RABO AJALI CHAPTER 5

RABO AJALI





CHAPTER 5





Kallan juna Naufal da Umairah sukayi cike da mamaki, batare da sunyiwa juna magana ba,
suka bi bayanta, a harabar gidan suka iske ta ruk’unk’ume da jakar kayanta,
a hankali Umairah ta k’arasa inda take rakub’e ta sanya hannu da d’ago Neelah,
jikinta Neelah ta fad’a tana tana sakin kuka tace ” na yarda dake sosai nasan bazaki tab’a cutar dani ba,
dan Allah kada ki bari ya k’ara yi min abinda yayi min, dan Allah ki nisanta ni dashi,
cikin mamaki Umairah ta mayar da kallanta kan Naufal suka d’an kalli juna,
kana ta d’ago Neelah tace ” kin san shine…!? +

Bakin Neelah na rawa cike da tsoro tace ” eh shin…..! ganin Neehal ya nufo su fuskarshi d’auke da murmushi,
yasata tsayar da maganar ta, had’i da kafe shi da ido cike da mamaki,
ta jima tana kallanshi tana san tantancewa Neehal ne koba shi bane,
dan taga d’an bambamci a tsakanin su, dan Neehal yana da dimples shi kuma wannan da yayi murmushi bataga kumatunshi ya latso ba,
haka fuskar Neehal akwai gashi (kasumba) a fuskarshi wacce ta kwanto har zuwa hab’arshi,
amma wannan bashi dashi, ganin yadda Neelah ta kafe Naufal da ido yasata maimaita mata tambayar ” kin san shine…!?

Ajiyar zuciya Neelah ta sauke had’i da mayar da kallanta ga Umairah,
tace ” a’a yayi min kama da wani bak’in mugu azzalumi ne, sai yanzu na gane bashi bane,
cikin mamaki Umairah tace ” mugu…! azzalumi kuma…!?

“Eh…! Cewar Neelah, Umairah bata kuma magana ba ta kamo hannun Neelah suka koma cikin gidan,
ta bayanta Naufal ya zura hannunshi ya rungume ta yana kissing kumatunta, k’uri Neelah tayi idonta kan Naufal bata ko k’iftawa,
dan ganin Naufal tayi tamkar Neehal saboda tsananin kamar da suke yi, ganin yadda Neelah ta saki baki tana kallan Naufal,
yasa Umairah tsammanin ko dan taga sunyi hug & kissing d’in juna ne,
rolling ido Umairah tayi had’i da sakin Naufal ta kalli Neelah tace ” wannan shine miji na sunanshi Naufal Bilal Lagosa,
daga yau ya zama Uncle d’inki, kasa magana Neelah tayi dan har lokacin tana zaton Neehal ne,
d’an murmushi Naufal yayi yana kallan Umairah yace ” k’anwa kika samo mana ne…!?

“Yes..! we will talk letter tayi maganar tana rik’o hannun Neelah,
murmushi Naufal yayi tare da nufar inda Neelah take tsaye yace ” ya sunanki….!?

Shiru Neelah tayi ta kasa furta koda kalma d’aya, kallan Umairah yayi yace ” ya dai ko k’anwar ta mu bata magana ne…!?

” Tana magana a dai tsorace take ne, kasan akwai rashin sabo, sai a hankali,
kasancewar gidan babban ne yasa ta bawa Neelah tank’ak’amen bedroom,
me d’auke da bathroom & toilet, an k’awatashi da Italian bed complete set, & sofa bed,
cikin bathroom harda tub bath, sosai d’akin ya k’awatu, ta dafa kafad’ar Neelah tana murmushi tace ” daga yau nan ne d’akin ki nan zaki rink’a kwana, waccen k’ofar band’aki ne, ta fad’a tana zaunar da Neelah saman bed,
saurin mik’ewa Neelah tayi cike da tsoro jin gadon ya lotsa tana zama,
” lafiya..!?

Cewar Umairah, cikin k’auyauci tace ” yo locawa yayi,
taso tayi dariya amma saita kanne tace ” ai haka yake, sunanta kafita, karki ji tsoro ki zauna kinji,
kiyi wanka, idan kin gama ki fito parlor mu ci abinci, Neelah ta amsa da to,
fita Umairah tayi ta nufi bedroom d’in Naufal, Neelah kuma ta mik’e ta nufi k’ofar da Umairah ta nuna mata tace ban d’aki ne,
tsaye tayi sororo tana bin ko’ina na bathroom d’in da kallo had’i da tantamar anya nan ban dak’i ne kuwa,
ganin kwata-kwata bayyi mata kama da makewayi ba, yasa ta rufewa ta koma ta zauna,
har Umairah ta gama wanka ta shirya ta dawo parlor ta zauna tana jiran Neelah amma shiru bata fito ba,
jin shiru yasa Umairah mik’ewa ta shiga bedroom d’in Neelah, koda ta shiga iske tayi zaune k’asan carpet,
” au wai bakiyi wankan ba…!?

STORY CONTINUES BELOW


Cikin sanyin murya tace ” banga makewayin ba, na higa wancan amma naga kamar ba can bane,
guntun murmushi Umairah tayi kana ta kama hannunta suka shiga bathroom d’in,
ta nunnuna mata komai da yadda ake amfani dasu, kana ta nuna mata wardrobe tace ” nan zaki rink’a aje kayanki,
tayi maganar tana saka mata ledar kayanta ciki, zama tayi bakin gado har Neelah ta fito daga wanka,
ta nunnuna mata kayan shafa, da yadda ake amfani dasu,
bayan Neelah ta gama shiryawa suka fita parlor suka zauna saman dinning table,
wanda masu aikin Umairah suka gama shirya abinci, ko wajen cin abincin sai da Umairah ta koya mata,
dakyar Neelah ta d’an ci abinci dan kasa cin komai tayi،
har suka gama cin abincin idonta yana kan Naufal tana san tabbatarwa Neehal ne ko ba shi ne,
bayan sun gama cin abincin Umairah ta kalli Neelah tace ” kije kiyi bacci, ki huta zuwa gobe sai muje mu kasuwa ayi miki siyayya,
zuwa Monday muga abinda Allah zayyi, murmushi tayi tare da cewa ” nagode sosai,
simple smile Umairah tayi mata, kana ta tafi bedroom d’inta ta zube kan gado,
ta fad’a duniyar tunani, ita dai tasan Neehal yana da dimples amma wannan bashi dashi,
sannan Neehal yana tara gashi a fuskarshi da kanshi, amma Naufal bashi dashi, sannan Naufal yafi Neehal ‘yar k’iba kad’an, shi kuma ya fishi tsayi,
sannan Naufal yana da sakin fuska, murmushi da dariya amma wancan bashi dashi,
har dare ya raba Neelah batayi bacci ba sai da ta tabbatarwa kanta Naufal ba Neehal bane,
dan akwai bambamci mai yawa tsakaninsu.

Bayan Naufal da Umairah sun shiga bedroom tayi mishi bayanin komai da komai babu abinda ta b’oye mishi,
sosai ya tausayawa Neelah, yayi matuk’ar murna da jin dad’in zuwanta dan yasan koba komai zata d’ebewa Umairah kewa,
yace ” Allah ya taya mu rik’o Ubangiji ya bamu ikon rik’e amanarta hannu bibbiyu,
Umaira ta amsa da “amin ya Allah,
washe gari suna zaune a dinning table Neelah ta saki ranta sosai danta tabbatar ba Neehal bane,
” ki shirya zamu fita, zamu je gidan mu daga can zamu je kasuwa,
cewar Umairah, murmushi tayi had’i da cewa ” makarantar fa….!?

Dariya Naufal da Umairah sukayi, had’i da cewa ” da wuri haka…!?

“Ai sai ki bari sai kin huta ko….!?

Cikin murmushi tace ” hutu kuma..!?

“Ai ba wani hutun da zanyi, gwara na fara makaranta da wuri,
” tom sai ki tambayi Uncle d’inki, ni ba ruwa na, cikin tsokana Naufal yace ” wanne Uncle d’in da ko magana ank’i yi mishi…!?

Kallanshi tayi tana murmushi tace ” kayi hak’uri Hamma’am, jiya a tsorace nake sosai,
shiyasa na kasa magana, sunana Neelah, ” masha Allah, k’anwarmu, shekararki nawa…!?

” iliben ye, (11 years), cike da mamaki Naufal da Umairah suka kalli juna kana suka mayar da kallansu ga Neelah ” kin fara karatu ne dama…!?

Suka fad’a a tare, yadda sukayi maganar ya bata dariya, cikin dariya tace ” eh na gama primary tun bara,
kai Naufal ya jinjina tare da kallan Umairah yace ” inaga komai zaizo da sauk’i, abinda za’ayi a samo mata extra lesson teacher da zai rink’a koya mata a gida,
bayan makaranta, sannan a makarantar ma ta rink’a tsayawa lesson bayan an tashi,
haka islamiyya mu samo mata malamin da zai rink’a zuwa gida yana koya mata,
kai Umairah ta jinjina cike da gamsuwa tace ” hakan yayi, thank you so much dear,
tayi maganar tana d’ora hannunta saman nashi, yayi murmushi tare dayi mata light kiss, yace ” ku tashi mu tafi, dan ina son mu iske Daddy a gida,
” ni a shirye nake mayafi kawai zan d’auko, yace ” ok nima a shirye nake, suka kalli Neelah, tace ” nima haka.

Motar Naufal nayin parking a harabar gidansu Mamy su Suhaila suka fito da gudu suna cewa ” oyoyo Yaya,
yana rungume dasu ya shiga cikin gida, while Umairah da Neelah suna biye dashi,
a parlor suka iske Daddy da Mamy zaune, cikin girmamawa suka zube k’asa suka gaida iyayen nasu, ganin haka yasa itama Neelah zubewa ta gaida su Mamy fuska a sake suka amsa musu,
Umairah ta kalli su Suhaira tace ” ga k’awa nan na kawo muku kuje ciki maza kuyi wasa,
gaba d’ayansu suka kama hannun Neelah suka shiga ciki da ita,
cikin nutsuwa Umairah tayiwa su Daddy bayanin komai, kasancewar su masu san mutane da taimako ne yasa suka ji dad’i sosai,
gaba d’aya suka amsa da Allah ya bamu ikon rik’e amanarta hannu bibbiyu,
Daddy yace ” ina ganin a saka ta a makarantar su Suhaima,
haka ma a sakata a islamiyarsu,  sosai Naufal yaji dad’in maganar Daddy, yayi kuma na’am da ita, Mamy tace ” inaga ganin a barta anan ta zauna tare dasu Suhaira zaifi,
idan tana ganin yara zata fi saurin sakin jikinta, Umairah tace ” no please Mamy ki barta can a wajen mu,
sai ta rink’a yin weekend a nan, Mamy tayi murmushi, tare da cewa nima na samu ‘yar uwa a family yanzu ba ni kad’ai ce bafulatana ba,
Daddy yace ” uhnnn abin nema ya samu, Mamy tana dariya ta kwalawa Neelah kira,
cikin girmamawa Neelah tazo Mamy ta mik’a mata hannu alamar tazo,
ba musu Neelah taje jikin Mamy, cikin harshen Fulatanci Mamy tace,
” shekararki nawa..!?

STORY CONTINUES BELOW


Sosai Neelah tayi mamakin jin Mamy na Fullanci tar daga ji ba koya tayi ba,
ganin mamaki k’arara a fuskar Neelah yasa Mamy yin dariya, 
tace ” nima Bafulana ce kamar ke, amma ni a Yola nake, 
tayi maganar cikin harshen Fulanci,  Neelah ta bata amsa  cikin fulanci  ” dama akwai Fulani a birni ma…!?

Mamy ta tuntsure da dariya, babu wanda yaji abinda suka ce sai dariyar da Mamy tayi,
kana tace ” sosai ma, ai babu inda babu Fulani cikin duniyar nan,
Neelah taji dad’i sosai jin ta samu mai jin fulatanci, cikin fullanci Mamy ta tambaye shekaratunta, da garinsu, ta bata amsa,
Mamy tace ” ki d’auke ni tamkar Dadanki kinji nima in sha Allah zan d’auke ki ‘yar ciki na, Neelah ta amsa da to,
Daddy yace ” to yau fa anga dangi sai abinda Allah yayi, Mamy tace ” nima haka kuke yi min kai da yaranka,
nima yanzu Allah ya bani ‘ya Bafulatana,
sosai su Suhaira sukayi ta wasa da Neelah itama ta saki jiki dasu sukayi ta wasa kamar ba bak’uwa ba,
sai yamma kana sukace zasu wuce kasuwa, Daddy ya bawa Umairah kud’i masu yawa yace tayi mata siyayya, 
sukayi godiya ita da Naufal, sosai aka jibgowa Neelah kaya kala-kala tun daga kayan sawa,
har zuwa kayan shafe-shafe, unders, kayan kwallliya, kayan bacci, k’ananan kaya, takalma, mayafai, hijabai, hand bag, etc,
basu dawo ba sai yamma lik’is, bayan sun biya sun kai wasu wajen d’inki, 
Umairah ta taya ta shirya kayan cikin wardrobe had’i da nuna mata yadda ake amfani da wasu daga ciki,
ta saka ta tayi wanka ta canja kaya, suka fito parlor suka zauna suna kallo.

BAYAN SATI BIYU

Duk wani shirye-shiryen makarantar boko da islamiyya Naufal ya gama yiwa Neelah shi,
har lesson teacher d’in an samu mata ya fara zuwa yana kowa mata a gida, kafin this coming Monday ta fara zuwa makaranta,
islamiyya kuwa tuni ta fara zuwa ajin su d’aya dasu Suhaila, haka ma an samar mata Malamin addini da zai rink’a zuwa gida yana koya mata,
daga b’angaren Neelah kuwa ta saki jikinta sosai, ta kwantar da hankalinta, 
ta mayar da hankali sosai kan karatun da ake koya mata, kasancewar she’s gifted,
yasa duk abinda aka koya mata take d’aukewa zama d’aya, ba’a tab’a koya maya abu sau biyu ba,
duk abinda aka koya mata sau d’aya ya shiga kanta kenan, dayake ta riga ta saka karatun a ranta,
ta k’uduri niyyar cimma burinta, ta saka a ranta karantun ne kad’ai zai taimaka mata wajen cimma burinta,
shiyasa bata bacci koda zata kai har asuba sai ta tabbatar ta haddace abinda aka koya mata,
abu d’aya ke damun Neelah kewar Dada da Abpanta, sai kuma rashin lafiyar da take fama da ita,
sama-sama cikin dare zazzab’i da ciwon kai yana yawan rufe ta, 
sannu a hankali rashin lafiyar ta soma cin jikinta, ta yadda har d’and’anon bakinta dana abinci ya d’auke mata,
kwata-kwata bata jin dad’in komai, bata sha’awar komai, Umairah da Naufal suna zaune saman dinning table,
suna cin abinci, Naufal yace ” lafiya kuwa Neelah har yanzu bata fito ba….!?

Kallan corridor’n da bedroom d’in Neelah yake  tayi kana tace ” inaga bacci take yi,
Naufal yace ” je ki dubo ta, babu musu Umairah ta mik’e ta nufi bedroom d’in Neelah,
da sauri ta k’arasa ganinta nannad’e cikin blanket tana ta rawar sanyi da kerrrrma,
cikin tashin hankali Umairah ta k’arasa gareta tare da tallafo ta,
tana tambayarta ” lafiya Neelah meke damunki….!?

Neelah na bud’e baki zatayi magana amai ya kwace mata, bayanta Umairah ta shiga shafawa,
batare data kula da jikinta da aman ya b’ata ba, sai da ta gama aman, 
ta d’ago kanta cikin sanyin jiki tace ” I sorry Unty, murmushi tayi mata cike da tausayawa danta fahimci tana san tace I’m sorry Aunty ne, kana ta d’auketa ta shiga bathroom ta gyara ta,
kana ta fito da ita ta canja mata kaya,
ta kalle tace ” dama baki da lafiya Neelah…!?

Cikin sanyin jiki ta d’aga mata kai alamar eh, ganin shiru yasa Naufal biyo bayan Umairah,
” lafiya kuwa…!?

Cewar Naufal yana shigowa, ” bata da lafiya sosai, Umairah tace kamar zatayi kuka,
” bata da lafiya…! meke damunta…!?

Yayi maganar yana ciro waya daga aljihunshi, ” wallahi ban sani ba, dialing number Nauman yayi, bugu d’aya ya d’aga, 
bayan sun gama gaisawa Naufal yace ” ga mu nan zuwa hospital yanzu, 
Nauman yace ” okey sai kun zo, kallanshi ya mayar kan Umairah yace ” jeki shirya ki fito mu kaita hospital, 
” ok, kawai tace ta fita, a hankali yakai hannunshi jikin Neelah da niyyar ya gyara mata kwanciyar,
mugun shock d’in daya ji ne ya sanya shi saurin janye hannunshi daga jikinta,
tare da d’an kallanta, da k’arfi yaji gabanshi yayi muguwar fad’uwa, 
a fili ya furta ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, dai-dai lokacin Umairah tana shigowa,
a firgice tace ” lafiya Naufal….!?

Dan tayi zaton ko mutuwa Neelah tayi, ” lafiya mana, yayi maganar yana k’ok’arin fita,
tace ” dan Allah d’auke ta bazata iya takawa ba, gabanshi ne ya kuma fad’uwa a karo na biyu kallan Umairah yayi yaga dukta tsatstsare shi da ido,
cikin sanyin jiki ya sanya hannu ya d’auki Neelah, tare da runtse idonshi da k’arfi saboda jin yadda bugun zuciyarshi ya tsananta,
a kujerar bayan mota ya kwantar da ita, kana ya zagaya ya shiga,
har suka k’arasa asibitin Naufal baice komai ba, sai Umairah dake ta faman shafa kanta tana jera mata sannu akai-akai,
Naufal na d’auke da Neelah a hannunshi suka shiga office d’in Nauman,
da sauri ya mik’e Naufal yayi saurin mik’a mishi Neelah, hannun Nauman naa tab’a Neelah yaji wani irin abu ya tsarga mishi tun daga tafin k’afarshi har zuwa tsakiyar kanshi,
har yana neman sakin Neelah, Naufal yayi saurin tare ta,
cikin kasala da mutuwar jiki Nauman ya kalli fuskarta da saman goshinta inda gashi ya kwanta,
a hankali ya motsa lips d’inshi yace ” masha Allah, Ubangiji yayi halitta anan,
Umairah tace ” please kaje a duba ta bata da lafiya,
murmushi Nauman yayi idonshi kan Neelah yace ” matar big Bros ina kika samu wannan kyakkyawar gasken….!?

” Queen of beauty, yayi maganar batare daya sani ba, Umairah tace ” dan Allah ka duba ta, tayi maganar da k’arfi,
sai lokacin Nauman ya dawo cikin hayyacinshi, tare da cewa ” sorry matar big Bros,
neman zaucewa nake yi dan naga wacce tafi kyau, kyau, yayi maganar yana fita, yayinda Naufal yabi bayanshi da wani irin kallo me wuyar fassarawa,
shi da kanshi ya shiga duba ta, sakamakon daya gani ne yayi masifar d’aga mishi hankali,
dan haka yayi tsammanin ko tun rud’ewar da yayi ne daga farkon ganinta,
dan haka ya kira nurse’s yace ” please ku duba ta sosai,
ya fad’a had’i da barin lab d’in, yana shiga Umairah tayi saurin mik’ewa,
tare da tambayar meke damunta, murmushi yayi yana shafa kanshi yace ” ai yau naga abinda ya rud’a ni har yasa na fice daga hayyaci na, 
yau naga zallar madarar kyau, sai yau naga MATAR DATA DACE DANI, TA KUMA DACE DANA AURA,
ido kawai Naufal ya zubawa Nauman batare dayace komai ba,
Nauman na cikin zuba Nurse ta shigo da sakamakon Neelah, 
da sauri ya mik’e ya amsa yana murmushi idonshi na sauka akan result d’in ya murtuke fuska,
tare da kallan Nurse d’in yace ” what…!?

“Kina hauka ne…!?

Da sauri Naufal da Umairah suka mik’e tsaye, Naufal yayi saurin wartar takardar daga hannun Nauman ya shiga dubawa,
sororo Naufal yayi batare daya iya furta koda kalma d’aya ba,
ganin tashin hankali ya bayyana b’aro-b’aro a fuskar Naufal da Nauman yasa hannun Umairah na rawa ta amshi takardar,
cikin hankali tace ” what…!?

“Me!?

” Kamar ciki nake gani ko!?

Tayi maganar a lokaci d’aya a rud’e,
“Ciki harna wata hud’u that’s impossible, k’ara k’arb’ar takardar Naufal yayi yana dubawa yaga  pregnant positive, har 4 months,
cikin mamaki Naufal yace ” ya za’ayi yarinya k’arama ‘yar 11 to 12yrs tayi ciki,
impossible, batare da Nauman yace komai ba ya fita, direct scanning room ya nufa tare da Neelah, 
koda ya d’ora scanner akan mararta k’iri-k’iri yaga d’a yana yawo,
ido kawai Nauman ya zubawa scanner minti d’aya zuwa biyu sayya maida kallanshi ga Neelah tare da sauke ajiyar zuciya,
yana cikin haka Naufal da Umairah suka shigo, muryar Umairah na rawa ta cewa Nauman ” ba gaskiya bane ba ko….!?

Sai da ya fitar da numfashi kafin yace ” uhummm had’i da nuna musu Babyn dake ta wutsil-wutsil cikin scanner,
yace ” ga tabbas kina gani wallahi ciki ne da ita harna watanni hud’u………….!Cikin tashin hankali da rud’ewa had’i da tsoro da firgici Umairah ta kalli Naufal tace ” ban gane ciki ne da ita ba, me kake nufi….!? +

Cikin rashin fahimta Naufal yace ” kamar yaya fa ban gane inda kika dosa ba….!?

A kid’ime Umairah tace ” ban gane baka gane ba, ina nufin waye yayi mata ciki…!?

Tayi maganar out of sense dan gaba d’aya ta gama fita daga hayyacinta,
tsayyawa Naufal ya gyara tare da kallan Neelah, ya kalli Nauman kana ya mayar da kallanshi ga Umairah,
yace ” tayaya za’ayi nasan wanda yayi mata ciki bayan tare na ganku,
ke fa kika kawo ta gidan ba ni ba, ko kin manta ne…!?

Kai Umairah ta dafe tana fitar da numfashi tace ” OMG!,
am very sorry dear wallahi rud’ewa nayi ne, but how…!?

” She’s just 11 to 12yrs fa impossible, Umairah ta fad’a tana kallan Nauman still tana dafe da kanta,
d’an kallan Neelah Nauman yayi kana yace ” babu impossible a al’amarin Ubangiji,
kada fa ki manta shine mai kumfa ya kum, daya ce kasance zai kasance,
dan haka ki nutsu ki dawo cikin hankali da hayyacinki, kada ki shiga hurumin Ubangiji,
abinda ya kamata mu fara tambaya cikin waye…!?

“Wa yayi mata cikin…!?

Jiki a sanyaye Naufal yace ” gaskiya nayi matuk’ar mamaki ace yarinya k’arama kamar wannan da ciki,
wannan rashin imanin ai yayi yawa, ya za’ayi mutum ya haik’ewa yarinya ‘yar 10yrs…!?

“Wallahi nima abinda yake bani mamaki kenan yana d’aure min kai, me mutum zaiji a jikin wannan fisabilillahi in banda rashin imani kawai…!?

Cewar Nauman idonshi kan Neelah, ” to amma dama is possible mace tayi ciki age of 11yrs….!?

Umairah ta fad’a tana yarfa hannu,
” sosai ma anyi haka yafi a irga, dan akwai youngest mothers in the world, 
a garin Peruvian akwai yarinyar me suna Lina Marcela Medina ta haihu a ranar 14 may a shekarar 1939, 
ta haifi d’a namiji mai suna Gerardo,
tana da shekaru biyar da watanni bakwai, da kwanaki 21, (5yrs 7months 21days,) 
an haifi Lina a shekarar 1933/23 September,
sannan akwai Liza Yelizaveta Pantueva ta haihu tana da shekara shida  a 19 August 1934, a k’asar Soviet wanda yanzu take matsayin Ukraine,
akwai Anna Mummenthaler ta haihu tana da 8yrs 9 months a 5 December 1759, a k’asar old Swiss wacce yanzu itace Switzerland,
anan k’asar mu  ta Nigeria ma an tab’a yin haka a shekarar 1884 da 1893 yara ‘yan 8yrs sun haihu, a garin Niger mai suna Mum-zi, da Zi, 
Estelle P 1908, ta haihu tana da 9yrs, a United kingdom, 
akwai Maria Eulalia Allende itama ta haihu tana da 9yrs, a Argentina,
Sally Deweese ta haihu tana da 10yrs a United state, wallahi idan nace zan kawo miki su sai mu kwana anan bamu gama ba,
dan akwai su da yawa sosai, daga 5yrs up to suna iya haihuwa sai dai idan Allah bai so ba,
amma kiyi browsing zaki gansu da yawa, cikin sanyin jiki Umairah tace ” amma da mamaki ace ‘yar 5yrs ta haihu,
” wannan ba abun mamaki bane, tunda mu musulmai ne, 
mun san Allah mai kowa mai komai yana iya yin abinda yafi haka,
Allah ne yaga damar azurta ta da haihuwa tunda k’arancin shekarunta,
kallan Neelah Umaira tayi tare da k’ak’aro murmushin k’arfin hali tace ” kin tab’a sanin namiji….!?

” A’a wannan wacce irin tambaya ce Umairah…!?

“Idan bata san namiji ba a ruwa tasha cikin….!?

STORY CONTINUES BELOW


” Ko kin tab’a ganin wacce tayi ciki haka nan, ko duk rud’ewar ce haka…!?

Naufal ya jera mata tambayoyin lokaci d’aya, kusa da Neelah taje ta zauna tare da jawo ta jikinta,
tace ” kina da aure….!?

“Cikin sanyin jiki ta d’aga mata kai alamar eh, ” what aure…!?

Naufal da Nauman suka fad’a lokaci d’aya a zabure, d’ago kai Umairah tayi ta kalle su,
tace ” eh haka al’adarsu take  kasan mutanan k’auye suna saurin yiwa yaransu aure,
gudun fad’awa zinace-zinace,   kuma Alhamdulillah hakan yana yin tasiri sosai,
Nauman yace ” amma gaskiya dai bai kamata ace ana yiwa yara aure suna da k’arancin shekaru haka ba,
kodan gujewa yoyon fitsari, da sauran cututtuka, ” a’a fa Nauman haka musulunci yazo dashi,
kuma haka Allah yace ayi, idan kuma zaka ja da cewar Allah ne to,
duk abinda Allah yace ayi yinsa shine mafi alkhairi a gare mu,
haka duk abinda yace kar muyi mukayi sai munga ba dai-dai ba,
yanzu da ana auren wurin da zinace-zinace, luwad’i da mad’igo basu yawaita a cikin al’umma ba,
” muryar Neelah na rawa irin ta marasa lafiya tace ” amma wanda aka aura min baya so na,
kuma bak’o ne, zuwa garin mu yayi, shine ranar da zai tafi ya saka min k’aton maciji anan d’ina,
tayi maganar tana nuna gabanta, dariya ce taso kufcewa Nauman da Naufal,
amma suka kanne, gudun karta kawo wani abun,
Umairah kuma ta had’e rai,  magunguna masu kyau Nauman ya bata, kana sukayi sallama.

Suna tafiya a mota Umairah ta kalli Naufal tace ” muje gidan su Mamy,
” gidan su Mamy kuma, muyi me acan…!?

Yayi maganar hankalinshi nakan tuk’in da yake yi,
” eh mana ai dole muje muyi musu bayani, dan bamu san abinda zasu ce ba,
batare da yayi magana ba ya karya motar ya nufi gida wajen su Daddy, 
a harabar gidan suka hango Daddy da Mamy tsaye da alama fita Daddy zayyi,
da sauri Naufal yayi parking ya fito Umairah da Neelah suka bi bayanshi,
ganinsu yasa Daddy tsayawa had’i da zuba musu ido suna jiran k’arasowar su,
Naufal na shirin durk’usawa Daddy ya mik’a mishi hannu suka gaisa,
kana  Naufal yace ” Daddy idan ba sauri kake yi ba, mu shiga ciki muyi ‘yar magana,
” komai saurin da nakeyi ai dole na saurare ka,
murmushi Naufal yayi had’i da cewa ” godiya nake my Dad,
gaba d’ayansu zaune a parlor  Daddy da Mamy sun zuba musu ido suna saurarn abinda zasu ce,
ajiyar zuciya Nauman ya sauke kana yace ” Daddy Neelah ciki ne da ita,
cikin rashin fahimta Daddy yace ” wacce Neelahn….!?

” Hummm Daddy wannan Neelahn yayi maganar yana nuna Neelah,
” ban gane ciki ba, wanne irin ciki badai na haihuwa ba ko….!?

Cewar Mamy cike da rashin gaskatawa, ” wallahi Mamy cikin haihu na ‘ya’ya,
yanzu daga hospital muke sai da aka gwada ta har sau uku amma duka sakamakon irin d’aya ne,
duk da haka Nauman bai gaskata ba sai da yayi mata scanning muka gani da idon mu,
shiru Dady yayi ya kasa magana, Mamy kuwa ido ta k’ura mata tana nazarinta,
kafin cikin harshen Fulatanci tace ” kina da aure ne Neelah…!?

“Eh..!, ta bawa Mamy amsa, cikin Fulatancin Mamy ta kuma cewa ” ina mijinki….!?

Cikin Fulatanci Neelah tace ” ya gudu ya barni, ” kamar yaya ya gudu ya barki….!?

Cewar Mamy, ” eh dama ba d’an garin mu bane, zuwa yayi shine aka aura min shi,
ranar da zai tafi shine ya saka min k’aton maciji da k’arfi anan d’ina,
tayi maganar tana nuna gabanta, ta cigaba da cewa ” sai da nayi kwana biyu ban farfad’o ba, 
ta fad’a cike da yarinta da k’auyanci, ” ya Salam! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,
wannan rashin imanin har ina, gaskiya wannan mijin naki ya cika mugu marar inami,
kwata-kwata bashi da tausayi, Allah ya saka miki, Ubangiji ya isar miki,
Allah ya d’and’ana mishi kwatankwacin rad’ad’in da kika ji,
kasancewar da fulanci suke maganar yasa babu wanda ya fahimci abinda suka ce,
ganin yadda fuskar Mamy ta sauya yasa Umairah cewa ” Mamy wani abun ne…!?

Cikin sanyin jiki Mamy ta gaya musu abinda Neelah ta fad’a mata,
gaba d’aya suka jajanta, Daddy ya sauke numfashi tare da kallan Neelah yace ” kiyi hak’uri da sannu Allah zai saka miki,
dan Ubangiji ba azzalumin sarki bane, baya zalunci baya barin ayi zalunci,
Neelah ta amsa da “to Abpa,  Naufal yace ” to Dady yanzu meye abin yi….!?

STORY CONTINUES BELOW


Numfashi Daddy ya fitar gami da d’an kallan Neelah kana yace ” dole aje a sanar da iyayenta,
kasan wasu mutanen akwai raguwar fahimta, kwata-kwata basu da fahimta,
muna iya barinta anan ta haihu a samu matsala,
ko iyayen nata suce anan akayi mata cikin, dan haka dole Umairah ke da Naufal da ita Neelah gobe kuje ku sanar da iyayenta,
idan sun amince ku dawo da ita, mu bama k’in mutane duk yawansu,
idan basu amince ba, ku barta bayan ta haihu sai ta dawo,
kuka Neelah ta saka jin abinda Dady yace, tana cewa ” ni ina san karatu, dan Allah ku taimaka min ku barni nayi karatu,
ta haka ne kawai zan cimma buri na na rama abinda d’an birni yayi min,
daga nan ta kwashe duk irin bak’ak’en maganganun daya rink’a gaya mata ta fad’a musu tas,
gaba d’aya suka jinjina kai suna mamakin wannan d’an birni, sunan da Neelah ke kiran Neehal dashi kenan,
Naufal yace ” amma wannan akwai tijararre d’an iska mara hankali,
waya san gobe, ai bai isa ya yanke hukuncin abinda zai samu rayuwarki ba,
gaskiya wannan baida hali, Allah nayi miki alk’awarin duk ranar da aka ganshi sai na kwatar miki ‘yancinki,
sai na rama miki duk abinda yayi miki shege marar mutunci marar tarbiyya wanda bai gaji arziki ba,
hannu Daddy ya d’agawa Naufal tare da cewa ya isa,
yayinda Mamy ta zuba mishi ido tana mamakin yadda ya fututtuke yana fad’a,
Daddy ya mayar da kallanshi ga Neelah yace ” karki damu kinji ‘yata,
in sha Allah zan tsaya miki kiyi karatu, ko iyayen naki basu barki kin dawo ba,
zan kai muku makarantu garinku, sannan nima da yardar Allah nayi miki alk’awarin,
duk ranar da mijinki ya dawo nima sai na rama miki kwatankwacin abinda yayi miki,
ajiyar zuciya ta sauke kana tace ” to nagode sosai, bayan sun gama tattaunawa Daddy ya fita,
su Umairah basu bar gidan ba sai dare, da safe suka bi jirgin Taraba,
daga airport direct garinsu Neelah suka nufa, sosai Naufal yayi mamakin yadda garinsu Neelah ke cikin surk’uk’i,
ganin an shigo garinsu yasa Neelah washe baki ta shiga murna tana dariya,
tana d’okin ganin Abpa da Dadanta, suna tsayawa Neelah ta fito da gudu ko bari motar ta k’arasa tsayawa batayi ba,
Abpa na alwala yayinda Dada ke dama fura suka hangi Neelah ta nufosu da gudu,
cike da murna Abpa ya mik’e yana dariya ya tari Neelah, tana isa gare shi ta fad’a jikinshi,
had’i da cewa ” nayi kewarka sosai Abpa’am, dariya yayi yana shafa kanta yace ” ni ma haka,
” mu da ba’ayi kewarmu ba mu munyi taki, cewar Dada, sakin Abpa Neelah tayi tana dariya ta nufi Dada,
Abpa na niyyar yin magana idonshi ya sauka akan Naufal, a fili ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa ” kai ne kuma…!?

“Ina kuka had’u..!?

Abpa yayi maganar idonshi kan Naufal, cikin rashin fahimtar inda maganar Abpa ta dosa yasa Naufal kallan Umaira,
itama ta kalleshi suka kalli juna, ” wannan shine miji na Naufal, Umairah ta fad’a tana murmushi, tsaida idonshi Abpa yayi akan Naufal na tsayin lokaci harya hak’ik’ance da ba Neehal bane,
danya ga bambamcin da Neelah ta gani tsakanin Neehal da Naufal
bayan an nutsa an kawowa su Umairah fura da nono da gashashshen nama,
sunci sunyi hani’an kana Naufal yayiwa Dada da Abpa bayanin komai.

” Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,
Allahumma ajirni fi musibati  wa’aklifni khairan min ha,
abinda Abpa yayi ta maimaitawa kenan har tsayin lokaci,
kana daga bisani, ya kalli Neelah tare da shafa kanta yace ” karki damu Neelah,
ke kuma irin taki k’addarar kenan, haka Allah ya tsara mana,
karki damu da sannu Allah zayyi maganinshi, ya kuma nuna mishi a kwaryar shansa,
nasan Allah baya tab’a yin abu babu dalili duk abinda kaga Allah yayi akwai dalilin dayasa yayi shi,
haka Allah baya d’orawa bawanshi abinda bazai iya ba, kai ta d’aga mishi duk da har lokacin Neelah bata fahimci akan abinda ake magana ba,
cikin sanyi da tausayawa Naufal yace ” to wai Malam ina mijin nata yake, kuma waye shi….!?

Batare da Abpa ya kalle shi ba yace ” muma bamu sani ba….!?

“Baku sani ba kamar ya…!?

Cewar Umairah, idon Abpa a k’asa dan kwata-kwata baya san kallan Naufal,
saboda tsananin kamar shi dayake yi da Neehal, dan gani yake tamkar Neehal d’inne,
dan da farko ma daya ganshi ya zata Neehal ne sai da ya nutsu yayi mishi kallan k’urulla kana ya gane kama ce kawai,
d’an d’ago kai Abpa yayi kana ya soma basu labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k’arshe,
ya kwashe komai tas ya fad’a musu, batare daya rage ko kalma d’aya ba,
” kam! amma wannan anyi mugun butulu, a ceci rayuwarka da auran yarinya amma kayi mata haka….!?

STORY CONTINUES BELOW


“Gaskiya wannan ko’ina ya fito ba cikekkan mutum bene, baida kyakkyawar zuciya,
wallahi Allah ko baku mishi Allah ya isa ba da sannu Allah zai isar muku,
Naufal yayi maganar cikin zafi, yayinda Umairah tayi jugum ta kasan furta koda kalma d’aya,
” bakomai akwai Allah kowa yayi nagari dan kanshi, Abpa ya fad’a cikin rawar murya kamar zayyi kuka,
Naufal yace ” kada ku damu in sha Allah ni da matata da iyayena zamu rik’e Neelah,
tamkar ‘yar cikin mu, zamu bata dukkan kulawa, zamu bata damarta a hannunta,
ta d’auki fansa kan wannan bak’in azzalumin mijin nata,
bayan sun gama tattaunawa Naufal yace ” to mu zamu koma, kuma da Neelah zamu tafi,
Abpa ya sauke numfashi tare da cewa ” a’a ku barta anan har zuwa ta haihu idan Allah ya sauke ta lafiya,
in yaso sai ta koma can birnin amma yanzu a barta anan,
” a’a Malam ka taimaka ka barmu mu tafi da ita, kaga Neelah yarinya ce k’arama,
wata k’ila haihuwar tana iya zuwar mata da matsala wacce ba’a fata,
kaga idan tana birni ai da sauk’i ko…!?

“Ku barta anan d’in in sha Allah babu wata damuwa, idan ta haihu aka nutsu,
sai ta bar abinda ta haifa anan ta koma, jin abinda Abpa ya fad’a yasa Neelah soma kuka,
tana cewa ” a’a Abpa’am dan Allah kada kayi min haka ka barni na koma kodan na cika buri na,
Allah Abpa’am harna fara karatu kuma ina ganewa sosai,
” ai ba hanaki komawa zanyi ba idan kika haihu zaki koma,
babu yadda Naufal da Umairah basu yi da Abpa kan ya barsu su koma da Neelah ba,
amma fafur yak’i, dole tasa suka hak’ura,  Neelah sai faman kuka take sosai ta rik’e Naufal da Umairah kam,
sai dakyar aka rabasu suka tafi, Umairah cike da tsantsar bak’in cikin rabuwa da Neelah,
a ranar suka koma Abuja, basu je gida sun sanar dasu Mamy ba sai washe gari,
Naufal ya sanar da Daddy da Mamy duk abinda Malam Liman ya sanar dashi kaf,
har fyad’en da mijin Neelah yayi mata, sosai sukayi ta taraddabin abun suka kuma tausaya mata,
had’i da nema mata sakayya a wajen Allah.

BAYAN SATI D’AYA

Cikin k’ank’anin lokaci gaba d’aya labarin dawowar Neelah ya cika k’auyen Sunkhanni,
jama’a suka d’auka taje birni tayi CIKIN SHEGE shine aka dawo da ita k’auyen,
tun ana rad’e-rad’in maganar a bayan idonsu Abpa har ma takai ga an fito fili ana fad’a,
ba hali Abpa ko Dada su shiga jama’a sai kaji ana yadda musu magana, 
Abpa zaune wajen Me gari anata ta hira, Abpa yayi jigum,
abun duniya ya isheshi, Me gari ya kalli Abpa yace ” Malam Liman,
shiru Abpa bai amsa ba, Me gari ya kuma kiran sunanshi, ” Malam Liman, 
amma shiru Abpa bai amsa ba, a hankali Me gari ya sanya sannu ya d’an tab’a Abpa,
yayi firgigit gami da cewa ” uhnnn, Me gari yace ” Malam Liman lafiya inata magana shiru….!?

Kafin Abpa yayi magana Hard’o yayi caraf ya amshe da cewa ” kaiko Me gari wannan wacce irin tambaya ce bayan kasan hali dayake ciki….!?

“Ai dole ka kanshi haka, mutumin da ‘yarshi ta fita yawan karuwanci ta dawo harda cikin shege,
ai dole ya shiga damuwa, Malam Liman zayyi magana wani daga gefe yayi amshe da cewa,
” abun kunyar da ba’a tab’a yinshi a cikin garin nan ba, amma gashi muna ji muna gani,
za’a kawo mana fasa gurbi ta b’ata mana yaranmu, da sunan garin mu,
abinda muke ji wai-wai a k’auyukan kewaye damu, yau muma shine ya shigo mana cikin garin mu,
ace yau a cikin k’auyen nan aka samu wacce tayi cikin shege za’a haifa mana d’an shege,
Hard’o yace ” ai wallahi kamata yayi a tsire su gaba d’ayansu, ko a jefe su,
wani yace ” ko ayi musu korar kare daga garin nan a kuma yi musu iyaka da garin  gaba d’aya zuri’arsu, 
haba wannan abun kunya har ina….!?

Cikin fad’a Jauro (likitan k’auyan) yace ” ku wad’anne irin mutane ne kamar kafirai…!?

“Wad’anda basu yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau ba,
wai ma uban waye yace muku cikin shege tayi….!?

” Yarinyar da anan gaban kowa da kowa kuka shaida d’aurin auranta, ko kun manta…!?

Hard’o yace ” kai dalla tafi can lusari asararre auren da akayi shi tun bara wancan shine batayi ciki ba sai yanzu dan an renawa mutane hankali za’a ce tayi ciki….!?

STORY CONTINUES BELOW


“To wai ma idan ance mijinta ne yayi mata ciki ina mijin nata yake….!?

Wani ya fad’a, Hard’o yace ” kai dalla rabu dasu wai mu za’a mayar sakarkaru,
mijinta baya dad’e da guduwa ba….!?

Cikin shak’iyanci wani yace ” a’a inaga a ruwa tasha ko kwantaccen ciki ne sai da taje birni kana ya tashi,
Hard’o ya tuntsure da dariya had’i da cewa ” nima ina ganin hakan ne,
kasa jure maganganun da suke jifanshi dasu ne yasa Abpa mik’ewa batare dayace komai ba ya bar wajen,
da sauri Jauro ya mik’e tare da kallansu yace ” ku dai Allah ya wadaranku wallahi,
kana yabi bayan Abpa da gudu Hard’o ya d’aga murya yace ” ka fad’a mishi sai munzo koyar yadda ake shan ciki a ruwa, yayi maganar cike da shak’iyanci, har bakin bukka Jauro ya raka Abpa yana bashi hak’uri had’i da kwantar mishi da hankali.

K’ASAR DUBAI, A BABBAN BIRININSU ABU DHABI

Sosai Neehal da Najwah suke more rayuwarsu, suna cin duniyarsu da tsinke,
hankalinsu kwance babu wani abu dayake damunsu, 
kwallo d’aya zaka yiwa ma’auratan ka fuskanci suna cikin dawwamamman farin ciki,
hankalinsu kwance suke rayuwa, suna karatunsu, gani nayi Neehal ya fito daga bathroom,
d’aure da towel a k’ugunshi, da alama daga wanka ya fito, 
cak ya tsaya had’i da kallan Najwah bakinshi bud’e cike da mamaki,
ta cikin mudubi ta hange shi tsaye ya kafe ta da ido, ido d’aya ta kashe mishi gami da cewa ” da wani abu ne….!?

K’ugunshi ya rik’e yana nufarta yace ” wai har yanzu baki gama shiryawa ba…!?

Rolling ido tayi had’i da cewa ” ji wai wanda ya fito daga wanka yana d’aure da towel shike cewa wanda ya saka kaya bai shirya ba,
tayi maganar tana dariya, isa yayi gareta cikin takunshi na isassun maza masu ji da kyau, kud’i da gata,
ya sanya hannunshi ya rungumota ta baya, ya zagayo da hannunshi kan cikinta yana shafawa,
ya d’ora hab’arshi kan hafad’arta yana murmushi yace ” amma ai kin san dole sai kin gama shiryawa kana zaki shirya ni ko…!?

” Kuma naga ke kanki baki gama shiryawar ba, balle azo kai na,
hannunta ta d’ora kan hannunshi dake saman cikinta,
tana dariya tace ” tab! kaima kasan ban iya shirya k’ato kamarka,
ido ya kafe ta dashi gami da maimaita k’ato, cikin ranshi,
a fili kuma yace ” waye k’aton…!?

Tana dariya tace ” kai mana,  tunda ka girma ai ka zama k’ato, 
d’an kallanta yayi na wucin gadi kana ya kawar da kanshi ya soma shiryawa,
har ya gama shiryawa bai kuma yi mata magana ba, 
tana zaune ya d’auko expensive perfumes d’inshi ya fesa,
ya fito d’as dashi tamkar wata daren goma sha hud’u,  kayan jikinsu iri d’aya sak shi yana sanye da cot black color,
neck tie & abun gaban aljihunshi red color, gashin kanshi yasha gyara yayi luf-luf dashi,
zallar madarar kyau da yarintarshi sun fito, while Najwah ta sanya gown mai red & black color,
gown d’in marar hannu doguwa har tana jan k’asa,  ta d’aure gashin kanta da red ribbon, 
sosai itama tayi kyau,  da gani fita zasu yi ta musamman, hannunta sak’ale da nashi, suka fita,
driver na ganinsu ya taso jiki na tsuma dan gaba d’aya ma’aikatan gudan sun san halin Najwah,
jiki na rawa driver ya bud’e musu mota suka shiga, ya bud’e ya shiga ya zauna a mazaunin driver,
cikin girmamawa yace ” ina zamu je Yallab’ai….!?

Invitation card d’in da aka basu na gayyatar birthday d’in ‘yar shugaban makarantarsu,
(Abu Dhabi University Dubai) ya d’auko ya duba  inda za’ayi party birthday d’in,
kana yayiwa driver bayanin wajen, tunda Neehal da Najwah suke a rayuwarsu basu tab’a ganin wajen,
daya tsaru yayi kyau sosai ya k’awatar kamar wajen da aka tana danyin birthday d’in BASRAH ba,
suna sak’ale da juna suka shiga, duk da wayancin wad’anda suke wajen,
fararen fata ne, haka bai hana Neehal d’aukar hankalinsu na, 
fuskar Basrah cike da fara’a ta nufo su Neehal tana cewa ” wow…! masha Allah alaika ya Muhammad,
k’ayataccen murmushinshi yayi wanda ya k’ara bayyanar da kyanshi,
kusan gaba d’aya matan Larabawa da Turawa & Indiyawa hankalinsu ya koma kan Neehal,
ganin irin kallan da ake yi mishi yasa Najwah k’ara matse shi gam,
k’asa yayi da muryarshi yadda babu me jin abinda zaice sai Najwah,
yace ” kiyi controlling kishin ki, komai kika ga sunyi su a wajen su ba komai bane, 
al’adarsu ce haka,
fuska ta b’ata tare da cewa ” al’adarsu ce kallan mazan mutane…!?

“Suje can suyi abunsu ni dai karsu sake su tab’a min miji na, wallahi inba haka ba, suga ruwan tijara,
murmushi yayi tare da cewa ” tijara…!, wacce irin tijara kuma….!?

“Ka bari idan sun tab’a ka sai ka gani,  ” hummm wallahi ki kama kanki a wajen nan,
Ta bud’e baki zatayi magana MC ya soma magana da microphone cikin harshen turanci,
” hey..! Ladies & gentleman silent please, gaba d’aya akayi shiru,
kana ya cigaba da cewa ” yanzu in sha Allah Basrah zata yanka cake, 
yayi maganar yana nuna Basrah dake tsaye gaban cake, k’awayenta na zagaye da ita,
tafi aka fara ana yi mata wak’ar ” happy birthday to you”,
cikin nutsuwa fuskarta d’auke da fara’a ta yanka cake d’in,
a baki ta bawa k’awayenta dake zagaye da ita, suma suka bata, ana ta tafi,
cake d’in ta yanka ta nufi Neehal dake tsaye sak’ale da hannun Najwah,
ganin ta nufo shi gadan-gadan yasa gaban Neehal mahaukaciyar fad’uwa,
a tsorace ya kalli Najwah kana ya mayar da kallanshi ga Basrah, dake takuwa cikin takunta me jan hankali,
kallanshi ya mayar ga Najwah yace ” please karkiyi yunk’urin komai, 
kallan Basrah tayi data kafe Neehal da ido tana sakar mishi shu’umin murmushi,
murmushi itama Najwah tayi had’i sa gyara tsaiwarta tana jiran k’arasowar Basrah,
gam Neehal yayi mata mugun rik’o yadda bazata iya kwacewa ba,
idonshi kan Basrah yana murmushin yak’e, Basrah na dariya ta sakawa Neehal cake d’in a baki,
had’i da shafe sauran cake d’in a fuskarshi tana dariya, gaba d’aya wajen aka d’auki tafi raf-raf-raf,
take fuskar Najwah ta soma canjawa, kalar kwayar idonta ta rikid’e zuwa ja,
gashin dake jikinta suka mimmik’e tsaye, still Neehal na rik’e da ita gam,
bayan an gama yanka cake anci an sha, MC ya sanar da za’a soma rawa,
dum light aka mayar da hasken wajen, DJ ya saki kid’a, kowa ya soma takawa, kamar dai yadda kuke gani anayi a clubs,
Neehal na rik’e da Najwah suna d’an takawa suna rawa, ya soma yi mata magana k’asa-k’asa,
” please Najwah kiyi controlling kanki danni kawai, 
ki taimaka ki kawar da kanki na rana d’aya kawai please, yayi maganar while suna rawa,
ta bud’e baki zatayi magana Basrah ta iso wajensu hannunta d’aya d’auke da glass cup tana shan ruwan inibi,
cikin salon d’aukar hankali da shigar jikinta dake kusan tsirara,
ta kalli Neehal ido cikin ido tana murmushi, kana ta mayar da kallanta ga Najwah cikin harshen turanci tace,
” please ki bani aron shi na minti kad’an muyi rawa, ta fad’a care free kasancewar su a wajen su wannan ba komai bane,
ba kuma abun damuwa bane, ba wai da wani abu ko wata manufa cikin ranta ba,
murmushin yak’e Neehal yayi tare da cewa ” no bana rawa da mata,
martanin murmushin ta mayar mishi had’i da bawa service d’in wajen glass cup d’in dake hannunta,
kana ta rik’o Neehal tana cewa ” common handsome, tayi maganar in sexy way,
Basrah ta d’auki hannun Neehal d’aya ta d’ora saman k’ugunta,
ta d’ora d’aya saman kafad’arta, kana ta rungume shi suka soma takawa, 
ido Najwah ta kafe su dashi zuciyarta na tafarfasa, zafi da rad’ad’in zuciyarta na azalzalarta,
idonta suka koma asalin jajaye kamar gauta, take gumi ya soma keto mata, lips ta cije da k’arfi har tana jiwa kanta ciwo,
amma kwata-kwata bata kula da yadda ta taune lips d’inta jini na zuba ba,
idonta na kafe kan hannun Neehal dake saman k’ugun Basrah, da yadda Basrah ke rungume dashi,
guntun murmushi ta saki lokacin da idonta ya sauka akan wuk’ar da aka yanka cake,
a hankali ta isa wajen wuk’ar take, ta sanya hannu ta d’auka,
had’i da k’ura mata ido tana juya ta, murmushi ta kuma saki a karo na biyu,
kana ta nufi Basrah, hankalin kowa yayi soma kwata-kwata babu wanda ya kula da Najwah,
Neehal na k’ok’arin kwace jikinshi daga Basrah ya hango Najwah ta nufo su gadan-gadan rik’e da wuk’a,
ido ya zaro cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, amma kafin yayi wani yunk’uri Najwah iso garesu,
had’i da cakawa Basrah wuk’ar, ba zato ba tsammani Basrah taji wuk’a ta lume a jikinta,
tsananin azaba ne ya sanya ta sakin gigitacciyar k’ara wacce tasa kowa tsayawa cak…………………!Sai lokacin hankalin kowa yakai kansu Neehal har suka lura da abinda ke faruwa,
cikin kad’uwa Neehal ya sanya duka hannayenshi ya toshe bakinshi,
tare da kwalalo dararan idanuwanshi waje kamar zasu fad’o k’asa,
gaba d’aya mutanen dake hall d’in suka d’ora hannu aka had’i da bud’e baki,
cikin sanyi Basrah ta sanya hannu ta shafo jinin dake zuba daga jikinta,
had’i da kallan jinin, muryarta na rawa tace ” it’s my blood, tayi maganar tana zubewa k’asa a sume,
cikin zafin nama Neehal ya sanya hannu ya tare ta, cikin k’ank’anin lokaci Ambulance da motar police suka iso wajen a tare,
batare da b’ata lokaci ba aka d’auki Basrah aka sakata cikin motar,
gami da manna mata Oxygen dan sun lura bata numfashi,
yayinda police suka fara cikiniya da Najwah wajen kama ta,
sosai ta shiga turje-turje tana tujewa, wai ita baza’a kamata ba,
ganin ana k’ok’arin tafiya da Najwah yasa Neehal saurin mik’ewa,
ya isa wajen police d’in yana yi musu magana amma ko kallanshi babu wanda yayi,
da k’arfi Najwah ta rik’e Neehal had’i da sanya kuka tana cewa ” dan Allah kayi musu magana karsu raba ni dakai please,
wallahi zan iya mutuwa idan suka ce zasu raba ni dakai, suna janta, while Neehal yana binsu,
d’aya daga cikin mutanen dake wajen ne ya isa ga Neehal ya rad’a mishi,
” kayi mata magana, kuma kaima ka nutsu, wallahi in banda ma ita mace ce sun san daraja da k’imar mace da tuni sunyi maganinta,
kayi mata magana ta nutsu ta bari a kamata dan tuhumarta ake yi da laifin kissan kai,
kasan wannan k’asar ba irin k’asar ku bace, ko d’an sarkin Dubai ne yayi abinda tayi sai an kamashi an hukunta shi,
dan haka kayi mata magana karta k’arawa kanta laifin sa’insa da hukuma,
cikin sanyin jiki Neehal ya saki Najwah, yana ji yana gani tana ihuuu tare da mik’o mishi hannu aka dannata cikin motar ‘yan sanda,
suka tafi da ita, jikinshi na kerrrrma ya nufi mota, driver na ganinshi ya taso,
gabanshi na dukan uku-uku dan kallo d’aya zaka yiwa Neehal kasan babu lafiya,
batare da yayiwa driver magana ba, ya mik’a mishi hannu, kamar driver yasan abinda yake nufi ya mik’a mishi key d’in mota,
Neehal ya shiga had’i da figar matar kamar wanda zai tashi sama yabi bayan su Najwah. +

Lokaci d’aya suka isa police station d’in, da sauri Neehal ya bud’e motar ya fita baiko tsaya rufewa ba,
cikin cell aka saka Najwah, tana ta kuka duk da bata yi danamar abinda ta aikata ba,
hannu ta shiga mik’owa Neehal ta tsakanin k’arfunan cell tana cewa ” please heartbeat ka fitar dani daga nan,
bazan iya kwana anan kai kana can ba, kada wata ta bika ku kwana tare,
halin da Neehal yake ciki bai hanashi jin zafin kalmar Najwah ta k’arshe ba,
ido ya kafe ta dashi na d’an lokaci kafin yace ” ke kin fi kowa sanin ni ba fasik’i bane,
ba kuma mazinaci bane, wallahi irin abubuwan nan da kike yi suna k’ona min rai Najwah,
da wanne kike san naji yanzu, da k’ok’arin fitar dake daga nan….!?

“Ko da Basrah da kika cakawa wuk’a, ko kuwa da ciwon kan da kike bani….!?

” Allah ya sani kina bani ciwon kai Najwah I’m very tired, 
yayi maganar cike da k’osawa, zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu,
had’i da cewa ” enough..! enough Najwah, yayi maganar yana kawar da kanshi gefe,
dan be iya kallan kwayar idonta yayi mata fad’a, cikin nutsuwa ya isa gaban DPO dake zaune yana kallansu,
babu irin rok’o da magiyar da Neehal bayyi kan abashi belin Najwah ba amma DOP ya hanashi,
yace ” kayi hak’uri bani da ikon baka matarka saboda laifin data aikata yana da girma a dokar k’asar nan,
dole sai an jira anga abinda ya samu Basrah Al-shamry, 
babu wani abu da za’a iyayi har sai an jira anga warkewarta,
kana daga baya kuje kotu, idan kuka yi sa’a Basrah Al-shamry ta yafe mata,
ces d’inta zaizo da sauk’i laifinta zai ragu, sai dai kawai kuyi magana da Human Right ta k’asa,
kasancewar tana da hakk’i kan kowanne d’an k’asa, idan aka yi abu koda mutum ya yafe dole Human Right tana da hakk’i,
dole tasa Neehal hak’ura dan duk inda ya buga babu sauk’i, baibar police station d’in ba sai 12:30 na dare, Najwah na ganin zai fita ta fasa kuka, tana kiran sunanshi,
batare daya juyo ba yayi ficewarshi, daga police station direct hospital ya nufa wajen Basrah, ya iske kusan gaba d’aya ahalinsu a hospital d’in,
cikin nutsuwa da sanyin jiki Neehal ya k’arasa wajen ya mik’awa mahaifin Basrah da sauran mazan dake wajen hannu suka gaisa,
suka amsa mishi ba yabo ba fallasa, cikin harshen turanci ya shiga basu hak’uri,
a tak’aice mahaifin Basrah yace ” please ka bari ta farfad’o tukunna,
Neehal ya bud’e baki zayyi magana Abbun Basrah ya d’aga mishi hannu,
batare daya kuma magna ba ya koma gefe dasu ya zauna, baibar wajen ba sai da aka kira sallar asuba, 
kana yayi musu sallama, ya fita, a masallacin dake cikin hospital d’in yayi sallah kana yayi gida,
duk da yana matuk’ar cikin b’acin rai da damuwa hakan bai hana shi missing Najwah ba,
a parlor saman sofa ya zube had’i da d’aga kanshi sama idanuwanshi lumshe,
kasancewar bai samu bacci ba yasa bai jima ba bacci yayi awon gaba dashi,
cikin baccinshi yayi mafarkin Neelah tsaye cikin mawuyacin hali,
dakyar ta d’ga hannunta ta shiga mik’o mishi hannunta cikin matsanancin kuka,
tana cewa ” ka taimake ni, ina buk’atar taimakonka, dan Allah ka taimake ni,
tana daga kwancen tana mik’o mishi hannu yaga wasu irin mutane masu wasu irin halitta,
sun zo kanta suna tuntsura dariya had’i da cewa ” taimakon wa kike nema….!?

STORY CONTINUES BELOW


“In dai daga wajen wannan bak’in azzalumin kike neman taimako bazai tab’a taimaka miki ba,
suna maganar Neelah na cigaba da cewa ” ka taimake ni, ka taimake ni,
gaba d’aya mutanen suka b’ata rai gami da cewa ” bazaki daina neman taimakon shi ba…!?

Still Neelah batayi shiru ba, a zuciya d’aya daga cikin mutanen ya d’aga ta ya fyad’a da k’asa,
matsanancin ihu tayi da tsananin tace ” Allah ya isa tsakani na dakai,
d’aya daga cikin mutanen ya kalli Neehal fuska a had’e yace ” ta tafi ta barka sai ka rayuwa a duniya cikin kwanciyar hankali in gani,
yayi maganar had’i da kwad’awa Neehal mahaukacin rodi aka,
a haukace Neehal ya farka yana shafa kanshi, had’i da ambatun sunan Allah,
ya jima haka kafin nutsuwar shi ta dawo jikinshi, cikin sanyin jiki ya kalli agogon bangon dake manne a parlor’n,
ganin k’arfe tara saura ya sashi sauran mik’ewa ya shiga bathroom ya watsa ruwa a gaggauce,
da hanzari ya shirya ya fita ko breakfast bai tsaya yayi ba, 
hospital ya fara zuwa ya iske har lokacin Basrah bata farfad’o ba,
bai bar asibitin ba sai da akayi sallar azhur kana yayi musu sallama ya tafi,
daga nan police station ya wuce, koda ya isa iskewa yayi har lokacin Najwah bata bar kuka ba,
kallo d’aya yayi mata yaji tausayinta ya kama duk ilahirin jikinshi,
taci kuka ta gadewa Allah idanuwanta sunyi luhu-luhu sun kumbura sumtum,
a hankali ya k’arasa gareta ya tsaya gabanta, yana kallanta, cikin b’acin rai ya had’iye k’ululun bak’in cikin daya tokare mishi mak’ogwaro,
yau Najwahnshi rufe a cikin cell yana ji yana gani amma babu yadda zayyi,
a hankali ya zura hannunshi ta tsakanin k’arfunan cell ya shiga goge mata hawayen fuskarta,
yana cewa ” shhhhhhh ya isa haka, kiyi shiru kinji my heartbeat,
kin san babu abinda nafi tsana a rayuwata kamar na ganki cikin damuwa,
balle har naga hawayenki yana zuba, so please kiyi hak’uri ki daina kukan,
ki dage da addu’a da rok’on Allah in sha komai zaizo da sauk’i,
cikin sanyin jiki ta d’aga kanta, cikin muryar kuka tace ” dan Allah kayi k’ok’arin ka fitar dani daga nan,
bana san rayuwa babu kai babu abinda nafi tsana kamar nayi nesa dakai,
gani nake kamar idan nayi nesa dakai hakan ne zai bawa wata mace damar shiga jikinka,
fuska ya tsuke tare da janye hannunshi daga saman kumatunta daya tallafe fuskarta,
da sauri ta kuma rik’o hannun nashi daya zame, tace ” I’m sorry dear,
d’an guntun murmushi yayi mata had’i da jinjina kanshi, haka Neehal yayi ta zarya tsakanin police station da hospital har tsayin sati biyu,
amma Basrah bata farfad’o ba, sai a randa ta shika sati biyu a kwance ta farfad’o,
Neehal na reception shida wasu daga cikin danginta,
yaji ana sanar dasu Basrah ta farfad’o, da sauri ya mik’e jikinshi na tsuma ya nufi d’akin datake kwance,
koda yaje zai shiga dakatar dashi wani daga cikin ‘yan uwan Basrah yayi,
Neehal yace ” please ka barni na shiga naga halin datake ciki mana,
mutumin yace ” idan ka shiga me zakayi mata….!?

“Lafiya zaka bata ko ko kana san ka k’arasa ta ne….!?

Mutumin yayi maganar yana huci, Neehal yace ” ya kamata ku gane it’s not my fault,
mutumin zayyi magana Basrah ta bud’e baki dakyar cikin harshen larabci tace ” meyasa haka ne Ammu…!?

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta d’ora da cewa ” dan Allah ka barshi ya shigo,
batare da mutumin ya k’ara cewa komai ba ya matsa Neehal ya shiga,
mahaifinta da mahaifiyarta tare da wasu daga cikin danginta, sun zagaye ta,
suna had’a ido da Neehal ta sakar mishi murmushi, ta yunk’ura tana k’ok’arin tashi,
da sauri mahaifiyarta ta kama ta, ta zauna ta tallafe mata bayanta da pillow,
cikin karaya da irin kallan da ‘yan uwan Basrah ke jifanshi dashi,
ya k’ak’aro murmushin k’arfin hali, cikin harshen turanci yace” sannu ya jikin naki…!?

“Alhamdulillah idonta kanshi, Allah ya baki lafiya, ta amsa da ” amin ya Allah,
cikin sanyin murya yace ” I’m very sorry Basrah, wallahi bada….!, dakatar dashi ta ta hanyar cewa, ” karka damu ba komai,
komai ka gani ya faru muk’addari ne daga Allah,
Allah ya riga ya tsara dole hakan saita faru, dan haka babu wanda ya isa ya canja,
dukkanin mu kuma musulmai ne mun yarda da k’addara mai kyau ko mara kyau,
Amminta zayyi magana tace ” please a’a Ammi, koda munce dole sai an d’auki mataki akan matarshi, me hakan zai canja….!?

STORY CONTINUES BELOW


“Dame zai amfane mu, wacce riba zamu samu, ko zai bani lafiya ne, ko ko zai dawo da jiya ta zama yau….!?

Ta jefawa gaba d’aya ahalinta tambayar, dukkansu sukayi shiru babu wanda yace k’ala,
ta cigaba da magana ” hakan babu abinda zai jawo mana sai surutu da ci baya,
ace munyi shari’a da bak’on mu, ace muna shari’a da d’alibin makarantar mu,
ko yanzu nasan matarshi ta d’auki darasi a rayuwar ta, kuma nima na d’auki nawa darasin,
so please kuyi hak’uri dan…. sallamar police ce ta katse Basrah,
bayan sun gaisa sunyi mata ya jiki, kana suka tambaye ta kan maganar shari’a,
Basrah tace babu komai ta yafe, suka k’ara tambayarta ta tabbatar musu da ta yafe,
kallansu suka mayar da Neehal suka ce ” ka godewa Allah ta yafe maka, yanzu sauranka da human right kawai,
Basrah tace ” suma human right d’in ace musu na yafe, ba sai sun wahalar da kansu ba, 
d’aya daga cikin ‘yan sandan yace ” wannan baki da iko akai, dan itama tana da hakk’i akan duk abinda ya shafi k’asarta da dan k’asar,
dole tasa Basrah ta sanya mahaifinta ya tsayawa Neehal a wajen human right,
har aka samu komai ya dai-daita, sai dai hukumar k’asa ta haramta musu shigowa Dubai har tsayin shekaru uku,
haka kuma an kore su daga makaranta saboda matarshi tayi ta’addanci,
ta fito da makami cikin taron mutane, wannan hukuncin da aka yanke musu ma,
dan su musulmai ne, sun kuma yi sa’a k’asar musulunci ce,
da sauran k’arashen duniya ne da sai abinda Allah yayi, a haka ma duk ranar da zasu k’ara shigowa Dubai bayan 3yrs,
sole sai sun rubutu apologise letter daga Nigerian Embassy zuwa Dubai Embassy,
ba’a fi sati d’aya da sakin Najwah ba suka dawo Nigeria, tun suna Dubai Daddy ya samu labarin abinda ke faruwa,
amma ko da suka dawo bai nunawa Neehal ya san komai ba, ido kawai ya zuba mishi yana san ganin iya gudun ruwansu,
Neehal, Naufal da Najwah na zaune gaba d’ayansu a dinning table a gidan su Mamy,
har Mamy ana cin abincin ana hira, Daddy ya fito daga b’angaren shi, da alama fita zayyi,
Mamy ta d’an kalle shi tare da cewa ” Alhaji fita zakayi baka karya ba…!?

“Da anyi niyyar bani ai da an kirawo ni, ido ya rufe anga ‘ya’ya, sai da akaga zan fita sannan za’a yi min tayin rowa,
yayi maganar cikin barkwanci, ” ayi min afuwa, a taimaka min azo aci abincin nan,
murmushi yayi yana zama kan d’aya daga cikin kujerun yana cewa ” to tunda an rok’e ni bari na ci,
amma da ba’a bani hak’uri ba da ban ci, Naufal yace ” Daddy nasan bazaka iya fita batare daka ci abinci Mamy ba,
” au haka ma zaka ce, to bari ka gani, yayi maganar yana mik’ewa, 
Neehal yayi saurin tare shi yana dariya yace ” rabu dashi Daddy na,
sai da dai aka rok’e ka zaka ci, Mamy tayi murmushi had’i da cewa, 
” duk matar da bata san hidima da buk’atun mijinta ba mata ta rako duniya,
tayi maganar tana kallan Najwah, tare dayi mata hannunka me sanda,
amma kwata-kwata bata fahimci inda maganar Mamy ta dosa ba,
Daddy ya kai colaki d’aya na abinci bakinshi tare da cewa ” Son yaushe zaku koma makaranta ne….!?

Yayi maganar idonshi kan Neehal, kallan juna Neehal da Najwah sukayi,
kana cikin rawar murya Neehal yace ” sai after 1 month,
murmushi Daddy yayi irin nasu na manya yace ” Allah ya kaimu,
yayi maganar batare daya kalli Neehal ba, yayinda Najwah keta aikin zare ido,
aje spoon Neehal yayi had’i da mik’ewa yabar wajen, Daddy yabi bayanshi da kallo, cikin ranshi yace ” yaro dai yaro ne,
direct part d’inshi ya wuce ya shige bedroom ya kwanta saman Italian royal bed,
idonshi na kallan sama ya fad’a duniyar tunanin abinyi da mafita,
danya tabbatar muddin Daddy yasan abinda ya faru sun gama karatu kenan har abada,
a hankali ya mik’e ya soma kai komo dan ya rasa mafita,
ganin an d’auki lokaci ya rasa mafita yasa shi kiran Nauman a waya,
Nauman nayin nayin picking wayar Neehal yace ” kana ina aboki na….!?

” Gani a gida amma yanzu zan fita zuwa Shagalinku, ” okey to biyo ka d’auke ni, ” gani nan, kawai Nauman yace had’i da dropping wayar,
ba’a d’auki lokaci ba Nauman ya k’araso ya kira Neehal a waya ya sanar dashi yana bakin get,
fita yayi ya bud’e gaban moyar Nauman ya zauna, tare da kwantar da kujerar motar ya kishingid’a,
ya d’ora hannunshi saman goshi, ganin yanayin abokin nashi ya tabbatar mishi akwai wani abu a k’asa,
d’an kallanshi Nauman yayi kana yace ” lafiya dai Aboki…!?

Tsoki Neehal yaja yana kawar da kanshi gefe, cikin sanyin murya yace ” wallahi ina cikin matsala ne,
” Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, wacce irin matsala Aboki…!?

” Najwah ce ke neman d’ora min ciwon zuciya wallahi, ” ta d’ora maka kodai ka d’orawa kanka….!?

“Ba an gaya maka yadda zaka yi maganinta ka kasa ba, sai kayi ta zama da ita haka,
bak’in cikinta ya kashe ka itako taje tayi wani auren tunda haka ka zab’a,
dukkansu shiru sukayi kana can Nauman ya numfasa yace ” uban me ta kuma yi yanzu….!?

Idon Neehal lumshe ya sanar da Nauman duk abinda ke faruwa,
” kambu lalle wannan karan ta taro match, ku da Daddy ba ruwa na,
Nauman ya fad’a yana yin parking a harabar Shagalinku, ” muje ko…!?

Nauman yace yana fita, tsoki Neehal yaja kana ya fita, suna zama service yazo ya tambaye su abinda suke so,
Nauman ya bada oder, kana ya kalli Neehal yace ” ranka ya dad’e mijin Najwah me za’a kawo….!?

Kallan banza Neehal ya watsawa Nauman had’i da cewa ” an gaya maka ni irinka ne…!?

Cikin dariya Nauman yace ” iri na dame..!?

“Meye banbancin dake tsakani na dakai…!?

” Yadda nake yawon cin abinci a titi haka kaima kake yi, har gwara ni ma ace bani da mata,
amma kai wai nan sunan kana da aure, harara Neehal ya k’ara watsawa Nauman batare dayayi magana ba,
” ayi hak’uri Angon Najwah bani nakar zomon ba rataya aka bani,
” kaga zaka ban shawara ko sani gaba zakayi kana tsokana…!?

“Wa ni zan baka shawara….!?

” Tab…! kaje ka nemi me baka shawara tun dare bayyi maka ba, 
ku da Daddy ba ruwa na bazan bada shawara ba abu ya kwab’e a had’a ni da ubana,
” please aboki na ba maganar wasa nake yi maka ba, wallahi ina cikin matsala kasan idan Daddy ya sani akwai damuwa,
shiru Nauman yayi na tsayin lokaci kafin yace ” why bazaka nemar muku Oxford University America ba,
ka nemar muku the same course da kuka soma yi a Dubai wanda Dady ya sani…..!?

Baki Neehal ya washe cikin farin ciki yace ” wow! Aboki na shiyasa nake san yin shawara dakai,
saboda kana da kwanya , sai dai wani hanzari ba gudu ba kana ganin za’ayi komai a gama nan da 1 month dan nayiwa Daddy k’aryar nan da wata d’aya zamu koma….!?

“Why not…!?

” Sosai ma kuwa hakan zata yiyu, ka bari gobe sai mu fara processing ko….!?

“Allah ya mu cewar Neehal yana sauke ajiyar zuciya while idonshi kan Nauman, Nauman yace ” aboki na ni da naga samu naga rashi,
cikin rashin fahimtar inda maganar Nauman ta dosa Neehal yace ” ban gane ba…!?

“Wallahi wata yarinya na gani fara sol bafulatana, daga kallo d’aya na kamu,
naji farat d’aya so da matsananciyar k’aunarta sun shige ni,
Allah ban tab’a jin son mace kamar yadda naji na yarinyar nan ba,
take naji na samu macen aure dan irin kalar matan danake so ce,
” ikon Allah yau Nauman da maganar mace har da aure, lalle wannan ta cika a kirata da *TUTAR MATA*,
tunda har ta zauta aboki na daga kallo d’aya, a ina take….!?

“Matar Big B ta taho da ita daga yawan k’auyukan da take yi,
da k’arfi gaban Neehal ya buga danya tuna lokacin da Umairah take sanar da Daddy,
wannan karon Hard’o-Koa’la zasu je, bakin Neehal na rawa yace ” daga wanne gari ta taho da ita…..!?

D’an shiru Nauman yayi yana tunani kafin yace ” Taraba, a k’aramar Hard’o-Koa’la,
” ya sunanta….!?

Neehal yace bakinshi na rawa, cikin takaici Nauman yayi kwafa tare da cewa bari kaidai kawai abokina,
ai baka san babban abin bak’in cikin ba, sai dana gama aiyana irin rayuwar soyayyar da zamuyi,
me cike da farin ciki naga samu da rashi, ” nace maka ya sunanta ?

Nehal ya kuma tambayar Nauman, murmushi Nauman yace …………………..!!Murmushi Nauman yayi had’i da cewa ” ban san sunanta ba,
Neehal yace ” please ka tuna mana, Nauman yayi shiru yana tunani, 
amma ya kasa tuno sunan Neelah, kanshi ya girgiza a hankali yana cewa ” wallahi na kasa tuna sunanta,
a fili Neehal ya sauke ajiyar zuciya batare daya ce komai ba, har Nauman ya gama cin abincin Neehal bai kuma cewa komai ba,
washe gari Neehal da Nauman suka bazama Neeman admission a Oxford university,
Allah ya taimaki Neehal cikin sati biyu an shiga na uku suka gama komai,
while duk abinda suke Daddy na sane dasu, ido ya zuba musu,
bayan Neehal ya gama komai da komai, ya sanar da Najwah sosai tayi farin cikin jin zasu koma karatu,
koda Neehal ya sanar da Daddy cewa  next week yake son su kuma Dubai makaranta Daddy bai nuna mishi komai ba,
yayi mishi addu’ar fatan alkhairi, ya amsa da amin, bayan kwana hud’u jirgin su Neehal ya d’aga zuwa America. +

************************************

Sunkhanni

Duk inda kake tunanin k’unci da matsatsin rayuwa Neelah ta shiga,
sosai take cikin damuwa dan ba hali ta fito ko kewayen bukkarsu sai yara su biyo ta suna yi mata ihun tayi cikin shige,
dole ta koma zaman bukka, ya zama na ko k’ofar bukkarsu bata fitowa,
idan kaga ta fito daji zata je idan tana buk’atar band’aki, ko idan zatayi sallah,
Abpa da Dada na cikin bukka, Neelah ta fito ta nufi daji dan tanasan kewayawa,
bayan ta gama biyan buk’atarta ta taso da niyyar komawa bukkarsu,
dandazon yara wanda a k’alla zasu kai 20 suka shiga binta a baya,
suka yi mata ihuuu tayi cikin shige, wasu na d’iban k’asa suna bud’a mata a jikinta,
wasu na jefanta da duwatsu, haka suka taso ta gaba har bukkarsu suna jefanta da duwatse,
Dada da Abpa suna daga cikin bukka suka fara jiyo ihuuun yara suna cewa ” ku bud’e ta tayi cikin shege,
ihooo me abin kunya, ganin yadda yaran suka jiwa Neelah ciwo,
ga jini yana ta zuba daga jikinta yasa Abpa saurin k’arasawa gareta,
ya tsugunna dai-dai tsayinta yana goge mata jinin dake zuba,
cikin muryar kuka Neelah tace ” dan Allah Abpa ka barni na bar k’auyen nan,
ka barni nayi nesa da mutanen nan marasa inamani da tausayi,
wad’anda basu san tawakkali ko milk’alil zarratun ba,
Abpa zayyi magana ya jiyo muryar Dada na cewa ” Malam tunda nake dakai, tunda kake yanke hukunci akaina har Allah ya kawo mu ka fara yanke hukunci akan Neelah,
ban tab’a bud’ar baki nace maka komai ba, ban tab’a yi maka musu ko nayi jayayya da maganar ka ba,
ban tab’a fitowa na nuna maka hukuncinka akan mu bayyi min ba,
ko yayi min ko bayyi min ba ina hak’uri na amsheshi hannu bibbiyu,
a yau ina san nayi abinda ban tab’a yi ba a iya tsayin rayuwarmu,
ina san na saka maka baki a harkar gida da hukuncinka, ina san na rok’e ka alfarmar daka bar Neelah ta koma birni,
shiru Abpa yayi yana sauraren maganganun Dada harta dasa aya,
yau karo na farko a rayuwarshi daya ji Dada ta kira ainahin sunan Neelah,
haka ta saka baki akan maganar shi, ya d’an dad’e kafin ya d’ago ya kalli Dada yaga tayi mishi k’uri da ido,
a hankali ya mayar da dubanshi ga Neelah, yaga itama ta kafe shi da ido,
murmushi yayi had’i da cewa ” shikenan bakomai,
duk da Neelah bata jin dad’i hakan bai hana ta yin tsalle ta fad’a jikin Abpa ba,
ya rungume ta yana dariya yace ” kin fa girma yanzu Bingel,
cikin bukkarshi ya shiga ya d’auko takardar da Umairah ta rubuta mishi number,
lokacin da zata tafi ta bashi tace koda ya canja shawara ya kirata,
in sha Allah zata zo ta d’auki Neelah, bukkar Mani me waya Abpa ya nufa,
bayan ya isa sun gaisa da Mani kana Abpa ya mik’a mishi number yace ” dan Allah kira min wannan number,
Mani ya amshi number tare da cewa ” Malam Liman ka san cikin karkarar nan babu hanyar sadawar kira,
dole sai mun tsallaka rafi munje hayin dutse kana zaka iya magana,
Abpa yace ” ashsha bakomai muje, suna tafe suna hira har suka isa,
batare da b’ata lokaci ba Mani ya kira number Umairah,
Umairah na kwance saman sofa kanta saman k’irjin Naufal, yana ta rarrashinta kan tafiyar Neelah,
sosai Umairah ta shiga damuwa tun bayan tafiyar Neelah,
jin wayarta na rori yasa Naufal mik’a hannu ya d’auko ya mik’a mata,
batare data amshi wayar daga hannunshi ba tace ” waye….!?

STORY CONTINUES BELOW


“Number ce kawai ba suna, fuska ta d’an ya mutsa kana tace ” barshi bazan amsa ba,
wayar ya mayar ya aje a inda take, har wayar ta katse basu kuma bi ta kanta ba,
aka kuma kira, amma bata d’auka ba, sai da aka kira sau biyar bata yi picking ba,
Mani ya kalli Abpa yace ” to basu d’aga ba,
Abpa yace ” shikenan mu tafi, Naufal yana shafa kan Umairah yace ” dear…!,
” uhnnnn tace, ya cigaba da cewa ” bai kamata keda kike huld’ar jama’a a kira ki k’i d’agawa ba,
tunda kin san a koyaushe ana iya kiranki dan neman taimako,
d’an shiru tayi kana tace ” kira number, ba musu Naufal yayi dialing number,
kasancewar su Abpa basuyi nesa da barin wajen network ba,
wayar ta soma k’ara, Mani ya duba wayar ganin number da Abpa yabayar a kira mishi ce,
yasa Mani d’aga wayar had’i da mik’awa Abpa yace ” Malam Liman gashi sun kira,
jikin Abpa na rawa ya amsa yana cewa ” to to masallah, jin muryar Abpa da Umairah tayi yasa ta saurin mik’ewa zaune,
sallama Abpa yayi mata ta amsa cikin zumud’i bakinta na rawa tace ” Abpa ya Neelah tana lafiya…?

Murmushin jin dad’in yadda ta nuna damuwarta akan Neelah yayi ,
kana yace ” tana  nan lafiya, na kira ne dama danna sanar daku idan ba damuwa kuzo ku tafi da ita,
idan kun samu lokaci,  baki Umairah ta washe tana mik’ewa tsaye tace,
” aiko gamu nan yanzu ma da izinin Allah, Abpa yayi murmushi tare da cewa ” karki matsawa kanki ki bari ku shirya a nutse, 
” a’a Abpa yanzu ma a shirye nake dan baka san yadda nayi kewar Neelah bane,
” to shikenan ba damuwa Allah ya kawo ku lafiya,
” Amin ya Allah cewar Umairah tana dropping call d’in, cikin zumud’i ta kalli Naufal dake zaune ya kafe ta da ido,
while deep down gabanshi na muguwar fad’uwa jin wayar da take yi, ” oya zuwa Taraba ya kamamu dear,
Abpa yace muje mu taho da Neelah, murmushin yak’e yayi yayinda gabanshi ke cigaba da fad’uwa, 
batare data jira jin abinda zaice ba ta rik’o hannunshi tana cewa muje mu shirya mubi jirgi.

Gaf da sallar Magrib su Umairah suka isa bukkarsu Abpa, 
sosai Neelah tayi farin cikin ganin Umairah, bayan sun ci abinci anyi sallar isha sukayiwa su Dada sallama suka bar k’auyen Sunkhanni,
bayan fad’an da Abpa yayiwa Neelah kan rik’on amana da gaskiya,
a ranar suka kuma biyo jirgin dare suka koma garin Abuja, washe gari suka je har gida suka sanar dasu Daddy dawowar Neelah,
sosai dukkansu sukayi farin cikin dawowarta musamman su Suhaira,
kasancewar an riga an gama komai na makarantarta tun farkon zuwanta,
yasa babu wani b’ata lokaci ta fara attending school,  boko da Islamic, bayan malaman dake zuwa gida suna yi mata lessons, 
haka ma a school bata dawowa gida bayan an tashi tana tsayawa school lesson, 
sosai Neelah ta dage da karatunta ta mayar da gaba d’aya hankalinta kan karatu,
bata kwanciya bacci har sai ta haddace gaba d’aya abinda aka koya mata,
Allah kuma ya taimake ta cikinta ba mai matsawa bane bata wani laulayi, kamar ma ba mai ciki ba.

BAYAN WATANNI UKU

Cikin Neelah ya cika watanni bakwai amma dayake yarinya ce da akwai k’uruciya tattare da ita,
yasa take yin abu gabagad’i dan lakuta da dama sai Naufal da Umairah sun tsawata mata,
haka ma idan taje gidansu Mamy,  taita biyewa su Suhaila suna guje-guje da tsalle-tsalle sai  Mamy tayi mata da gaske kana,
haka a b’angaren karatunta ta mayar da hankali sosai dan da zuciyarta da ruhinta,
take yin karatun ta k’udurce a ranta koda zata rasa rayuwarta wajen neman ilimi sai dai ta rasa, 
amma bazata tab’a sarewa ba, hakan yasa take yin karatun a zuciye cike da son cimma burinta, 
haka duk wani abinda Neelah ke buk’ata,
Umairah da ‘yan aiki ne keyi mata, Umairah ta hanata yin komai,  babu abinda take yi sai dai ta ci ta sha tayi karatunta,
haka ma Nauman da Naufal suna bata kulawa sosai ita da abinda ke cikinta,
tun cikinta na 5 month’s suka fara siyayar kayan haihuwa,
zuwa 6 month’s sun gama siyan komai na haihuwar, 
Neelah na zaune saman bed k’afuwanta cikin ruwa tana karatu, jin wani abu ya tsarga mata a mararta yasata zabura, 
a hankali-a hankali ciwon da take ji ya fara tsananta yana yin gaba-gaba,
tun tana cije lips harta fara murk’ususu a k’asa ta fasa kuka,
jin azaba ta tsananta har tana neman sak’ewa yasata fara rarrfe tana daga durk’ushen,
ta isa ga wayar landline dake d’akin tana daga durk’ushen ta had’a uban gumi,
jikinta ya jik’e sharkaf da gumi ta latsa kira, cikin bacci Umairah taji ringing,
tana daga kwance ta laluba ta d’auki kan wayar landline dake kan bedside d’inta,
tana kara wayar a kunnenta ta jiyo shashshekar kukan Neelah,  dakyar ta iya cewa ” kizo Aunty zan mutu,
a zabure Umairah ta mik’e had’i da dirowa daga kan gadon  tana kiran sunan Naufal,
cikin nutsuwa ya bud’e idonshi ganin yanayin da take ciki yasashi saurin mik’ewa, 
yana cewa ” lafiya…?

” Neelah… kawai ta iya cewa a kid’ime ya mik’e yana cewa subhanallahi, 
tare suka shiga bedroom  d’in Neelah ganinta durk’ushe yasa su k’arasawa gareta da sauri,
ganin halin datake ciki ya k’ara razana su, suka rud’e sosai, dan ta fita daga hayyacinta dara-daran idanuwanta sun fito waje sunyi jajir dasu kamar garwashin wuta,
gashin kanta duk a yamutse, sanyin ac bai hanata jik’ewa da gumi ba,
da sauri Naufal ya koma bedroom ya sanya jallabiya da 3 quarter ya zari key d’in mota,
bedroom d’in Neelah ya koma batare da b’ata lokaci ba ya d’auke ta cak yayi hanyar fita,
saboda rud’ewa Umairah bin bayanshi tayi ta manta da babu kayan arziki a jikinta,
tana k’ok’arin fita harabar gidan kanta ba ko d’an kwalli,  yace ” a haka zaki fita…?

Sai lokacin Umairah ta kula da jikinta batare datayi magana ba ta koma ciki da gudu ta zira doguwar riga had’i da bulla hijab,
a bayan mota inda aka kwantar da Neelah ta zauna tare da d’ora kan Neelah akan cinyarta tana shafa kanta gami dayi mata sannu,
A harabar hospital yayi parking ya fito ya d’auke ta yayi cikin hospital da gudu had’i da kwalawa Doctor kira,
jikin Doctor da nurses na rawa suka nufo Naufal, babu b’ata lokaci suka karb’i Neelah aka shigar da ita labour room,
Naufal da Umairah na tsaye gaban labour room suna ta safa da marwa, 
cikin sa’a Nauman yazo zai fita yana rataye da cot a kafad’arshi, 
ganinsu ya yasashi yin turus cikin sanyin jiki ya k’arasa inda suke, ” lafiya Big B….?

A d’an razane ya jiyo ya kalli Nauman, da sauri Umairah tace ” Neelah ce take labour, ” what….?

” Wanne irin labour?

Nauman ya tambaya a k’agauce, Naufal yace ” eh tana cikin labour room,
cikin mamaki Nauman yace ” but cikinta is 7 months fa, bai jira jin abinda zasu ce ba ya shiga labour room d’in,
sai bayan 3hrs da shigar Nauman kana ya fito yana goge gumi da sauri Naufal da Umairah suka isa gareshi,
Nauman ya sauke numfashi kana yace ” bakawaini zata haifa, 
amma duk da haka bazata iya haihuwa da kanta ba, saboda k’ugunta yayi k’ank’anta da fitar d’a, kuma nak’uda take yi mai bak’ar wahala,
har yanzu abu d’aya ake, 
cikin tashin hankali Umairah ta fasa kuka tana fad’ar ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, 
cikin karaya Naufal yace ” to yanzu meye abin yi…?

Nauman ya numfasa had’i da cewa ” gaskiya ina ganin ayi mata CS kawai dan tana shan bak’ar wuya,
idan aka tsaya b’ata lokaci komai yana iya faruwa, 
” dan  Allah kayi koma meye please,  Nauman yace ” ai na riga da nasa hannun ayi mata aikin kum……..
”  kazo Dr AA yana kiranka,  Nauman bai kuma magana ba ya juya ya koma cikin labour room d’in,
batare da b’ata lokaci ba aka gama duk wani shirye-shirye aka shigar da Neelah Theater room,
ana kwala kiran sallar asuba dai-dai lokacin Naufal da Umairah suka jiyo kukan Baby daga cikin Theatre room,
kallan juna sukayi  had’i da mik’ewa tsaye,
fuskar Nauman d’auke da fara’a ya fito hannunshi d’auke da Baby girl, 
Umairah tayi saurin nufarshi tana sauke ajiyar zuciyar,  bakinta na rawa tace ” ya Neelah….?

” Neelah zaki fara tambaya ko Baby…?

Yayi maganar yana murmushi Umairah tace ” a’a ni ta Neelah nake yi,
Nauman zayyi magana nurse ta fito rik’e da wani Baby a hannunta,
cikin mamaki Naufal ya kalli Nauman yace ‘yan biyu ta haifa….?

Cikin murmushi Nauman yace ” ba ‘yan biyu bane ‘YAN UKU TA HAIFA BIYU MAZA D’AYA MACE,
da sauri Umairah da Naufal suka kalli Nauman gami da had’i bakin cewa ” ‘YAN UKU….?
2

Dai-dai lokacin da yaran Neelah suka tsandara kuka yayin fad’owarsu duniya, 
Neehal ya farka a gigice daga daddad’an baccinshi, tare da fad’owa k’asa timmm daga saman bed,
a rud’e ya farka ya had’a uban gumi sharkaf yana ta nishi tare da kalle-kalle kamar zautacce……!Cikin kid’ima da tashin hankali yayi saurin mik’ewa tsaye zumbur, 
a matuk’ar tsorace duk ilahirin jikinshi na kerrrrma yana kalle-kalle wanda idan za’a kasheshi bai san dalilin faruwar hakan ba,
k’arar fad’owar da yayi daga saman gadon ne ya farkar da Najwah daga baccinta,
saurin mik’ewa tayi ganin yanayin  da yake ciki,  ” lafiya! mike damunka my life….!?

Tayi maganar tana k’arasawa gabanshi, k’ok’arin motsa lips d’inshi ya soma yi yana san yin magana amma ya kasa,
ganin haka ya Najwah rungume shi, gami da shafa kanshi had’i da bubbuga bayanshi kamar baby,
lakur yayi a jikinta yana sauke ajiyar zuciya had’i da fitar da numfashi har ya samu nutsuwarshi ta dawo.

**********************************

Cikin matsanancin mamaki Umairah tasaki baki had’i da zaro ido tace ” ‘yan uku….?

Fuskar Nauman cike da murmushi tamkar shi akayiwa haihuwar,
yace ” yes of course, kinga ikon Allah ko…?

Hannu Umairah ta mik’a ta amshi Baby daga hannun nurse had’i da washe baki,
tace ” Alhamdulillah! Alhamdulillah  ala kullu alin Allah mun gode maka abisa wannan kyautar,
lalle *RABO AJALI…!* ne sau d’aya tak fa ya tab’a sex da ita amma kaga dayake *RABO AJALI…!* ne har ‘yan uku,
nasan duk inda mijin Neelah yake a fad’in duniya na tabbatar sai ya ji a jikinshi,
Naufal da farin ciki ya hana shi magana yana rungume da Baby boy d’aya a k’irjinshi, 
idanuwanshi lumshi yana jin wani irin sanyin dad’i na ratsa duk wata gab’a dake jikinshi,
zuciyarshi nayi mishi sanyi yayinda yake ji dama yaranshi ne,
ina ma shi Allah yayiwa wannan ni’imtacciyar kyautar mai cike da rahama,
a hankali so da k’aunar yaran ke ratsa magudanar jiki da tsokar jikinshi,
  nurses suka fito daga Theater room suna tura gadon da Neelah ke kwance zuwa rest room,
da sauri suka bi bayan nurses d’in Nauman da Naufal na rungume da Baby boys,
while Umaira na rungume da Baby girl, kan bed aka kwantar da Neelah had’i da jona mata drip,
d’aya daga cikin nurses d’in ta kalli su Umairah tana murmushi tace ” to Auntyn Babies a bada su za’a sanya su cikin kwalba,
cikin rashin fahimta Naufal yace ” kwalba kuma wacce iri?

Nurse d’in zatayi magana Nauman yace ” eh! dole za’a saka su a kwalba na 1 to 2 month’s, 
” akan wanne dalili….?

Cewar Umairah idonta kan Nauman, sai da yayi murmushi kana yace ” bakwaini ne basuyi kwari sosai ba,
suna buk’atar cikin mahifiyarsu, Umairah tace ” to amma dai ai a  bari su Daddy su zo su gansu tukunna ko…?

Nauman yace ” rufa min asiri ni na isa, yaushe su Mamyn zasu k’araso…?

Ya fad’a yana kallan Naufal, sai lokacin Naufal ya tuna ba’a sanar dasu Mamy ba,
kanshi ya dafe had’i da cewa ” ya Salam..!, Umairah ta kalle shi had’i da cewa ” me..!?

” Gaba d’aya mun manta bamu sanar dasu Daddy ba, yayi maganar yana dialing number Daddy,
Daddy dake zaune  kan sallaya yana azkar kafin ketowar alfijir wayarshi dake saman bed ta soma ruri,
har wayar ta gama ringing bayyi picking ba,  k’ara kiran wayar Naufal yayi a karo na biyu,
harta kuma tsinkewa Daddy bai d’aga ba,  Umairah tace ” baiyi picking ba…!?

” Eh ina ga yana azkar ne, ya fad’a yana mayar da wayar cikin aljihunshi tare da mik’ewa,
ya kalli Nauman yace ” muje muyi sallah, batare da Nauman yayi magana ba ya kwantar da Babyn hannunshi,
haka ma Naufal kana suka fita, a masallacin asibitin sukayi
sallah suna fitowa kiran Daddy na shigowa wayar Naufal,
cikin girmamawa ya gaida mahaifin nashi kana ya sanar dashi Neelah ta haihu,
Daddy yace ” masha Allah me aka samu…!?

STORY CONTINUES BELOW


” ‘yan uku ta haifa Daddy biyu maza d’aya mace, da sauri Daddy yace ” ‘yan uku fa kace Naufal…!?

Naufal yayi murmushi had’i da cewa ” wallahi kuwa Daddy amma CS akayi mata kuma bakwaini ne,
” Alhamdulillah  Allah ya raya Ubangiji ya bata lafiya, ga mu nan zuwa,
ko da Daddy ya sanar da Mamy haihuwar sosai tayi farin ciki had’i da yin addu’o’i,
k’arfe takwas na safe driver yayi parking a harabar hospital, Daddy da Mamy da su Suhaira suka fito,
cike da d’okin ganin Baby Suhaima ta nufi cikin hospital Daddy yace ” to gand’oki kun san d’akin da suke ne….!?

Kansu suka girgiza alamar a’a, Mamy tace ” to da ina zaku….?

Waya Daddy ya ciro ya kira Naufal ya sanar dasu sun k’araso, 
Naufal ne yayi musu jagora har d’akin, saman table Naufal ya aje basket d’in abincin da su Mamy suka kawo,
cikin girmamawa Umairah ta durk’usa har k’asa ta gaida Mamy da Daddy, suka amsa cikin fara’a,
itama su Suhaima suka gaida ita, gaban gadon da Neelah ke kwance  Daddy da Mamy suka je while tana ta baccinta kasancewar har zuwa lokacin allurar baccin da akayi mata bata sake ta ba,
Daddy ya shafa kanta yana murmushi yace ” sannu kamar tana jikinshi,
Suhaira tace ” Daddy bata jinka fa bacci take yi,
Daddy yace ” au haba bacci take yi….!?

Suhaira tace ” eh! Daddy yace ” ai ban sani ba, yayi maganar cike da barkwanci,
gaba d’aya aka saka dariya, Daddy da Mamy suka taka zuwa gaban gadon da aka kwantar da yaranta,
ido Daddy da Mamy suka k’urawa yaran had’i da yin shiru  suka kafe yaran da ido batare da sun furta koda kalma d’aya ba, 
a hankali Daddy ya d’ago kanshi ya kalli Mamy itama ta kalle shi, had’i da sauke ajiyar zuciya a tare,
ganin irin kallan da Mamy suke yiwa yaran yasa Umairah mik’ewa ta nufi wajen,
tana cewa ” lafiya Mamy….!?

” Daddy me….! kasa k’arasa maganar tayi saboda mahauciyar fad’uwa da gabanta yayi,
dan sai a lokacin ta kula da tsananin kamar yaran da family’n Lagosa,
cikin tsoro da firgici Umairah ta sanya hannu ta rufe bakinta, gami da zaro idanuwa waje,  cikin rawar baki ta kira sunanshi ” Naufal,  ” lafiya…!?

Naufal yace,  batare da tayi magana ba ta shiga nuna mishi yaran da hannunta, 
da sauri Naufal ya nufe su danshi a zatonshi ko wani abun ne ya samu yaran, 
” lafiya meke faruwa…!?

Naufal ya kuma tambaya a karo na biyu,  jikin Daddy a sanyaye ya sanya hannu ya d’auki Baby girl, 
yana dubbuba ta sosai,  karaf idon Daddy sauka akan tauwadar Allah dake kumatun Babyn wacce gaba d’aya zuri’arsu birni da k’auye suna da wannan shaidar tauwadar Allahn, 
koyaya ka had’a alak’a ta jini da ahalinsu dole za’a ganka da wannna shaidar, 
cikin sanyin jiki Daddy ya kalli fuskar sauran yaga suma dukkansu suna da ita, 
bakin Mamy na rawa tace ” Alhaji kalli goshin yaran ga irin gashin goshinka nan, 
wanda gaba d’aya yaranmu na dashi tun daga kan Naufal har zuwa kan auta, 
bakin Umairah bud’e tayi saurin kallan fuskarsu taga d’an kwantaccen gashin daya zarto ya b’ullo saman goshinsu, 
tabbas irin na Daddy ne wanda gaba d’aya ‘ya’yanshi na dashi, jikin Mamy na rawa ta juya gefen kunnansu na dama, 
danta k’ara tabbatar da zarginta,  aiko ta ci karo da d’an k’ullutun da ake haihuwar yara dashi a zuri’arsu, 
taga gaba d’aya suma yaran nada su,  haka gaba d’ayan Lagosa Families na dashi, 
kallan Naufal Daddy yayi rungume da macen a jikinshi, 
cikin fushi Daddy yace ” ka cuce ni,  ka b’atawa zuri’armu suna, 
duk irin tarbiyar dana baka amma da irin wannan sakayyar zaka saka min, 
ashe dama haka kake Naufal….!?

” Ka b’ata wayonka ka tarwatsa dukkan yardar da nayi maka, 
ka kuma bani mamaki, Daddy ya k’arasa maganar jikinshi na tsuma, 
  ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,  Allahumma ajirni fi musibati wa’aklifni khairan min ha, 
abinda Naufal ya shiga maimaitawa kenan yana dafe da kanshi, tare da yin baya taga-taga zai fad’i, 
bango ya tokare shi,  danshi kanshi ya ga zunzurutun kamar Babies d’in da ahalinsu,  
shi kanshi ya san tabbas duk inda yaran suka fito daga cikin zuri’arsu ne, 
kallan da Mamy da Umairah ke jefanshi dashi ne yasa shi cewa ” wallahi tallahi na rantse da girman Allah, 
ban tab’a ganin Neelah ba sai ranar da Umairah tazo da ita, k’afata bata tab’a taka Taraba ba sai ranar da muka je da Umairah, 
nasan bani da mafita,  bani shaida ko bakin kare kaina daga zargi, 
Allah ne kad’ai zai fitar dani amma walla……! tassss tassss Daddy ya kifawa Naufal gigitattun marika guda biyu a jere,
cikin zafin rai Daddy yace ” ni sa’an ka ne da kake neman raina min hankali..? 1

STORY CONTINUES BELOW


“Idan ba kai ne ubansu ba uba waye uban su?

” Kai kanka ka tabbatar duk wanda yayiwa yaran nan kallo d’aya yasan daga tsatsanmu suka fito, 
sannan tsabar ranin wayo kace bakai ne ubansu ba,  Daddy ya fad’a jikinshi na rawa kamar mazari, 
kuka Umairah ta fashe dashi tana cewa ” to idan babu wani abu tsakaninku meyasa ranar da muka zo gida ta haukace….!?

“Kuma meyasa ranar da mukaje garinsu mahaifinta yace ” ina ta kuma samo ka…!?

” Wallahi nima ban sani ba,  amma na tabbatar akwai wani abu a k’asa, 
dan ni bani da wata alak’a da Neelah ko yaranta,  Billahil azim,  
abu d’aya ne zai warware wannan abun shine DNA test,  shi kad’ai ne zai fitar ni, 
ya kuma bayyana gaskiya,  a fusace Mamy dake tsaye ta kasa magana tace ” DNA d’in ubank….! 
salatin da Neelah tayi ne ya hana Mamy k’arasa fad’ar abinda tayi niyya, 
saurin goge hawayenta Umairah tayi had’i da nufar Neelah, a hankali Neelah ta soma bud’e idonta, 
tare da sanya d’ayan hannunta marar cannula ta dafe kanta, while d’ayan na dafe da mararta, 
bakinta yana maimaita salatin Annabi, a hankali -a hankali Neelah ta ware idonta tun tana ganin dishi-dashi harta fara gani tar, 
a hankali idonta ya sauka akan Umairah, cikin k’arfin hali ta sakar mata murmushi, 
had’i da soma k’ok’arin mik’ewa zaune,  cikin nutsuwa Umairah tayi saurin rik’e ta, 
jikin Naufal a sanyaye ya fita ya kira Doctor kasancewar Nauman ya tafi gida tun kafin zuwan su Daddy, 
tare suka shigo da Doctor ya dudduba ta jad’i da cire mata k’arin ruwan,  ya kalli Daddy yace ” kar’a bata madara ko abinci me nauyi, 
Daddy ya amsa mishi da to,  kana Doctor ya fita, kasancewar   lokacin da Neelah ta farka, 
sama-sama taji maganganun Mamy dana Naufal yasata kiran sunan Daddy da Mamy a hankali, 
” Daddy….!  Mamy….!,  cikin sanyin jiki suka amsa,  tana daga kwancen cikin muryarta da bata fita sosai tace,
” kada ku zargi Hamma na akan abinda bashi damasaniya akai,  kada ku alak’antashi da abinda bashi da alak’a dashi, 
wallahi tallahi Daddy Hamma bashi da alak’a dani da yaran nan, 
asalima ban tab’a ganinshi ba sai ranar dana zo garin nan,  yana dai kama da Baban su ne sosai, 
dan nima ranar dana fara ganinshi nayi zaton shi ne,  sai daga baya na fahimci kama ce kawai, 
amma wallahi bashi bane babansu,  bashi da wata alak’a ko dangantaka da abinda na haifa,  
na rantse da Ubangijin sammai da k’asai na rantse da girman Allah, ta k’arashe maganar hawaye na zubo mata, 
jin irin rantsuwar da tayi yasa zuciyoyin Daddy da Mamy da Umairah suka yi sanyi, 
had’i da sauke ajiyar zuciya,  Daddy ya matsa kusa da ita ya shafa kanta had’i da cewa, 
” kada ki damu Neelah na yarda da abinda kika fad’a amma tabbas  jiki na yana bani yaran nan jini na ne, 
akwai dai wani abu wanda mu bamu san dashi ba Allah ne kad’ai yasani,  sai dai muyi addu’ar Allah ya baki lafiya yaran kuma Allah ya raya su Ubangiji ya amfani rayuwarsu, 
duk aka amsa da “Amin, Mamy ta sanya hannu ta gogewa Neelah hawaye, 
ruwan Lipton Umairah ta had’a mata kana ta taimaka mata ta tashi zaune ta shiga bata tea d’in a baki, 
bayan an nutsa Mamy ta kalli Naufal da Umairah tace ” ku tafi gida ku kintsa inyaso kwa dawo da yamma, 
ba musu suka tafi,  yayinda su Suhaima ke ta k’ok’arin tab’a yaran Mamy ta hana su, 
bayan sallar ishaa Umairah da Naufal suka shigo d’akin, suka iske Neelah zaune tana shan tea, 
Umairah ta aje basket d’in abincin da suka shigo dashi,  ta k’arasa ta zauna bakin gadon, 
fuskarta  d’auke da fara’a tace ” ya jikin naki….!?

Muryarta a hankali ta amsa ” da sauk’i,  Naufal yace ” ya yaran…!?

D’an tsukakken bakinta ta turo kana tace ” ni ina ruwa na dasu,  tayi maganar cike da yarinta, 
Naufal da Umairah suka zaro ido had’i da cewa ” ban gane ba ruwanki dasu ba….!?

Mamy tayi murmushi tare da cewa ” wallahi tun bayan tafiyarku nake ta fama da ita, 
amma ko ganinsu tayi tak’i,  ta tab’a su ma tak’i balle ta d’auke su, 
nayi harna gaji amma ko kallan inda suke tak’i yi,  Umairah tace ” kai Neelah please kar laifin mahaifinsu ya shafe su, 
cikin shagwab’a Neelah tace ” Allah ba haka bane,  Naufal yace ” to yaya ne?

STORY CONTINUES BELOW


Mamy tace ” kasan fulani akwai kunya da kara,  ga kawaici,  “uhmm kaji san kai cewar Daddy yana shigowa, 
Mamy ta kalleshi tace ” to ko ba hakan bane…!?

” Wa ni na isa nace ba haka bane,  yayi maganar yana rik’e hab’a alamar tsoro, duk suka sanya dariya, 
bayan an nutsa Daddy yace ” ya kamata a yiwa yaran nan hud’uba,
Naufal ya kalli Neelah yace ” wane sunan kike ganin ya kamata a sawa yaran?

Murmushi tayi had’i da cewa ” duk yadda kukayi dai-dai ne,  ni bani da wani zab’i, kuyi duk yadda kuke so, 
sosai suka ji dad’in kalaman Neelah har ransu,  cikin jin dad’i Daddy yace ” a’a ki fad’i idan kina da sunan da kike son a sawa yaran ki, 
baki ta zumb’uro gami da cewa ” ni ba yara na bane,  yaran Aunty Umairah da Mamy da Hamma’am ne, 
su za’a tambaya sunan da za’a saka musu, duk sukayi murmushi 
cikin ransu suna yaba hankalinta,  
dukda ta kasance yarinya k’arama,  Daddy yace ” to ya sunan Babanki da Mamanki…!?

D’an shiru tayi kana tace ” Daddy a saka sunanka dana Mamy da sunan Hamma na, 
babu sunan wanda ya dayace a sakawa yaran nan bayan sunayenku, 
Naufal zayyi magana ta langwab’e fuska gami da cewa ” please  Hamma, 
sosai Daddy da Mamy suka ji dad’in jin tace a saka sunansu,  sunyi farin ciki sosai, 
Daddy yayiwa yaran hud’uba,  macen aka saka mata sunan Mamy Taheerah za’a rink’a kiranta da NAILAH, 
sai mai sunan Daddy Bilal za’a rink’a kiranshi da NAIL, Naufal yace ” please Daddy a saka sunan Neehal instead of nawa, 
ina da burin idan Allah ya bani haihuwa na saka sunanshi, 
batare da Daddy yayi magana ba yayiwa d’ayan Baby boy d’in hud’uba da sunan NEEHAL, 
za’a rink’a kiranshi da NEELMAH,
k’arfe 11:10pm na dare Mamy ta kalli su Umairah tace ” ku tashi ku tafi gida, 
Umairah tace ” a’a Mamy ni zan kwana da ita ki tafi gida,  Mamy tace ” ya aza’ayi haka Umairah…?

” Ai dole ni zan kwana da ita,  idan wani abu ya taso cikin dare fa,  dole sai babba, 
dole badan Umairah ta so ba suka tafi, da daddare Nauman yasa aka saka yaran cikin kwalba, 
bayan sati aka sallami Neelah daga hospital direct gida Mamy ta wuce da ita, 
duk da Umairah taso su wuce can gidanta da Neelah,  amma Mamy ta hana tace dole sai anyi mata wankan jego na kwana arba’in, 
bayan wata d’aya aka dawo da yaran daga hospital,  sunyi b’ul-b’ul dasu gwanin sha’awa, 
kyau da kamanninsu da Neehal ya k’ara fitowa sosai, 
ranar da aka maido yaran Umairah na gidan suna zaune bedroom d’in Neelah suna hira, 
suka jiyo kukan Baby daga falo Umairah ta kalli Neelah tace ” badai har sun iso ba?

Baki Neelah ta tab’e tare da cewa ” ni ina zan sani..?

Batare da Umairah ta kuma magana ba ta mik’e ta fita parlor,  zaune ta iske Nauman, Mamy da Daddy kowanne rik’e da Baby d’aya, 
ta k’arasa fuskarta d’auke da murmushi tace ” har sun iso kenan Mamy…!?

Tayi maganar tana mik’a hannu ta amshi Baby girl, 
macen nata kuka da alama yunwa take ji, Mamy ta kalli Nauman tace ” takwara yunwa take ji, 
kuma har yanzu Mamansu bata da wani Maman arziki,  Nauman yace ” madara da babies food za’a rink’a basu , 
yanzu zan fita na siyo,  Daddy yace ” Nauman ya maganar Nurses  d’in da za’a samu masu kula dasu?

” An samu da tare dasu ma zamu taho, guda hud’u kace ko?

Daddy ya amsa da ” eh guda hud’u,  biyu su rink’a yini dasu,  biyu kuma su rink’a kwana dasu, 
inyaso sai a ninka muku albashinsu sau uku,  Nauman ya amsa kana ya fita bai jima ba ya dawo, 
da kayan ciye-ciyen Baby nik’i-nik’i tare da nurses 4, Umairah tayi musu bayani so ake su rink’a kula da Baby, 
idan yau biyu suka kwana gobe sai wasu biyun su kwana,  bayan salary d’in su za’a rink’a basu ninkinshi, 
aka yi musu bayanin mahaifiyarsu yarinya ce bazata iya shawayar dasu nono ba madara da baby food za’a rink’a basu, 
bedroom d’in kusa da Neelah aka basu aka jibe kayan baby kamar za’a bud’e shago su kansu nurses sunyi mamakin kayan, 
washe gari Daddy yasa aka yanka rak’uma uku da shanu da raguna akayi walimar sunansu, 
sosai Daddy ya kashe mak’udan kud’i aka ci aka sha, akayi hani’an,
koda Mamy tayi mishi magana akan kud’in da Daddy ke kashewa murmushi yayi tare da cewa ” wallahi Taheerah duk inda yaran nan suka fito jininmu ne, 
jikokinmu ne kuma kome daran dad’ewa gaskiya zata bayyana,  itama Mamy sosai ta gamsu da maganar Daddy, 
bayan suna Umairah taso abata yaran da Neelah su koma gidanta, 
Mamy tace ” ya za’ayi a baki yara har uku keda ko haihuwar fari bakiyi ba, 
ki dai bari idan sun girma saiki d’auka,  dole tasa Umairah ta hak’ura badan taso ba.

BAYAN WATA HUD’U

Sosai Neelah ta warke sumul yadda kasan bata tab’a yin jinja ba,  tana gama arba’in Umairah ta matsala dole ta koma gidanta, 
daga b’angare d’aya tuni Neelah ta koma makaranta ta tattara gaba d’ayan hankali da nutsuwarta akan karatunta, 
ta dake da karatu boko da arabi,  ya zamana duk makaranta an santa saboda tsabar k’ok’arinta, 
duk set d’insu babu mai k’ok’arinta ita ke d’aukar 1st position a gaba d’aya set d’insu,  
daya set result suke yi makarantar ba class by class ba, 
duk wani Quiz da Competition da ita ke zuwa,  haka ma a b’angaren islamiyya nan ma tayi fice sosai, 
dan har musabak’a take fita, tayi fresh sosai,  dan koda taje hutu sunkhanni mutane da dama basu gane ta ba, 
yayinda da Abpa da Dadanta suka ji dad’in ganin yadda ta canja, 
haka da suka ji labarin abinda ta haifa sunyi mamaki sosai.

Su Nail sun k’ara girma dan suna da wata shida da haihuwa har sun fara rarrafe, 
farare tas-tas dasu wanke hannu ka tab’a,  sosai suke samun kulawa, 
yayinda suna k’ara girma tsananin kamarsu da mahaifinsu na k’ara fito,
Mamy na zaune a falo wajen k’arfe tara na dare,  ta jiyo Nailah ta tsandara kuka, 
dayake tana da rigima sosai da me sunan Neehal (Neelam) suna da rigima sosai, 
jin an d’an jima bata daina kukan ba,  yasa Mamy mik’ewa ta shiga bedroom d’in, 
ta iske ta zaune dankwarkwar cikin gadanta, Mamy tayi murmushi had’i da d’aukarta tace ” rigimammiya, 
tana d’ago ta taga pampers d’in jikinta ta jike da fitsari, “k’azama!  Mamy tace tana dariya, kana ta sauke ta kan gado tare da cire mata pampers da rigar jikinta, 
gaban Mamy ne yayi muguwar fad’uwa lokacin da idonta ya sauka akan rowar dake gefen cikin Nailah _(rowa ne wani bak’in abu ne me kamar tabo)_ 
ido Mamy ta ware sosai danta tabbatarwa kanta abinda ta gani,  ganin tabbas rowar ce (Lagosa Family mark), 
yasa jikin Mamy na rawa ta aje Nailah ta nufi Nail da Neelmah hannunta na rawa ta d’age musu riga taga gaba d’ayansu suna da ita, 
hannu Mamy ta d’ora aka had’i da fasa kuka tana cewa ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, 
tayi maganar tana fita da gudu had’i kwalawa Daddy kira a razane……..!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *