RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 12 BY HALIMA K/MASHI
Shatima ya saki Amna cikin sauri, ranshi ya
mugun baci ya ce,
“Gaskiya wannan karon ba zan
amince da abin da ki ka zo da shi ba, shi ya sa ki kaqi in kai ki kowane asibiti?”
Ta ce, “Wai me ya sa ka ke son mu yi rigima
ne? Duk abin da iyayena suke yi saboda lafiyata ina tsammanin jin dacinka ne, da kuma hutar da kai a kan
was abubuwan?”Shatima ya ce,
“A bar ni mana in yi daidai
Karfina. Ni fa sai ina ganin kamar ana nuna ban isa ba,
ko kuma na kasa Ta ce,
“Ok, in lokacin ya zo sai ka fada wa Dad
din ba zan je ba”.
• Ta juya ta fita cikin fushi.
Ya yi shiru a cikin dakin, wata zuciyar ta ce
masa, kada ka bi da fushi, ka bi komai a sannu. Ya fito shi ma, ba ta falon kai tsaye dakinta ya nufa ya same ta
kwance a kan gado. Ya zauna ya dafa ta,
“Kin yi fushi kenan?”
Ba tare da ta dago ba ta ce,
“Ta ya ya ba zan yi
fushi ba, kowane lokaci sai ka dinga nuna bacin ranka
in an ba ni kulawa. Har ka sa na soma tunani, na saka shakka a cikin son da ka ce kana min
Ya tashi ya dago ta zaune, sannan ya rungumeta,
“Ki yi hakuri matata. Tsananin sonki ne ya sa bana son ki yi nisa da ni”
Ta sa hannuwanta ta ta dago fuskarshi,
“In haka ne ba sai mu tafi tare ba?”
Ya kalli cikin idonta,
“Akina fa?”
Ta ce, “Shine kadai matsala”Yace
“Ina son mu je asibiti a duba ki, don a
tabbatar min cikin lafiya
Ta ce, “Yana lafiya fa, ko a saudi da muka je
sun auna ni sosai”
Ya ce, “To ,,,,,,,,,fa?”
Ta ce,Cikin watan da za mu shiga ne, biyar ga
wata”Ya ce,Yaushe ne tafiyar?”
Ta ce, “A na kan shirin tafiya kenan, zai yiwu
ma cikin satin nan don na ce ma su Dad bana son in fara labour kafin a kai ni”
Ya ce, “Aiki ki ke so a yi miki?”
“‘Ni na fi son aiki in samu baby ba tare da na
wahala ba Shatima ya ce,
“To Allah sauke ki lafiya Ta ce,
“Amin Ya ce,
“To ya za a yi da kayan gadon can na
waje?”Ta ce,
“Ni na san ya za a yi da shine? In akwai
gurin da za ka ajiye ta ka ajiye kawai”
Ya ce,
“In ba dakin Salma zan kai ba, ba ni da
gurin da zan aje”
Ta ce,
“Ni fa ba abin da zan yi da shi”
Salma tana juye shinkafa a kula don ranar mai
da yaji take son ci, sai ta ga maigadi da Shatima suna
shigo da kayan gado. Ba ta ce komai ba, suka shiga da
su dayan dakin suka jujjingine har da sif. Ta yi musu
sannu, Baba maigadi ne kawai ya amsa. Yana fita
Shatima ya kalle ta, “Kayan Amna ne kada ki Bannata musu”
Salma ba ta iya amsa masa ba, domin dai ta san
duk cikinsu babu wacce za ta yarda a kai mata ajiyar
kayan kishiya. Wata zuciyar ta ce Ki ka sani ko don
ba ki da kaya a dakin ne, da kina da shi ba zai zo ya
cire naki ya sa ba
Sai ta amince da hakan, kuma ta ji ta sauke
haushin da ta ji. Wannan shine ya sa kullum Salma take da kyakkyawar zuciya, don tana da kyautata wa
kowa zato.
Duk da Shatima ya yi iya kokarinshi don kada
Amna ta fita wata Kasa da sunan haihuwa sai dai hakan
ya ci tura don ya yi kokarin kai ta asibiti dan ya hada
baki da likitan ya kara a kan lokacin da ake tsammanin
haihuwarta. Sun je an samu nasarar yin hoton, kuma an
Kara kamar yanda aka sa. Nufinshi kafin su yi shirin tafiya ta haihu.
Amma sai dabarar tashi ta tada musu da
hankali, har ma ta sa suka soma haramar tafiyar. Amna ce ta yi mugun daga hankalinta tunda ta ga takardar
hoton, kusan wata daya da kwanaki ya Karu a kan
dukkan hotunanta na baya. Cikin damuwa ta kira mahaitinta ta sanar da shi, ya ce lallai ta shirya su tafi a
cikin satin nan maimakon na sama.
Dole Shatima ya sa ido suka aiko aka dauke ta
suka tafi. Abin da bai sani ba ma iyayenta suna shake
da shi, domin nasu ganin ya kamata ya dauki uzuri gurin aikinshi su tafi tare. Amna ce ta ke nuna musu
cewa, aikin babu damar hakan. Ya shiga mugun tashin
hankali da damuwa. Aliya ce ta rungume shi tana
lallashi tare da ba shi magana. Hakan ya sa shi son
kasancewa tare da ita a ‘yan kwanakin nan.
Sati uku da tafiyar su Amna aka ciro santalelen
yaro mai kyau kama da ubansa, mahaifin Amna da
kanshi ya kira Shatima yana masa albishir da samun
karuwar. Murna sosai Shatima ya yi tare da kiran nasa
mahaifan ya sanar musu. Nan da nan labarin haihuwar
ya watsu a dangi. Hajiya aka shiga shirya kayan barka.
Shatima yana kwance a kan katifarsa ranar
dakin Salma yake. Kwanaki uku kenan da haihuwar,
amma maijegon ta ki daga layinsa. Ya san tana fushi
ne tunda suka tafi sau daya ya kira ta, shi ma Aliya ta
matsa masa. Ya tura mata sako yana mai rokon
alfarmarta cewa ta daga, sannan ya sake kira. Ta dauki
wayar ta yi shiru duk da tana jin sallamar da yake dokawa.
Ya ce, “Ki yi hakuri Honey, ko mene ne tunda
mun zama iyaye bai kamata muna fushi ba. Zafin rabuwa da ke har kuka na yi, shi ya sa bana kiranki”Cikin shesshekar kuka ta ce, “Ka nuna min
matsayina, kuma na gani. Sai dai kullum in tayi
Momy karyar mun yi waya kana gaida su, don kawai
kada mutuncinka ya zube amma ba ka gani”
Nan Ya yi lallashinta, da kyar ta sauko sun yi waya sosai, kuma za su dawo cikin satin da za a shiga.Dun Ya ce, “Suna fa?”
Ta ce, “Sai satin sama”
Ya ce,A nan za a yi mishi huduba?”
Ta ce, “Dad zai masa dama ya ce mu yi
maganar sunan da za a sa mishi da kai”
Don ya sake faranta mata, ya ce, “Na ba ki zabi zumata
Ta ce,Kamanninka da yaron ya sa na darsa
sunanka a zuciyata, in ni zan zaba ina son a sa mishi
Muhammad Ja’atar”Ya ce,
“Yanda ki ke so haka za a yi, amma na
sa za a yi taron rada suna a gidanmu can Zaria, bikin
mata sai kun dawo”
Ta ce Haka ya yi”
Ya Ce.
“To a turo min hoton yaron nawa in
ganshi”Ta yi dariya,
“Ka ci sa’a da na ce sai randa
• muka dawo ka ganshi”.
Ya ce, “Da ma ni mai sa’a ne tun daga lokacin
da na mallaki zuciyarki
Ta sake sakin dariyar jin dadi sannan ta ce,
“Zan turo maka yanzu ta whatsapp”
Ya kalli yaron cike da so tsantsa da kauna, fari
ne tas cikin kayan jarirai masu kalar sararin samaniya.
Tabbas yaron yana kama da shi sosai. Ya mike ya
dauki jallabiyarsa ya zura.
Salma tana zaune tana assignment ta dago ta
dube shi, shi ma ya kalle ta tamkar zai yi magana
amma sai ya fasa. Ta maida kai ta ci gaba da rubutunta
domin inda sabo ta saba da yanda Shatima ya rikide
yanzun. Ta kula kwanakin nan yana cikin farin ciki da walwala.
Dakin Aliya ya shiga ya nuna mata hoton
kyakkyawan yaronsu. Ta yi farin ciki tare da fadin,
“Yaron nan kama yake da kai sak!”
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe