RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY HALIMA K/MASHI
dauki take away din ya fita da shi kar maman
Kausar ta gani. Badi’atu ranar ba ta yi bacci ba tana tunanin lallai ta fado cikin matsala. Ba dai har za ta soma karbar hukuncin kin yarda ba abin da iyayenta suka so ba, domin ita ta soma yin da ta sani tun yanzun,. Wa za ta tunkara da matsalarta?
Salma ta sauka a kofar gidansu ta ciro dari
biyu ta ba dan acaba ya ba ta canji, jan akwatin tayi ta nufì cikin gida. Lokacin karfe tara sauran yan
mintuna, Inna ta shiga bandaki ta ji karar jan
akwatin. Da sauri ta fito don ta ji ko karar menene. daidai lokacin Salma ta saki akwatin a tsakar gidan ta nufì daki da son kuka.
Cikin sauri da faduwar gaba Inna ta aje
buta ta bi Salma daki tana fadin,
“Lafiya! Bikin ne ki ka zo tun yau? Ta saki zancen ganin Salma tana kuka. Ta kunna makunnar wutar dakin haske ya gauraye dakin. Inna ta kalli fuskar Salma a razane ta ce, “Hatsarin mota ku ka yi?”Salma cikin kuka ta ce,Shatima ne ya doke ni” maganar yasa Jikin Inna ya dauki rawa,Duka kuma
wane iri? Me ki ka yi masa haka?”
Salma ta ce,Wai kawai don nace sai ya
sake ni, shine ya yi min duka” Inna ta fusata cikin bacin rai ta ce,Tashi ki koma dakinki ba ni da masaukinki. Tuntuni baki san ba ya sonki ba sai yau?”Salma ta ce,Inna..Ta katse ta,
“Tashi da Allah ki fice min a nan, in ma ba za ki koma dakinki ba, to ki nemi
gidan wata uwar duk irin karamcin da wannan
yaron yake mana ba don son naki yake mana ba? Shekaran jiyan nan ya turo wa Yayanku Auwal kudin sadaki na auran nan nashi.
Hayarmu kwanan nan ya biya da guntu-guntu saboda hidima da ta masa yawa, amma wai ki bude baki ki ce ya sake ki saboda gata da ya miki yawa? Ai dukan da ya miki ya yi kadan tunda ya bari ki ka iya fitowa da Kafarki, da karya ki ya yi sai ya fi burgeni
Haushi ya sa Inna ta kai ma Salma dundu
Itare da fadin,Fice min
Salma ta tashi ta dauki jakar tana sabon
kuka, har ta gota akwatinta Inna ta ce,
“Dawo ki dauki kayanki, wane shegen ne za ki bar maWa?”Salma ta jakar tana rusa kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa. Inna tana biye da ita tana fadin,Je ki duk inda za ki?’
Don ta ji Salma na fadin,
“Ni ba zan koma can gidan ba” . Tana fita Inna ta sa sakata. Salma ta fi minti bakwai tana kuka a kofar
gidansu, har sai da ta ji idanunta suna radadi,
sannan ta fara tunanin zuwa gidan Yaya Hadiza.Ta tare mashin ya dauki kayan ta hau. Har ya yi
kwanar gidan yaya Hadiza sai kuma ta kalli layin su Hajiya Kaka, ta ce da mai mashin ya juya ya shiga layinsu Hajiya Kaka.
Har sun kulle gidan ta yi ta bugawa,
Salihu matashin da ke gidan dan dan uwan
Hajiya kaka ne, tuni yake gidan zaune yana
karatu. Shine ya fito ya bude kofar. Ganin
Salma ya cika da mamaki, yana fadin,
“Anty lafiya na ganki haka?” Ta ce,’
“Salihu dauki mu je ciki. Kaka ta yi
bacci ne?”Ya ce,Ba ta yi ba, don yanzun na kai
mata manzafi da ta sa na siyo mata
Ya dauki akwatin yana fadin, “Anty kunyi hadari ne?”Salma ta ce,Humm”
Maryama tana shafa ma kaka man zafi
suka ji sallamar Salihu, tare suka amsa, ya shigo da akwatin hannunsa. Kafin su ce ta wane ne, Salma ta shigo. Duk da kallo suka bi ta, ta zauna a bakin gado. Hajiya Kaka ta ce,
“Kamar Salamatu nike gani fuska kumbure, ko dai idona ne Maryama ta ce, Ita ce, ko hatsari ku kayi?»Salma ta soma kuka tare da fadin,
“Ba hatsari. ba ne, Shatima ne yayi min haka”.
“Shatima?” Kaka ta nanata cikin mamaki.
Salma ta ce,Dukana ya yi, kuma na je
gida Innarmu ta koro ni”.Hajiya Kaka tace,
“Maryama tashi ki debo mata ruwan dumi ta shiga bandaki ta dan gasa fuskar tata. Salihu kai kuma zo ga dari biyu canjin da ka kawo
min yanzun ka siyo mata
maganin ciwon jiki”Ya ce,TO”
. Ya fita yana tambayar kansa
dalilin da Shatima ya yi wanna danyen aikin.
Bayan ta dan dumama fuska, Maryama ta
hado mata shayi ta sha, sannan ta sha magani.Kaka ta ce,
“Kwanta, za mu yi magana da
safe”Shatima ranshi ya baci karshe, ya shiga
dakin Aliya ta ganshi tamkar an jeho shi. Ta
dube shi,Yanzun ka shigo?”
Ya ce,Je ki kwaso min jakata a kofar yarinyar can Salma yake nufi ta sani, kuma tunda ta
ganshi rai bace, to lallai wani abu ya afku. Ta
kwaso kayan idanunta na kan falon Salma wanda yake a hargitse. Ta dawo dakin ta ci gaba da
ririta shi, aka kai ruwan wanka, aka hada abinci, har ta samu ya sauko amma har yanzu bai ce mata komai game da Salma ba. Ga shi tana son jin abin da ya faru. Ya dauki Abulkhairi ya fita ya nufi grin Amna, ya je ya duba su sannan ya dawo.Ta ce,Na ga falon Salma a hargitse,lafiya dai ko?”Ya ce, “Kila tana kwalema ne”. Sha dayan dare da mintuna Shatima harya yi shirin kwanciya duk iyaka kokarinshi na son share Salma ya kasa, domin ya ga jinin bakinta a hanninshi. Ya aje turaren da yake fesawa na bacci, ya nufi fita.
Aliya dake kwance a kan gado ta dago ta dube shi. Fita za ka yi baban Abulkhair?Ya ce,
“Yanzun zan dawo”
Tana jin fitarshi ta taho sadaf! Sadaf!! Ta
leka ta windo, sashen Salma ya nufa. Kamar ta
fita ta bi shi, amma tana tsoron kada ta fita shi
kuma ya juyo. Dole ta daure ta ci gaba da
tsayuwa a gurin. Yana shiga ba ta falon, ya shiga
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe