QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 21

QADDARAR SUMAYYA









CHAPTER 21








Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance
cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin
yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa
zancan cikin na nan a falonsa.
Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya
cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya

saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake

buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya
karba ya fice.
Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai
qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan
bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai
hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun
shikewa kansa komai, hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke
zuwa ya masa share share.
Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi
izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan
baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.
Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya
amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato
sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya
wuce gaisuwar, hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da
kayan ya musu sallama ya fice.
Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron, yana da muradin ganin cikinsa
gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta, hakan babu wanda
ya masa zancanta, jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a
qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga
zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo
klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
“Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa”
ya fada yana gyara tsaiwarsa, mamaki ya cikata,kamar tace wani abun
kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.
A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan
rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d’anta
ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN
QADARARTA, hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
“Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau
nake”
“Na san da wannan ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da
lafiyar abinda ke cikinki ko” maman ta fadi
“Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi” tausayinta ya
kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda
mukhtar din ya buqata
“Kin gani ai,sai kije ku gaisa” ta fada ta juya tana ficewa, hajibinta ta
janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.
Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon
cikin ya fito fiye da waccan karon, hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta
ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda
ta tsaya sannan tace
“Ina yini” ba tare data daga kai ta dubeshi ba
“Lafiya lau,ya jikin naki”
“Alhamdulillah” ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da
abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri harya lura
da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare
qofa da shi ya furta
“Ga guri zauna” bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
“Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini
yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen
faruwarsa ba”ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na
sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take
wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake
kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana
zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.
Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda
bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar
wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace
“idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya
kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan
dawo na karba in sha Allah”
“Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya” ta fada tana mai shigewa
gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na
zafi.
Babu kowa cikin tsakar gidan nasu kai tsaye ta fada dakin tana jan
numfashinta tana jin zuciyarta na mata nauyi,qwalle ke layi kan
kuncinta daya na bin daya,a addafe ta nemi gefan katifa ta zauna tana
jujjuya kanta cikin zuciyarta tana addu’a wadda bata tantance mai take
roqa ba,abu daya zuwa biyu zata iya tantancewa shine haushi da tsanar
mukhtar dake mata yawo cikin zuciya,sai kuma zainab wadda take jin
ba zata iya yafewa karan tsayen da ta yiwa rayuwarsu ba musamman ita
din,wanda gangar jikinta da zuciyarta bata saba da kowa ba sai
mukhtar din tun zamanin quruciya zuwa girma.
Ta dauki a dalla mintuna talatin a haka kafin sautin qarar wayarta
dake yashe gefe ta katse mata yanayin da take ciki,sunan anty dije ke
yawo bisa screen din,tamkar an kwance qullin dake zuciyarta taji
zuciyar ta karye hawaye ya sake balle mata tun kafin ta kai ga daga
wayar.
Muryarta kawai anty dije taji jikinta ya bata akwai damuwa,fada ta
shiga yi tun kafin taji matsalarta akan kan mene ne zala dinga bata
ranta,ta gaya mata me aka mata waye ya bata mata,ganin ta gaza bata
amsa yasa ta katse kiran ta nemi layin maman,tana daga daki ta juyo
muryar maman da alamu anty dijen ta sameta,jikinta ta komar ta
jinginar a bango ta lumshe idanunta tana matse hawaye.
Batasan ya sukayi da mama ba daga bisani ta kirata ta gaya mata
idan har taga ba zata iya ba tayi tahowarta abuja gurinta ta zauna ta
haihu a nan,godiya ta mata tare da ce mata to ba don tana jin tafiya can
din ba,maida kanta tayi ta kwanta sosai saman katifar tana maida ajiyar
zuciya
***
La’asar ce sosai misalin qarfe biyar na yammacin,tana zaune saman
kujera ‘yar tsuguno tana tsinke danyan zogale, halima na bakin kurfeti
wanda take kwashe tuwon dare,mama na saman tabarma daga gefen
sumayya tana daka gyada da daddawa,sai zainab wadda ke wankin
kayan sumayyan wanda basu wuce kala hudu ba, hira suke irin wadda
ta shafesu,sosai hirar kewa sumayya dadi don har qyaqyata dariya take.
Sallamar yaro ce ta katse musu hirar wanda ya sanar musu mukhtar
na gaidasu,mama ce ta fadawa yaron yace ya shigo wanda hakan ya
sanya sumayya sakin zogalen hannunta ta dafa qasa tare da yunqurawa
ta miqe,bat faralar dake fuskarta ta bace,a hankali ta juya ta shige dakin
yayin da maman ta bita da kallo lokacin da take qoqarin zura hijab a
jikinta.
Yara ne suka fara shigo da kaya,akwatu ne har seti uku matsakaita
masu kalar ruwan hoda da ruwan toka(ash and pink)masu azabar
kyau,sai da suka ajjiyewa suka fice sannan mukhtar din ya shigo.
Sanye yake da shadda ruwan madara(milk)dinkin tazarce wadda
tayi masifar masa kyau,sosai ta dace da shi duk da irin ramar da
yayi,kamar ko yaushe ya gaisa da maman cikin kunya da nutsuwa kafin
shiru ya biyo baya na ‘yan daqiqu sannan yace
“Kaya ne mama gasu nan,idan akwai abinda babu ciki sai a sanarmin
don Allah mama” addu’ar fatan alkhairi tayi sannan daga bisani ya
miqe bayan ya ajjiye wasu kudi gaban maman ya fice yana kiran halima.
Kusan duk cikin kunnenta komai ya faru,idanunta na a rufe har ya
fice daga gidan,wani gudu gudu zuciyarta ke mata tare da wani zafi,duk
sanda ta tunashi kota jishi ko ta ganshi wani miki ke motsawa cikin
zuciyarta, har yanzu cikin jin haushinsa da zarginsa babu abinda ya ragu
cikin zuciyarta,a ko yaushe zuciyarta na gaya mata tunda mukhtar ya
zargeta aduniya waye zai gasgata ta?,waye zai yarda da gaskiyarta,a
haka ta zame ta kwanta ko zata samu sauqin zugin da zuciyarta ke
mata.
Bayan sallar isha’i mama ta nunawa mallam akwatunan,bai buda ba
yayi addu’a dai kawai,cikin sauri halima da zainab da suka qagu suga
meye a ciki suka matso gaban akwatim suka soma budewa,sumayya na
daga saman kujera Wadda tunda ta yiwa malam sannu da zuwa bata
sake cewa komai ba,sanye take da hijabi hannunta riqe da qaramin
alqur’ani tana karantawa qasa qasa,sam idanunta bai kansu karatunta
kawai take kamar batasan meke faruwa ba.
Ba qaramin tafiya da su halima kayan sukayi ba,kallo daya zaka
musu ka tabbatar mukhtar yayi rawar gani,kaya ne masu dan uban
kyau da tsada unisex,takalma huluna,riguna fidoji,tarkace dai kala kala
wami abun ma basu san sunanshi ba,akwati biyun duka na jarirai
ne,yayin da ta qarshen atamfofi ne super biyu,lace daya shadda
daya,sai materials masu kyau guda biyu jaka takalmi da mayafi sai
sarqa da awarwaro,kana kallonsu kasan na uwar yaro ne na fitar suna
“Masha Allah,wannan yaro ko yarinya anyi dan gata,don Allah anty
sumayya dago ki gani” zainab ta kasa shiru ta fadi haka. A hankali ta
daga idanunta ta watsawq zainab din wanda ya sata dawowa
hayyacinta,sai tayi shiru ta sadda kai yayin da sumayyan taci gaba da
karatunta ba tare data sake tofawa ko dubansu ba.
Qememe taqi yarda a ajjiye kayan a dakinta kusa da ita,tun yaya
abubakar na tsokanarta suna dauka wasa ne har suka gane bil haqqi da
gaske take,don kuka ta fashe musu da shi,tilas ya abubakar ya karbi
kayan ya musu ma’ajiya a dakinsa.
****
****
****
****
Tunda ta idar da sallar isha’i ta kwanta bayan taci tuwon dare,wani
mugun ci tayi masa har halima na mata dariya tana tsokanarta duk da
yadda take jinta a takure saboda yadda baya da mararta ke ciwo kadan
kadan. Bacci taso ya dauketa saidai yaqi zuwa juyi take lokaci bayan
lokaci saboda yadda kwanciyar taqi mata dadi duk da cewa idan da
sabo ta saba tunda cikinta ya fara nauyi, a haka har su halima suka
gama bidirinsu suka shigo suka kwanta bacci ya kwasheta idanunta
biyu.
Sannu a hankali taji ciwon yana ci gaba da qaruwar mata daga
mararta zuwa baya,sai ta miqe a hankali jin motsin mama da tayi a
tsakar gida tana rufe kitchen da alama bata kwanta ba,tana qoqarin
shiga daki sumayyan ta kira sunanta,waiwayowa tayi cikin mamaki ta
amsa don a tunaninta ta jima da yin bacci tunda ta riga kowa kwanciya.
“Mama marata da baya ne kemin wani irin ciwo,gashi na kasa bacci”
idanu ra zuba mata tana nazarinta sannan tace
“Tun yaushe ne?”
“Tun dazu” ta fada tana cije lebe saboda yadda aka mintsineta, kai ta
gyada sannan ta juya ta bude dakinta maimakom dakin malam da take
niyyar shiga tace da ita
“Shiga ki kwanta anan ina zuwa” ta fadi tana sake juyawa zuwa dakin
malam din.
Koda maman ta dawo bakin gado ta sameta zaune saboda
kwanciyar ta gagareta, ji take kamar ana tsaga mararta ana karya gadon
bayanta,tuni gumi ya fara yi mata sallama,yarfa hannu take tana kiran
sunnayan Allah tare da mirgina kai hagu da dama,kofin hannunta
maman ta miqa mata cike da tausayi tace ta shanye, kallo daya tayi
mata ta tabbatar naquda take,daga kai tayi ta shanye baki daya sannan
ta dire kofin a wahalce,cikin mintina qananu ciwon ya sake yin gaba.
Awa daya ta wuce shiru biyu shiru hakan ya sanya mama ta sake
komawa gun malam ta kuma karbo mata wani rubutun ta sake
shanyewa,tun tana daurewa har hawaye suka qwace mata ba tare data
shirya baba shakka zamantowa uwa ba qaramin abu bane haka ta
dinga rayawa cikin zuciyarta.
Qarfe biyar saura na asubahin ranar talatar ya zamanto mata ranar
tarihi a gurinta,dai dai lokacin da yaron cikinta ya shaqi iskar
duniya, kukansa ya karade ilahirin gidan wanda ya sanyawa ilahirin
wanda ke gidan yana bacci farkawa, malam kuma dake zaune
dungurguryayi hamdala ga ubangiji yana qarawa.
Ware idanunta tayi sosai sanda iskar sanyin asuba ke busata,tana
son tabbatarwa kanta da gaske ne abinda ke cikinta ne ya iso duniya
yake cala kuka haka?,da gaske ne a yau itama ta zama uwa?,ta shiga
sahun iyaye?,da gaske yau itama zata riqe ta kalla ta kuma raini danta
na cikinta?,ta fita daga sahun juya?,wannan kalma ta zama tarihi cikin
rayuwarta?,a yau ta haifawa mukhtar da wanda yake buri gareta buri
gareshi,sai dai kash,ba zaya samu irin tanadin da suka yiwa rainon da
zasu bashi ba,wata qaqqarfar QADDARA ta shigo ta farraqa
kasancewarsu tare,a yau zasu raineshi ne a mabanbantan gurare,sai ta
saki kuka a fili wanda cikin zuciyarta tana tasbihi ne ga ubangiji,cikin
mamaki mama ke dubanta
“Lafiya ko wani guri ke miki ciwo kuma?” Ta tambaya sanda take tsaka
da qoqarin dauke yaron da gyara gurin,kai ta girgiza tana ci gaba da
kuka,tuni maman ta gano kukan me take saboda haka taci gaba da
aikinta tana cewa
“Godiya ya kamata ki yiwa ubangiji ai”.
Kafin gari ya waye tuni komai yayi tsaf daga uwar har dan har gurin
da akayi naqudar,maman ce ta shigo da yaron dake nannade cikin
shawul ruwan sararin samaniya bayan sunqufe shi da akayi cikin
lallausan kayan sanyi suma ruwan bula din,malam ta kaiwa shi bayan
ya dawo sallar asubahi ya ganshi,ya sha addu’a kuwa bayan wasu
sirrika da ya hada ya dangwala masa a baki,sumayyan na gefan gadon
mamam riqe da kofin shayi mai kauri da maman ta hada mata kan ta
fita da yaron, har yanzu ta gaza shanyeshi saboda bacci dake dibarta
“karbeshi ki ganshi sumayya ki masa addu’a”maman ta fada tana dora
mata shi saman cinyarta bayan ta karbo kofin shayin data samu ta
shanye.
A hankali kamar mai tsoron tabashi ta sanya hannu ta tallabeshi,take
idanunta suka cika taf da qwalla,a sanyaye ta sanya hannu ta yaye rufin
fuskarsa idanunta suka sauka kan fuskar tasa wadda idanunsa ke rufe
ruf yana ta sheqar bacci cikin lumana da kwanciyar hankali,kallo daya
tayi masa ta hango kamanni na kai tsaye da yaje da babansa duk da ba
idanunsa biyu ba,a kallon farko taji wata iriyar qauna da soyayyar yaron
ta mamayeta,irin qauna ta da da mahaifi,tausayinta kuma ya samu
gurbi cikin zuciyarta karon farko data tuna irin siradin da rayuwarsa ta
tsallake kafin ya kai ga isowa zuwa ga wannan fili da muke kira da
duniya,sai gashi Allah ya nuna ikonsa,yaro qato kyakkyawa mai cike da
qoshin lafiya,wanda ko cikin mafarkinta bata taba tunanin zata haifi
kamarsa ba
“Bawan Allah” ta furta ba tare da tasan a fili ta ambaci hakan ba qwalla
na kwaranyo mata,daga shi tayi zuwa fuskarta ta karkata kunnensa na
dama ta karanta masa kiran sallah ta karkata na hagu ta karanta masa
iqama sannan ta ambata masa sunansa *ABDALLAH* bawan Allah.
Murmushi mama tayi ta dubeta
“Amma kya jira babansa yazo ya zaba masa suna ko?” Kai ta girgiza
“Kiyi haquri mama,ni yafi kamata mama na sa masa suna, ni kadai
nasan wahalar da nasha,daga ni sai ubangiji na ma…….” Sai ta kasa
qarasawa saboda karyewa da zuciyarta tayi
“Kukan ya isa haka,yau ranar murna ce,ajjiyeshi kusa da ke,maza so
nake ki kwanta kiyi bacci sosai” bata musa ba din tayi yadda maman
tace,tun tunaninnika na bijiro mata har wani nannauyan bacci mai dadi
yayi gaba da ita.
A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar
asubahi cikin gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar
bai tashi ba kamar yadda bai aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne
fal zuciyarsa yau ya wayi gari da shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai
iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da lafiyar abinda ke cikinta
ba, kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje kwana yake tashi.
Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya
jawota ya duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a
kunnensa,runtse idanunsa yayi zuciyarsa ta soma quna saboda muryar
wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu tsana mai tsanani ba irin na
mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale murya da
wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda
take kira da malam ya bata wannan sa’ar ya kuma tabbatar mata bayan
sallar asubahi ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta
cika da farincikin samun nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar
asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin tana ta magana ya mata shiru ya
sanya ta fashewa da wani makirin kuka
“Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina
ni a ciki?,duk iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya
kubuta,duk tarin hidima dana dinga yi da ita rana daya duk ka mance
ka watsar da alkhairi na a gareku ka sakeni,kuma ma tunda an samu
cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka maidani daki na ko?”.
Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata, cikin harzuqa ya dakatar
da ita
” ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya
haramta ne sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya
halatta bazan iya zama da kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da
na raina da kaina ta iya min haka babu wata diya mace da ba zata iya
aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda haka
gargadina dake na qarshe, kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar
hanyar da kika san zan biidan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba”daga
haka ya katse kiran ya ajjiye wayar a fusace.
Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan
ta dubi qawar tata
“Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha
wajen malam ta tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake
gaya min?,to wallahi wannan karon babban aikin zan saka a masa koda
duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin daurawa” kafada ta daga
tana fadin
“Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki
saki naira kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba
sai ke” miqewa tayi ta fice daga dakin fuuu tana fadin
“Ai anzo gurin kuma”.
A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a
karo na biyu yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi
gabansa ya fara faduwa ganin sunan abubakar kan screen din,cikin
sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe idanuwa yayi wata rahama na
sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa albishir mafi
dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa
masa yaro, baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar
madaukakin farinciki shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya
katse.
Faduwa yayi saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai
tasbihi ga ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya
shiga wanka, cikin mintina talatin ya fito, kai tsaye gaban sif dinsa ya isa
bayan ya tsane jikinsa,ya bude yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke
hannayensa yana duban kayan kala bakwai da suke sababbi
dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya
na da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya
dinkasu saboda ya sanyasu tun daga rana ta farko da aka haifa masa
yaronsa har ranar suna, baya iya manta lokacin da take dariya tana
tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya zauna yana
yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne
farincikin da yake ciki, baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina
jin ciwon abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar
tsallakewar cikin gashi har yau Allah ya nufa ya iso duniya.
Da qyar ya samu ya hadiye wani dunqulen abu mai daci sannan ya
miqe ya shirya cikin wani yadi mai kyau na maza fari sol wanda ya masa
kyau sosai,ko abinda zai sawa cikinsa bai nema ba ya fito don dama ba
ko yaushe yake samun damar karyawar safe ba,yana shirin tada
motarsa ya kira ya yahansu ya shaida mata,hamdala ta dinga yi matiqa
da gaske tana jin dadi a zuciyarta,ta kuma shaida masa lalle ya biyo
gidan nata kafin ya wuce.
Kafin sha daya na safe tuni gidan ya cika da jama’a ‘yan uwa da
abokan arzuqi,kowa barka yake mata tare da tayata farincikin wannan
rana da akajima ana saka ran zuwanta,sam ita bata san me ake ba
ma,bacci take sosai ita daya a dakinsu,yaron shima nashi baccin
yake,sai da ya farka ya fara kuka alamar yunwa sannan mama ta baro
dakinta wanda suke zaune da mutane ta shigo dakin ta tasheta,sai data
sake hada mata shayi mai kauri ta sake sha sannan ta dora mata shi
saman cinyarta ta fara koya mata yadda zata shayar da shi,runtse tayi
sannan ta fara qorafin zafi maman tace
“A haka zaki daure har ki saba”.
Sallamar da kunnuwanta ya jiyo shi ya sanya jikinta saki,sai ta
zubawa bakin qofar dakin ido tare da barin qorafin da takeyi, halima ce
ta shigo
“mama ga yaya mukhtar”
“To ya shigo mana” ta fada tana gyara mayafin jikinta,qasa sumayya
tayi da kanta tana duban yaron dake saman cinyarta yana tsotsar nono
a hankali,sallama yayi cikin dakin sannan ya qaraso a nutse hannunsa
dauke da qatuwar baqar leda,baki daya idonsa na kan sumayya da
yaron wadanda kowannensu yake jin mabanbantan yanayi a kansa
cikin zuciyarsa,wata qauna ta musamman yaji ta dirar masa tun kafin
yayi tozali da gudan jinin nasa,yayin da tausayi da kuma wata daraja ta
sumayya ta daban yaji ta ginu a ransa,a mutunce suka gaisa da maman
sannan ta miqe ta fice,shiru ya ratsa dakin bayan ficewar tata,shi yana
zaune yana aukin kallonsu ya rasa daga inda zaya fara,yayin da itama
taqi motsin kirki dukkan idanunta na kan yaron nata tana dubansa,tana
jin yadda yake zuqar mama har cikin ranta,ci gaba yayi da dubansu
wani yanayi na ratsashi,sai suka burgeshi sosai,karo na farko da yaji zai
iya yafewa sumayyan kome tayi masa,yana ji a yanzu ta cancanci
yafiyarsa.
Cikin qwarin gwiwa da karsashi yayi gyaran murya tare da
muskutawa yace
“Sannu sumayya”ta dan cije lebe kadan sannan ta amsa can qasa
“yauwa”
“Sannu da qoqari,Allah ya saka miki da alkhairi,na yafe miki sumayyan
duk wani abu da kika yimin” da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta
kau da kai
“Bana buqatar yafiyarka tunda ni din ban aikata maka ko wanne laifi
ba, hasalima ni nafi cancanta da a nemi yafiya ta” mamaki kalaman
nata suka bashi,bai kai ga furta komai ba mama ta sake shigowa
hannunta dauke da kofi cike da kunun kanwa yana tururi
“A’ah,baki bashi shi ya ganshi ba,ki cire shi haka idan ya gama ganinsa
yaci gaba da sha ko” ta fada tana dire kofin tare da ficewa.
Bata kammala ficewar ba ya taso da kuzarinsa ya qaraso gabanta
sanda ta cire maman daga bakinsa tana gyara masa rufa,ya miqo
hannunsa ta dora masa shi saman hannun nasa tana fadin
“Ga abdallah nan”sai ya cira kai ya dubeta,tabbas suna ne mai kyau da
asali,ko shi din ma sunan yayi masa, baice komai ba ya koma da baya ya
zauna inda ya tashin yana kallon yaron, baisan fuskarsa ta wadata da
murmushi ba, baisan hawaye na bin fuskarsa ba sai da yaga digarsu kan
kuncin yaron wanda hakan ya sanya yaron bude idanunsa yana
kallonsa,wata qaunar sumayyan ke son dawowa cikin zuciyarsa,ko
babu komai koda ta aikata laifin tayi fama da dakon wannan qaton
babyn cikin cikinta tsawon watanni tara ta kuma yi naqudarsa ta haife
masa,rana da wani matsayi na daban wanda babu diya macen da ta
takashi cikin rayuwarsa,ita din ma dubansu take tana daga zaune,wani
wawan rauni keson ziyartar zuciyarta,saidai zargin saurin yanke
hukunci na mukhtar da rashin bincike ke naushin zuciyarta,sai ta dauke
kai daga dubansu tana jin kuka nason qwace mata tana qoqarin maida
shi.
Ya jima zaune yana aikin kallon yaron da yi masa addu’a tamkar zai
maidashi ciki,sam kamar ma bashi da niyyar tafiya, har sai da aka sake
yin baqi sannan ya miqe ya dora mata shi saman cinyarta,ya sunkuya ya
sumbace har tana jin hucin numfashinsa wanda hakan ya sanya ta ja da
baya,ya dago yana dubanta bayan ya ajjiye ledar da ya shigo da ita a
gefanta ya dora kudi a sama
“ga wadan nan ko zakuyi amfani da su,ban yarda a dorawa kowa wani
nauyi wanda yake nawa ne,Allah ya qara muku lafiya”ya fada yana
juyawa ya fice daga dakin a sanyaye tamkar bai son tafiyar
Cikin kwanakin hidima aka dinga yi sosai cikin gidan,duk wani dan
uwa na jiki ko aboki babu wanda baizo ya tayasu murna ba,mukhtar
kuwa kullum qafarsa na gidan babu ranar da bazaizo ganin fuskar
Abdallah ba,sau tari saidai sumayyan tasa a miqa masa shi tana daga
cikin gida.
Yaya yahanasu tazo a kunyace saidai ita daya don sauran duk sun
kasa zuwa,atamfa ta kawowa sumayya turmi biyu sai dan qaramin
akwati na qarshen wanda ta cikoshi da kayan baby,ba wanda ya nuna
mata komai suka karba suka mata godiya.
Suna akayi na gani na fadan tamkar tana gidanta,hatta anty dije
dake abuja bala barta abaya ba sai data halarta ita da yaranta baki
daya,duk da cewa suna tsaka da zangon karatu amma sai da suka dauki
uzuri suka zo,rago da saa mukhtar ya yanka masa,sosai abdallah yaga
gata,yaron yazo da farinjini da goshi mai yawa,qauna da soyayya ko ta
ina,kowa gwada masa kalar tasa yake yi.
****
*****
*****
Jego take sosai irin na daa shi mama take mata,sosai take gasata ta
kuma cikata da cimaka,irinsu romon nama,tuwon dawa kunun kanwa
kunun gyada da sauransu,hakanan babu fashin wankan ganye safe da
yamma take yinsa har sai data cika kwanaki arba’in harda doriyar
kwana biyar,zuwa lokacin ta murje ta dada kyau,idan ka dubeta ba zaka
taba cewa ita ta haife abdallah ba,yayin da abdallahn yayi wani irin
wayau da qiba dauka da nishi ajjiyewa da nishi,kullum mukhtar na
hanyar gajin yaronsa,sau tari yakan bawa mama da malam tausayi
yadda baya ko gajiya,duk sanda zaizo hannunsa dauke da wani abu
yace na abdallah ne, har da abinda bazai yi masa amfani a yanzu ba
saidai ko nan gaba,itakam sumayyan bata ma yarda su hadu bada
yaron take ta shige daki,yakan jima yana yiwa yaron wasa tare da jin
qaunarsa da kewar mahaifiyarsa cikin zuciyarsa.
****
*****
*****
****
Rayuwa ta mata kyau saboda ta samu gata yadda ya kamata,cikin
watanni uku abdallah ya soma iya zama,wata na biyar rarrafe ya
miqa,sosai yaron yake da shiga zuciya da daukan hankali,saboda tsafta
da kukawa da yake samu, ko yaushe zaka ganshi tsaf cikin shiga ta gayu
kamar wani saurayi,idan manyan kaya ta sanya masa kai kace babban
mutum ne,idan kuma qananun kaya ne sai ka dauka saurayi ne,baya
rabo da qamshi shi yasa har maqota aikowa suke daukarsa,zuwa
wannan lokaci mukhtar wani lokacin yakan zo ya daukeshi ya jima
wajensa wani lokaci har kasuwa yake leqawa da shu,tun tana bata rai
mama na mata fadan na zata raba da da uba ba har ta saki ranta ta
haqura,wata goma ya qware a tafiya sosai,idan ka ganshi sai ka zaci
yayi shekara daya da rabi ne.
A lokacin yaya abubakar ya sama mata foam na wata makaranta
dake koyar sana’o’i,ta zabi ta koyi yadda ake saqa da humra turaren
wuta da na kaya da na tsugu no, hankali kwance take zuwa
makarantarta ta dawo don bayan layinsu take,abdallah kuwa bai cika
rigima ba sai idan yaso,saboda haka a gida take barinsa taje abinta ta
dawo,koda ya sa rigima ma zainab ko halima kan daukeshi su kai mata
shi,a lokacin ta sake wani kyau da cika,saika rantse da Allah bata taba
aure ba balle har ta haifi yaro.
*****
******
******
Qarfe hudu da mintuna ta iso gida a gajiye,tana sallama abdallahn
ya kubce daga hannun zainab dake shafa masa hoda a wuya da alama
wanka aka sake masa,riga ce mara hannu a jikinsa sai wando three
quater,yayi kyau sosai,da gudunsa ya taho ya tareta yana mata
gwalantu wanda ke nuna alamar fara koyon magana,daga shi sama tayi
tana juya shi suna qyalqyala dariya sannan ta direshi tana amsa
maganar zainab wadda ke mata qorafin yau abdallah ya bata kaya sunfi
uku
“Kunfi kusa ai, bake ke kareshi ba idan zala masa fada” tayi maganar
tana qarasawa bakin fanfo don daura alwala tana sake fadin
“Mama fa?,naji gidan shiru” zainab dake tattara kayan kwalliyar
abdallah ta amsa mata
“Eh sun fita ita da ya halima gidan maman shafa’atu ganin salima”
“Kice biki ya kusa kenan”
“Wlh saura ‘yan satittika basu wuce uku ba”
“Allah ya sanya alkhairi” ta fada tana gyara daurin dankwalinta ta shige
daki donyin sallah abdallah na biye da ita a baya yana mata surutu.
Tana kammala sallar abdallah na saman jikinta yana faman qiriniya
da nuqurqusarta taji sallama kamar ta bahijja, kafin ta yunquro taji ana
tambayar tana nan zainab ta amsa da eh, bahijjan ce kuwa, hannu
bibbiyu ta karbeta sai da suka fara gaisawa ta sanar mata tare da abdur
rahman suke yazo ganin abdallah,idanu ta zaro tana dariya
“Iyeee,kice da tare da larabawan madina kuke kada kai ace har an
gama karatun?” Cikin murmushi bahijja tace
“A’h,yadai samu hutu ne yace tunda ya shekara bari yazo yaga gida”
“Da kyau…..Zainab zoki dauki carfet ki shimfida masa a zaure(soro)”ta
fadi tana murmushi tare da qoqarin miqewa.
Tare suka fito da bahijjan saboda abdallahn na hannunta,ji take
kamar kada ta ajjiyeshi yaron ya shiga zuciyarta sosai.
Tun kafin ta qarasa soron wani kalar qamshi na daban ya ziyarci
hancinta,zaune yake ya hakimce kan carfet din,yana sanye da shadda
ruwan siminti sai qyalli take,kansa saye da baqar hula, baki ta riqe tana
murmushi, sosai abdur rahman din ya sauya,ya zama wani babban
mutum lokaci daya,kai bakace abdur rahman din dake tayata zama
bane sanda tana amarya mai qarancin shekarun da basu gaza goma
sha uku ba,ya zama mai cikakkiyar kamala da haiba,fatar nan tayi fresh
da ita,duk yadda taso ta zolayeshi da tsokana kamar yadda suka saba
sai ta kasa sanda shi yake tsokanarta da iyeeem ba,yarinya ta girma
gata da yato ta zama mama,bayan sun gama barkwancinsu
kasancewarsa mutum mai yawan son barkwanci sannan ya shiga
jajanta mata abinda ya faru tun daga samuwar cikin abdallan zuwa
haifeshi,suna tattaunawa yana wasa da abdallahn har bahijja ta gaji ta
tashi ta koma ciki wajen zainab ta barsu a nan.
Sosai yaron ya masa ya tafi da shi har ya gaza boyewa sai da ya
furta,murmushi kawai tayi suka ci gaba da hirarsu a haka mama ta
cimmasu,a mutunce suka gaisa tana mamakin ganinsa da sauyawarsa
ta tambayeshi mutanan gidan ya amsa duka lafiya ta dubi sumayya
“Amma ai abdur rahman ba bago bane da zaki barshi a soro,maza tashi
ka dawo tsakar gida” cikin tsokana yace
Atoh mama na sani ko rowar gidan ake min,ni kuma naga gun hira
kuwa har na koma,tunda nayi aboki” hararar wasa sumayyan ta masa
tana cewa
“Dadinta ai na maka tayi kace ala tunda mama bata nan nan zaka
zauna” ta fada tana shigewa cikin gidan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *