuwa makarantar.idan suka dawo tare suke bitar dukka
karatuttukansu,wani dadi hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka
gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin duhu sai da Allah ya kawo musu
SUMAYYA HASKE.
Ya sake bude mata shafi ne daga lokacin da karima ta cika wata biyu
da rabi da barin gidan,sauyin data fara gani daga lukman din,kusan tun
bayan tafiyar karima sumayya ta dorashi kan ibada saboda gunewa
faruwar wani abu,cikin sati gaba daya ta fuskanci ya zama mai son jiki
da wata muguwar kasala,da qyar yake iya sallolinsa na farilla balle akai
ga na nafila,idan qur’ani suka dauko zasuyi tilawa yadda suka saba sai
ya soma gyangyadi daga nan sai bacci,idan sallar asuba ce kullum sai
ya makara sai tayi da gaske,duk wani abu na ibada ya zama very lazy
akansa,tun abun na bata mamaki har ya soma bata tsoro,hakan ya
sanya ta samu hajiya da maganan,sam bata kowa komai ba tace
sumayyan taci gaba da haquri da kuma qoqarin ci gaba da dorashi a
hanya har ya daina,kuma itama zata yi masa fada
A hankali sai abun ya soma cin tura,hatta idan yana bacci bai da aiki
sai kiran sunan karima,idan ya tashi kuwa washegari haka zai yini babu
wannan walwalar sam.haka kawai yake jin rayuwarsa da zuciyarsa cikin
takura da qunci.ji yake kamar yana cikin wata kurkuru,burinsa kawai
yaga karima cikin gidan,saidai duk da haka bai taba furtawa sumayya
ba.
Bayan sati d’aya_*
Bayan sallar isha’i ne dukkansu suna zaune a falom gidan banda
hajiya dake bangarenta saboda yau da wuri ta kwanta,sumayya da
nuratu da nuwaira na zaune tana koya musu aikin gida(assigment)da
aka basu a makaranta,basma na saman kujera tana bacci tun sanda
suka gama cin abincin dare,sai islam dake kwashe kwanukan da suka ci
abinci da su tana shigarwa kitchen.
Lukman ne ya fito falona gaggauce wanda tunda ya dawo daga
kasuwa yana cikin daki bai fito ba sai yanzu,hannunsa riqe da dan
mukulli,daya hannun nasa kuma riqe da hularsa, kana ganinsa kamar
wanda aka jefo ko aka tunkudo,daga kai sumayya tayi tana dubansa
sanda ya giftasu zai fice ganin bai cewa kowa komai ba
“Abban nuwaira” waiwayowa yayi yana dubanta tare da amsawa
“Ina zaka fita haka tara na dare?” Ta fada a marairaice
“Sorry airphort zani.yanzu zamu dawo” ya fadi yana ficewa da sauri jin
wayarsa na ringing,kanta ta maida suka ci gaba da assigment din da
yaran,hakanan taji gabanta na yawaita faduwa,hasbunallahu wa
ni’imal wakil ta dinga maimaitawa,suna gamawa ta tattara yaran duka
suka tafi dakinsu,sai da kowa ya sanya kayam baccinsa ya karanta
addu’ar kwanciya bacci suka kwanta sannan ta rufo musu dakin ta
koma nata dakin,alwala tayu tayi shafa’i da wutirinta sannan ta zauna
ta karanta suratul mulk,har ta gama abinda take bata ji shigowarsa
ba,saboda haka ta sanya hijabinta ta nufi bangaren hajiya.
A kashingide ta sameta riqe da carbi.ganin sumayyan ya sanyata
zama tana murmushi
“Yanzu kuwa nake zancanki a zuciyata” itama murmushin take tana
cewa
“Hajiya baki bacci ba?”
“Kin ganni nan wlh banyi ba,gabana ne yake ta faduwa sai na tuna dazu
banyi waraddallahu ba,sai nake yinta yanzu (waraddallahul lazina
kafaru bi gaizihim lam yanaluu khairaa,wa khafallahul mu’umininal
qital,wa kanallahu gawiyan aziza,ana karanta ta ne qafa dari bayan
sallar asaba kariya daga dukkan kaidin wani maqiyi dake nufarka da shi
in sha Allah”
“Ai gwara hajiya” ta fada tana tunanin faduwar gaban da itama take ji
tayi dai dai data hajiya kenan
“Ina lukman din kuma?”
“Ya dan fita ne hajiya yara kuma sun kwanta saboda makaranta goben”
“Sannunki kedai sumayya,Allah yayi albarka” “amin hajiya”ta fada tana
murmushi kanta a qasa,shiru ne ya biyo baya kafin su soma taba hira
kadan kadan,ganin har sha daya na dare tayi ya sanyata yiwa hajiyan
sallama ta koma sashenta.
Tana zaune har sha daya da rabi sannan taji muryar lukman,a
hankali ta tashi ta leqa,shine a gaba janye da akwati daya hannun
jaka,sai KARIMA dake biye da shi a baya,da sauri ta saki labulen ta koma
da baya tana kiran sunayen Allah,sannu a hankali nutsuwa ta saukar
mata,sai ta daura alwala ta kwanta,don jikinta na bata lukman ba zaya
nemeta a yau ba.
Ilai kuwa bata sake jin motsinsa ko na karima ba har bacci yayi awon
gaba da ita.
******
******
Washegari yadda suka saba haka tayi bata fasa ba,ita ta tashi yaran
baki daya sukayi sallar asuba,sannan ta dafa ruwa mai zafi islam ta fara
yi sannan nuwaira ta dinga yiwa qananan tana tura su islam na shiryasu
ita kuma tayi daga qarshe, sumayya kuma na kitchen tana hada
breakfast da wanda zasu tafi da shi makaranta,abinda dukka a da basu
saba yi ba amma a yanzu ya zame musu jiki.
Sun shirya tsaf suna karyawa ya zagaya ta buga dakin karima don
taga idan sun tashi ta tura yaran su gaida mamansu kan su wuce,saidai
har ta gama bugunta ko tari bata ji anyi ba,abinda bata sani ba lukman
na jin bugun.ya kuma san sumayyarsa ce,kamar ya zura a guje ya bude
saidai ina sam bai isa ba,saboda bai samu umarni ba,tunda ta dawo a
jiyan qasan zuciyarsa ke a cunkushe cike da baqinciki bacin rai da
tsananin tsoronta,amma a fili tsantsar farinciki ne da tsananin biyayya
bayyane a fuskar tasa,abinda zai baka mamaki tunda ta dawo bai taba
kwatanta tambayarta inda ta tafi da aurensa a kanta ba kuma ba tare
da izininsa ba har na tsawon wata biyu ba,a lokacin ma yana bandaki
yana wanke mata tana son shiga wanka saidai ya hada qura a tsawon
wata biyu da bata nan tunda ba wani ke shiga ba gun nata na a rufe ne.
Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu
ma ya iso ta dubesu
” mamanku fa ta dawo jiya da daddare”ta tsammaci zata ga tsantsar
farinciki a fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa, babu wani zumudi
ko doki,nuwaira kuwa tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta
rakasu suka fice sannan ta dawo ta gyara falo zuwa kitchen ta barwa
mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta leqa bangaren
hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata ‘yan gyare
gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi
tayi ta karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata
kewa,zuwa yanzu sum shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji
babu dadi kasancewarta mai son yara.
Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai
ba har sai da taji cikin taqama tana fadin
“Ina yara na” cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na
cewa
“Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu” cikin harzuqa tace
“Eh wato suma an shige musu za’a shanyesu a rabani da su kenan?” Sai
ta saki wani shu’umin murmushi tana kada kai
“Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma” ta
fada tana yin gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi
bayanta,kai ta jinjina bayan fitarsu
“Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un” ta fada tana kada kai ganin hannun
agogo nason komawa baya game da lamarin lukman din.
Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada
l.l Bl
8-26 PM
hajiyan ma ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da
aure,sosai hajiyan keji qarfin zuciyarta sam babu wani dar da taji balle
taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda lallai idan kayi sakaci da addu’a
babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da cewa akwai
QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU’A
Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata, baki ta saki tana kallon
yadda suka sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira
da islam,lallai sumayya ta sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu
farraqu ba ita da au ta barsu suka shaqu haka,tana gani suka sauya
kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna sanya hijabansu
sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su kariman
ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a
tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take
“Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama”
nuratu ta fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta
amma sai ta wayance da cewa
“Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga
dawowarku daga boko ko hutawa bakuyi ba” islam ce ta maqe wuya
tana cewa
“Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa
ana wuceka a karatun” ido ta kuma zarowa mamki na sake
kasheta,lallai sumayya tayi amfani da irin surkullensu ta rabata da
yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa
“Don ubanki da ni kike jayayya, ku cire kayanku nace babu inda zaku”
sumayya ce ta bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa
“Haba maman nuratu, meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa
farincikin zuwan yaranki makaranta,ba girmanki bane” sai ta waiwaya
ga yaran da sukayi carko carko suna kallon karimar
“Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura” da sauri suka fice kuwa
daya bayan daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli
sumayya
“Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na
baki shi nake jira” tana gama fada ta fita
“Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin
ubangiji nake nemawa rayuwata” ta fada tana gyara dakin yaran da
suka bata tare da killace kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su
wanke
Baki daya sai aka koma ‘yar gidan jiya kan halayen mukhtaryayin da
bangare guda sauyawar yaranta da haijiya ke ciwa kariman tuwo a
qwarya,saidai ta kammala dukkan wani shirinta na maida hannun
agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan ya sanya ta sanyawa
kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci gaba
da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar.
******
*************
Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe
saboda yanayin sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin
rana ita da mai aikin gidan qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu
dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar tunda karima ta dawo gidan
bata ko dubi kitchen ba.
Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su
dawo,bude qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli
qofar,karima ce cikin kwalliya da daurin ture kaga tsiya.jambaki kamar
zai digo daga bakinta,itace a gaba lukman na biye da ita janye da
trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya mamaki,qarasowa
tayi bakin gadon tana duban sumayya
“Mijinki ko mijina?..o.ho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi
tafiya,wadda itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku” ta
qarashe tana dariya dariya,ta waiwaya ta dubi lukman dake
tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana dubansa sai ya saki
murmushi
“Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai” sai ta juya ta fice.
Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi
daga kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa
“Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane
sumayya,haka nan nake jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake
jin idan naci gaba da zama da ke akwai cutarwa,sumayya ki yafemin
akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har cikin zuciyata
amma bazan iya zama da ke ba…”
Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin” ta
fada cikin rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake
shigowa dakin,cikin daga murya tace
“Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a
jirashi ko?” Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya
hannunsa a aljuhunsa ya fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu
kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata bayani ba tasan takardar
meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da qwai ya
fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice
karima ta rufa masa baya.
Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa
ba taji islam na girgiza kafadarta
“Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba” sai ta daga
kai ta kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko
cirko,alamun damuwa duka sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai
ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin tausayin kanta,don nasu mai sauqi
ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta maza ta hadiyeta,ta
qaqalo murmushi tana cewa
“Wa’alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar
taku bane,muje maza a shirya yau kun dawo a makare ko?” Ta fadi tana
saukowa daga kan gadon,biyo bayanta sukayi kowa na bata labarin yau
na makaranta,tana shiryasu tana biye musu.yayin da qarqashin
zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta musamman
nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya
ba tunda a yanzu an samu kan ‘yan uwanta da kakarta, sosai tayi
jarumtar danne damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso
dagota,don ta saci kallonta sai daya taga tana dauke qwalla,duk sai
yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki, duk inda sumayyan tayi tana biye da ita
da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko giftawar karima
ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data juyo ta
sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi.
Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin
gado ta koma tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata
buqata cikin akwati ta zira hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta
saka takalmanta.
Sallama tayi bangaren hajiyan ta amsa mata tana murmushi tana
tsokanarta
“Yau sanyi ya boyeki ko sumayya” ganin yanayin fuskar sumayyan ya
katse fara’ar hajiyan,gefan hajiyan ta zauna kanta na a qasa
“A’ah lafiya kuwa sumayya?” Cikin rawar murya tace
“Zuwa nayi muyi sallama hajiya zan tafi” cikin tashin hankali tace
“Sallama,tafiya zuwa ina?” Kasa bata amsa tayi saita miqa mata
takardar dake nade a hannunta,da sauri hajiyan ta karba tana
dubawa,salati ta saki.”‘yaushe hakan ya faru?,me yasa ban gaya min ba
dazu yamin sallama zai je ghana,sumayya..” sai ta rasa abinda zata
fada
“Haka lukman zaimin?,to wallahi nima bani zama a gidansa,yaci gaba
da zama da karima ita kadai” Cewar hajiyan,sai kuma ta saki kuka,da
sauri sumayya ta goge nata hawayen ta kama hannun hajiyan tana
girgiza kai
“A’ah hajiya don Allah ki daina masa kuka,zaki sake jefashi cikin wani
bala ‘in bayan bai fita daga wanda yake ciki ba,hajiya, lukman danki ne
ke kika haife abinki,ke kika san zafinsa,idan bakiyi yaqi a kansa kin saita
rayuwarsa ba duk duniya wazai miki wannan aikin, hajiya ke zaki zauna
kici gaba da aikin da na fara”wajen mintuna ashirin ta kashe tana yiwa
hajiyam bayani tare da jan hankalinta sannan ta fara samun nutsuwa
” naji sumayya,nan zaki zauna gurina,tilas na nemo lukman duk inda ya
tafi,dole ya dawo da ke,akwai sauran igiya daya tsakaninku”kai ta kada
tace
“A’ah hajiya,kada ki tilas ta shi wanda hakan zai iya haifar da wani abun
daban,babu abin buqata a yanzu fiye da dawowarsa kan hanya,Allah ne
mafi sani kan dalilin faruwar hakan, na yadda cewa wannan ma na cikin
QADDARAR rayuwa ta, koda yaushe Allah nake miqawa zabi kan
rayuwata ya zaba min abinda yake gani shine dai dai ba abinda ni nake
ganin shine dai dai ba,na gode masa ma da ya bani ikon fiddaku ke da
su islam daga halin da na riskeku,abun da nake so hajiya kimin
alqawari shine, ba zaki sake zubda masa qwalla ba,ba zaki saki
addu’o’inki ba,ba zaki bar su islam su koma irin rayuwarsu ta baya
ba,sannan ba zaki gaji da nemawa lukman kubuta da tsiraba,wannan
yaqin naki ne,duk na dora miki hajiya zan kuma tayaki da addu’a”
“Insha Allahu sumayya in sha Allahu,Allah ubangiji ya albarkaci
rayuwarki,kuma in sha Allahu ina mai tabbatar miki da yardar Allah zaki
sake dawowa gidan nan,duk inda lukman yake zan nemeshi zan
nemeshi ya dawo da ke” ta fada zuciyarta a raunane,cikin irin wannan
yanayi mai ban tausayi sukayi sallama.
ZAINAB”
Kamar yadda suka tsara ita da zinatu hakan ce ta kasance,qarfe goma
na safiyar washe gari a gidan malam ta yi musu,duk da dan uban ciwon
da jikinta ke mata amma sam bata kula ba,burinta kawai ta ganta
gaban malam din,da yake safiya ce bata taras da mutane da yawa ba a
gidan mutum daya ne ya fito suka shiga.
Kamar ko yaushe mutumin da suke kira da malam ya kuma shiga rigar
malamai yayi bake bake yana zaune kan buzu,yaci babbar riga da
rawani gefelitattafan addini jere wadanda ko zaka kasheshi layi guda
bazai iya karantawa ba balle har ya iya gane me ya karanta din.
“Zainabu abu,ina fata buqata ta biya don na ina nan ina ta kewarki,ban
manta daren mu ba na….
“Dakata dalla malam,ni zaka yaudara?, kayimin aikin banza lalataccen
aiki da tunda na fara yawon bin malamai ba’a taba min matsiyacin aiki
irinsa ba,to wallahi da sake bazai yiwu ba”turbune fuska yayi ainun
yana dubanta
“ke kisan fa agaban wa kike,bana son tsiya”‘sake harzuqa tayi tana
cewa
“Eh dole mana ka fadi haka,bayan ka gama amfana da albakatun jikina
ko?”
“Ke sha shashasha,ai ba kanki farau ba,kuma ke kika kawo kanki,dama
tunda kika rabu da Allah babu irin qazantar da ba zaki fada ba,kinga ki
fadamin abinda ke tafe dake kada ki batamin lokaci customers na tafe a
hanya kada ki bata min aiki” cikin masifa ta sake takowa gabansa tana
dubansa
“Amma malam bansan kai ba qaramin dan akuya bane sai yau,to
wallahi baka isa kaci bulus ba,ni babu wanda ya isa ya takani wallahi na
qyaleshi ban dau fansa ba ko uban waye kuwa” dariya ya barke da ita ya
dinga qyaqyatawa har suka saki baki suna kallonsa
“Saidai cin bulus na gaba,bulus kuma ai na gama cinta tunda na hadaki
da CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI2″ wata saukar guduma sukaji bisa
kawunansu,ba zainab kadai ba hatta da zinatu
“Cuta mai karya garkuwar jiki!” Zainab ta tambayeshi cikin
qarajidariyarsa ya ci gaba da yi yana kada kai
“Qwarai kuwa,wannan tsaraba ce da muke baiwa dukkan macen data
bijirewa Allah,ta zabi biyan buqatar duniyarta akan ta lahira” sulalewa
kawai tayi a gun,zinatu ta fasa kuka tayi kanta,ganin suna neman tara
masa jama’a ya sanyashi samo mai adaidata sahu ya dorasu ya saita
musu hanyar asibiti.
MUKHTAR
Tun ranar da sirrin ya yaye masa baki daya ya sauya,tamkar ba mukhtar
ba,hatta da abdallah sai da ya samu sauyi da naqasu wajen kulawar da
yake samu,.ya kusa wata bai zuwa ko ina yana gida,sai abdallah ya
matsa da rigima yake fita waje ya dan tattaka da shi a qafa ya
dawo,babu abinda ke bijiro masa sai tausayin sumayya da tunanin da
wanne ido zai kalleta?,ko wane minti daya tana dawo masa ne da irin
abubuwan da ya aikatawa sumayyan,tun daga auren zainab zuwa ranar
rabuwarsu,wasu abubuwan gani yake tamkar a mafarki suka faru ba a
zahiri ba,kuka kam ya yishi sau babu adadi,baisan iyaka ba,yana so yaje
ya warwarewa su malam komai amma yana jin wata ‘yar banzan kunya
da nauyinsu wadda a da bai jita ba,kusan ya mance kwanansa nawa
rabonshi da gidan,saidai ya zame masa dole yaje gidan don sauke
nauyin dake kansa.
**
Zaune take gefan gado sanye da hijabinta tana ci gaba da sharce
hawaye,tsahon kwana biyu da faruwar lamarin amma ta kasa tsaida
hawaye a idanuwanta wanda ita kanta ta rasa dalilin haka,kukan nata
ya dadu ne tun bayan gama wayarsu da anty dije wadda kejin tamkar a
kanta hakan ya faru.
Halima ce ta shigo dakin
“Yaya sumayya kije inji malam” jikinta ya qara sanyi a zatonta magana a
kanta ne bata qare ba,duk da cewa babu abinda ya fada face yi mata
addu’a bayan ya gama saurarar rayuwarta a gidan mukhtar,fada daya
yayi mata na rashin neman taimako daga wanda tasan ya fita gogewa
da sani kan irin wadan nan lamuran,al’amura ne da kake buqatar
addu’a koda daga wajen iyayenka ne daga bakunansu,tunda addu’ar
tasu karbabbiya ce a wajen ubangiji.
Cikin sassanyar murya tayi sallama a falon nasa,da abdallah idanunta
suka soma tozali,ko kadan batayi tsammanin ganinsa a lokacin ba shi
ko mahaifinsa,ai da gudu ya baro jikin mukhtar din ya iso inda take
tsaye ya riqeta yana kiran amma na,jikinta da zuciyarta baki daya a
raunane suke,hakan ya sanyata zubewa shima ya fado jikinta,sai ta
rungumeshi a jikinta tayi qas da kanta hawaye ya balle mata a
boye,cikin dabara take shareshi.
“Sumayya” taji malam ya kirata
“Na’am” ta amsa murya a sarqe
“Ga mukhtar nan yazo neman gafararki kan abunda ya faru tsakaninki
da shi a baya,wanda mu nasan ya riga da ya wuce a gunmu saidai
tsakaninku dai” ya fada yana miqe ya fice ya turo halima ta zauna da su
tunda ya sani a lokacin bai halatta ya barsu su kebe ba,har a sannan
tana matsayin matar lukman har zuwa sanda ta kammala idda.
Dauke idanunsa yayi da sauri daga kanta saboda tunawa da yayi matar
wani ce,rabonsa da ya sanyata a idanunsa ya mance,tun kafin aurenta.
“Sumayya,nazo gareki a matsayina na mutum mai tarin laifi,a
matsayina na mutumin da yafi kowa laifi duk duniya a gurinki,nasan
cewa kalmomina basu isa su haqurqurtar da ke kan abinda na aikata a
gareki ba cikin jahilci,gaggawa da yanke hukunci cikin rashin
bincike tun ranar da na san gaskiyar lamarin naso neman gafararki
amma hakan bazai yiwu ba saboda kina gidan wani.yanzun ma mama
da malam mazo sanarwa ya gayan kina kusa,don girman Allah sumayya
na roqeki ki yafemin,koda kuwa wannan ne alfarma na qarshe da
zakiyimin,babu shakka zainab ta zalunce ni ta zalunceki ta kuma
zalunci danmu,kimin afuwa don Allah” tsam ta miqe ba tare da tace
komai ba ta dauki abdallah ta fice daga falon,sai yayi qasa da kansa
zuciyarsa na masa zafi.yayin da nauyi ya kama halima,sai ta miqe tabi
bayan sumayya itama.
Ranar bacci barawo ne kawai ya dauketa,zafi goma da ashirin ke bugun
zuciyarta,ta duba ta laluba kaf rayuwar aurenta babu wanda ya ruguza
farincikinta sai mata ‘yan uwanta,babu abinda ta aikata musu don
kawai sun hada miji?,me yasa kishiya ta zame mata qalubale cikin
rayuwarta baki daya?.
Sannu kwanaki suka dinga hada satittika,satittika suka hadu suka bada
watanni,ta miqawa Allah dukkan lamarinta baki daya,ta yadda babu
bawan da ya isa ya gujewa qaddararsa,watanni uku cif cif iddartata
cika,ta godewa Allah bisa baiwa da ni’inar lafiya da ya bata,ta watsar da
dukkan wani abu ta rungumi rayuwarta,riqon Abdallah ya dawo
wajenta,hakanan taci gaba da makarantarta na koyon sana’o’i,wanda
zuwa lokacin ta qware sosai wajen iya humra kwalakca da turaren daki
na kaya da na tsuguno.ya abbakar shi ya bata jari ta soma
gwadawa,Allah kuwa ya sanyawa abun albarka don ciniki take
sosai,don kana shigowa gidansu zakasan ana saida humra balle kuma
jikinta,nutsuwa sosai ta sake zuwa mata,wani girma da hankali na
musamman ya soma gameta,mukhtar kuwa har yau bata yarda ta sake
ganinsa ba ma bare ya dagula mata lissafi.
*****
Qarfe bakwai na bayan sallar magariba ta gangaro cikin layinsu
abdallah na sabe a kafadarta,tun daga makaranta ta wuce gidan anty
maryam qanwar mama sai gab da magariba ta fito.
Tana gab da gidan nasu ta kula da motar wadda ko daga bacci ta tashi
zata iya ganeta,motar mukhtar ce,sai ta dauke kai tana qoqarin wucewa
cikin gidan,saidai abdallah dake kafadarta wanda ya soma zillo ganin
babansa yaqi bada hadin kai,tilas taja tunga ta saukeshi da niyyar ta
wuce ta barshi a gun,saidai tana dagowa daga durquson da tayi ta
tsinci mukhtar din tsaye a gabanta
“Zan wuce malam” ta fada ranta a hade
“Kiyi haquri malama” ya fada da irin salon muryarta, kicin kicin tayi
ganin yadda yake son maida lamarin wasa
“Ka bani hanya da Allah kana batamin lokaci bana son shirme” tsit yayi
yana kallonta,ita kanta sai taji kalma ta mata nauyi,don haka ta basar ta
hanyar gyara hannun hijabinta
“Sumayya” ya kirata da wani irin salo wanda ada can yake kiranta da
shi,kira ke da idan yayi mata take jinsa har cikin jikinta
“Ki yafemim sumayya,a kullum tsahon wata biyar kenan cikin neman
yafiyarki nake,idan na kira baki dauka,idan nayi miki saqo baki
reply.kiyi haquri ki yafemin,na yadda nayi babban kuskure a rayuwata
amma na girbe abinda na shuka ai,na rasaki na tsahon wasu
shekaru,ban taba tunani a baya akwai abin zai rabani da ke ba idan ba
mutuwa ba,tunda na rabu da ke sumayya ban taba samun nutsuwa ta
minti guda ba,Allah ya hukuntani tunda har kin shiga gidan wani
sumayya,ki zama mai afuwa da yafiya kamar yadda na sanki nasam
halinki a baya,mukhtar dinki ne sumayya bazan daina neman yafiyarki
ba matuqar baki yafemim ba har sai ranar da numfashina ya bar gangar
jikina..”da sauri ta katseshi don yana neman karya mata zuciya
” don Allah ka bani hanya,na gaji da jin kalaman bakinka”‘murmushi ya
saka yana kada kai
“Shikenam sumayya,idan kinso ma ba zaki sake gani na ba tunda haka
kika buqata,amma bazan daina neman afuwarki ba,na barki lafiya”‘ya
fada yana juyawa ya danqawa Abdallah wani dan madaidaicin kwali ya
wuce motarsa,sai ta samu kanta da tsayawa cak a gun ta kasa tafiya har
ya bar layin,tausayinsa nason rinjayar zuciyarta,tuna wahalhalun da
tasha shi ya bijiro mata ya taurarar da zuciyarta,kama hannun abdallah
tayi suka shige ciki.
***
****
Tunda ya bar gidan yaso tilastawa kansa cireta daga zuciyarsa saidai ya
gaza hakan,wata sabuwar soyayya da qaunarta ke yawo ko ina cikin
jinin jikinsa fiye da irin qaunarta da yake ji a da,sai ya soma komawa
wani iri,ko da yaushe cikin tunani,ga wani matsanancin ciwon kai dake
matsanta masa wanda ke kwantar da shi.yana mamakin yadda ya kasa
haqura da ita,ji yake tamkar idan ya haqura da ita din zai rasa
numfashinsa,hakan ya sanya ya shirya da kansa wani dare bayan ya
yiwa abbakar waya ya sanar masa ya gayawa malam zaizo zasu
tattauna,idan da hali abubakar din ma ya zauna.
Qarfe takwas yana sitring room din malam din dake qofar
gidansu,hakan ne ya sanya babu wanda yasan da zuwansa a cikin
gidan.
Duk yadda ta kai ga tunanin duniyar gidanta zata sameta yadda
takeso ba haka abun yazo mata ba,komai na neman lalace mata bayan
ta tabbatar da cewa tayi nasarar tuge sumayya daga gidan,gaba daya
yaranta yadda ta sansu a yanzu ba haka suke ba,baki dayansu kansu a
hade yake,qarami na girmama babba, haka babba na tausayin
qarami,nuwaira na cikinsu tamkar cikinsu daya da ita,ita ke jagorancin
ragamar sauran a matsayinta na babba,duk yadda taso ga sake raba
kansu abun yaci tura,duka ne a yanzu basa tsoron dukanta,da tayi abu
zasu ce mama babu kyau fa abu kaza,ko daya daga cikin tarbiyyar da
sumayya ta dorasu babu wadda suka watsar,a yanzu haka sunfi qaunar
zama wajen haijiya akan wurinta,saboda babu abinda ke shiga
tsakaninsu sai duka hantara da tsawa saboda basa mata yadda
takeso,babu mai bin umarninta cikinsu matuqar ba kan dai dai bane
hatta da qaramarsu basma,bata fuskanci sumayya ta gama da rayuwar
gidanta ba sai da yaran suka dinga gudunta,idan ranar makaranta ne ba
zata sanyasu a idanunta ba sai dare,don idan suka dawo daga boko don
kada ta hanasu zuwa uslamiyya gun hajiya suke togewa su shirya su
wuce abinsu,ranakun qarshen mako kuwa gun hajiyar suke wuni,idan
ka gansu a bangarensu to wani abu suka zo yi suyi su sake komawa.
Lukman kuwa mallakar data yi masa sai ra soma damunta,ba irinta
take buqata daga gunsa ba,.ya zama kamar irin dolayen nan,komai tace
sai yace to,ya zama kamar qaramin yaro,hatta wanka da cin abinci sai
tace yayi,sai ya zame mata qarin nauyi cikim rayuwarta,bashi da wani
tunani ko kadan,ko wuta tace ya sanya hannunsa ba musu zai
tsumbula,abinda ta fuskanta har yau sumayya na maqale cikin
zuciyarsa,sau tari zai zauna ya yita kallon qofar dakinta babu
qaqqautawa har sai tazo ta koreshi,hakanan ko sunan sumayya yaji an
kira koda a hanya ne sai yayi firgigit kamar wanda aka tasa daga
bacci,idan kuwa su nuwaira na zaune suna hirarta sai ya zauna daga
gefansu yana saurararsu yana tambayarsu kan wasu abubuwa ko sanya
musu baki,a kan hirarta da suke zama suyi sai da karima ta tara su ta
musu dukan tsiya,ta kulle nuwaira kuma a daki sai da hajiya ta shigo
taci mata mutunci ta bude ta tace kada kuma ta sake dukar mata jikoki
itace abar a daka ai basu ba,nan ta saki baki ta dinga caccabawa
hajiyan magana,bata bu ta kanta ba ta kada kan jikokinta suka fice.
Wannan shine halin da karima ke ciki.
******* ***************
Kansa na sunkuye a qasa yana mai jin nauyi da kunyar abinda zai fito
daga bakinsa,saidau tilas ya furta din saboda yana mai cike da fata da
burin inganta rayuwa ne ta mutum uku,shi abdallahınsa da
sumayyarsa, kasa magana yayi har sai da malam ya maimaita fadin ina
jinka.yayin da ya abubakar ya gyara zamansa, kawu sulaiman wanda
yake qani ga malam ma yazo kawowa malam ziyara suyi hira kamar
yadda suka saba kasancewar su biyu suka rage raye a duniya ya tadda
zuwan mukhtar din
“Malam,ina mai jin kunyar neman wannan alfarma daga gunku,nasan
cewa na muku laifin da dukkan iyaye zasu ji babu dadi a cikin
ransu,saidai malam wannan alfarma da zan nema ina fatan zata shafe
dukkan wani abu mara kyau da ya faru a baya,sannan zata inganta
rayuwar mu baki daya” dan shiru yayi sannan daga bisani ya dora
“Malam,don Allah don annabi ina son ka bani auren sumayya karo na
biyu” shiru dakin ya dauka kowa da abinda yake saqawa cikin
zuciyarsa,tsawon wani lokaci babu wanda yayi magana,jinjina kai
malam yake kafin ya motsa
“Mukhtar,babu shakka kai mutum ne na qwarai,wanda shine babban
abinda yaja hankalina karon farko na baka auren sumayya,na sani na
shaida cewa dukkan wani abu da ya faru tsakaninku sharri ne da
makirci wanda babu wanda bazai iya fadawa cikinsa ba,abu na biyu
kuma sakaci da addu’a,na ukunsu rashin game hankali guri guda tare
da yin dogon nazari da bincike kan lamura,ammm..mukhtar”
Sai ya dago yana mai amsawa zuciyarsa na gudu daya bayan daya,duk
da cewa yana da cikakken fata na cewa zai cimma nasara
“A qa’ida ta addinin musulunci bazawara ita ke da ikon zabawa kanta
miji,saidai idan har anga tana neman jefa kanta wajen wanda bai
cancanta ba bayan ga wanda ya cancanta a gefe,kada ka manta
sumayya bazawara ce ita ke sa ikon zabawa kanta miji duk da nasan
cewa ko a yanzu nayi mata zaben miji ba zata musanta min ba,to amma
dai zan bata damarta, mukhtar,bazan hanaka neman sumayya
ba,amma kadai zan amince ne idan ta yarda da aurenka”.
Shiru yayi kafin daga bisani yace
” malam,na gode da wannan alfarmar da ka yimin,amma ina mai
neman alfarma ta gaba”
“Uhmmm,ina jinka”
“Malam,don girman Allah ina neman alfarma a gunka da ka karbi
sadakin sumayya daga gurina,nayi maka alqawari tsakanina da
ubangiji na matugar sumayya taqi aminta da ni zan karbi sadakina zan
haqura,na maka wannan alqawarin” shiru ne ya sake biyowa
baya,kowa da abinda yake nazarta qasan ransa,malam na gudun shiga
haqqin sumayya,.yayin da ya abbakar ke tunanin tabbas dama ce
wannan,don shi kadai yake iya fahimtar yaren sumayya,saidai ya hango
alamun rashin amincewa qarara a fuskar malam.yayin da mukhtar ke
duqe yana mai cike da fatan samun nasara.ya abbakar ne yayi saurin
yankan hanzarin malam din
“Malam,ina ga ka bawa mukhtar wannan damardomin ni na shaida
cewa sumayya na son mukhtar,hakanan na tabbata ba za’ayi nadamar
karbar sadakin nan ba in sha Allahu gyara ne zai tabbata a tsakaninsu”
kusan abinda kawu sulaiman ke ayyanawa cikin ransa kenan,don ko shi
yana tausayin sumayya da abdallah,saboda haka ya ari bakin malam ya
ci masa albasa
“Kaje muntari,an baka wannan damar,kaje ka kawo sadakin amma tare
da manyanka zaka dawo”. Jinsa yayi kamar ba a duniya yake ba,godiya
ma rasa wacce iriya zaiyi.ya tabbata yana jin karsashin samun nasara da
shawo kan sumayyansa.
k**
**
Kasancewar juma’a ce ta zamo washegarin ranar,qarfe hudu bayan
sallar la’asar mukhtar ya iso gidan shida kawunsa wato mahaifin abdur
rahman da kuma baffansa wanda yake wa ne ga innarsu da qanin innar
yasu su hudu kenan,kawu sulaiman da babban dansa sai yaya
abubakar su suka sake karbar sadakin sumayya karo na biyu,wanda ita
wadda ma ake batun sam batasan ana yi ba,don a lokacin ta tafi kitso,ta
dawo dai ta tadda mutane cikin sitting room din malam,saidai batasan
ko su waye ba tunda bata shiga ciki ba cikin gida ta zarce,bayan malam
din ya sallami kowa ya shigo cikin gida ya tadda mama ya buqaci
ganinta sannan ya sanar mata tare sa gaya mata baya son ta sanrwa
kowa har sai sun hada kansu da kansu,to ita din macace,kuna tasan
burin kowacce mace ta zauna da uban ‘ya’yanga,hakanan kowa ya san
nagarta da kyawun halayen mukhtar tun kafin wannan qaddarar ta
afkowa rayuwarsu.
ZAINAB
Tunda ta farka daga suman da tayi take qaraji tana kuka,sai data
tada hankalim duk marasa lafiyan dake dakin,babu yadda zinatu batayi
kan ta lallabata ba amma taqi yin shiru,duk yadda take jin dadin halin
da taga zainab din a ciki amma ji take kamar ta zura da gudu,dadi take
ji sosai da wannan labarin na samuwar cutar qanjamau jikin zainab
din.ganin yadda zainab din ke firgita musu marasa lafiya ya sanya suka
canza mata daki.
Kusan kwana tayi a haka kafin daga baya ta fara sassauta qugin da
takeyi saboda ta fara jin sassaucin radadin da takeji a zuciyarta.
Tana jingine a bango har zinatu ta gama bata shayin,saidai har a
lokacin bata ce komai ba sai faman jinjina kai da take,kanta ta daga ta
kalli zinatu da jajayen idanuwanta kamar na maza murya a kausashe
tace
“kin gayawa wani a gidan mu abinda ke faruwa ne”kai ta kada tana
aijiye kofin hannunta
“A’ah,babu wanda na gayawa”
“To bana buqatar kowa ya sani”
“To” kawai zinatun ta fada tana dariyar mugunta cikin zuciyarta.
“Cutar qanjamau zinatu” tayi furucin tana kallon zinatu tamkar mai
neman tabbaci kan wata magana,cikin fuskar tausayin qarya tace
“Don Allah ki bar daga hankalinki zainab,mutum nawa ne masu irin
cuwin ke rayuwarsu hankali kwance”
“Dalla can malama daqiqiya kawai,bani da dama kenan ta komawa
mukhtar ko kin manta?” Shiru zinatu tayi zagin da tayi mata yana mata
ciwo amma ba zata iya maidawa ba
“Zinatu,hakan fa yana nufin mutuwata gab take da ni kenan”
Kallonta kawai zinatun tayi ba tare da tace komai ba,kamar zararriya sai
ta miqe tsaye tana girgiza kai
“Inaaa,wallahi bazai yiwu ba,wallahil azim bazan mutu ni kadai ba,kai
ka zama silar kasancewata cikin wannan hali, kaine sila, kai ka jawo
min” ta fada tana zarya cikin dakin,mayafinta ta figa ta yafa tana fadin
“Ki nemo kudinsu ki biyasu ki sameni a gida zamu warware” tayi
maganar tana ficewa daga asibitin.
muje zuwa masu karatu