RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY HALIMA K/MASHI
don ta samar da sotsan tsamara gauraye. Ashe ita tana
aikin banza ne, gara ma da ta sani tun da wuri.
Ta dago jajayen idanunta ta kalle shi, yana da
Kimar da ba za ta iya maida mishi magana ba, don haka
ta sake sunkuyar da kanta.
Alhaji yace
“Duk abin bai kai a yi wannan
tone-tone ba, kada in Kara jin an yi zancen saki, ko
asiri www.Dailynovels.com.ng
Ya dubi Hajiya Amina, yace
“In kin ci gaba
da dagewa a kan wannan maganar zan ta sa ki har
gaban Hajiya Azumin, sannan mu je gurin malam su bani hujja’
Ya nuna ta da yatsa,
“Kin san zan iya Alhaji Musa ya ce,
“Wannan shine gaskiyar
magana
Mama ta ce, «Ni wallahi duk wannan abu ba a
son raina suka faru ba. Ban so aka tono wadannan zantukan ba, tunda ban san komai a kai ba. Mun dai z0
duba mara latiya
Alhaji yaja tsaki, “Ga shi mun rasa jam’in
magariba a kan zantukan nan marasa tushe, bare makama
Ya kalli Hajiya,
‘”Ke ce babbar mai laifi a cikin
wanna al’amarin”
Ya kalli Salma «Tashi yarinya kin ji daga
wanna durkuson
Salma ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta yunkura
da niyyar tashi. Kafafunta sun yi tsami, ba za su iya daukarta ba, don haka ta koma ragwat! Ta zauna.
Alhaji Musa ya ce,
‘”Sannu, Kafafun naki duk
sun yi tsami ko?”
Ya sa hannu a cikin aljihunsa ya ciro kudi ya
kirga naira dubu goma sha biyar ya mika wa Shatima, ya ce,
“Ga shi ka sai mata waya ko karama ce, don ita ma ake saka mata katin ko da iyayenta sa gaisa
Ta dubi Alhaji Musa ta ce,
“Baba na gode”.Muryarta tana rawa.
Yace
“Babu komai “yata”
Yaci gaba,
‘da Kowacce ta koma gurinta ta zauna lafiya da mijinta da
“yar uwarta, zuciya daya
Amna ta kalli Hajiya,
“Babu maganar asiri-asiri ko?”
• Alhaji ya amshe,
“Babu wata magana da ta
shafi asiri, duk sharri ne’ www.Dailynovels.com.ng
Ta ce,To, ku gaida gida”.
Ta nufi sashenta cikin jinjina abin da ya faru.
Aliya ta mike tana fadin, “Ga shi ko abincin ma
ba ku ci ba. To ku gaida gida”
Salma ta bi Aliya da kallo, ba ta shakka ita ce ta hada komai. Ta soma tuno wasu abubuwa da ta yi mata masu kama da ingiza mai kantu ruwa.
Salma ta yunkura ta mike da kyar ta dubi su
AlhajiBaba ku gaida gida”
Ta kalli su Hajiya,
– “Sai anjimanku, Allah ya
tsare hanya Su Alhaji suka ce,
“To sai anjima, ki yi hakuri
kin ji ko?”Hajiya ta tabe baki tare da raka Salmar da harara.
Nan Alhaji ya yi ma su Hajiya fada sosai,
sannan suka ce,
“Ku shirya bari mu yo sallah mu zo
mu wuce”
Salma ranar da zazza6i ta kwana, haka kuma ba
ta jin cewa za ta je a yau. Lokacin da Shatima ya shiga
gurinta da safe tana nade a zanin gado a can tsakiyar
gadonta. Ya kira sunanta,
“Salma”.
Da kyar ta daga idanunta jajir ta ce, “Na’am.”
Ya ce, “Ya ya dai, ba ki da lafiya ne?”
Ta maida idanu ta rufe, zuwa yanzu ba ta son taji ko ta ga Shatima. Ta ce,
*”Dan zazzabi ne’
Ya hau gadon ya saka bayan hannunshi a
sassan wuyanta. “Kai! Haka jikin naki ya yi zafi? Tashi
in kai ki asibiti www.Dailynovels.com.ng
Ta yunkura tare da fadin, “Ka barshi kawai, zai
bari anjima kadan
Ya ce, “To in turo Aliya ta duba ki?”
Ta ce,
“Ka barta anjima kadan zan warware”
Ya ce,
“Yaushe ki ka soma gardama da ni?”
Salma ta yi shiru,
Ya kama hannunta,
“‘Sakko in kai ki asibiti”
Jallabiya ta saka
suka tafi.A bakin
makarantarsu suka tsaya, ya rubuta *yar takarda ya ba
wa mai gadi ya ce ya kai ofishin shugaban makaranta.
An ba ta allura da magunguna, ya dawo da ita
gida. Ya shiga gurin Aliya. Da ma ta ga fitarsu, ya ce,
don Allah ta lura da ita ba ta da lafiya.
Aliya tace, “To”Yana fita ta zauna cikin fargaba, kar dai ita ma
wannan cikin gare ta? Na ba ni ni Aliya, nice kenan
zan zama karshe?”
Ta mike da sauri tare da fadin, “Bari na je
dakin Salmar na gani”
Ta same ta kwance kan kujera. Salma tana
gaminta a ranta ta ce, “Allah ka yi min tsari da duk
sharrin da matar nan ta zo min da shi
Aliya ta je gabanta ta tsaya tare da rike kugu,
“Ashe ba kya jin dadi?”
Salma ta ce,
“Uhum”.
Aliya ta ce,
“*Ko ke ma cikin ne?”
Salma ta ce, “Oho! Ni ma ban sani ba”
Ta sake matsawa kusa da ita,
“Wane irin gwaje-
gwaje aka yi miki?”www.Dailynovels.com.ng
Salma ta yi mata banza. Tsaki ta ja ta fita tana
mitar, yana fadin ba ya sonta amma ga shi nan da
cikinsa a jikinta.
Salma ta shiga kunci da bakin ciki sakamakon
kalaman Shatima. Duk da wautarta da Kuruciya ta san
Shatima ya ba da ita badawa ta karshe, ya kunyatata
gami da tozartata. Ta yanke ma kanta dakatar da son
Shatima, sannan za ta ja baya da shi. Za ta ci gaba da
kallonshi a matsayin Yaya kurum
***
Kwanci tashi asarar mai rai inji masu iya
magana. Amna da Nafisa ciki na ta girma. Domin
Amna tana da shidda, Nafisa tana da wata biyar.
Shatima ya samu Amna da batun zuwa awon
ciki, ta ce masa ita sai sun dawo daga umara. Ya dube
ta cikin al’ajabi,
“Za ku je ummara yaushe?”
Tace
“Jibi insha Allahu za mu tafi da su
Momy
Yace, “Ikon Allah, shine ban isa ki fada min
ba bare ki nemi izinina?”www.Dailynovels.com.ng
Ta ce,
“Jiya Mom ke fada min ni ma’
Shatima ya yi shiru cikin bacin rai. Ya sauke
ajiyar zuciya, abu daya zai sa ba zan hana ki ba, amma
gaskiya a guji shigar min hakki”
Ta dube shi.
“Ban gane ba? Kana nufin da sai
ka hana?”Yace
“Kwarai kuwa
Ta yi *yar dariya irin ta rainin wayo, ta ce,
“Kai
kana da son rigima”
Ya kauda zancen don ba ya son su fara sa’insa,
don haka sai ya ce, “Ke nan ba ki nan za a yi bikin su
Hannatu, yaran Yayan Alhaji marigayi na Kaduna?”
Ta dan yatsina baki,
“Ko ina nan ka san bai
zama lallai inje ba don bana son hayaniyar mutane
Shiru ya yi yana kallonta, don tuni ya lura ba ta
son duk wani al’amari da ya shafi danginsa, domin ko
kwanan baya da Hajiya Kaka ta yi rashin lafiya babu
yanda bai yi ba a kan su je a duba ta ba, amma ta ki,
kuma sauran duk sun je. Amma bari ya yi mata uzuri ta haihu.
Bikin “ya’ya biyu za a yi, babban dan Kaka
wanda ya rasu, bikin a Zaria za a yi shi. Haka kuma
bikin zai kama ana saura sati daya azumi. Da Amna ta
HMMM LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe www.Dailynovels.com.ng