QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 5

QADDARAR SUMAYYAH





CHAPTER 5




Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayijim yanajiran amsa sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar “Da wa nake magana?”,cikin karyar da murya akace ” mukhtar baka ganeni ba,fa’iza ce fa“ “Fa’iza?,wacce fa’iza” wani murmushi akayi mai fldda da sauti cikin siga ta nufin jan hankali”Fa‘iza amaryarka mana”.
Hade rai yayi kana cikin dakiya yace”ok,ya akayi?”,sake marairaice murya tayi “Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?” “Yayi kyau,ina gajiya?” “Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin sake zuwa guna bakayi,haba” “Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?” Kai ta girgiza kamartana gabansa,cikin ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa “A’ah ba shi bane” “Fadi uzirinki kai tsaye”. Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana “An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka bawa uwargidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantarciki da falo”tana direwa ya dora “Ko?,a wanne hadisin?”.
Fara quluwa tayi amma ta dake”haka na ya dace ai” “To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki haqqinki” ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don kada kwabarta tayi ruwa “Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba” tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki. ltama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare. Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tanajiran dawowartajta ta gyare mata jikinta fes,zuwa la’asar ta fito shar,fatarta ta sake wani kyau da haske. . Tsokanarta sosai mukhtarya dinga yi,yana mata waqa “Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)” dariyar
itama ta dinga yi. Ranarjuma’a akazo aka mata lalleja da baqi,ta aika halima da zainab suka karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya. Wuni tayi babu laifi ta dan tarajama’a,sosai mutanen unguwar suka yi mata kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata sunajira a kawo amarya su karbeta. Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya kada ‘yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshejikinta sannan ta nerni baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo. Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na dare babu ita babu alamarta,hakan ya sanya maqotan suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa ‘yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za’a bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama suka tafi,maman nana kawai ta rage. ‘
Qarfe goma na dare maman nanan na shirin tafiya itama ganin shirun yayi yawa sai ga hayaniyarsu data motocinsu,hakan ya sanyata ta koma ta zauna tana tsumayin isowarsu,saidai ga mamakinta yadda akeyi a al’adance a fara kai amarya ga uwargida su ba hakan bane,dakinta suka bude kai tsaye suka shige da ita suna faman yada kirari tamkar jinin maroqa “Shiga da bismillah uwar ‘ya’yan mukhtar”.
Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana ” maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba“dan murmushin kwantarda hankali tayi mata “Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni’imal wakeel,ni’imal maula wa ni’iman nasir” kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya hannunta ta share tana mai bata qwarin gwiwa tare da hana kanta da kama kuka.
Labule aka bankade aka shigo,fiddausi ce goye da ‘yarta,ta dubi sumayyan sannan tace “Kije dakin amarya,yaya bara’atu na son ganinki”,cikin mamaki maman nana ta dubeta ” a’ah,ai ba’a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?”duban maman nanan tayi sai ta juya ta fice ba tare da tace komai ba. Ko minti daya ba’a qara ba saiga yaya bara’atun ta shigo “Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da sumayya kawai zakiyi,don zama fa’iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don ta tafi ba,saboda haka ke sumayya inajiranki”, wani abu yazo ya tokarewa maman nana a wuya,tamkarzata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun yajuye kan sumayyan wanda bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji. ltama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya har zuwa dakin amarya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.
Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata shigowa dakin,wata ‘yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube fuskarta da mayafi tace ” to sumayyatu,ga ‘yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman lafiya,muna fatan zaku hada kanku ku zauna lafiya” “Kowa ya kwana lafiya ai shi yaso ato,fa’iza dai gata nan zama daram ila yaumut takunu” yaya bara’atu ta karbe zancan daga gun tsohuwar,rai bace maman nana ta daga kai ta dubi yaya bara’atu,mamaki take bata,wai ‘yar yarinyar da duka duka take cikin shekaru na sha takwas take zagewa babba da ita tana yadawa wadan nan habaice habaicen da suka girmi kanta,babu lallai ma kan nata ya iya dauka,ina laifi ma ta bar yaranta masu shekara sha hudu sha biyar su gayawa sumayyan?,wata qila ace wadan nan sune dai dai da ita,amma ba ita ba wadda ta kusa linka shekarun sumayyar ba. . Ta tabbatar idan taci gaba da zama cikin dakin tabbas za’ayi batacciya da ita,bata so kuma wani abu na tsiya ya hadasu,tunda duk tsiya tafiya zasuyi ba zasu shekara ba,kuma gidan dan uwansu ta shigo sunci albarkacinsa,tunda mukhtar kowa ya shaidi halinsa,sai ta kama sumayyar ta miqar sannan ta ari bakinta taci mata albasa,don ta fuskanci ba zata iya magana ba kuka take qasa qasa kanta duqe “Insha Allahu baba babu wata matsala,don sumayya bata da damuwa mu mun shaideta tun tana tatsitsiyarta muke tare da ita,zaman Ipy an sameshi an gama da izinin Allah” “To Allah ya yarda ‘yar nan” cewar tsohuwar. Da sauri ta janye hannun sumayyan suka fice saboda ta soma ganin bakinsu yana motsi suna shirin fara qananun maganganu,sai data tabbatar sumayyan ta samu nutsuwa kana tayi mata sallama ta tafi,zuwa lokacin suma ‘yan kawo amaryar suna qofar gida suna shirin tafiya. Sha daya na dare agogon falon nata ya nuna mata,gidan yayi shiru kowacce na dakinta,sauqinta daya akwai wutar nepa da ta haskake ko ina cikin gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana ci gaba dajan hasbunallahu wa ni’imal wakil,harzuwa lokacin da taji an turo qofar gidan an shigo,sai ta miqe tsam a tsorace kasancewar basu taba barin qofar gidan nasu haka ba.
Tanaji aka rufe qofa ta biyu hakan ya alamta mata cewa mai gidan ne,ta sauke ajiyar zuciya duk da cewa tana tsayen bata zauna ba. Da sallama ya daga labulen dakin idanunsa ya sauka a kanta,ta kowa yayi a hankali ya shigo dakin yana dubanta yadda tayi carko a tsaye,cikin sanyin murya yace
“me kikeyi a tsaye haka kamar wadda taga wani abun tsoro” ta saki ajiyar zuciya,muryarta
a sanyaye tace Ji nayi ana taba qofa ne”,murmushi yayi yana ajjiye ledojin hannunsa
” ke kam farar kura ce sumy”sai tayi murmushin yaqe tana kawar da kai,ta qarasa inda yake tana masa sannu da zuwa ya amsa yana zama kan daya daga cikin kujerun falon Hada min ruwan Wanka sumayya” ta danyi sororo kamartace wani abu sai kuma ta fasa tace t0. Wanka yayi sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan uwansa har kusan sha daya da rabi.
Motsi suka dingajiyowa a tsakar gida,kallojuna suke suna sauraron motsin ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta dubi mukhtar “Ya mukhtar bacci nakeji” “Hala ma korata kike da dabara ko?”kai ta kada zuciyarta a cunkushe ” a’ah ya mukhtar ba haka bane”shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da sukeji na qara qarfi kadan kadan. Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo dasu ya tura mata daya sannan yace “Tashi muje ki rakani” daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkartace ba zata ba amma sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba da take ganin qimarsa. Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar dakin. . A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala saman fuskarta. Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi qoqarin cewa “Sannu amarya” “Uhmmm” kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani ya gangaro ga rufewa “Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada kanku ku zauna lafiya ….. haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci rashin gaskiya ba …… akwai wani sauran mai magana?”. Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa “In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu Allahya baka ikon yin adalci a tsakaninmu” “Amin amin” miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe “Muje na rakaki ko” duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan murmusa,ina dakin fa’izan ina dakinta.
A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a sanyaye yace “Kiyi addu’a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a ranki,mukhtar naki ne kinji ko” kai ta gyada Sai da safe” ya fada yana juyawa a sanyaye. Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta “Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni” kai ya gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin “In sha Allah” sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe mata qofar. ‘ Ta rufe idanunta a hankali tana fatan bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kam gadon su.

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *