RAI BIYU CHAPTER 21 KARSHE
Yana zaune saman kujerarsa yana juyawa wayarsa ta yi ringing, yana duba mai kiran yayi dariya, da gangan ya ki dauka domin a yanzu ba zai iya da rigimarta ba, idan ya dauka ba zai tsira ba idan kuma ya dauka still dai masifar ce zata masa. Haka ta jera masa kira har uku sannan ya dauka. “Kina ta damuna da kira kuma kin san ina tare da budurwata” “Au haka ma zaka ce min?” “To kin fi son na yi miki karya?” “Kana ina?” “Ina gurin budurwata, ba ke kika ce karna dawo ba?” Ya katse wayar, shi kuma ya mike tsaye yana dariya ya fice daga office din, cike da so da kaunar matarsa ya fito daga lifter kallo daya zaka masa ka fahimce yana cikin farinciki, rayuwa yake da matarsa irin rayuwar da be tsammani zai samu daga gurin Nawwara ba, irin son da take nuna masa be tsammaci samunsa a gunta ba, rayuwa suke irin rayuwar da ko a littafi aabu ce mai wahalar samu. A yanzu ya zama mutum kawar kowa ciwon da yake jin kamar ba zai barshi ba, gashi yanzu ya samu sauki tun bayan jinyar da yayi a india, he can now read Quran daga fatiha har bakaqa and Nawwarar tana tare da shi da Noor what else zai roka bayan godiya ga Ubangijinsa? 2 A masallacin da ke unguwarsu Sama road ya yi sallah la’asar sannan ya shigo cikin gida, a hankali ya yi parking dan baya son ta ji tsayawar motarsa. Yasan by this time Noor yana makarantar islamiya dan haka Gimbiyarsa ce kawai a gidan, yana fitowa daga motar ya leka window kitchen hangota da yayi tsaye gaban fanfan yasa shi jindadi sai ya dawo kofar shiga falon ya tura kofar a hankali ya shiga, amman hakan be sa ya tsira ba, sai saukar ruwa ya ji a jikinsa. “Haba Madam miyasa baki min adalci babu ne?” “Adalcin kenan kai waya ce ka jikani” “Amman dai dazu da kayan bachi a jikinki na jikaki, ni kuma shadda ce kuma gurin zan ce zan je fa” “Fade kawai kake amman babu wata mace da zata kulaka” “Inji wa? Kin ga yadda ake rushing din na kuwa kai ni fa handsome guy ne irin na bugawa a jarida ma” Ta ji haushi har da zuba masa ragowar ruwan gorar a jiki. “A haka din duk ka wani tsufa ai ni kadai zan iya da kai” “Ko yanxu ina driving wata har kashe min ido daya take” “Karuwa ce” “Wane irin karuwa kuma? Kin ganta kuwa kyakkyawa ga dogon hanci ga karamin baki gata fara kuma ga katon ciki haihuwa yau ko gobe sai shegen matsifa ta fitini kowa ta hana kowa sakewa” Ta jefa masa gorar ruwan tana ƙaƙarin kuka ita ala dole ta yi fushi da gaske, yayi saurin kai hannu ya rika ya juyo da da ita sai ya risina ya kara kunnensa dai dai cinin cikinta. “Yi hakuri Babe na fada min ya Baby yake?” “Ban sani ba” Ta fada tana kokarin ture kansa daga cikinta. “Ni dai Allah yasa karki haifo min fitininayar yarinya, Wallahi Nawwara kin cika masifa” “Au haka ma zaka ce” Ya yi saurin rufe bakinsa ya mike tsaye. “Mantawa na yi” Ya jata ya zauna saman kujera sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa. “Fada min miye na wannan fushi? ” Ta kara turo baki. “Baka siyo min komai ba” STORY CONTINUES BELOW “Daga gurin budurwata na ke kin san kuma…” Be gama ba ta ja masa kunne har sai da yayi yar kara. “Wace budurwa kuma ba zaka daina jana ba?” “Wallahi ba wasa na ke miki ba, akwai wace ta dauki min hankali sosai, bana son jin muryar kowa sai nata bana son ganin kowa sai ita sunan kawai idan na ji raina fari yake” “Nawwara ce” Ya fada da fuskar zolaya sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume suna dariya. Hannunsa ya kai ya shafa cikin ya lumshe ido. “Ban tsammaci zan kara samu wani dan ba bayan Noor but look at us right now” Murya kasa kasa yake mata maganar kamar mai rada, har kasan ruhinsa yake jin son Nawwara da duk wani abu da ya dangance ta, more especially ma cikinsa da take dauke da shi a yanzu bayan ya cire rai daga haihuwa tun bayan a abunda ya faru da shi amman gashi yau Nawwararsa tana dauke da cikinsa. A yanzu ba shi da wani buri da tunani sai na Nawwara, ko da wasa baya son abunda zai bata mata rai, idana yana zaune tare da ita a gida har baya son fita ita kuma ya yi nisa da ita suna makkale a waya, tunaninta ta dinga addabarsa kenan kamar yadda ita tuaninsa yake hanata sukuni, lokatu da dama idan zai anbaci sunan wata sai ya kira Nawwara shi da kansa wani lokacin yana mamakin kansa, a lokacin da ya fahimce cewar tana da ciki sai ya kasa sukuni kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda murna da jindadi. Yau ma kamar kullum Jibril be sake fita ba tun da ya dawo, tare suka karasa girkinsu na dare, around six direba ya dauka Noor daga islamiya, da gudu ya shigo yana sallama tare da fadin. “Daddyna ya dawo” Yana shigowa Jibril ya safkeshi ya yi sama da shi. “Oyoyo dan daddynsa” Dauke da shi ya shiga bedroom dinsa wato dakin Noor dakin da aka kawata da kayan wasan yara da duk wani abu na jindadi. “Ka cire uniform ka zo muje masallaci an kusa sallah” Ya fada yana direshi saman gado. “Okay Daddy” A nan jibril ya juya ya shiga bedroom din Nawwara, a gaban madubi ya sameta tana gyara kayan da ke gurin, a jikin kofa ya ya jingina yana kallonta har sai da ta kammala sannan yaje ya rumgume ta baya ya dora kansa saman wuyanta. “Ke baki gajiya da aiki ne? Ba na ce ki bari sai gobe mu gyara ba” “Haka kake ce min tun shekaran jiya ai, Noor ya dawo” “Eh ya dawo yana dakinsa uniform din islamiya zai cire” “Ya cire ya zo nan sai na masa duka ai” “Mi kuma yayi miki?” “Da ya gama cin abincin rana haka ya bar min plate a falo ya wuce islamiya kuma na sha fada masa ya daina min haka amman ya ki” “Saboda wannan zaki dakeshi” Ta yi shiru, sai kawai ya yi dariya ya kara rumgumeta, domin a yanzu ya saba da halin abu kadan zata ce sai ta hukunta shi ko Noor ko da kuwa abun be kai ya kawo ba, tun da ta dauki cikin nan ba wani zaman lafiya, kullum da kalar fitinar da take masa shi da Noor. A bakin kofar bedroom din Noor ya tsaya ya leko kansa dan yasan laifin da ya yi ya ce “Daddy muje an fara kira” Suna hada ido da Nawwara ya yi saurin komawa yaja kofar. “Ni gaskiya sai na dakeshi ko kuma kai na hukunta ka” STORY CONTINUES BELOW “Hukunci ai ba zai wuce na cewar ba zamu ci miki abinci ba, ni kuma sai na dauki da na muje restaurant mu ci abinci mai dadi” “Ba dai irin nawa na” “Har ya fi naki dadi ga waiters din da iya tarbon baki” Ya fada yana kanne mata ido daya. Ita kuma ta dauki filo ta jefa masa ya gwace yana mata dariyar keta. Washe gari ma haka ta tashe da masifar ta kamar kullum, sassauci daya ta samu bayan Noor ya wuce school ya dora kanta saman cinyarsa ya bude suratul kaffi yana karanta, ita kuma tana saurare har bachi ya dauketa, bayan ya gama ya dauke kanta ya maida saman matashin kai ya shiga kitchen ya shirya musu abun karyawa, bata farka ba sai kusan goma na safe. Da taimakonsa tayi wanka ta saka abaya black, sannan suka dawo falo suna karyawa. Shi yake feeding dinta ita tana feeding dinsa kamar yadda suka saba har a gaba ko da kuwa Noor yana nan. Basu gama karyarwa ba aka danna door bell amalar akwai wani a bakin kofar, har ta kai je zata tashi sai ya zaunar da ita. “Bari na duba” Yana bude kofar ya karbi sakon da ke hannun mutumen sai ya maida kofar ya rufe, ya dawo yana fadin. “Rufe idonki” “Mi zaka bani?” “Just close your eyes please” Mikewa tayi tsaye ta soma zagayensa ita ala dole sai ta ga abunda ya shigo da shi shi kuma ya rika juya hannayesa ta kasa ganin a dole ta hakura ta rufe idanuwanta. “To na rufe” “Ban yarda da wannan rufewan ba, juya bayanki” Ba musu ta juya baya, zuciyarta cike da zumudin son ganin abunda yake boye mata. Da sauri ya juya ya koma gurin kofar ya bude musu suka shigo da kayan da suke dauke da su suka dora saman center table sannan suka fice da sauri, har lokacin Nawwara bata juyo ba duk ta tana jin kamar motin abu a bayanta. “Juyo ki bude idonki” Juyowa tayi sai dai bata bude idon ba, har sai da ya sake fadin ta bude idonta. A hankali ta soma bude idon sai idanuwanta suka sauka kansa. Still har yanzu hannayensa suna bayansa da alama akwai abunda yake cigaba da boyewa. “Minene tau?” Ya nuna mata tsakiyar falon inda center table yake, what a surprise katon cake ne a saman teburi an rubuta masa HAPPY BIRTHDAY MY PRINCESS, da mayan haruffa da sauri ta doshi gurin tana kallon cake din cike da excitement. Katuwar farar paper da ke gefen cake din da aka kawata da flowers da masu harufa an rubuta FOR MY LOVELY WIFE, ta kai hannu ta dauka ta bude jikinta ya rawa ta soma karantawa. _Happy birthday to someone close to me, today my queen was born, the queen of queens, how can I forget your birthday Queen? The woman whos make feel better person, she’s stay by my side i learned many things about life and love, she’s the only woman i love and i know lucky is the man who is the first love of a woman, but luckier is the woman who is the last love of a man, you got it all Baby, I loves you yesterday. I love you still. I always have .. I always will. Happy birthday to you my heart_ Dagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta cike da kwalla. “My soul i love you so much” Hannunta ya kama ya saka mata zoben da ke hannunsa mai alphabet din NJ. “Happy birthday Princess” “Thank you, ni na manta da yau ne birthday na ma” Ta kwantar da kanta jikinsa tana hawaye. “Ni kan ba zan manta ba, taya zan manta birthday din babbar mace kamar wannan? Matar da ita farincikina mace da ta zame min RAI BIYU, kuma muka zama RAI BIYU ni da ita” STORY CONTINUES BELOW Ta yi farincikin da abunda ya yi mata har bata iya misalta jindadinta, haka yake mata a ko da yaushe yana surprising dinta da abunda zai sata farincikin ko ya kara mata son sa a zuciyarta. A ranar farinciki ya hana Nawwara bachi kamar yadda yake hanata a duk lokaci da wani abun farinciki ya same ta, baya da bukatar godiyarta domin yana tunanin duk wata hanya da zata gode masa ta yi masa yawa, shine ya kamata ace yana gode mata ko dan canjin rayuwar da ya samu. *** *** *** BAYAN WASU SHEKARU….. Rayuwa ta canja mana, lallai dukan abunda Allah ya rubuta zai samu bawa babu makawa sai ya sameshi, lokuta da dama muna son abu sai ya zamo ba alheri ba ne a garemu wani lokacin kuma mukan ki abu kuma ya zama shine alheri a garemu, shiyasa ka bawa Allah zabi shine abunda ya fi domin shi zai zaba maka dukan abunda zai zama alheri a gareka ko kuwa kai kana ganin kamar ba alherin ba ne. Kaddara data rubuta cewar ni matar Jibril ce a karo na biyu ita ce ta sake rubuta min farincikina da jindadi a gidansa, abunda ko da a mafarki aka cemin zan yi rayuwar jindadi da farinciki a gidan Jibril ba zan yarda ba amman yau gashi ina ganin kamar ma nafi kowa ce mace dace da mijin aure, you deserved happiness shine a abunda yake yawan fada min kuma yake ta kokari wajen ganin ya faranta min a rayuwata. Lallai Jibril bango ne shafi kuma jigo a rayuwata majinginata mai share hawayena a duk lokacin da kuka ya tunkaroni. 1 Bayan yankewa Siraj da abokan ta-addacinsa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso bamu da sauran fargaba ni da Jibril, ba ma kamar yanzu da hankalina ya kwanta sosai ganin cewar Zinatu ta yi aure, macen da take barazana ga rayuwata da kuma ta miji, irin rayuwar da nake a gidan mijina rayuwace da ko wace mace mai aure zata so kasancewa a cikinta, domin kuwa Jibril yana sani na manta da damuwata a duk wani fargaba da yake tare da ni, a da na yi tunanin rasa Yar’uwata Habiba da na yi da kuma Mahaifina farinciki ba zai sake ziyarta ta, ashe shirme na ke ta yi Allah ya tsara min wani jindadi da farinciki a gidan Jibril. Wani lokacin na yi dariya idan na tuna irin kiyayyar da na nuna masa ko kuma na ce irin soyayyar da na yi da Bilal wacce na ke ganin kamar idan babu shi babu farinciki a rayuwata, lallai yan karon magana sun yi gaskiya da suka ce karshen kiyayya soyayya domin kuwa ni da Jibril a yanzu kamar mu hade junanmu muke wa ma zai ganmu a yanzu ya zaci mun taba wata rayuwar ta bakinciki da kiyayyar juna. Lokuta da dama na kanyi ma Allah godiya akan zabin da yayi min na auren Jibril sama da Bilal domin kuwa a yanzu na gane irin tazarar dake tsakaminsu da kuma irin rayuwar farinciki da jindadi da Bilal yake ciki, domin shi ma na samu labarin irin rayuwar jindadin da yake da matarsa tun bayan da kama aiki a kamfanin hakar man fetur na dangote dake Lagos, wata kila da ni ya aura da mahaifiyarsa ba ta barmu munyi zaman aure kamar yadda ta barshi yana zaune da matarsa a yanxu ba. Na kanyi kokarin taimakawa a duk gurin da na ana bukatar taimako domin kuwa a yanxu na fahinci yadda rashi yake da kuma shiga halin rayuwa, duk a yanxu muna cikin ni’imar Allah Al-hamdulillah. Inna ma a yanxu ba zaka ganta ka ce ita ba ce, domin sun tare da sabon gidan da Jibril ya siya musu, duk wani wulakanci da halin ko inkula da familyn suke nuna mana a yanzu ya wuce mu ne kan gaba a komai, ashe daman rashin yake sa ake wulakanta mu kamar marar galihu. Bayan Haihuwar Nana Asma’u wato yata ta biyu da take bin Noor na sake haibuwar Bashir wanda na kira da Babana, sai kuma na sake haihuwar Fatima da Aisha, a duk lokacin da muka samu hutu mu kan kwashesu muje hutu Abuja. Idan kuma muna sokoto ranakun Assabar da Lahadi sai na sa direba ya kaisu gurin Inna a can suke hutun sati, har bana son su dawo saboda hayaniyarsu. A ranar da muka samu hutun karshen shekara nasa ya kaimu Katsina gurin Hajiya Aisha wato matar margayi Alhaji Dahiru, ta yi mamakin ganinmu kamar yadda na yi mamakin halin da na sameta a cikin, da bakinta take fada min, zaman abuja ya gagareta saboda gadon da Alhaji ya bar masu ta soma business da shi tana zuwa har Dubai da china amman abun be karbu ba sai ya kare a yanzu ma babban danta ne yake dauke da ita sai taimakon da sauran yayanta nata suke kawo mata, na yi mamakin ganin har yanzu Salima bata sake wani auren ba wato autarta wacce ta kasance kawata a lokacin da nake gidan, na ji mutuwar aurenta tun lokacin da Hajiya Aisha ta so a hada Jibril da ita a lokacin da aurenta ya mutu. Kwanan mu biyu a garin muka koma garin Abuja gurin da yara suka fi jindadin zama. STORY CONTINUES BELOW MUSTAPHA POV. A ko yaushe yana yi ma Allah godiya da ya bashi Jidda a matsayin mata, domin kula da soyayyar da take nuna masa, a yanzu yana ganin ko Nawwara ya aura ba zai sameta ba, shi kansa a yanzu ya zage dantse yana nuna mata kula sosai domin ko da wasa baya son bacin rai Jidda kamar yadda ita ma bata son bacin ransa. Gudun wannan yasa ya nemi transfer aka maida shi Kaduna domin a ganinsa idan ya yi nisa da mutumen da yake ganin kamar barazana ne a rayuwarsa zai fi samun kwamciyar hankali, musamman ma Nawwara da ya kasa cirewa a zuciyarsa. A Kano ta haifa masa Amina da Amal wato twins duka mata, a lokacin har baya iya misalta irin farincikinsa, a dole tasa suka tattara suka dawo garin sokoto da zama har yaran suka yi kwari duk da kasancewar can yake aiki sai dai yaje ya dawo. Bayan yara sun yi wayo ya dauki matarsa suka koma Kaduna tare da mai ronon yara saboda rage mata aiki, ita kanta Jidda a yanzu take jin ta yi dacen abokin rayuwa, domin kuwa be rage ta da komai ba, irin soyayyar da yake nuna mata har sai ka zata ita ya fara so ba Nawwara ba. A haihuwarta ta biyu Nawwara ta so ta je amman Jibril ya hanata saboda yana ganin Mustapha a matsayin masoyinta, be duba aminta dake tsakaninsu da Jidda kirkiri ya hanata zuwa a tunaninsa idan taje can Mustapha zai ganta kuma a gidansa zata sauka, shi be ga dalilin da zai sa ya barta taje ba. Babu irin fushi da fadan da Jidda batayi da Nawwara ba akan hakan domin ita a nata tunanin Nawwara ce ta ki zuwan ba wai Jibril din ne ya hanata ba, domin a yanzu tana ganin kamar Nawwara da Mustapha an zama yan’uwa ba dai masoya ba, domin tun aurensu da Mustapha be taba mata maganar Nawwara ba ko da wasa, idan ma ta dauko masa maganar abunda ya shafeta sai ya nuna mata baya so hakan yasa bata taba zancen Nawwara ko wani abunda ya shafeta a gaban Mustapha. A lokacin da Nawwara ta haifi Aisha Mustapha be hana Jidda zuwa ba duk da yana bakin aiki a lokacin sai ya sa direban abokinsa ya kawota har sokoto domin ahi kansa a lokacin ta matsa masa da zancen gida, tayi marmarin gida. Bayan suna da sati daya ta dawo domin ya bukaci hakan, ita kuma bata son tsabawa matsa, kawayenta har zolayarta suke wai ta cika son mijinta da yawa, ita kuma ya nana musu cewar shi ma yana ji da ita ne, kuma ya san darajarta kamar yadda ta san tashi darajar. A zamantakewar rayuwarsu abun burgewa ga ko wadanne ma’aurata abu ne mai wahala ka ji kansu ne, tana kokarin kare mutuncin mijinta Jidda bata daga cikin matan nan da zasu zauna suna fadin sirrin mijinsu ko kuma familysu wanda ya zama ruwan dare a yanzu, hakuri shine abunda ya gina gidanta kuma ya ingantashi, da kuma bawa juna shawarwari, tana saurin bawa mijinta hakuri idan ta bata masa rai ko da kuwa ita ce mai gaskiyar, idan ta ga abunda be mata ba ta kan fito ta yi nuna masa ko kuma ta masa magana sai ya gyara saboda gaba, shi ma haka yake mata idan ta bata masa rai ko da masa wani abun ba daidai ba ya kan fito ya fada mata. Basa kunlatar junansu da komai wannan ne yasa a kullum suke cikin farinciki da kaunar juna marar misaltuwa. NAWWARA POV. Rayuwa ta koya min abubuwa guda uku zuwa hudu, na farko shine hakuri wanda shine jigon komai da komai na rayuwa da kuma zaman duniya, na koyi juriya da kuma jajjircewa akan komai na rayuwa, akan yasa na kara tabbatar ayar nan da Allah yake fadin lallai ne bayan ko wane tsanana akwai sauki a tare da shi, sam ba zaka ganni a yanzu ka ce mi ce a wacan duniyar mai hayaki da gobara ba, har sai idan na bude maka shafin rayuwata. Rauwa ta da koya min zama da mutane da iya rike sirrin, ba kowa mutum ba ne na kwarai kamar yadda Siraj ya ha’incin Jibril akwai kawayena na kwarai irin su Jidda da Salima, kawaye da a yanzu sun ce na ce muau aminar muna kiran junanmu da yan’uwan juna. Yar’uwata haka na rubuta a Number Jidda kamar yadda ita ta rubuta My Blood Sisi a numberta. Wani lokacin idan na zauna ina tunanin yadda rayuwa ta zo mana ni da Jibril sai abun ya rika bani dariya da kuma mamaki, lallai abunda duk Allah ya so ga bawa babu wanda ya isa ya hana shi ko da kuwa duniya zata taru akansa ne, abunda kuma Allah ya rubuta zai sameshi sai ya sameshi no matter what. Hakika soyayya bata tsufa sai dai masoya su tsufa, ban taba yarda da wannan ba shiyasa kullum cikin kwaliyata na ke da yin duk wani abun da zai daukewa Jibril hankali, ban yarda akwai wata mace da zata iya daukewa hankalin mijina ba, sai dai ni na dauke masa hankali daga wasu matan, idan yana gida ina makkale da shi, domin yarana sun bude ido sun ganni tare da Abbasu so na abun mamaki bane idan na kwanta a jikinsa kamar yadda dukansu wani lokacin suke zuwa mu kwanta tare mu tausheshi muna dariya. Idan kuma baya gida to waya tana kunnena ina jin labarin duk wani abu da ya gani a waje, kamar yadda nima nake labarta masa dukan abunda na aikata a gidan matukar ba aiki yake ba. Sakwannin barka da safiya kan sun zame min kamar jiki dole ne kullum sai na tura masa a waya, ko kuma na rubuta masa a paper ma aje masa. Goodnight massage kuma kullum sai na tura masa kamar yadda shi ma yake turo min, wa zai ga rayuwarmu a yanzu ya ce mune a wacan lokacin? Lallai na yarda Kaddara ta riga fata! Kamar yadda aka rubuta a iv yau ce ta kama 23 ga watan November, yau ake daura auren Sakina da angonta wato Mahmoud, hakan yasa na tashi da wuri na yi duka aikina amman hakan be hanani yin latti zuwa gida ba domin Jibril ya yi rantsuwa ba zan bar gidan ba sai na gyara masa ko ina kuma sai na tafi da yara kamar yadda yake min a duk lokacin daya fuskanci bana son zuwa da yara gida. Ko da tara tayi na gama komai na yi ma yara wanka ni ma na yi. Aai dai ba mu shirya ba domin bana son au bata atamfar ankonsu tun yanzu kara su kara wasu tufafin da aka dinka musu na cin biki kamin mu isa can. Muma tsaye harabar gidan gurin mota muna jiran fitowarsa ya aje mu gida domin direbansa baya nan yana can ana hidima da shi ni kuma ya ki yarje min na toka motata wai a ganinsa ban gwari yadda ya kamata ba, hakan yasa indai da yaransa zan je yawo baya bari na yi driving sai idan ni kadaice ko kuma ni da shi. Farar shadda ce a jikinsa ta karbeshi sosai kai ka ce ma shine angon, fuskarsa sai annuri take, yana ta kamshin turare. Kallo daya na yi masa na ji kaunarsa ta kara shiga zuciyata, hakan yasa na kasa dauke idona akansa har ya shiga motar ya yi mata keys. “Wannan irin kallo haka barakkala Masha-Allah karki cinye ni” Sai duk muka sa dariya har yara da suke bayan mota. Ni dai ban ce masa komai ba har muka isa gida yana aje mu ya wuce gurin daure aure da aka ce goma na safe za ayi. Mun yi biki lafiya mun kare aka kai Sakina Birnin Kebbi gurin da Mijinta yake aiki, kasancewar mai mata ne ta aura sai dai asalinsa shi ma dan sokoto. Ranar data zagoyo Assabar babu kowa gidan sai ni da Jibril, a ranar muka sha soyayyar kamar wasu sabbin ma’aurata, washe gari shi ya girka mana abun karyawa domin ni ban tashi ba sai da rana ta fito. Haka muke a duk lokacin da yara basa nan sai abunda muka manta ne kawai bama yi amman ko wace irin kulawa da soyayyar na yi kokarin nunawa mijina kamar yadda shi ma yake muna min, muna jindadin zama da junanmu sama da yadda duk wani mai tsammani yake tsammani, ba mu da wata fargaba ko tunani a zama da muke da juna,muna karan junanmu da sunan da yayi mana dadi, idan kuma yana fushi da ni nasan irin sunan da yake min ka kaka da kakkani, ko ya kira da wani suna a cikin kayan girki, nima kuma na akan masa wannan lakanin kamar yadda yake min. Al-hamdulillah a ko yaushe na kan yi ma Allah godiya da ya bani miji kamar Jibril domin ni da shi RAI BIYU ne bayan RAI BIYU da na rasa wato Habiba da kuma mahaifina. A yauzu a kullum ni nawa godiya ne a garin Allah. ___________________________ Al-hamdulillah nima na gode Allah daya nani ikon gama RAI BIYU Lafiya,