QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 12

  • QADDARAR SUMAYYAH






  • CHAPTER 12





  • Aqofar gidansu mai adaidaita sahun ya ajiyeta ta biyashu sannan taja akwatinta zuwa ciki. a Ta jima a soron ‘tsaye gabanta na faduwa,tana mtuqar shakkar iyayenta,saidai hakanan taji ana ingizata zuwa barin gidan,wani irin qunci takeji idan tana cikin gidan,numfashi ta ja sannan tayi shahada ta shige. Qannanta na tsakar gida suna karyawa jlkinsu sanye da unifoarm din islamiyya innarta kuma na daga cikin rumfarsu, “Lah sannu da zuwa yaya sumayya” suka fada halima na karbar mata akwatinta tare da shiga da shi cikin rumfar tasu ita kuma tabi bayanta.
  • “Lafiya sumayya da safiyarnan?” Innarta tambayeta cikin fuskar mamaki,gefan kujerar ta samu ta zauna sai kawai ta fashe da kuka ba tare da tace komai ba,baki innan ta sake tana kallonta kafin daga bisani ta yiwa halima nuni da hannu kan ta fita ta basu guri,daga qarshe itama data gaji da tambayarta sai ta miqe ta fito tsakar GIDA ta hau ayyukanta ta barta cikin dakin.
  • Wuni guda innan na tambayarta amma ta gaza cewa komai,to me zata ce mata ya korota daga gidan,ba matsala bace tsakaninta da mijinta ba ballanta ma tace,ba wani abu sukayi ba,to meye da’lilinta,sosai hankalin innan ya tashi ganin taqiyin maganar,gashi kuma malam din baya gida sun tafi musabaqa ta jaha da ake gudanarwa daga shi haryayan ta abubakar,amsa daya ta iya bata data tambayeta ina mukhtar din ta sanar masa yayi tafiya,sai kan innar ya sake daurewa,har dare tana zuba ido ko zata ga wani kan sumayyar amma shiru haka suka wayi gari. Mamaki innarta ta tashi da shi na ganin washegari sumayyan ta sake sarai,walwalarta take kamar babu wani abu da ya shalleta,wannan damuwar da tazo da ita jiya duka yau babu ita. Tunda suka dauko hanya daren jiya yake Allah Allah ya iso gidan nashi don yayi tozali da sumayyar tasa,qarfe uku da minti biyar dan adaidaita sahu ya ajjiyeshu qofar gidan nasa ya sallameshi ya shige gidan bakinsa dauke da sallama fuskarsa qunshe da murmushi don yana da yaqinin samun tarba mai kyau kasancewarya tafka sa’a cikin ranar girkinta zai dawo din.
  • Mamaki ne ya maye gurbin doki murmushi da fara’ar da yakeyi ganin yadda tsakar gidan yake a tarwatse babu cikakkiyar tsafta,sallama ya sakeyi karo na biyu saidai shiru babu amsa,a hankali idanunsa suka sauka kan dakin sumayya,take yaci karo da kwad’on da take kulle dakin duk sanda zata fita mamakinsa ya sake ninkuwa,ko da can sumayya sanda take da qananun shekaru ainun bata taba fita ba tare da uzininsa ba koda kuwa maqota ne,ya maida kallonsa dakin fa’iza yana sakaye,ya qarasa ya tura ya leqa kansa ciki bata nan,ya tura bandakin ya leqa nan ma bata ciki,jikin bango ya koma ya jingina tare da ajjiyejakar bacco din hannunsa,ba fa’iza ce damuwarsa ba sumayya ce,lambarta ya lalubo ya kira saidai an sanar masa da cewa a kashe take,ya maida wayar cikin aljihunsa yana maida ajiyar zuciya tare da shiga tunani.
  • Maganar fa’iza ta katseshi wanda da alama da wasu dake daga waje take maganar,ya zubawa qofarsoron idon har ta qaraso,da fari tayi turus,sai kuma ta qaraso tana dubansa “Au …… ashe kai ne ……. ashe yanzu zaka dawo ….. na dauka sai anjima gashi ban tanada ma komai ba”
  • “Ina sumayya take?” Ya tambaya ba tare da ya kula da surutun da take zuba masa ba,wani abu ya takore wuyanta,wato ta sumayya ma yake ko,zai gane kuransa ne wlh,baki ta tabe sannan tace
  • “Ka bani ajiyanta ne?”idanunsa ya ware baki daya har sai da taji tsoro ” ke bana ciki da iskanci ni kike gayawa haka,zan tattaki ne wallahi naga uban da ya tsaya
  • miki,banza sha sha sha,ina sumayya take nace miki”cikin gunguni tace “0ho,nidai da asussuba naga ta hada kayanta ‘a fice bansan inda taje ba”. Bai qara bi ta kanta ba ya shige dakinsa ya ajjiye kayan hannunsa,da sauri ya sake zaro wayarsa saboda tunawa da yayi waccan satin sumayyan ta saka masa lambar wayar innar tata ta gaya masa ya abubakar ne ya siya mata waya. Bugu biyu zainab ta daga tana fadin “ ya mukhtar ga innar can bari a kai mata”da sauri ya katseta “A’ah zainab,ina yayarku” “Gata can a daki a kwance” “Tun yaushe tazo gidan” “Tun jiya” “0k” ya fada sannan cikin sauri ya ajjiye wayar,kayan jikinsa ya cire sannan ya flto ya nufi tsakar gida,yanajin motsin fa’izan daga kitchen bai bi ta kanta ba ya tara ruwan wanka ya fada bandaki. .
  • Sai da ya rama sallar azahardake kansa sannan ya shirya cikin wani yadin kufta ruwan toka(ash),ya feshejikinsa da turare,yayi kyau matuqa,take zatinsa da kwarjininsa suka fito,yana sanya takalminsa sau ciki irin na maza fa’iza ta shigo dakin hannunta dauke da plate data ciko da jallope din taliya wadda keta zuba qauri saboda uwar wutar da ta babbaka mata saboda saurin da take ta kawo masa yaci tun kafln yaje ya maido da sumayya gidan plan dinta ya rushe.
  • “A’ah,mutari ina zaka daga dawowarka,ga abinci na maka ai koshi ka tsaya kaci” kallo daya yayi mata ita da taliyar tata yaci gaba da sanya takalmansa yana daga duqen ya jefeta da “Bani da buqata” gabanta ya fadi ganin asara qiri qiri na shirin riskarta,kwana uku tayi tana tattalin kayan tarkacen da ta dafa taliyar da shi sai gashi cikin mintinan da basu gaza biyar ba yana son janyo mata asara.
  • Matsowa tayi kusa da shi cikin marairaicewa da tausasa murya irin wadda bai taba riska daga gareta ba ta soma hila‘tarsa,da sauri yaja baya tare dajan matsiyacin tsaki ganin tana gab da shafa masa maiqon abincin,maqullin babur dinsa ya zara ya fice ya barta tsaye a nan dafe da kai.
  • Tana kwance cikin falon yaro yayi sallama ya shigo “Wai mukhtar ke magana a qofar gida” inji yaron,zumburta miqe zaune saboda wata muguwar faduwar gaba data tsinci kanta a ciki,da sauri ta qule uwar daka sanda taji muryar inna na sanya hijabinta tare da cewa yaron ya shigo.
  • Ta window ta dinga leqensa sanda yake tsugunne gaban innan kansa qasa yana gaidata,sosai ya mata kyau,mukhtar akwai bala‘in kwarjini da kyawun siga,sonsa da qaunarsa ke dambarwa cikin zuciyarta,gefe guda kuma wani mashahurin tsoro fargaba da qin son komawa cikin gidansa ke kai kawo cikin wani Irin qarfi cikin qirjllinta,saita koma gefan gado ta zaunajiki sanyaye tana fidda qwalla. Tana jin shigowarsu cikin falon shi da innar,ta sa baki tayi kiranta,sai data kirata kusan sau hudu sannan ta samu ta fito,kanta a qasa tana digar qwalla,gefe ta samu ta takure kanta a qasa ta gaidashi,ya amsa yana dubanta,har yanzu mamakin daya daureshi tun farko shi yaqi sakinsa,me ya samu sumayyar?,me yayi mata ta baro gidansa ba tare da saninsa ba?. “Ka ganta nan,nima hakanan na ganta da sassafe bansan me ya faru ba,kuma juyin duniya meke faruwa taqi cewa komai,to gaka nan dai gata” inna ta fada tana dubansu 
  • “Wlh nima inna dawowata na taras bata nan,amma ki sake tambayarta inna ko wani abu nayi mata”waiwayawa tayi cikin daurewar fuska dake nuna bata son wargi tace ” ke sumayya …… dubeni da kyau banason rashin mutunci da iskancin banza,ki gaya mana me mijnki yayi miki?”cikin muryar kuka tace “Babu inna,babu abinda yayimin wallahi” cikin hargowa da bacin rai innar ta sake cewa “Babu abinda yayi miki don iskanci shine zaki debo qafa ki taho gida,to ki tashi tun muna shaida juna tun kafin mahaifinki ya dawo sawunki a likkafa ki tattara kayanki kibi mijinki” wani irin kuka ta fashe da shi tamkar ana cire ranta ba tare da ta iya cewa komai ba,juyin duniya inna tayi mata ta tashi ta bishi taqi,har duka ta kai mata amma a banza,ganin hakan ya sanya mukhtar tarar innar yace Inna,ki barta,barta kawai,idan malam din ya dawo ko zuwa gobe ne sai na dawo” bacin rai tsantsa ne cikin ran innan haka mukhtar din ya fita. Sake qara sautin kukan nata tayi can qasan zuciyarta na mata zafi,ta rasa dalilin da ya sanya ta yiwa mijin nata haka,can qarqashin zuciyarta itama son binsa take,son kebancewa take da shi,tana da buqatarsa,tana buqatarjin duminsa amma tsanar gidan ya taso ya danne komai. 
  • Tun innan najin haushinta dajin haushin kukan nata har abun ya fara bata tsoro,addu’a ta soma cikin zuciyarta tana fata ba abinda take tunani bane ya afkawa sumayyan. Tunda ya koma gidan ya qulle kansa cikin dakinsa,fa’iza ta sake dawowa da niyyar bashi taliyar,nacin duniya yaqi bude qofar,da taga haka kuma ta lura bai dawo da sumayyan ba sai ta watsar da shi tayi komawarta daki tare da kwafar da taliyar cikin kwandon shara tunda burinta dai ya cika,dama ba wai damuwa tayi da yunwar cikinsa ba,aikinta dake cikin taliyar take yiwa kuma komai ya tafi dai dai. 
  • Tun a daren da malam din ya dawo ta zayyane masa komai,shiru yayi cikin dogon nazari,innar tayi niyyar taso masa sumayyan ya dakatar da ita yayi yace ta barta zuwa safiya sa hadu. Qarfe bakwai da rabi na safe ta shigo dakin malam din sanye da hijabi,ga mamakinta sai ta tadda su tare da mukhtar,gabansu kayan kari ne wanda malam din ya gama karyawa kasancewar da wuri yake karyawa ya kuma takura mukhtar wanda shayi kadai ya iya sha. “Sumayya,me ya hadaki da mai gidanki wanda harya sanyaki fitowa daga gidanki ba tare da izinin mai gidanki ba?bayan ba haka muka baki tarbiyya ba” Shiru tayi qwalla na taruwa cikin idanunta ta daga kai ta dubi abba malam din,inna da zuciya ta hasalota tace “Tsabar rashin mutunci ne da sakarci kawai ba komai ba” da sauri malam din ya dakatar da inna ta hanyar daga mata hannu sannan ya sake duban sumayyan “Uhmmmm,ina jinki” ya fada yana zuba mata idanunsa,motsa bakinta ta shiga yi sai ya fahimci tamkar bata son yin magana ne saboda haka ya bata qwarin gwiwa “Kada ki ji tsoron komai kada ki kuma damu,ki gayamin ko ma mene,mu iyayenki ne baki da kamar mu,baki da wanda zaki gayawa damuwarki sama da mu kinji ko?”kai ta gyada 
  • sannan ta bude bakinta qwalla na ziraro mata ” Abba ……. bana son gidan,haushin gidan da d’akina nakeji,tsoron dakin ma nakeji,bana iya bacci,wani abu kullum sai ya fito ta bango yana kiran suna na …… “shiru ne ya ratsa dakin,kowa da tunaninsa,tausayinta ke yawo cikin ransu. 
  • Bayan dogon nazari da abba malam yayi sannan ya magantu “Kin tabbata kina addu’o’inki kuwa?” Shiru ta danyi sannan cikin karyewar murya tace “Eh inayi amma wani lokaci ina mantawa bana yi” kai yajinjina “Shikenan babu komai,wani lokaci kuna sakaci da addu’a har shaidanu ke samun damar rabarku su cutar da ku,ba komai ki shirya kibi mai gidanki zan baki qarin wasu addu’o‘in ki hada dana gunki,ki tabbata kin dage dayi babu fashi,insha Allah babu abinda zai sameki”. Ga mamakinsu sai ta fashe da kuka kamar wadda ake zarar ranta ” Allah abba malam bazan iya komawa ba,tsoro nakeji abba,don Allah ku qyaleni”idanu suka zuba mata baki daya,bayan wani lokaci malam ya maida kansa ga mukhtar ya dafashi “Kayi haquri mukhtari,ka bar min sumayyah anan,bayan kwana uku kacal kazo ka dauketa,kayi haquri kuma kada ka damu,ba zata wuce kwana ukun ba” kansa a qasa cikin girmamawa yace “To malam,na gode” ya miqe ya fita suka bishi da kallo. 
  • Inna ce ta soma cewa cikin laushin murya “Meye hikimaryin haka din malam?” “Zaki gani habiba,ku shiga ciki ke da ita sai ki dawo ki dauko kin jakar fatar can ta cikin
  • uwar dakina” “To” ta amsa sannan ta miqe ta kama hannun sumayya dake ci gaba da kuka suka koma ciki. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *