RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY HALIMA K/MASHI
Alhaji ya’ce, “Barsu duk wannan ba za ta hana mai rai mutuwa ba, sai dai in lokacinsa bai
yi ba Shatima ya ce,Haka ne, Allah ya ba mu
sa’a Ya rusuna yana gaida Alhajin, bayan ya
amsa ya ce,Ni fa sai na ji kamar muryarka,
amma da na ga tun jiya zuciyata ta ke min gizo ina jin muryarka, sai na tsammaci yau ma haka ne” Shatima ya ce,Ai haka kawai na aje
gidana na nufo in ga jikin”.
Hajiya ta shigo hankali tashe, tana fadin,
«Wallahi su taho min da ‘yata gida, ai ko ba zata sabu ba” Alhaji da Shatima suka dubi Hajiya duk cikin son Karin bayani. Hajiya ta ce,
“Ku ji abin tsiya, wai Badi’atu ba za ta dawo gida ba in ji uwar mijinta da kishiya. Su suke aurenta da zasu hana?”Alhaji ya ce,
“‘Saurara Hajiya Amina, inhar mijinta bai yarda ba gara ta zauna. Ai na zaci ya barta ne” Hajjya ta ce,Ba fa miji aka ce ba, uwar mijin fa Alhaji! Ita kuma a wa?” Shatima ya ce,
“Hajiya uwarshi ta isa ta hana shi, ki ka sani ko lokacin da suka fada mishi da ya je gurin uwarshi sai ta ce kar ya bari? Kuma kin ga bazai iya zuwa ya ce musu
ba za ta ba, da yake ita uwar a tsaye take shi ne ta same su Hajjya tamkar ba ta gane karatun da Shatima ya yi ba, sai ta sake fadin,
“Shi ke auranta ko ita?”Shatima ya ce,
“Hajiya ki kwantar da hankalinki, duk da na gari dole ya bi zancen iyayensa. Kar ki gurgude ma Badi’atu aure” Hajiya ta ce,
“Ka rufe min baki da Allah,ya dade bai mutu ba, auran banza ance min duk ta lalace, wai komai sai abin da iyayensa da matarsa suka ce” Alhaji ya ce,Ki bi sannu, yanzun dai ki
ce su dawo za a san yanda za a yi a samu
maslaha”Hajiyar ta fita da sauri tana fadin,
“Tab! Ai ni dai su taho min da yata”
. Ko da ta je ta dauki wayarta abin da kawai ta ce shi ne,Ku tattaro ta ku taho da ita.
Shatima ya ce,Allah kenan, Hajiya taja
ma Badi’atu matsala”Alhaji ya ce,
“Kamar ya ya?” Shatima ya dafe baki,
domin zatonshi zancen zuciya yake yi. Alhaji ya tashi zaune,Me ya’ sa ka ke ganin Hajiya ce taja ma Badi’atu?”Shatima ya ce,To ni ai dole in fadi haka. Hajiya ta manta ita ce ta hana ni maido Salma,sannan ta ce uwarsa ba ta isa ba”Alhaji ya ce,Tuni na zargi Hajiya a
cikin matsalar nan shi ya sa aka ce ko ba ka da ya’ya kar ka sake ka takura dan wani. Domin kana da na yan uwa. Amma kai duk wannan tsawon lokacin me ya hana ka fada min?” Shatima ya ce,Na san ranka zai baci,
kuma bana son ku samu matsala a kaina
Alhaji ya ce,To ka barta cikin ruwan
sanyi za ta saitu. Ka kara hakuri ka san an ce
mata komai shekarunsu tamkar yara suke”
Shatima ya ji dadì sosai, da zai tafi ya je
gurin Hajiya ya samu ta zabga tagumi, ya ce,
“Hajiya ina son mu karashe magana, zan tafi
Ba tare da ta dube shi ba, ta ce,Je ka
Ya ce,Hajiya kar kisa damuwa a zuciyarki fa”
Ta dubi Shatima cikin sanyin murya ta ce,
‘”Dole in damu, yarinya karama ta fada cikin
kaddarar aure Shatima ya ce, “Allah zai warware Tayi dan tsaki Shi ya sa duk wanda yaQiji bayaqi gani ba. Ina laifin Safwan ta
Fututtuke taqi shi? Shatima yace
“Allah dai ya sa ba shi ne mijin ba. Ki yi bakuri”
Ta ce,Ai su ne da hakuri don na ce su
Momiyo su yo min gaba da yata ba zan dauki
wulakanci ba Shatima ya ce,A bi sannu Hajiya, babu kyau fa mutum ya shiga hurumin aure, kin san komai Hajiya”Ta dube shi,Je ka abinka kawai”.Shatima ya fita, shi ma ranshi ya shiga
damuwa da lamarin Badi’atu, kowa ya san yanda yaya yake son Kanwa.
Shatima ya shiga gidan Inna da nufin
gaida ta kamkar yanda ya saba, suka gaisa ta
tambaye shi mai jiki, ya ce da sauki sosai.
Ta ce,Salma ke sanar da ni jiya da ta
biyo daga makaranta”Ya ce, Ya samu sauqi””.
Inna ta Ce,Yanzun Alhaji ba ka je gurin
Kaka ba ko ma me za ta yi maka?” Ya ce,
“Zan je insha Allahu Inna kwanan
nan, Kakar ce ta fiye rigima tunda ta ga ana
lallaba ta”Ta ce,Zaman nan ya yi yawa, ga shi ana neman kusan wata sama da bakwai. Ka kokarta ta koma ga azumi ya kusanto Ya ce,
“In Allah ya yarda zan yi kokari”
Shatima suna waya da Safwan, batu ne na
harkokin kasuwancinsu. Gidan mai aka bude na Shatima ne, amma an biyo shi bashin miliyan ashirin, ya ce zai ba da domin ya san ya yi wa Alhajinsu karkaf kafin gidan man ya samu. Safwan ya ce,Insha Allah za ka bada kwana kusa, domin kai ma kana da albakar kasuwanci”.Ya ce, “Wai amaryarka ta dawo kuwa?”Shatima ya ce, “Kai dai bari, Kaka fa taki sam-sam” Safwan ya ce,
“To kai in har ka tabbatar ba ka sonta ai gara ka sahale mata, domin akwai daukan alhaki”
Shatima ya ce,Da ma kai ma na fada
maka bana sonta ko? Safwan ya ce,Eh mana, ni fa kwanan baya har sako na bada a bata na wasu yan kudì
domin da ka ce min ba ka sonta, duk tunanina bama za ka ba ta abin kashewa ba”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe