QADDARAR SUMAYYAH
CHAPTER 3
Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali tare dajaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin ‘yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata itama ta samu nata rabon,ta dora da cewa “Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu dake,haka kema baki damu kanki ba,ci da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani” maganar sai ta bama sumayya dariya da kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.
Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan tace “Ya mukhtar” “Ya akayi sumy?” Ya fadi yana saurarenta.
Sai datajawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ta dubeshi,cikin nutsuwar nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani “Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta ba”,cikin rashin fahimta ya tambayeta ” da akayi me fa?”ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace “A ganina bai kamata ka dinga sa’insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutarda kai ba,a ganina auren nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa‘iza ta haihu sai an fara cewa danka kafin ace dan yaya yahanasu k0?” Ta dan sarara da maganar tana hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta. Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska “Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?”.
Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa kawai take ” na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba’a yi mata lefe ba?bayan haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk wanda yaga laifina k0 ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin”sai ta tashi daga saman kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kana ta fashe da kuka. Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yanajin bata can can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki daya zuwajikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin “Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min” sai da taja hanci kadan sannan tace “Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata”
“Shikenan an gama,sunci darajarki” sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace “Na gode”.
Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta ” Allah yayi miki albarka”ya fada yana sakinta “Amin ya mukhtar” ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa k0 yardarsa na tare da ta ubangiji.
Cike da farinciki ta koma cikin gidan saboda albarkar da yasa mata ta faranta mata,taci gaba da kintsa ragowar ayyukan da suka rage mata,bata jima da kammalawa ba ta zauna
tana hutawa wayarta ta dauki qara,da sauri ta daga ganin sunan abbanta na yawo bisa screen din wayar. Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa mata yana tambayarta gida da kuma mukhtar tace ai yama fita. “Mamanki ta gaya min mukhtar zai qara aure” “Eh abba malam”
“To ina fata ba zaki watsa mana qasa a ido ba,ba za kiyi watsi da tarbiyyarda muka baki ba” “In sha Allahu malam” “To Allah ubangiji ya albarkaceki ya albarkaci aurenki” daga haka ya dora mata da nasiha cikin hikima da ilimi,cike da fadar Allah da ma’aikinsa,hakan ba qaramin sake kwantar mata da hankali yayi ba,ya qare nasihar tasa da fadin
“Babu wani abu da kike buqata?” “Eh babu malam” ta fadi hakan saboda babu abinda mukhtar ya gaza da shi,don har kudin kashewa yakan qimanta ya bata,ya danganta da yanayin samun da yayi a kasuwa. “To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba k0 wajejen
satin sama,zan aiko abubakar (yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu” farinciki ya cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara hudu da aure mukhtal ya fitar dana aurenta na ainihi ya sauya mata su.
“Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri”
“Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin
gidanki” “Da yardar Allah malam” ta amsa masa daga haka sukayi sallama. Sosai malam yake son
sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi ma tabar gurin sanda malam din ke gaya mata,
ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa sai qannenta su hudu. Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha’i wa matasa da dattijan unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya da sha‘awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin qazamar rayuwar da mafi yawancin ‘yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.
To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren Sumayyan.
Da fari ‘yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa. Da fari sun karbi sumayyan a matsayin ‘ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda haryau suna bisa wannan bigire basu sauka daga kai ba Wannan kenan …..
Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.
A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da yace yana sha’awa hartana ta masa dariya wai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da budewa yana fadin “Yauwa amaryata kuma uwargida na” qeya tajuya masa tana turo baki “Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe” cikin sigar tsokana ya dan talle mata qeyar data turo masa
“Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi’!” Duk da tasan wasa yake sai ta juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake
“Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?” Bai so maganartayi tsayi don bata masa rai maganar take balle ita saboda haka yace “Haka ne” a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.
Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi “Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba” cikin son samun qarin bayani yace “Wanne irin shiri?,name?” “Banga wani sauyi ba agidan nan?” “Kamar wanne iri fa” ya sake tambayarta “Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar qasa kayi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba’a jima da yi masa fenti mai tsada ba fes yake
kamar yau akayi”. Banza yayi da ita kamar baiji ba harsai da ta qosa tace masa ” kanajina kuwa ya mukhtar?” “lnajinki kuma bazan yiba,ke wallahi azim kika sake yimin magana makamanciyar haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta qara gaba dama ba nina gayyatota ba,haba,dame kike so naji?”.sai ya miqe a fusace ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta. Jikinta ne yayi sanyi,tayi dana sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta lallashe shi.
Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar ‘yan yaranta duka suna gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake maqotansu,tace ya duba mata don Allah fararqasa kwano nawa zai isa dakin zuwa tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa ta qirgo ta bashi harda kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa yajiqa mata sannan ya tafi ta
masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.
Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai bilkisu,fatima,hauwa’u,khadija,aisha,ummi,asma’u sai nana ta gurinta ” maza kowa yaje gida ya cire kayanjikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti”cikin zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna. Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan la’asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.
cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa “Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske take‘dariya ta
qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin
” to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti shi yasa na siyo da kaina mukeyi ni da ‘ya’ya na”da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take mata tamkar mamanta tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.
kai maman naana ta dafe tana cewa “Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da jikinki,Allah ya shiryeku” ta fada tana dariya “To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse sai kunyi” murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin “AI’ kuwa mun gode” da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin ‘yan qananun mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba. Magana ba zata yiwu yau ba sumayya zan dawo gobe,tunda yau kun zama ‘yan qwadago yinin fenti kukayi” ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne masu kyau ingantattu na ‘ya’yan itatuwa data saba bata.
Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba tare da yace komai ba,qaunarta ke sake ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan haryau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zatayi da tun sanda yace ba zaiyi ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.
Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne ‘yan italy masu kyau da tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba’a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da yaran gidanta suka tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa a gwiwa ba yaje har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba’a barshi a baya ba,kayan kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thirter,sai ta dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar yadda yake al’adarta.
Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk ya cika sumayyan,ta fuskanci ita ‘yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa ba,
ba qaramin kyau dakinta ya sake yi ba sai ka rantse Itace amarya .
Hmm