RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 21 BY HALIMA K/MASHI
Ya ce, “Haka ma na gode, shagwabar ma
ina so”Ta bude motar ta fita. Ya bi ta da kallo,
wani sonta yake ji kamar kada ya fita. Sai da ta
shige sannan ya tafi.Shatima ya samu Alhaji ya fada masa yasa Hajiya ta je gidan Kaka don ta ce sai Hajiyar ta je tukunna. Alhajin ya ce, to za su yi
maganar, ya ce shi yanzun a kan Badi’atu ne,
mijin bai zo ba bare ta koma, tunda ta ji sauki
ai gara kuma a san me ake ciki. Shatima ya ce,
“Alhaji kada ka sa a maida ta ka bari su zo da
kansu Alhaji ya ce, Mun yi magana da
Babanku alhaji Musa zai kira waliyyin shi
mijin nata a ji manufarsu ko?” Shatima ya ce, “To a yi haka din, don inso samu ne, gara ya ba ta takardarta Alhaji ya ce,Shi aure rai ne da shi babu
kyau mutum ya yi sanadiyyar kashe shi: In
Allah ya Kare shi shi kenan
Shatima ya ce, “To shi bari ya tafi.
Da ya shiga gurin Hajiya tace me ya sa
bai tafi Abuja ba tunda yau litinin? Ya ce, shi
fa gaskiya so yake matarshi ta dawo. Hajiya taCe,
“‘To ka je, ai ni tuni na bar wannan zancen Shatima ya co,Sai kun sa baki don Kaka taqi sam”. Hajiya tace “Shi kenan, za mu yi
magana da Alhaji”Yana isa Kaduna ya tadda Aliya ta cika dam. Ya ce,Lafiya?”Ta ce,Babu komai”. Sanin cewa Shatima kan shiga damuwa a loakcin da ya ganta a damuwa ya sa ta yin haka. Amma ga mamakinta sai ta ga ya shashantar ya ci gaba
da harkokinsa. Sai data lura ya shiga
bandakinta sai ta dauki wayarta tana yin wayar
Karya zuwan da Madina kawarta,Wai Madina
dazun muna magana da ke katin ya kare, in
fada miki wai Salma ta kira ni tana zagina, har
da boye lamba wai mijin da muke takama da
shi ga shi nan yana binta, kuma ba za ta dawo
ba sai ya….
Ta yi saurin/ sauke wayar don ta ga Shatima, ita a dole wai ba ta son ya jiba
Ya dube ta,Wace Salmar ce ta zage
ki?” Ta sunkuyar da kai,Ban so ka ji
wannan zancen ba”.Ya ce,Ina ki fada min kin ki”
Ta soma zubar da hawaye, “Salma ce ta
kirani tana ta zagina, tare
da fada min maganganu a kanka”Ya ce,
“Yaushe ta kira ki?Ta ce,Dazun gurin karfe uku
Shatima ya tsura ma Aliya idanunshi cikin mamaki, ya ce,Mu ga lambar da ta kira
ki”Ta tashi da sauri ta dauko wayar ta nuna
mishi wani kira da aka yi babu suna. Ya duba
lokaci, karfe uku saura minti biyar ya gani
Tabbas kira ne kuma babu lamba, amma ba zai
yarda cewa Salma ba ce, don ya duba tsawon
maganar da Aliyan ta yi kusan awa daya in ya
yarda Salma ta kira ta uku saura minti biyar
kuma sun dauki kusan awa daya suna waya,
kenan har lokacin da ya dauki Salmar karfe
uku da mintina suna ta waya ne har zuwa
lokacin da ya aje ta hudu saura ya nufi
masallaci, kafin ya je gurin Hajiyarsa? Ya sake
duban Aliya wadda ta tsare shi da ido tana kallon irin nazarin da yake yi, kuma tana son
jin yanda zai dauki abin. Ya ce,
“Ba Salma ce ta kira ki ba, ki dai
tuna sosai” Aliya ta ce,Haba Baban Abulkhairi,
Salma ce ta kira ni, na fa san Salma, yau muke
tare? Kuma ga ma abin da ta fada Ya ce,
“To amma in lokacin da na gani a
wayar haka ne, to tabbas ba Salma ta kira ki ba,
don lokacin muna tare da Salma. Kuma babu
wanda ta kira haka ba a kira ta ba
Aliya ta yi shiru cikin mutuwar jiki,Salma ce dai ni na ji, na rasa gane kanka
yanzun duk ka canza, kana zaton zan iya yi ma
Salma sharri kenan ko me ka ke nufi?”
Ta soma kuka,Na rasa wanda ke son
shiga tsakanin yarda da amanar da ke tsakanina
da kai Shatima cikin takaici ya saki wani
murmushi, sannan ya ce,Ban so in nuna miki
na gane dukkan makirce-makircen da ki ke
hadawa ba, don ba na son kunya ta mutum, na
so mu je a hakan, amma na san matsayin da na
aje ki. To sai na lura cewa shi fa makaho in ba
a zungure shi ba, bai san ana kallonshi ba, don “haka yau zan fayyace miki komai ko da Allah
zai saki daina.Aliya na ji kunya sosai lokacin da na fahimci ke ce ki ke rura wutar tsana tsakanin
Salma da Hajiyata, sannan duk sirrin gidana
yana kunnen Hajiyata cikin salonki na son ki
hada ni da ita. Haka kuma kina rura wuta
tsakanina da matana ta irin sigar da ba zan taba
fahimta ba, sai dai kin manta cewa, Allah ba ya
zalunci, kuma duk daren dadewa zalunci ba ya
dorewa. Aliya kin ba ni kunya, kin zubar da
girma da kimar da kullum nike kallonki da ita.
Amma ina son in fada miki wani abu daya,
tsakanina da matana babu saki, har ke ma da kike wannan abin. Sai dai kowacce cikinku da irin
matsayin da na dora ta, ke kin sauko daga naki
“‘matsayin, kin zubar da kaso tamanin da biyar
daga cikin kimarki da mutuncinki a gurina.
‘ Saura da me? Ki tarairayi na gurin abokan
Zamanki in kin bari ya zube dama shi madara
ne, ba ya dibuwa. Sannan ban karbi wannan
sharrin da ki ka yi wa Salma ba. Abu na karshe
shawara ce, ki dakatar da wannan abubuwan
don ba za su sa ki yi nasara ba. In kuma kin ci
gaba, to za ki barbadar da ragowar Kimar taki”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe