RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 15 BY HALIMA K/MASHI
Ta kalla ta Bata rai, “Gaskiya Maman Afra
ba zan iya shan wannan ba, zan yi amai”
Ta ce,In kin sa a ranki cewa za kiyi ba”
Ta kama hannunta ta dora mata kofin, tare
da fadin,Zan Kara hada miki wani kala yanzun,
sannan ki sha da niyyar biyan bukata”
Amna tana bata rai tana komai ta shanye
garin dakan, sannan ta kuma shanye gumbar data ba ta. Ta sha zuma, ta sha tsimi, har sai da taga ta kusa aman da gaske sanan ta barta. Ta ba ta wasu na matsi, ta ce,
“Kayan nan ba su da wata illa, masu kyau ne, kuma za ki dawo ina nan. Yaushe mijinku zai dawo?” Ta ce,Yau ne, amma dakin Aliya yake
sauka, sai ya tafì dakina” Ta ce, “Wai har yanzun yarinyar nan ba ta dawo ba?”Amna tace, Ba ta dawo ba, kuma wani abin al’ajabi Baban Jafar yaqi fada min dalili. Ko da sau biyu na taba tambayarsa, sai ya ba nì amsa iri daya wai ba matsalata ba ce” Maman Afra ta sa dariya tare da fadìn,Ni kuma ya burge ni, domin ke ma ba zai fada ma wata sirrinki ba
Amna ta ce,*Ai kuma hakan yake, Baban
Jafar ba zai taba yin zancen wata ba ko da sunan wasa, kuma yana son hada kan yaranshi in dai yana dakina ba ya karanta ma Jafar kananan labaran da nike karanta masa, sai dai ya ba shi labarin yan uwansa su Ashraf,
ya kawo abubuwan da ya san Jafar na so ya ce in ji su. Kullum yana damun Baban
wai ya kai shi gurinsu, kayan wasanshi haka zai ba da wai a kai ma kannenshi” Maman Afra ta ce,Gaskiya salonshi yayi sosai, ki ke ki taimaka a kan haka, in yara suka samu kyakkyawar tarbiyya tunda farko suna
tashi da hadin kai. Amma wani lokacin iyaye
mata ke kashe wannan dangantaka, wata sai ta ja ya’ yanta daki ta yi ta cusa musu mummunar akida tana rushe ginin da uban yake yi” Amna ta ce,Haka ne, amma ni ba ni da wannan ra’ayin, ina son yara su tashi da hadin kai* Mamaki Amna ta yi a ranar da Shatima ya kwana a dakinta. Ta kira Maman Afra ta kasa magana, sai dariya. Maman Afra ta ce, Adana sirrinki, na san da ma za a yi haka, wancan na baki dandane,- yanzun in kina so sai ki shirya kudinki in sa ki a kan layi”
Amna ta ce,Zan shigo” Yau da gobe asarar mai rai, cikin Badi’atu wata tara, da kuka ta kira Hajiya wai a z0 a dauke ta in ba haka ba za ta mutu. Hajiya ta tsorata sosai don ba ta san cewa Badi’atu tana cikin matsala ba. Anty Momiyo ce suka je sun samu Badi atu ta rame, ta yi baki. Nan ta soma karanto matsalolin da ta ke fuskanta. Ta ce,Har zuwa yanzun ba a sai ko wando na jariri ba, wai matarshi ta ce ba yanzunba, kuma kowane lokaci za ta iya haihuwa. Abinda ya ba su mamaki ko da mijin ya dawo suka yi masa zancen tafiya, wai sai sun yi shawara. Washegari da kanta Maman Kausar ta shigo har gurinsu suka gaisa, ta
ce musu,Gaskiya babu maganar tafiyar Badi’atu, domin mu ba ma wannan al’adar’
Anty Momiyo ta ce,Tofa! Ai mu shi muka yi wa magana ba ke ba Ta ce,
“To ai shawara muka yi da shi da
mahaifiyarsa. Amma tunda kun ce hakan bari
kwa ji daga bakinsa, ko na mahaifiyar tasa”
Baba Ladi yar uwarsu da suka zo tare, tace,
‘”‘Ai mu ba ruwanmu da wata mahaifiyarsa”
Maman Kausar ta fita, Anty Momiyo tace,
“Ai kawai Baba Ladi mu tashi mu hada kayan yarinyar nan mu nuna musu babu fashi.
Kalli don Allah yanda Badi’ atu ta koma”
Baba Ladi ta ce,Kafin haka, jira mijin ya
zo mu ji ta bakinshi”
Shatima yana tsugune yana gaida Hajiya,
nufinshi da sun gaisa ya wuce dakin Alhajinsa
don duba jikin Alhajin, ya zo bai ji dadì ba. Haka kuma ba ya son jin komai daga bakin Hajiyar don kullum zancen daya ne, ya saki Salma. Shi kuma wata irin kauna da
son Salma yake ji wanda ba zai iya fassarata ba, amma sai Hajiyar ta ce,
*”Zauna ina da magana da kai ka sani”
Ya ce,Hajiya ai kin fada min maganar
Salma ce”Hajiya ta ce, “Ni fa babu daga Kafa sam-sam ba za ka bar garin nan ba, sai ka sake ta Shatima ya ce,Hajiya kin san ban isa in
kai takardar gaban Hajiya Kaka ba’ Ta ce,
“Shi ya sa kwanan baya ka dauki
Salmar a mota har da wulakanta Aliya a
gabanta?” Shatima ya ce,In ji wa?”Ta ce,
“Bari ka ji, duk abin da ke faruwa a
gidanka na sani. Wato ga
*yar iska ina nan ina hakilon ka sake ta, ashe kai kana can kana
lallaba ta kana kiranta a waya, sannan har ka ganta babu izininka ta tafi yawonta, amma ka
dauke ta har kanama matarka mai haihuwa
tsawa? To ka dawo min da kudadena don na san ita za ka sakar ma ta cinye su. Bari ma ka ji..Kiran wayar da aka yi ta Hajiya ita ce ta
sa ta fadin,Je ka dubo shi kazo yau sai an yi
an gama, in ma Kakar za ta rike ta ne bayan ka sake ta, sai ta ci gaba da rike ta. Ai daman kai tuni ka fada ba ka sonta, wannan faman ma da nike yi da kai duk aikin asiri ne, na sani”.
Shi dai ya fice cikin sauri ya shiga gurin
Alhajinsa. Alhaji yana kishingide yana duba jarida, Shatima ya ce,
“Alhaji ba ance ka samu hutu bane?”Ya ce,
“Ubana ai gani a kwance ban fita ba”Ya ce,
“Amma ka dauki jarida kana dubawa?”
Ya ce,To in ban fita ba kuma ban duba
halin da duniya take ciki ba Babana nan ma sai zuciyar mutum ta buga Shatima ya yi dariya, sannan ya zauna tare da fadin,
“Ai kwakwalwarka ake bukatar ta
huta”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe