QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 31

QADDARAR SUMAYYA






CHAPTER 31







Wuni nafisa tayi ta kasa sukuni da tausayin sumayya,a haka auwal ya dawo ya taddata,baki daya wani qaunarta na sake shigarta,haqiqa bata yi zaben tumun dare na aminiyar qwarai ba. +

Washegari da kanta taje gidan anty dije dauke da ledar mayuka da turarukan data siya matan,dariya sumayyan ta dinga tana kallon tarkacen kayan,ko ba’a fada mata ba tasan cewa sunfi qarfin mai rangwamen gata irinta,saboda zuwa yanzu kanta ya soma budewa,tana iya gane abu mai tsada,balle ta san nafisan sarai,komai nata designer ne,kuma komai nata a set dinsa take amfani da shi
“Wai kina nufin ni kike so na dinga amfani da wannan kayan?”
“Qwarai kuwa da wace?” Kai ta kada tana dariya
“So nake naga kin sauya sis,so nake naga kin fara sabuwar rayuwa” kai taci gaba da kadawa tana dubanta,kafin tace wani abu anty dije ta shigo dakin,kayan ta dinga dauka tana dubawa tana dariya
“Allah yasa a baki hadin kai”
“Idan ma taqi ina kallon fatarta zan gane,don sun tabbatar min suna da kyau,suna gyara fararen mata” itama ta fadi tana dariyan,godiya anty dije ta taya sumayya,sun jima suna hira kafin nafisan ta koma gida don dora abincin dare,don auwal baison take away idan ba lalura ba ta kama.

Anty dije ke jinjina tsadar kayan
“Bansan ya zata kaya ba idan kayan suka karbeki ba,suna da kyau amma akwai tsada” cewar anty dijen.

Kiran wayar daya shigo wayar sumayya ita ta katse hirar da sukeyi din,fuskar ta washe baki bude take fadin
“Amiran baabaa ce anty”
“Kice ina gaidata” inji anty dije tana miqewa don ficewa daga dakin ta fara jiyo hayaniyar minal da khalipha da alama rigima suke shi da ita
“Autan baabaa(haka take kiranta idan taso tsokanarta)”
“Mutanen uk,wai nikam yaushe zaku dawo,nifa na gaji wlh daga gida sai makaranta,ni daya kamar mayya,idan bakuyi wasa ba fa zaku ganni wlh na biyo sahu” dariya sumayya ta dinga yi ganij dududu watansu nawa ma da tahowa
“Kamar yaune fa zaki ga mun dawo din,yi haquri takwara” dariya sukayi baki daya sannan suka soma taba hira,amiran na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsu
“Amiran umman khalipha,baabaa fa ya karbi kudin aurena har da sa rana watanni shida masu zuwa dai dai sanda zan kammala degree dina” ta fada cikin nuna farinciki,cikn zumudi sumayyan tace
“Kai haba dai takwara”
“Wallahi amira,amma nikam tsoron yin auren nan nakeji takwara,duk da saifullahi na matuqar sona da qaunata,hakanan na amince da tarbiyya da halayyarsa” gefe daya na zuciyar sumayya itama jimamin da take mata kenan,saidai ba lallai abinda ya samu dan uwanka kaima ya sameka ba,kowa da tashi kalar qaddarar,bare amiran ita ba mai mata zata aura ba,ita daya ce a gunsa
“Meye wani abun tsoro?misali su ummee da sukayi auren su wani abu kika ga ya samesu?” Kai ta kada kamar tana kusa da ita
“Um um,kawai banson rabuwa ne da gida,ina son family na”
“Ba shakka familynki abunda zaka yi marmari da begensu ne idan ka barsu,duk wanda ya kalli yadda kuke son juna ba zaiyi mamakin haka ba” sumayya ta zantawa ranta,amma afili sai ta bagarar da zancan da nuna rashun muhimmancinsa
“Duk mace ‘yar wani gidan ce,ko su su ummeen ce miki akayi gidanku ne gidansu,suna nasu familyn fa suka baro ko?” Sai amiran ta qyalqyale da dariya
“Kinji umme tace ah to,ashe taji me kika fadi,kinsan abinda anty maamaa ta gama gayan kenan dazu” itama dariyan tayi,ta shiga tsokanar amiran
“Kawai kice mu fara shirin baki,ina ga ba zamu wuce wata guda da dawowa ba zamu shiga hidima,ummm,bari na gayawa anty dije mu fara taru”
“Ahto,don kune amarori,shi yasa na dage saidai asanya wata shidan,daa qasa da haka za’a saka,nasan kafin sannan kun dawo”ci gaba da tsokanarta sumayya tayi a haka suka rabu cikin barkwanci. +

Bayan ta aje wayar ta samu anty dije na sauyawa minal kaya da alamu bata wadancan tayi don ba’a jima da yi mata wanka ba
” nikam saura qiris na sauya qawa,wannan qawa tawa qazamiya ce”sumayya tayu maganar tana duban minal tare da yamutse fuska
“Yadai fi wallahi,duk gidan nan babu mai bata kaya kamar nata”inji anty dije,fuska ta kyabe tana shirin sakin kuka
” na daina anty,wayyo Allah na”ta fada tana bubbuga qafafunta zata hau bori
“To shikenan,ya isa,ai ke qawata ce ta amana,babu mai rabamu,uwata ce fa ta kaina” sai ta soma dariya tana tsallen murna sumayya na dubabta tana murmushi,duk yaron data gani tuna mata yake da abdallahnta,dauke kanta tayi ta maida ga anty dije
“Anty an sanya bikin amira fa,wata shida mai zuwa” sakin maballin da take ballewa minal tayi dama ta kusa gamawa ta juyo tana duban sumayya
“Tabdijan,kice akwai gangami kenan,bikin auta guda?,bikin amira ni ‘yasu?” Antyn ta fada cikin jinjina lamarin,kai sumayya ta gyafa tana nade qafafunta saman gado tana murmushi
“Jar uba,kice abuja zata motsa,familyn baabaa prof za’ayi bikin da aka jima ba’ayi kamarsa ba,to ai ina ga da na su mahmoud za’a hada tunda suma wata bakwai ne inaga yayi saura cikin ranar auren da aka sanya musu ko,Allah ya nuna mana,sai mu fara shiri tun yanzu,sumayya kuna da biki” inji anty tana murmushu gami da jinjina kai
kai
“Wallahi anty haka tace,ni kam mai zan iya cikin hidimar,ni da ban taba bikin qawa ba?”
“Aikuwa dole ki ware ayi komai da ke,yadda amira ta daukeki kada kuce zaki watsa mata qasa a ido,nasan halayyarki sarai” dariya sumayya tayi ganin yadda antyn ta camfata tana kwantar da kanta saman filo
“Allah ya bamu iko to anty” kan ta gama rufe bakinta kira ya shigo wayarta,lambar alqasim ne,tana mamaki da har yau bai rabu da ita ba,bayan ta zayyana masa ita din bazawara ce har da yaro,sai ta latse wayar ta kasheta baki daya tana jan qaramin tsaki ta gyara kwanciyarta abunta,ita yanzun babu mai daga mata hankali,ko lukman idan ya kira sai taga damar dagawa,darajar yaranshi dake sonta kawai take dubawa,badur rahman je kadai ke da wannan qinar na daga kiransa a duk yayin da ya kira din. +
Cikin qanqanin lokaci da fara amfaninta da mayukan da sabulan taga banbanci,ita a karan kanta taga sauyi,wani laushi da santsi fatarta ke sake yi tamkar wadda ke zuwa gyaran jiki,baki daya qamshin jikinta ya sauya zuwa wani qamshi na musamman ma daban wanda ya kama kayanta sabida turaren da take amfani da shi set na man da sabulun,cikin watannin da basu gaza biyu ba sumayya ta sake komawa wata ta daban,komai nata ya sauya,sau tari laila na tononta tana cewa
“Wlh anty sumayya kin koma ‘yar gayu” hakan ya yiwa nafisa dadi qwarai a ranta,bisa dukkan alamu zata cimma qudurinta cikin sauqi kan sumayyan,tana son sumayyan ta zama wani sashe na familynsu,dukkanin halayyarta sun mata babu na yarwa. 8

******* ******* ********

Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta taba aure,’yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.

     Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala makarantar koyon girki da mu’amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a yanzu kusan anty dije ta zama ‘yar kallo ta fannin 
annin kitchen,kowacce rana da kalar abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi suje suyi siyayyan kayan da za’a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce ‘yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar ‘yar gari ce a garin,ranar haka zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu. +

*******     ********    *******

     Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.

      Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha’awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.

       Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance
“Hey!” Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen.
Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta
“Waye wannan sumayya?” Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa
“Nima ban sanshi ba” ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba
“Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?”
“Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba”
“Ala kyauta” nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame. +

        Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba. 1

  *******  ******   ********

         Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa’adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura.

        Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare.

       Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana
tsokana
“Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za’ayi ne?” Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace
“Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum”
“Amin” cewar anty dije. +

       Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba.

         Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al’adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu. 2
Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala.
Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa ba
“Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota” cewar khalipha wanda shi daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan
“Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?”
“Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?” Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata
“Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za’ayi ki bace wajen da duka ko ina cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?” Ta rufe maganar tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar tambayar
“Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata” laila sau ta sanya dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer da akeyi
“Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda za’a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan adam” dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a wuya,ita za’a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi. +

        Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a gift din biki
“Anty,banfa daukawa amira komai ba”
“To me za’a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace”
“To” ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a qirjinta.

        Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu dogaye da za’a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya mayya tayi,karamcin nafisa ya girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta
“Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci darajanki sister”, anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu’ar kade fitina,cikin kaya suka shirya kwalaben yadda ba zasu fashe ba.
+

*********   ******   ********

    Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta soma masa qwalla,khalid kuwa ba’a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya auwal ne ya janyeta yana rarrashinta
“Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki” da qyar ta tsaya sukayi sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu.Mamaki ne ya kama sumayya ganin su a VIP wannan karon,tasan dai ba’a VIP din suka zo ba,sai tayi zaton ko daga gwamnatin tarayyar ne,abinda ta lura kuma da shi shine iya su kadai ne,baki ta tabe don batasan meke faruwa ba ta fiddo wani littafi da nafisan ta bata ta fara duba shafin da take,don son bata sha’awar yin hira yau,kewar zulaiha da nafisa take,ba shakka sabo turken wawa,karatun ya soma yi mata dadi,yayin da wani qamshi mai taushi ya dinga shiga hancinta,qamshin yayi mata,sai ta lumshe ido tana jin yadda ke ratsa qofofin hancinta,sai tayi tsammanin wani abun ne a cikin jirgin,lol
“Barka da dare uncle” taji su laila na fada,cikin mamakin yadda lailan mai shegen rawar kai da surutu ke magana a kintse ya sanyata ajiye littafin ta dago kai da niyyar tsokanarta,so tayi tace
“Allah ya nuna mana ma’aiki yau laila ke magana cikin nutsuwa irin haka?”sai maganar ta maqale mata,zaune yake kujerar dake bayanta wadda ke daura da mazaunin uncle farouq,magana suke qasa qasa da uncle farouq din,idanu suka hadu,da hanzari ta juya ta maida idanuwanta mazaunin gabanta,qirjinta na bugawa da sauri,ta rasa wannan wace iriyar masifa ce haka,ba dama ta ganshi yanayinta ya burkice,anya ma ba maye bane wannan mutumin,sanye yake da fararen suit qal wadanda suka dace da takalminsa,yayi kyau cika da wani irin kwarjini,bata san me ya shigo da shi jirgin da zashi nijeria ba,idan bata manta ba anty dije ta gaya mata gun aikinsa na dubai
dubai
” matsa man sumayya,ina ta magana tun dazun kamar wata kurma”anty dije ta fada tana tsaye kanta,jiki babu qwari ta matsa din anty dijen ta zauna tana bude zip din jakarta tace
“Kun gaisa da mustapha ne?,wannan karon zashi nijeria ba lokacin zuwansa ba,nasan baabaa zaiji dadi,dan gaban goshi zaizo,diyar ambassador din nijer anan ya dubawa aikin da yayi mata a dubai,baban nata abikin baaba prof ne sun taba aiki tare” kanta kawai ta kada ba tare data iya amsawa ba,bata ma ga mai ya hadata da wannan sharhin ba,giyar qaunar ahalin baabaa ta kama su anty dijen sosai,ko da yake babu abinda KARAMCI baya iya maida maka mutum ta raya a qasan zuciyarta
“Kinga muma yau mun dana,gamu a VIP,mustapha yayi abinda ya saba” ta fada tana dariya tare da qoqarin kashe wayarta,duk maganar da anty dijen keyi bata fahimtarta,zaune take kurum,ta rasa abinda yasa jikinta sam baison hada inuwa daya da shi,ta tabbatar da cewa taqi jininsa ne tun ranar da ya yarfa ta gaban tarin jama’a,har yanzu tana iya jin zafin abunda yayi mata,baka san waye mutum ba,bakasan wanne yana yi yake ciki ba amma kayi masa haka amatsayinshi na dam adam irinka?,itakam jin anty dije kawai da take yaba kyawun halayensa,eh,ta yadda da mutunci da karamcin ahalinsu amma bata jin shi yana ciki. +

        Laila ta sake taimakawa wajen dagula lissafinta data nace da tabata kan sai ta juyo taga abinda take nuna mata cikin laptop dinta
“Idan ba zaki iya kalla ke daya ba zan karbi abata kinji ko?” Hakan data gaya mata shi ya sanya ta sarara mata.

     Mintuna arba’in kowa ya nutsu a kujerarsa yana abinda zai fishsheshi,duk yadda ta kai ga matse fitsarin da take ji amma yaqi sarara mata,ta fuskanci ya zame mata dole tayi,ko kusa bata son tashi daga inda take,saboda matsawar zata shiga bandakin tofa sai ta gifta ta kusa da su,a hankali ta waiwaya sai taga baki daya ya aza hankalinsa ga system,hakan ya bata qwarin gwiwa ta miqe anty dije ta matsa mata ta wuce,cikin sanda kamar wata barauniya haka ta wuce,baima san da wucewar wani a gun ba har ta gama fitsarin ta dawo.

        Daidai lokacin da yake magana da uncle farouq cikin nutsuwa,muryarsa ta shiga dodon kunnuwanta,ya salam,muryar mukhtar take ji muraran cikin tashi muryaf,ya ilahi wannan kamanceceniyar murya dame tayi kama?,ta tabbata abinda take ji yana da nasaba da muryar mukhtar dinta wanda ko wanne lokaci yayi magana tuna mata da shi yaje,ji take kamar shine a raye a kusa da ita,har marmari take taji ya furta wani abu.

        Dumi da taji yana ratsa rigarta da qarar fasgewar cup shi ya ankarar da ita karo da tayi da daya daga cikin ‘yammatan ma’aikatan dake kara kainam baiwa kowanne passinger abinda yake da buqatar ci ko sha,baya tayi jikinta na rawa yayin da itama budurwar tayi baya tana baiwa sumayyan haquri cikin harshen nasara,a qa’ida sumayyan ke da laifi,saboda tayi qoqarin kauce mata amma sai data bugeta,iya tafi da custumer nasu ya sanya take bata haquri tare da bata hanya ta wuce ko kuma ta koma toilet ta wanke hadaddiyar doguwar rigar shadda dake jikinta wadda sabuwa ce kar ranar ta soma sanyata,lemon green da aka yiwa adon orange,mayafin data nannada saman kanta shima orange ne,ba tare da wani dogon tunani ba ta wuce zuwa mazauninta sabida ta kasa tantance me ya kamata ma tayi.
Qarasawa tayi dauke farantin da pieces glasses din cup din tana baiwa mustapha haqurin bari ta sake kawo masa wani,sai a sannan ya daga kansa daga abinda yake yi din,kallon da yayi mata ya rudata,sai ta fara yi masa bayanin ta kawo ne sukayi karo da madam ya zube,da hannu ya tsaidata yace taje kawai bai buqata,haquri ta bashi sannan ta juya,ya fahimci me ya faru,don yana iya jiyi anty dije na tambayar bata qone ko taji ciwo ba ko?,tsaki yaja qasan ranshi yana ayyana anya tana da lafiyan qwaqwalwa kuwa,haduwarsu ta farko ya tuna,sannan ya gangaro haduwarsu ta biyu,haduwarsu a mall da girmanta tana wani hawaye shabe shabe kamar ‘yar yaye,sai kuma yau,yaso tambayar alhj farouq sai kuma ya tuna ba abunda ya shafeshi bane yaci gaba da harkansa,amma ya barwa ransa akwai wani abu a qwaqwalwarta don bai taba ganinta a nutse ba.
1Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya
“Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi” dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta tana gintse dariyar. +

          Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za’a shige da shi cikin gida ne tunda su zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon tuhuma
“Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa”
“Bab….babu komai,qafata ce ta harde” bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab suka jera zuwa cikin gidan
“Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata” da sauri ta dubi anty dijen,ya akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka qarasa cikin gidan. 9

       Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?.Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban
“Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya” kamar mai jira sai taji qwalla ta cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen
“Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina so ki sauya kanki ne” da sauri ta tareta
“Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni” tausayin sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi
“Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane saboda yayi ne cikin rashin sani……ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine mukhtar ba….any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan da kike shiryawa a jaka?” Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi
“Kano nake so gobe na tafi” idanu ta zaro
“Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?” Marairaice wa tayi
“Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa ‘yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?”
“To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam”
“Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed him alort anty,shima kuma nasan haka ne” kama baki tayi taja dariya
“Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki gaskiya ne” kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta
“Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda kayan su malam” duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya da ita haka ta amsa mata da to. 

       Misalin uku na rana suna zaune suna cin abincin rana amira ta shigo,bisa dukkan alamu daga makaranta take,don ga handout nan a hannunta da key din motarta,wani daj ihun farinciki ta saki tana qarasowa kusa da sumayya,gaisawa sukayi da anty dije tana tsatstsokanar su laila khalipha da minal,baki daya tace sun sauya,lallai garin ya karbesu,sai ta maida dubanta ga sumayya
Umman khalipha wai wannan amiran umman khalipha ce ko wata kuka samo a can?” Dariya suka saki baki daya kowa ya gane me take nufi,cikin salon zolaya itama sumayyan tace
“Sun baro waccar a can,wannan musanyota sukayi” dukan cinyar sumayyan amira tayi tana fadin
“Kina kallon mudubi kuwa?,wallahi kin bala’in zama wata queen namesake,ni zan fara yiwa alqasim wannan albishir din” harara ta aika mata tana murmushi
“Ban aikeki ba,bismillah sa hannu muci abinci” idanuwanta ta maida kan abincin wanda saura duk da miya suke ci banda ita,fara da man take jin ci don an dade ba’a hadu ba
“Wai wai,an kuwa zanci,shinkafa da wake da manja ne da yaji ko?,ga kuma salad,rabona da abincin nan da dewa,ina son fara da mai da yaji,su kam saidai suyi miya,musamman idan waccan baturiyar tazo,bama tasan fara da mai ba,idan taga wani yana ci har kyabe baki take wai muna cin abinci gaya” ta fada itama tana tabe baki,murmushi anty dije tayi
“Dan gidanku yayarki ce dai,kuma kinsan baki isa ku fadi ba gaban maigidanta” amsa mata ta soma bayan tayi cokali daya
“Me ruwa na da su,shima shi yaga zaya iya,haka kawai mutum bashi da maraba da gauro,kowa yana ci gaba ta fuskan family amma banda shi,haka kawai jiya har na kwanta ya tada ni wai na hada mishi fruit salad baturen kawai ga abinci ba zaya ci ba wai yayi masa nauyi”
“Ke amira,zakici gidanku,ba yayanki bane?” Saki tabe fuska tayi kakar zata saki kuka
“Ni umman khalipha bama wannan bane ya qonan raj,Allah anty su’adah ‘yar rainin sense ce,na shiga kai mishi naji suna waya,ta baro america ta biyoshi dubai wai bata tadda shi,yace bai nan yana naija wai gobe zata biyoshi,wannam ai ba matar aure bace matar yawo ce,kuma kowa yw zuba mishi idanu wai matarshi ce haka suka tsara rayuwansu,to wallahi aure zamu masa” baki daya ta basu dariya saboda salon yadda tayi maganar bilhaqqi,har sumayya na qwarewa sai data kurbi ruwa
“To ba sai ki masa ba tunda kece gaba da shi,kijimim tsaurin ido,musty zaki ma aure?,yo ko adam ai bai usa yace zaya yi masa aure ba bare ke” tsaki sumayya ta ja bayan ta samu tarin ya tsaya tana dan dukan cinyar amiran
“Kinga malama,ki dinga maganar da zata amfanemu,juyo muci abinci” waiwayowa tayi tana duban sumayya
“Uhmmmm,wallahi kuwa,don wannan babu ranar sauyawarsu” sai tayi qasa qasa da murya
“Kefa kawai nake jira ki dawo a fara tsara mai yiwuwa,jibi za’a kawo lefe fa,kuma da sati uku zasu zo kwanakin bikin”
bikin”
“Komai kika tsara dai dai ne,amma ni jibin zan wuce kano” idanu ta zaro tana tsaida cin abincin da take
“Me kika fada namesake,ina ce miki jibi kawo lefe kina cemin jibi zaki tafi kano,a satin nan fa zamu je dubai siyo kayan kitchen,tare da ya musty zamu koma,shigowar nan da nayi passport naki nazo karba za’a buga mana visa” cabdi,wane musty din,mustaphansu?,ta godewa Allah da ya bata idea din tafiya kano,don ko ana yankan jikinta ba zata bisu ba,wannan dan jin kan?,dan wulaqancin dan rainin wayo?
“Kice wani abu mana kinyi shiru,duk kin rusan plan,wallahi idan baki je ba da wannan matar tashi zaya hadanu siyan kayan kitchen,bayan babu abinda tasan amfaninsa a kitchen saidai ta ganshi da ido,sai shegen izza da dagawa,zata siya min kayan shirme ne masu dan banzar tsada tana ganin kudin mijinta ne,kamar an gaya mata shi mai kudi baisan ciwo da zafinsu ba” ajiyar zuciya ta saki
“Banji dadi bane amira,amma zuwa kano ya zame min dole jibi,malam na son ganina” ta hada da qarya,sai anty dije tayi saurin tashi ta doshi kitchen don kada amira ta roqeta ta hana sumayyan zuwa,don qaryan sumayyan ta mata dai dai,koda tana abuja ba zata barta taje ba,don ta fuskanci inuwa daya bata zaunuwa tsakanin sumayyan da shi uban gayyar,bare tafiya ma wata uwa duniya babu muharramin sumayyan ba zata yarda tayi ta ba. +

        Shuru amira tayi wanda hakan ke gwada baki daya bata ji dadi ba,jikinta a sanyaye taci gaba da cin abincin,sai da daqiqa kusan biyar ta shude sannan ta iya cewa
“Malam yafi gaban komai amira,sai kin dawo Allah ya kiyaye,amma don Allah ki dawo da wuri,sannan kimin alqawari zaki shiga ayi komai da ke,zaki dauki kanki kamar diyar baabaa,wallahu tun wancan satin baabaa ke tsokanata,wai idan baki dawo ba baisan ya zanyi ba,qila saidai ya daga bikin ko?” Murmushi tayi,alqawarin yayi mata girma da yawa,amma tilas ta dauka,anayi da kai yafi ba’a yi da kai,masoyinka kuma yafi maqiyinka
“Kada ki damu,nayi alqawari in sha Allah”
“Amma kafin ki wuce zaki shigo ki gaida su ummee,daga nan kiga ankon da aka fitar ko,ku hudu amma kalar naku daban,ke da qawaye na su uku”
“Me zai hana,in sha Allah” ta fada kawai din a wuce gun,amma mai zai kaita gidan a irin wannan lokacin da wannan mutumin ke qasar,daga haka ta ware suka ci gaba da hirarsu.
********  ********   ******** +

    Tun dare ta kasa bacci,gani take kamar gari bazai waye ba,bata ji kwanciyar hankali ba sai data ganta a mota sun dauki hanya,babu wanda ta gayawa tana zuwa don so take tayi masu ba zata.

       Qarfe daya da minti ashirin na azahar a qofar gida tayi musu kasancewar sun fito ne da wuri,ita ta fara shiga kafin driver din su anty dijen ya soma shiga mata da akwatunta da qatuwar jakar dake dauke da kayan tsaraba.

        Halima ce a kitchen,mama na bakin fanfo tana daura alwalar sallar azahar,yayin da zainab ke mopping falon mama wanda ta dage labulensa,hakimin abdallah na kwance abinsa saman kujera yana kallon cartoon,zainab na mopping din tana mitar ya hanasu kallon kowacce tasha sai ta ‘yan aljanu,mama na fadin ai yafi,sunfi son suyita kallon waqe waqe da raye rayen banzan nan da wofi. 1

       Tana sallamar halima ta saki kwashe miyar da takeyi ta fito,zainab ta saki mopper,yayin da mama tayi tsaye tana dubanta tare da amsa mata sallamar fuskarta dauke da madaukakin murmushi,kusan a tare suja ruqunqumeta suna ambatar sunanta,dadi ya cika kowannansu,sam abdallah bai fahimci me ake ba sai da suka shigo falon,dirowa yayi daga kan kujerar yayi kan sumayya yana kiran
“Mamiiiiiiii naaaaaaa” baki daya ya cukuikuyeta kamar zai shige jikinta,itama tsam ta rungumeshi tana dariya farinciki fal zuciyarta kamar an wanketa da ruwan qanqara.

      Baki daya sun baibayeta,idanuwanta na kam abdallah,photocopy na mukhtar take kalla,cikin shekara guda tal ya sake wani girma da wayo na ban mamaki,ya fara zama dan saurayi,shekara kusan biyar ba wasa bace,girman dan mutum babu wuya,duba daya ya wadatar da kai ka gane yaron na samun gata da kulawa,don suturar jikinsa ma kadai amsa ce,zainab da halima kowa da abinda zai fadi
“Yaya sumayya kin ganki kuwa?,kamar irin hajiyoyin nan”
“Yaya sumayya kin zama budurwa wallahi,irin ‘yammatan abujan nan,gaskiya tafiyan nan ta karbeki,kaman an canjoki baki daya” dariya take ta rasa abin cewa,tunda ta sauko daga mota ta lura da kallon da jama’ar unguwar tasu ke mata wasu ma kamar basu ganeta ba,haka su halina suka cikata da surutu har sai da mama ta korasu halima taje ta zubo abinci ta kaima driver a waje din da yayi salla zai koma,sannan ta zubowa sumayyan ma, zainab kuma ta kai mata kayan daki,sai bayan fitarsu sannan suka ji kunnuwansu,abdallah na maqale jikinta yana ta bare choculets yana gama musu aiki.

       Haka suka wuni ba wanda ya fita a gidan,sai maqota dake shigowa jifa jifa yi mata sannu da zuwa,wanda wasunsu labarin yadda sumayyar ta koma suka ji suka zo ganewa idanuwansu.

      Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki
“Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni”
“Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake matarsa ta haihu)”
“Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba”, malam ne kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu’ar katari da miji na gari ita da ‘yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje ta kwanta.

********  ********   *******
Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi
“tunda gaki Allah ya dawo dake auren ‘yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu” murmushi tayi ta dan sadda kai a zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan?
“Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi”
“Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin mijinta,shine cikakken mutuncin ‘ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai muyita addu’a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi haquri ka kuma nemi lada a wajensa”
“Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi” kai ta sunkuyar,jikinta yayi sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa. +
 Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu.

       Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har tazo,dariya ta saki tana dubanta
“Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki”
“Ina zakiji ‘yar gaban goshin malam” zainab tayi caraf ta karbe
“Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce” karyar da wuya amina tayi
“Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?”
“gaya musu dau matar yaya” ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara’a tana cewa
“Ga babbar jika,ga babbar jika a mata” yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin gidansu sumayya.

       Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka
“Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?” Dariya ta saki
“Haka kowa ke fada anty”
“Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na yarda kinfi abban yusra kyau” dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama.

   *******   ******   ******
Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman yayi mata. +

      Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya cikin mintuna arba’in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka sallameshi suka nufi gidan. 2

        Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin
“Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja” kallon mamaki sumayya ke masa kafin ta maida dubanta ga halima
“Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?” Murmushi halima tayi
“Me zai hana,yaron dake wuni a gidan” shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga gidan.

      Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara’a takewa sumayya sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data ja abdallah jikinta tana fadin
“Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi” murmushi sumayyan tayi a aladabce
“Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen”
“Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama” ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata ta sadda kai
“Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa”
“Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?” Kai ta kada tana fadin
“Eh,lafiya qalau suna gaisheku”
“To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama abinci”
“Halan bata da lafiya ne hajiya?” Sumayya ta tambaya tana duban bahijja
“Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta ina lafiya zata samu”
“Gaskiya kam” sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai yawa tattare da su.

        Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa
“Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?” Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima
Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba” Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen
“Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo”
“Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka” dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace
“Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku” kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi. +

      Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci.

      Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa.

        Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta
“Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata” abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata
“Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida” karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota.

      Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja murfin ta rufe
“Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?” Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane.
Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa masa gorar tana masa godiya
“Ai yiwa kaine” ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi. +

        Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta tanka
“Kada fa ka cinyeni”
“Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa” kunya kalamansa suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi
“Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji ‘yan magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za’a bude asibiti,ya muke ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki”
“Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara” ta fada tana dariya qasa qasa
“Kada ki yimin haka sumayya” ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun
“Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za’a kammala bikin zainab,na tabbata idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace” hannunshi ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki
“Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a dakina”ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a dakinsa sai kace wani mace
“Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi”
“Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya abbakaf,ki turon bahijja” ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin farinciki na ratsashi.
Sosai wannan karon zaman kano yayi mata dadi,har vata so ta tuna zata koma abuja,tayi ziyara gidajen ‘yan uwan mamanta,kowa yaji dadin ganinta. +

        Ranar bude asibitin abdur rahman kuwa baki daya ‘yan gidan sunje,maama kawai suka bari a gida,sosai asibitin yayi kyau,duk da yake ba wani girma gareshi ba,kamar wajen bada magani ne amma na islama wato islamic medicine center,amma akwai dakuna guda goma masu dauke da gadaje saboda halin lalura da za’a iya kawo mutum ciki,yaso sumayyan ta tsaya su wuce gida sabida akwai walima daga nan sai ya dawo da su amma taqi saboda yana cikin jama’a masu tayashi murna bai kammala sallamarsu ba,bugu da qari tana kunyar hajiya kada suje tare yayi wani abu da zai fallasa su,a gurguje taje ta yima hajiya da kawu murna suka koma gida.

       Ko da yazo ya taras ta tafi sai da ya kirata yayi mata qorafi,dariya kawai tayi ta bashi uziri,yace ya haqura amma da sharadin zata rakashi randa zai fara zama office dinsa,binshi tayi da to don samun mafita ba don zata din ba.

        Sosai ta miqe qafa abunta,gida yayi mata dadi,wani lokaci tana gida wani lokaci tana gidan ya abubakar amina ke dauke ta,a irin hakan wani weekend abubakar din ya zauna gida bai fita,lissafi ya zauna ya yiwa sumayya na kudadensu,ita kanta tayi mamakin yadda kudin keta ci gaba yana habaka,kada ma na Abdallah yaji labari,tasan hakan kuwa baya rasa nasaba da kyakkyawan ruqo da abubakar ya yiwa dukiyar tasu
“Na gode yaya abubakar,Allah ya qara zumunci ya raya maka zuriyarka”
“Haba sumayya,ai dukiyar maraya da mutane sunsan bala’in dake ciki da basu taba ta ba,ko kin manta cewa Allah S W T yake cewa ‘haqiqa wadanda suke cin dukiyar maraya da zalunci(barna da mugunta)haqiqa suna cin wuta ne a cikinsu,da sannu zasu shiga wutar sa’ira,duk mai hankali babu abinda zai kaishi afkawa wanann babbaf musibar,bare ke da kike ‘yar uwata,idan banyi miki ba wa zan yiwa” kai take gyadawa cike da gamsuwa
“Gaskiya ne,Allah ya sa mu dace”
“Amin” ya fada yana qwalawa amina kira wadda tunda taga zasuyi magana ta basu guri,babu yadda sumayyan batayi ta zauna ba taqi. 1

       Cikin kudaden da sukayi lissafi an fidda riba mai yawan gaske wadda take ta shekara daya,ta raba ta kashi biyar,daya ta baiwa mama,daya ta baiwa malam,daya ta ajjiye a hannunta zata yiwa zainab siyayyan kayan kallo,plasma t.v,d.v.d,home thierther don sauran daidaikun kayan kitchen,don su kadai suka rage,tuni ya abubakar ya kammala siyan komai,daya kuma ta baiwa ya abubakar,zata kashewa abdallah sauran kason duk da babu abinda ya rasa,qememe suka qi amsa baki dayansu suka maida mata kudin,don su a ganinsu itace abar atallafa maga,sai data yiwa malam qwalla tace albarka take nema sannan ya amshi na gunsa yace zai bawa maman nata a ciki,ya abubakar ma biyu ya raba ya dauki rabi suka dawo mata da saura,itakam bata san me zata yi da su ba sukaje uta bata da buqata,itama ta 
kashe,murmushi tayi donbita kam bata da matsalar komai,sutura harda sababbi wadanda bata taba sanyawa ba tana da su,abinci da abunsha ma sai wanda ta zaba,ya abbakar ta fadawa yace zai bude mata accnt kafin ta tafi ta karbi atm din,hakan yayi mata ta sake yi masa godiya,babu abinda zata ce da Allah sai godiya,ya bata iyaye da ‘yan uwa masu sonta. +

        Wani abu ta cira cikin kudin ta baiwa ya abbakar taje waya take so guda biyu,kwana biyu tsakani kuwa sai gashi da manyan wayoyi masu bala’in kyau,saidai sun danci kudi,ta bare dayar ta jona a caji ta barwa mama ta hannunta,ba wani jimawa tayi ba uncle farouq ne ya sauya mata ita kafin su tafi,dayar kuma ta ajjiye da niyyar ta kaiwa anty dije tsarabar kano.

          Satin ta biyu a kano amira ta soma matsanta mata da waya,murmushi tayi
“Ina nan tafe nan da wani satin,ina cewa saura sati biyu dai ko?”
“Zamuje gombe,zanyi sati daya,gaskiya ki tabbatar sister kin dawo din cikin satin nan,Allah baki daya plan dina ya rushe,nafison naga komai kina kusa,komai ni baya min yadda nakeso,nasan da kina kusa abin sai yafi haka,kinga rashin zuwanki dubai wlh har kusan fada mukayi da anty su’ad,baki ga tarkacen da taso hadomin ba kawai abu idan ya burgeta a ido ko bata san amfaninsa ba sai tace a dauko,sai da na botsare mata nace bana so,harda hadani da ya man yace ta barni ja zabi abinda nakeso,tunda na fita sanin muhimmancin kayan kitchen” sosai ta bawa sumayya dariya,idan tana wani abun kamar qaramar yarinya
“Shikenan,zanyi qoqari na dawo insha Allah,gida ne akwai dadi wallahi”
“Na sani,amma pls sister kiyi qoqari don Allah”
“Insha Allah” da haka suka rabu
**    ******     *******

        Sosai kano ta riqeta,don har aka cinye satin bata samu ta tafi ba,ko kaya ma bata soma hadawa ba,bata qi ita ta shekara ba a haka,ranar juma’a da daddare tana kwance falon mama suna hira,mama zainab halima da ita,wayarta dake hannun zainab wadda ke bude mata watsapp instagram da wattpad,ta rantse sai sumayyan tayi,ta gaya mata idan ta fara zata bata labari,kira ne ya shigo hakan ya sanyata ta miqe ta miqa mata tana fadin
fadin
“Anty amira ce” tashi tayi daga kwanciyar tana dariya,tun kan ta daga wayar tasan me zata fadi
“Tom,mr qorafi,yau an shiga uku”
“Kema idan da gaskiya ai bai kamata ace baki koma ba,duk nacin da yarinyar nan ke miki,ina cewa dududu bikin ranar laraba za’a fara ko”
“Wallahi mama gida dadi banson tafiya”
“Ai shikenan” maman ta fada tana ci gaba da gyara carbinta da ya tsinke,kasancewar kiran har ya katse ya sanya sumayya saurin bin kiran. +

      “Yanzu sis kin kyauta min kenan fisabilillahi” abinda ta soma fada kenan muryarta na rawa kamar zata saki kuka
“Ayyah,afuwa mana namesake don Allah……”
“Babu abindq zaki gayan,wai na dawo na taras har baqi sun fara zuwa amma babu ke ba dalilinki,da agombe fa za’a yimin lalle amma naqi saboda ke,yanzun haka fa babu abinda aka yimin,ba lalle ba gayaran gashi,gayaran jiki kawai nayi,yau kwanansu uku mash qunshi suna jira amma naqi shikenan na gode” ta fada tana katse wayaf,sai taji duka babu dadi,ta dinga qoqarin kiranta amma kiran yaqi shiga,fuskarta ta nuna damuwa sosai
“Shikenan,ai gobe kya hada kayanki ki tafi ko?”
“Saidai ko jibi mama” ta fada cikin damuwa tana miqawa zainab wayar tare da komawa ta kwanta bayan ta tura mata tex na cewa tana tafe jibi insha Allah 1

  ******   ********     ******

       Tun da wuri washegari suka kammala komai ,sumayya ita tayi girkin tazarce sukayi har dare shinkafa da miyar kifi da salad,tayi wanka ta koma daki don ta fara hada kayanta.

       Batayi cikakken awa da zama ba ta fara jin ana sallama a tsakar gidansu,halima da zainab na makaranta,daga ita sai mama,maman kuma ta shiga daki don tayi qailula,sau ga duba agogo,sha daya da rabi na safe,sake yin sallamar akayi wanda kunnuwanta suka dinga jiyo mata kamar muryar amira,dakwalin material din jikinta ta daura ta rufe dogom tsefaffen gashinta,wanda ta mance rabonta da kitso sai gyara kawai da yakesh da mayukan wanke kai irin wanda nafisa ta koya mata amfani da su.

        Idanuwa ta qwalalo ganin amiran tsaye a tsakar gidansu,mamaki ya mamaye sumayyan,amiran ce a gidansu?,amiran baabaa prof da kanta?,ita da wasu ‘yammata ne guda biyu wansa zasuyi sa’anni,sai wata tsaye daga can gefe mai aikin amiran ce sumayyan ta ganeta,dariya ta qwace mata ta nufeta hannunta rufe da bakinta
“Tabdi jan,don Allah da gaske biyoni kikayi?”idanuwanta ta juya tana fadin
“dole kiyi mamaki ai sabida baki daukeni da muhimmamci yadda na daukeki ba”
“Ni da ke bata baci namesake,yi shiru ku shigo kada mama ta jiyo nasan wallahi tayaki zata yi” dariya amiran ta saki yayin da sumayya ke karbar hand bag din amiran,kalar kayan jikinta wadda wani lafiyayyen material ne mai zubin lafaya,hade yake da mayafinshi da jaka har da takalmin qafarta baki daya,sosai amiran ta sauya,gyaran amarci ya ratsata,kana ganinta kasan ba qaramin gyara aka yi mata ba. 1

         Jin surutun mutane shi ya tada mama daga daki sanda sumayyan ke tunqurin zuwa ta sanar mata da zuwan amira tana dariyar yadda amira keta santin Abdallah,cewa take sam bata yarda ita ta haifeshi ba,yayin da su humaida ke bayan amiran suma basu yarda ba
“Mama,ga amira,kinga wai biyoni tayi bayan na gaya mata gobe ina hanya”
“Ato,ke kanki kinsan baki kyauta ba,kin ganta yau nace ta tafi tace sai ta gaka gayaran kaya” harara amira ta aikawa sumayya
Wallahi mama ni na damu da ita,sam bata damu da ni ba,ki tambayi su  eesha wallahi kullum sai nayi zancanta”baki sumayyan ta qunshe,tasan an tabawa amiran inda ke mata qaiqayi,cikin girmamawa da mutuntawa amiran ta gaida mama ita da sauran qawayen nata guda biyu aisha da humaida eeasha da humy,fuska a sake maman ke amsawa tana tambayarsu mutan gidan duk da bata sansu ba
“suna nan qalau mama suna gaisheki da kyau”
“Madalla,muna amsawa” ta fada tana miqewa
“Sai ki samo musu abin sha ko?” Cewar mama,ta fahimci me maman ke fada,pure water garesu ba ruwan roba ba,bata kuma tana gani amiran ta sha ruwan ledar ba,sai ta sanya hijabinta tana cewa
“Ina zuwa minti biyu”
“Ina zuwa kum”
“Drinks zan samo muku ko zaku sha pure water da zobo?” 
“Wallahi kina dadawa kanki laifi,ni wacece da bazan sha pure water ba,in zaki dawo ki zauna ki dawo,Allah kuma sai na baki punishment,gidanmu zaki dinga kwana har a gama biki kin jawa kanki” dariya ta bata,don bata ga dalilin da zai sanya ta kwana gidansu ba. 

       Ruwan ta ajjiye musu da lemon sannan ta zauna suna sake gaisawa
“Kinsan Allah a jiya na tubure sai na taho kano sai da baabaa ya yankar mana ticket sannan na sama mishi lafiya”
“Da nine shi zaneki tsaf zanyi” humaida ce ta saka dariya
“Wake dukan amarya,marayar ma auta” sauka sa dariya baki dayansu.

       Hira suke sosai har sumayya na mamakin yadda amira ta saki jiki cikin gudansu sumayyan,babu wani nuna raini ko wani abu,duk da gidan nasu baifi bangaren guda daya na ma’aikatan gidan ba,har azahar tayi ta zubo musu abinci tana dari dari ko bazata iya ci ba duk da dadi da abincin yayi saboda ba baya bace wajen iya girki fanninta ne,ga mamakinta ma duk ta fisu kwasar abincin tana ta zuba santi,eeshan ce kawai sumayyan ta fuskanci ba’a sake take ba,rashin sabo ne ko kuwa meye oho.

        Suna idar da sallar la’asar ta dubi sumayya
“A gidannan fa zamu kwana,Allah yasa a taimakemu a bamu wajen kwana” dariya sumayya tayi,sauqin kan amiran na daya daga cikin abinda ke burgeta tattare da ita,sam ba zaka ce ita ‘yar wani bace ba,bata dauki kanta da zafi ba
“Gurin kwana kam akwaishi,saidai ban sani ba lallai ya dace da ku ba,katifar tamu ta yaku bayi ne”To zageni mana kawai amiran umman khalipha” sosai ta sanyata ta dinga qyalqyala dariya har sai da maganar esha ta katseta
“But mirah nayi zaton hotel zamu kwana ko?ko gidan baabaa dake nan garin”
“Tun tuni na gaya miki ba zamu kwana hotel ba,ba mutunci a ciki muna ‘yammata a ganmu a hotel,gidan baabaa kuma bansan key din taqamaimai na wajen wa ba,da nan da can din duka daya ne,nan ma gidanmu ne” bata qara cewa komai ba sai taja ta nade tana danne dannen waya. +

       Wayarta amiran ta daga tayi waya na wasu ‘yan mintuna sannan tace
“Ummee ta turo masu lallen sun biyomu,nan da la’asar zasu iso,inaga sai ran monday da safe sannan zamu tafi,gun mama zan mata kwana biyu,Allah sumayya gidanku dadi,mama na kirki wallahi” murmushi tayi kawai tana sake ganin sauqin kai irin na amiran.

       Hudu saura masu lallen suka iso,babarbariya ce ta usuli wadda ta shahara tayu suna wajen yiwa matan maya da ‘ya’yansu lallai lokutan biki irin haka,idan ta yiwa amarya lalle yana iya wata daya da rabi kafin ya bar fatarta,Allah ya hore mata sirrin yin lalle,bayan sunyi sallah sunci abinci mama ta sanya aka gyara musu dakin da ya abubakar ya bari,wanda akwai qatuwar katifarshi labule da kafet wanda ya malale dakin,yace dama bazai cire komai ba a bar masa dakinsa haka don haka can suka zauna,yayin da amira ta sauya kayan jikinta ta zauna aka fara yi mata lallen sumayya kuma ta fita ta baiwa zainab kudi suka sake yo cefane,tuni mama ta bayar an siyo musu lemo da ruwa na roba catoon uku uku,kafin wani lokaci zainab din ta dawo ta fara qoqarin sake dora wani girkin ita da halima,inda tace suyi fried rice,kubra mai aikin amira ta fito don tayasu,sai suka bata soya kajin da suka siyo.

        Baki sumayya ta bude sanda ta dawo,kamar ba hannu ke zana lallen ba,ko makaho ya shafa yasan qunshin amarya ne,gashi nan an zana shi har kusa da gwiwar hannu,baya ga ja da ka yi kata a tafin qafarta zuwa samam qafar,baqin kuma aka yishi daga idon sahu zuwa sama,dakin baki daya ya bade da qamshin mahallabiyya
“Wai wai wai,gaskiya ne amaryar saifullahi,kinga kyan da kika zuba kuwa?”
“Aini ke nake hangowa,na tabbata sai kin fini yin kyau” murmushi tayi tana shafa hannayenta wadanda suke farare qal,ta manta rabonta da qunshi ma
“Wannan hannun nawa ai babu kyau da lalle zai musu” humaida ce ta bushe da dariya
“Wannan mu kike zagi amiran umman khalipha mu da muke baqaqe”
“Rufan asiri ayimin afuwa” inji sumayyan tana dariya kafin ta samu waje ta zauna gefan amiran,a daren amira kadai aka samu yiwa,sai washegari sannan aka yiwa su sumayya eesha da humaida,ita sumayya kadan ma tasa aka yi mata,kwalliyar yatsu ne sai yar kadan daga gefen hannun.

       Suna cin abincin rana wanda sai yamma suka samu damar ci amira ta amsa waya sannan ta ajjiye wayar tana tsaki
“Bansan ma wanda ya gayawa anty su’ada ina kano ba,tabi duk ta uzzurawa mutane,wai muje zoo road inda take kai dinki mu amso mata,har gida tailor yazo ya karbi dukka dinkunanmu amma ita taqi bada nata sai data aiko da shi inda ta saba kamar fadin Allah,yanzu da nace ba zani ba ta hado ni da waccan zazzabin” ta qarashe maganar tana jan tsaki,eesha dake danne danne a wayarta ta ajiye itama tana jan tsaki tare da yamutsa fuska
“Nifa wlh laifinku nake gani,yadda kuka sakar mata take yadda taga dama,tana daukan kanta wata tsiya,idan nice wallahi da tuni na jima da saita mata hanya,amma Allah ya kai damo ga harawa zata gane kurenta” babu abinda amiran tace mata tunda tasab meke akwai a qasa 
asa tsakaninsu,sumayya bata ce komai ba sai da suka gama maganganunsu sannan ta dubi amiran
“Ina cewa zaki yi haquri da ita ne ki bata girmanta ko din darajar ta ta matar yayanki ko,kwana nawa ya rage ku rabu?”
“Dama ganinta ita ake idan ba sha’ani irin wannan ya kama ba ko tata ta kawota” eesha ta kuma fada tana haqiqancewa,sai sumayya ta juya ta dubeta taba mamakin zaqewarta,ai idan bata taushi amirar ba bata zugata ba ta yiwa matar yayanta rashin kunya
“Nifa bansan wajen ba namesake”
“Ni na sani,ina tunanin kamar mun taba karbo dinkinta indai itace su’ad”
“Zani idan zaki rakani”
“Me zai hana” ta fada tana taya kubra hada kwanukan da suka gama cin abinci,kubran ma nada kirki da saurin sabi,kusan da ita ake duk wani aiki ba ruwanta. +

STORY CONTINUES BELOW

        Wayarta amiran ta sake dauka tayi danne danne ta kara a kunnenta
“Kana ina……..ka kawo mana mota nan da awa daya zaka kaimu zoo road” ta katse kiran ta ajjiye wayar gefe.

          Gab da magariba suka gama shirinsu su duka,tuni driver din dake kano wanda ke kula da gidan baabaa dake kano wanda ya fara zama nan tun sanda sukayi aure da ummee,ya iso da jibgegiyar motar sai qyalli take,baki dayansu suka fito,suna shiga bayan an rufe qofar motar eesha ta kalli sumayya,wadda ke sanye da wani kyakkyawan material,yana daga cikin kayanta masu tsada,siyayyar anty dije ce,riga da skert aka yi mata wadanda suka yi mata cif,maroon ne da orange sai adon stone da aka yi masa,ta sanya hijabi mai hannu dan madaidaici orange,tunda ta sanya kayan eesha ke kallonta,baya ga kyauwun sumayyan da ya fito muraran da tsabar dirin jiki da Allah ya bata sai kuma kudin da material din ke da shi,saboda mamanta na business na kayan sawa na mata
“Wai baki gajiya da hijabi ne,kina da kyau da wayewa amma ki dinga fama da hijabi?” Ta fada cikim sigar gatse,murmushi kawai tayi bata tanka mata ba,ta sani izuwa yanzu ita kanta ta yarda da kanta,tasan babu inda ba zata shiga a goga da uta ba,ta fannin iya dressing da kyau da komai ma,kawai bata da ra’ayin yin wata shiga ne a yau,hijabinta take ra’ayi,ganin bata ce mata komai ba sai tayi shiru itama,haka kawai take kishin kyan sumayyan,ganin gidansu ba gidan masu kudi bane amma take da kyau har irin haka,baya ga haka ta taba aure,wanda ta tabbata ita din data fito daga gidan wadata bata da rabin kyawun sumayyan,mamaki yana sake kasheta idan ta kalli abdallah aka ce danta ne,ta yaya matashiya mai kyau aji da qananun shekaru sa’arsu zata haifi santalelen yaro irin haka mai shekaru kusan hudu?.

       Amira wadda wayar da suke da saifullahi ta habata tankawa ta dubi eesha bayan sun gama wayar
“Wai sumayya kike cewa bata gajiya da hijab,hmm,bata ga damar yin kwalliyar vane,da ko ke ba zaki nuna mata kwalliya ba” 
“Kuma wallahi dressing din na mata kyau sosai,yana dacewa da kayan data saka,ke gwara ki dinga boye wannan kyan naki,idan ba haka ba samarin nan na yanzu ‘yan garari idonki idonsu wallahi baki da sakat” cewar humaida,dariya ta basu baki daya,banda eesha data tabe baki tana danna waya.
Motar na shirin tashi sukaji amira na tsaida drivan,ta bude murfin motar tana yinqurin fita,da ido sumayya ta bita,ashe malam ta hanga ya dawi dauke da leda,tana kallonta ta isa gareshi tana yunqurin amsar ledar hannunshi,yana ganinta shima ya saki fara’a yana son hanata karba amma sai data amsa ta bishi cikim gida da ita,ajiyar zuciya sumayya ta saki tana lumshe ido,mutunci qima da qaunar amira na sake daduwa a gurinta,tun jiya data rakasu gaida malam ta lura da girman da take bashi,don sun jima suna hira da amiran sumayya sai ta zama ‘yar kallo. +

       Sai bayan wajen minti goma ta dawo cikin motar hannunta dauke da daata manya wankakku guda hudu,ta maida murfin moyar ta rufe tana baiwa drivan umarnin yaja su tafi
“Baba naje yiwa sannu da zuwa,kinga ma na karbo tsarabar kasuwa daata ne ko yalo?” Ta fada tana tambayar sumayya,Murmushi tayi
“Daata ce,shi yalo ai fari ne”
“Ohk,ni bana banbancewa,baabaa ne dama ke cinsu wajenshi nake karba” ta fada tana sanya datar a bakinta,sai data cinye daya sannan tace musu
“Babu wanda zan yiwa tayi fa cikinku”
“Cinye abarki,muma nasan ya ajiye mana” inji humaida,murmushi tayi taci gaba da cin abunta kafin daga bisani tace
“Jin malam nake kamar baabaa wallahi,ina son malam,ki bar mana shi mu tafi da shi abuja” dariya ta qwacewa sumayya sai data yi mai isarta
“Gaki nan gashi indai zai biki mun baku shi” 
“Hmmm,ai dan kinsan ba zashi ba dq baki bamu shi ba” da irin wannan barkwancin suka qarasa zoo road din suka karbo dinkin suka dawo.

      Motar na saukesu ta hango abdur rahman tsaye jikin tashi motar hannayensa harde a qirjinsa,ya zubawa motar cike da kishi yana dubanta,dama a jagule yau ransa yake jin gobe zata koma abuja,da yana da dama tabbas babu inda zata koma,zamanta zatayi a kano kusa da shi har ta zama mallkinsa,sam hidimar su amira ta mantar da ita zuwanshi,cewa su amira tayi tana zuwa sannan ta nufi wajenshi.

        Idanunsa ya dora a kanta sanda ta iso tana murmushi
“Maimakon ka shiga kafin na qaraso,zooroad mukaje karbo dinki,Allah yasa baka jima ba a tsaye”
“Yanzu nazo” ya fada bayan ya saki ajiyar zuciya,ta fuskanci a dagule yake,ta kuma san me ya jagula ran nasa,kusan hirar dai sama sama aka yita ya dubeta bayan sun gama sallama zata shige ciki
“Ki kula min da kanki,ki kulq da amana ta”
“Insha Allahu” tace tana dariya aciki,wai kishi ke cinsa.

        A gun mama ta tadda amira,humaida na daki tana sauya kaya,eesha na kwance itama a dakin tana waya
“Wai waye wancan din da ya wani qwafe yana kallon mutane?” Amiran ta fada tana batsewa,dariya ta subuce wa sumayya ganin yadda take cika
“Ke,ki iya bakinki,mijina ne”fuska ta yatsina
“I see,shi yasa kika wani tafi gunsa daga saukowarmu daga mota?” Maida dubanta tayi gareta
“Meye matsalarki ne ke?” Baki ta tabe
Hmmm,ina cewa ni na fara yi miki tayin yaya na kika ce ba zaki aureshi ba sabida ke da aure sai a lahira,amma ya akayi kike kiran wannan da mijinki?” Dariya kawai sumayyan keyi tana bude envalope din da ya kawo maga,sam ta manta sun taba magana makamanciyar haka da amiran da batayi subul da bakan wannan magana ba,sabida tasan tuburar amiran yanzu sai ta tubure mata
“Duk abinda Allah ya rubutawa bawa dai cikin KUNDIN QADDARARSA” ta fadi tana murguda baki tare da janyo kayan mama da take ninkewa taci gaba da ninke mata,haka nan maganar ta daki zuciyarta,a hankali ta daga kai ta dubeta,sai taga ita sam bata ma damu ba ninke kayan take abinta tana wasa da abdallah dake zaune gefe yana hada motarshi daya kukkunce ta,bakinta yayi kata nauyi sai ta kasa tankawa,miqewa tayi ta bar falon amiran ta saci kallonta tana dariya ciki ciki. +

          Qarfe biyu suka isa airphort wanda tun a jiya amiran ta siya musu ticket,qememe wannan karon abdallah yace sai yabi mamarshi,amira tayi uwa tayi makarbiya tace ai tabbas tafiya da shi babu fashi,sosai yaron ya shiga ranta tamkar mahaifiyarsa,zasu bi jirgin MAX AIR dazai tashi daga kano zuwa abuja qarfe uku na rana,sumayya dai mamaki ya cikata,idan vanda asarar kudi da basa gani suna da mota mai kyau wadda zata iya kaika abuja cikin awanni uku ma amma sai anyi asarar siyan ticket,bata da magana tunda aikin gama ya gama,gasu cikin gajimare,sai taji kewan mamanta da malam na kamata,tamkar ta koma gida haka take ji,tayi zurfi a tunani har sai da amira fa tabota
“Ku tunanin wannan mutumin kike?” ‘Yar qaramar dariya ta saki tana gyara zamanta
“Ki fita daga idanunshi fa,na lura tun jiya kin sanya mishi ido” yatsina fuska tayi
“Idan anqi fa,mi barni nayi abinda nakeso kishi nake,don me zai wani aureki bayan muma muna da buqatarki cikin gidanmu,haushinsa nake ji gaskiya” baki ta saki tana dubanta,sai kuma ta dauke kai tana murmushi,ta lura da gaske amiran take,haka take bata barin abu cikin zuciyarta,irin mutanan ne masu fadim gaskiyar abinda ke zuciyarsu,idan ta biye mata sai suyita yi,kamar tasan me take tunani sai tace
“Mamaki kike ko?,haka nake,bana iya boye gaskiya ta,bana kuma boye abinda ke yawo zuciyata,mu biyu ke da irin wannan attitude din a dakinmu,shi yasa tamu tafi zuwa daya ni da shi” ta fada tana daga yatsunta tana murmushi
“Attitude dinki keta shafa fa amira,leave me alone please,rigimarki wlh yawa gareta,saifullahi zai sha fama” dariya ta tuntsire da ita har tana dan ranqwafawa sumayyan na tayata,daga haka kuma suka dau wata hirar daban amiran na nunawa sumayyan irin kayan gadon data zaba cikin wayarta,sosai kayan suka tafi da imanin sumayyan,ta musu addu’a sosai kan samun kyakkyawar rayuwar aure ta gari,wanda addu’o’in sun faranta ran amira sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *