RANA DAYA CHAPTER B
Rawa bakinta yake tana kakkarwa tace, “Ummi wallahi ban yi mishi komai ba wallahi bani bace.”+
“Da Allah rufa mana baki!” Mummy ta katse ta. “A jinki bama sane ne da kalan rashin hankalin da kikeyi masa a gidan? Tun yaushe yaron nan yake hak’uri dake? Gashi nan k’arshenta kin sanya masa ciwon zuciya amma karki damu komi yazo k’arshe Allah tada kafad’an shi ya rubata miki takardan sakinki ki huta shima ya huta kowa ma ya huta.”
“Mummy dan Allah kar kiyi mun haka wallahi inason Afzal kuma wallahi ni ba ni bace sanadin wannan rashin lafiyan nasa Ummi you’ve got to believe me” ta juyo tana kallon Ummi a raunane “Ku tambayi D’anladi me gadi wallahi ahaka muka tsince sa a d’akinsa dan Allah ku yarda dani” sede ba wanda yako kalleta a cikinsu ita kanta Ummi kuka takeyi. Mummy ko ta had’a tagumi tana tunanin yadda zata fara sanar da Daddy wannan labari me d’aci.
“Dr dan Allah kuyi duk abinda ya kamata ku tabbata d’ana ya rayu shi kad’ai gareni bazan iya rasa saba dan Allah kuyi mun rai.”
“Karki damu Hajiya we’ll keep him under an intensive care da ikon Allah ze samu sauk’i sede ku sanya sa a addu’a abu da zuciya ba guarantee, Allah de ya bashi lafiya.”
“Ameen amma Dr dakata dan Allah, shin baku gano ko mey ya jawo masa wannan ciwo ba?”
“Tukuna muna kan jiran sauran sakamakon su fito amma ina da tabbacin cewa tunani ne yayi masa yawa dake BP nasa ma ya hau, tabbas akwai abinda yake damunsa na tsawon lokaci wanda ya rik’e a ransa yake kuma bi da zuciya.”
“Ai na fad’a” Mummy tasa baki “Bin duk kalan halayya da rashin hankalin da fand’ararriyar ‘yarnan keyi masa ya jawo mai wannan ciwon zuciyan. Kinyi asara wallahi Nazeefah kinyi asara.” Banda kuka ba abinda Nazeefah ke iya yi, k’iri-k’iri tasan ba ita bace da laifi amma ake blaming nata ya zatayi idan wannan labari ya iske Daddy? Wayyo nata ya k’are.
“Nagode Dr zan iya shiga ganinsa?”
“Sosai ma kuwa excuse me.” Yana ficewa Ummi ta shige d’akin Afzal a karo na farko da idanunta suka sauk’a akansa ba se hawaye ba, kuka ta shiga yi na sosai da k’yar k’afafunta suka iya takata izuwa gefen gadon nasa. Hannu ta aza akan oxygen supply da aka sanya masa sannan ta koma gashin kansa tana shafawa a hankali yayinda take zubda hawaye sosai.
“Afzal Ummi ce” ta furta yayinda kuka yaci k’arfinta. “Afzal Baba na Allah tada kafad’anka in shaa Allahu zaka samu sauk’i sede na rasa dalilin da zaisa kana da uwa a raye amman ka gwammaci ka rik’e damuwanka wa kanka kai kad’ai. Meyasa Prince? Idan Nazeefar ce bakaso a yau ka sanar da Abbanka wallahi mey hana raba auren nan se Allah why do you have to do this to yourself?” Rungumosa tayi tana kuka na hak’ik’a se chan ta iya ta fito daga d’akin ta nufi inda Mummy ke zaune itama ta zauna. Nazeefah dake tsaye daga gefe ne ta k’araso ta durk’usa gabanta.
“Ummi dan Allah kiyi hak’uri kibar kukan nan haka.”
“Mey kika ma Afzal Nazeefah? Na d’au da kikazo kika sanar dani halin da kuke ciki zaki canza al’amuranki ne ku soma zaman lafiya a gidan meya faru?”
“Ummi wallahi bani bace, duk abinda nasan ze 6ata wa Afzal rai ina k’ok’arin dainawa, wallahi ba nice sanadin rashin lafiyarsan nan ba. A sume haka muka samesa a d’akinsa da D’anladi daman tun jiya daya dawo gida ya rufe kansa a d’aki ban kuma jin motsinsa ba you have to believe me.”
“Hmmm I wish I could Nazeefah” amsan da Ummi kad’ai ta bata kenan sannan ta kau da kanta. Gun Mummy takeso ta nufa amman bata shirya shan wata marin ba dan haka ta tattara kanta taja gefe. Satan idonsu tayi sid’ak-sid’ak ta shige d’akin Afzal d’in. A hankali ta k’arisa gefen gadonsa ta tsuguna yayinda take zubda hawaye sosai. Hannunta dake kakkarwa ta d’aga ta sauk’e akan fuskarsa tana shafawa a hankali yayinda wani irin so da tausayinsa yake sake shiga zuciyarta.
STORY CONTINUES BELOW

“Afzal?” Ta kirasa a raunene tana shafa gashin kansa.
“Afzal wai nice sanadin rashin lafiyarka? Wai nice na janyo maka wannan ciwon? Dan Allah ka farfad’o ka fad’a musu ba ni bace. Afzal suna shirin rabani da kai, Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba dan Allah ka tashi ka musu bayanin komai Afzal I love you, I love you so much and I’m not willing to let you go, I’m here, I’ll always be by your side dan Allah kar ka bani kunya ka tashi.” Kanta ta sauk’e akan k’irjinsa a hankali tana me cigaba da kukan tsuma zuciya. Ta dad’e a hakan badan tana so ba ta tashi ta fice se don kar azo a kamata.
Abba dake Morocco Ummi ta kira ta sanar dashi halin da ake ciki. A karo na farko kan ma yak’i amincewa don yadda kansa ya d’aure. Ciwon zuciya de? A dalilin mey? A iya zamansa da Afzal be ta6a sanin Afzal nada zurfin ciki ba toh meya faru? Kode zancen Ummi gaskiya ne, Nazeefah ce ke k’untata masa shiko yake bi a rai har abun ya kai ga haka? Aiko ya zama dole a d’au mataki dan akan zumunci baze rasa ran d’ansa guda ba. Ba shiri ya shiga booking flight of return.
Wajajen k’arfe takwas na dare likita ya dawo ya duba Afzal sede har yanzu ba cigaban da aka samu hak’uri ya basu kan su bari zuwa gobe. Ummi kam ba aikinta se kuka, har da Daddy yazo dubata ya tafi bata bar kukan ba. Ran Daddy ya matuk’ar 6aci, ya sani duk hakan na faruwa ne saboda laifin daya ta6a aikatawa, alhak’inta ne ke binsa shiyasa Allah ya basa ‘ya gagararriya kamar Nazeefah. Oh Allah! Ko kallon Nazeefah da ke ta faman rantsuwa beyi ba ya fice. Sauk’a har k’asa tayi gun tana kuka me tsuma zuciya.
Wajajen k’arfe goma Mummy tace zata tafi, Ummi na jiran tafiyan Nazeefah amma shiru koda ta tambayeta se yaushe zata tafi kuwa tace mata ita anan zata kwana sede Ummi ta hanata bata son ko cikin dare idan Afzal d’in ya tashi ganin Nazeefah akansa kuma hakan ya sake haifar masa da wata rashin lafiyar dan su duk sun gama yarda cewa Nazeefah ce sanadin komai. Haka badon tana so ba aka sa driver ya dawo da ita gida, ko abinci ta kasa ci sallah kawai tayi ta kishingid’a jikin sallaya tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari Mummy ta shirya breakfast ta kai wa Ummi haka Nazeefah ma, sede har izuwa wannan lokaci Afzal be farfad’o ba basu Ummi kad’ai ba harta shi kansa likitan ma jikinsa yayi sanyi har ya soma tunanin ko Afzal d’in ya shiga state of comma ne. Sultan da se a yau labari ke iskesa ne ya shirya ya taho. Ko daga jin batun yasan ba komai bane ze jawo wa abokin nasa ciwon zuciya banda tunanin Amal. Sosai ya tausayawa Afzal da yaga irin critical condition da yake ciki yayinda yake jin haushinsa kuma, ai dama seda ya fad’a masa ba inda zurfin ciki ze kaisa banda halak’a amman yak’i ji. Yana zaune a d’akin ne shida Ummi da Mummy Nazeefah tayi sallama zata shiga don ajiye masu basket na abincin ranan data dafa.
“Ban ce miki kar na sake ganin kin tako k’afar ki cikin d’akin nan ba? Duk abinda kikayi masa be isheki ba nan d’in ma sekin biyosa kin k’arasa sa?” Mummy ta kurarata. Magana ma ta kasa kawai maida k’ofan tayi ta fice ta nemi gu ta zauna ta shiga kuka, shin yaushe ne zasu amince akan cewa ba ita bace sanadin wannan rashin lafiya?
Sultan da kansa ya d’aure ne ya juyo yana kallon Mummy da tayi maganan “Aunty me kuma had’in Nazeefah da condition na Afzal? Bade ita kuke zargi ba?”
“Da wa kakeso a zarga idan ba ita ba Sultan? Abokin naka be ta6a baka labarin kalan zaman da sukayi da ita a gidan bane?” Ta tambayesa.
“Sure yana bani kawai de I don’t think itace ta janyo masa wannan ciwo besides ai zatto ma zunubi ne kamata yayi ku jira ya farfad’o ya sanar daku da bakinsa kafin ku hau tsagwamanta haka.”
“Ko wa kakeso mu zarga? Idan ba Nazeefah ba to waye ne? Dan Allah ka sanar dani idan ma mutanen office ne I am ready to deal with them tell me Sultan” cewar Ummi.
STORY CONTINUES BELOW

“Ba mutanen office bane.”
“Then waye ne?”
“Nima bansani ba amma kam ba Nazeefah bace.”
“Allah farfad’o da Afzal d’in koma wanene ze sanar dani” cewar Ummi had’e da cigaba da shafa gashin kansa. Sallama yayi musu akan yana zuwa ze dawo anjima. Yana fita ya kira numban Amal wanda ta d’auka bada dad’ewa ba.
“Assalamu alaikum.”
“Wa’alaikumus salam” ya amsa.
“Ya sultan ina yini?”
“Lafiya ya kike? Kina gida?”
“Eh lafiya?”
“Ki jirani ina zuwa” batayi musu ba tace “Allah kawo ka” ta sauk’e wayan. Anya kuwa lafiya? Yau Ya Sultan ne bashida fara’a haka ko kad’an?? Numban Afzal data gaji da kira ne ta sake gwadawa sede kaman yadda take tsammani haka ya gama ringing be d’aga ba toh meke faruwa ne? In minutes like 30 sega Sultan ya iso k’ofan gidansu. Fitowa yayi ya mata waya kan gashi bata 6ata lokaci ba ta sanya hijabinta ta fito.
“Ya Sultan yau kaine a gidan namu?”
“Eh Amal dalili ya kawo ni” ya sanar da ita straight forward.
“Toh ina jinka.”
“Kin ko san Afzal ba shida lafiya yanzu haka as we speak? Yana kwance a gadon asibiti rai na a hannun Allah.”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” tasa salati yayinda ta nemi duk wani nutsuwarta ta rasa. “Ka ce mey????” Ta tambaya bayan tsawon lokacin data d’auka.
“Afzal na gadon asibiti haka as we speak fighting for his life” ya sake nanata mata. Take idanunta suka ciko da hawaye ashe dalilin daya sa ko ta kira baya d’agawa kenan toh meya samesa? Meya samu yayanta? Innalillahi!
“Ya Sultan dan Allah ka fad’a min wasa kake hatsari yayi ne? Meya samesa?”
“Wasa kuma Amal? Ana wasa da rashin lafiya ne? Ko baki gwada layinsa bane tun jiya?”
“Wallahi kona gwada baya d’agawa se nayi tunanin ko yayi fushi dani ne.”
“Mey ya had’aku? Fad’a kukayi ne?”
“Ya Sultan ni ba wannan ba meya samu Yaya? Hatsari yayi ne?”
“Ko d’aya yasamu heart attack ne.”
“Ciwon zuciya??” Ta nanata had’e da zaro idanunta waje. “Me ya had’a Yaya da ciwon zuciya Ya Sultan dan Allah kace wasa kake.”
“Ba wannan a tsakanin mu Amal and bazan 6oye miki ba kece nan sanadin wannan rashin lafiya nasa.”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ni kuma Ya Sultan? Dan mey zaka ce nice sanadin rashin lafiyan Yaya bayan kasan nafi kowa damuwa da lafiyarsa da kuma farin cikinsa, dan Allah ka rufa mun asiri” kuka ta shiga yi sosai.
“Na k’aryata hakan Amal so kike kice har yanzu baki fahimce komai ba?”
“Komai game da me fa?”
“Taya zakice har yanzun baki gane cewa Afzal na son ki ba? Tayaya Amal?” Wani irin sara kanta yayi mata yayinda jiri ya d’ibeta daba don Sultan da yayi saurin tareta ba da tuni ta sha k’asa, k’aryata zancensa ta shiga yi tana kad’a kai yayinda take kuka na hak’ik’a.
STORY CONTINUES BELOW

“Ya Sultan baka gane bane, baka gane ba Yaya ba sona yake ba. Yaya baze ta6a sona da wata manufan ba, dan Allah kabar fad’in haka.”
“Dalili? Kibani k’wak’k’warar dalilin da ze hana Afzal sonki Amal, kin d’au duk hidimar nan da yake miki a banza ce? Ko mey yakeyi muddin ke kika kira bari yake and be at your service you think it shall go in vein just like that?”
“No amma kuma idan har dagaske ne Yaya yana sona da ya sanar dani idan beyi hakan ba kuwa ko Papi ne ze samu ya fad’a mishi baku gane bane Yaya ba sona yake ba.”
“Sosai yana da niyyan yin hakan sede baya son ya raba miki hankali ne daga karatu Amal, so yake se idan lokacin yayi ya sanar dake kwatsam se gashi kin samu wani har kun daidaita taya kike tsammanin zeji? Taya ciwon zuciya baze kama shi ba?”
Salati kawai Amal ke ta nanatawa bayan nan ta kasa furta koda uffan. Meyasa bata gane cewa sonta Yaya yake ba?
“Nide na fad’a miki kuma ina sa ran zaki d’au mataki ki ceto mana ran Afzal ke kad’ai keda ikon hakan.”
Taya ya Ya Sultan? Ta tambayesa cikin kuka sosai “Ya za’ayi nayi hakan? So kake in je in samesa a matsayina na mace in ce masa ina sonsa bayan banji daga bakinsa shi yana sona ba?”
“I’ve said my own amman duk abinda ya samu abokina bazan yafe miki ba.”
“Ya Sultan ya kake magana haka? So kake in haukace in rasa raina? Kafi kowa sanin yadda farin cikin Yaya yake da matuk’ar muhimmancin a rayuwata. I’m willing to sacrifice everything for Yaya amma Ya Abdul fah? Meyasa Yaya be sanar dani tun wuri ba har ya bari soyayyan wani ya shiga zuciyana?”
“Ban sani ba nima Amal, Afzal nada wani irin hali ko abu na damunsa bai son nunawa ko ni nan da nake miki wannan magana bawai shi Afzal d’in ya sameni ya fad’a min hakan bane, ni na karance sa har na gano hakan. Afzal na sonki Amal, idan har da zakiyi adalci kuma kema kin sani ba wanda ya kamanci soyayyar ki kaman shi. Rai ne kawai Afzal be d’auka ya baki ba, is about time kiyi repaying all the kind gestures da ya miki, nasan da ciwo amma ya zama dole ki rabu da Abdul naki kibawa Afzal soyayyar ki it is the only thing that can save his life.” Shiru tayi tana share hawayenta, “Shin bazan iya zuwa in duba sa ba? I want to see him, I want to see him so badly.”
“Hakan zeyi wuya amma zanyi iya k’ok’ari na inga kin samu ganinsa.”
“Are you free yanzu? Zaka iya kaini?”
“Sure let’s go.” Asibitin suka koma inda ya barota acikin mota ya fito ya samu Ummi yake ce mata taje gida ta huta ze cigaba da kula da Afzal zuwa lokacinda zata dawo bata masa musu ba ta kira driver ya kaita gida. Dama ba Nazeefah ba Mummy don haka ya shigo da Amal ya tsaya daga bakin k’ofa yana guarding nasu. Rawa jikinta yake sosai yayinda ta k’arasa cikin d’akin nasa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa. Wani irin mumunar tausayinsa ne ya kamata, ina ma ace zata iya kar6e rashin lafiyan nasa ita tasha wahala a maimakonsa. Sam wannan rashin lafiya be kamace sa ba, “Yaya?” Ta kira sunansa a hankali.
“Yaya dagaske ne? Dan Allah ka tashi kace musu k’arya ne. Yaya in har abinda suke fad’a gaskiya ne meyasa baka sanar dani ba? Yaya kafi sanin kowa yadda nake sonka, I’ll sacrifice everything for your happiness mesa baka sanar dani da jimawa cewa wannan ne k’udurinka akaina ba har kabari na shigo da Ya Abdul cikin rayuwata? Kana tunanin da kaina zan gano hakan ne? Tabbas yaci ace na gane hakan amma banyi ba, I’m so sorry for every pain Yaya please forgive your Lily” tasa k’asan hijabinta tana share hawayenta. Tafi minti biyar zaune a gun tana aikin kuka akansa kawai taga alaman yayi blinking idonsa.
STORY CONTINUES BELOW

“Ya Sultan!” Ta k’wala masa kira ba shiri ya shigo ciki yana tambayarta ko lafiya. “Yaya ne yayi motsi get his doctor” a guje ya fice dan nemo likitan. “Yaya please open your eyes it’s me your Lily, I’m right here kaji? You can do this” kalamun kwantar da hankali tayita furta masa a hanakli ya shiga bud’e idon nasa har ya bud’esu duka had’e da sauk’esu akanta.
“Yaya you’re alive! You’re alive” tasa ihu tana share hawayen farin cikin dake sauk’o mata. Kallonta kawai yake amman ya kasa cewa komi ahaka ne har Sultan ya dawo da Dr’n Afzal inda ya masa wasu gwajin ya tabbatar da cewa condition nasa is stable sannan ya fice.
“Yaya baka gane ni bane? It’s me your Lily.” Maida kallonsa akan Sultan yayi idonsa suna d’auke da d’imbun tambayoyi gano hakan Sultan yayi saurin cewa “bari in kira Ummi ina zuwa” nan ya fice ya barsu su biyu a d’akin.
“Yaya?” Ta kirasa sede ina yak’i koda juyawa ya kalleta. “Yaya I’m sorry, I’m so sorry dan Allah ka juyo ka kalleni” nan ma shiru. “Yaya I’m so sorry dan Allah ka dena fushi dani kayi hak’uri” sede fa duk had’asa da Allahn da tayita yi yak’i koda kallonta. Haka ba yadda ta iya ta mik’e tabar masa d’akin.
“Ya haka?” Sultan daya ga yadda take kuka yayi saurin tambaya.
“Yaya yak’i ya kalleni balle ma yamin magana, Ya Sultan ban san ya zanyi ba dan Allah ka basa hak’uri.”
“Yak’i ya miki magana kaman ya?”
“I told you Yaya ba sona yake ba kune baku gane ba, I can’t do this anymore ni zan tafi kawai.”
“Ah’ah ki tsaya tukuna” d’akin Afzal ya shiga ya zauna gefensa.
“Ya jikin naka?” Ya tambayesa.
“Meyasa ka kawo ta nan? Ina su Ummi?” Abinda ya soma cewa kenan.
“Abinda kad’ai zaka iya cewa kenan?Ka lek’a lahira ma bazaka zubar da wannan halin naka bako?”
“Ba abinda na tambaya ba kenan ina Ummi? So kake su ganta? Mesa kake abu baka tunani ne kam Sultan? So kake se sun ganta sunyi zargin wani abun?”
“Ai ko basuyi zargeta bama ni zan sanar dasu komai.”
“Komai kaman ya?”
“A tunaninka baki na zeyi shiru ne? Na riga na sanar da Amal gaskiyan al’amarin cewa kana sonta sauran idan su Ummi sun iso suma in fad’a musu haka kawai ina ji ina gani bazaka cigaba da punishing Nazeefah ba bayan ita batayi komai ba.”
“Kayi meh kace?” Afzal ya tambayesa cike da tashin hankali yayinda zuciyansa ya tsinke da sauri ya rik’e wajen daya fara yi masa zafi. “Gara ka kwantar da hankalinka kabi komi a hankali dan idan wani attack d’in ya sake kamaka se lahira yanzu.”
“Amma me na fad’a maka? Ni na fad’a maka ba son Amal nake ba don mey zaka sameta kace mata ina sonta? What is the meaning of this Sultan?”
“Aww har yanzu bazaka yi admitting son da kake yi wa yarinyar nan ba?”
“Sultan just get out idan har kasan suratan banza zaka cigaba dayi ka tashi ka bar min d’aki.”
“Yanzu kai fisabilillahi baka tausayawa kanka da ita Nazeefah harda Amal d’inma? Wallahi girman kan nan ba inda ze kaika illa halaka Nazeefah bata san hawa ba bata san sauk’a ba aka d’aura mata laifin komai, Amal na da wanda takeso amman ya zama mata dole yanzu ta rabu dashi saboda kai duk hakan be isheka ba bazaka hak’ura ka amince da komai ba?”
STORY CONTINUES BELOW

“Ni ban rok’eta tabar wanda take so ba Nazeefah kuwa ni bani na fad’awa su Ummi suyi blaming nata ba saboda haka nima kadena blaming d’ina.”
“Da kyau” yace dashi had’e da mik’ewa yabar masa d’akin kafin ya fita har Amal ta tafi nemanta ya shiga yi chan sega Nazeefah shigowa.
“Ina yini?” ta gaishesa.
“Lafiya Nazeefah ya hidima?”
“Alhamdulillah wai Afzal ya farfad’o?”
“Eh yana ciki kije ki samesa.”
“Toh ya naga kaman kana neman abu? Lafiya?”
“Ko kinga wata yarinya da farin hijabi a hanya?”
“Wata doguwa hakan nan?”
“Eh ita.”
“Ina shigowa naga tana tsaran napep.”
“Toh shikenan thank you.” Da haka ta wuce d’akin Afzal knocking tayi sannan ta shige. Basket na abincin ta ajiye akan table sannan ta k’arasa ta zauna a gefensa.
“Afzal ya jikin naka?”
“Da sauk’i” ya amsa k’asa-k’asa.
“Thank you for staying alive, Allah k’ara maka lafiya.”
“Ameen thank you” ya amsa.
“In sa maka abinci?”
“I’m not hungry.”
“Afzal kaman ya baka jin yunwa? Rabonka da abinci tun yaushe? Dan Allah kayi hak’uri in sa maka koda kad’an ne kaji?”
“Nace bana jin yunwa” bata sauraresa ba ta d’iba ta d’au ruwa tazo ta zauna gefensa. “Tashi ka zauna kaji? Please don’t say no.”
“Afzal magana fa nake maka dan Allah kayi hak’uri ka tashi” kaman wanda baze motsa ba ya shiga mik’ewa sede hakan ma ya gagara k’arshe seda ta taimaka masa. Abincin ta d’aga ta mik’a masa “Zaka iya ci ko in baka?” Beko kalleta ba ya amshe plate d’in bayan da ya k’are wa abincin kallo ya maido da kallonsa a gareta.
“Afzal lafiya?” Ta tambayesa saidai still kallonta yake. “Afzal tunanin ko wani abun na sa maka aciki kake? Dan mey zan cutar da kai? Wallahi ba komai aciki ina iya d’ibawa inci a gaban ka idan baka yarda dani ba” ganin ta mik’e yayi saurin cewa “Don’t bother ki zauna” komowa tayi ta zauna yayin da ya shiga ci a hankali.
Murna kenan zan so kuga farin cikin daya bayyana a fuskan Nazeefah rabonta da tayi farin ciki irin na yau a rayuwarta har ta manta. Finally Afzal ya d’and’ana girkinta yau. Zama tayi tana kallonsa yayinda yake ci a hankali dududu beci ya kai rabi ba yace ya k’oshi. Ita a hakan ma ta gode.
“In had’a maka ruwa kayi alwala ko?” Nan ma kai zalla ya gyad’a mata bata kai da mik’ewa ba sega Ummi ta shigo. Da gudu tayi kansa had’e da rungumosa yayinda hawaye ya ciko mata a ido.
“Prince you’re back! Alhamdulillah! Alhamdulillah!” A hankali ta sakesa ta shiga shafa fuskansa “Prince na d’au zaka tafi ka barni.”
“Come on Ummi, I’m here.”
“I missed you.”
STORY CONTINUES BELOW

“I missed you too bari inyi sallah.”
“Haka fa kafin nan kaci abinci? Barin aika driver yaje ya siya maka don miyan kuka akayi a gida.”
“Karki damu Nazeefah ta taho da abinci.” Ita bata ma lura da presence na Nazeefah ba seda ya ambaci sunanta.
“Nazeefah?” Ta juyo da mamaki tana kallonta.
“Na’am Ummi?”
“Prince?” Ta juya tana kallonsa shima.
“Yes?” Ya amsa.
“Kana lafiya? Ko a kira ma likitan ka?”
“Why wani abu ne?”
“Prince mun d’au ai idan kaga Nazeefah ciwon naka ze tashi ke Nazeefah ba ance ki kiyayi shigowa d’akin nasa ba kar wani abu ya samesa” Shiru Nazeefah tayi dan ko bata san me zata ce ba, tsana k’iri-k’iri both mahaifiyarta da surikarta suke nuna mata. Idanunta ta d’ago a raunane tana kallon Afzal tana jiran jin ko zeyi magana dan shi kad’ai yake da ikon wanketa daga wannan daud’a da su Ummi suke ganinta da.
“Meyasa?” Ya tambayi Ummi a k’arshe.
“Prince meye silar ciwon nan naka? Ba Nazeefah bace?”
“Waya ce muku itace?”
“Prince mey kake fad’i wai kam?” Ta tsaya kallonsa da mamaki.
“Nazeefah batayi komai ba I’ll ask you to keep her away from this.” Tirk’ashi wai meke faruwa ne? Ummi ta tambayi kanta “Kaje kayi alwalan zamuyi magana idan Abbanka ya iso munyi waya dashi d’azu jirginsu ya tashi.” A nitse ya mik’e ya k’arisa bayin ya d’auro alwala kamin ya fito har Nazeefah ta shinfid’a masa sallaya. Sallolin daya rasa ya shiga ramawa. Ana cikin haka Mummy ta shigo itama suka gaisa bayan da ya idar d’in take sanar dashi abinda ke tafe da ita na cewa Daddy ya turota ne akan idan har ya ga baze iya ba da rashin hankalin Nazeefah ya sawwak’e mata kawai su koma gida yanzu tunda de tace ita bazatayi hankali ba. Kafin Afzal yayi magana Ummi ta rigasa.
“A’a shiko Alhaji ai ba haka akeyi ba, zama yakamata shi da Abban Afzal suyi da shi Afzal d’in kansa a dai-daita koma menene koba haka ba?”
“Dan Allah kibar maganan nan Hajiya Mariam banason ganin ranan da za’ace ga ‘yata nan ta kashe d’an wani kuma idan aka cigaba da tafiya haka tabbas wataran Nazeefah zata aikata hakan tunda gashi ta d’au hanya har ta sanya masa ciwon zuciya.” Shiru Afzal da suke tsammanin zeyi magana yayi. “Afzal?” Ta kira sunansa yayinda da ya d’ago kai yana kallonta “Mey kace kai?”
“Mummy ni Nazeefah bata yimun komai ba don haka bazan saketa ba kuma ina rok’anku da kudena blaming nata akan laifin da ba ita ta aikata ba” Wani irin sanyi Nazeefah ta jiyo a ranta bata tsamman Afzal ze kareta haka ba.
“Wani irin magana kake ne wai Prince? Idan ba Nazeefah ba toh waye?”
“Ni ba wanda ya d’aura mun ciwo banda Allah, kuma na rungumi k’addara.”
“Ya kake neman raina mana hankali ne kam Prince? Dama ansan ai lafiya da rashinsa daga Allah ne ko ka ta6a jin jinin mutum ya hau ciwon zuciya ya kamasa ba tare da tashin hankali ba? Wallahi to kar kayi magana Abbanka na nan tafe idan yazo se muga ko wannan silly answers d’in zaka basa Hajiya Fatsuma tashi in raka ki Afzal is not willing to talk.”
STORY CONTINUES BELOW

****
Amal ce kwance akan katifarta se aikin kuka take, gabad’aya ta rasa meke mata dad’i tun dawowanta gida bata sake lek’a waje ba. Ba yadda Mami batayi da ita ba amman tak’i fad’a mata ainihin meke faruwa. Toh ma ta ina zata fara? Ta ina zata fara sanar da Ya Abdul wannan zance? Wayanta ta jawo ta shiga viewing pictures nasa da kuma nasu da suka d’auka tare, tana son shi tana son shi na sosai bata jin zata iya rabuwa dashi aman kuma ta d’ayan 6angaren bata son Sultan da shi kansa Afzal d’in da kuma duk wanda wannan labari ya iskesa suyi mata kallon butulu. Sedai har yanzu takasa amincewa da maganganun da Sultan ya sanar da ita, gashi abin haushi sun kasa dena yawo akanta.
***
Ba yadda Ummi batayi da Afzal ba akan cewa ya taho gida da ita amman yayi insisting yace shi fa Nazeefah ze bi. Haka nan suka komo gida tare ta tambayesa ko me yakeson ci. A karo na farko kam babu ya sanar da ita. Seda tayita had’a sa da Allah sannan yace indomie ma yayi. Ba tare da 6ata lokaci ba ta wuce kitchen ta shiga girka masa. Nan ya d’auko wayansa dake cikin wardrobe, gabad’aya gani yayi battery d’in yayi draining. Had’awa yayi bayan ya kawo wuta ya soma cin karo da sak’on Amal da sauri ya bud’e ya karanta kaman haka.
‘Get well soon Yaya, my prayers are with you.’
Duba lokacin da sak’on ya shigo yayi yaga wajajen k’arfe shida ta turo. Maida wayan yayi yayinda ya fad’a duniyan tunani. Yanzu da wannan shirmen da Sultan ya tafka masa da wani idon ze sake kallon Amal?
Washegari Abba ya turo driver akan ya taho da Afzal idan kuma jikin nasa baze iya barinsa ba shi da kansa yana iya tahowa su tattauna komai. Wanka yayi ya karya sannan suka fice. Suna is ya zarce parlourn Abba inda yaci karo da Sultan, take gabansa ya fad’i don mey za’a kira Sultan? Yana da tabbacin cewa aikin Ummi ne wannan. A nitse ya k’arisa d’akin ya zauna se kallon Sultan yake ko idonsu ze had’u yayi masa ido komin mey kar ya fad’i komai amman yadda kukasan gunki tun zaman Sultan ko kewaye-kewaye yak’i yi. Gaisawa sukayi da Abban yake tambayansa ya jiki sannan da Ummi bayan nan Abba yayi gyaran murya.
“Ina jinka Prince meya faru?”
“Abba babu” ya amsa kansa a duke.
“Idan kun kasa jituwa da ita Nazeefan ne ai seka taho gida kamun bayani amfanin idan iyayenka suna raye kenan bawai ka tsaya kana bin abu a zuciya ba.”
“Abba ni Nazeefah bata yimun komai ba.”
“Sorry ban fahimce ka ba.”
“Nazeefah has nothing to do with this Abba” ya sake nanatawa Ummi dake gefensa ji tayi wane ta hankad’esa don haushi ita ta rasa dalilin da yasa yake rufa mata asiri.
“Toh wanene?”
“Babu.”
“Nace wanene?” Abba ya sake tambayansa cikin tattausar murya.
“Abba matsala muka samu a office wanda nayita bi da zuciya shikenan.”
“Prince d’ago kai ka kalleni” ba gardama yayi hakan “Yanzu ni zaka kalli cikin idanu na kayi mun k’arya wallahi sam wannan ba d’abi’ar ka bace I’m very disappointed in you.”
“Abba kayi hak’uri.”
“Sultan?”
“Na’am Abba” ya amsa.
“Tabbas nasan kana sane da duk wani abinda ke faruwa tunda Afzal ba shida amini sama da kai I’ll ask you to tell me what is really going on idan ko kayi mun k’arya Allah na kallonka.” Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar da Abba gaskiyan batun ne koko a’a. Amma ai dan abokinsa besan ciwon kansa ba doesn’t mean shima ya biye masa.
“Sultan magana nake maka.”
“Abba a gaskiya ni ban san mey zahirin maganan ba don ko ni nan Afzal be ajiye ni ya sanar dani abinda ke damunsa ba sede in baka amsa base on yadda na karanci yanayin sa.”
“Bismillah ina jinka.”
“Akwai wannan yarinyar da Afzal keyi ma hidima wanda da zama yayi zama na soma ganin alamun son yarinyar a tattare da shi koda na gwada masa magananta akan cewa is about time ya sanar da ita k’udirinsa kuwa se abin ya koma fad’a ransa ya 6aci. Toh kwatsam kawai se mukaji yarinyan ta samu wanin da har sun dai-daita dashi sunyi nisa. A tunani na wannan ne dalilin daya jefa Afzal cikin wannan hali dan tun daga lokacin ban sake gane kansa ba ko office nasu naje acikin tunani nake tsintansa kullum.” Tunda Sultan ya soma bayanin Afzal ya dukar da kansa k’asa amman baze ta6a yafe masa wannan d’anyen aikin daya masa ba.
“Ko kasan yarinyar da kuma iyayenta?” Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar dasu gaskiya koko a’a sarai ya sani idan yayi hakan Afzal na iya fushi dashi har abada don haka ya kad’a kai “Ban san komi akanta ba Abba banda hotunan ta da nake gani da a wayansa kafin ya goge.”
“Shikenan Sultan nagode Allah sak’a maka da alheri kana iya tafiya.”
“Ameen Abba, Ummi ni zan wuce.”
“Mungode sosai Sultan ka gaida gida” yana ficewa Ummi ta maido da kallonta akan Afzal “Ai dama na sani nasan za ayi haka kai baka san ciwon kanka bane kake neman kai kanka ga halaka akan mace iyye? Macen da kana da tabbacin zata amince da k’udirinka muddin idan ka sanar da ita amman kak’i har wani can ya sace maka ita? Meye amfanin mu Afzal da bazaka zo ka sanar damu damuwanka ba?” Shiru yayi bece komai ba.
“Afzal?” Abba ya kirasa.
“Na’am” ya amsa.
“Wacece wannan yarinya?”
“Abba ni fa ba wata yarinya ni kaina ban san a ina Sultan ya had’o wannan labari ba ya baku kaman yadda na fad’a maka matsala muka samu a office na kusan rasa aiki na shine nabi a zuciya.”
“Nace wacece yarinyar?”
“Abba I’m sorry amman kaman yadda na fad’a maka ba wata yarinya.”
“Afzal wai meke damunka ne? Kai bakasan zurfin ciki na kai mutum ga halaka ba?”
“Ya isa Hajiya Mariam bar shi tashi ka tafi Allah k’ara ma lafiya.”
“Ameen nagode” yana kaiwa nan ya mik’e Ummi ce tabi bayansa tare da k’wala masa kira.
“Prince meke faruwa ne? Meya sameka? Prince idan baka sanar dani damuwanka ba mawa zakayi hakan? Wallahi koma wacece wannan yarinya da kakeso kasa zuciyanka a ruwan sanyi dan ka riga ka sameta just tell me wacece ka kuma bani address nata.”
“Ummi nagode amman ya kamata ki gane cewa ba wata yarinya.”2
“Da kyau Prince yau ka nuna min matsayina dake ba ni na tsuguna na haifeka ba dole ina tambayanka abu kana 6oye mun.”
“Ummi please wani irin magana kuma kike?”
“No ka tafi nagode” nan ta juya ta shiga tafiya duk kiran da Afzal keyi mata tak’i juyawa har ta k’arasa site nata.
Tunanin had’uwansa da Sultan kawai yake a dalilin mey ze fad’awasu Abba gaskiyan al’amarin?
Getting enough of her strawberry lips, a hankali yayi breaking kiss d’in had’e da mik’ar da ita suka zauna “Ya kamata kayi wanka Habib Albi akwai office gobe.”+
“Kin manta tare zamuyi wankan ne?”
“Toh tashi muyi ka samu ka huta ka kwanta.”
“Ni massage (tausa) nakeso.”
“Komey kakeso zanyi maka Habib Albi yanzu de ka mik’e tukun.”
“Kafin nan” yayi maganan had’e da zaro roban da Nazeefah ta basa akan ya bawa Amal “Ga wannan daga gun ‘yar uwarki” amsa tayi tare da kaiwa hancinta don shinshinawa “Wow turaren wuta!” Ta fad’a cike ca jin dad’i. “Allah sarki Nazeefah yanzun zan kirata inyi mata godiya kafin in manta.”
“Yakamata kam.”
“D’an mik’o mun wayana” nan da nan ta kira Nazeefah tayi mata godiya inda ita kuma ta nuna mata ba komai.
“Yauwa Kitten may I ask you something?” Ya tamabyeta bayan ta ajiye wayan.
“Anything Habib Albi.”
“Shin ya kikesa turaren wutan kine?”
“Mey kaga?”
“Unlike na Ummi da Nazeefah naki hayak’in baya yin yawa se k’amshi zalla.”
“LOL Habib Albi kai baka san shuwa da turaren wuta bane? I think tun ina shekara goma na fara kunna turaren wuta.”
“Nasani I’m just curious so tell me.”
“LOL okay ni ba se dab zaka dawo nake sawa ba, timing lokacin da zaka shigo nakeyi se in kunna 20-25 minutes before haka.”
“Window a kulle ko a bud’e kike sawa?”
“Ina kulle windows in sauk’ar da curtains, idan nabi gidan da turaren gabad’aya se in bashi kaman 10-12 minutes ya kama haka sannan in bud’e windon kad’an in kunna fan hayak’in ya fita, yana d’an fita se in sake kullewa kar k’amshin yabi iska shima a hankali har hayak’in ze watse gabad’aya yabar k’amshi.”
“No wonder mana kullum inyita mamaki.”
“Yanzu ka gane?”
“Yes Kitten” ya amsa nan da nan suka d’aura towel suka nufi bayi inda sukayi wanka, sun dad’e aciki sannan suka fito d’aure da alwala. Sallan isha suka idar suka kammala Azkhar nasu sannan suka sanya kayakin baccinsu. A hankali ta kwantar da Afzal akan k’afarta sannan ta shiga yi masa tausar, kasancewar hannayen nata sirara suke kuma k’anana se ji yake kaman cakulkuli takeyi masa. Duk lokacin da ta ta6asa seya sa dariya haushi ya bata k’arshe ta turesa daga jikinta.
“Ni na fasa yi” ta fad’a a fusace had’e da gangarawa wajenta. Bin ta yayi ya haye kanta ya shiga showering mata kisses tun daga wuya har izuwa fuska yana teasing nata sannan ya mik’a hannu ya kashe musu wutan d’akin. Xxx
Washegari bayan sun idar da sallan Asuba ta taya Afzal shiri dukda cewa da yayi karta damu ta koma bacci ze iya shirya kansa, seda ta rakasa har waje sannan ta dawo ciki ta koma bacci. Kaman yadda yake kiran Amal kowace safiya da yake gun Nazeefah haka ma ya kira Nazeefar yau suka gaisa seda ya tabbata bata da wata matsala sannan sukayi sallama.
Wajajen k’arfe biyu Amal ta d’au waya ta kira Afzal bayan ta tamabayesa ya aiki tayi gyaran murya “Habib Albi se nawa kake tashi daga office yanzu?”
“Wani abu ne Kitten?”
“I miss Mami and Papi” ta sanar dashi.
“Kina son kije ki dubasu?”
“Eh.”
“Toh ba ga motarki ba?”
“Toh Habib Albi na iya tuk’i ne?”
STORY CONTINUES BELOW

“Haka kuma fa semun koya miki a hankali.”
“Nifa tsoron tuk’i nake.”
“Toh haka zaki ta kallon motan naki Kitten?”
“A’a in zaka iya seka nemo min driver yana kaini duk inda nakeso amma nikam bazan iya tuk’i ba.”
“Me zai hana ki Kitten? We’ll discuss that later so kikace kinason ki duba su Mami?” Kai ta gyad’a wane yana gabanta.
“Alright bari inyi clearing schedule d’ina se in taho muje.”
“Dagaske Habib Albi? Ban shiga ma hak’k’in office ba ko?”
“Ai aikin office na zuwa ne a bayan farin cikin Kitten d’ina so I’ll be home in a jiffy kinji?”
“Toh Habib Albi seka zo I love you.”
“I love you most Kitten” da haka ta katse wayan. Girkin nata tayi sauri ta kammala ta zubawa mai gadi nasa sannan ta shirya kan dining. Bayan nan ta tsaya yin shawara ta kunna turaren wuta ne kota fara shiga wanka daga k’arshe de ta fara da shiga wankan. Bayan ta fito ta shafa mai ta tsara kwalyarta sannan ta sa wata bak’ar lace da touches and stone works na golden sannan ta fice parlour. Show glass nata ta bud’e ta ciro kwalban data juye turaren wutan da Nazeefah ta bata, haka kawai taji bari ta gwada kunnasa taji k’amshinsa yau. Gawayinta na kamawa ta zuba cikin kasko sannan ta barbad’a turaren akai se sauri take kar Afzal ya taho yanzu ya tarar da hayak’i. Tana zuba turaren akan gawayin kawai wani irin hayak’i ya shiga tashi tunda take bata ta6a ganin abu haka ba hurawa ta shiga yi a hankali amma ina se k’aruwa hayak’in yake har yana sanyata tari, shin wani irin turaren wuta ne wannan Nazeefah ta bata? Gashi nan da nan ya k’one ya fara bada warin k’onuwa da hanzari ta fita waje dashi ta k’ofan kitchen ta zubar.
Sabon gawayi ta d’ibo zata had’a kwatsam taji k’aran motan Afzal sosai gabanta ya fad’i parlourn ta dawo da wuri amma ta rasa ta ina zata fara fidda wannan uban hayak’i. Inda ma ace hayak’i ne zalla da da sauk’i amma ga warin k’onuwa gabad’aya ya d’umama gidan yau ta shiga uku. Afzal na bud’e k’ofan parlourn yayi sauri ya koma baya dan wani irin hayak’in dayaci karo da.
“Subhanallahi!” Yayi exclaiming da sauri had’e da zaro hanky yana toshe hancinsa. “Kitten ki fito kafin hayak’in ya miki illa” yace da ita yana mamakin ya akayi take tsaye har yanzu cikin tsabar hayak’in nan. “Kitten hurry!” kamar wacce k’wai ya fashe ma aciki ta fito ta samesa a waje.
“Ya haka meya faru?” Yayi saurin tambayanta.
“Yaya-” se kuma tayi shiru, gabad’aya ta kid’ime.
“Abu ne ya k’one miki?” Kai zalla take iya kad’a mai “Ya gidan da hayak’i haka toh? Ga kuma warin k’onuwa.” Har ta bud’e baki zata sanar da shi turaren wutan da Nazeefah ta bata ne ba kyau se kuma ta tuna nasihan da Mami tayi mata na cewa;
_Ko da wasa karki fara ki had’a kansa da na matarsa, komin mey ta miki kar kice zaki kai k’ararta gunsa idan har kece da gaskiya toh Allah da kansa ze wanke ki dan shi ba azzalimin bawa bane_ wannan lafazi yasa ta canza ra’ayinta tayi shiru.
“Yes??” Ya sake tambayarta jin tayi shiru.
“Ermm… Naje ina kula da girki ne se har turaren ya k’one akan gawayin I’m sorry.”
“Shikenan ba komai ina de baki k’one ba?”
“A’a.”
“Shikenan don’t worry mu zauna anan se hayak’in ya ragu kafin mu shiga.”
“Barin shiga in bubbud’e windows d’in in d’aga labule zefi fita da wuri.”
“So kike ki shak’i wannan uban hayak’i har seya miki illa Kitten?”
“Toh Yaya in ba haka ba baze fita da wuri ba har ka samu kaci abinci mu fita.”
“Toh muje in tayaki se muyi da sauri.”
STORY CONTINUES BELOW

“A’a ka jirani anan.”
“No Kitten I insist” haka suka k’arisa ciki suka shiga bubbud’e windows d’in, da hanky mak’ale a hancin Afzal amma dukda haka wari da hayak’in be barsa ba, gabad’aya jikin Amal yayi sanyi sam ba haka taso abinta ba. A waje suka zauna seda hayak’in ya ragu sannan suka koma ciki bin parlourn tayi da turaren Khumra don kashe warin. Bayan ta sirka masa ruwa yayi wanka suka fito dining don cin abinci sede tun d’azun yake kallonta gabad’aya tayi shiru ba walwala tattare da ita.
“Kitten?”
“Na’am?” Ta amsa tana d’ago kai.
“Yau achan zaki zauna?” Kai ta gyad’a zalla “Why?”
“Yaya I’m sorry.”
“Why? What for?”
“For the inconvenience wallahi ban san ya akayi turaren ya k’one haka ba please forgive me.”
“Ohh Kitten!” Ya numfasa “Come here” ba gardama ta mik’e daga kujeran nata ta samesa, a cinyarsa ya zaunar da ita “It’s really okay dear, kullum kinayi me kyau dan an samu akasai yau kuma seya zama abun magana? Kidena damun kanki kinji? Ni baki mun komai ba.”
“Thank you” tace dashi cikin sanyi, shi da kansa yayi serving nasu sannan ya shiga feeding nata seda suka k’oshi tukun suka jira La’asr yayi suka yi sallah suka shiga shiri, se wajajen biyar da rabi suka dawo gida se hira Mami take jansu da.
Bayan sallan Maghrib Amal da Afzal suna zaune a parlour Afzal ya mik’ar da k’afafunta akan cinyansa tana tayasa kallon sports se wayanta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Nazeefah ke kira bata hankara ba ta d’aga.
“Assalamu Alaikum.”
“Wa’alaikumus salam Nazeefah” ta amsa ‘”Yar uwa ya kike?”
“Lafiya k’alau ya gida da wahala kuma?”
“Wani wahala ne kuma, gida k’alau ya Ya Afzal?”
“Lafiyanshi k’alau.”
“Nace kinyi amfani da turaren wutan nan kuwa?”
“Eh.”
“Gosh! Dama kira nayi ince karkiyi amfani dashi bashida kyau yanzu Mummy ta kirani take sanar dani matar da ta sayar matan ta cuce tane” ta shirya mata k’arya don dama da gan-gan ta bata turaren wutan sanin bashida kyau.
“Ayyah wallahi har na kunna d’azu.”
“Ba dad’i ko?”
“Unfortunately gashi yata hayak’i kuma yana k’onewa gabad’aya ya d’umamamun gidan.”
“Subhanallahi Ya Afzal na gida kuma? Kinsan bayi son hayak’i.”
“Wallahi abun beyi ba sam, ina cikin sawa ya dawo.”
“Allah sarki kiyi hak’uri dan Allah ban san bashida kyau ba da ban baki ba.”
“Ba komai Nazeefah ai bazaki cutar dani da gan-gan ba.”
“Toh bari in barki haka kar in shiga hak’k’in Ya Afzal.”
“A’a fa karki damu.”
“Toh ki gaishesa seda safe.”
“Allah bamu alkhairi” da haka sukayi sallama. “Huuh!” Tayi exhaling had’e da ajiye wayan “Waye ne? Nazeefah ce?” Ya tambayeta.
“Eh tana gaisheka.”
“Ina amsawa maganan mey naji kuke haka?”
“Batun turaren wutan ne kasan wanda ta ba nin na kunna ashe wai bashida kyau matar data had’an bata k’ware ba seta damfari Mummy dama kira tayi tace kar in kunna nace ai tun d’azu na kunna.”
STORY CONTINUES BELOW

“Ayyah kinga bama laifinki bane kike ta tada hankalinki daga turaren wutan ne.”
“Ai toh naga baka son hayak’i ne shine hankalina ya tashi.”
“Next time ki kwantar da hankalinki kinji?” Kai ta gyad’a mar a hankali sannan ya shiga tickling toes nata ya na mata cakulkuli, dariya ta tsaya yi na sosai chan wajajen tara da rabi suka kashe TV’n suka yi wanka suka kwanta.
Washegari da yamma Afzal ya koma gun Nazeefah, tsaf ta gyara gidan ta itama ta kunna turare sede hayak’in ne yayi yawa. Bayan sun yi Sallah sun ci abinci suna zaune a parlour Afzal yayi gyaran murya ya kira ta “Rabba’atul Bait?”
“Na’am Ya Rouhi” ta amsa.
“Shin ya kike sa turaren wutan ki ne kam?”
“Mey kaga?”
“I’m just curious ya kike sawa?”
“Dab zaka zo nake sawa.”
“Shiyasa hayak’in yake yin yawa.”
“Yana damunka ko?”
“I’m sorry but yes kinsan bana son hayak’i.”
“I’m sorry a haka fa na bubbud’e window ma dan ya d’an ragu.”
“Kinsan ya Ummi takeyin nata?” Beso ya ambaci sunan Amal ba gudun kar hakan ya sanyata kishi. Kai ta kad’a a nitse.
“Kunnawa take 20-25 minutes idan tana expecting bak’o saboda hayak’in ya tafi.”
“Toh Ya Rouhi k’amshin ai se k’are kafin nan.”
“Nop kinga zaki kulle windows ki sauk’ar da curtains seki sa ki basa like 10-12 minutes haka ya kama, then ki d’an bud’e window ki kunna fan ya tafi da hayak’in yana d’an fita sekiyi shutting back windows d’in kinga haka k’amshin ki yana nan hayak’i kuma ya tafi.”
“Kai amma Ummi akwai fasali na gane Ya Rouhi nima haka zan fara sawa in shaa Allah.”
“Yauwa Rabba’atul Bait shiyasa nake sonki.”
“Uhm Ya Rouhi?”
“Yes Babe?”
“Wallahi wata tambaya nake son inyi maka amma bana son kamin mumunar fahimta.”
“What is it? Feel free to ask me.”
“Bazaka mun mumunar fahimta ba?”
“Just ask me Nazeefah.”
“I’ve been curious for a while tun da aka kusan auranka ciwon zuciyanka be sake tashi ba shin dama mey dalilin? Meyake jawo maka attack d’in?”
“Naze-“
“Please tell me Ya Rouhi the last time I asked you banji dad’in yadda ka nuna mun a fili bazaka iya sanar dani ba I felt like you didn’t trust me as your wife.”
“Ba haka bane Nazeefah of course I do trust you.”
“Toh yaya ne Ya Rouhi ai idan da ka yarda dani komi naka zaka iya sanar dani nasan da Amal ce ta tambaya da tuni ka sanar da ita.”
“No please don’t ever say that again kaman yadda Amal take matata kema haka ne so ki daina tada hankalinki kina ganin kaman nafi sonta fiye da ke, I love you both okay?”
“Okay Ya Rouhi kayi hak’uri idan magana na ya 6ata maka rai.”
“Ba komai ya wuce.”
“So zaka iya fad’a mun?” Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk’e “I’m very sorry Nazeefah amma Amal ce sababin ciwon nawa, rashinta a kusani dani shi yake haddisa mun ciwon nawa.”
“Amal?” Ta tambaya cike da mamaki bil adad “Rashin Amal Ya Rouhi?”
STORY CONTINUES BELOW

“Yes Nazeefah, Amal.”
“Wow!” Ta numfasa yanzu akan Amal Mummy ta mareta ranan a fuska? Yanzu akan Amal tsakaninsu da Ummi ya kusan 6aci? Wow! Ai dama seda jikinta ya bata haka amma tak’i amincewa ashe gaskiya ne in bahaka ba kanta ya mugun d’aurewa yadda ciwon nasa be sake tashi ba tun da ya kusan aure.
“Amma ban fahimce ka ba Ya Rouhi shin ba auran soyayya kukayi da ita Amal d’in bane dama har kake tsoron rasata haka?”
“It’s a long story Nazeefah.”
“Will it be okay if you tell me?” Numfasa yayi sannan ya fara kaman haka;
“I’ve known Amal for three years now tun kafin muyi aure muke tare da ita amma ba a matsayin saurayi da budurwa ba don daga baya ne nayi developing feelings mata lokacin kuma ita har sunyi nisa da wani saurayinta Abdul kin gane sababin ciwon nawa?”
“Anytime ka gansu tare se ciwon naka ya tashi kai kuma ka kasa sanar da ita kana sonta?” Kai ya gyad’a zalla.
“Toh ina shi saurayin nata yanzu?”
“Yana Canada.”
“Ya sadaukar maka da soyayyanta kenan?”
“Yes Nazeefah.”
“Allah sarki gaskiya na ji ma wannan masoya guda biyu Allah sa hakan shi yafi alkhairi a gareku duka.”
“Ameen Rabba’atul Bait I hope I’ve answered your question.”
“Yes you did Ya Rouhi muje ka watsa ruwa mu kwanta gobe office ko?”
*****
Haka kwanaki suka ta shud’ewa yayinda shak’uwa da soyayya keta dad’uwa tsakanin Afzal da Amal, a yau jirginsu na zuwa Saudi ya tashi kad’an ya rage Amal batayi kuka ba sanda jirginsu yazo tashi tsabaragen tsoro.
Da zuwansu yau sun samu sati kenan lafiya k’alau suke zaune, kullum suna cikin fita shopping da wajajen shak’atawa, tsaraba da dama Afzal ya sai wa Nazeefah wasu ababen ma Amal ce ke cewa ya saya mata, sosai yake jin dad’in yadda Amal ta d’au Nazeefah da zuciya d’aya.
Yau a d’aki sukayi deciding su yini Amal na mik’e akan gado tana latsa wayarta yayinda Afzal ke tsaye gaban mirror ko mey yakeyi oho.
“Arghh!” ya saki k’ara bisa yankewan da yayi da reza.
“Subhanallahi lafiya?” Amal ta tambaya. Ba shiri ta mik’e lokacin da taga jini na bulbula daga yatsn nasa.
“Innalillahi! Habib Albi!” Tissue taja da wuri gaban mirron ta shiga tare mai jinin “Omg I’m so sorry sannu” tace dashi a rikice tamkar zatayi kuka da mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shi da ya yanken ma hankalinsa be tashi ba kaman yadda nata ya tashi. Iska take hura masa tana ce mai sannu ba makawa.
“Kitten calm down yanka nefa kawai.”
“But yankam ai deep ne Habib Albi sannu” iska ta cigaba da hura masa sannan tajasa izuwa bayi, spirit ta bud’e “Ka rufe idonka zeyi zafi” dariya sosai ta basa “Ce miki akayi rago ne ni?” A hankali ta shiga bulbula masa akan ciwon, wincing kad’an yayi Amal kam sekace ita aka sawa akan ciwo se tashi tsikan jikinta yake. Cike da lalashi tana hura mai iska tana ce mishi sannu ta mishi dressing ciwon ta tasa bandage. Se kallonta yake yayinda wani irin wutan sonsa yake ruruwa a zuciyansa.
“Kitten it’s okay.”
“It’s not Habib Albi baka ga yadda yata jini bane?” hannun nasa ya zame daga nata had’e da rik’o k’aramar kunkuminta seda ya matso da ita kusa da shi “Bade kuka kike shirin yi ba Kitten?”
STORY CONTINUES BELOW

“No” ta amsa ciki-ciki mik’awa yayi had’e da kissing soft lips nata, sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya sannan a hankali tayi pulling out. “Thank you Kitten” ya furta yana maida gashin ta baya.
“What for Habib Albi?” Ta amsa tana zagaye hannayenta a wuyansa.
“For everything sweetheart, I can’t imagine life without you, Allah yayi miki albarka I love you so much.”
“Ameen Habib Albi I love you most” peck ta masa placing a kumatu “Muje ka huta” d’akin suka koma ta mik’e akan gado tana duba messages nata yayinda ya canza kayan jikinsa da jini yad’an 6ata. Hankalinta gabad’aya ya duk’ufa akan chatting da takeyi da Maamah kawai taji Afzal ya k’wace wayan kafin tace ya bata ya mik’e a jikinta had’e da kwantar da kansa a saitin k’irjinta wane d’an wani yaro.
“Habib Albi-“
“Lets sleep Kitten bacci nakeji.”
“Toh ka tsaya in gyara kaji?”
“Ni haka nakeso” murmusawa tayi sannan tayi placing mai light kiss acikin gashin kansa yayinda take shafashi a hankali. A haka har bacci ya d’aukesu duka.
Sati biyu sukayi sannan suka dawo Nigeria, a ranan da suka dawo Nazeefah ta shirya musu abinci da dama ta kai musu haka Ummi da ma Mami, washegari sukayi sorting out tsaraban kowa suka kai musu, da yammacib ranan ya wuce gidan Nazeefah. Bayan sun k’are dinner sun dawo d’aki ta zaune gefensa akan gado inda take sanar da shi batun makaranta akan cewa in a week time zasu bud’e.
“Yes haka Amal tace kekam final semester d’inki kenan ai ko?”
“Yes Ya Rouhi.”
“Toh Allah nuna mana graduation nakun.”
“Ameen thank you nace ba..” se kuma tayi shiru.
“Yes what is it?”
“Ya Rouhi are you okay with it in d’auko mey aiki? Kaga semester’n nan na neman concentration sosai bazan zo in iya da aiki da shara d’innan ba shine nace idan ka amince na riga nayi magana da wata mata yaranta are ready to work for me and Amal.”
“Itama Amal tace tana buk’atan mey aikin ne?”
“Bata fad’a ba amma nasan zata buk’ata ai Ya Rouhi ita da course nata yafi nawa wuya ma ai kaga zata fini buk’ata ma.”
“Hakane kam so masu aikin kwana ne ko na jeka ka dawo?”
“Na kwana ne saboda daga k’auye za’a kawo su bawai anan suke da zama ba.”
“Masu aikin kwana kuma Rabba’atul Bait?”
“Ya Rouhi nasan me kake gudu karka damu yara ne fah Khaleefah ma ya girmesu d’ayar 16 d’ayar kuma 14 kaga ai baza a samu wata matsala ba in shaa Allahu.”
“Toh zanyi ma Amal magana.”
“Yauwa duk abinda akwai seka sanar da ni muyi making arrangements ya zammana de sun fara aikin tun yanzu ba se an bud’e makaranta ba.”
“Jazakillahu khair Rabba’atul Bait yadda kikeso wa Amal abinda kikeso wa kanki.”
“Ameen Ya Rouhi an zamo d’aya ai yanzu zamu kwanta ko?”
STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi kaman kin sani a gaje nake.”
“Akwai gajiya ai ko nayi maka tausa tukun?”
“Baki gaji ba?”
“Ai bana gajiya when it comes to you” mik’ewa yayi kan gadon ta shiga yimai tausan a hankali tana relieving mai tension.
*****
Kwana biyu yayi mata sannan ya dawo gun Amal.
Amal fa ba wasa kitso taje aka rangad’a mata k’anana sannan ta sha lalle ja a tafin hannu ta baya kuma akayi mata bak’i irin na zamanin nan mey kyau. Kafin Afzal yazo ta gama girkinta ta bi gidan da turare se k’amshi zallah ke tashi.
“Oyoyo Habib Albi” taje tayi hugging nasa da gudu.
“Oyoyo my Kitten” sun d’au kusan minti d’aya manne a jikin juna sannan ya d’agota a hankali “Masha Allah kin ganki kuwa?”
“Nayi kyau?” Ta tambayesa tana wasa da yatsun hannunsa.
“Yes Kitten yakamata in biya kud’in wankan nan.”
“Awwn thank you Habib Albi” ciki suka k’arisa suka nufi d’akinsu inda ya rage kayan jikinsa suka haye kan gado “Yau mey aka girka mun Baby?”
“Your favorite!” Ta sanar da shi.
“Spaghetti?
“Uhumm.”
“Wow! Ya kike toh?”
“Lafiya k’alau ka baro Nazeefah lafiya?”
“Lafiya k’alau tace in gaisheki.”
“Ayya ina amsawa jiya ma Mami tana nan ai tazo muka yini mun.”
“Allah sarki ya take?”
“She’s fine” ta amsa se kuma taga yadda Afzal keta kallonta tun d’azu da fari ma tsarguwa tayi kode jan bakinta ya hau kan fuskanta ne?
“Habib Albi lafiya?”
“Matso kiji” matsowa tayi kusa da shi hakan be masa ba seda ya aza ta kan cinyansa “Kitten?”
“Yes?”
“Anya kuwa?”
“Anya kuwa mey Habib Albib? Wani abun ne?”
“Anya babu ajiya na anan?” Ya tambayeta had’e da aza hannunsa kan cikinta wani kunya maras misaltuwa taji ya rufeta “Kai Yaya” nan ta shiga kare fuskanta.
“Seriously naga kin k’ara freshness ne ai skin naki se wani glowing yake.”
“Toh Yaya naje k’asa me tsarki ba dole ba ko ka manta kwanana na hud’u kacal daga dawowa daga Saudiyya?”
“Ina sane kawai de ina tambaya ne.”
“Toh ka kwantar da hankalinka ba komi anan” ta fad’a tare da aza hannunta akan nasa dake manne da cikinta.
“Kai Kitten kode 6oye mun kike ne?”
“A dalilin mey zan 6oye maka Habib Albi?”
“Toh yaushe rabon ki da kiga period naki.”
“Ni bana son tambaya” ta fad’a tana neman mik’ewa hannunta yayi saurin ja “Ai sai kin amsani.”
STORY CONTINUES BELOW

“Yaya mana hannu na” saketa yayi a hankali “So answer me.”
“Yaya jiya fa nayi wankan sallah.”
“Kitten k’arya kike mun ko?”
“Yaya na ta6a maka k’arya ne?” Ta maraice fuska.
“Toh shikenan very soon nasan seed d’ina zeyi germinating.”
“Muje kaci abinci toh.”
“Yauwa Nazeefah tace in fad’a miki ta sama muku masu aiki tunda kun kusa komawa school kar aikin gida yayi interfering muku da school.”
“Mey aiki kuma Habib Albi?”
“Yes haka tace.”
“Na mey? Ni bana buk’atan mey aiki da safe kafin in fita school zan iya kammala aiki na, ranan da nake da lectures 7 kuma idan na dawo gida se inyi abu na.”
“Gajiyan baze zo ya miki yawa ba Kitten I think shawaran Nazeefah fa yayi mey aikin zata taimaka miki kinga kafin ki dawo daga school ta gama miki komai kika dawo girki kawai zakiyi ki huta.”
“Habib Albi ni gaskiya bana so.”
“Toh yanzu ya kenan? Ince wa Nazeefah bakiya so? Ai bazata ji dad’i ba tunda har tayi wa mutanen magana kuma tun daga k’auye tace za’a kawo su.”
“Kyansa dama ta tambayeni ko kai kafin tayi musu maganan.”
“Hakane amma ai ita bata d’au zaki k’i taimako ba.”
“Ba wani nak’i bane Yaya kawai ina ganin bana buk’ata ne.”
“Zaki buk’ata fa Kitten keda kike yin tough course aikin gidan zezo yayi miki yawa.”
“Toh shikenan tunda kaima ka goyi bayan hakan.”
“I’m sorry if I’m forcing you into this kinsan halin Nazeefah ba sena fad’a miki ba kina k’i yanzu zata ce bakiya appreciating effort nata ne ta fara k’ananun suratai kawai kiyi hak’uri ki amince shine kwanciyan hankalinmu duka. Bazan 6oye miki ba ko ni banji dad’in yadda seda ta gama komai sannan ta sanar dani ba amma haka nima nayi hak’uri.”
“Hakane kam ba komai zan kirata inyi mata godiya.”
“That’s by Babeh let’s go eat toh I’m craving for your delicious already.” Hannunta acikin nasa suka nufi dining suka ci abinci ba da dad’ewa ba Maghrib ya shiga ita kad’ai tayi nata kasancewar Afzal ya soma fita Masallaci yanzu.
Washegari***
“Ya Babe shiru har yanzu? Cewan Rumaysa daga d’ayan 6angaren.
“Wallahi layin Ya Afzal nake ta gwadawa amma bai d’auka nakega suna meeting ne so nike in tambayesa izini kamin in fito.”
“Toh ina jiranki.” Kashe wayan tayi 10 minutes later ta sake trying numban Afzal amma still baya d’agawa. Se chan k’arfe uku taga call nasa na shigowa da hanzari ta d’aga.
“Babe ina ka ajiye wayanka?”
“I’m sorry meeting muke se yanzu muka fito ya akayi?”
“Izini nake son nema zani gidan k’awata.”
“Toh bismillah go ahead you’re permitted.”
STORY CONTINUES BELOW

“Thank you Ya Rouhi.”
“Aha bye.” Dama ashirye take key’n motarta ta d’auka kawai ta fice chan gidansu Rumaysa ta wuce inda ta nuna mata ‘yan matan. Bayan sun gaisa Rumy ke tambayarta “So wacce zaki d’auka?”
“K’aramar kai ai babban zata fi mana harka da kyau senu kaiwa Amal babban.”
“Toh Hindu ga Aunty’nki Nazeefah ita zata d’aukeki aiki ke kuma Safiyya zamu kaiki wa amaryarta” kai duka suka gyad’a “kina iya tafiya ko Hindu na?” Cewar Nazeefah “Bari muyi magana da yarki” ba musu ta mik’e ta fice.
“Yauwa kaman yadda na fad’a miki wannan itace Aunty Nazeefar itace wacce mukeso ki bamu had’in kai dan fitar da shegiyar da ta aure mata miji.”
“Duk abinda kukace shi za ayi Aunty.”
“Yauwa Sofin gaye ga waya nan Aunty Nazeefah ce tace a sai miki za kuna waya da ita ta ciki koda wasa kuma kar kiyi saving lambarta saboda ba’a san yadda abu ze zo ya kasance ba da kinga lamba me 08102 toh nata ne kin gane?”
“Na gane.”
“Good kuma kina yi mata ladabi da biyayya kinji?” Nazeefah ta kar6e Rumaysa “Sunanta Amal amma Aunty zaki na ce mata duk aikin da takeso a gidan kinayi mata shi ba ruwanki da yi mata sata, duk abinda kikeso ki kirani zan baki kina ji na ai?”
“Eh Aunty.”
“Yauwa zuwa gobe zan zo in d’aukeki da ‘yar uwarki in kaiki gidan nata.”
“Toh Aunty.”
“Rumy ta fad’a muku albashinku ko?”
“Eh dubu goma.”
“Yes sannan naki zanna k’ara miki extra dubu goma akai ko wani k’arshen wata idan har zakiyi mun aiki me kyau zuwa lokacin da zan samu in cimma burina.”
“Toh Aunty godiya nake.”
“Yauwa bayan nan kuma ko k’anwarki ce karki sanar da ita, wannan magana ya rage sirri a tsakanin mu kin gane?”
“Na gane Aunty.”
“Toh Babe barin koma.” Har waje Rumy ta rakata sannan ta dawo ciki.
Washegari kaman yadda suka tsara Nazeefah tazo ta d’aukesu gidan Amal suka fara wucewa lokacin Afzal ma bai gida ya fita office. Sannu da zuwa Amal tayi musu ta shigo dasu “Bari in d’auko muku ruwa.”
“A’a ‘yar uwa (yadda take kiran Amal) karki damu ai daga gida nake wannan ne masu aikin zan d’au k’aramar in baki babban tunda daman ke yayata ce.”
“Kai Nazeefah ai kece babba a gidan nan.”
“Toh nide zan d’au k’aramar Hindu ke kuma babban Safiyya.”
“Toh Safiyya sannu da zuwa:”
“Yauwa Aunty nagode.”
“Safiyya ban da rashin kunya kinji ko? Yi kinyi bari kin bari.”
“In shaa Allah Aunty.”
“Toh bari zamu wuce gida muma.”
“Toh kin shigo da kayakin ki duka ko?” Amal ta tambayi Safiyya.
“Eh Aunty” ta amsa.
“Toh bari mu raka ku” nan suka rakasu har gun mota bayan sun dawo ciki Amal ta kai Safiyya d’akin data bata wanda zata na kwana aciki. D’aki ne harda bayi aciki ga gado da drawer harda dressing mirror. Yadda ake kunna shower da kuma yadda ake flushing ta nuna mata sannan ta bata waje ta watsa ruwa.
Bayan Afzal ya dawo daga aiki ya watsa ruwa ya d’an huta take sanar da shi akan cewa Nazeefah ta kawo mata mey aiki d’azu “Bari inyi mata magana ku gaisa.”
“Ko gobe ma baza mu gaisa bane Kitten?”
“Toh ai kana fita office da wuri bari de ku gaisa yanzun lemmi speak with her” Nan ta mik’e, tare suka taho da Safiyya tana binta a baya daga baki bakin parlourn ta tsuguna ta gaishe da Afzal cike da ladabi da biyayya, shima ba yabo ba fallasa ya amsa.
Washegari bayan Amal ta shirya Afzal office ta dawo ciki ta koma bacci se wajajen goma ta tashi, wanka tayi tasa kaya sannan ta fito da mamaki ta tsaya tana bin parlourn nata da kallo yadda Safiyya ta share tayi mopping, dining ta zarce nan ma ko ina sparkling yake. “Wow!” Ta furta wai ita da take shirin koya mata yadda zata na yin aikin?
“Safiyya!” Ta k’wala mata kira.
“Safiyya!”
“Na’am Aunty” ta amsa tana shigowa ta k’ofar kitchen. “Ina kwana?” ta tsuguna ta gaisheta.
“Lafiya kin tashi lafiya?”
“Lafiya k’alau Aunty.”
“Sannu da aiki ga ko ina yayi kyau.”
“Nagode Aunty Tv’n ne banso in goge ba kar in ta6a wani abun.”
“That’s so thoughtful of you, zan gwada miki da kaina amma kafin nan kin karya?”
“A’a tukuna.”
“Toh bari in shirya mana breakfast” nan da nan suka shiga kitchen d’in Safiyya tana tayata, bayan sun gama tayi wanke-wanke sannan Amal ta nuna mata yadda zata na goge TV da stand d’insa. Bayan sun gama Amal ta sallameta ta wuce d’akinta. Tana cikin buga game a wayarta Nazeefah ta sa mata kira nan ta d’aga tare da kashe muryarta yadda ba waje baze jita ba.
“Assalamu Alaikum Aunty.”
“Wa’alaikumus salam Safiyya ya kike?”
“Lafiya Aunty ina kwana?”
“Lafiya k’alau ya wajen aikin naki? Ba wata matsala ko?”
“Babu komai.”
“Ta baki abun karin kumallo?”
“Eh flask d’in ma ta ajiye mun a gaba na wai in d’iba da kaina.”
“Mak’ira kawai, ke kika shirya wa Ya Afzal breakfast ko ita da kanta?”
“Ita da kanta nace zan tayata tace zatayi da kanta inje in kwanta.”
“Mak’ira mey ta girka masa?”
“Dafaffen dankali ne da sauc da wani abu kaman nama nama aciki.”
“Lallai aikin ki na kyau kwanan nan zamu fara aikinmu akanta kede ki tabbata kina mata duk wani ladabin da ya kamata.”
“Toh Aunty.”
“Yauwa karki manta kina goge lamba na daga call logs naki duk sanda muka gama waya.”
“Toh Aunty ki gaishe mun da Hindu.”
“Tana bacci idan ta tashi zan sanar da ita sai anjima.”
“Yauwa nagode” da haka sukayi sallama.