- QADDARAR SUMAYYAH
- CHAPTER 16
- Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon
- mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa’iza ba domin ba halinsa bane,amma
- halayyar fa’iza har ta kai haka?.
- “lna naki abincin?” Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi
- “Ya d’aki”
- “Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a |eda ki saka a share a zubar,shiga
- kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai” ya fada
- yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta flce don aiwatar da abinda ya
- umarceta.
- nhntn-tltihni-i-nnn-t-nn
- Cikin kwanakin ta dage sosaida addu’ar neman tsari,ta santabbas sham nmutum
- girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa’iza,ta fahimci irinsu matan da suka
- dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zashiya aikata komai saboda kishi,sosai
- take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar
- fa’izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa’izan zata shekara tana takalar tashin
- hankali bata bi ta kan(a,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu
- ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.
- tittitQICO-nnnn-i-nn
- Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta
- dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar
- sun makara basu tashi da wuri ba
- “Ya mukhtar,kamar kakarin amai nakeji fa a tsakar gida” shi din ma taji amma sam bai da
- muradin f’Ita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
- “Eh nima naji” yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
- “Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa’iza ce fa” shiru ya sake mata ganin hakan ya
- sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da saurarankakarin wanda yakefita
- tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsaya kashingida.
- Zuciyarmusulunciya sanyata ta kasadaurewa,saita miqe ta fidda hijabinjikinga ta
- nufl qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
- “Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi Ma 3 dubata ba,bamu
- san meke damunta ba” kai ya girgiza
- “Dawo tausa nake so kimin”
- “Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar”
- “Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan” ya fada yana maida kansa ya kwantar kan
- pillow,saijikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka tajuyo a sanyaye
- tahayegadon.
- A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara
- qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana
- dariya qasa qasa
- “Raguwa kawai sarkin kuka” ya fada yana lakucemata hanci,dariyata sakiya shigamata
- cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma’aurata wanda hakan shi ya hanasu Htowa da
- wuri.
- Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin
- fa’izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi
- da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin
- “Hasbunallahu Iafiya fa’iza?”
- “Banida lama” ta fada qasa qasada qyar,ta daga kaita kalli mukhtar da bai qarasogun
- ba,yanatsayeabunsa bakinqofar dakin sumayyanyana daura agogo
- “Yayamukhtar,koasibiti zamu?”Baicekomai ba sai hannunsa da ya sanyacikin aljihun
- wandonsaya zaro naira dubu biyuya miqa mata
- “Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya” ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya
- fice.
- Tanajin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran ba,duk da
- yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara sannan ta wafce
- kudin dake hannunta
- “Babu inda zaki rakani munafuka” ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi
- cikin zuciyarta tana fadin
- “Allah ka shirya,wato hali zanan dutse”.
- Tana daki tana shafa mai bayan ta kammala wanka ta jiyo fitar fa’izan.
- Suna zaune zasu ci abincin dare bayan ya kammala komai,tana gabansa tayi kyau
- cikin kwalliyar laceja mai adon baqi tana zuba masa abincin data shirya musamman
- saboda shi fa’iza tayi sallama ta shigo dakin fuskarta qunshe da murmushi hannubta riqe
- da farartakarda,daya daga cikin kujerun dakin sumayyan ta samu ta zaunajuskarsa a hade
- ya dubeta
- “
- daga ina kike takwas na dare?”sai ta rausayar da ido
- “Haba mana muntari,ka tsaya kaji ji da nazo maka da daddadan labari”
- “Ba wannan ba ki fara amsa min tambayar da na miki tukunna
- “Kash,labarin da zan baka yanzun duka yafi wannan muhimmanci,amma tunda ka nace sai
- kaji to daga asibitijikina ya rikice sai na wuce gida na kwanta acan,sai da magariba na
- danji dama dama” shiru yayi ya soma cin abincinsa,ganin haka ya sanya tace
- “Ka godewa Allah muntari,Allah ya kusa cika maka burinka da ka dade kana fata,ka kusa
- zama baba,an auna niinadajuna biyuharnawatabiyu”. I
- Qwarewa yayi da lomar abincin da ya kai bakinsa,sai ya soma tari babu
- qaqqautawa,cikin hanzari sumayya ta miqa masa ruwan tana jujjuya maganar cikin
- ranta,indai hakan gaskiyanetoyatabbata ITACE BATA HAIHUWA?. I
- Sai da ya sha ruwan sosai sannan ya ajjiye cup din,hannu kawai ya miqawa fa’iza
- wadda keta doka murmushi tana tunanin farinciki ya sanya mukhtar qwarewa,tabbas
- burinta ya kusa cika,zaman sumayya cikin gidan ya kusa zuwa qarshe,ta kusa raba mukhtar
- da kowa sai ita.
- Takardar ta miqa masa don ta fahimci ita yaje son gani,ya bude ta sosai ya shiga
- nazarinta daga farko har qarshe,gashinan rubuce a jiki,cikine dan sati takwas,amma sati
- takwas fa suka rubuta,harya bude bakinsa zaiyi magana sai kuma ya fasa,a yanzun ba
- muhallin yin maganar bane akwai muhallin yinta,saboda haka ya nannade takardar ya
- cusa cikin aljihunsa ya janyo abincinsa yaci gaba da ci.
- Dukkaninsu sumayyan da fa’iza sai suka zuba masa ido cikin mamakin ganin bai ce
- komai ba,fa’izan ce cikin zaquwa da sonjin abinda zaya fadi din tace
- “
- ya baka ce komai ba muntari,Allah ya yi maka kyautar da ka dade kana jira amma banga
- ka nuna komai ko kace min komai ba”kansa ya daga ya dubeta
- “Naji ai kuma na gani,zankuma magantun amma lokacinyin maganar ne baiyi ba,jeki sai
- da safe Allah ya inganta k0?” Jiki a sanyaye ta miqe ranta cike fal da mamaki,tayi zaton zai
- dauketa ne suyirawa suyijuyin murna,ta yadawa sumayya habaici yadda taga dama,amma
- duk da hakan ai lokaci na zuwa.
- A sanyaye sumayya ta dubeshi bayan fitar fa’izan
- “Amma yaya mukhtar kamar bai dace ba abinda kayin,sai nake ganin murna ya kamata ka
- nuna irin wadda baka taba nunawa ba,d’a fa da kuje muradi shi Allah zai baka?” Kansa ya
- daga yana dubanta fuskarsa qunshe da murmushi,sai kuma taga ya qyalqyale da dariya
- “Yanzu my sumy koda haka ne ya cancanci nayi murnar hada iri da waccar matar?,fa iza fa?
- Wadda ni da ke duka munsan halinta,bani da muradin samun zuriyya da kowacce mace a
- duniya sai ke,kecenakesoki zamo ta farkoda kika samamin zuria,ki bar maganar nan don
- Allah bana so in sakejin bakinki game da ita indai na isa da ke”
- “Insha Allahu” ta fada zuciyarta na karyewa,ina rna inama,ina ma tana da qarfin yaqi da
- QADDARARTA?,ina ma tana da ikon baiwa kanta haihuwa?,ina ma ace zata iya samarwa da
- mukhtar cikon farincikinsa,duk da bata da wannan ikon amma bata jin dai dai da daqiqa
- daya bakinta zai rufu koya gajiya wajen roqon mai badawar da ya albarkaceta ya azurta ta
- ya kuma bata haihuwa saboda karamci tausayi da kumajin qansa,sai tayi qas da kai
- hawaye na diga,da sauri ya daga kanta suka hada idani,da murmushi yake dubanta gami
- da kada kai
- “Bana so sumayya kin sani,ko ya kike sumayya haka nake sonki,sonki so ne na fisabilillahi
- cikin zuciyata ba don wani abu da kike da shi ko kika rasa ba” bata buqatar itama bata
- ransa saboda haka ta saki murmushi tasanya hannunta da kanta ta goge hawayen.
- Sosai fa iza ta soma tsiro da tsurfa kala kala,gobe ace wannan jibi tace wancan,da
- fari sumayya na qoqarim yo mata mukhtar na fuskantar haka yace bai yarda ta sake
- hidimta mata kan komai ba,idan tana so ta tashi ta girka da kanta,nan ma ya fuskanci an
- shiga babin barna da almubazzaranci shima ya soke yace taci duk abinda ka dafa ko ta
- haqura,sosai abun ya qona ranta,duk yadda taso samu yaqi samuwa.
- Sai aka tsiro tsirfar zuwa dubiya kuma,daga bangare mukhtar zuwa na fa izan,saidai
- ko da wasa bata ga qafar yaya yahansu ko yarama ba,saidai fadima da (a zo,ita din ma
- sama sama fa’izan ta mata sannan ta tattarata ta watsar,sai data gaji da zama ta ja
- qafafunta ta tafi,gidan sai ya zama kamar wani gidan biki,wuni sumayya take tana karbar
- habaice habaice daga bakunan maziyartan gidan kala daban daban,bata tabajin tsananin
- so da buqatuwar haihuwa ba irin na wannan karon,sai a zama wata mai raguwar
- zuciya,mikin datajima tana dannewa cikin zuciyarta na rashin magaji ya zame ma a sabo
- fil,duk sanda suka goranta mata sai ta kasa daurewa har sai ta zub da qwalla ta rage
- radadin da takeji cikin zuciyarta.
- Cikin hakan mukhtarya fuskanci ta fara rama,juyin duniya yayi tambaya tace masa
- lafiya babu abinda ke damunta,tilashinsa ya haqura saidai ya zuba ido sosai bisa yadda
- lamuran gidan ke gudana.
- A irin haka katsaham ya dawo gida ranar qarfe uku da minti talatin da takwas ana
- shirye shiryen kiran sallar la’asar,wasu masallatan ma harsun fara kiran,a lokacin tana
- qofar kitchen zaune tana hada girkin dare,yayin da dakin fa iza ke qunshe da baqin da
- qafarsu bata daukewa zuwa gidan da sunan dubiya,suci na rana wani lokaci idan an
- kammala na dare ma suci sannan su tafi,musamman ranar girkin fa’izan wanda taso
- qwarai a dauke mata girki mukhtaryace bata isa ba.
- Yazo kuwa a gaba dai dai sanda sukejeranto gorin nasu,bai kula kowa ba sai da
- suka kammala duk abinda suka 20 da shi suka karkade qafafunsu,kowacce tazo fita sai tayi
- turus ganin mai gidan zaune tsakar gida kusa da sumayyan yana tayata aikin kitchen duk
- da babu wanda yacewa kowa komai cikinsu,sai su kama borin kunya kana su fice sumi
- sumi.
- Sai da suka gama ficewa tsaf sannan yayi kirab fa’izan ya kafa mata sharudai,duk
- randa ya sake ganin qafar wani ya shigo har cikin gidansa ya ciwa matarsa mutunci to
- sawunta a likkafa ta hada kayanta ta bisu tum gabanin ya dawo gidan,wannan hargagi shi
- ya sakejanyo tsana da jin zafln sumayya mai yawa a zukatan mutane da yawa masu qinta
- musamman uwar tafiyar fa’izan,ta kuma sake cin alwashi mai yawa akan sumayya,wannan
- kuma shi ya kawo taqaitar zirga zirgar ‘yan bani na iya din
- RANA DUBU TA BARAWO’
- Tunda ta tashi yau kanta ke ciwo,don haka a daki ta kusa yini,koda yaranta suka zo
- ma gida ta korasu don bata son hayaniya,naana ce kawai ta zauna kasancewar duka ta fisu
- nutsuwa. a
- Har tayi baccin qailula ta farka yarinyar na gefa nta zaune,ta miqe tana salati duk da
- cewarkan nata ya rage ciwo amma bai sauka ba duka,ta cire hijabin data kwanta da shi
- sabida zazzabin da ta fara ji ya flta tsakar gida ta dauro alwala,cikin takaici taje duban
- tsakar gidan yadfa yayi kaca kaca,girkin fa’iza ne amma bata damu ta gyara ba haka
- al’adarta take,matuqar sumayyan bata gyara ba to saidai gidan yayi ta zama haka,to ita din
- ma bata da qyashi son jiki k0 ganin ido batq damuwa wai don bata gyara ba yin abinta
- take,hatta da wankin toilet zata iya rantsewa bata taba ganin fa’l’zantayi ba tunda ta shigo
- gidan.
- Tana shiga d’aki ta sanya naana taje ta share mata tsakar gidan ita kuma ta tayar da
- sallah.
- Kafln ta kammala sallar nanan ta gama kasancewarta yarinya mai kazar kazar da son
- aiki shi yasa sumayyan ke sonta,ta dawo gefanta ta zauna tana kallon sumayyan harta idar.
- Tana shafa addu a ga mamakinta fa’iza ta shigo d’akin dauke da coolerdinta ta dire
- tayi ficewarta,tana nannade abun sallar sai ta lura naana nata kallonta tana kuma satar
- kallon kwanon abincin,tasan akwai magana a bakinta ne ta kasa fadi,kuma hakan yana da
- nasaba da hanasu dauko magana daga wani guri su gaya mata.
- Harta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha’awar cin komai taga yari yar
- naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamarqwalla ce a idonta,a hankali ta miqe ta
- zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna
- “Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kikeji?” Sai ta girgiza kai
- “To mene ne gaya min” cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace
- “Antysumayya don Allah kada kici abincin nan” sai sumayyan ta hade rai tana dubanta
- “Me yasa?”
- “Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta koma
- kitchen ta bude flaskdin ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki tajuya ta rufe ta wanke
- hannunta” sosaitaji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran damar da zasudinga
- labe ko qoqarin dauko gulmar fa’izan suna kawo mata,saboda haka ta sake hade rai
- “Ke me yasa kika labe kina kallonta?” Da saurita girgiza kai
- “Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya daureta
- shine fa na gani” shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata son ta baiwa kanta
- qofar da zata zargi fa’iza kan abinda idanunta basu gane mata ba,saboda k0 ubangiji ya
- fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta kada bayan ta koma ta
- kwanta
- “Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?”
- “To anty” ta fada tana kada kai
- “Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi” ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko alawa guda
- uku yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata fiya son basu kudi
- ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar yaransu,don ba kowa keson ka
- yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba da su,randa kuma basu samu ba
- su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye.
- Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta kauda tunanin
- daga ranta ta shiga addu’a cikin zuciyartaALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI’ITA ta dinga
- maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata maganinsa ya sanya
- tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta.
- Kodaya dawo yau bai samu yin wanka ba saibayanyayi sallar magariba,yasan cewa
- ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa kansa,hakan ne ya sanya yana
- shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya manta da towel dinsa hakan ya sanyashi
- futowa.
- Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa ya sanya shi
- dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji 3 jikinsa tamkar zai sake maimaita
- kansa ne a yau,a hankali ya zarw sllppers dinsa ya taka zuwa qofar kitchen din,idanunsa
- suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa’iza wadda ke dauke da dafa dukan
- shinkafa qarshen qurewar girkin fa’iza kenan.
- Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta fuskanci cewa
- sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci alwashi kota halin
- qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta ko dura ce sai tayi mata.
- Tana karkade hannunta cikin nishadi taji carafan riqe hannunta,tun kafin ta fahimci
- wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar faduwa,a hankali tamkar
- wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu da mukhtanwani matsanancin
- tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari cikin wandonta sakamakon yadda taga
- idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu wuce biyar ba.
- Wani laflyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne hali taje ciki ya
- sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata gigitacciyar qara sabodaji
- taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi yayi silar
zaburarsumayya ta miqe ta
- fito a razanetana tsammanin ko gobara ce ta kama gidan nasutunda ta bar fa’iza ne cikin
- kitchen.
- Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa’iza da mukhtar yayi zuwa filin tsakar gidan
- “Subhanallahi”sumayyata fada da qam tana nufar inda fa’iza take don ta d agata
- “Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni
- da ke,sai nayi matuqar saba miki” taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da
- bata taba zata yana da ita ba.
- Yadda ya sake nufo fa’iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya ta janye gefe
- jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu’a da tazo bakinta tare da neman agajin
- Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a gidan,yayin da tsoron da
- fa’iza taji ya sanyata sakinihun neman agaji domin tsantsar bala’in da zata fuskanta ya flto
- muraran cikin idanun mukhtar tun kafln ya kai ga aiwatar da shi a kanta.