QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 29

QADDARAR SUMAYYAH








CHAPTER 29








Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da kuma yaqini cikin zancanta,itama dubanta sumayyan keyi kafin ta saki murmushi sannan ya kada kai
“Ni nayi kuskure amira,ni na yi masa kallon mukhtar dina bayan bashi bane kamanceceniyar iya murya ce kawai,koma waye zaiyi zaton ba lafiya tunda baisan farkon lamarin ba,amira,bana jin so ko qaunar ko wanne namiji bare na yi sha’awar zaman aure da shi,banqi a ce nabi mukhtar ba muyi zamanmu cikin rahamar ubangiji,abunda kawai nake tausayawa abdallah na” ta fadi cikin karyewar murya da rauni,duk da qoqarin kaucewa hakan da takeyi,tausayinta ya sake kama amira
“Da gaske amiran umman khalipha kin taba aure kuma ma har da boy?” Ta tambaya cikin zumudi,kai ta gyada mata tana murmushi
“Zanso naga boy din nan,na tabbata zaiyi kyau kamar mamarsa” wannan karon har dariya taso sara,saboda ta tabo gudan jininta,yaron da shima tun kafin ya shaqi iskar duniya ya fara fuskantar gwagwarmaya da matsalar rayuwa,koda ya shigo cikin duniyar ma ba’a barshi ya huta ba sai da aka so saida rayuwarsa,zainab ta fado mata,ko yanzu tana wacce duniya,baki daya sai taji son aure ya sake fita daga zuciyarta,itakam yanzu me zata ci da aure
“Amma zanso amira ki amincewa qudirina,na tabbata cewa rayuwar yaya man zata sauya zuwa yanayin da muke masa fata da hange,zan iya cewa ANTY SU’AD bata da wani amfani a rayuwanshi” cewar amira tana duban sumayya,kai ta shiga girgizawa
“Duk mai qaunata amira ba zai sake min sha’awar aure ba a yanzu,nikam me zanci da aure,auren ma na mai mata”
“Me kike cewa ne?,amira zanso sanin wace ke,na tabbatar akwai wani abu a rayuwarki ba wai mukhtar bane zalla” miqewa tayi a hankali ta zauna tana duban amiran
“Babu lokaci,duba kiga goma na dare”
“Ko zan kwana anan nasan babu damuwa,ina son ki ban labarinki don Allah,naji anty dije na fadin wasu abubuwa da ban gane ma kansu ba”murmushi tayi
“Me zakici da labarina banda kayan sanya hawaye a ciki,babu komai a labarina face wuya da naci game da kishiyoyi da abokan zama na” idanuwa amiran ta zaro
“Kina nufin bama aure daya kika yi ba amiran umman khalipha?,ina cewa zamuyi sa’anni dake fa?” Dariya tayi wannan karon
“Hala mass com kika karanta ko,ina ce miki dare yayi amma baki damu ba?”
Dariya itama ta saki tare da miqewa ba don taso ba
“Zan tafi,amma zan dawo ki bani labarinki”
“Sai kinzo,sai da safe na gode”
“Nice da godiya kuma kiyi haquri da abinda ya faru”
“Babu komai QADDARA CE!” ta ambata wani abu na taba ranta,juyawa amiran tayi ta fice tana murmushi +

****** ******* *******

Sukuku haka ta wuni washegari,duk da ba wani abu take ji na ciwo a jikinta ba amma baki daya bata da kuzari kamar wadda aka zarewa laka,da yammaci tana kwance a falon,babu kowa gidan daga ita sai anty dije,su laila sun tafi gidan kakarsu,itama rashin qwarin jiki ne ya hanata zuwa taji muryar amira tana sallama,miqewa tayi daga kwanciyar tana amsawa tare da maida daurin dankwalinta da ya zame,sai taga ashe su biyu ne ita da anty maamaa,miqewa tayi fuskarta qunshe da fara’a tana musu sannu da zuwa,kitchen ta juya ta dauko lemo saman tray ruwa da kofuna ta ajjiye musu sannan ta haura sama don kiran anty dije.

    Tare suka sauko,fuskarta dauke da fara’a itama take musu lale da zuwa,ta zauna suka gaisa sannan sumayya ta gaida antyn kafin ta waiwaya ga amira suka gaisa
“Zuwa nayi dubiya,jiya muna cikin gida ashe haka abu ya faru,sam ban sani ba sai dazu da mahmoud ya shigo yake gayan,sai kuma farida itama ta sanarmin su suka kawota gida”
“Wallahi kuwa,abin sai addu’a,damuwar dake ranta ce ta mata tasiri har ta haifar da hakan”
“Allah ya kiyaye gaba,baki daya ma banga mustaphan ba yau,yana ta shirye shiryen komawa,inason tambayarsa ya akai hakan ta faru,banji dadi ba sam bai kyauta ba,ai ba’a haka…..sannu sumayya ya jikin?” A kunyace kanta na qasa tana murza yatsun hannunta,tana jin tamkar ta jawowa kanta wani babban abun kunya ne,kada ma wasu su tsammaci saboda shi ta suma tace
“Na warke ai anty”
“Allah ya sawwaqe ya qara afuwa”
“Amin anty dije ta amsa,amiran ce ta dubi sumayya
“muje ina son in ganki”tana dariya,sai ta miqe tayi gaba amiran ta biyo bayanta.
       Bakin gado suke zaube baki dayansu amiran ta kalleta
“ina alqawarina?”
“Labarina bazai yiwu ba yanzu amira,ki bari na sake samun sauqi ko?”shiru ta danyi tana kada kai
“To shikenan,Allah ya qara baki lafiya”
“Amin” ta fada tana murmushi,jefi jefi amiran ta dinga sako mata hita,wata ta ‘yan uwa wata ta qawayenta wata ta gidansu duk don ta sake sakin jiki,yawanci duka bata sansu ba,amma abun yana burgeta,saidai tayi murmushi kawai,a nan ta fahimci su’ad itace matar mustapha.
Suna zaune anty dije ta leqo tace anty zata tafu,miqewa tayi tana cewa
“Nima tafiya zanyi,zamu je unguwa ne yau duka ‘yammatan,sai na dawo”
“Allah ya tsare,na gode ki gaida ummee”
“Zataji kuwa,don batasan abinda ya faru ba,da yau ya man ya shiga uku wallahi,inaga ma sai na guntsa mata batun” ta fada tana dariya gami da ficewa,sumayyan nason ce mata kada tayi amma tuni tayi gaba abinta. +

      Kiran wayar bdur rahaman ita ta qarasa tayata hira har sha biyu na dare sunata hira,yana ta bata labarin yadda shirye shirye suka kankama na bude islamic clinic dinshi,yana so ya soko mata maganar yadda yayi missing dinta da kuma yadda yake son ganinta saidai yana tsoron kada damar da ya samu ya rasata,sam bata gaya masa zata zo kano ba har sukayi sallama.

  *******    *******   ********

      A hankali ya dinga takowa cikin tafiyar sa ta qasaita har cikin falon baabaa prof din,sanye da short sleev polo t.shirt jaa da touches na baqi,straight leg trouser sai safa a qafarnshi,hannunsa soke a aljihun wandonsa,wanda ya zame masa al’ada idan ya sanya qananun kaya,idan ba waya hannunshi to zaka samu hannayen cikin aljihu ko harde a qirji.

       Sallamarsa ce ta sanya baabaan dago kai yana dubansa,mai hali bai sauya halinsa,wasu daga al’adar turawa har yau sunqi barin mustaphan,ko da yake ta yaya zasu barshin bayan har yau shima bai bar cikinsu ba,sam baison manyan kaya,da wuya ka ganshi da su,cikin girmamawa ya qaraso ya duqa gaban baabaan yana gaida shi,amsawa shima yayi saidai fuskanshi sam babu walwala sabanin yadda ya saba ganinsa
“Yaushe ne zaka koma” hannayensa soke cikin juna ya amsa kamar wanda baison yin maganar
“Cikin wannan satin in sha Allah”
“Allah ya lamunce”
“Amin ya Allah”. Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu,shi mustpha na sauraron me baaban zai gaya mishi tunda shi ya aikata takanas sashensa aka kira shi,yayin da shi kuma baaban yayi banza da shi,yana so yau ya qure miskilancinsa,yaci gaba da bude shafukan jaridar dake hannunsa,sam baka rabashi da duba jaridu,duk da bai cikin sabgogi da al’amuran gwamnati a bayyane amma a badini gangar jiki da zuciyarsa na tare da su.

      Har ya kammala karatun jaridarsa baiji yace komai ba,hasalima da ya daga kansa sai yaga ya jingina bayansa da jikin kujera gami da miqe qafafunsa idanuwansa a lumshe,ajjiye jaridar yayi yana sauke ajiyar zuciya,glass dinsa ya zare shima ya ajjiye gefe yana dubansa
“wato ba zaka iya tambayar dalilin da ya sanya na kiraka ba kenan”miqewa yayi ya zauna sosai yana duban baaban
“nayi zaton baka kammala abinda kake bane,banson kuma katse ka”shuru yai ya jinjina kai,duk cikin ‘ya’yansa bai haifi kamar mustapha ba har yau ta kowanni fanni ya tsrerema ‘yan uwansa maza da mata me ya kaika ture yarinyar mutane har ta suma”
“Yarinyar mutane har ta suma?” Abinda ya dinga maimaitawa ciki kwanyarsa kenan,sam ya mance wace ce,wa baabaa ke fadi ya ambata cikin zuciyarsa
“Yarinya baquwa ‘yar gidan alhj farouq” har ga Allah bai fuskanci kan wa baba ke magana ba,don shi baki daya ya mance lamarin,baaban ya kalla kamar yanason qarin bayani kan abinda yake cewa,baabaan yasan irin kallo,indai mustaphan yayi ba shakka yana buqatar qarin bayani
“Tashi kaje,ka kyauta ka kuma yi abinda ya dace,nima zanyi abinda ya dace din” duk da bai gane da wa yake nufin ba amma ya miqe kasancewar ya riga ya bashi umarni,cikin girmamawa ya rusuna yana cewa
“A huta lafiya” baban bai amsa shi ba har ya miqe ya juy,har ya taka daya biyu sai kuma ya juyo ya dawo ya sake rusunawa aladabce
“Dambun naman naka ya qare?” Ya fahimci me yake nufi,dambun naman da sumayya tayi masa ne,ya ganshi yana ci ya tsokaneshi da cewa gun saidawa aka siyo masa don yasan baison cimar siyarwa,yace idan ya qare zai masa magana ya sake siyo masa a inda aka siyo
“Bai qare ba” baban ya bashi amsa idonsa akanshi har ya miqe,baiyi qarya ba,mustaphan daban yake cikin yaranshi,kamar yadda yake da wasu baqin halaye haka dabi’unsa na kula da iyayensa suke,daban ya daukesu,martaba da darajarsu bai hada ta daya data wani halitta ba,cikin kowanne yanayi ko motsi nashi yakan sanya shi gaba,fatarshi da addu’arshi daya Allah ya azurta shi da zuriyya dayyiba saliha,wadda zata ji qansa yadda yake jin qan nashi iyayen. +

*****  ******   ******   *****

      Daren da zasu tafi kanon kasa bacci tayi baki daya,tsaf ta gama hada komai,hatta da kayan da zata sanya goben ta waresu gefe,cikin irin wannan zaman taji kuwwar wayarta,ta janyota tana dubawa,baquwar lamba cr,maidata tayi ta aje don a yanzun tsoron daga baquwar lamba take,sai data fuskanci wayar na neman hanata sakewa ya sanya ta dagawa,muryar alqasim ce ta bayyana,yasan kadan daga aikinta ta datse wayar wanda baya fatan haka,saboda yaci wahala kafin ya kai ga samun lambarta,hakan ya saka ya cikata da magiyar ta tsaya ta saurareshi,bai kyautu ta watsa masa qasa a ido bo saboda qimar mahmoud,hakan ya sanya ta tsaya tana sauraronsa zuciyarta fal da mamakin inda ya samu ainihin lambarsa,gaisuwa sukayi ta mutunci ya sake mata sannu da jiki ta amsa masa,shiru yayi kamar ba zaice komai ba hakan ya sanya ta buqaci kashe wayarta,wanda shi ya zaburar da shi ya soma magana,tatsuniyar gizo dai bata wuce ta qoqi,
“Alqasim,ni bazawara ce na taba aure,ko da ina da ra’ayin aure banda ra’ayim auren saurayi,ballantana ma mi ban hango shekarun da na tsara ba kafin na sake aure,babu lokaci,saboda haka ina mai godiya bisa qaunar daka nunan,kuma ina mai baka haquri tare da addu’ar ubangiji ya baka wadda ta fini” ta kaiwa qarshe ta kashe wayar ta cillar gefe tare da mirginawa ta kwanta ta runtse ido tana son bacci ya dauketa ko zata samu damar tashi gobe da wuri ta shirya.

********    *******   *******
Qarfe sha daya na rana dukkan shirin tafiya ya kammala,wannan karon har da abban laila zasu tafi a mota daya,sun gama komai har motar ma drivern ta faka ta bakin get din gidan,duka suna ciki zaune,abban laila kawai da ya shiga yiwa baaba sallama suke jira,wanda sabonsa ne baiyin kowacce tafiya bai sanarwa baban ba,saboda ya daukeshi a mazaunin mahaifi. +

     Anty dije ce tayi mantuwa cikin gidan,botiki ne data zubawa mama sabulun salo mai yawa a ciki wanda su zainab zasu hada sabulun gyaran jiki,sau biyu tana aiken laila bata ganshi ba,ganin zata bata mata lokaci kada abbansu ya fito ba’a dauko ba ya sanyata tura sumayya.


        Kunnenta maqale da waya suna waya da abdur rahman,yayin da daya hannun ke riqe da dan botikin,ta sanyo qafarta waje kenan kunnenta ya jiyo mata muryar tasa ginshira yana fadin
“Amma why not kubi jirgi,akwai jirgi daga nan zuwa kano 12″dariya uncle farouq yayi
“wannan kam ai su ku manya,ba damuwa,awa biyar ne ba dadewa zamuje” hannu ya bashi yana fadin
“Allah ya tsare”
“Amin amin,wataqil kafin mu dawo kun koma,sai gani na gaba” murmushi kawai yayi ya juya,har a lokacin tana labe bakin qofar,hakanan jikinta ke rawa har wayar hannunta ta subuce ta fadi bata sani ba
“Ah ah,ashe kin dauko me kuma kike a tsaye a nan?” Anty dije ta tambayeta wadda ta biyo sahunta jin shirun yayi yawa
“Ba komai…fitowa zanyi dama” ta fada muryarta na rawa tana durqusawa tare da soma tattare wayarta data watse a gun,bin wayar anty dije tayi da kallo cikin ranta tana tambayar me ya faru har ta kammala tattarewar ta juya tabi bayanta bayan ta rufe gidan. 
Luf tayi cikin motar idanuwanta a lumshe,duk da hayaniya da karadin da suke tayi cikin motar amma babu ita,bata san me ya haddasa mata mutuwar jiki ba,batasan me take tsoro ba,abu daya ta sani muryar na daga mata hankali,muryar na sanyata ta tuna da mukhtarinta,anty dije ma tayi tsammani bacci take saboda ta san jiya batayi wani isashshen bacci ba,yau kuma ta riga kowa sammakon tashi,tun tana jin hayaniyarsu sama sama har bacci barawo yayi awon gaba da ita. +

      Kamar kullum yau ma sun tsayawa wannan restaurant din don cin abinci saidai banda ita,zaman ta tayi cikin mota sai takeaway sukayi mata sannan suka wuce.

      Yamma lis suka isa kano ta dabo tumbin giwa,ko da me kazo an fika,gari ba kani ba dajin Allah,wani farinciki ya dinga shigarta tun kafin su qarasa gida,iskar garin na kano take shaqa sosai,taje farinciki ya lullube zuciyarta,doki ya mamaye zuciyarta,kewar mama malam abdallah dama su zainab suka dawo mata sabuwa fil,kamar kuwa uncle farouq ya sani yace a fara biyawa gida a sauke sumayyan,anty dije zatayi qorafi kan ba haka ba su wuce gida idan sun huta baki daya sazo gobe yace a’a sam tana son taga mamanta,hakan ya mata dadi matuqa duk da ta boye dokinta,suna sauketa kuwa suka wuce kan sai gobe zasu shigo,tana fara’a ta daga musu hannu sannan ta sanya kanta cikin gidan yaran maqota na shiga mata da jakarta. 1

      A tsakar gidan ta ware muryarta tana kwada sallama,abdallah ne ya soma fitowa da gudu halima na biye da shi,da gudu ya qarasa wajenta yana kiran
“Mami na”
“Abdallah na” itama ta fada cike da kewa ta durqusa tare da ware hannayenta ya fada ciki ta miqe rungume da shi tana dubansa fuskarta fal murmushi,ya qara kyau wayo da girma kamar ba abdallahnta ba,kallo daya zakayi masa ka tabbatarwa kanka yana cikin kwanciyar hankali tare da samun cikakkiyar kulawa,yayi bul bul da shi,fes kamanninsa da babanshi kan fuskarsa.

       Dakin mama ta shige tare da su halima da maman,tana sanya kanta falon taga amina zaune matar abubakar ciki a gaba,baki sumayyan ta bude tana kallonta
“Antynmu kice kema kina gidan namu yau?”
“Gidanku ko gidanmu,aike kam yanzu baquwarmu ce” dariya sumayya tayi
“Allah sarki anty amina,kice kinyi nauyi shi yasa kika kasa tasowa ki tarbeni” dariya aminan tayi a dan kunyace saboda mama na gurin,gaban maman sumayya ta qarasa idonta a kanta tana jin wani dadi na gajin mahaifiyar tata,itama maman kallonta take,a gabanta ta durqusa ta gaidata,cikin farinciki maman ta amsa tana tambayarta ina dijen kuma,nan ta sanar mata sai gobe zasu shigo,hira ce ta barke babu qaqautawa tsakaninsu abdallah na kan cinyarta,yaqi yarda ko nan da can yaje,halima ke dungureshi tana cewa
“Zata tafi ta barmu da kai ne mai qaton kai da kaqi zuwa wajen kowa” amina ke kareshi
“Barshi malama,yaro da uwarsa,ai yayi qoqari ma,yaushe rabon da ya ganta?” Har magariba suna hira,sai da aka gama sallah magariba sannan sumayya ta cewa zainab ta hada mata ruwa zata yi wanka,dariya zainab tayi
“Wankan lafiya da daren nan?”
“Bazan iya bacci ba sai nayi wallahi” dariya ta kuma yi Kice ba banza ba yaya sumayya kika dad wannan dan banzan kyan,wallahi abuja ta karbeki,baki ga yadda kika koma ‘yar gayu ba”
“Hada min ruwan sai kizo kici gaba da sharhin naki” sumayya ta fadi tana dariya,anty amina ce ta karbe
“Gaskiya ai ta fadi,wallahi garin ya amsheki sosai”
“Kin biye mata kenan antynmu” ta fada tana dariya anty aminan na tayata. +

       Bayan tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwar riga ta wani cotting din yadi mau gajeran hannu,ta yane kanta da dan qaramin mayafi ta dawo falon mama,a nan suja zuba tuwon dare baki daya idan ka dauke maman,suna ci suna ci gaba da hira,har yanzun idanuwan maman ma kanta,ita kanta tasan diyar tata ta soma sauyawa kamar ba ita ba,ta tabbatar sauyin rayuwa ya fara samuwa a gareta,cikin zuciyarta ta dinga mata addu’ar Allah ya azurta ta da miji na gari,wanda zaici gaba da dawainiya da ita cikin ingantacciyar rayuwa. 
      Suna gab da kammala cin tuwon malam da yaya abubakar sukayi sallama,amina tayi saurin janyo hijabinta ta sanya,yau malam da kanshi ya shigo falon maman,fuskanshi shina dauke da farincikin ganin diyar tasa,cikin girmamawa ta gaida malam din ya amsa yana tambayarta mutan abuja,tace kowa lpy suna gaida ka,amma gobe su antyn zasu shigo,madallah malam din yace sannan ya fice yana cewa bari ya barta ta huta da gajiyan hanya,murmushin jin dadi kawai tayo ganin yadda kowa cikin ‘yan uwanta ke qoqarin nuna mata qauna da kulawa.

       “Hala nan gaba kadan zamu kasa ganeki sumayya,irin wannan kumatu haka” sosai ya bata dariya,bama ita kadai ba duk jama’ar falon,don babu wata qiba da tayi tsabar tsokana ce,saidai duk wanda ya kalleta zauga yadda fatarta ta murje tayi kyau,hutu da wayewa suka sake bayyana a jikinta,sai da ya gama tsokanar tasa sannan yace
“Dazun dama nake cewa ko baku zo ba cikin satin nam zaki ganni kafin ku wuce london,inaso muyi maganar kudin abdallah dake hannuna,sun fara yawa gaskiya ya kamata kuma ayi tunanin sake fadada wani kasuwancin da su” dubanshi tayi
“Haba ya abbakar,kaima fa kamar uba kake gunsa,duk abinda ka yanke dai dai ne,baya ga haka ga malam ga mama ga yaya yahanasu ko su sun isa kayi shawara da su ku zartar da duk hukuncin da ya dace ko?”
“Eh duk munyi magana da su kuma su suka ce aji ta bakinki,amma koma me ake ciki kan ki koma zamuyi magana,yaushe zaku koma?”
“Ba zamu wuce sati daya ba”
“To ba damuwa….ke taso mu tafi” ya fada yana miqewa,amina tasan da ita yake,sai ta shiga yunqurin miqewa
“Dakata mata mana,yanzu fa ta gama cin abinci ko fada mata baiyi ba,koma ki zauna ki shirya a nutse” cewar mama tana hade rau,dariya ta kama sumayya,ba shakka idan da duka haka surukai suke da ba’a dinga samun baraka tsakanin surukai ba.
Idan kin gama ki kirani a waya,zan je ayimin aski” ya fada yana ficewa ta amsa da to. +

      Halima ce ya shiga tsokanarta kan tafiyarsu london
“Yaya sumayya dama nice,ki barmim don Allah” haka ta dinga fada,murmushi kawai tayi tana kallonsu,abinda basu sani ba ita din ce ke jin dama ita ce su,basu taba fuskantar wata matsala ba,ko yaushe suna tare da mamarsu da babansu,suna cikin garinsu,basu da wata damuwa da ke hanasu bacci ko ta sanyasu a halin tunani,tana ganin quruciya ce kadai ke sasu sha’awar zamowa ita.

        Sai takwas na dare amina suka tafi da ya abubakar,zuwa lokacin itama bashin baci da gajiyar hanya sunyo mata kabbara,tilas ta musu sallama ta dauki abdallah da yayi bacci kan kafadarta suka nufi daki.

  *******   *******   *******

     Washe gari kusan tare sukayi aikin gidan ita da mama,kasancewar qarfe shida da rabi su halima na fita makaranta sai goma na safen suke dawowa a irin wadan nan ranakun,a yanzu haka ma shirin tafiya musabaqa suke wanda suna daya daga cikin wadanda aka zaba,sunayi suna hira irin ta tsakanin da da uwa,zuciyoyinsu fes,sumayya na jin gata ga mamanta kamar kar ta sake tafiya,yayin da maman ke farincikin sauyawar diyar tata,tara da rabi suka kammala har karin kumallo,wanka sumayyan ta shiga tayi sannan ta shirya cikin atamfarta super wadda tayi mata kyau ainun,ta dan taba kwalliya kadan sannan ta sanya hijabinta ta nufi dakin malam.

     Karyawa take sanda ya shiga,ta gaidashi ya amsa mata yana fara’a
“Mutanen abuja yau anyi kwanan kano” kanta tai sunkuyar tana dariya
“Ai malam,duk wanda ya bar gida gida ya barshi” tace tana wasa da yatsunta
“Wannan kuma gaskiya ne” labari take bashi kadan kadan game da abinda ta fahima kan rayuwar garin har mama ta cimmasu a haka
“Qarfe sha daya ne daurin auren fa malam” maman ta tuna masa,a gogo ya duba sannan ya miqe
“Au,au,ai kuwa na manta,gashi sha daya saura kwata,hira ta dauken hankali,idan na dawo ma qarasa ko?”dariya tayi.” To,a dawo lafiya”
“Allah yasa”.

      Falon mama ta koma don ta karya itama,tana tsaka da hada tea abdallah ya tashi,dole ta bar karyawar ta yi masa wanka ta karbi kayansa wajen mama ta sanya masa
“masha Allah”ta fada tana dubansa tana murmushi ganin yadda yayi kyau,shima sai ya maimaita abinda tace din,dariya ya bata dai dai sanda mama ta shigo bayan ta sallami malam
“gaskiya mama bakin yaron nan ya kuma budewa”
“Ba dole ba,yaron dake zuwa makaranta me zai hana bakinsa budewa”, su halima ne suka shigo hakan ya sanya ya qyaleta yayi wajensu can yana buga musu rigima,gefe ta koma ta soma karyawa tana jinsu tana dariya cikin ranta.
        Sallamar abdur rahman data jiyo ita ta sanya ta kusa qwarewa,da sauri ta dauki ruwa ta sha,tare da janyo mayafi ta yafa kafin a amsa iso,yana sallama cikin falon ta soma tattare kayan breakfast din ba tare data kammala karyawa ba ta maida kitchen,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,don bai tsammaci tazo garin ba,bayan sun gama gaisawa da mama ta miqe ta fice,su halima ma suka gaidashi sannan suka fice don sauya unifoarm da kama aikin abincin rana na gidan.

       Idanu ya zuba mata har sai da taji nauyinsa ta kau da kai
kin kyauta qwarai,tunda har baki iya gayamin cewa zaki zo kano,matsayin yaya ma da nake tunani an bani ashe ba haka abun yake ba na bar murna” murmushi ta saki tana kada kai
“Ba haka bane,afuwa,suprise naso baka”
“Da shi dai kike so ki fake,amma inda hakanne ai da a yau da safe zaki kirani ki gayan,ko kuma tun a jiyan ki sanarmin kina zuwa kano ko?”
“To nayi laifi babban yaya ayi haquri” ta fadi cikin raha,numfashi ya dan dauke kadan,kwata kwata baison sunan,wannan sunan bai masa ba,so yake yaji ta kirashi da wani suna dake qunshe ko yake nuni da zallar qauna,kai ya gyada kawai yana murmushi,sabida ya lura idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kaishi dare
“Ina abdallah?” Sai ta dan ware idonta kamar tana nemansa
“Yanzun na masa wanka na bashi abinci,ina zaton ya fita”nashi idanun shima ya waro
” kan me zaki dinga barmin yaro yana fita waje?”dariya ta danyi
“To duka ma yaushe na dawo garin ni?,abdallah ya riga ya saba da fita tunda ya tashi gidan yara” halima ya kira yasa ta dauko masa abdallahn,ba dadewa ko ga dawo da shi,yayi budu budu da qasa da alama ya sha wasan qasansa ya qoshi,kicin kicin da fuska abdur rahman din yayi ya hau fada,tilas ta tashi ta sake gyarashi. +

       Sai da ya tabbatar ta gyarashin sannan ya miqe yana dubanta
“Har zaka tafi?” Ta rigashi fadi
“Eh,dama ai zuwan ba naki bane,tunda ba’a gayan zuwan ba,amma zan dawo ko zuwa gobe,idan ba gobe ba jibi,akwai muhimmiyar magana da nake so mu tattauna” shiru ta danyi 
“Allah ya nuna mana,ka gaida bahijja da hajiya don Allah”hararar wasa yayi mata
“bazan gaya mata ba,maruqar ba zaki je ki gaidata ba,ko kara ma sumayya fa baki da ita”dariya tayi a kunyace,ita kanta tasan bata kyauta ba
“Kayi haquri in sha Allah bazan koma ba sai naje na gaida hajiya” kafada ya daga yana fadin
“Da dai yafi” sallama ya musu ya danqawa abdallah kayan qwalama kamar yadda ya saba sannan ya wuce.

       Kwanakin ta a kano jinta take kamar wata sabuwar duniya,wuni suke hira,hakama anty dije idan ba wani gu zata ba tana gun mama,ranar da abdur rahman yace zaizo har yammaci taji shiru,hakan ya sanya ta shirya don zuwa tsohuwar unguwarsu kamar yadda tayi alqawari,halima da zainab ne ‘yan rakiya,sai laila wadda a gidan ta kwana,sumayyan tayi kyau cikin wani leshi wanda daya ne daga cikin kayan sallarta da uncle farouq ya siya mata,mayafi ta yafa bisa matsantawar halima,duk da babba ne amma tayi kyau matuqa,talkalmi da jaka komai da tayi amfani da shi ya dace da kalolin jikin lace din,sai oga abdallah shima da tayi masa kwalliya cikin qananun kaya,da rufaffen takalmi irin na maza.

      Tana tsakar gida suna sallama da mama suka ji sallamarsa a soro kamar yadda ya saba bai shigowa har sai an masa izini,maganar da suke da mama ta katse tana duban soron,sai da maman ta sanya hijabin sannan aka masa iso,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,tayi masa kyau fiye da duk lokutan da ya saba ganinta,yai yayi kamar yayi sallama da mama ya fito saidai ita tasan ba tafiya yayi ba,suna fitowa suka ganshi hakimce jikin mota,shi din ma yayi kyau cikin wani yadi mai taushi ruwan qwaiduwar qwai,gaban motar kawai ya bude mata tare da cewa
“Bismillah” kai ta rausaya ganin yadda ya tsareta da idanu kawai ta shige,su laila suka shiga baya sannan ya shiga ya tada motar.

        Sai da suka fice daga layin sannan yace
“Ina zuwa ranki ya dade?” Kanta ya sake rausayarwa tana murmushin sunan da ya laqaba mata
“Tsohuwar unguwar da muka zauna ni da ya mukhtar” wani kishi ne ya soki zuciyarsa,amma sai ya danne ba tare da ya nuna ba,kamar ta fahimci mekw tsinkulinshi sai tace
“Zanje mu gaisa da yara da iyayensu da muka zauna tare”
“Hakan nada kyau” ya bata amsa,da fari motar tayi shiru,sai daga bisani abdur rahman din ya sako hira,kadan kadan suke tabawa har suka isa unguwar.
Unguwar na nan kamar yadda ta santa,saidai tsohon gidansu da suka zauna wanda mutanen da suka siyeshi suka masa kwaskwarima,gidan maman naana suka fara shiga,taso ta kasa gane sumayya sai da naana ta fito daga daki,da gudu ta nufi sumayyan tana ihun kiran sunanta,rungumeta tayi tana dariya itama tana kiran sunanta,daga nan maman naanan tayi mata iso zuwa falo
“Wallahi sam fuskarki taso bacemin sumayya saboda canzawar da kika yi,kin sake zama babbar mace?” Maman naanan ta sake fada cikin mamaki,murmushi kawai sumayya tayi sannan suka fara gaisawa,naana na gefe bakinta yaqi rufuwa,tashi tayi taje ta siyo wa sumayyan pure water mai sanyi da lemo,dubanta sumayyan tayi tana murmushi,ba zata manta ba wannan na daya daga cikin rainon da ta yiwa yaran na girmama baqo,ashe har yau basu manta ba,ita kanta nanan ta girma ta sauya,nan sumayyan ta dinga tsokanarta na ganin girman da tayi. +

      Kafin ta bar gidan sai ga yaran na shigowa daya bayan daya,da alama nana ke shiga gida gida tana gaya musu zuwanta,dui wadda ta shigo rungume sumayyan take cikin jin dadi,itama mamakin girman yaran take,kusan awa daya da wani abu tayi a gidan sannan ta dinga shiga gida gida yaran na rakata,kowa mamakin sauyawarta yake inda ita kuma sam bata ganin sauyawar da tayi,duk gidan data shiga sai ta ajjiye musu dubu daya,cikin kudin da ya abbakar ya bata jiya a ribarta na kudinta da ake juya mata,sunyi murna kuwa sosai,sai magariba sannan suka bar unguwar duka abdur rahman na cikin mota yana jiransu.

        Sai wajen isha’i suka koma gida,don daga qofar gida da ya ajjiye motar masallaci ya tafi sallar isha’i,sai da ya dawo yayi kiranta a waya kan ta fito ya dawo,sanda ya kira din fitowarta kenan daga wanka,don ranar ta gaji da wuri take sonyin bacci.

        A sitting room dinsu ta sameshi wanda halima ta bude masa ta masa masauki a can,kamar kuwa tasan sumayyan bata son komawa cikin motar,kallonta yake sake yi,komai ta sanya kyau yake mata,rigar data sanya ba wata ta azo a gani bace amma ta mata kyau duk da hijabi ne a jikinta saidai qarami ne.

       “Sumayya,zuwa yanzu na gaji da zaman kare a karofi da nakeyi,lokaci yayi da zamu fukancu gaskiya baki dayanmu,ni na sani cewa bazai yiwu naci gaba da biye miki a yadda kike so ba,kamar yadda kema kika sani cewa indai da rai da lafiya malam bazai taba barinki babu aure ba” abdur rahman yayi shiru yana maida numfashi tare da nazartar yanayin da sumayyan ta shiga sannan ya dora
“Ko baki so sumayya dole a ce mukhtar ya koma ga Allah,kin sani na sani haka ma duniya ta shaida,don wani wanda kake so ya rasu ba shine zaisa kace kai kuma ka bar yim taka rayuwar ba,yin hakan dai dai yake da gayawa Allah bai maka dai dai ba kenan,tunda ya dauke wanda yaga dama ne ya kuma bar wanda yaga dama babu wanda ya isa ya tilastashi,gata daya zaki masa shi da yaronshi ki killata kanki a gidan aure,ki bani dama sumayya na cike miki gurbin farincikin da kika rasa”
“Sumayya!” Ya kira sunanta cikin kaurara murya
“Inason yau ki gayamin matsayina,mu bar wannan zaman qaryar,zaki iya aure na ki zauna da ni?” Shiru tayi maganganun abdur rahman na ratsata,babu shakka gaskiya ya fada mata,wanda shine ya fara gaya mata karo na farko tun bayan rashin mukhtar idan ka dauke malam da mama
“Idan har kin yarda ki barni na yiwa malam magana,tunda a yanzu yana tunanin na janye tunda har kin sake wani auren,ya taba gayan hakan cikin wasa,saidai ni sam cikin zuciyata ba haka bane,har yau sumayya sumayya ce bata sauya ba a idanuwa na”
Shiru ya sake yi don ya bata damar fadin ra’ayinta da abinda ke zuciyarta.
Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala’alla zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah” ta qarashe maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d’a namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu’ar samun zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi
“Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama bayan ni,kinyi alqawari?” Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance zuciyarta ba lafiyayya bace?
“Baka da wannan damuwar” ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi sallama. 2

       A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa. 1

       Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah irin na al’ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama malam da qannenta iya son ranta,abin dadin uncle farouq ya qara musu kwanakim yace su cikashe kwana goma,randa suka cika sati suka soma zaga ‘yan uwa da qawayen anty dije suna musu sallama,kusan ko ina da sumayyan aka je don itama ta yiwa dangi sallama,kwana biyu suka kammala ya rage musu kwana biyu su koma abuja don fara shirin tafiya uk london. 49

     Washegarin ranar da zasu tafim bayan ta gama hada kayanta baki daya ta shirya tsaf ta shirya abdallah,ta riga data yiwa driver magana zata unguwa,gidan yaya yahaa take son zuwa don yi mata sallama,anty dije tace zaya zo ya kaita,qarfe sha biyu na rana ya iso,ta yiwa mama sallama ta dauki abdallah suka tafi.
Daga falo suke amsa sallamar tata,yaya yahanasun ce kawai ta dauki murya,jamila fatima da fiddausi nr zaune duka a falon,gefe kwanon koko ke da kofuna da alama shi suka gama sha,baki daya fiddausin ta fige ta fita kamanninta tayi baqi kamar ba ita ba,yaranta uku a yanzu (banda yaran data haifa wanda sumayya taje sunansa)har yau tana gida babu wani ci gaba,uwar miji tace ba zasu iya ba ta cika haihuwa,danta ba qarfi gareshi ba,sai su fatima da rashin aure kan lokaci yasa suka soma tsotsewa,jamilan ta qwallafa rai kan wanda takeso shi kuma yayarsa ta hana tace auren gida zaiyi,fatima ma kuwa babu maganar kowa,baki dayansu anty dijen ke riqe da su,abun akwai tausayi,mataimakin madogarar dama qwaya daya ne MUKHTAR,a yanzu da babu shi kuwa babu wani mai dubansu,dukkaninsu washe bakin ganinta suke itama tana amsa musu fuska sake har tayi matsugunni kan daya daga cikin kujerun,tuni abdallah yayi wajen yaya yahanasu,ta rungumeshi tana shafa kansa tare da duban fuskarsa,qwalla ta cika mata idanuwanta har ta soma gangarowa,duk sanda taga yaron mukhtar yake tuna mata,kamanninsu daya,tana jin kanta a mai laifi,a wadda tayi silar maida shi maraya,kullum kwanan duniya sai ta yiwa zainab Allah ya isa. 3

STORY CONTINUES BELOW

      Baki dayansu jikinsu yayi sanyi ganin yadda yayan ke share hawaye,tuni itama sumayya ta fara goge tata qwallar,tsawon mintuna kafin su bawa zukatansu haquri sannan suka shiga gaisawa,baki dayansu kunyar sumayyan sukeji,ga wani girma da suke bata na daban,ranar anan ta wuni,har la’asar,sai ina kasa ina ka ajjiye suke da ita,sai da tayi sallar la’asar sannan tayi sallama da su bayan ta ajjiye ma yaya yahanasun sabulai klien da su maggi cikin leda mai layi layi,sannan ta baiwa fatima da jamila dari biyar biyar,fiddausi dubu daya duk cikin irin kudadenta.

       Hakanan ta tsinci kanta bayan fitowarta da yiwa mai a daidaita sahun data tsaida kwatancan gidanta,ma’ana gidan qarshe da suka zauna da mukhtar,wanda tun wajen raba gado ya shigo cikin kasan su,daidai madaidaicin get din gidan ya ajjiyeta,ta sallameshi ta dauki abdallab,jakarta ta laluba cikin sa’a muqullan na ciki ta sanya ta bude fa shiga.

      A hankali ta dinga takawa tana duban gidan,duk taku guda na dawo mata ne da duk wata rayuwa tata da ta shude can baya,sannu a hankali zuciya da gangar jikinta suka raunana,ta dinga takawa a sannu har ta kai ainihin falonsu,duk kayanta na jere ma ciki babu abinda ta fitar,saidai gidan yayi qura sosai saboda rashin kasancewar kowa a ciki,shimfide abdallah tayi saman kujera wanda ya soma bacci tun cikin adaidaita,idanuwanta suka wurga zuwa qofar da zata sadaka da bangaren mukhtar,sai ta miqe tana duban qofar harta sada kanta da ainihin dakin gadonshi,babu komai ciki kamar yadda mamallakin gun bai duniya,sai ta gaza riqe hawayenta suka fara sintiri kan kumatunta,gefe guda ta duqe tana bin bango saboda rawar da jikinta keyi ta rushe da kuka mai tsuma rai da zuciya,ta jima tana kokawa sannu a hankali har nauyin dake cikin zuciyarta ya soma raguwa,ta share qwallar tata ba don ta qare ba ta juyo da niyyar miqewa,abdallah ta gani tsaye bayanta yana kallonta
“Wa ya saki kuka ammi?”hannu ta miqa masa alamar ya taho,ya taho din kuwa ya fada jikinta ta rungumeshi tana ci gaba da goge hawaye. Sai data samu nutsuwa cikin ranta sannan ta qarasa zagaye gudan,duk inda ta taka da abinda zau tuna mata,a haka ta kai har biyar da rabi sannan ta lalubo abdallah dake can wani gu yana wasansa ta sauya masa kaya ta rufe gidan suka fito idanu jajur na kukan da ta sha. +

       Washegari suka kama hanyar abuja,hankalinta yasi dagawa na barin abdallah da zata sakeyi,bata so yayi maraici irin na mahaifinshi,babu uwa babu uba,saidai ganin yadda sam bai damu ba shi ya kwantar da hankalinta,da fari ya soma maqale maqale amma daga bisani sai ya ware har da shi a masu daga mata hannu,ajiyar zuciya ta saki bayan sun hau hanya sosai ta maida idanuwanta ta rufe,sam bata son komawa abujan nan,tafi qaunar garinta kano,koba komai kowa nata yana can,da zata iya data roqi su anty dijen su barta a can din,saidai yin hakan tamkar butulci ne ga qaunar da anty dijen ke nuna mata fiye da dukkan wata ‘ya dage cikin danginsu,duk da ‘yan maganganu da ke fara tsowa na hassadar riqon nata da antyn keyi. 1

       Kasancewar basu taso da wuri ba shi yasa basu suka isa gida ba sai takwas na dare,a gajiye kowa yake,saboda haka kowa gun kwanciya ya nema idanuwa cike da bacci,dama tuni sunci abincin darensu kan hanya.

       Washe gari da gyaran gidan suka tashi,suka kintsa ko ina,kafin wani lokaci gidan ya dawo hayyacinsa,basuyi dai break da wuri ba saboda aiki.

        Zuwa la’asar har abincin dare sun gama,su khalipha na dakinsu suna gayaran kayayyakinsu tare da fara ware wanda zasuyu tafiya da shi,sumayya na zaune falon tana hutawa,hannunta riqe da waya tana neman lambar mama don su gaisa ta kuma ji ya abdallah yake,sallamar amira ita ta katse mata abinda take shirin yi din,ta shigo sanye da yadin sartin baqi sidik wanda aka yiwa doguwar riga,sai dan madaidaicin jan mayafin data yane kanta da shi,cikin fara’a sumayyan ke dubanta har ta qaraso ta samu wajen zama
“Mutanen kano ta dabo,sauka ba sanarwa?”
“Kada ki qorafi,saukar dare ce,har yanzun kuma bamu gama watstsakewa ba,sai dazun muka gama saita gidan”
“Gaskiya kam,ko mu muna nan muna hutu,baqi sun tafi sun barmu da kewa,gidan ba kowa duka ba dadi,kowa ya koma inda ya fito,dadin abun daya nima next week zamu koma school” murmushi kawai tayi,suna hutawa tamkar sunyi hidima da baqin,bayan komai akwai masu aiki dake gudanarwa
“Gaskiya kam ansha baqi,saidai Allah ya bada lada”
“Amin” amira ta fada tana lalubo wata number cikin wayarta qirar iphone 7
“Ki duba dakina can wajen bedside drower akwai black bag ki kawomin gidan umman khalipha” abinda tace kenan cikin salo na bada umarni ta kashe wayar,sumayya ta ajjiye lemo da ruwa gaban amiran tana tambayar maman husna,murmushi tayi tana daukar gorar ruwa
“Husna mutuniyarki,sun koma inda suka fito” idanuwa sumayyan ta dan fiddo
“Suma ba nan suke ba?”
Eh,mijin anty farida custume ne,basu zama gu daya,yau suna can gobe suna nan,amma lokaci lokaci suna zuwa hutu da kuma lokacin bikin sallah kamar haka” kai ta jinjina 
“Allah ya taimaka”
“Amin”hira suke tabawa kadan kadan har ta shigo bakinta dauke da sallama. +

     Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai kyau,amsa tayi sannan tace
“zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha”
“To madam” ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin
“Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri” murmishi ta saki tasa hannu ta karba tana godiya tare da fadin
“Mai yawan kenan” tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta
“Naga kina sonshi ne sosai”
“Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan” 
“Ina fata kin yaba”
“Qwarai da gaske” suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya. 2

      Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba tare da tasan ta fadi ba
“Na shiga uku ya man yau kuma?” Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta
“Ok,to yaya” ta fada tana miqewa
“Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta”
“Ok,muje na taka miki” sumayya ta fada tana miqewa
“Na gode” ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta take sosai.

          Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace
“Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?”
“Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam”
“Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana” shiru ta danyi gabanta na duka tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani
“Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba” dan qaramin murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai ko kadan bata sha’awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru.
“Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda” ta fada da siga biyu don bata da niyyar zuwa din
“Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode”
“Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma” 
“Zasuji” ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga ahalinta.
Cikin sati guda suka kammala duk wani shiri nasu na tafiya,ya kama ranar lahadi zasu tashi zuwa uk,hafiz ne kadai abun tausayi,don su kansu su laila sun daina dariya da tsokana sai tausayinsa,ranar asabar da daddare abbanshi da anty dije suka kaishi gidan kakarshi sannan suka dawo. +

        Da daren ana ya gobe zasu tafi tana zuge jakar matafiyanta wayarta ta dauki qara,bata duba ba ta dauka ta kara kunnenta,sai taji muryar lukman,murya a sanyaye  bayan sun gaisa ya soma fadin
“Da gaske sumayya baki damy da ni ba baki damu da yaranki ba,kizo kano kiyi kwanaki har goma ki kasa gayan,bare kice zaki ki gaida hajiya,sumayya me muka yi miki haka?” Sai a lokacin ta tuna ma tace zata gaida hajiyan abdur rahman,baki daya ya mance,ta kuma san shima yana sane shiru kawai ya mata ya zuba mata na mujiya
“Kayi haquri,babu abinda kuka yimin,tunda naje ban zauna ba munata shiga kasuwa da sallamawa ‘yan uwa da dangi?”
“Sallama wacce iri” dan jim tayi tana jin nauyin fada masa,saidai dole ne ya sani din yanzu
“Gobe in sha Allah zamu tashi zuwa uk,sai bayan shekara daya zamu dawo” baki daya jikinsa ya saki,jijiyoyinsa suka yi laushi,idanunsa ya lumshe wadanda ke masa zugi,ya budesu da qyar muryarsa kamar wanda zai saki kuka yace
“Da qyar ne idan ban rasaki ba sumayya,burinsu nuwajra na ki dawo musu bazai cika ba,na saddaqar sumayya kin subuce min” ya fadi yana kada kai tamkar yana gabanta,shuru tayi ba tare data ce komai ba,don batasan me zata ce din ba,itama sai ya kashe mata jiki baki daya,tausayin yaran ya taso mata,nannauyar ajiyar zuciya y saki
“Shikenan sumayya,ina miki fatan alkhairi,Allah ya tsare ya dawo daku lafiya,saidai hakan bai nuna na miqa wuyan rasaki,bazan fidda da rai da rasakin ba sai randa naga an daura miki aure da wanu wanda nake fatan wanin ya zamanto nine” ya qarashe muryarsa na dan rawa,sabida ba zaya taba mance kulawa da kwanciyar hankali da farincikin da ya samu a aurenta ba,duk da cewa baki daya zaqin da dadin na wasu taqaitattun watanni ne,amma hakan ba zai taba barin kwanyarsa ba har ya mutu,sumayya ba irin matan da kake saurin mancewa da rayuwar da kayi da su bane,tana da wata iriyar baiwa ta musamman mai tsayawa a wuya
“Na gode,a gaida yaran”
“Zasuji,da fatan zan samu number dinki ta can idan kun isa ko don ku dinga gaisawa da yara”
“In sha Allah” ta fada tana datse kiran,jikinta a sanyaye ta sauke wayar,tana mamakin yadda ta shiga rayuwar wasu mazaje,har suke iya bata muhimmanci mai yawa haka a rayuwarta,bayan ita din bata ga wani abu da take da shi ba wanda za’a kwadaitu wajen zama da ita,da wannan tunanin taci gaba da aikinta har ta kammala ta kwanta don ta huta. 6

     *RANA BATA QARYA*
Dukkansu sun hallara cikin lafiyayyar zungureriyar motar data dauke kayansu baki daya,wanda baabaa prof shi ya bada ita yace a kaisu a cikinta,anty dije data shiga sallama da su ita da uncle farouq suke jira. +

        Harara anty dije ta aika mata da ita bayan sun fito wadda batasan ta mece ba har sai data bude baki tayi magana
“Kinji dadi a ranki ko?,ai yanzu sai ki shiga ki musu sallamar tunda mai gidan da kansa ya nemeki” sosai taji kunya da har baabaa prof ya cigiyarta,bata son shiga gidan sam,haka ta sauko a hankali ta nufi gidan cikin shigar wata iriyar gown mai dogon hannu A shape,wadda anty dijen ce ta siyo musu tace ita zasu sanya,tayi rolling da dan madaidaicin mayafinta,kayan sun mata kyau matuqa,saidai baki daya jinta take a takure saboda rashin sabo,ta riga ta saba ta adana jikinta cikin hijabi.

