RAI BIYU
CHAPTER 4
Na ɗan faɗaɗa fuskata da murmushi kaɗan na kuma gyara tsuwata. Shi ko haƙoransa a watse har ya ƙaraso kusa da ni. +
“Miyasa baki shiga ciki?”
“Waɗannan jibgin securities ai ba za su bar ni na wuce ba”
“Haka zuciyarki ta nuna miki, ai su aikinsu tsaro ba hana mutane shiga ba, kin tsorata ne?”
“Sosai ma”
Sai kawai yasa min dariya har da tintsirawa.
“Haba sai ka ce wacce bata zauna ƙasashen turawa ba, ai zaki saba da su ne, amman fa zan yi fama da kishi dan suna sakewa da mata sosai”
“Kishi?”
Na tambaya cike da mamakin kalaminsa, haka wani lokacin ya ke sakar min magana kamar mai suɓul da baka.
Sai kawai ya shafa fuskarsa be bani amsa ba ya zuma hannayensa aljihu ya kama hanya.
“Mu je”
Kai kawai na kaɗa, na bi bayansa yana gaba. Faɗuwar gabana ne ya ƙaru yayinda da muka doshi ƙaton gate ɗin nan, yana isa suka buɗe masa ƙofar da biyo ɗazu ya wuce suna zolayarsa ni kuma ina bayansa.
Tafiya mika mai nisa sosai sannan muka isa katafaren kamfanin, hakan ya bani damar kallon gurare da dama a harabar gurin, daga dama wani ɗan madaidaicin guri ne mai kamar ma’aikata an rubuta masa RESTAURANT, sai kuma wani ƙaranin gate dake can hagu an rubuta masa PARKING SPACE, a can gefen gurin kuma an wani gate ne mai zagaye da falawoyi an rubuta masa GARDEN GROVE. Duka cikin manyan harufa masu ƙyali da burgewa.
“Gurin nan na da girma sosai Bilal”
Na faɗa ina kallon gaban kamfanin da duk madubi har takalminka kana gani a ciki da duk wanda zai zo bayanka, gida sama ne mai hawa biyar, na gane haka ne ta windows ɗin dana ƙira, hawa-hawa har biyar.
“Yeah kin ga can gurin cin abinci ne, can kuma duk wani mai abun hawa can zai aje shi, garden kuma gurin hutawa ne ko kuma fira ko meeting haka, kamar idan wanda ba ɗan kamfaninba ya zo ganinka zaku iya tsayawa a can ku yi firarku”
Ya ƙarasa yana nunnuna min guraren, ni kan sai bawa idona abincin na ke, gaba ɗaya na zama baƙauya sam ba zaka taɓa cewa Nawwara ce wacce ta taɓa zama a London ba, ko da yake shekaru da yawa yanzu na zama baƙauya. Ƙofa biyu ce a gurin ko wacce ƙatowa, ɗaya a dama ɗaya a hagu mutane na ga suna ta shiga da damar masu fitowa kuma na fita ta hagun, muna ƙarasawa sai ƙofar ta buɗe mana da kanta a ƙasan gurin inda mutun zai ɗora ƙafarsa an rubuta WELCOME ɗa manyan haruffa masu ƙyali. Tsaye na yi ina kallon yadda mutane ke zirga-zirga ba dan ina tare da Bilal ba dan zan iya rantsewa wata ƙaramar duniya ce na shigo, kamin ka shigo fuskar kamfanin duk madubi ce cikinsa kuma komai kamar zinari yake, ga wasu manya-manyan plasma da ke tallata abubuwan da kamfanin ke yi.
Reception ne ke facing ɗin duk wanda ya shigo, ma’aikatan gurin na sanye da suit maza da mata. a dama da Reception ɗin manya lifted ne guda huɗu, a hagu kuma Excavator ne babban guda biyu na hawa da kuma na sauka, a can gefe kuma wani ƙaton guri ne mai kamar falo an jera ƙasaitatun kujeru ga plasma a gurin, ko ina security camera ne a gurin, ac ta ko’ina ratsa jikin mutum ya ke. 1
“Nawancy…”
Kiran da Bilal ya yi min ne ya dawo da ni hankalina, har na kalli inda ya dosa, na rufa masa baya da sauri. lifted da ke farko ya danna, sai da muka yi tsayin minti biyu zuwa uku sannan ta buɗe mutun uku daga cikin lifted suka fito sannan muka shiga, bayan mun shiga muka juyo muna fuskantar ƙofar sai ya kai hannunsa a maɓallan da ke gurin ya danna number four, sai lifted ta rufe.
“Wow…”
Na furta ina lumshe ido. Sai kawai Bilal yasa min dariya, har da ciro wayarsa yana ƙoƙarin min video. Lokacin da lifted ta buɗe mun tarar wasu na jiran mu fito ta su shiga. A nan na ma ashe wata duniyar ce, da komai na ta na glass ne, mutane sun kasu kashi-kashi, wasu na ta aikin akan documents wasu na gaban computer.
“Haka aikin na ku ya ke?”
“Yeah nan na masu diploma ne, kin san mu NCE ne da mu muna hawa na biyu”
Yana min maganar muna cigaba da tafiya har muka isa wani ƙofar wacce kana tsinkayar wanda ke ciki shi ma kuma yana tsinkayarka. Buɗe min yayi na shiga sannan shi ma ya shiga ya nuna min gurin zama, yana mikawa wanda ke gaban conputer hannu su gaisa.
“Manir”
“Ya Bil ya aikin?”
“Ba daɗi, ga baƙuwar da na ce maka zata kawo takardunta”
Wanda aka kira da Manir ɗin ya juyo yana min wani kallo baki a sake.
“Wow Welcome Ma’am, gaskiya tana da kyau sosai gata fara mashallah”
Bilal ya shafa yancinsa yana satar kallona fuskarsa ɗauke da murmushi, yanayin yadda Manir ɗin ya yi min ya karantar da ni kamar akwai abunda Bilal ɗin ya ce masa a kaina.
“Sannu ya aiki?”
“Hooooo i beg see golden eyes”
Ya furta yana ba Bilal hannu su taɓe. Na yi ma Bilal wani kallo da shi kansa ya san ba na lafiya ba ne, sai kawai ya miƙa hannu ya karɓi takardun hannuna ya miƙa masa.
“Gashi ka shigar da bayanan mu zamu wuce”
Ya miƙa hannu ya karɓa yana dariya.
“Okay ba matsala, Allah ya sanya alheri ya tsare, perfect match”
Har na buɗe baki na ce wani abu sai Bilal ya yi saurin buɗe ƙofar.
“Muje Nawancy”
A dole tasa na miƙe tsaye na nufi ƙofa, ƙamin na ƙarasa sai yayi saurin tare ni.
“Sorry Nawancy bari Oga ya wuce”
“Wane Oga?”
“Mai kamfanin”
Jin hakan yasa ni miƙa wuya dan na hango mai tarin wannan dukiyar, sai dai ban yi sa’ar ba dan har ya shige Lifted. A nan Bilal ya ba ni hanya na fito muka jera muka nufi lifted da muka shigo ɗazu, ƙashim turaren da na ji ya sani faɗuwar gaban da har ya haddasa min ciwon kai a take, saboda na tsani wannan ƙamshin kamar yadda na tsani mutuwa, jin sunan turaren kaɗai zai iya haddasa min hawan jini saboda tunawa da mai shi.
“Wannan da ya wuce ogan mu ne, mahaifinsa ne ke da wannan kamfanin, shi baya son idan na zo a lifted kai ma ka zo, sai dai kowa ya ja baya har sai ya zaɓi wacce zai shiga idan ya shiga sannan kowa ya shiga, kuma baya son yaga mutun ba a gurin aikinsa ba, abu kaɗan kan iya sakawa ya ƙoreka aiki, ba shi baya ɗaukar ƙaddara idan kika fasa masa kofi sai an cire cikin albashinki, ba a latti zuwa gurin aiki, minti ɗaya kika ƙara daga lokacin da kike zuwa aiki sai an rubuta, da kin yi haka sau goma sha biyu zai koreki, idan wata matsalar ta same ki sai kin faɗi dan wuri ki rubuta takardarki ki aika idan ba haka ba zai koreki” 2
“Kai amman ya cika tsauri, sai kace turai”
“Gashi ba shi da dariya, kuma baya son kallo”
Na haɗe yawu ina jijina lamarinsa, domin nima kaina bana son kallo. Ya cigaba da ba ni labarin kamfanin da kuma yadda suke abubuwansu har muka iso bakin ti-ti.
“Kamfani da ke saffara duk wani abu da shafi ƙarfe, kuma kamfani da ke siye da sai da hannu jari, ga kwangiloli kala-kala kamfanin yana yi, kuma akwai wasu ƙananan kamfaninni da suke ƙarƙashin kulawarsa”
“Ayyah za su ɗauke ni aiki kuwa?”
“Za su ɗauke ki kan, amman sai kin yi haƙuri da kuma kin jure ba a makara ba a ɗauke ƙafa, kuma ba a kuskure”
“I will try”
Sama-sama yake ta labarta min abubuwan akan kamfanin, kamin ya tarar min Napep, ya faɗa masa inda zai kai ni, ya miƙa masa dari biyar ya ce ya bani ragowar canji.
Ni kan jikina har rawa yake na isa gida na labartawa Habiba abunda idanuwana suka gani da kuma ji.Tun da na baro kamfanin sai komai na titi ya riƙa burgeni, idanuwana har yanzu kallon komai suke kamar kamfanin wata ƙila saboda labarin da ke ƙumshe a bakina ina son na labarta musu Habiba da Inna yadda gurin ya ke da kuma aikin shi kansa.
Tunawa da zancen Bilal ya sani dariya tare da furta sunansa a fili. +
“Bilal kenan wai zan sha fama da kishi”
Ajiya zuciya na sauke ina tuna irin kallon da Mutune yake min ɗazu, lallai da akwai abunda Bilal ya faɗa masa akaina.
“Sauke ni a nan”
Na faɗa ganin Mai Napep ɗin yana ƙoƙari wucewa ta har cikin unguwarmu, ba kasafai na ke son napep ko achaɓa ya sauke ni ƙofar gida ba.
“Ba ni canjin”
Ya buɗe akwatinsa na kuɗi dake cikin napep ɗin ya ɗauko ɗari uku ya miƙa min, ni ko na ƙi karɓa.
“Haba Malam ya zaka ɗauko ni daga Koko road ka kawo nan kawo nan arƙila kuma ka ce zaka cire har ɗari biyu”
“Haba Hajiya kuɗin nan fa Mai gidane ya bada su ba ke ba, miyasa ku mata kuke son tauye mu ne wai”
Hannu ya kai ya ɗauko naira hansin ya miƙa min, ina ƙoƙarin karɓa na ji takun mutun a bayana yana katsawa mai napep ɗin tsawa.
“Kai wane irin mahaukaci ne zaka kawo mashin ɗinka a nan ka tarewa mutane hanya nonsense mtssssss”
Juyowar da zan yi sai idanuwana suka yi arba da Mustapha, mutun na biyu da na tsana a duniya, ba da ni yake maganar ba amman sai na ji kamar da ni yake saboda tsanar da na yi masa da kuma sanin yadda baya ɗaukar kowa da mutuncin a unguwarmu.
Tassss na wanke masa fuska da mari sannan na katsa mashi tsawa kamar wata uwarshi. 1
“Haka kuke ba ku ganin kowa da mutuncin, kowa a gurinku wulaƙantaccene, uban kowa baka ganin mutuncinsa a unguwarnan, sha-sha-sha marar tarbiya”
Mamaki da al’ajab ya kafe shi a gurin ya kasa ko da motsa idonsa balle ya yi wani motsi. Ni ko a zuciyata tsoro fal marata har ta cika da fitsari, amman a zahiri kallonshi na ke kamar yadda shi ma yake kallona sam ba zaka kalli fuskata ka gano akwai alamar tsoro a tare da ni ba.
Matsowa ya yi kusa da ni ya ɗaga yatsansa ya nuna kamar zai yi magana sai kuma ya cige bakinsa ya yi ƙwafa ya juya koma cikin motarsa, ribas ya yi ya koma inda ya fito da alama ya fasa shiga unguwar ma.
Sai a lokacin na samu sa’idar sauke ajiyar zuciya na juyo gurin mai Napep ɗin na karɓi hansin ɗin da yake miƙa min.
“Kai amman ke wannan ƴar bala’i ce, Allah ya raba mu lafiya”
Ba shi kaɗai ba ko mutanen da ke kusa da mu sun yi mamakin yadda na wanke mutun kamar Mustapha da mari, ni ba mafaɗaciya ba, kuma kowa yasan halin Mustapha a unguwarmu, ni kaina sai a yanzu na ke jin kamar ba ni ce na mareshi ba, wata ƙila kuma saboda na tsane shi ne shiyasa har idona ya rufe haka.
Sai dai mamakina yadda ya ƙyale ni be rama ba, yaron da harararsa ma baka isa ka yi ba saboda yana taƙama ubansa wani ne a cikin garin sokoto. Da wannan tunanin da kuma mamakin dalilin ƙyaleni da ya yi na iso gida, duk wani ɗuki da na ke na labartawa su Inna gurin aikin sai ya kau saboda wannan abun da ya faru tsakanina da Mustapha ya tsaya min a rai.
Ko da na shiga na samu Habiba tana da fa shimkafa da wake, Sakina na daka barkono (Yaji) Inna kuma na ɗaki kamar kullum.
“Har kin dawo ashe ba a daɗewa”
Cewar Habiba tana ƙara tura itacen murhu.
“Eh kin san da yake ba aikin ba ne, takardun ne kawai za a kai”
“Allah ya baki sa’a ya sa su ɗauke ki”
“Amman Babban Kamfanine Habiba, ba lallai ne su ɗauke ni aiki ba”
STORY CONTINUES BELOW
“Zan riƙa tufa musu fatiha a tsakar dare”
Na yi murmushi, kana na doshi ɗakinmu dan cire mayafina. Bayan na fito na doshi ɗakin Inna, ita na fara labartawa yadda kamfanin yake kamin Habiba ta shigo mana da abinci mu soma ci gaba ɗayanmu, ko lokacin da Baba na dai baya ƙwanar ya ga mun raba abinci daga manyan mu har ƙanana, sai dai kowa ya wanke hannunsa a ci a guri ɗaya, yana yawan faɗa mana cin abinci tare yana saka zumuncin da nishaɗi da kuma son juna, kuma ta nan zaka iya karantar halin mutun da lurar shi irin cin abincin da ya dace ya yi. Hakan yasa suka muka saba bama iya raba abinci inda wanda za a ci ne, ko da ɗayan mu baya nan sai mun jira ya zo ko da kuwa Jamila ce ita da ta kasance ƙaramarmu, balle kuma Noor da ko ina muka je baya cin abinci sai da ni matuƙar ina gurin.
Na bijiro musu da zancen marin da na yi ma Mustapha, a take hankali Inna da Habiba ya tashi har ma da Sakina
“Ina ruwanki Nawwara ai ba da ke yake ba, kuma ko da ke yake ai kya shafa kanki lafiya ki bashi haƙuri, yanzu wannan abun da ya faru da mahaifinku be isheki ishara ba? So kike ki ƙara jawo min wani?”
Cewar Inna. Habiba kuma ta ɗora da cewar
“Da ma ba ki mareshi ba Nawwara, kar ya ce kuma zai miki wani abun, kin san halinsa idan ma ya ƙyale iyayensa ba za su ƙyale ba”
Ganin yadda hankalin Inna ya tashi ƴasa ni yin ƙarya.
“Ke wasa na ke daman kawai ina son naga yadda zaku yi ne, ban mare shi ba kuma da ya zo yana faɗa da mai Napep ɗin ma na bashi haƙuri”
“Da Gaske?”
Na gyaɗawa Inna kai ina dariya saboda ta yarda. Sai dai na lura da Habiba kamar bata yarda da ni ba, har muka gama cin abincin ban ga yanayin Inna ya dawo dai-dai ba.
Bayan sallah la’asar Jidda ta shigo gidanmu, a lokacin ina zaune waje ni da Habiba Inna kuma tana ɗaki, Sakina da Noor da Jamila suna islamiya. Kusa da ni ta zauna ina kallin bakinta na san da akwai magana, sai dai tana tsoron furtawa ganin Habiba na kusa da ni. Murmushi na yi na ce
“Saki jikinki Jidda faɗa min ko minene ai Habiba kamar ni ce, dukan abunda kika sani nawa to Habiba ta rigaki saninsa, abunda duk na ke iya faɗa miki to Habiba ce ta fi cancanta na fara faɗawa, ni da ita abu ɗaya ne bama ɓoyewa juna abu”
Sai ta yi ƴar dariya.
“To ai ban sani ba ko gidan ba su ji ba ne”
“Minene?”
“Cewa aka yi wai kin mari Mustapha”
Habiba ta yi min wani kallo tana jiran ta ji abunda zai fito bakina.
“Ba wai ba ne na mare shi ɗin ɗazu”
Habiba ta riƙe baki
“Ashe da gaske ne”
“Na ɓoye ne saboda na ga kamar ran Inna ya ɓace”
Jidda ta kama hannuna.
“Ke ko miya kaiki? Miya haɗa ku?”
Shiru na yi ina tunanin irin amsar da zan bawa Jidda, domin bata san shine mutumen da ya yaga rigar mutuncin Habiba ba, a lokacin da abun ya faru ban labarta mata ko wanene ba kawai dai na faɗa mata cewar Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin.
“Ba komai kawai wai dan Mai Napep ya tsaya a bakin hanya shine ya zo yana mana rashin mutunci, ni kuma na mare shi”
“Aka ce mari har uku wai, ai ƙara da kuka mareshi basa ganin mutuncin kowa a unguwar nan”
Na zaro ido
“Ɗaya ne kaji mutane da canja magana kuma, wai yanzu zancen nan har ya kai miki”
“Wallahi ina zaune gida aka kawo min shi, wai ƙawata ta mari Mustapha, ai ko ni kika mara sai zancen ya zagaye unguwa balle kuma Mustapha guda”
STORY CONTINUES BELOW
Dariya na yi, domin a yanzu duk wani tsoro da ke raina na ɗazu ya gushe. Labarin kamfanin na ɗaukowa Jidda ina ta faɗa mata yadda abubuwan suka, ita kanta da bata je gurin ba sai da abubuwan suka burgeta saboda yadda na tsaya na tsara mata komai kamar anyi a gabanta.
Har muka ci firarmu da Jidda muka suɗe Habiba bata saka bakiba, Jidda kuma bata bar gidanmu ba sai da ta yi sallah magariba sannan na rakata sannan na dawo.
Shikafar ɗazun na ɗauko na ɗumana na zuba mana muka zauna gaba ɗayan mu muka ci, ban da Inna da daman nata daban ake zuba mata balle kuma yau da ta ce ba zata ci ba. Muna cikin cin abincin nokiyar da ke gefena ta yi ringing, abun ka da wanda ya daɗe ba shi da waya tun da na saka layin ba a taɓa kirana da shi ba.
Number Waje ma’ana ba nunber nigeriya ba ce, cikin rawar jikina na ɗauka dan nasan mace ɗaya zata iya kira na da wannan layin wato Salima
“Hello Ƙawata”
Sai ta amsa min daga ɗayan ɓangaren.
“Ƴar’uwata, kin jefar da ni kullum ina kiranki bata shiga”
“Wallahi bana da waya ne a yanzu, wannan ma ara min aka yi na saka layina”
“Allah sarki ya gida? Ina Baba da Inna?”
“Sai dai Inna tana nan lafiya ƙalau, Baba kan Allah ya yi ikonshi”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, yaushe? Miya same shi”
“Rashin lafiya kwana biyu”
Na yi ƙarya saboda ba kowa zaka iya faɗawa dalilin mutuwar Baba ya gasgata cewar Baba be yi satar ba, duba da yadda muke fama da rashi. Bayan ta yi min gaisuwa ta yi ma Inna sannan ta yi ma Habiba, Sakina da Jamila sannan suka maido min da wayar.
“Kin rasa RAI BIYU masu muhimmanci Nawwara mutuwa mai ɗaci , kin rasa Abban Noor yanzu kuma Babanki Allah ya baki ikon ɗaukar wannan lamarin”
“Amin Salima na gode”
“Inshallah idan na dawo Nigeria zan zo har nan na yi miki gaisuwa”
“To Allah ya yarda”
Daga haka muka yi sallama, na amsa mata da to ne kawai ba dan na gamsu zata zo ɗin ba, duk tsawon zaman da muka yi da ita bata taɓa tako ƙafarta sokoto ba ai ba zata taɓa zuwa ba.
Da gudu Noor ya zo gurin yana ƙoƙarin karɓar wayar.
“Momy waya baki waya? Momy kira min Gwaggota Murja kin ji”
Haka yake idonsa idon ganin waya, baya da magana sai ta a kira masa Murja wato Ƙanwar mijina wacce ya shaƙu da ita sosai.
“An ya ma sun ji maganar rasuwar baban ku kuwa?”
Maganar Inna tasa na ɗago kai na kalleta.
“Ina zasu ji tun da ba a nan suke ba kuma babu waya a lokacin”
“Ya kamata dai kan ki faɗa mata”
“Bari na mata please Call me dan ba ni da kati gaskiya”
A take na aikama mata please Call, ko minti biyu ba a ƙara ba sai gata ta kirani, mun gaisa sosai sannan na bata Inna, ita ta labarta mata cewar Baban mu ya rasu, ta shiga ɗimuwa da kiɗima sosai, har da kukanta kamar Babanta ne ya rasu.
Bayan ta yi min gaisuwa ta faɗa min zata shaedawa sauran ƴan’uwan margayi Sadiq zasu zo har sokoto su yi min gaisuwa, duk ƙoƙarin dakatar da ita da na yi akan zuwan sai ta nuna min sam ba zai yiyu sai ta zo, ai daga sokoto zuwa Kebbi ba wani nisa ba ne. Sun daɗe suna waya da Noor sannan bashi yaranta suka yi magana sai ta kashe.
Takwas da rabi wayar Bilal ta shigo, ina ɗauka ya shaida min yana waje. Sai da na faɗawa Inna sannan na tashi na saka Hijab ɗina na fita. Jikingine da ƙofar gida na same shi, ina masa sallama ya amsa fuskarsa da murmushi har wani ƙyali take.
“Nawancy”
“Bilal”
Sai yasa dariya.
“Ina jin daɗin ki kira sunana yana mugun daɗi a bakinki”
Na yi murmushi ina rausayar da kai. Bayan mun gaisa ya bijiro min da fira cikin har da zancen marin da na yi Mustapha, sai na nuna masa ya yi min ba dai-dai ba ne shiyasa. Sai tara da rabi muka yi sallama.
WASHE GARI….
Yau kan ba laifi dukanmu mun tashi cikin walwala, Sakina da Jamila tuni suka wuce makaranta, Habiba ma shirin makarantar ta ke, ni kuma ina gyaran gida, Inna kuma na ɗaki tana bachin safe.
“Nawwara canjin kuɗin Koko yana nan ƙarƙashin fillo, Inna ta ce a siye ruwa”
Cewar Habiba tana tsaye riƙe da littafan makarantarta.
“Yau Fanfan ba zai zo ba ne hala?”
“Yau kwana biyu be zo ba, ruwan da muke amfani da su sun ƙare, ƙara a siya da wuri idan ma ya zo kin ga kaɗan kawai za mu ɗebo”
“Allah ya bada sa’ah”
“Amin na tafi”
Fitarta da kamar minti biyar, wata matashiyar yarinya ta shigo sanye da dogowar rigar atamfa da wani minafukin gyale a kafaɗa, sallama ta fara yi na amsa mata.
“Assalamu alaikum”
“Wa’alaikissalam”
“Sannu ina kwana?”
“Lafiya ƙalau”
“Dan Allah nan ne gidan Musa Kafinta?”
“Nan ne, lafiya?”
“Lafiya ƙalau, Sunana Shafa Ibrahim ni ƴar jarida ce ina aiki da jaridar Arewa a yau, tare da abokin aikina na ke ina son mu tattauna da iyalansa ne akan abunda ya faru”
Ta ƙarasa tana miƙa min katin shedarta.Na kai hannu na karɓi cati na duba, sunanta ne da kuma hotonta a jikin catin hakan ya tabbatar min da cewar lallai ƴar jaridar ƙwarai ce. Na mayar mata da katinta. +
“Ba mu san komai a kai ba, waya faɗa miki nan gurin kuma?”
“Jama’a ne suka kwatanta min, kuma na tabbatar min da cewar ƴan sanda suka duki margayin har ya mutu”
Na nuna mata ƙofar fita raina a ɓace.
“Fita ki bar mana gida, mutanen da suka labarta miki abunda ya faru ki je can su ƙarasa miki, mu bamu san komai ba”
“Haba Baiwar Allah…”
“Ki fita Wallahi ko na sa taɓarya na fasa miki kai yanzu”
Da gudu ta juya ta fice daga gidan. Ni kuma na cigaba da aikina zuciya na zafi har na gama gyara komai, ciki na shiga na samu Inna har lokacin tana bachi Hijabina na saka na ɗauki kuɗin da suke ƙarƙashin filo na fita neman mai ruwa.
Karo na ci da Dpo dake tsaye jikin motarsa yana kallon ƙofar gidanmu, ban gama tabbatar da shi ɗin ne ko a’a ba saboda yau a cikin kayan gida yake.
“Assalamu Alaikum Malama”
A maimakon na amsa masa sai kawai na watsa masa wata muguwar harara.
“Ni ba gurinki na zo ba, matar gidan na ke son magana da ita”
“Bachi ta ke”
“Ki taimaka ki tashe ta kuma ki nema minlH izinin shiga cikin gidan”
“Saboda?”
Ya gyara tsayuwarsa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa.
“Na ga dai ke ba ƴar jarida ba ce, be kamata ki tsare ni kina min irin waɗannan tambayoyin ba, beside ni ba gurinki na zo ba gurin Inna na zo”
“Gida mallakinmu, mahaifiya bachi take baƙincikin kashe mahaifinmu da ka yi take ragewa saboda hawan jini”
Ban tsaya jiran abunda zai ce ba, na cigaba ta tafiyata. Sai ya zagayo ta gaban motarsa ya sha gabana, cikin ɗaga murya ya fara magana.
“Miyasa kuke rayawa zuciyarku cewa ni na kashe mahaifinki? Mi mahaifinki ya yi min da zan kasheshi? Idan na kashe shi wace riba zan ci?”
Nima cikin zafin rai na zaburo masa.
“Saboda zalincin ƴan sanda, yayarka ta laƙaba masa sata bayan kuma be sata ba, kuka yi ta dukansa har sai da kuka kasheshi akan kawai sai ya amsa laifinsa, wannan ba halinku ba ne? Saboda yayarka tana taƙamar kai dpo ne yasa kuka wulaƙanta mana mahaifi cika tozarta shi sannan kuka ɗauki gawa kuka kawo mana, yanzu kuma kana raina mana hankali har kana wasa da hankalinmu”
Ya matso kusa da ni ya nuna ni da yatsa yana magana cikin jin zafin kalaman da na yi masa, har haƙoransa na ƙasa na haɗuwa da na sama yana cizonsu tare da zaro min ido.
“Karki sake saka bakinki a akan aikina, karki sake yin furucin akan abunda kika jahilta, i hate nonsense, na zo nan ne dan na faɗa muku karku kuskura bada bayanin mutuwar mahaifinku ga ƴan jarida”
Na yi baya-baya ina hawaye, tare da murmushin da ya fi kuka ciwo.
“Kamin ta zo nan ashe sai da ta bi ta gurinka, ka yi nasara ban faɗa mata komai ba, amman yanzu kan ni zan tara ƴan jarida da kaina na labarta musu irin zaluncin da kuka mana, wato so kuka a rufa muku asiri kar kowa ya ji ko? Ta yadda muma zaku samu damar ɓatar da mu, Wallahi Allah ba zai barku ba azzalumai macuta-”
Ya ƙara matsowa kusa da ni har sai da na matsa baya.
“Ki tara ƴan jarida, ki faɗa muku ƴan sanda sun kama mahaifinki sun masa duka har ya mutu, za su tambaye ki dalilin hakan, kuma ki faɗa muku komai karki ɓoye, ni da ke za a ga waye zai ji kunya, idan ba ki yi haka ba to baki haifu ba!”
Yana kaiwa nan ya haɗa hannunsa na dama da na hagu ta taɓa saitin fuskata, har sai da na rufe ido. Sannan ya buɗe motarsa ƙirar 406 ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama, ko da na ɓuɗe idona ƙurar motar kawai na gani hawaye ya sauko daga idona, lallai wannan shi ne a dakika a hana kuka, kuma a mareka a ƙwace maka jaka!
Kasa zuwa kiran mai ruwan na yi saboda kuka da ya ci ƙarfina, na koma cikin gida da sauri. Bana son na tashi Inna balle har ta ga hawayena hakan yasa na shige ɗakinmu na kwanta saman tabarma, na ci kuka na sai da na ƙoshi sannan bachi ya yi gaba da ni.
Motsin shigowar su Habiba ne ya tasheni daga dogon banchin da ya ɗaukeni, babu komai a mafarkina sai wacan tashin hankalin da ya faru, Baba ne kawai na ke ta gani sai kuma irin zamantewar da muka yi a gidan kamin rasuwarsa.
Ko da na fito na samu Inna ta farka har suna fira da Habiba ma da ke cire safa.
“Nawwara kin tashi?”
Inna ta tambaya tana kallona, sai na zauna bakin ƙofar ina amsa mata.
“Eh ashe rana ta yi”
“Tun ɗazu su Noor suka dawo na ce kar ya tasheki kin gaji da yawa, ƙara ki samu bachi ki ɗan huta”
Kallo ɗaya Habiba ta yi min ta ɗauke kai, kamar ba ta ganni ba, hakan ya karatar da ni da akwai wani abu a ƙasa, sai dai ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauki bula na shiga banɗaki, bayan na fito na yi alwala na shiga ɗakinmu dan Sallah.
A ciki na sameta tana ɗaura zane, naje kusa da ita na tsaya.
“Habiba kamar akwai abunda ya ke damunki?”
Ta ɗaga kai ta kalleni a maimakon ta yi magana sai ta kawar da kai ta soma magana.
“Nawwara ɗazu da zanje makaranta na haɗu da Mustapha, na tsayarda shi na bashi haƙuri akan abunda kika masa, sai yake tambayata ke yayata na ce eh, shine ya ce wai tun da yake a rayuwarshi wata mace bata taɓa ɗaga hannu taareshi ba ko da uwarsa ce sai ke, akan me zaki mareshi, bayan da ke yake magana ba, kawai ya buga motarsa ya yi tafiyarsa. Nawwara miyasa kika mareshi? Zaki ƙara ja mana matsala” 2
“Shiyasa kike jin haushi na? Babu abunda zai faru Habiba, kuma bari kiji na faɗa miki ko da Mustapha zai yanka ni ya dafa namana ya soma ya ci, ba zan bashi haƙuri ba, ke ma kuma kinyi kuskure da kika tunkare shi kika ba shi haƙuri wannan ba halinki ba ne Habiba”
“To ya kike son na yi? Bamu da wani gata sai na Allah mutane kamar jiranmu suke su yi mana abu, yanzu idan wani abu ya sake samun family mu ban san ya zan yi ba, Allah kasa ni ce zan fara bin Baba na gaji da wannan rayuwar”
Ta fashe da kuka. Ni kuma na riƙeta muka zauna tare ina rarrashinta.
“Babu abunda zai sake faruwa inshallahu, na miki alƙawari, share hawayenki kar Inna ta ji”
Ta ɗaga min kai tana share hawayen.
Haka muka zauna cikin jiran tsamanin abunda zai same ni daga Mustapha domin na san ba zai bar ni ba, Habiba ma kullum cikin tunanin wannan abun take, bata ƙaunar ko waje na leƙa saboda gani take kamar zan iya haɗuwa da shi ya yi min wani abu. Wasa-wasa muka kwashe sati uku babu abunda ya faru sai dai tunanin abun zai faru ya hanani sukuni ni da Habiba, a cikin satin ne su Murja da Hajiya Umaima da Hasana suka zo min gaisuwa tun ɗaga Kebbi. Wato Yayar tsohon mijina da kuma ƙannensa, mahaifiyarsa kuma ta yi min aike ni da Noor. Ba su kwana ba ranar da suka zo ranar suka koma bayan mun yi ma Noor tsaraɓar kayan maƙulashe da kuma tufafi, Inna kuma suka kawo mata atamfa da buhun kishinka ƙarami.
Ranar da suka kwana biyu da tafiya ina zaune tsakar gida misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe wayata ta yi ƙara alamar saƙo, ban kulata ba dan na daina ɗaukin aikin a yanzu tunani ba zan samu ba, tun da kullum ina sa ran ganin saƙon kamfanin amman sai na samu saƙon mtn. Sai da na gaji da kwancin da nake na tashi zaune ya miƙa hannu na ɗauki wayar da ke kusa da ni ina dubawa. Ina ganin sunan Kamfanin One-On-One jikina ya fara rawa, cikin zumuɗi na buɗe saƙon Congratulations na ga an rubuta a sama.ban iya tsayawa karanta sauran ba na buga tsalle ina ihun daɗi.