RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY HALIMA K/MASHI
ya’ kwana suka sha soyayyarsu. Tsaraba ta yo masa
masu yawa, kayan sawa, agogo da sauransu. Tana
sonshi da kananan kaya, kuma su ta kwaso masa. Ya ce,Da na sani na ba ki kudin kayan baby kin sayo a can
Ta ce,Momy ta ce, sai an je Dubai don mun
duba babu wasu sabon yayi a can
Shatima ya ce,Amma online za ku siya ko?”
Ta ce, “A’a su Momy za su je karshen watan
nan”Ya ce,
“Nawa zan bada?”Tace Ka bada yanda ka ke da shi, Dady ya cika”.Ya ce, “Hamsin ya yi?”
Ta dube shi tare da zaro idanu, “Hamsin kuma?Ko kudin durowa ba zai kai ba®
‘ Ya ce, “To ni dai kin san Allah a cikin account
dina dubu dari biyu ne da arba’ in. yanzun sai dai in ba
ku dari-dari ke da Nafisa. Can kudin makarantar Salma
inà zaton za su koma Monday din nan
Amna ta ce,Ka bada haka din
Ya kira Natisa, ga ta ga Amna, ya ce, zai ba su
dubu dari-dari kudin siyayyar haihuwa. Nafisa ta ce, to
sun gode.
Bayan fitarta Amna ta ce, “Kawai ka yi transfer
zuwa account din Momy, don ba zan iya ce mata komai ba. Kudin durowar baby din ma ai ya fi darin”Ya ce, “To ni kam karfina kenan’
Ta ce,Ai ita ma jikanta ne sai ta cika Ya yi murmushi, tare da fadin,
“Haka ne
Salma tana cikin damuwa, Shatima ba ya zuwa duba ta da safe kamar yanda ya saba. Ta kan leka ta
window ta ganshi yana shiga dakunan sauran. Ta yi kuka ta gaji, domin ta san karatunta ya zama labari. Kuma ko ranar girkinta da wuya ya shigo dakinta. Ya
daina ba ta kudin nama, komai dai ya tsaya mata cak!A lissafinta yau litinin, kuma yau za su koma makaranta, ta ce ba za ta shirya ba, sai wata zuciyar ta
ba ta shawarar cewa, ta shirya ta ga me zai faru? Tsaf
Ta yi cikin kayan makaranta, amma ta kasa kari. Ta je window ta tsaya tana leken fitowarsa. Tana kallo ya
shiga gurin Aliya da Amna, don akin Nafisa ya
_kwana. Tana ganin ya yi gurin motarsa, Nafisar ta raka
shi, ita ma ta fito ta gaida Nafisa. Da kyar ta amsa sannan ta nufi motar, ya riga ya shiga ya tada, har yana
yin baya. Ta dan bubbuga gilashin. Yanda ya waiwaya cikin harara ta san ya ganta tunda ta zo gurin.Ya waiwaya ya kalli Nafisa, ta shige dakinta
sannan ya sauke gilashin. Da sauri ya katse ta daga
gaisuwar da ta soma yi cewa,Yaya ina.
Ya cE
“Adana gaisuwarki bana bukata”
Ya sa hannu a gaban aljihunshi ya ciro dari
biyar ya jeho mata,
“Ga shi ki hau mashin, ba za ki
Kara shigar min mota ba
Ta duka ta dauka, sannan ta dago ta kalli
fuskarshi, a tamke bai ko kalli inda take ba ya zuge
gilashi. Salma ta juya fuskarta fal damuwa, don sun yi
kadan ta sani ba dakatar da karatunta ba sai dai tana jin
ya rage ma karatun nata karsashi A makaranta babu wanda bai gane tana cikin
damuwa ba, Salma Dankasa ta matsa da son jin damuwar aminiyar tata, sai ta ce mata ba ta jin dasi ne
kawai. Ko da ake musu karatu tana dai sauraro, amma
ba ta fahimta.
Salma Dankasa ta ce, ta raka ta asibitim cikin
makaranta. Salma ta ce, a’a ba za ta je ba, tana da
magunguna a gida.
Ranar ita ce da miji, ga shi kuma bai ba ta
kudin cefane ba, don haka sai ta dumama sauran
miyarta ta dafa farar shinkafa. Karfe shida da rabi na
yamma tana wanka sai ta ji motsin shigowa da kaya.
Ta san Shatima ne, amma ba ta san kowane irin kaya
ba ne. da ta fito shi ta gani tare da wani suna kokarin
shiga da katifa cikin daya daga cikin dakuna biyun da
babu komai.
Ya dube ta, “Zo ki kwashe tarkacen da ke cikin
dakin nan”
Da sauri ta shiga, babu wani tarkace sai *yan
kayan da ba ta fara amfani da su ba. Ta maida su a
durowar kicin. Dakin babu datti don kullum sai ta
share shi ta goge ko da babu komai. Ya sa katifa da filo
guda biyu. Kafet din tsakar daki duk a Kasa ita, dai
tana zaune tana kallonshi, da ya gama kuma suka fita.
Ta Ieka dakin, har zanin gado ya saka. Bayan is’ha’I ta
ji shigowarshi, ta fito sai ta ganshi da talatijin, da tasoshi ana canzawa. Sai tara da rabi ta ji fitarsu tare, taje kicin ta hada mishi abinci. Tana fiowa yana
shigowa, don haka yana shiga dakin i’ta ma tana shigowa Tun kafin ta yi taku na uku a dakin ya katse
mata hanzari da cewa,
“Ko ma da shi, na koshi”
Washegari ma da safe bai dubi abin karinta
ba, ya aje mata dubu daya wai na cefane da kuma na
makaranta. Salma ta ce, “Na gode
Bai tanka ba ya fice.
Ta shirya ta nufi
makaranta. Duk satin ba ta da sukuni, babu walwala ba
ta damu da kudin da ya rage mata ba. Damuwarta ya
yafe mata su koma Kamar da. Sai dai yiwuwar hakan
da kyar ne, domin yanda Shatima ke mu’amalantarta a
yanzu tamkar bai taba saninta ba, ko kuma babu wani
sabo a tsakaninsu. Duk ranar da yake dakinta ba ya
zama a falonta sam in ya dawo ma ba zai shigowa sai
bayan isha, kuma abincinta tuni ya daina ci, ya ma fada
mata cewa ta daina zuba mishi. Tana kallo tsakanin
Aliya ko Nafisa duk wadda ya ga damar cin abincinta
sai ya sa ta kawo masa har dakin.
Haka kuma da safe yana da
“yar karamar hiter
da kayan tea sai ya hada abinshi, in kuma yana son
dankali ko wani abu haka, sai ya sa matansa su kawo masa.
Tun Salma tana kuka har ta dake ta saba da
sabuwar rayuwar da ya tsirar musu ita da shi. Ba za ta
tuna dariyarshi da ta gani ta karshe ba. Ba ta taba
tsammanin haka yake da daukewa da dakewa ba sai da
matsalar nan ta shigo. Yanzu shakkarsa ma take yi, da wani mugun tsoronsa da ya darsu a zuciyarta.
Wataranar asabar tana shanya kayanta tana
sauri taje ta yi assingment sai ta ga shigowar motoci
guda biyu. Ko ba a fada ba ta san bakin Amna ne, dan su ke zuwa akai-akai, kayan haihuwa ta ga ana shiga da
su, tun daga kan gadon jarirai zuwa durowa da sauran
kaya. Salma ta yi murmushi har zuciyarta ta yi doki zasu sami jarirai a gidan. A fili ta ce,
“Ashe zamu sha suna?”
Kayan da ke cikin akin baki aka fito da su
zuwa barandarta, aka jera kayan jaririn a ciki komai
blue mai haske. Amna ta kalli dakin ji take yi tamkar
ta haihu yanzu. Ta sa hannu tana shafa cikin ranta fal farin ciki
Haka da Shatima ya shigo ba a dakin yake ba,
dakin Nafisa yake amma sai ya nufi dakin saboda
ganin gadon Amna a waje. Ya shiga, tana zaune a kan
kujera a falo tana kallon wani shiri da take bi a tashar
Africa. Ta dube shi tare da amsa sallamarshi, ya isa
gurinta da tambaya,
“Shin me ya faru a dakin can na ga
kaya a waje?”
Ta ce Kama ni in mike”
Ya kamata tare da fadin,
“Sannu”. Suna shiga
dakin, Shatima ya rungume Amna ta baya yana shafa
cikinta, ya ce,
“Har na kosa baby ya zo gaskiya dakin
nan ya yi kyau, sai na ji kamar ya zo yanzun”
Amna ta shafa hannuwansa da ke kan cikinta, taCe,
“Wallahi honey ni ma haka na ji. Allah dai ya saukeni lafiya
Ya ce,Ameen-ameen kullum addu’ata kenan
“To kin ki mu je a yi miki awo
Ta ce,Ni fa ba a nan zan haihu ba, Dad ya ce
England za mu je a can aka haife ni”
Shattima ya saki amna cikin sauri ranshi yai mugun baci yace,
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe