QADDARAR SUMAYYAH
CHAPTER 17
Duban sumayya cikin shaqaqqiyar murya yace
“Jeki ki rufemin qofar gidan” tsayawa tayi tana dubansa jikinta na rawa,ta fuskanci me yake
nufi wato don kada ma ihun fa’iza ya sanya ta samu masu kawo mata dauki kenan
“Jeki ki rufemin qofar gida nace” ya maimaita cikin tsawa ganin bata da niyyar tafiya,jikinta
na rawa ta wuce taje ta rufo,bata kai ga dawowa tsakar gidan ba kuwa taji ana bugun qofar
gidan,daga inda yake ya bata umarnin kada ta bude ta dawo ciki.
Ga mamakinta fa’iza ke bawa mukhtar haquri hannu bibbiyu take roqonsa,bai ko
dubeta ba sai sumayya da ya kalla
“Shiga kitchen ki dauko min cooler dinki wadda take zuba miki abinci” babu musu wannan
karon ta shiga ta fito da ita,.ya nuna maga gaban fa’iza da ido ta dire anan din ta koma gefe
ta tsaya jikinta na rawa.
“Maza bude ki cinye abincin dake ciki yanzu yanzun nan” wani rugugin aradun
tashin hankali ya rufto mata,tirqashi,ai data ci abincin ciki gwara mukhtar din ya kwana ya
wuni yana jibgarta,domin cin abinci koda shinkafa qwaya tak dake ciki ne dai dai yake da
ban kwana da duniyarta,sai ta zube a qasa tana sake roqarsa yayi haquri kuskure tayi kuma
ba zata sake ba,wani murmushi mai tauri da d’aci ya saki
“Ko baki fada ba ai dama har abada ba zaki sake aikata irn wannan mummunan aikin ba
cikin gidan mukhtar,afuwa daya da zan iya yi miki idan kina da buqatarta shine ki dauki
abincin nan ki cinye salun alun”
“Wallahi muntari bazan iya ci ba,zan iya rasa rayuwata,kayi haquri”sai yayi turus ya zuba
mata idanu cike da fargaba da kuma bacin rai
“kice ma niyyar kisan kai kika yi?,sumayyar tawa zaki kashemin?”ya fada cikin wani irin
zafin rai,da sauri ta girgiza kai tare da sake debo wata rantsuwa don gyara baran baramar
da take gab da sake tafkawa,ganin taqaddamar take qarewa har muntarin na nade hannu
zaiyiwa fa’iza dure ya sanya sumayya dake gefe kamar mutum mutumi magantuwa,ta
tabbata tunda har fa’izan ta toge kan bazata ci ba komai zaya yi mata ya nuna akwai wani
mummunan abu da ta qulla cikin abincin,wanda su kansu basu san meye ba,ba kuma su
san sakamakon da hakan zaya haifar ba idan taci din
“Ya mukhtar,ka qyaleta don Allah, koma meye tunda Allah ya kubutar da ni bayan muna da
masaniyar ba wayon mu bane sai mu gide masa ko?”
“Ok,haka ne fa” ya fada yana gyada kai tare da duban sumayyan,saidai kallo daya tayi
masa ta fuskanci bawai yana nufin ya haqura din bane
“Shikenan ki bar cin abincin” ya fada yana juyawa zuwa dakinsa.
Murmushin nasara da farinciki fa’iza ta saki tana duban sumayya duba na wulaqanci
“An gaya miki haihuwa kayan banza ce?,ni na sani ko darajar cikinsa dake jikina kawai ta
isheni,banza mara amfani ke zaki ci gaba da diban kayan takaici juya kawai wad.
Fitowar mukhtar dauke da belt ita ta maqale sauran zazzafar maganar da take da
burin ci gaba da yabawa sumayya,tsayawa yayi gabanta yana gyara belt din tare da fadin
babu batun cin abinci amma wallahi baki ci banza ba,sai na fanshe wahala da baqinciki
rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankalin da kika shigo kika haddasawa
gidanmu,kinga gobe sai ki koyi darasin zaman duniya”kafin su ankara ya fara jibgarta tako
ina,tsoro da firgici ya hana sumayya tabuka komai,abinda iyatsawon rayuwarsu bata taba
gani mukhtar yayi ba,duka duka koda ga qaramin yaro bare ga matarsa ta aure,lallai babu
shakka fa’iza na shirin koyawa mijinsu mummunar aqida idan bata tashi tayi da gaske
ba,don daga haka miji ke farawa idan ba’ayi wasa ba.
Ta nufeshi da hanzari da niyyar dakatar da shi saidai tuni ya hankadata gefe cikim
zafin rai ba tare da ya san yayi ba,a rashin sa’a ta fadi kuwa kan hannunta wanda sai da ya
bada wani sauti ta saki kalmar wash! Cikin azaba,bata sake yunqurin tashi ba ta zubawa
sarautar Allah ido.
Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya dakata yana dubanta
“Ki tatattara duk wani tarkace naki da kika san kin shigo gidan nan da su ki koma inda kika
fito,na sakeki saki biyu” wani ihu ta kurma kamar zautacciya tana shirin miqewa tsaye
“Wallahi baki isa ba muntari,zama daram wallahi sai na haife abinda ka qusa min ma
rainshi sannan” wata dariya ya saki sannan ya miqa hannunsa ya fincikota tare da fusge
zanin jikinta.
Idanu sumayya dake zaune dirshan kan sumunti ta qwalalo ganin abinda ya fado
jikin fa’iza wanda da shi ake canza tafiya ake burga ake kira ciki ne,cikin ma kuma wai na
mukhtar dinta,tarin zannuwa ne aka hadasu aka qulle cikin zani daya fa’izan ke daurawa
“Indai ciki ne gashi nan yau kin haifeshi ko,rainonsa kuma sai ki ajiyemin kayana ko ni zan
raini abu na” ya fada yana qyalqyalewa da dariya,gaba daya wani muzanci ya kama
fa’ iza,me kenan?,meke shirin faruwa?,dama mukhtar yasan ba ciki bane shi yasa ya
qyaleta,shi yasa bai nuna farinciki ba da result din bogi data bashi,bata kammala karanta
wasiqar jakin ba maganar mukhtar din ta kuma katseta
“Kin maida mukhtar wawa shashasha jaki irinki ko?,don kinci sa’a na qyaleki tun lokacin
ban hukunta ki ba kan raina kin wayo da kikayi ba?,to wallahi kada ki yadda na fito a wanka
na taddaki cikin gidan nan, idan ba haka ba kowanne laifi da kika aikata cikin gidan nan iya
tsawon zaman da kikayi cikinsa sai na miki hisabinsa tare da hukunci akansa daya bayan
daya” ya fada yana yarda belt din ya dauki sabulunsa da ya watse gefe ya shige wankansa.
Cikin tsananin radadin ciwukan da taji ta miqe ta shige dakinta,bata yi ko minti biyar
ba ta fito dauke da jaka da hijabi, har ta gota ta dawo da baya ta dubi sumayya
“Wallahi wallahi kada ki dauka kinci nasara a kaina.yanzu aka fara wasan” ta fada tana mai
ficewa da sauri jin motsin mukhtar na niyyar fitowa saga bandakin.
Bin qofar data fice din yayi da kallo domin yaso ya taddata,sai a lokacin ya maida
dubansa ga sumayya
“Me take gaya miki?” Bata amsashi ba sai niyyar miqewa da take amma ta kasa,ganin haka
ya sanyashi qarasa gurinta da sauri yana nufin riqe mata hannu ta saki qara da sauri sabida
gun ciwon ya taba
“Subhanallahi, hannu kuma sumayya?” Ya tambayeta yana duban gun,banza tayi da shi
cikin son yunqurin tashi yayi niyyar taimaka mata da sauri tace
“Barni,bana so” ta tattara qarfinta ta miqe ta nufi dakinta.
Binta yayi a baya da sauri,tana shirin shiga dakin ya cafkota,qara ta saki saboda
hannun ya riqe,sosai ya murde hannun har sai da ya bada qara alamun inda ya gulle ya
koma dai dai, kafin ya kammala ta gama hada gumi,jikinta yayi laushi ya jata cikin jikinsa
yana goge mata hawaye da gumin da ta hada.
Cikin kujera ya aijiyeta yana maida ajiyar zuciya ya fice zuwa dakinsa.
Sai da ya sanya kaya sannan ya dawo d’akin, kamar yadda fuskarsa ke cushe ba
annuri haka itama ya taddata yadda ya barta,dauke fuska tayi taqi kallonsa,sai ya durfafeta
take ta sanya kuka
“Ya salam,sumayya ko hannun ne?” Cikin muryar kuka tace
“Ni ka matsa daga nan ka fita tsoro kake bani ya mukhtar”
“Tsoron me?”ya tambayeta
” duka yaya mukhtar?,me yasa kake so ka koyi duka?,ba girman namiji bane,ba abokiyar
yinka bace mace,matar ma matar aurenka ya mukhtar nima zaka iya duka na kenan?,me
yasa kayi gaggawar sakinta ya mukhtar saki babu dadi fa ba shike gyara mace ba wasu
lokutan,ba masalaha bane”‘dariya da mamaki maganar suka cakudu suka bashi,sai ya dan
murmusa sannan ya sake matsowa kusa da ita ya riqe daya hannun nata
“Sumayya, mukhtar dinki ne ke baki tsoro?,na taba ko ramqwashinki sumayya bare
duka?,bana fatar wannan rana tazo wadda zata kasance na sanya hannu na na doki
sumayyata,sumayya…bazan iya jure abinda zai taba ki ba zuciyata bata da wannan
jatumtar,bazan iya ci gaba da zama da ita ba koda in.a sonta balle ban taba qaunarta ba ko
dai dai da second daya, ke ta taba fa sumayya ke taso rabawa da ni,amma kiyi haquri
kinji,bana son wani abu ya sake shiga rayuwarmu ya jirkita mana farincikinmu kiniji, ina so
mu dawo da rayuwarmu ta baya mu sake shimfidata har ma tafi ta baya idan da hali”
3
Shiru yayi yana jira ko zata ce wani abu saidai shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya ba
tare da tace komai ba,sai ya saki hannunta ya miqe
bari na samo mana abinda zamuci,don ban amince da kayam girkin gidna nan ba sai an
fiddasu an sake wasu ko zuwa gobe ne in sha Allah”har ya fita binsa take da ido ba tare da
tace komai ba.
Gurasa ya siyo musi da balangu sai damammiyar fura mai kwakwa da madarar
hollandia a ciki wadda yasan sumayya na so.
Sai da ya juye komai a faranti sannan ya umarceta ta sauko ta ci,noqewa tayi tana
sharar qwalla,.ya santa sarai saboda haka ya hade rai tamau sannan yace
“Ke banson shirme,sau ko kici abinci na gaya miki,bana buqatar in sake ganin wanin bacin
rai tattare da ke kan wata banza fa’iza” hakan ya sanyata jiki a salube ta sauko din,shi ya
dinga bata da kansa har ta qoshi.
Daren gaba daya ya lalace gun lallashi da tarairayarta gami da kwantar mata da
hankali,tare da kwatanta mata son da yake mata,sosai taji hankalinta ya
kwanta,nutsuwarta na dawowa,cikin kaso dari na damuwarta babu kaso casa’in.
Ko washegari ma bai fita kasuwa ba,yaron shagonsa ya baiwa maqullin shagon shi
kuma yayi zamansa da sumayya.ya tayata suka gyare kitchen din ya fidda duka kayan
abincin ciki ya bayar,da kansa ya fara sauke kayan fa iza dake kitchen din,tsayawa tayi tana
kallon ikon Allah,da ya fuskanci tana niyyar hanashi tuni ya buga mata gargadin babu
ruwanta.
Bata san abun azimun bane sai da ta ganshi da akori kura,ya shigo da masu akori
kurar wadanda nan qasan layinsu gidan mai akori kurar yake,ya bude dakin fa’iza suka
soma tattara kayanta suna durawa cikin motar,sai da suka kammala tsaf sannan ya basu
adreshin gidansu fa’izan yace su kai musu.
Duk yadda taso yi masa qorafi babu fuska haka ta dinga hadiyar maganar da dai
daya har ta haqura ta cinye qorafinta duka,shima hakan ya masa dadi don ta fuskanci yau
wani warkajami yake cikin gidan hankalinsa kwance cikin wani nishadi da ta jima rabon da
ta ganshi cikinsa, hatta yaranta yau ba wanda ya bari ya shigo su kadai sukai zamansu.
Yana maqale da ita wajen biyar da rabi na yamma bayan ya gama musu girki sunyi
wanka acewarsa ciwon hannu take babu abinda zata yi suka dinga jiyo wani mahaukacin
bugu.
Da fari tsaki yayi ya gyara kwanciyarsa tare da sake rungume sumayyan dake jikinsa
yana bata labari,sai yaji bugun naci gaba da qarfi amma sam baida niyyar tashi,dubansa
tayi a narke gabanta na bugun uku uku haka nan tace
“Ya mukhtar,bugun fa sake qarfi yake ka duba don Allah”
“Qyalesu my sumy ko waye idan ya gaji ya tafi yau angonci nake” dariya ya bata har sai
data dara saboda yadda yake maganar yana wami sake maqale mata tare da kashe ido
“Tsohon ango ko?”
“Koma dai meye” ya bata amsa.
Bugun ya wuce hankali saboda haka ta matsa masa har sai da yaje ya bude.
Muryar wadda ta jiyo tana shigowa gidan ya sanya labbanta na rawa ta furta
“Innalillahi wa inna ialaihi raji’un,Allahumma ajirni fi musibaty,wa akhlufni khairan minha”
ta yayimo hijabinta ta sanya tana zaman jiran tsammani tare da kasa kunnen dramer dake
faruwa a tsakar gidan.
Wani banzan kallo yaya yahanasu ta jefawa mukhtar bayan ya bude mata qofar,qare
masa kallo tayi yana sanye da vest da boxer
“Qwarai,oh ni yaha jikar asabe da larai,wannan yarinya anyi(ta qundumo ashar),wato
abinda ka raina wataran sai ya baka mamaki, duk inda muje zatonki kin wuce nan
kenan,lallai ne malam ya iya aiki,wato bayan sakin wulaqancin da ka yiwa yarinya kayi
mata tsinannan duka da ya sanya cikin jikinta ficewa babu shiri shine kuma waccar
qaramar karuwar ta qwamusheka a gida,kasuwar ma wato baka zuwa bare kazo guna,duk
abinda zanyi wato saidai nayi ko?” Ba mukhtar ba hatta da sumayya mamaki sai da ya
kashesu.yanzu dama fa’iza na iya tunkarar yaya har ta gaya mata abinda ya wakana?,har
tana da bakin cewa mukhtar ne ya zubda mata ciki,mukhtar ji yayi inama fa izan na gefan
yaya yahanasun a yanzu da babu abinda zai hanashi kwashe mata haqwaran gaba yaga ta
yadda ma zata sake auruwa ta dadin rai,shi zata yima wannan qazafin?.
Kafin ya kai ga cewa komai ta nufi dakin sumayya tana fadin
“Shigo shegiya tsinanniya,wallahi yau dukan da aka yiwa fa’iza a kanki zan qareshi” cikin
wani irin hanzari da zafin nama ya sha gabanta.ya tattokare bakin qofar yana kada kai
“Bata ci nanin ba yaaya nanin kuwa ba zata cita ba,silar fa izan tana can ta samh gocewar
qashi tana jinya” haba yayan ta riqe sai kuma ta saki kuka tana tsinewa sumayya da debo
mata jafa’i kala kala
“Irin jaraba irin bala’i mukuwa mun kwasowa kanmu,ba’a taba qaruwa da ke ba sai masifa
da kika janyo mana,zuriar da muje son samu kinyi sanadiyyar da aka zubdata kika kori
kuma mai kawo mana sanyin idaniyarmu”.
Daga cikin dakin kuka sumayya takeyi sosaijin yadda ake ambato iyayenta da basuji
ba basu gani ba ana tsine musu tare da jifanta da miyagun kalmomin da bata taba jinsu ba
tunda tazo duniyar.
Tuni ran mukhtar yayi masifar baci,idanunsa suka sauya launi
“wai yaya kin mance wace fa iza?,kin manta dibar albarkar data ke muku,ina cewa ke da
kanki sau nawa kina neman na saketa?”
“Ta riga da ta yimin bayani,ba cikin hayyacinta take ba,duk cikin makircin waccar
la’ananniyar Allahn ce,kuma koni na zargi haka a lokacin, saboda ba haka fa’iza take
ba,saboda haka ina umartarka ka dawo da fa’iza yanzu yanzu ko rayuka suyi mummunan
baci”.
“wai yaya meye laifin sumayya ne?,me tayi muku ne?,laifinta kawai dan bata haifa
muku abinda sam bata da ikon bawa kanta ba?,kuna tunanin cewa da ana saida haihuwa
sumayya ko ni zamu lamunci mu zauna har zuwa wannan lokacin bamu saida komai namu
mun siya ba?,to wai shin ma idan ta haihun ba kanta ta haifawa ba,waye zai fita jin dadi
idan ta samun?,meye naku ne wai a ciki?,jiyaka kice matar qaninki ta haihu ko?,ita kuwa
cewa zata yi NA HAIHU NA SAMU D’AN KAINA,to idan ma nace banason haihuwar baki daya
me ya shafeku a ciki?..kiyi haquri yaya amma fa’iza ta bar gidan nan,ta bar gidan nan
har abada…taje na saketa saki uku na cika mata dayan'”sai yayi shiru yana kaida
numfashi,ita kanta irin hakan bata taba shiga tsakaninsu ba bai taba gaya mata magana
har irin haka ba,sai taga ma kamar bai cikin hayyacinsa,tabbas fa’iza ta saku amma ba zata
taba qyale sumayya taci riba ba,sai yayi shigewarsa dakin sumayyan ya turo qofar ganin
haka ya sanyata ta fice tana sharar ido,gani take ba haka sumayya ta bar dan uwanta
ba,bata taba ji iya shekarun zamansu sunyi fada ko ya kawo qarar sumayya ba,har kullum
cikin yabonta da kyautata mata yake,to ta yaya za’ayi hakan ta faru idan ba asirceshi sukayi
ita da malamin ubanta ba?((aqidar mu ta hausawa kenan, matuqar ba’a zuwa rabaku fada
ko ba’a jin kanku tofa fassarar itace kin asirceshi sai yadda kika ce ko kuma shi ya shanyeki
tsoronsa kike,kyautatawa babu yadda bata maida zamantakewar ma’aurata,kyakkyawar
zamantakewa mai cike da ababen ban sha’awa,kowa na tsoron batawa abokin
rayuwarsa, kowa burinsa kyautatawa da farantawa abokin rayuwarsa,Allah kasa mu dace).
Sam ya kasa rarrashin sumayyan duk da yadda take kuka,kwanciya yayi saman
doguwar kujera yana dafe da kansa idanunsa a lumshe,abu daya ya iya furtawa
“Hasbunallahu wa ni’imal wakik,wannan wacce iriyar QADDARA CE?”.
Tilas sumayyan ta lallashi kanta,don ta fuskanci a yau din mukhtar ya fita shiga bacin
rai,kada zafin ya masa yawa hakan yasa ta shanye duk wani bacin ranta ta maida komai ba
komai ba ta shiga hidimar kwantar masa da hankali da dukkan wani aiki da kalamai da
zasu samar masa da nutsuwar,babu laifi ta dan cimma nasara,amma duk da hakan kwana
yayi cikin ciwon kai,saidai cikin ikon Allah zuwa washegari ya warke sumul.
Duk da haka bai fita din ba amarcinsu suka ci gaba da ci,wanda hakan ya sake dasa
wata sabuwar shaquwa tsakaninsu da qauna mai tasiri a gangar jiki da zuciya,sai sumayya
ta jita cikin wata sabuwar duniya,cikin wata duniyar data jima rabon da tajita,sai yanzu ta
fara sanin ciwon kanta,sai yanzu hankali ya soma shigarta,sai yanzu ta fara gane zaqi da
madaci.yanzu tasan me kalmar kishi da kishiya ke nufi,tabbas babu shakka sai a yanzu
tasan tana kishin mukhtar dinta tana kuma qaunarsa musamman a yanzu data dandana ya
bambancin zaman yake,wani sabon kishin mukhtar din ta koya har dariya yake mata wani
lokaci ya tsokaneta,a yanzu ta sake sanin cewa a kwai qaunar haihuwa sosai a tattare da
ita,tana jin ita kadai ta rage mata,hakan ya sanya ta miqe da addu’a sosai saboda ganin irin
qalubalen da ta fuskanta abaya wanda bata da buqata ko fatan sake fuskantarsa a
rayuwarta ta gaba.
Cikin lokaci qanqani rayuwarsu ta koma kamar yadda take,komai ya wuce tamkar bai
faru ba,farinciki da walwala ya wanzu a tsakaninsu,sannu sannu budi ya dinga zuwa ma
mukhtar din wanda hakan ya sanya shi wadata sumayyan tasan da dukkan wani kayan
more rayuwa wanda hakan ya sake tsayawa cikin zuciyar yaya yahanasu da
muqarrabanta,duk da cewa tayi dif cikin rayuwarsu tamkar bata ciki,tunda ta fice daga
gidan ranar da aka cikawa fa’iza sakinta bata sake tako koda qofar gidan ba,duk da yadda
sumayyan ke zage damtse wajen kyautata musu da shiga dukkan harkokinsu wanda a
qarshen natijar bacin rai ne,amma tsananin kara da alkunya yasa take maida komai ba
komai ba take ci gaba da yin duk abinda ya dace.
A wani yammaci bayan ta kammala duk ayyukanta na al’ada,ta dandasawa mukhtar
din kwalliya cikin wata atamfa brown mai adon mint grean dinkin riga da skert ya mata
cifwaccan satin ya dauketa bayab sallar magariba suka shiga mudassir and brothers store
ya siya mata kala biyu hadi sarqa da mayafi,sosai ta haska farar fatarta tayi kyau matuqa.
Yana shigowa ya sureta yadda ya saba ya daga sama yana juyi da ita tana qyalqyala
dariya kafin daga bisani ya direta yana kallonta gami da sauke haki.ya riqe qugu yana
dubanta
“My sumy gaskiya kin fara qiba,gaba kadan zan fara kasa iya dagaki” baki ta murguda cikin
salo na shagwaba
“Daga ranar kuwa zan sanya maka ragon maza”,cafka ya kai mata tayi nasarar zillewa,don
tasan kwanan zancan idan ya kamota.
Muqulli taga ya zaro cikin aljihunsa ya daga mata yana kadashi,sai ta juya idonta
alamun tambaya,da ido ya mata nuni kan ta shiga ciki da dauko hijabinta,babu musu ta
shiga ta sanya ta fito.yayi gaba ta bishi a baya taba saqe saqe.
Motace sabuwa dal fake a qofar gidansu honda civic mai qofa biyu,saidai ba qaramin
kyau tayi ba fara tas da ita colour din da sumayyan ke so,tana daga soron ya daka tsalle ta
daneshi tana fadin
‘da gaske ya mukhtar mota ka siya?”
“Wayyo my summy ‘yar lukuta,sauka na gaya miki” maqe kafada tayi alamaf taqi haka ya
shiga da ita har falonta ya direta saman kujeru tana ta faman murna
“Wayyo yaya mukhtar,wallahi tayi kyau,kace muma munyi mota,Allah ya sanya alkhairi
yaya ya hadaka da dukkan alkhairinta ya rabaka da dukkan sharrinta,Allah yasa ta zame
maka alkhairi da mu baki daya” sosai yaji dadin addu’arta, lumshe idanu yayi yana fadin
“Amin my sumy,Allah yayi miki albarka” ya fada yana dubanta, sosai yake sake
qaunarta,tana burgeshi har yau,duk abinda ya faru cikin gidansa zamanin zamansu da
fa’iza ba’a taba ji ba a gidansu balle ta dauki qafa kai qara.
Hure masa idanu tayi taba tambayarsa me yak tunani,murmushi ya saki
“Ke nake tunani my sumy,ina godewa Allah da ya bani ke,fata na kuma mutuwa ce kadai
zata rabamu,itama da da hali idan tazo ta daukemu tare a hadamu kabari daya” sai ta hade
rai tana turo baki
“Me ya kawo zancanta kuma yaya mukhtar”
“Na daina kada ayi fushi dani yau a hanani rawar gaban hantsi” ta fahimci me yake nufi sai
ta saki murmushi cike da kunya.
“Kishirya idan aka fito sallar magariba zamuje na d’anaki,daga nan sai muje gidan
mama(mamarta)da gidan yaayaa mu nuna musu su sanya albarka ko?” Duk da cewa taji
dadi saidai sam bata son zuwa gidan yaya yahanasu don bata taba shiga ta fito ba tare da
guzirin bacin rai ba,sai ta dake ta amsa kawai tare da nuna farincikinta,sosai yaje nazar
amma bai taba gani ta bata ranta don yace zasuje gidan ba,duk da yana lura da yadda taje
samun musgunawa ta wajen kallo ko magana daga garesu,sosai yake yaba karamci da
haquri irin nata,shin meye aibunta ne da baza su sota ba?,meye laifinta?,me sumayya ta
rasa ne?,
Aibunta da laifinta don kawai har zuwa yanzu bata haihu ba,wanda babu wani bawa
da yake da qwanjin kokawa da QADDARARSA dole sai ta cimmasa gwargwadon tsawon
lokacin da buwayi gagara misali yaso,shin wai wa ya isa ya sanya ubangiji ko ya hanashi?,a
duniya akwai wani bawa da yake rayuwa dukkanin burikansa sun cika?,A’a,idan kuwa haka
ne to ba shakka bawa baya yiwa kansa abu face da hukunci da yardar mai duka,babban
misali matayen annabi,har suka koma ga mahaliccinsu babu wadda ta haihu cikinsu face
guda daya,rashin haihuwa ba aibu bane kenan face wata jarrabawa da idan ka daureta
zaka samu lada da rabo mai dimbin yawa,idan da aibu ce ubangiji ba zaya jarrabci matan
halitta mafi soyuwa gareshi ba,halittar da yayi duniya da lahira saboda shi wato annabi
muhammadu SA W,da wannan tunani ya daura alwalarsa ha fice ita kuma ta tanada masa
ruwan wankan da zayayi idan ya dawo kafin su fice.
Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea grean,sosai tayi masa
kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima.ya kulle gidan suka fito.
Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga daya
bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa addh’a,sosai yaji
dadi cikin zuciyarsa shima,.yayi bismillah ya tada motar suka fice daga layin a hankali.
Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar gidansu
sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana murmushi,tamkar yau
ne ta fara zuwa gidan sai murna take.
A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai dake kunne a
gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai
“A’ah,sumayya da kece haka da daren nan?” Mama ta fada tana sake bude tabarmar da
take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa
“Wallahi mama nice,ke kadai ce?”
“Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa”
“Malam fa?”
“Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya”
“Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe…bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya shigo
ku gaisa”
“Au tare ashe kuke…maza shigo da shi” inji mama tana janyo hijabinta dake gefanta ta
Zura.
Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su sa mata
albarka,tayi kuwa addu’a sosai don babu damar ta leqa malam din baya nan,nan ya fice
qofar gida ya barsu.
Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu gidan yahanasu.ta
miqe suka yi sallama da maman ta fito.
Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar suna
ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta qarasa
cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida ya
abbakar.ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar ke dura
mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda kunyar malam
da takeyi.
“Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku” cewar malam yana shigewa gidan bayan sunyi
sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan kwalliya,qin
karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna godiya suka shige
gidan.
Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
“Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu
shakka sai na aura masa halima ko zainab” murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan
koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri’a da
yan gidansu.
Mintina qalilan suka isa gidanya kashe motar ya fice ta bishi a baya bakinta cike da
addu’a.
Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan busawa a
yan kwanakin.ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama da ita ta
kowanne bangare na qasar nan.
Da fara’ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse ‘yar fara’ ar
data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtaryayin da sayyada taqi
motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya mukhtar din
dubanta fuska a hade
“Ke,tashi ki bata guri” tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa sarai,daki
suka shige ita da jamilan baki daya.
A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta amsa
mata suka shiga hira da mukhtar din.
Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta aijiye gaban mukhtar
din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa
“Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu” zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta dinga
jifansu da harara tana qwafe da su.ya maida dubansa gun yaya yahanasun
“Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe” sai ta harareshi
“Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya”
“Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida kuma
nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki”
“Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana
wannan masifar” ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi nisa
sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna hayaniyar
murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya taimaketa sayyada ta leqo
tace ta fito su tafi.
Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya hana
musu tafiya
“To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu yi
maka addu’a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin” bai amsa ba ya ciro dubu
uku ya miqa mata yana fadin
ga wannan ku qara”hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu yaja
motar suka wuce.
Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa da ita
gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan gidan,da
tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu yoghourt manyan
roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta mata,a hankali ya
dinga janta da hira da labarukan ban dariya, sosai ta sake sake masa jiki tana qyaqyata
dariya wanda hakan shima ya masa dadi.
TSUGUNNE BATA QARE BA
Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata shi,sanye suke da
kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana zaune kan qaramar
kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki.yayin da ita ke kwance saman
doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din ashqui,kusan bata taba
zama ta kalli film din complete ba sai yau.
Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda
yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa.ya dubi wayar sai
yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma sunyi da
wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai yayi zaton shine
saboda haka ya daga
“Assalamu alaikum” mukhtar din ya fada,kana yayi,jim kusan daqiqa talatin sannan ya
sake cewa
8:40 AM
“Wacce zainab?,daga ina?” Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya kife wayar
yaci gaba da binda yakeyi.
Ba’a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba tare da yayi
niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba da abinda yakeyi
din ransa na quna.
Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja
hankalinta,tana
daga kwancen ta dubeshi
“Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni” ta fada a shagwabe,bai dubeta ba
yace
“Bazan daga ba,barta kawai” sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.
Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta sake
tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar barcinta da ya
salube tare da fadin
“Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta”
“Kema ba zaki daga ba” ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya ta
saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta sanya
hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon taci nasara
ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.
A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar macace tana
gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye.