RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 23 BY HALIMA K/MASHI
Ta ce, Zan tura abina ne daga wayar Aisha
ka aje min. bai san dalilin da ya kasa hana taba, illa dai ya ce.
“Kar ki yi min wasa da wayà. Tun kafin ta
nemo Aishar ta soma daukar sabbin hotuna da wayar ta Shatima ta sake zuwa ta Dauki Jafar suka yi wasu. Aliya ta sha mamaki ganin wayar Shatima a hannun
Salma, ta tura
duk hotunan da ta yi a
wayoyin jama’a sannan ta je ta kai masa. Lokacin saura su ‘uku a cikin dakin da suka ci abinci. Ta mika mishi tare da godiya, sannan tace Yaya ni ma fa
zan je kai Anty Badi’ atu”.
Ya ce,Ina?”
Ta yi shiru don jin yanda ya amsa da karfi.
Munnir yace
“‘Katsina mana
Shatima ya hade rai,
*Koma ciki malama
babu inda za ki je
Za ta yi magana ya ce,
“Bana son jin komai”
Salma jiki babu Karfi ta fita ta koma cikin
gida. Dakin Hajiya Kaka ta shige ta takure a bakin
~ gado. Hajiya Kaka da take zaune kan sallaya suna
hira da wasu
*yan uwansu ta kalli gadon tare da
tambayar wane ne nan ya yi rijib a gado?
Salma cikin damuwa tace
“Nice
Hajiya Kaka tace
“Salamatu ce?’
Salma ta ce. “Ni ce Kaka’
Ta ce.A’a na ga kin saka kaya kin fita
yanzu?”
Salma cikin shagwaba ta ce,
*Yaya Shatima
ne wai ba zan je raka Anty Badiatu ba, kuma Kaka yadace a ce shi yana babba ya mu hudu matansa ace babu wanda ya je rakiyar Kanwarsa gidan miji?” Kaka tace
*Zance yake yi, dole kuwa a samu
mai zuwa a cikinku. Ina Shatima, a kira min shi”Salma ta ce,
“Sal dai in sa a kira shi kar ya ce
Karansa na kawo
Hajiya Kaka ta ce,
*Kira min Saude ta sa a yi
min magana da shi”
Salma ta fita cikin murna ta bar Hajiya Kaka
tana fadawa wadanda suke zaune tare, kirki da hangen nesa irin na Salma.
Tace
“Yarinyar nan ga ta karama amma
lissafi gare ta irin na manya, ga ta da kokarin kyauta ga girmama mutane
Saude ta shigo tana fadin,
“Ga ni kaka, ina
shiryawa ne za mu kawo amare ki musu fada a kai su
gurin iyayensu a zo a tafi, don Badi’ atu tuni Alhaji
ke waya su zo tafiya da nisa”
Kaka ta ce,
“To ku kokarta ko a tafi. Yanzu, ban da shirme irin naShatima a ce ko
daya cikin matansa babu mai
zuwa?” Anty Saude ta ce Ai ba zai yiwu ba, tunda ita babbar cikinta ya girma ita karamar mu je tare ko
kuma Maman Jafar tunda Nafisa babu hali ita
wanna ga tsohon ciki’ Kaka ta ce,
“Kira min shi an ce yana dakin
•bakina Salma tana jiyo muryar Shatima yana gaisawa da mutane a falo ta shige bandakin Hajiya Kaka. Tana jin lokacin da yace
“Kaka ga ni, an ce
kina nemana ruwa a jallo Ta ce.
“Zauna dan nan ka fada min in ji ko
gaske ne. wai babu wanda zai je a cikin matanka Yace
‘Me za su je kuma su yi kaka?”
Tace Ka ji zancen banza, kai ne fa babba a
cikin gidanku, matanka hudu amma babu wadda zata raka kanwarta, ai ko dai da ka ji haushi. Babu wadda fa ta je jere cikinsu’
Shatima ya ce,
“To wa za shi cikinsu, Nafisa suma cikin hidima suke, Aliya ta yi nauyi, ita ko
Amna ba son shiga jama”a take yi ba’
Salma ta bude Kofar bandakin ta fito daidai
lokacin da Kaka ke fadin, “To ai ga Salamatu”
Ya kalli Salma,
“Kin zone kin kawo karata?”
*Yan dakin suka sa baki da cewa,
*Gaskiya matanka ya dace su wakilceka a wanna tafiya’ Jin baki ya yi yawa ya ce,
“To shi kenan
Kaka su je duk wadda za ta
Ya dubi Salma, “Ki same ni a dakin baqi
Kaka ta ce,
“Kada in ji ka yi mata fada, ba
Kara ta kawo ba”Ya ce,
“Kar ki damu Kaka kudin shan ruwa a
hanya zan ba ta Salma ta kalle shi don ta, ya sakar mata harara. A tsorace tabi bayansh, motarshi ya shiga ita ma ta bude ta shiga. Ya rufe ta da fada, ta
sunkuyar da kai yana fadin,
“Ke shegen yawo ki kasa a ranki shi ya sa har ki ka kai Karata, ina ta lura da
rawar kanki da ki ka kama yanzu. Jiya ina kallonki
Salma ta yi saurin dubanshi tare da fadin,
“Mene?’Ya ce,
“Mayafi ma aje shi ki ka yi ki ka kama
yawo haka jiki duk a matse, kina manta cewa kina da aure ma ko?”
Salma ta sauke ajiyar zuciya ta godw ma Allah
da ya sa iya rashin mayafin ya gani. Ta girgiza kai tare da fadin,
“Bana mantawa Allah kuwa
Ya ce,
“Kuma tunda kin matsa sai kin je ki je
din, amma ki
sani duk wani motsinki zan sani,
sannan kuma ko naira ba zan ba ki ba
Ta saki fara’a,
“Babu abin da zan yi ma, babu
komai in bà ka da kudi
Yace, “Ina da shi, ba zan bada babe
Salma ta ce,
“Yaya in har kana ga zuwana din
ba ka so Allah a barshi. Da ma dai rashin dacewar aCe mu ba mu je bane kana kai babba shi ya sa har na
yi magana Yace
“In kin zauna ma me za ki yi min? ki
je kawai abinki”Ta ce,
“To na gode, bari inje in shirya”
Har ta fita, yace
“Amsa Dubu biyu ya ba ta, ta sa hannu biyu ta karba,
ta ce, “Na gode
A Katsina gidan amarya ya yi kyau, duk da
cewa kowa da barinsa. Ita da kishiyarta amma gida daya suke, irin tarbar da suka samu daga dangin
mijin su ne suka saka ran cewa ta karbu gurinsu.
kishiyar ce dai sai dai a ce Allah ya kade fitina,
domin kanta tsaye washegari bayan an yi budar uwargidan don a hada su, tace
“Kar ku ce min
amana, don ba a bada amanar kishiya
Anty Saude ta ce,
“To, mu dai fatanmu a
zauna lafiya, zama na amana”
Ta ce,Idan ta so haka za a zauna
Duk suka sha mamaki, don haka da suka
dawo dakin Badi’atu suka yi ta mata nasiha, tare da
jaddada mata hakuri. Da za su taho Badi’atu ta sha
kuka, haka ma Salma.
A Zaria kuwa bayan tafiyar
‘yan kai amarya
Katsina, Shatima ya samu su Aliya ya ce su shirya su
koma don gobe zai wuce Abuja. Amna dama a takure
take, nan suka koma gidan Hajiyan Shatima don shiryawa. Aliya kuma ta ce, bari ta je gidansu su
gaisa tunda ba taje ba. Har ta ce da zai barta zuwa gobe. Yace
a’ a, su gama komai zuwa bayan
magariba. Ya dauki mota ya nufi gidan su Nafisa
lokacin motocin daukar amare sun fita da suke nan an kuma kwashi jama’ a. Har,zai juya don ya san kila
HmMm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe