RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 22 BY HALIMA K/MASHI
Aliya cikin kuka ta durkusa,”‘Ka yafe
min don Allah, ka ci gaba da kallon mutuncina,
ka maida ni matsayina na tuba ba zan Kara ba”
Shatima ya ce,Ba zan miki alkawari
ba, amma in kin daina kin taimaki kanki”
Ta sake fashewa da kuka, “Duk tsananin
son da nike maka ne ya kawo haka”.
Shatima ya yi murmushi, “So ba zai sa
ki cutar da ni ba Aliya”. Ya lumshe ido yana
tuno yanda yake kallon son shi tsantsa a
Kwayar idanun Salma. Ya sauke ajiyar zuciya,
“Zan tashi zuwa Abuja komai dare yau. Amna
ba ta dawo ba, ina bukatar ki hada min kaya
kin ji?”Ya sa kai ya fita, ya barta cikin nadama
da bakin ciki. Duk kwanakin Shatima jinshi yake
kamar wani sabon matashin yaro a shekararshi
ta farkon shiga soyayya don sai ya zama
koyaushe cikin tunanin Salma da son hirarta
yake, sai dai ba shi da wanda zai yi hirarta da
shi, ba ya ga Munnir. Amma kuma Munnir din
yana nuna zancen Salma ya ishe shi, don ko
karatun ne ya ci a ce ya haddace tunda kullum
abu daya ne ake nanatawa. Ya zan yi Salma ta
dawo? Munnir Salma ta waye in tana magana
sai in ga kamar wata sarauniya, sai ta zabi
kalmomin da za ta yi min magana da su.
Haka kuma yanzun Shatima ya fi ganin
kusancin Abuja zuwa Zaria fiye da Kaduna,
don haka inda mota ya zo ya kan wuce
Rigacukun ya isa Zaria, ya je gidan Kaka ko da
a ce Salma ba za ta ce mishi kala ba.
Haka ita ma Salmar a bangarenta tana
Bata dara da dama gurin tunanin Shatima,
kuma ta gama yarda cewa tana sonshi sosai
don koyaushe tana sauraron kiranshi kO
zuwanshi ko da ba za su yi magana ba. Bugu
da kari ga tausayinshi na zirya à hanya wanda
har ya sa ta soma ganin zafin Kaka da ta ki
sauka daga kujerar nakin da ta hau. Sai dai
babu damar ta nuna hakan don ita ce ta sama
mata “yancin da ta samu wannan kimar yanzu.
Shawara daya ta bai wa kanta shine, mikewa
da addu’ar Allah ya yayyafa wa abin ruwan
sanyi don ta yi azumi a dakinta.
Kaka ta kalli Hajiya da Alhaji, sannan taci gaba da Kwantale bakin da ke jikin goron data dauka za ta ci hajiya ta sake cewa Kaka don Allah ki yi hakuri, wallahi tuni kunya ce ta hana ni zuwa inda ki ke, na yi laifi mai yawa,amma ni matarsa Aliya ita ce ke zuwa ko ta kira ni tana fada min abubuwa game da yarinyar, amma ni da tuni na watsar da batun iyalanshi Kaka ba ta tanka ba, Hajiya ta dubi Alhaji, “Ka’ce wani abu don Allah Alhaji, Kaka
ta yafe ni Alhaji ya dan saci kallon Kaka, sannan
ya ce,Ni me zan ce? Rakiya kawai ki ka roqi
alfarma in miki don kina jin kunya, ni tuni
Kaka ta gargade ni da cewa na cire bakina cikin
wanna magana Kaka ta yi dan murmushi don jin wata dabara irin ta shi Alhajin, sannan ta ce,
“Yanzun mece ce maganar da ke tafe da ku?”
Hajiya ta ce, “*Hakuri za a yi Salma ta
koma dakinta” Kaka ta ce,To ai ni ba ni ba ce Salma din ba ko? Salma ita ce da magana in ta hakura za ta koma sai ta koma? Hajiya ta ce,
“A kira ta sai in ba ta hakuri mani, don durkusawa
wada ba gajiyawa ba ne. sai ka tashi da tsawonka”.Kaka ta ce, “‘A yau ki ka san hakan?” Ta ci gaba,Gaskiya Hajiya Amina kin
ba ni mamaki sosai, na zaci za ki riki sirikanki
kamar yanda ni na rike ku. Na taba cutarki?”
Hajiya ta ce,A’a wallahi”Ta ce,To me zai sa ki cuci “yar wasu kice sai an sake ta? Shi ya sa aka gasa miki taki yar, ga ta nan har yau ba ta san matsayintaba Hajiya ta ce, ¿’Ai kaka na ga ishara ganin idona. Jiya Safwan ya turo lauyanshi suka kai maganar kotu, shine yau ana kai sammaci suka hado dan aike dà takardar saki. Da Safwan din ya ce zai sa a je a nado shi, ni da Alhaji muka
hana, tunda ya sake tan shi ke nan, ni yanzun
bana son wani tashe-tashen hankula, sai a je a
dibo kayanta kawai”,.Kaka ta ce,
“Allah ya kyauta”.Ta daga murya ta ce,
“Ke! Salamatu!!”Salma wadda ta kashe kunne don ta ji me ake fadi, amma ba ta jiyo ba don tazarar dake tsakanin falon da dakin, ta ta amsa tare da tahowa. Sanye da hijabi ta durkusa cikin kunya tana gaida surukan nata. Hajiya ta ce, “Ki
matso kusa da ni Salma, zo nan’*. Ta kalli Kaka, da kai ta yi mata alama don haka ta matsa. Hajiya ta janyo ta zuwa
jikinta,Salma ki yi hakuri kin ji? Ki min
uzurin wannan ba zan sake ba”Salma cikin kunya ta ce,Hajiya, uwa ba ta laifi a gurin ‘ya’yanta, ban taba kallonki da wani laifi ba Ta ce, “Duk da haka ki yafe, furta in ji”Salma ta ce, “Na yafe Hajiya, ni ma ki yafe min” Alhaji ya ce,’Ke me ki ka yi *yar nan? Ba ki da laifi sam-sam” Kaka ta sake yin doguwar nasiha ga Hajiya game da cusa kai da surukai suke yi cikin lamarin ya’ yansu. Har ma ta yi bayanin irin aurar da irin wannan kutsen yake
kashe wadanda ba za su lissafu ba. Sannan ta
ce su je gida su turo mata Shatima don biyan
diyyar jinin da ya zubar ma Salma. Hajiya da Alhaji suka dara cikin raha,Hajiya ta zage
“yar fos din hannunta ta ciro
kudin ta kama hannun Salma ta damka mata
Kudi sababbi, Salma ta ce,Ki barshi Hajiya”
Ta ce,A a ni na ba ki”.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe