RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 13
ya nafi dakim Nafisa sai ya tuna yau a gurin Salma
yake. Ya juya ya nufi dakinta.
Tana kan Darduma a can kuryar dakinta, tunda
tayi sallah ta kasa tashi, ga faduwar gaba don
lokaci-lokaci sai ta dafa Kirji. Matuka ta tsorata da
fushin Shatima, har yana fadin zai mata duka!
Tana jiyo sallamar Shi tsoro da fargaba suka
hanata amsawa. Ya aje• hularshi a kan kujera ya
nufi kicin. Ya dauko goran ruwa guda daya, ya zauna.
Duk da babu sanyi da ya daga sai da ya sha fin
rabi, sannan ya aje goran. Yayi ajiyar zuciya. Ya
dauki wayarsa ya kira Nafisa, tana dagawa ya ce ta kawo masa jakarsa nan dakin Salma.
Babu-gardama Nafisa ta dauko ta nufo dakin
Salma. Da alamu wannan bacin ran na Shatima ya
saka matan nashi, shiga taitayinsu, musamman
Salma.
Tayi sallama a Rofar dakin ya daga murya ya
Ce Shigo mana, kin coge kamar wadda za a cinye
ta.” Ta shiga ta mika mishi tare da fadin “An www.dailynovels.com.ng dawo
lafiya?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce, “Lafiya?”
Ta wurga, ido tana kallon falon Salma, cikin
mamaki duk da take ji a family ana cewa su Salma
matsiyata Ne bata yi tsammanin tsiyar har ta kai
haka ba.
Ta taba baki tare da fadin “Uhum!” Ya dago
daga kokarin da ya ke na ciro Laptop a Jaka ya ce,
“Ya ya?” Ta girgiza Kai tare da sake kallon dakin
ta ce, “Babu komai,
‘ Ya ce, “To kina iya tafiya.
Ya fahimci dakin take ma wanna yatsinan.
Salma da ke ciki tana jin su. Lokacin tana ta
shawara a kan ta fito ko kar ta fito? Jin fitar Nafisa
sai ta yi ta maza ta fito.
Cikin tafiya tamkar Wahainiya ta nufi kicin. Ta
dauko Tiren da ta jera kuloli guda biyu, daya farar
shinkafa daya miya. Sai dan karamin kwanon silba
da ta zuba naman yau farfesun shi tayi.
Ta bude dan kwandon da ta yanka ganyen latas
da kokumba, shima ta dora.
Ta.zo ta dire tiren, kan ya zube ma saboda
yanda jikinta ke Bari ta sauke daga tiren ta jere, ta
koma ta dauko cokali da plate, da goran ruwa da
kofi.
Ta dago da niyyar tambayarshi ta zuba.
mishi, sai suka hada ido. Cikin sauri ta sadda kanta har da dauke numfashinta. Domin ta zaci zai
antaya mata mari ne.
Jin shiru ta sake dagowa. Muryarta na rawa ta
Ce.
“Yaya in zuba maka?”
-Na koshi.
* Ya fada a
daKile. Da gudu ta mike kuma a rikice zata yi
daki, tamkar ya kwashe da dariya sai ya dake ya
ce.Ke” Kamar zata saki fitsari ta tsaya cak
amma ta kasa waiwayowa.
Ya ce,
“Zo nan ki kwashe kayanki, ko nine zan
kwashe miki?”
•Ganin rawar jikin tata zubar da abincin a Rofar
kicin, da rasa me zata yi sai ta fashe da kuka. Yana
kallonta yayi murmush: ya dauke kai Ta kwashe www.dailynovels.com.ng
ta kai kicin, tazo ta haye gado ta kudundune.
Lokacin ne Shatima ya samu dama har ya yi
dariya sosai. Sai kuma ya ji zuciyarsa tayi masa
sauki. Ya yarda da batun Likitoci, da suka ce
dariya tana rage damuwa.
Yana bude aiki zai fara, sai •yaga sakwanni a
Emel din sa. Tun karfe uku sakon ya shigo cikin
akwatinsa, suna da meeting a Abuja karfe tara na
safe.
Yayi hamdala da yaga sakon yanzu, da sai da
safen zai gani.
Dole Zai yi bukin din jirgin safe na karfe
takwas.
Salma bata yi bacci sosai ba, tana jin Shatima
ya shigo har da gyara mata kwanciya. Tana jin shi
yayi alwala ya tada nafila.
Da asubahi ta tashi tayi sallah, ta fito zuwa
kicin. Kan sallaya
taganshi yana
karatun
Alkur’ani, irin dan Karamin nan.
Taje ta dafa ruwan zafi, sannan ta soma suyar
dankali kafin shida ta hada komai. Ta fito ta samu
ya fito wanka yana cikin dakinta yana saka kaya.
Tsam! Ya tsuke cikin suit bulu me duhu, rigar
ciki bulu me haske. Tayi saurin dauke kanta
lokacin da taga zai waiwayo. Ya iso gurinta, tayi
saurin tsugunnawa tana fadin, “Ina kwana?”
Ta dauke numfashinta jin bai amsa ba, kuma
bata yi zato ba sai taji an kama kafadunta an mikar
da ita. Idanunta a lumshe hawaye suna kwaranya.
Cikin taushin murya ya ce, www.dailynovels.com.ng
“Salma!” Ta bude
idanunta a hankali, sunyi jajir. Ya ce, ‘
“Wai kukan
me ki ke yi haka?”
Cikin rawar murya ta ce,
“Ban
san ranka zai baci ba, jiya wallahi da ba zan ce zan
bi ka ba.
Ba zaton shi ta sulale Kasa kan gwiwarta.
“Ka
yafe ni don Allah.” Ya zauna a kan kujera. “Tashi
ba kiyi min laifi ba, jiya ne raina yana bace ba
laifinki ba ne.
* Ya dauki hankicin shi da ke gefe
Ya share mata hawaye.
Ya ce,
“Tashi ki kawo min abin karin.
” Ta ce,
“Na kawo.
” Ta juya don hada mishi shayi. Yana
kallonta tun da ya hada shayi a gabanta, shi kenan
kullum haka take hada mishi babu kuskure
Suga da yake irin ta kwali yake amfani da ita ta san adadin da yake so. Ta
mika mishi, sannan ta sa cokali me yatsu ta ciro
mishi yankan Biredi guda,uku, tasa a cikin plate,
sannan ta aje mishi kwai da dankali.
Ya ce,
“Sannu da Rokari, kina Koari sosai
Ta dube shi “Na gode.
” Cikin jin dadi ta nufi kicin
don kammala kayan da ta yi aiki da su. Yana goge
baki da ‘yar takardar share baki. Ya ce, “Zan tafi
Abuja.
Ta dan ware ido cikin mamaki ta ce,
*Kuma
yaushe za ka dawo?”www.dailynovels.com.ng
Yace
“Yau insha Allah
Ya nuna mata dubu daya a kan kujera, “Ga kudin
namanki nan.
” Ta ce,
“To Allah Ya dawo da kai
lafiya.” Ya shafa kumatunta “Na gode.
Ya fita ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Ya
sallami sauran ya fita. Maigadi ya ce,
“Alhaji yau
motar babu lafiya ne?” Ya ce, “A’a zan hau Jirgi
ne zuwa Abuja, yanzu zan dauki motar haya ne.
YADDA ZAN FAHIMCI MUJINA
Na daya, na fahimci baya cin danyan kifi, na
biyu ba ya son a shiga huruminsa in yana cikin
fushi, na uku yana son komai a gaskiya.
Tayi murmushi da ta karanta, a fili ta ce,
*Insha
Allah sai na gama fahimtar halayensa.
* Ta tashi ta
maida littafin. Ta dauki kudin nama ta fita zuwa
grin Maigadi, sai aka kwankwasa Kofa
Yaje ya bude, cikin mamaki sai ta hango Yaya
Hadiza, cikin mura taje ta rungumeta. Ta dauki
Amira don murna. Yaya Hadiza ta ce, “Duk cikin
murnar za ki dauki wannan Katuwar yarinyar”?”
Da gudu ta dawo ta ba Maigadi sako ta Koma.
Hadiza ta ce “Kin gan mu sai yau ko?” Salma taCe Wallahi kullum ina ta kewar Inna, ya ba kuzo da ita ba?”
Tace
“Sai ta fita takaba sannan zata zo Suna ta hira, Hadiza tace
“Kin yi fari kin Kara dan
Tsawo, amma ba kiba. www.dailynovels.com.ng
Salma ta Ce,
kuma sai ina ganin kamar nayi Kiba.” Ta ce, ‘
“Kin
dai yi kyau, Kila Kibar sai nan gaba.
Ranar ta yini har yamma suna hira. Ta
ba Salma shawarar yanda zata dinga adana kudi
maimakon cin kilon nama kullum. Ta ce, “Na dari
uku ya ishe ki, sauran sai ki ke adanawa. Sai ki ga
kin tara kudin da za a gyara miki daki, duk abin da
babu a sai miki kafin Allah ya ba ki ciki ki haihu
mutane su zo.”
Salma tace
“Sai dai in tambaye shi in ya
yarda, don bana son in yi masa rashin gaskiya, na
kula ba ya son haka.
Hadiza tace Ke amma sakarai ce ko? Ance
miki maza suna son a rage musu kudin cefane
ne?”‘ Salma tayi shiru a ranta tace
*Don shawara
na dauka, amma sai ya yarda, kawai wataran ya
ganni da kudi ya ce ina na samo…?°
Hadiza ta katse mata tunani da cewa,
“Ke fa
har yanzu sakara ce ko?” Salma ta ce,
“Naji Yaya
Hadiza, zan adana.
“To ina ki ke zuwa
kitso?”
sai dai in dan kama da kaina in yi kalaba
Ta ce Ai da yake ma gashin naki ba shi da
zuciya, ko an yi banza da shi sai yayi ta hauka
Salma ta ce Shi ko Yaya ma da na ce ina son “
kitso sai ya ce ya fi son gashin a haka, sai dai in ina son a gyara min in mishi magana
Hadiza www.dailynovels.com.ng
“To shi kenan, kin ko fara zuwa
Makaranta?” Salma ta ce,
“Nasan ya na sane shi
yasa bana mishi zancan
Da za ta tafi, Salma ta ce “Gashi bani da kudi
sai dari biyun Yaya da ya ce in aje masa, bari dai
in debo miki biskit su Amira sa ke zuwa
Makaranta da shi.
Hadiza tace
“‘In kuma yazo yaga an diba fa?”
Salma ta ce, “Nawa ne ya sai min har da alawa, shi
baya cin irin su.
” Hadiza tayi dariya tar da fadin
“Yar gata
Ta saka hijabi da nufin raka Hadiza har bakin
titi. Hadiza ta ce “A’a babu ruwana, kin taba yin
rakiya ne?” Salma ta ce,
“Ban taba fita ko wajen
Gate ba, Allah ina son in fita
Suna cikin jayayya sai ga wata bakar mota.
Shatima ya fito wani abokin aikinsa ya kawo shi.
Ya fadada fara’arsa.
“Sannu da zuwa,
” Ta ce,
“Yauwa Alhaji. www.dailynovels.com.ng
Suka
gaisa. Ya ce
“Ba dai za ki tafi ba?”
Tace
“Wallahi zan tafi ne tun safe nazo.
” Ya ciro kudi a
aljihun wandonshi ya mika mata.
“Ga shi ki hau mota.
” Ta ce,
“Da ka bar shi.”
Yace
“A’a ki amsa, ni na ba ki.” Ta amsa tare da
godiya. Salma ta kalle shi, “Yaya zan dan rakata
titi.”
Ba tare da ya kalleta ba ya ce,
“A’a, ki koma
daga nan.
Ta tsaya cak! Ta mika ma Hadiza ledar
hannunta. Ta ce, “Ki ce ina gaida Inna, ki bata dari
biyar cikin kudin da ya ba ki.
.” Hadiza ta ce, “Ko
ba ki ce ba zan bata. www.dailynovels.com.ng
Ta koma daki ta same shi a cikin dakin bacci,
yana rataye suit din shi a jikin madubinta. Ya ce,
“Wato za ki fita ba izini ko?” Ta ce,
“Ban zaci
zaka yi fada ba. Yace
“To ko waye ya zo ban amince kiyi
rakiya gaba da Gate ba.
Ta ce,
“To Yaya, insha
Allahu.
” Nan ma ta dauko littafin rubutunta, shima
ta rubuta, har ya kalleta ya fito bandaki.
“Me ki ke yi da littafin?”
Ta ce, “Ina yin ‘yan
rubuce-rubucena ne yace
“Yana da kyau haka.
To me ki ka ba Hadiza din?”
•Ta kalle shi “Ai bani
da ko sisi, sai kudin ka dari biyun ka da ka ce in
aje maka.
Yace
“Kuma a dakin ba ki da abin bata?” Ta
girgiza kai tareda dan tabe baki,
“Me gare ni Yaya, na dai ba; Yaranta biskit dina, tunda shi ai
ka ce nawa ne ko?”,
Ya cc, “Eh.” Tace
“Ka ji abin da Ya Hadiza tace?” Ya tattaro hankalinga garè ta da tambayar.
“Me ta ce?”www.dailynovels.com.ng
Ta ce, “Wai in Rage siyan nama da
yawa sai in tara kudin, wai in sai kamar ,na dari uku nace sai na tambayeka in ka yarda
Yace to sauran kudin ayi me dasu? Wai in adana sai a siya min abinda bani dashi
Yace to ai ta baki shawara ne ni bani da matsala da haka in kina ra,ayin rage cin nama kina iya yin hakan tace na gode yaya•Yayi murmushi,
“Sarkin
godiya. Gobe za a kawo form na Makarantar, ki.
Ba ta san lokacin da ta buga tsalle ba har ta kai
inda ya ke ta kuma rungume shi, tana fadin
“Na
gode Yaya.
Yayi dariya,
“Ki samu nutsuwa in
fada miki.”
Ta durkusa a gabanshi,
“To Yaya na nutsu.”
Ya ce Makarantar a nan Unguwar take kusa da
titi, sannan maza ne da mata, in kin shiga ki kama
kanki bana son kiyi abota da wadanda ba za ki
karu ba, ki sa kai kiyi abin da ya kai ki.”
Salma ta ce Insha Allahu zan kiyaye.” Ya ce
“Ban ce musu ke matar aure ba ce, kin ga ke za ki
HMMM LABARIFA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE
www.dailynovels.com.ng