        Gabanta na faduwa ta sanya kanta zuwa sashen baabaan
“Laaah ilah” taji an ambata a bayanta,da sauri ta juya,amira ce ke tsaye tana kallonta,fuskarta dauke da dariya hannunta riqe da mayafi
“Ai yanzun nake sauri naje rakiya kada ku tafi ki barni,na lura sam wlh amiran umman khalipha baki damu da ni ba,nike ta taki”
“Kiyi haquri don Allah kada kice haka,yimin jagora na yima baabaa sallama”bata amsa ba face gaba data soma yi wai ita taji haushi sumayyan tabi bayanta tana dariya,saidai kafin su qarasa din bakin amiran ya kasa shiru
” gaskiya dole amiran umman khalipha ki dinga boye jikinki cikin hijab,dama haka kike?,wannan idan muka jera ai sai ki kashe mana kasuwa,haka kika hade?”ta fada cikin sigar wasa da mamakin irin kyawun sumayyan,wani irin kyau me tsari da ban sha’awa,dariya sosai ta baiwa sumayya har ta kai mata duka ba tare data shirya ba,itakam babu wani kyau sam data gani daga gareta,ita amiran bata kalli kanta ba,kyau hutu wayewa da kwalliya duka,ta ina zata kashe mata kasuwa,ita bama neman kasuwar take ba don haka taci kasuwarta hankali kwance,ta qarashe sauran maganar a fili,dariya sosai ta baiwa amiran
“Wai kina nufin ba zaki sake aure ba?” Wani abu ne ya soki sumayya sai ta kasa amsawa,kai kawai ta kada mata ba tare da tace komai ba,ganin hakan ya sanya amiran jan bakinta tayi shiru,don dama ko can ita ba mai yawan bin qwaqwqwafi bace har suka isa sashen baban.
Yana falonshi zaune kan kujerunsa na alfarma,idanunsa saye da gilashi yana kallon tashar VOA,gefansa jarida ce,daya barin kuma damammiyar furarsa ce da umme ta gama dama masa yanzun nan,don ko falon bata kai ga ficewa ba. +

       Cike da kunya girmamawa da mutun tawa ta isa gabanshi kanta a qaaa,kwarjini dattijon yake mata kamar malam dinta,cikin ban girma ta gaidashi sannan ta gaida ummee dake zaune gefansa,ta amsa itama fuska sake,hakanan take jin nauyin mutanen,duk da baki dayansu baifi gani biyu zuwa uku tayi musu ba
“Da tafiya zaki mama na bakimin sallama ba?,haba,shekara daya ba nan kusa bace bafa?,kika sani ko kafin ki dawo ta Allah ta kasance a kanmu” sai taji ba dadi,ita din saurin karayar zuciya,zuciyar tata ta karye,duk sai taji babu dadi har sai data dago ta dubeshi,ya tuna mata da mukhtar dinta yayin da mutuwa ta daukeshi a ranar da yake shirin sake angwancewa da ita,tabbas mutuwa bata da sabo,amma bata fatan hakan ta kasance kan dattijon,tana jin qaunarsa a ranta kamar malam dinta,duk sanda ta kalleshi yana tuna mata da malam din
“Bama fatan haka baabaa,Allah qara muku tsawon kwana da lafiya mai amfani”
“Amin amin” umme amira da baban suka amsa baki daya,amira ke turo baki tunda baban ya fadi maganar,ta kasa shiru sai data tanka
“Wai baabaa fata kake ne ka mutu ka barmu,kullum sai kayi zancan mutuwa,bayan ko aurena ni auta baka gani ba,ga yaya mahmoud da usama” dariya yayi irinta dattawa sannan yace
“Mama na kenan,banda abinki ita mutuwa ina ruwanta da wanu tsari naka,duk sanda tazo daukarka zata yi bafa zata fasa ba,ko babu ita akwai rabuwa,zaka rabu da mutum wanda ba lallai ka sake ganinsa,kamar yadda har yau nake burin ganin wani tsohon abokina da mukayu rayuwa a karkara tare,har yau Allah bai nufi zan ganshi ba,har yau kuma yana raina” tuni idanunta ya soma digar hawaye kanta na a qasa,baabaa yayi mata fami sosai,baima lura da ruwan hawayen nata ba,ya ciro wasu kudade irin na qasar engaland din masu kauri ya miqa mata
“Ungo wannan mamana,kiyi amfani da su kinji sune tsarabata” bata son ta daga kai yaga hawayenta,sabida haka ta sanya hannu bibbiyu ta amsa tana masa godiya mai cike da fatan alkhairi sannan ta miqe ta juya ta fita,amira ce ta kalli baabaa
“Baabaa,zan rakasu airphort don Allah” umme ce ta cafe zancen
“Umhummm,wato zaki raka qawarki ko?,ina cewa nan su’ad tayi tayi ki rakata randa zasu tafi kika qi,sai yanzu jikinki na rawa zaki ce zaki,to ba inda zaki din”
“Saurara KILISHI,Allah shike hada qauna tsakanin mutum da mutum,haka kawai Allah ya hada jininta da yarinyar,barta taje,mama na sai kun dawo,daga nan kada ki biya ko ina,ki dawo kizo kimin lissafin me kike buqata na komawa makaranta kinji” cikin murna kamar qaramar yarinya tace
“Yauwa baabaa na,na gode”ta juya da sauri don ta ruski su sumayya. 14

       Cikin motar amiran ke basu labarin yadda garin yake,duk da yake akwai banbancin gari,garin data zauna su ba nan zasu zauna ba,su laila an kasa kunne ana kwashewa,murna da doki sun cikata burinta kawai su isa.

       Cikin qanqanin lokaci suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnmdi azikwe dake garin abuja,bai wuce mintuna talatin ba lokacin tafiyarsu yayi,sabida haka uncle farouq ya sallami driver din wanda ya tilasta amira yiwa sumayya sallama saboda tare zasu koma,duj fuskarta ta nuna rashin jin dadin tafiyar tasu,kai kace sunyi mugun sabo da juna
” nikam irin wannan qauna haka da amira ke gwada miki,bata da saurin sabi da sakin jiki wa mutane fa,amma ke naga ta sake miki”murmushi sumayya tayi kawai tana miqawa anty dije kudaden da baaban ya bata,kanta qulle tamau da mamakin wanne irin arziqi baabaa ke dashi haka,duk da batasan kan kudaden waje ba amma tana jin labarin darajarsu fiye da namu na naija,kuma yanzu haka wadanda ke hannunta ba daya biyu uku biyar bane,sunfi haka,ido itama ta zaro
“Wa ya miki kyautar wadan nan kudin?”
“Baabaa ne”
“Kai baabaa,baabaa,alkhairinsa yawa gareshi,Allah ya saka masa da alkhairi”
“Amin,amma anty su basujin kyauta haka” murmushi ta kuma
“Haka suke,hannun kyauta garesu,suna da mutunci da karamci,yaci ace kisan ko su waye su din,amma bari mu shiga jirgi zan gaya miki su waye su” bata kai ga amsawa ba wayarta da zuci zucin ta kashe ta soma ruri,number amira ce,cikin mamaki ta daga
“Ya mahmoud ne zai magana da ke” ta fada tana hadata da shi
“Babu fada me ya kawo gaba gimbiyarmu,yanzu fi sabilillih zaki bar naija amma ko ki sanar da abokina why?” Murmushi ta danyi
“Tunda ka sani ka wakilceshi ya mahmoud,kaa gaya masa”
“A’ah,wannan saqon ai na masoya ne,amma tunda kince haka zan gaya masa,ta inda kuma zaki wanke kanku guna indai ni yayanne ki bada num dinki idan kun isa na bashi” dariya ma ya bata,saidai yana da qima idanuwanta,shine mutum na farko da ya fara tararta cikin fara’a da girmamawa sanda ta tsoma qafarta gidan baabaa prof
“Babu matsala”
“To ina godiya,inawa umman khalipha fatan alkhairi ki sanar mata” ya datse layin,tana shirin maida wayar jaka saqon fatan alkahiri daga abdur rahman ya shigo mata,ta karanta a gurguje ta mayar masa da reply. 
       Idanu sumayyan ta shiga bazawa bayan tsintar kanta da tayi cikin jirgi ya soma dagawa da ita zuwa sararin subhana,bata samu nutsuwa ba sai bayan shudewar wasu lukatai sannan,anty dije ce a damanta
“Bari na cika alqawa ko,na gaya miki tarihin gidan baabaa prof”
“To anty ina jinki”

  *IYALAN GIDAN BAABAA*

     BAABA prof ba shine asalin sunanshi ba,suna ne da ya samu ta dalilin zuzzurfan ilimin boko da yayi har ya kaishi ga zama professor,cikakken sunansa shine MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GWAMBE,haiffen wani qauye da ke cikin pantami,mahaifinsa Adamu wanda aka fi sani da mai dabba,wanda ya ci sunan nashi ne sabida yadda Allah dora masa so da iya kiwon dabbobi tun yana qanqaninsa,ga tausayi ga dabbobi,bama dabbobi kadai ba hatta da mutane,ana amfana qwarai da tarin dukiyar da Allah ya huwace masa,wajen taimako ga mabuqata,bafulatani ne gaba da baya,ma’abocin iya kiwo,wanda kuma Allah ya albarkaceshi da tarin dabbobi,kama daga tumakai awakai raguna tinkiyoyi da shanu bila addin,wand kaf qauyensu da kewayenshi babu wanda ya kaishi yawan garke,matarshi daya khadijatu,ita ta haifa masa muhammadu da yayyensa guda biyu,dukkaninsu suna ganiyar samartaka suka rasu sai muhammadun kadai da Allah ya bar masa,yaro ne da yafi shiga ransa duk cikin yaranshi,ya debo kyawawan halayensu tsaf har da ma qari,sannu a hankali muhammadu ya girma aka hadashi aure da wata yarinyar wani 
malami maqocinsu mai suna naja’atu,cikin watanni tara kacal Allah ya albarkaceta ta haifi MUKHTAR baabaa prof,wanda ba’a jima da haihuwarsa ba Allah ya yiwa mai dabba rasuwa,ya rasu ya bar matarshi,bayan share makoki aka raba gado aka baiwa khadija matarsa da dansa muhammadun,ya karbi dukiyar mahaifinsa kuwa a sa’a don habaka tayi tayi,abu ya dinga dad gaba,saidai daga baya ya fuskanci kamar kiwon wahala ce kawai,ya saida shanun ya rage wasu daga ciki ya barwa mukhtar kyauta halak malak,yace shima ya taba aikin gado,dama can shi mai son kiwo ne,tare suke fita da shaqiqin abokinsa wanda tun yana da shekara daya a duniya baida aboki sama da SULAIMAN sule,babu abinda ke rabashi da sule,hatta bacci ma wani sa’i tare suke,musamman idan matar babanshi taso tsiyar tata,tausayinsa yake,qaunarsa yaje fusabilillah,mahaifiyarsa ta raau tun randa ta haifeshi ko waiwayowa batayi taga abinda ta haifa din bata yi ba,sai suka qulle sosai,muntari baida qani balle ya debe masa kewa,haka sule ma baida dan uwa sai hashimu,shi kuwa bai isa ya rabeshi ba don tuni altine ta shiga tsakaninsu ta raba zumuncin Allah qarfi da yaji,duk da hashimun na qaunar dan uwansa,tare suka dinga fita kiwo shi da sule,yayin da babansa muhammadu kuma ya soma saida zannuwa a cikin garin gwambe,dukkaninsu Allah ya sanya musu albarka baki dayansu,har mamakin yadda dabbobin muntarin keta habaka babansa muhammadu keyi,shida sule kiwo suke haiqan,duk da babu dabbar sulen ko daya a ciki amma sabida qaunar dake tsakaninsu wani lokaci a shike fitar ma muntarin da su,altine tayi dukan,tayi dukan don ta raba tsakninsu saboda yadda taga suke na samun kulawa a gidansu muntarin amma a banza wai man kare,saboda tare malam muhammadu ke musu komai,bai rasa ci ko sha ba balle sutura,ba’a rabasu a gidan sule dai dai yake da muntaru,data gama dukan zata kuma gansu tare,abun ya tsaya mata a rai,sai ta koma ziga gun babansa,to shi din ma baici nasarar rabasu din ba,saboda yadda qauyen aka soma zaginsa shi da matarsa kan yadda suka qwallafawa dan marayan Allahn. 2

       Cikin haka turawa suka shigo qauyen nasu,suka kawo musu makarantar boko har cikin garin nasu,kowa ya tsame dansa yace babu shi a wannan batu,muntari na bala’in sha’awar karatun,ya samu babansa ya sanar masa kan ya sanyasu shi da sule,da fari shima yace sam kada muntarin ya sake wannan magana,bayan dogon nazari da malam muhammadun yayi sai ya amince,ya hadasu da sule ya kaisu amma yace saidai suyi jeka ka dawo(day),altine zani a hannu ta shaidawa mahaifin sule abinda malam mahammadu yayi,ai kuwa ya wanke qafa yaje har gida ya ciwa malam mahammadu mutunci,a lokacin sule na gidan tare da muntari,kuka ya dinga yi yana jan baban nasa kan ya daina zaginsa amma ya mangareshi ya qara gaba,tilas malam ya lallashi sule kan yayi haquri tunda babansa baya so,haka ya haqura ba don rai naso ba,ya ci gaba da fitar da shanun muntari kafin ya dawo daga makaranta sai ya taddashi a jeji suci gaba da kiwon tare da yammaci su dawo gida,malam muhammadu yace ya ya daina,ya bari idan muntarin ya dawo sa fita tare su dawo tare,amma sam yace a’a,ai shi da muntarin duka daya ne,duka a lokacin basu wuce shekara goma sha uku uku ba. A haka shanun muntari suka sake yawa,ga cikakkiyar lafiya dake garesu,ganin haka ya sanya muntari ya shawarta da malam muhammadu zai raba dabbobin biyu ya baiwa sule rabi,saboda wahalar da yake da su ko shi sai haka,ba musu dukka suka amince har da mahaifiyarsa,randa ya sanar da sule cewa yayi bazai karba,shi don Allah don qauna da amincin dake tsakaninsu yake masa,tilas daga qarshe malam muhammadu ya tilas ta shi ya karba,godiya ya dinga musu harda hawaye,din suna da yawa baiyi tsammanin mallakar wani abun duniya kwatankwacin haka ba. +

      Randa yaje da maganar gida da yammaci ne,altine kasa bacci tayi sai data dangana da bokanta,kafin wayewar gari ya yiwa sule kurciya,kurciyar data kawo rabuwarsa da muntarinsa,rabuwar da har yau fuskokinsu basu qara ganawa ba,duk da yadda muntarin keta nemansa ko ina loko da saqo na garinsu saidai babu labarinsa,tun da quruciya yake nemansa har girmansa,har yau yana kewar dan uwansa kuma amini shaqiqinsa sule saidai har yanzu Allah baisa an dace ba. 1

      Muntari yayi kuka yayi kuka har wasu ma suka tayashi kokawa,da qyar aka samo kansa,amma shima daina kiwon yayi ya haqura ya kama karatunsa gadan gadan,bayan rasuwar khadijatu mahaifiyar malam mamman kaka ga mukhtari baabaa prof,garin ya daina musu dadi baki dayansj,sai ya tattara ya koma cikin ainihin garin gombe inda dama kasuwancinsa ya riga yayi qarfi qwarai a can,ya saida dabbobin muntari saidai muntarin yaqi a saida wanda ya baiwa sule,ya samu fili daya na babansa ya zubasu ya maidashi kamar dan qaramin gidan gona yaci gaba da kiwata masa su,yayi alqawarin duk randa Allah ya sake hada fuskokinsu matuqar yana raye saiya cika wannan alqawari.

     A kasuwa mahammadu ya zuba kudin muntarin,suka ci gaba da juyawa tare,gefe guda kuma ga karatunsa bai fasa ba,kafin wani lokaci muntarin ya zama dan birni sosai,ya goge,ilimi ya ratsashi,ya zama saurayi wamda har ya kammala secondry dinsa ya soma jami’a.

       Kyau tsantsa irin na usilin fulani Allah ya baiwa mukhtar shi,tsantsar farin jini kamun kai kamala da kwarjini wanda shi ya janyo masa tarin masoya maza da mata,yana faran faran da son jama’a,’yammata kuwa ba’a cewa komai,duk da ‘yamata ne irin na da,masu tsananin kunya da kamun kai,da wuya kaji tace tana sonka,saidai ka gani a ayyukanta,a hakan ma ana ganin kansu ya bude suna jami’a,a jami’ar ma babu yawan matan,sabida har lokacin jama’a basu karbi karatun boko ba sam sai daidaiku.

        Zuwa lokaci dukiyarsu ta sake ninkuwa,irin dukiyar da a lokacin tsoro ma kake asan kana da ita saboda yawanta da rashin hanyoyin boyeta da sarrafata kamar a wannan zamanin,tuni malam muhammadu ya tashi daga malam ya koma alhaji,ya tamfatsa gida irin na masu kudin da,irin gidan da a da saidai gida na sarauta,mai sarautar ma wanda ya isa,kamar sarki ko waziri,gwamna ko shugaban qasa,tun mota da babur da handset sai wane da wane mukhtar yake hawa yake riqewa,arziqi ya zauna musu na ban mamaki,gefe guda bai fasa kiwata dabbobin sule ba,wadanda sukayi albarka suka zama hamshaqin gidan gona,wanda ke fidda kaji,madarar shanu,qwai,a kuma sarrafa yoghourt wanda yayi sunan ba gombe kawai ba har a arewa a wannan lokacin,duk abinda aka saida yana tara kudin a gu na daban yana ajjiyewa sule,har lokacin bai fasa nemansa ba,bai fidda ran kuma ganinsa ba,yakan ce IDAN DA RAI DA RABO.
Kaf qauyensu babu wanda baici arziqinsu ba,mutanen da suka kai maka Allah yayi yawa sa sh,tun a lokacin mai zuwa maka a jirgi sai wane da wane,hatta da mahaifin sule wanda altine ta yashe ta gudu ta barshi cikin tsananin talauci da yunwa,mkhtar ya fidda kudi cikin kudin sule ya biya masa hajji,kafin ya dawo aka buge gidan sa aka sake masa gini da ya dace da irin wancan zamanin,kuka ya dinga yi yana shiwa muntari albarka yana roqon Allah ya bayyana masa dansa,don hashimun ma ta gudu da shi baisan inda yake ba,sosai baban sulen yaci arziqinsa kafin Allah yayi masa rasuwa. +

       Muntari baabaa prof sun hadu da matarshi ta farkoZUWAIRIYYA wadda ake kira KILISHIa makaranta,a lokacin yana karatun degreed dinsa na biyu a jami’ar bayero dake kano,diya ce sarkin rano,yarinya ce mai kamun kai,miskilanci da haquri,akwai dan jin kai tattare da ita dan kadan wanda jinin sarauta dake yawo jikinta ya haddasa hakan,saidai akwai fada da tsiwa idan ka tabota,kusan abinda ya zama silar qulluwar alaqarta da mukhtar kenan,haduwarsu wajen cin abinci dake makaranta,sukayi fada daga qarshe ya nemota ya nemi soyayyarta,ta dan garashi sannan daga bisani ta amince ta yarda da aurensa,ba wani lokaci aka dauka ba kasancewar akwai sanayya tsakanin alhj muhammadu da mahaifin kilishi,saboda shahararsa a kasuwanci,zaka samu wani lokaci akwai alaqa ko abota tsakanin masu sarauta da ‘yan kasuwa.
       Babu bata lokaci akayi komai aka gama,alhj mahammadu ya danqarawa tilon dansa gida cikin kano da kudinsa da kansa a daura da jami’ar bayero,wanda a sannan ba unguwa bace face irin unguwannin nan marasa gidaje sabbin unguwanni,a nan suka tare cikin qauna da aminci da kula da juna,shi yana nashi karatun itama tana nata hankali kwance,da ya gama ya juya masters ita kuma data hada degree ta tsaya hakanan ta maida hankalinta kan kula da gidanta,macace data iya zaman aure,tsantsar kula da miji,iya tarairaya da nuna qauna,shekara uku da aurensu suka samu qaruwar d’a namiji,ba bata lokaci mukhtar baabaa prof ya sanya ma yaron sunan kakansa wato adam,shekara na zagayowa kilishi ta sake sambalo d’a namiji wanda C.S aka yi mata.

      Abinda basu taba gani ba wato alhj muhammadu yazo gidansu,da kansa wannan karon yazo ganin jariri bayan sallamarsu daga asibiti zuwa gida,tun a daren kilishi da adam ke kira ummee ta dinga dariya tana fadin lallai wannan yaro yayi goshi,sanda aljh ya daukeshi kallonshi ya dinga yi yana murmushi,yayi wata magana data sanyaya jikinsu ta kuma basu dariya
“Inama rai zai bani aron lokaci da rayuwa naga girman wannan yaro,ba shakka na tabbatar akwai wani lamari tattare da shi,shi na daban ne cikin yaran da nake gani,tun a daren da aka ciroshi jikina ya bani haka” kilishi da ta maida abun wasa dariya tayi
Alhj ya akai ka sani” da yake shi wasa yake musu tamkar jikokinsa,dariyar shima yayi
“Zaku ce na gaya muku,lokaci zai nuna,ba shakka shi MUSDAFA ne,zababbe ne”
“Shikenan baaba,ka sanya masa suna,dama sunanka nakeso na saka wannan karon,MUHAMMAD MUSTAPHA” yaji dadi qwarai a zuciyarsa,har ya gaza boyewa,ya daga mustapha yadinga masa addu’o’i,wasu cikin kunne wasu cikin baki wasu cikin ido,addu’o’i ne wadanda ko diyan cikinsa mukhtar bai masa su ba,yana son yaron,yana jinsa har cikin zuciyarsa,sosai ya roqa masa albarkar rayuwa duniya da lahira. +

       Mustapha bai cika wata ukuba duniya ba Allah ya yiwa alhj muhammad rasuwa,dan kasuwa mai gaskiya da amana,tausayi da taimako,kowa nashi ne,kowa cin arziqinsa yake,ba iyalansa kadai sukayi rashi ba hatta da kano da gombe baki daya,mukhtar ya dauko mahaifiyarsa ta dawo gidansa dake kano da zama,ya sake yiwa gombe nisa,abinda ya sake sakashi kenan ya rage zuwa gomve,sai yayi wata shida ko shekara baije ba,hakan ne ya sanya har sule yaje ya tafi basu hadu ba,sanda yaje aka gaya masa kamar zaiyu hauka,sai ya koma zuwa akai kai amma har ya gaji ya watsar sulen bai kuma dawowa ba,da alama har yanzu baqin abun da aka yi masa na cikin jikinsa.

      Nauyi sai ya sake yiwa mukhtar yawa,ga dukiyarsa ga wanda mahaifinsa ya bari aka raba musu,mahaifiyarsa ta dauki tata ta damqa masa,don bata da wani itama sama da dan nata,haka duka ya hada,ga karatu da ya kasa haquri ya bari saboda yadda yaji dadinsa,ga kasuwanci ya sakoshi gaba,bayan shekara biyar da haihuwar mustapha kilishi ta sake haihuwar ‘ya mace wadda taci sunan farida,zuwa lokacin sun fara ganin abinda alhj muhammadu ya fada akan mustaphan,ba shakka shi na daban ne tsakaninsa da dan uwansa,akwai banbance babance sosai,bayan haihuwarta ba dadewa itama innar mukhtar ra rasu tabi mijinta bata cika shekara ba aka haifi mai sunanta naja’atu suna kiranta da huda,haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu,ko yaushe arziqinsu bunqasa yake albarkacin taimako da suke yiwa bayin Allah da nemanta sa suka ci gaba da yi ta hanyar Allah. 4

        Mukhtar bai bar karatunsa ba sai da ya zama farfesa,a lokacinne suka hadu da ABDUS SAMAD wanda ya zame masa aboki,kusan bai qara amini tun bayan rasa sulensa da yayi sai a kan abdus samad,abdus samad na qaunar baabaa prof qwarai da gaske,a lokacin ya fara taba siyasa,ya shigeta da qafar dama,ko ince ya shigeta da gaskiya da amana,da magana daya tak idan ya fadeta,abinda yawancin ‘yan siyasarmu suka rasa,ba wani abu yake nema cikinta ba sabida babu abinda ya nema ya rasa a duniya,arziqin duniya da dukiya Allah riga da ya bashi saidai ya nemi na lahira,wanda yana amfani da dukiyarsa yana nema saidai Allah ya karba masa,ba takara ya tsaya ba,amma yana supporting gwanatin dake nema sabida yadda da yayi da ingancinta da,cikin ikon Allah kuwa ta samu nasara,hakanne ya sanya aka bashi matsayin AMBASSDOR jakadan nijeria a merica,sosai abdus samad yayi farinciki,don shima iyalinsa na can,matarshi daya alokacin hajiya khaulat,abinda ya zaunar da ita can acan abdus samad ya ganta ya aureta sabida mahaifinta pharmacist ne acan a wani asibiti yake aiki,,itakam tace ba zata bishi nijeria ba,tilas ya yadda ya aureta a can suka zauna a can,bai wani damu sosai ba,don shima acan yake nashi aikin irin ma surukinsa,damuwarsa kawai yaran da zai haifa kada su tashi da tarbiyyar can.
Gidan da abdus samad suke zaune me block biyu ne,hakan ya sanya yace muntari ya zauna a nan,amma yace a’ah,saidai abdus samad yazo su zauna qyatacce kuma yalwataccen gidan da gwamnatin tarayya ta bashi ya zauna iya wa’adin aikinsa,hakan suka tattaro suka dawo,duk da khaulat bata so ba,saboda macace mai tsananin izza girman kai da ji da kai,macace dake son taga kowa a qasanta ita ce a sama,hakan ya sanya jininsu yaqi haduwa da kilishi ummee,saboda sam bata da wulaqanci,barta da miskilancinta fada da rashin son raini,sam ta tsanu halayen khaulat,duk da yadda ita khaulat din ke maqale mata,saboda tasan daga babban gida ummeen take,bugu da qari girma ne da cinyewa a wajenta ace tana hulda da mace irin ummeen,mata a wajen ambassador muhammad mukhtar muhammad adam,kuma diyar gidan sarauta.

     Komawarsu america ummee bata saki tarbiyyar yaranta ba,basu fi shekara guda ba Allah ya hada baabaa prof da Bilkisu,yarinya mai tarbiyya hankali faran faran da jama’a,sanda ya zowa ummee da zancan tasi tayi bore,amma tilas ta haqura da mahaifinta ya tsawatar mata,yace a nijeria ma bilkisun zata zauna,sosaj khaulat taso zuga ummee,saidai ko kallo bata isheta ba,don jininsu bai gama haduwa ba,ita dinma tana da hankali,bata da shegen kishi da iskanci irin na ‘yammatan yanzu da zasu nemi tasarwa uwar gida hankali,tun kafin ta shigo ma sai suka fahimci juna,tana yawan kiran ummee a landline tasu suna gaisawa,tun ummin na basarwa har ta saki jiki,sai Allah yasa mata qaunar bilkisu har akayi auren,shekara guda ta haifi danta na fari mahmoud,baki daya suka je nijeria suna da yaranta baki daya,sukayi sati suka dawo.

        A lokacinne kaulat ta samu ciki,bata taba haihuwa ba,wannan ita ce haihuwar fari da zatayi,ita ta dakatar da haihuwar a cewarta bata da buqatarta a kusa,bayan wasu watanni ta haihu,ta haifi SU’AD,tun a sabitin tasa aka juyar da mahaifar,wannan wuya wai ba zata iya ba,da yake turawa ne ba ruwansu suka yi mata abinda take so. 4

          So da qaunar duniya ita ta dauka ta dorawa su’ad,yarinyar ta taso a sangarce,abinda take so shi take yi,babu kwaba babu hantara,kallon banza kayi mata sai ta saka ihu tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya sam tasu bata zo daya da yaran ummee ba musamman mustapha,miskilin yaro wanda jinin sarauta ke yawa a jikinsa kamar uwarsa tun yana da qananun shekaru,ko kallo yarinyar bata isheshi ba,idan tana gu bai zama,shu kadai ke iya bugunta ta haqura ta shanye bata kai qara ko ta tashi hankalin gidan ba,shi kadai ke hukuntata yadda yaga dama,hatta babanshi da shi yake hadata idan ta addabeshi,bala’in tsoronsa Allah ya dora mata da qulafucinsa,bai damu da ita ba amma idan ta wuni bata ganshi ba ta dinga binbini da tambotsan nemansa tana yiwa uwarta rigima,kota shigo wajen ummee ta liqe mata tana buga rigimarta,da ya shigo kuwa kallo daya zai mata ta shiga taitayinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *