QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 13

  • QADDARAR SUMAYYAH








  • CHAPTER 13




  • Qarfe goma na dare tana saman gadon innartata,juyi kawai takeyi tare da tuhuma da kuma bincikar kanta kan abinda ta aikata,batasan dalili ba batasan me yasa ba ammaji ta dinga yi kamar ana ingizata barin gidan,wata qauna da kewar mukhtar din suka kamata,halima ce ta shigo dauke da wayar innarsu “Yaya sumayya,yaya mukhtar ne” ta fada tana miqa mata wayar,da sauri ta miqe ta amsa wayar sannan ta kara a kunnenta halima tajuya ta fita,kasa cewa komai tayi har sai da yace “Sumayyah!” Muryarsa a tausashe
  • “Na’am” ta amsa muryarta na rawa
  • Sumayya …… me yasa kike son ki gujemin bayan kinsan zuciyata ba zatajuri haka ba?,sumayya ko cikin mafarki banson mu rabu bare a gaske,a zahiri kuma idanu biyu” tuni ta fara tara qwalla a idanunta,zuciyarta na sake karyewa
  • “Ya mukhtar ban sani ba,nima bansan dalili ba da ya sanya na tsani dakina ba,bansan dalili daya sa na tsani dakina ma baki daya ba,kayi haquri ya mukhtar …….. kaji?” Shiru yayi yana mamako,babu shakka gaskiya take gaya masa har cikin zuciyarta,ya riga da yasan sumayyan sosai,koma mene yanajin ya haqura ya bada kwana ukun kamaryadda malam yace yaci gaba da addu‘a kamin zuwan kwanakin,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “Shikenan….babu komai kada ki damu kinji,muyi addu’a mu jira kwanakin ukun kamar yadda malam yace” “To” ta fada,sai ya kawar da zancan ya soko wani don son faranta mata rai da kawar da zancan
  • “Yanzu me zan samu my sumy,nayi kewarki sosai,na dawo da kewar taki kuma na tarar kin min yaji” ya qarashe cikin sigar shagwaba,dariya sosai ya bata har ta dinga jiyo sautinta ta cikin wayar wanda hakan ya masa dadi sosai,kewarsa taji ya kamata kamarta bude idanu ta ganta gabanshi yajanyeta da hira har sai da ya qarar da dukka kudin dake cikin wayarsa sannan ya haqura.
  • cikin kwanakin duk wani hadi da malam din ya sani na kariya daga shaidanu ya hada ma sumayyan,suratul baqara itace ruwan shanta,ayatush shifa,da ayoyin karya sihiri,hadin ganyan magarya,man habbatus sauda shi take shafawa saboda yana kore duk wani shaidani da zai iya kusantarka,sai turaruka daban daban,azkar na safiya da maraice da wasu qarin addu‘o’in kan wanda takeyi Ita kanta cikin jiki da zuciyarta takejin salama da farinciki,dokin ganin mukhtar da son komawana dakinta take.
  • Ranar kwana na biyun da maraice sai ga abdur rahman,sosai tayi mamakin ganinsa yace mata yaje gidan bai tadda ta ba,wannan sabuwar abokiyar zaman nata ta gaya masa bata nan,ta tafi kuma ba zata dawo ba,bata boyewa abdur rahman din komai ba ta gaya mishi. Yajima yanajinjina kansa sannan yace “Idan zaki amince ina da buqatar muqullin dakin naki zan duba shi ko da taimakon da zan iya miki,kinsan fannin magungunan musulunci na karanta,yanzun haka ma yaya mukhtar din nazo kawowa katin gayyata zuwa bude asibiti da zamu dinga treating cututtuka da magungunan musulunci” cike da gamsuwa ba tare da haufl ba ta shiga daki ta miqa masa muqullin ya amsa ya mata sallama ya fice,a qofar gidan ya tsaya ya fidda wayarsa ya kira mukhtar ya shaida masa,take ya bashi izinin shiga,sai da yayi sallama sau biyar aka masa tare da dora
  • “Dalla a shigo an cikawa mutane kunne da wata sallama” a tunaninta yaya yahanasu ce ta mata aike,kai tsaye ya doshi dakin sumayyan ya bude ya shiga. Cikin nutsuwa ya dinga nazarin dakin bayan wasu addu’o’i da ya dinga karantawa a bayyane,fa’lza na tsakar gida kame da qugu tana leqen dakin gabanta na faduwa,addu’ana daya kada ya zamto ya karya duk wani kafl da shiri da tasa aka yiwa dakin. ‘ Tsawon mintina talatin ya kwashe cikin dakin yana karanta wasu ayoyi sannan ya kulle dakin ya fice,da kallo ta bishi fa’izar kamar idanunta kamar zai fado,sai da taga fitarsa
  • sannan ta saki ajiyar zuciya tare da zama gefan rijiya. Saidai bai wuce wasu mintina talatin din ba sai gashi ya dawo,hannunsa dauke da kaskon wuta mai garwashi sai qwarya,dakin ya sake budewa ya shiga bayan ya tari ruwa cikin qwaryan,zama yayi sosai kan daya daga cikin kujerun yayi bismillah ya fara karanta ayatur ruqya gabaki dayanta,sannan yabi kowanne lungu da saqo na dakin ya yayyafeshi tas da ruwan,komawa yayi falon ya ajjiye qwaryar ya bude wata farar leda mai dauke da ‘ya‘yan habbatus sauda ya watsa cikin dakin ya shiga turare dakin ciki da falo.
  • Kasa daurewa fa’iza tayi ganin sai da ta dangana da bakin qofar dakin sumayyan ganin hayaqi mai qauri na fitowa daga dakin,gabanta ya fadi tana tunanin wani qullin ake mata,cike da masifa tace 
  • “Wai malam waye kai ne?,meye haka da zaka shigo gidan mutane kana wasu qananun surkulle,bana ciki da rainin hankali da iskanci  ka fice mim daga gida tun ban tara maka mutane ba”. 
  • Dago idanunsa yayi ya watsa mata,take wani kwarjininsa ya daureta,jikinta yayi laqwas bakinta ya mutu,duk tijarar da taso yi ta koma ciki,kafeta yayi da idanu har ta saki qofar labulen ta koma dakinta,zama tayi bakin gadonta tana ta’ajjubin wanne irin mutum ne wannan yaron?,tana zaune nan har ya kammala ya kulle dakin ya fice. 
  • Gidan ya koma ya riski sallar magariba
  •  tare da malam sannan daga bisani ya nemi kebewa da shi,cikin falonsa dake zauren gidan suka shiga,bayan sun sake gaisawa abdur rahman din ya gabatarwa da malam maganar sannan ya dora da abinda na fuskanta malam ba qaramin mugun nufi aka nufi sumayya da shi ba,saidai koma mene Allah ya taqaita darajar addu’a ya rage kkkkk QADDARAR TATA,naje gidan kuma na aiwatar daga cikin abinda Allah ya horemin na sani kan irin wadan nan mashaakilat din,kuma in sha Allahu komai yazo qarshe babu abinda zai sake samunta da izinin Allah”gyara zamansa malam din yayi sannan yace “Hakane,tunaninmu yazo daya abdur rahman,mun gode qwarai da gaske daka nuna kulawarka kan lamarin,Allah yayi albarka,kuma in sha Allahu zamu ci gaba da addu’ar,Allah ya tsare gaba” “Amin amin malam” ya amsa a ladabce sannan daga bisani sukayi sallama ya bawa malam muqullin dakin shiya wuce. 
  • Qarfe takwas na dare suna tafe kan babur dinsa bayan ya daukota,wani farinciki ke ratsa zukatansu jinsa yake tamkar wani sabon aure. Murtala suya spot ya zarce ya siya musu kaza da damammiyar fura sannan suka qarasa gida. A tsakar gida suka taddata tana ta faman safa da marwa,tunda ya sheqa wanka ya fice da magariba ta kasa samun sukuni, gabarta qara daduwa take duk bayan wata daqiqa,qofargida kuwa ta leqata yafi sau a qirga tana addu’arganinsa ya dawo shi kadai,sallama sumayyan tayi hannunta dauke da leda kanta tsaye ta doshi dakinta,sai data tsaya bakin qofar dakin tayi addu’a sosai sannan ta shiga,cikin ikon Allah abinda ta zaci zata ji bata jishi ba,dakin gadonta ta wuce ranta qal tamkar babu wani abu da ya taba faruwa da ita,tabbas babu shakka addu’a takobin mumini ce. ‘ Sai da ya kulle gidan sannan ya tako zuwa tsakar gidan,ya ganta amma ya dauke kai tamkar bai ganta ba yana shirin wucewa,sam har yau ya kasa sonta,ya kasa jinta a jikinsa 
  • ko zuciyarsa ko da qanqanine,baisan dalili ba kwata kwata ya tsaneta bata burgeshi. 
  • Ganin da gaske wucetan zaiyi ga wani dan banzan kishi na sunkutarta ya sanya ta saurin shan gabansa “Wai me kake nufi ne?,wallahi babu inda zaka,daga dawowarta yau shine saboda rashin adalci zaka debi kwana ka kai mta,ai sai ka bari sai gobe ko” wani banzan kallo ya jefeta da shi,yau din cikin farinciki yake kuma baya buqatar abinda zai tarwatsa masa farincikin da yake sa ran samu a yau,cikin kakkausar murya yace “Ki matsa daga gabana,umarni ne ba shawara ba” ya fada a tsawace,taji tsoro amma taurin kai ya sanya ta shanye,ta bude baki zata sake magana ya sanya hannu ya janyeta gefe daya ya wancakalar yayi wucewarsa. 
  • Wani kukan baqinciki da takaici ta saka,wankin hula na neman kaita dare,duka magungunan da ya yahanasu ta amshi kudadenta ta kawo mata tana zuzuta mata aikinsu sam ba haka ta gani ba,haka kawai sun hadata da diyar malamai tana ta faman wahala da ita,wahalar ma ta banza,eh ta banza mana tunda k0 hankalin mukhtr din ma da akeyi don shi har yau ta kasajanyoshi gareta,kullum kwanan duniya kamar sake sabunta qaunar sumayyan ake cikin ruhinsa ba qoqarin fidda ta cikin zuciyarsa ba?,abu goma da ashirin kenan,sam wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa. ‘ A fusace ta shiga dakinta ta lalubi wayarta,lambar yaya yahanasu ta kira da niyyar yi mata wankin babban bargo saidai kash ta daki gurbi wayar tata a kashe take,da sauri ta sauya akalar kiran nata zuwa ga fadima,cikin sa’a ta sameta,tun kafin fadiman tace wani abu fa’iza ta soma sauke mata kwandon rashin mutunci,zagi na tsamar nama ta dinga luluqa mata tare da laqaba musu sunan macuta,sai da ta tabbatarta rage farashin baqincikin da take ciki sannan ta datse layin tana huci tare da cin alwashin gobe har gida zata yi tattaki taje ga yahanasun ayita ta qare,don ba zata dauki asara ba sai ta biyata kudinta,tunda ai ba ita daya ke da buri ba suma suna da buri don me zasu dinga cutarta suna wankarta ana 
  • amfani da kudinta kadai?. Kwanan baqinciki tayi tare da kusan qarar da daren nata wajen zirga zirga tsakanin dakinta da window din sumayya,su kam suna can wata duniya basu san ma me takeyi ba,kwanan farinciki qauna bege da faranta ran juna sukayi,yayin da tayi kwanan gadi da safa da marwar da babu lada. ‘ ‘tabbas duk wanda ya saki Allah yana tare da tarin wahala maras qarewa’ wannan kenan muje zuwa masu karatu,
  • cikin kwanakin da suka biyo baya damina ta shigo,wanda hakan shi yayi sanadiyyar zubewar ginin maqotan yaya yahanasu ya fadowa gidansu har yajanyo rushewar wani bangare na gidan,hakan ya sanya mukhtar yace su baro gidan su dawo gidansa don a samu sararin gyaran gidan nasu,ko bayan rasuwar mai gidan anty yahanasu kusan shine jigo dake d’awainiya wa su yaya yahanasun.
  • Qarfe biyu na azaharsuka iso gidan tare da yaranta biyu jamila da sayyada,sumayya na tsakar gida a lokacin tana wankin kayanta,da fara’arta ta taso tana musu sannu da zuwa tare da qoqarin karbarjakar hannun yaya yahansun bayan yara sun gama shigowa da sauran kayayyakin nasu d’akin fa’iza,kaucewa tayi gami da jifanta da wani kallo tana fadin “Kada ki kuskura ki taba min jaka,matsa da Allah ki bawa mutane guri” ta fada tana wuceta sauran yaran suka mara mata baya,a salube ta koma kan wankinta taci gaba da yi har ta kammala tana jiyo shewarsu cikin dakin fa’izan kai kace yaya yahanasun sa’arta ce,ya tabbatar cewa da ita ke shewa haka da yaya yahanasun sai tace bata da mutunci bata da kunya,amma ga fa’iza na faman shewa da qyaqyatawa gabanta,matar da ko sau daya sumayyan bata iya hada idanu da ita,biyayya take mata tamkar uwar mijinta haka ta dauketa sakamakon ganin irin girman matsayin da take da shi gun mukhtar. 
  • Tana kammala shanya kayan ta shige wanka saboda tana so taje kitso sakamakon ita ke da girki gobe,har ta fito ta gama shiryawa ko alamun dora abinci babu gun fa’iza,itama bata damu ba sai ta hada shayi kawai ta sha tayi focewarta ta barsu. 
  • Qarfe biyar ta dawo gidan saboda layi da ta taras a gidan kitson,tun daga qofar gida ta soma jin muryar fa’iza cikin balbalin bala’i,ta kutsa kai cikin gidan cikin mamakin ita da wa,dai dai lokacin da fa’izar ke fadin “Yo da kika damen da zancan ciki laifin uban waye mayun ‘ya’ya?,qanin naki yayi min cikin mana ya gani idan ban dauka ba,wata uwaryake yimin idan kwana nane banda kwanciya da zaki uzzura min,to wallahi babu ma mai kwanarmin cikin daki balle ya sanya min ido,dama daki ba daki ba yar zuciyar talaka,sai ku nemi gun kwana” ta fada tana komawa cikin dakin tare da banko labulenta. ldanu sumayya tabi tsakar gidan nasu da shi,ko ina kaya ne na yaya yahanasun a barbaje a qasa,gaban sumayyan ya fadi,jikinta yayi sanyi,ta qarasa tsakar gidan,hannu ta sanya tana tattare kayan nasu waje daya,tsawa yaya yahanasun ta daka mata “Kada ki sake taba mana kaya shegiya munafuka ‘yar gidan malamai,to wallahi bari na gaya miki idan ma shiga tsakaninmu kikayi da fa’iza kinyi kadan,hakan da takeyi bazai tunzura zuciyata ba tunda nasan ba cikin hayyacinta take ba,ke sayyada maza ku hade mana kayan gefe guda mu jira shi muntarin ya dawo” sororo tayi tana dubanta “Daina kallo na mayya,li’ilafi quraishi,ni baki isa ki cinyeni ba” sai ta kauda kai ta wuce kai tsaye dakinta ta bude ta shige. a 
  • Bata sake fitowa ba tayi zamanta cikin dakin,sai ta qirqiro wasu ‘yan qananun ayyaukan ma cikin dakin nata don kawar da duk wani tunani da zai dameta,tana aikin tana ambatar hasbunallahu wa ni’imal wakil,allahumk finihim bima shi’ka,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba,sai ya tafiyarda lokacinta cikin sauqi har aka kira sallar magariba,ta miqe ta fito domin daura alwala,suna zaune gefe daya na tsakar gidan da qullin kayansu,sosai har cikin zuciyarta taji babu dadi,bai kamata mukhyar yazo ya taras da su haka ba,ko babu komai ‘yan uwansa ne jininsa ne,kuma tayi imami cewa idan wani nata ne shima mukhtar din ba zaya wofantar da su haka ba,ta danne zuciyarta ta qarasa gurinsu,cikin sanyin murya tace “Don Allah yaya ki shigi dakina,ko da ba zaki zauna din ba ki shigo idan yaso idan ya 
  • mukhtar din ya dawo sai asan yadda za’ayi din” wani kallon banza ta bita da shi 
  • “Ke wallahi ki fita a idona,wai ke wacce iriyar mayatacciya ce ne,nace bazan shiga ba dole ne,to bari kiji,idan ma wani laqani aka baki na sai na shiga sannan zaki samu galaba a kaina to wallahi ki gayawa malaminki kunyi qarya kun kwana da yunwa” jikinta sai yayi sanyi ta kasa tafiya,zuciyarta na gaya mata basu zama masu kyautawa mukhtar ba indai yazo ya tadda jininsa a wulaqance,duk da tarin izgilu cin fuska da cin mutunci da ita yaya yahanasun kejifanta da shi,ba ita take dubawa ba karamcin mukhtar take dubawa. 
  • A haka mukhtar din ya shigo ya riskesu,tayi masa sannu da zuwa ta karbar kayan hannunsa duk da ba ranar girkinta bane,ya amsa yana duban yaya yahanasu.”a’ah,yaya yanzu kuka zone na ganku a nan a zaune ku da kayanku”kai ta girgiza “Inaaa,ai tun azahar muna gidan nan” cikin mamaki ya dubeta tare da zaro ido sai ya dubi sumayya yana jifanta da tuhuma,qas tayi da kanta don bata da ta cewa,ganin haka yasa ya dubi yaya yahanasun “Amma kuke zaune a nan?,kada kice min nan kuka wuni?” Waiwayawa tayi ta dubi sumayya “Sai ki bamu guri ko k0 ban isa ba?” Bata ce uffan ba ta koma dakinta duk da alwala ta fito da niyyar daurawa. 
  • Sai da taga shigarta dakin sannan ta maido dubanta ga fa’iza “Mutuniyartamu,wallhi lafiya lau ta karbemu,daga yi mata tambaya kan naji shiru har yanzu mun samu qaruwa ko a’ah ta shiga masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,qarshe tayo mana waje da kayanmu” sosai ransa ya baci,ya soma huci cikin fushi yace “Fa’izar?,to da tayi muku haka gidanta ne ko nawa?,bazan lamunci wannan iskanci ba” ya fada yanajuyawa zuwa ga dakinta wanda fa’izar na ciki tana jin kuwa tayi lakur abinta. 
  • Da sauri yaya yahanasun ta dakatar da shi “Kaga muntari bana son hauka fa,laifi muka yi mata mu muka bata mata rai,nasan kuma zata huce,don haka bance kaje ka sake bata mata rai ba,kadai lallabata har ta yarda mu zauna taren” jagale yayi tare da juyiwa yana duban yayar tasa,take kuma ya tuna sunfi kusa fa ita da fa‘izan,ya ma kamata a yau din ya qyaleta taga halin fa’izan taga wace ita ra’ayil ain wato ganin ido,saboda haka sai ya saki murmushi cikin salon canza shawarar da yayi farat daya,gyada kai yayi “Shikenan,muje to a lallabatan” da sauri suka miqe yaya yahanasun tana cewa “To,to ai kaga hakan yafi” tabi bayansa. Tana miqe daga kan gadonta tana taunar chewing gum dai dai,zama sukayi kan kujerarta dake fuskantar gadon,yayin da mukhtar ya qarasa gefan gadon ya tsaya,duk da cewa ransa a matuqar bace yake,ji yake kamar yajanyo fa’izan ya yi mata dan banzan duka ya watsar amma sai ya dake “Fa‘iza,me yasa ba zaki bar yaya ta zauna dakinki ba,ai ina ganin bai kamata ba” hura hanci take tana tunanin ko yanzu mukhtar ya soma tsoronta ne,inko haka ne kuwa tasa ta qare,tabbas sai kowa ma yaci ubansa cikin gidan “Mukhtar banga dama bane,bari kaji” ta fada tana miqewa zaune kan gadon Na farko bansan sa ido gaskiya kuma na fuskanci su sun fara koyar wannan halayyar,na biyu na fuskanci ni aka rainawa wayo,ga mai daki ciki da falo can ba‘a dosheta ba saini mai daki daya kamar zuciyar talaka” ba qaramin dukansa maganar tayi a zuciya ba amma ya hadiye don so yake ya  “Saboda haka su nemi gurin kwana don ni bazan zauna da wadan nan qattan a daki na ba” wani qullutun abu ne ya tokare masa wuya wanda ya hanashi sake magana,sai yaya yahanasu da tace “Haba ke kuwa fa’iza,kwana nawa ne duka duka mun koma gidanmu,ai ban zaci ko wani na turo gidan nan ki masa sauki a dakinki ba zaki kasa,kada fa ki manta nice silar zuwanki gidan nan” zabura tayi tana dakatar da ita “Kinga kada ki sake kice zaki mun gori,don ke kika kawoni gidan ai bake kike aure na ba,buqatar maje haji sallah kuma da taku buqatar ai ba haka siddan kika kawoni ba,sabida haka kuje ni don Allah kada ku cikan kunne,tunda kun nace sai kun zauna a dakin kuje zanyi tunani,ko kwana daya ne kuyi kafin ku koma inda kuka fito”. Ba qaramin daurewa kan yaya yahanasun yayi ba da kalaman fa’iza,duk yadda fadima ke gaya mata sai yau ta sake tabbatarwa da lamba daya ce ita wajen rashin mutunci tsiya 
  • da tsiyataku ” fa’iza ni kike gayawa haka”kanta tsaye babu kunya tace “Na fada din,ke kike aurena ne nace wai kawai da zaki takuran,wannan fa kamar kina 
  • lissafin sau nawa nake kwanciya da mijina ne”tuni maganarta sake dora yaya yahanasun kan dokin zuciya ” ke qaramar mara kunya,ko bani nake aurenki ba kinsan ina da power din da zan sa ungulu ta koma gidanta na tsamiya k0?” “Bismillah,sai mu gani ” ta fada tana murguda baki gami da turo daurinta gaban goshinta 
  • ta dage kanta idanunta na kallon ceiling din daki. 
  • tabbas tanajin yau idan bata nunawa fa’iza isar da take da ita a wajen mukhtar ba 
  • bata huce takaici ba,idanunta taf da bacin rai ta dubeshi “Mukhtar,ina so a yau yau din nan ka sawwaqewa fa‘iza,yanzun nan” ta qarashe cikin daga murya. 
  • Duk da cewa ranshi ya kai qololuwa wajen baci kan abinda fa’izq ta yiwa yaya yahanasun amma sai ya danne komai tamkar bai b’aci ba,ai dama duk wanda ya sai rariya yasan zata zub da ruwa,to ya kamata yaya yahanasun taga yadda tata rariyar ke zubar da nata ruwan,ruwan kuma da baiyi qasa a gwiwar malalowa ya jiqata sharkaf ba,kai ya kada sannan yace 
  • “Kan me zan saki fa’iza yaya,ni babu abinda ta yimin,hasalima fa’iza ai zabinki ce,kinga bai kamaci na wofantar da ita ba,zan riqeta hannu bibbiyu kamar yadda kika umarceni” tsawa ta daka masa 
  • “Mukhtar,kai makaho ne?,ko kuwa kai kurma ne,baka ganin abinda ta yimin bane,ni na umarceka nace ka saketa kamar yadda na umarceka ka aureta a baya” kai ya sake kadawa tare da yin tattaki don barin dakin yana cewa 
  • “Ki gafarceni yaya,amma yanzu na fara zama da fa’iza,don ni bata aikata min komai ba” sai ya fice abinsa ya barsu ana kallon kallo. 
  • Kira ya qwalawa sajida ya sanyata suka dinga jidar kayayyakinsu yana tayasu suna kaiwa dakin sumayya wadda ke zaune kurum tana ji da ganin sarau‘ar Allah,sai da suka kammala tsaf yaya yahansun na dakin fa’iza suna cecekuce,ganin abun na sake qamari ya sanyashi shiga dakin ya janyeta yana fadin “Kiyi haquri yaya yahanasu,kizo ku zauna dakin sumayya tunda itan da kuke so ta qiya“ sai ta waiwayo ta bishi da ido galala tana kallonsa,mukhtar din da baison bacin ranta?,mukhtar din da baiso a tabata amma yau an mata cin kashin data jima rabon ta da irinsa amma ya kasa cewa uffan,kardai mallaka fa’iza tayi masa wadda baya iya qetare umarninta?,ranta ya shiga suya ta shiga fatar cewa Allah yasa ba haka bane,batada wani zabi a yanzun illa ta bishi,idan yaso daga bisani tayi tunanin mafita a tsanake. 
  • Bayan sun shiga dakin ta zauna sannan ya kira sumayya ya fice zuwa dakinsa. 
  • Zaune ta tadda shi dafe da kansa,a hankali cikin kasala ta zauna gefansa,ta sanya tafln hannunta tana shafar bayansa a hankali,tasan fushin mukhtar din,saboda haka ta tabbatar ransa na a bace ne,kusan minti goma baice komai ba kafIn daga bisani ya dago ya dubeta “Sumayya” ya kira sunanta,a tausashe ta amsa sannan ya dora “Gasu yaya yahanasu nan zasu zauna dakinki,kinsanta sarai ita da yaranta baki daya,baki buqatar muraja’a kansu,na shaideki da haquri wannan halinki ne,to amma don Allah ki nunka haqurinki,baqunta zasu mana na wani d’an lokaci,insha Allah zanyi qoqari na kammala musu gyaransu cikin qanqanin lokaci,idan na kammala ma gini na sabon gida na can zan ara musu su zauna gudun fitina,kiyi haquri da su don Allah ki sake ninka kawaicinki” kai ta girgiza “Haba ya mukhtar,ai ba roqona zaka yi ba,umarni kadai zaka bada,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,nima yaya take agurina,insha Allahu babu wata matsala ko damuwa” “Na gode,Allah yayi miki albarka” 
  • “Amin yaya” ta fada tana sakin qayataccen murmushinta wanda har sai da ya sanyashi tsura mata idanu,hannu ta turo saitin idanunsa kamar zata tsone masa yaja baya suka saki dariya baki dayansu. 
  • Cikin dakin ya barta ya flta sallah,kasancewar tana faashin sallah sa’an nan kuma dakin nasa na hargitse don fa’iza ba kasafai take tsayawa ta gyara ba ya sanyata tsayawa tana dan kakkabe dakin haka ya dawo ya cimmata,kafin ya kai ga zama fa’iza ta fado dakin hannunta riqe a qugu ta nufeshi,ya fara cewa “Me aka girka” ran nan nashi a hade tsaf wanda ita a nata zaton aikin da take kansa ya fara tasiri ne,saboda haka kanta tsaye tace “Yau duka ma banyi girki ba wlh a gajiye nake” ta fada tana yatsina,sam ya tsaneta haryau 
  • ya kasajinta dai dai da qwayar zarra cikin zuciyarsa,bata dameshi ba dama bisa lalura kawai yake rabarta,qoqarin adalci ne kawai irin nasa tunda ta riga da ta rataya a wuyansa bisa alfarmar igiyoyinta uku dake hannunsa. Hannu ya miqa mata a daqile yace “Bani muqullan locker din kayan abinci na” ba musu ta fice don dauko masa,ya juya ya dubi sumayya “Yau ba’ayi girki ba gida na,me kuka bawa yaya taci ita da iyalanta?” Kanta ta duqar qasa sannan tace “Ka mance na tambayeka zani kitso?,tunda na Flta ban samu na dawo ba sai bayan la’asar,dana shigo kuma nima yadda ka taddasu haka na taddasu” kai ya gyada ba tare da yace komai ba,ta dawo da muqullin ta miqa masa,kai tsaye ya danqa su ga sumayya “Jeki ki samar mana da abinda zamuci” hannu biyu tasa ta amsa kana ta danyi jim,da kamar taqi abinda ya sata din,sai kuma taga hakan bai dace ba,idan bai isa da fa’iza ba ita ai ya isa da ita,miqewa tayi zata fice fa‘iza ta saki wani mugun murmushi,ga zatonta sumayya ta shiga cakwakiya mukhtar zai soma azabtar da ita kenan,fadawa tayi saman katifar kusa da shi tana fadin “Ammmmm …… idan kin gama kizo na gaya miki me ni kuma zaki dafamin” wannan karo kasa hadiye takaicinsa yayi sai daya juyo yace “Da yake baiwar gidan ubanki ce ko,wato saboda kinga na miki shiru ne ko …… hmmmmm ….. ki kiyayi ranar qin dillanci wallahi,wuce kije sumayya”,sai tajuya ta fice din,itakam ta ma rasa na cewa gaba daya,gaban fa‘iza ya fadi,kaddai jiya i yau ne dai mukhtar din,sai ta kasa hadiye qanin zagin da yayi mata ta miqe tsaye ” wacce rana ce ranar qin dillanci,ba ranar da hajar mai gari ta bata ba?,idan ba’a ganta a gun fa’iza ba sai me?”ta murguda baki tana niyyar ficewa,zuciya ce ta ciyoshi ya miqe cikin zafin nama ya flncikota ya zabga mata wani lafiyayyen mari,a gigice ta dafe kuncinta don bata zaci haka ba,karo na farko da mukhtar din ya soma taba lafiyarta,ashar ta danna sannan tace “Ni ka mara muntari,kayyasa kace yau da bala‘i,wallahi baka daki bulus ba sai na rama” . ‘ 
  • Daga hannunta tayi da niyyar kaiwa fuskarsa mari ya cafe hannun tare da murdeshi har sai ta qashin hannun ya bada wani qasss da alamu ya targadata,tsananin azaba ya sanyata sakin qara wadda ta sanya sumayya dake kitchen barin abinda take ta taho dakin cikin hanzari,dadin da taji data lura su yaya yahanasun da suka qure kallo cikin t.v dinta basu san me ake ciki ba,tun fara masa rashin kunyar duk cikin kunnenta ne saboda muryar fa’izan na sama ne sosai. 
  • Sanda ta isa dakin ya daga hannu da niyyar sake bata wani marin,cikin hanzari ta shiga tsakiyarsu ta riqe hannunsa,cikin taushi ta langabar da kanta tana duban tsakiyar idonsa wanda hakan shi ya karya lagonsa,ya zare hannunaa daga nata,bakinta bai mutu ba sai data wurga masa kalmar “Wallahi wallahi sai kayi dana sanin dukan fa’iza,sai ka biya farashin duka na da kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani” sannan ta fice. Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi sannnan tace “Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai ka fara bani tsoro sai ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da murmushi,take kaso 
  • saba’in cikin dari na bacin ransa ya zabge ya fadi sai ya dora hannunsa shima saman nata “Banaso ki farajin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan sake ba,kiyi haquri” kai ta girgiza tana murmushi 
  • “Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai” kasa magana yayi sai ya rungumeta kawai cikinjikinsa yanajin duminta,yana ganin girma da qimar wannan halitta mai tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma banda wannan,wala’alla ya iya jurewa. 
  • Sai da suka farajiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari ta fice tana ce masa tana zuwa. 




Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *