QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 9

QADDARAR SUMAYYAH







CHAPTER 9



Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqin zirga zirgar fa’izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu. Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa’izan,don tun sumayyan bata jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice ita kam sumayyan mamakin shegen cin abinci irin na fa’izan take. Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa’izan da mukhtar din,ba wai don tana burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa.yana so ne ya dasa mata qin abun ta yadda ba zata sake marmari
ko gigin nemansa ba Iya wuya kam ta shata don har taso ta zarta ta jiya,don yau har mikin jiya sai da ya dawo sabo fill baya ga sabon da tayo guzirinsa,kamarjiya haka yayi fitarsa da asuba,saidai wannan karon a masallaci yayi zamansa har gari ya ida wayewa,shi kadai ya dinga murmushi saboda yasan ya gama koya mata lesson. Tun daga ranar ta shiga kulle qofarta,dariya ya dinga yi cikin zuciyarsa yana fadin “Ta dauka wani damuwa akayi da abinta,bata san ko giyar wake na sha bazan sake rabarta ba” kewar sumayyansa ce kawai take damunsa sam fa’izan bata a cikin lissaflnsa. Har ta qarasa cinye kwanakinta bata sake yarda ya kwana dakinta ba,haka nan sumayya ma qin yarda take ganin cewa ba kwanakinta bane,bugu da qari kuma maman naana na tsumata,so take ta d’ai d’aita tunanin mukhtar din a duk lokacin da ya dawo hannunta.
Randa zai dawo dakinta tun safe takejin nishadi,ta shiga dakinsa ta masa gyaran tsaf lungu da sak’o ta k‘alk’ale ko ina,sai data kammala duk wani abu da ya dace sannan ta zauna tana jiran zuwan yammaci. Tana kan kujerar falon ta kwance bayan sallar azahar tana hutawa taji sallama qofar gida,saukowa tayi ta sanya hijabinta don ganin waye,don ta sani cewa ko digewa mai yin sallamar zaiyi ba amsawa ko saurarensa fa’iza zata yi ba.
Abdur rahman ne d’a ga qanin mahaifln mukhtar,gefansa qanwarsa ce bahijja wadda zatayi shekaru sha biyar,fuskarta qunshe da fara’a tayi masa iso kan ya shigo ta juya yabi bayanta,dai dai lokacin da fa’iza ke shimfida tabarmarta a tsakar gida da alamu zama zata yi,abinda bata taba ganin fa’izar tayi ba tsawon kwanaki takwas da zuwanta gidan,da kallo ta bisu suna gab da shigewa dakin sumayyan ta rabka salati Meye haka zaki kama ki shigo mana da gardi cikin gida?” Waiwayowa sukayi dukkaninsu suna dubanta “Gyara maganarki qani yake ga mukhtar,muje bahijja” ta fada tana dage musu labulen
suka shige. Ruwa ta gabatar musu da lemo wanda ta tanada cikin cooler dinta saboda mukhtar,kasancewar ya musu yawa yasa suma suka samu rabonsu Mutanen misra,kaga ko yadda ka koma abdur rahman,yaushe ka dawo ne?” Sumayya ta tambaya tana murmushi,karatu ya tafiyi qasar misra saboda schoolership da ya samu daga gwamnatin tarayya,kasancewarsa haziqin dalibi cikin daliban dake jaharwanda ke karantar fannin da ya shafi addinin musulunci,shekararsa biyar da taflya sai yau ya dawo,a lokacin da ya tafl din shekararta daya da aure da mukhtar,da gidansu jikin gidan mukhtar din yake kafin su tashi,wani lokaci idan mukhtar din nason flta kuma baiso ta fita abdur rahman din yake kira ya tayata zama,hakanne yasa suka saba har ya zama kamar wani abokin wasanta,a lokacin duka duka shekararsa sha bakwai shima.
Ruwan da yake sha ya ajjiye yana fadin
“Kwana na uku kenan,ashe yaya mukhtar bai gaya miki ba kenan?”kai take girgizawa
” bai gayamin ba kam ina ga ya sha’afa”
“Ya manta kam,irin wannan mace da ya ajjiye haka a gidansa babu kan gado” cewar bahijja don ita ta qulu da abinda ta musun,murmushi sumayyan kawai tayi,abdur rahman yace “ltace matar da aka ce ya kuma aure?” Kai sumayya ta gyada masa sai yace
“Masha Allah Allah to ya baku zaman laflya,lokacin ina misra ai munyi waya da alhaji yake gayamin don alokacin anata rikici ya mukhtar ya kai qarar umma yahanasun” kai kawai ta kuma jinjinawa cikin mamaki din ita bata ma san ya kai qarar ba,hira suka sha sosai,suka tuttuna baya sai wajen qarfe uku suka yi mata sallama suka tafi bayan abdur rahman ya bata kyautar abaya har guda biyu masu kyau ta rakosu har soro tana musu godiya tare da bawa bahijja dari biyar tace ta hau mota.
Ko da ta dawo fa’izan na zaune har yanzu a tsakar gidan,duka hirar da sukayi da alama na cikin kunnenta,alwala ta daura tayi sallar la’asar sannan ta shiga kitchen ta soma hidimar dora sanwar dare.
Ta shiga ta fita ta shiga ta flta tayi hakan ya kusa sau biyar,ganin haka ya sanya sumayya tayi zamanta a kitchen din taqi komawa daki saboda gujewa sake afkuwar abinda ya faru ran nan,sai data gama komai ta kwashe nashi zuwa dakinta sannan ta bar kitchen din. Sam bata nunawa fa’izan wanka zata shiga ba saboda ta gama gane ta tsaf,bata tashi shigewa bayan gidan ta banke qofa sai taga tana shirye shiryen shiga wanka,sai data fito taji fa’izan nata jan qwafa da tsaki,tayi dariya cikin ranta ta shige dakinta ta hau shiryawa. Kan idanunta ta tarbi mukhtar wanda sai data gwammace tayi komawarta daki,don kuwa
yana gama ajjiye babur dinsa ya sungumi abarsa kamaryadda suka saba a da can baya karfln qara aurensa ya dinga juyi da ita yana fadin Masha Allah my sumy,kyau kenan” duk da kunya ta dan kamata sai ta basar,ta gaban fa’izan ya wuce da “bai direta ko ina ba sai kan gado ya bita ya turmushe yana yamutsata tare da cakulkuli. Duk yadda taso qunshe dariyarta ko don fa‘iza amma ina abun ya faskara,haka ya sanyata ta dinga qyaqyatawa tana roqonsa ya bari,da qyar ta samu ta tsaida shi tana goge qwallar da ta hada,kunnanta ya kai bakinsa ya rada mata wata magana da ta sanyatajin kunya har ta rufe fuskarta da tafln hannunta. Ga mamakinsu sai ga fa’izan tazo cin abincin daren,duk da sumayyan bata so hakan ba amma ta basar saboda kada taga kamar ta wulaqanta ta,shi kuwa yazo mai wuya domin har wata shigar ya sanya sumayyan ta sake masa cikin qananun kaya. Suna kammala ci ta ja gefe ta sake sabon zama,da ido mukhtarya bita sannan ya dauke kansa yaci gaba da abinda yake,ba qaramin tsanarfalon tayi ba saboda yadda ya kere nata amma ta gwammace tayi ta zama ciki ko banza ta musguna musu ta hanasu sakewa. Gefansa sumayyan ta dawo ta zauna tana kallon yadda yake shigar da wasu bayanai cikin 
sabuwar laptop da ya siyo,tana da sha’awarta sosai hakan ya sanya ya saki aikin da yake yana koya mata. Sosai ta qulu amma hakan baisa ta bar dakin ba,har suka kammala ya miqe ya fita,cikin 
‘yan mintina ya dawo yana shigowa falon ya sunkuceta kamar dazu,harya kai bakin qofar dakin gadon ya waiwayo ya dubeta 
“Ammm,idan kin gama abinda kike yi ki rufe mana qofar,sai da safe“ ya fada yana 
shigewa,da gayya ya dinga takalo sumayyan har sai da ya fuskanci ta flce musu daga falon ta hanyar dukan kujera tare da banko qofar sannan ya saki murmushin mugunta yana saukowa daga gadon don ya rufe dakin. a Riqo hannunsa sumayya tayi tana masa kallo qasa qasa 
“Kai ko ….. ba’a haka ya mukhtar fa,nasan da gayya kake komai” murnushi ya saki har yana fidda sauti sannan yace Koma me nayi ita ta jama kanta,ta yaya haka kurum zaka dage sai ka cusa kanka inda baka da muhalli?,sai kayi zaman aure a inda ba’a da muradinka?” Ya fada yana sauka daga gadon tare da cewa Jirani nazo sai muyi hirar sosai” ya fadi yana kashe mata ido daya,dariya ta saka. Wani irin zama ne yake wakana a tsakaninsu,cikin abinda bai wuce sati uku ba gaba daya 
fa’iza babu layin da bata karade ba neman qawa,kasancewar duka maqotan nasu mutanan sumayya ne,hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba,bilhaqqi bata qaunar sumayya ko wani abu da ya danganceta,hatta da yaran dake shigowa gun sumayyan fa‘iza qorafi take a kansu,idan taso tana iya korarsu,wani lokacin idan kan idon sumayyan ne ta hanasu tafiya,tsoronta yaran keji hakan ya sanya wasu daga ciki suka janye shigowa,mutum ce ita ta jama‘a hakan ya sanya idan fa‘izan nason yawonta saidai tayi uwar zuwa can bayan layinsu. 
Tunda tazo gidan bata taba daukar tsintsiya da sunan shara ba baya ga ta dakinta,koda ran girkinta ne da ta kammala zata bar wajen yadda yake tayi gaba abinta,ko kadan sumayya bata lamunci qazanta ba ita zata killace komai ta gyara,ko banza tasan tana da lada. 
Ko kadan mukhtar baya daga mata qafa wannan shi ya rage kaso casa’in cikin dari na rashin mutuncinta,tun da can irin ‘yammatan nan ne da basuqi su fito da daurin qirji su dambatu da namiji ba,hakan ne ya bawa yaya yahanasu sha‘awa a gajeran tunani irin nata,tana ganin cewa ita daya ce zata iya zama cikin gidan muntari ta take kowa ta kuma kawo musu abinda suke so,duk da cewa fa’izar ta taba cikin shege tana gida aka zubar amma hakan ba aibu bane a gun yahanasu,tana ganin ma wata dama ce dake nuna zata iya haifawa muntarin d’iyoyin da take tsammatar zasu iya alfahari dasu,tarbiyya cancanta kunya asali da cikakkiyar nasaba basu zame mata mizanin ma’auni ba a gareta wajen hada qanin nata da ita.
K0 daya sumayya bata taba shaidawa muntarin fltar barbadar da fa’izan keyi ba,ta azawa ranta cewa idan kere na yawo zabo na yawo dole za a hade,abu daya ne da ta tsaya a kansa shine,bata yadda fa’izan ta shiga haqqinta kamar yadda ita bata shiga nata haqqin ba har ma da hurumi da shirginta baki daya,sai yanzu take sake ganin alfanun shawarar anty dije gareta,tabbas gaskiya ta gaya mata,kuma gata ta mata,ba dan hakan ba da zuwa yanzu Allah ne kadai yasan yadda fa’izan zata maidata. Duk yadda ta dauki lamarin shigowa gidan muntarin da sauqi ya fice haka,sai ta tadda soyayyar da muntarin kewa sumayyah ba irin soyayyar nan bace da tuggu ko makirci ke nasarar wargazata ba,soyayya ce mai azabar danqo da yauqi,amma ta daukarma kanta alqawarin sai ta wargaza zaman lafiyar sumayyar ko ta halin yaya,kafin ta waiwaya ta 
takawa su yaya yahanasu birki wadanda zuwa yanzu suka soma yi mata lissafin zuwa yaushe zata dauki ciki,bata son takura ko sanya ido cikin lamuranta,basu san wacece ainihin fa’izan ba har izuwa yau 

‘A WANI DARE’ 

Masu karatu ku biyoni,yanzu aka fara littafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *