RANAR NADAMA CHAPTER B KARSHE
tace” Dady a rayuwata ban taba zato ko tsammani akwai mummunar rana zata shigo rayuwata ba irin yau ban taba zaton zan fuskanci ranar takaici da bakin cikin irin nan ranar wallahi Dady wannan ranar ta kasance RANAR NADAMA a rayuwarmu saboda alhasssan ya gama kashe mana rayuwa da duniyarmu ya cuce mu yaci amana ya ha’incemu ya gurguntarmin da rayuwa da duniya ta ba abin da zan ce da Alhassan sai allah ya…” Wata irin gigitarciyar tsawo Dady ya daka mata yadaura magana cikin hargagi da nuna tsantsar bacin rai”baki da hankali ne hala ibar dawanau ce ke da alamun gushewar hankalin dakika gamu dashi zai iya sanyaki ki aikata komai koda kuwa zage iyayenki ne” ya shiga nuna ta da hannu cikin tsananin bacin rai ya daura da cewa “yadace ki sani mijinki mijikin ne bakowani Sirri ya kamata ace kin yi masa tonon BANKADA ba kisani ke da mijinki kun zama Abu daya komu iyayenki bai dace ace kina sanarmu sirrin tsakaninki da mijinki ba Dan haka ki
kiyaye”ya na dasa aya a zancen yafara kokarin mikewa momy tayi saurin dakatar dashi “Alhaji yakamata ka fuskanci yarinyar nan akwai alamun ayar tambaya cikin lamarin ta Dan allah kayi hakuri ka zauna mu fuskance ta” duban ta yayi cikin wani yanayi amma baice komai ba Yakoma ya zauna yayi shiru kamar mai nazari wani abun na daban momy ta dubi bunayya “ya kamata ki warware mana komai domin sanin inda zamu fuskanta akan wannan birkitaccen lamarin”bunayya da ke tafsman rusa kuka kamar ranta zai fita gabadaya tagama YANKE TSAMMANI mahaifin ta bazai yarda da ita ba musamman yarda taga yadau zafi bai ba maganar ta ta muhimmamci ba tabbas Alhassan ya gama da rayuwarta ya cuce ta cuta mafi muni da kassara rayuwa tabbas ta yarda irin tata KADDARAR RAYUWAR kenan da allah ya jarabeta da ita ba abin da zatace da Alhassan sai allah ya bi mata hakkin ta Dan ba yafe masa za tayi ba tunda har ya gayyatowa rayuwarta. Tashin hankali da bakin ciki Ya yafa mata ta nisa cikin kokarin shanye kukan nata “Dady ka fahimce ni wallahi abin da nake fadi har ga allah gaskiya ne ko rantsuwa zan iya yi maka Alhassan makashin rayuka ne Dan kungiyar asiri ne mashayin jinin jikin muta ne”
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’u na abin su momy da rukayya har dashi kan sa dady bakin su yashiga ambata cikin alamun tsoro da fargaba momy dake zaune bisa kujera sai gata baje a kasa tayi zaman dirshen gumi yafara karyo mata cikin firgita “ke yar nan bana son KAZAFI ki ji tsoron allah zaki mutu alhassan din me. Mashayin jini “cikin kuka tace ” wallahi ba karya azance na har ga allah baxancen kazafi ko kulla sharrin a cikin maganata Ku yarda dani”ta karashe cikin sakin kuka mai ban tausayi rukayya dake zaune gabakidaya jin duniyar tayi tana juya mata jiki a sabule ta karasa kusa da bunayya ta dafamata kafada”bunayya ki tabbatar da abin da kike fadi gaskiya ne”kai kawai tagyada mata hawaye na kwaranya saban fuskarta alhaji dake zaune abin duniya ya taru ya hana kwanyarsa aiki yarasa bakin magana kawai kallo yake bin bunayya dashi cikin rashin haiyaci momy tasake nisawa”yanzu ina alhassan din?” idanuwa bunayya ta kwalalo waje Sam yanzu baza ta iya cewa ga inda yake ba yo koma tasani yasin bazata fadi ba Dan tasan tqbbas suka hadu baza a kwashe ta tadi ba ganin da momy tayi bata da niyar magana yasanya ta sake kokarin tambayar ta amma ringing da wayar hannun rukayya ta dauka yasanyata saurin yin shiru ita kanta rukayya ta firgita da jin ringing din da Sauri takai dubantaga wayar sai kuma tadubi bunayya tare da tura mata wayar “amshi mijinki ne ke kira”jin abinda rukayya tace gsbadaya sai suka dauke numfashi cikin razana bunayya ta zabura tayi baya cikin rawar murya ta fara magana “Makashin rayuka mai zuke jinin mutane zaki ce nayi magana dashi gaskiya sai yau na tabbar ke wata ibar dawanau ce wallahi kina ganin mutuwa azahiri zaki turomin ita mai zai hana ke ki daga wayar amma kinji na rantse ba abin Da zai sanyani na dauki wannan kiran daga shi sai zarcewa lahira!!” Ta kareshe maganar cikin zanzaro Idanuwa daidai lokacin wayar ta tsinke ba ta jima ba aka sake kira nan ma ba Wanda yayi kokarin dagawa sai da akajero kiran sau shida sannan alhaji yayi kundunbalar cewa rukayya ta miko masa wayar bunayya najin abin yace ta zabura cikin kururuwa”dady ba fa gajiya da ganinka mukayi ba mu shirya yi maka zaman makoki yanzu ba in kana yiwa allah kar kada ga wayar nan zuke jininka zaiyi” hannun yadaga mata alamar ba ya muradin jin kalamanta bakin sa dauke da addu’o’in Neman tsari yayi kundunbalar daga wayar cikin sallama yayi cin sanyin murya daga can bangaren yaji an amsa anzarce dacewa “dafatan ina magana da danuwan mamallakin wannan wayar” alhaji yagyada kai kamar yana gaban San sannan yakokarta cewa “eh” akayi ajiyar xuciya sannan a ka zarce da cewa”muna bukatar ganin Ku saboda mai wayar yana cikin wani mawucin hali sanadiyar hatsari da ya gamu dashi akan titin zuwa gadon kaya yanzu haka angarzayashi asibitin murtala..” Dif alhaji yaji wayar ta dauke cikin ranshi yafara ambaton innalillahi wa’inna ilaihir raji’un bunayya dake a tsure ganin halin da mahaifinta yashiga nan da nan ta rushe da kuka “shikenan abin da nake gudu ya afku shikenan yakashe shi yakai shi lahira ….” Muryar alhajin ta katse ta” ke bana son sakarci” dif tayi ta na dubansa tare da ajiyar zuciya ya dubi hajiya da it a ma jikinta asabule izuwa wannan lokacin “kin ji wai tsautsayi ya gamu dashi na hatsari yanzu haka yana kwance asibitin murtala cikin mawuyacin hali da rashin haiyaci”sallallami momy tashiga yi rukayya kuwa mutuwa zaune tayi saboda tsoro bunayya dake tsaye kamar wacce aka dasa tashiga duban mahaifinta cikin rashin inda zancen nashi yadosa. minti na Biyar suka share ba Wanda yayi yin kurin yin magana kowa zuciyarsa sai jaje da tsoro take musamman bunayya Dan gabakidaya duniyar taji tayi mata wani banbarakwai komai ya kwance mata Dan guntun tunanin kwanyar ta ta yazuru dagu ya barta ta rasa abin da yadace tayi domin saita kanta “Ku tashi mu tafi asibitin” alhaji yayi furucin cikin sanyin murya idanuwa suka zuba masa cikin rashin haiyaci duk ya lura da yanayin dasuka shiga amma sai ya dauke musu kai ya mike ya dubi Momy”in kun shirya Ina jiranku a mota” bai jira tsinkawarsu ba yafice daga falon wata katotuwar ajiyar zuciya Momy tayi ta dubi rukayya ” shin zaki bimu ne ko gida zaki koma” idanuwa ta zuba mata tana gyada mata kai alamar zata bisu Dan ita ma tana bukatar karin haske cikin wannan RIKITACCEN AL’AMARIN cikin hanzari Momy ta mike tafada dakinta ta dauko mayafinta tadawo falon har yanzu bunayya na tsaye kamar wacce aka dasa bunayya ita na tsaye Momy tadubi bunayya fuskarta na bayyanar da damuwa matsananciya “ba wani mahaliki kuma bawa da ya isa ya cuci danuwansa bawa batare da yarda allah komai na duniya sai allah ya yarda yake faruwa kuma ko wacce irin KADDARAR RAYUWA da tasamu bawa dama tun fil’azal allah ya rubuta sai yafaru dashi ina mai shawartarki ki dauki ko wacce irin kaddara ce allah ya rubuta miki arayuwa ki rungumeta da hannu biyu bunayya kisawa zuciyarki komai ya faru dake daga allah ne” ta kareshe cikin muryar rarrashi da karfafa mata guiwa ta juya ga rukayya “taimaka Ku taho tare da hanzari Alhaji najiranmu” tana karasa maganar tafice da hanzari daga falon rukayya tadubi bunayya” daurewa zakiyi da yardar allah sai ya fidda miki da hakkin ki akan wannan azzalumin tashi mu tafi “cikin sanyi jiki nan dai rukayya ta taimaka mata ta gyara jiki su fice
Mota daya sukayi gabadayansu alhaji ya jasu har suka isa asibitin murtala cikin lokaci kalilin suna isa sukayi tambaya basu sha wahalar gane inda Alhassan yake ba sunyi matukar firgita da razana yanayin dasuka taddashi.. Gabadaya tsarin halintarsa ta sauya kallo daya zakayi masa bazaka so sake kallonsa ba fuskarsa kafataninta anannade take da bandeji illa idanuwa da shatin bakinsa kafarta ta dama ta karye saitin gwuiwa tayi rugu rugu haka hannayensa duk biyun sun samu karaya ai bunayya naganinsa ihu ta kurma ta kankame Momy jikinta sai karkarwa yake tana rusarku ta runtse idanuwan ta na mai rokon Momy ta taimaka ta fidda ita daga cikin dakin bazata iya kallon shi ba tsoro takeji haka tai tayi musu magiya amma kamar badasu take sunyi banza da ita rukayya ce takokarta janye can gefe ta zauna da ita tana rarrashinta a daidai wannan lokacin likintan dake kula da Alhassan yashigo suka gaisa da Alhaji fuskarsa na bayyanar da matsananciyar damuwa ” kai ne mahaifin wannan yaron ” likita ya watsowa Alhaji tambaya yana mai kafeshi da ido ya gyada masa kai alamar eh likitin yaci gaba da cewa” a gaskiya yana cikin ma wuyacin hali mai ban tsoro da ban tausayi yanzu halin da ake ciki kashin bayansa ya karye saboda buguwa da ya damu” alhaji cikin shanyewar tashin hankalin da ya tunkaroshi yace” ya ilahi likiti yanzu shin menene abin yi ” likita yayi shiru kamar mai son shirya maganar da zai sanar da Alhaji duk falon yayi shiru kukan bunayya ne kawai ke tashi Alhaji ya dubi inda Alhassan ke kwance cikin rqshin tsammanin kara cigaban rayuwa sannan yani sa yace “ina jinka likita yanzu meye abin yi ?” Yasake tambayarsa nan ma likita yayi shuri alamun yarasa Bakin magana Alhaji ya dubi Momy” tunda abin yakai ga haka kawai a sanar da iyayen alhassan domin su San halin da ake ciki tun wuri wannan ba karamar magana bace da tadace ace a tsaya janjaninta” Momy cikin sanyin jiki tace ” hakan shi yafi dacewa” cikin Sauri alhaji ya zaro wayarsa a ajjihu ya lalubo lambar mahaifin alhassan yakirashi badau lokaci ba aka daga nan yashi sanar dashi abin dake faruwa yana gama sanar dashi bai jira cewarsa ba yakashe wayar yadubi likita Wanda izuwa lokacij fuskatsa ta kara bayyanar da damuwa.
A hargitse suka shigo falon suna masu rarraba idsnuwa musamman inna mero wacce dankwali da zani duk rike a hannu saboda tsabagen kidima Malam ne yayi kokarin yin sallama duk kan mutan dakin sukayi kakorin amsawa cikin muryar sanyi ita kuwa inna mero inda Alhassan ke kwance ta tun kara ta isa ts dubeshi yanayin da taganshi ya sanya ta saurin kau da kai nan da nan idanuwanta su kashig zubda hawaye tana mai cewa”ikon allah da na allah yayi dakai kaddarar da ta afka maka kenan innalillahi wa’inna ilaihir raji’u allah kayi mana da kyau duniya da lahiran mu” ta rushe dakuka tare da dafa Alhassan din kowa na dakin yayi matukar tausaya mata Momy kuwa har da kwalla tashiga daukewa daga fuskarta malam mahaifin Alhassan ya dubi Alhaji dake tsayeshi da likita har zuwa wannan lokaci ” alhaji duk garin yay haka ta afku ” ya tambayi alhaji ya nisa yace” muma a waya akasa sanar damu yayi hatsari nan dai duk a ka sanar dasu yarda abin ya afku sunyi matukar kaduwa musamman jin halin da Dan nasu yake ciki sundau tsawon lokaci suna tattaunawa yarda abin zai kasan CE da halin dake ciki a halin yanzu mai yadace ayi shidai har yanzu likita yaki sanar dasu musabbain abin da ke faruwa Dan yasan tabbas hankalinsu sai ya dada tashi matuka gaya alhji yadubi in da rukayya take zaune” ya kamata ki je gida saboda kar mijin naki yaga Bakin ki” idanuwan ta jajir ta gyadawa alhaji kai ita Sam ta ma manta da wani wai miji domin kuwa taga alamun mazan sai a hankali gani take DUK HALINSU DAYA saboda tana zargin shima ta’addancin da yake aika tawa kenan wani bangare na zuciyar yayi saurin gargadinta’ki kula rukayya ba dukka aka taru a ka zama daya ba ZATO ZUNUBI ko da yaka kasance gaskiya karkiyiwa mijinki mummunan zato ki fuskanci wani Abu kowa da iron zuciyarsa akawai nagari akwai a a kasin haka’ nisawa tayi tana kokarin mikewa bunayya na dubanta da kodandun idanuwan ta “yanzu tafiya zakiyi rukayya” murmushi tayi “to ya zanyi air zan dawo da yardar allah” ta gyada mata kai. al’amarin Alhassan yayi matukar firkita rayuka ba ka Dan ba musamman iyayen sa inna mero kuka take haikam saboda ta YANKE TSAMMANI da samun Alhassan “Allah ya yanke maka wannan wahalar da na Allah ya jibanci lamarinka” furucinta kenan in tayi kuka aka rarrashe ta+
Bunayya da ke can gefen in taji inna mero na wannan zantukan na tausayawa Alhassan sai tayi matukar bata tausayi tabbas da tasan ta’addancin da Dan ta ke aikatawa da tayi gangawar kwashe masa albarka ta roki Allah da yayi saurin dauke masa rai daga cikin duniyar nan domin rage mugun iri
Girgiza kai tayi a daidai lokacin da wasu tawagar hawaye masu zafi suka zubo mata.
Duban hajiyar ta tayi wacce ita ma ta fara zare tsammani da rayuwar Alhassan musamman yanayin da yake ciki na rashin motsi jini na zubowa ta bakin sa Bakin kirin
“Da ma ace Allah ya saukar da muguwar azaba ga wannan mutum da ma ace Allah ya dauwamar dashi cikin tsananin rashin jindadi arayuwarsa da duniyar sa da ma ace ya dauwama cikin wannan wahalar har lahiransa” jin furucin bunayya yayi matukar girgiza mutanan da ke cikin wannan dakin cikin alamu na tuhuma mahaifin Alhassan da inna mero suka Shiga duban bunayya.
Amma ba wannan yayi magana a cikin su
Cikin bacin rai momy tace”kin ji na rantse in har nasake jin zancenki adakin nan wallahi sai na bata miki rai” inna mero da ta kadu dajin zancen bunayya ta dubi Momy” wai shin me ke faruwa ne da alamar akwai wani boyayyen al’amari da kuke boye mana”
Momy tashiga girgiza cikin shanyewar tashin hankali “bakomai wallahi umman Alhassan kawai wani hali yarinyar tun da abin nan ya faru”
Cikin nuna alamun rashin yarda inna mero tace zainab ban yarda ba akwai abin da kuke boye Mani da alamun akwai kamshin gaskiya amaganar yarinyar nan Dan Allah Ku sanar da ni ” momy tayi wata irin ajiyar zuciya cikin tsananin tashin hankali ta dubi mijinta sai taga shima yanayin sa ya canza cikin sanyi murya tace ” alhaji kayi wa yarinyar nan magana da takiyayi kalaman ta…”
A hanzarce inna mero ta tari momy “in ki nayiwa Allah da annabinsa ki bari asanar dani abin da ke faruwa zuciya ta ta fara zargin wani Abu dake faruwa kuke boye mana” ta juyar da kallon ta izuwa ga bunayya ” ke yar nan sanar dani abin da ke faruwa karki boye Mani komai”
Bunayya da tayi zuru da idanuwa tana duban kowa na cikin dakin cikin yanayi na tsoro tace da inna mero “bakomai”
“Ban yarda ba” cewar inna mero tafadi cikin nuna son bunayya ta bayya na mata komai
Tarin da Alhassan ya Shiga yi ne ya katse musu zancen nasu da sauri duk kan su sukayi kan sa lokaci guda yashiga amai naji hade da gudaje bakinkirin nan hankula suka kara tashi da gudu alhaji anas yayi waje yakirawo likita suka Shiga taimaka masa tsayin lokaci sannan suka samu kan sa sai numfarfashi yake kamar Wanda rai ke kokarin fita tsayin mintina biyu yayi dif kamar Wanda rai yafice daga jikin sa
“Bunayya bunayya bunayya” abin da suka ji yashiga ambata kenan cikin wahalalliyar murya
Hakan da sukaji duk sai sukayi ajiyar zuciya bunayya dake can gefe rakumi jikin ta yashiga karkarwa alamun na firgici ya bayyana a gareta jin da tayi Alhassan ita yake ambata
Cikin barin jiki da sanya tsammanin Alhassan zai samu wata rayuwar a duniyar nan inna mero ta mike jiki na rawa ta dubi bunayya “yar nan ta so ta so mijin ki ya farka ke ya ke ambato zoki ji menene me yake so”
Wata irin katagar tashin hankali taji ta rigizo mata a ran ta cewa kawai take ‘an ya inna mero ta San waye Alhassan a zahirin gaskiya tabbas ba ta Sani ba da tasani ba zata goyi baya wajan kai ta inna da za a raba ta da ran ta ba..’
‘Ke bunayya ba da ke ake magana ba ki tashi mana” muryar Momy ta katse mata zancen zucin da take nan ta Shiga zubda hawaye tana Jan jiki kamar mai kokarin zura wa da gudu “nasani kowa na cikin duniyar nan dole ya tsaneni nasan kowa zai so gushewata cikin duniyar nan tabbas nima bana bukatar sake numfasshi ko da na sakan daya ne cikin wannan duniyar da bata da tabbas kaicon rayuwa kaicon bakin hali irin nawa kaicon KWADAYI DA BURI irin nawa kaicon bakar zuciya mai son kawa irin tawa allah yayi gangawar gusar dani daga cikin duniyar nan ban ga amfani rayuwa a cikin ta ba ya takasan ce RANAR NADAMA danayi wacce bata da amfani”
Furucin alhassan kenan da yakokar ta fizgo shi izuwa waje cikin wahalallan yanayi bayan yaga ma kuka da tsanar kan sa
Kowa na dakin jikin sa yayi sanyi matuka gaya kowa binsa yake da kallo cikin mawuyacin yanayi na tsakanin rayuwa da mutuwa sabida kallo daya zakayi masa ka yanke masa tsammani samun rayuwa sai dai iko na rabbil izzati mai rayawa da kashe alaokacin da yaso a sanda yaso
“Ban fuskancin wannannzautantun zancen naka ba anya tabin hankali bai kusance ka ba alhassan”
Cewar inna mero cikin yanayi na tashin hankali da jin furucin Dan nata ta juya ta dubi momy da alhaji anas cikin yanayi na tuhuma “da alamun kuna boye mana wani rikitaccen al’amaari mai cike da tashin hankali yakamata kusanar dani tun kafin tashin hankalin da nashiga ya bugar min da zuciya ta saboda bazan iya daurewa ba…”Dan ki makashin rayuka ne”
A bazata sukaji muryar bunayya na fadin haka cikin dakewar zuciya da shanye kukan da ya tukaro ta+
Ai su momy ji sukayi kamar an turbudasu da ransu cikin kasa cikin tashin hankali momy tace
“bunayya baki da hankali mai yasa kike son wahalar da rayuka ne na gaya miki kar nasake jin furucin ki dan naga alamar izuwa yanzu furucin alheri ya tsere daga cikin harshenki da zuciyarki”
Cikin yanayi na dakiya bunayya ta mike daga zaunen da take tayi taku kamar uku izuwa tsakiyar dakin fuskarta na bayyanar da tsananin tashin hankali mai cike da Bakin ciki hawaye na safah da marwa saman fuskanta
“Izuwa wannan lokaci ya dace ace komai an fallasa shi kowa yasani boye boye ba abin yi bane. ta juya cikin gyatsine fuska tana duban alhassan dake yashe cikin wahalallen yanayi
“Wannan ba abin rufawa asiri bane wannan ba abin taimako bane wannan ba abin a rufawa wani Sirri nasa bane dan haka yanzu lokaci ne na tonon BANKADA ko ban tona masa ba shi zai bankadawa kansa mummunan aiki da yake dan haka ina mai rokon ki Momy da ki bari komai ya wanzu tun a nan duniya kafin can ranar alkiyama”
Ta karashe furucin ta cikin rushewa da kuka ta durkushe a nan
Da Sauri inna mero tayo kanta jikinta na karkarwa cikin tashin hankali tace
“in kinayiwa allah sanar dani abin da ake boye min da alama ranar bankada ce tazo kamar yarda kika fadi to ina so ki bankade min komai da kika sani wallahi na daukar miki alkawarin yi miki komai Wanda kike bukata in har ina da halin yi miki”
Bunayya ta dago kan ta cikin jam hanci tace “kin dauki alkawarin.yi mini komai da nake bukata in har nasanar dake sirrin da ake boye miki”
Inna mero ta gyada mata kai alamar tabbatuwar hakan
Bunayya tayi murmushi mai cike da tarin takaici da bakin ciki
” nasani in har nasanar dake abin dake faruwa sai kinyi tur da wannan dan naki sai kin yi allah wadai da haihuwarsa da kikayi sai kin ji dama ace barin sa ki kayi da kin san annoba zaki haifawa al’umman duniyar nan nasani wannan ranar sai ta kasace miki ta Bakin ciki da takaici RANAR NADAMA wacce baki taba mantawa da itaba a rayuawarki…”
Cikin gajiya da jin furucin bunayya inna mero ta katse ta
“duk ki ajiye wannan zantukan gefe sanar dani asalin komai dake faruwa dan wannan zantukan naki ba fuskantarsu nake ba sanar dani gundarin abin dake faruwa da Alhassan din Wanda zaisa naji tsanar haihuwarsa da nayi ko da dai…”
Sai kuma ta cinye sauran kalaman ta bayan ta nisa tace “ina sauraron ki”
Bunayya ta juya ta dubi iyayenta da sukayi zuru suna dubanta cikin yanayi na rashin jin dadi da kwanciyar hankali ji tayi gabadaya komai ya kwance mata ji take kokarin da take na fallasa komai nakokarin guje mata ta nisa tace “Dan ki kin haife shi kin tarbiyantar dashi da ya girma ki ka aurar dashi gareni saboda ya isa ayi masa auren kin nuna masa gata na kin kara wa ko ba haka ba ?”
Inna mero ta gyada kai alamun haka akayi
Bunayya ta cigaba da cewa
“Duk wannan kyautatawar da kikayi masa bai haka gurbata rayuwarsa da duniyarsa bai hana halaka da zuciyarsa wajan nakasta kansa ba KAWAR ZUCIYA da son abin duniya yasanya shi jefa kansa cikin matacciyar rayuwa wacce ta kai shi tabaro”
Bunayya ta nisa tana mai zubda hawaye tasake taku kamar uku cikin tsakar dakin ta juyo ta dubi alhassan ta nuna wa inna mero
“Wannan shi yayi maki bakin cikin samun jikoki da kike muradin samu daga wajan danki wannan shine yakashe min ‘ya’yana har guda biyar yanzu haka rai na shida ake Neman ran sa a takaice inna mero alhassan din ki Dan ki na cikin ki dan kungiyar asirine mashayan jinin mutane..”
Inna mero dake tsaye lokaci guda sai gata baje a tsakar daki hannunuta aka jikinnta sai bari yake ji tayi duniyar na juya mata wata katagar tashin hankali mai kunshe da bakin cikin jin furucin bunayya ita ta ruguzo mata cikin yanke tsammani da kara numfashi a duniya tashiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihij raji’u”
Cikin tashin hankali ta nema kuka don tayi amma ina kuka ya zura da gudu dan shima bai ga wajan zama ba nan dai ta shiga shassheka cikin yanke wa kai jin dadi ta dubi alhassan dake kwance ta dubi bunayya ta juya ta dubi momy alhaji anas mahaifin alhassan Wanda a daidai wannan lokaci gumi ne kawai ke keto masa na tashin hankali
Ta mai da kallon ta ga Alhassan Wanda izuwa wannan lokaci abin sai Wanda ya gani Dan gabakidaya yafice daga haiyacinsa numfashi ma sama sama yake yinsa
“Ta’addacin da fashi da makamin da ka sayo wa rayuwarka kenan cikin duniyarka”
Ta nisa alokacin wasu wahalallun hawaye suka zubo mata
“Nikuma irin tawa jarabawa da KADDARAR RAYUWA da ta sameni kenan alhassan bakayi wa rayuwarka ta najin zuwa lahira da abin kwarai ba ka nakasta rayuwarka ka gurbatata ka illa tata ban ta ba ganin mutun mai MATACCIYAR ZUCIYA irinka ba ban taba ganin watsattsen da irin ka ba haba da gaskiyar bunayya da take cewa in tasanar dani mugun aikin da ka sayo wa rayuwarka saina tsaneka nayi Allah wadai dakai nidai har ga Allah nasani ban gurbata maka rayuwa tarbiyya kula da kai nayi daidai gwargwado Allah ya gani amma sabida tsabar nemawa rayuwa jafa’i shine ka kinkimowa kanka abin da na sani da illaha rayuwa kai ya kaiya…”..
Story continues below

Wani wahalallan kuka ya kurce mata ta shiga yi. Duk dakin yayi tsit kukan inna mero ne sautin sa ke tashi kowa ya zuba mata idanuwa cikin tausayamata sai da tayi kukan ta ma ishi sannan ta sa habar zaninta ta goge fuskar cikin yanayi na kunar rai da takaici ta miki ko kallon inda Alhassan yake ba tayi Wanda adai wannan lokaci numfashinsa ya fara sarkewa
bayan ta bi su momy da kallo ta girgiza kai ta dubi mijin nata
“Malam tashi mu tafi zaman mu anan ba amfani gareshi ba kawai bata lokaci da dasawa rai ciwo mai tsanani Dan nasan tsbbas nacigaba da zama zuciya bugawa za tayi”
Ta fadi tana mai dauke hawayen da suka gangaro mata
Jiki a sanyaye alhaji Ana’s ya dubi momy muryarsa a sanyaye ya nisa “sam haka bai ka mace ki ba inna mero bai dace ki juyawa danki baya ba ko a cikin wani hali yake kisani kece sanadiyar zuwan duniyasa ke ce komai yafaru dashi bai kamata ki guje masa ba addu’a ya kamace ki yi masa domin samun shiriya amma in kikace kin yi fishi dashi wata halakar zai fada Dan haka ki sawa zuciyarki salama ki rungumi kaddara ko ta wani hali ta zo miki mai kyau ko akasin haka duk wannan abin dakike ganin ya faru jarabbata ce daga allah imanin bawansa ya ke gwadawa shin in ya jarebeshi da abu zai iya dauka ko a,a Dan haka yi kokari domin samun dacewa daga rabbil azzati”
Yani sa bayan ya gama kora mata bayani shiru tayi na Dan wani lokaci gabadaya taji jikinta yayi matukar yin sa hawaye yashiga kwararo mata ta na duban Alhassan duk sai taji tausayin Dan nata ya dalsu a zuciyarta (tsakanin uwa da d’a sai allah)
Nan ta koma ta zauna tayi shiru
Momy ta dubeta cikin sanyin jiki “kiyi hakuri komai na duniya mukaddari ne daga allah sai dai wani lokacin muma yan Adam da namu laifin sawa zuciya son abin duniya kwadayi da buri shi ke kai mu ga mahalaka Dan haka kiyi ma sa afuwa da addu’a domin samun shiriya”
Kada kai tashiga yi hawaye na zuba
Malam dake can zaune har yanzu yarasa Bakin magana Bakin ciki takaici da tarin haushi sune suka cika masa ciki har izuwa wannan lokaci ya rasa bakin magana…
Alhaji Ana’s ya dubeshi a sanyaye “ya kamata ace kace wani Abu Malam shiru bana ka bane akan wannan lamarin hakuri zakayi Dan komai ya rigaya ya faru sai dai akiyaye gaba”
Malam.yayi wata irin ajiyar zuciyamai karfi idanuwansa sun kada sunyi jajir ya dubi alhaji Ana’s” allah shi kyauta” abin da ya iya fadi kenan
A daidai lokacin Alhassan yayi wani irin yin kuri Wanda yasanya har gadon dayake sai da ya girgiza ya kyalayo amai na jini mai gudaje gudeja yarda kasan ma yanka dif kamar daukewar wuta gabadaya sukayi kan sa saboda yanayin da suka ga ya shiga na alamun rai yayi halin sa nan da nan inna mero tashi firgici da tashin hankali tana ambaton innalillahi wa inna ilai hir raji’un alhaji anas shine yafara isa kan Alhassan cikin yanayi na sanyin jiki ya sanya hannunsa I zuwa kirjin sa ba alamun motsi da sauri ya juya ba tare da ya tankawa kowa yafice daga dakin ofishin likita ya nufa ” likita da alamun rai yayi halin sa” alhaji Ana’s yafadi bayan I sa cikin ofishin da Sauri likita ya dago kan shi dake sun kuye yashiga duban shi cikin yanayi na jajan ta sannan ya nisa “mu je ” abin da yace kenan ya mike suka fice suna isa dakin suka tadda su carko carko in ka zare bunayya dake rakube jikin bango sai ajiyar zuciya take alamun taci kuka har ta godewa Allah likita yayi kan Alhassan cikin azama yana mai dubashi tsayin mintina biyu sannan ya sarara ya dubi alhaji anas yana mai ajiyar numfashi yasanya hankicif din dake hannunsa ya share gumin da yakaryo masa sannan ya nisa “alhaji da sauaran sa dogon suma yayi saboda wannan jinin da ya xuba a jikin sa amma bakomai zai farfado kuma yana bukatar jini ajikinsa matuka dalili kuwa jininsa yayi kasa sosai” yana zuwa nan azancen sa ya sa kai yafice daga cikin dakin cikin yanayi na yanke tsammanin wannnan al”‘amarin mai rikitarwa tsawon lokaci dakin yadauka cikin shiru ba Wanda yayi kokarin tsinkawa ajiyar zuciya ne kawai ke takai kawo kamar daga sama dakin yadau kuwwar muryar bunayya in da take cewa “shifa wannan da kuke jiran tsammani akan sa ba tashi zai yi lokacin sa kawai yake jira dama kun cire wannan IGIYAR ZATO da wannan likitan ya sargafa muku dan Allah shima kan sa ya sani wannan” ta nuna Alhassan sannan ta cigaba da cewa ” tamkar gawa da rai yake kallon wani mai rai kuke masa nikuma wallahi kallon matacce nake masa dan na tabbata in har ba wani iko na Allah da kyar yakara minti talatin a cikin doron duniyar nan da numfashi” hawaye suka zubo mata a fuska masu matukar radadi da zafi cikin nuna jarumta ta dubi momy da ta kafe ta da idanuwa cikin tsananin mamaki da jin furucin bunayya ta fara zaton kila ta fara zare wane dan tasan tabbas ba wani mai hankali da nutsuwa da zai ta furta irin wannan kalaman zafafa kan miji…maganar da bunayya tayi ya katse mata tunanin da ta fada “momy ki tashi mu koma gida wannan jiran tsammanin warabbuka da muke ya isa haka…ba fa komai zai amfanemu dashi ko da ya farka dan na tabbata wata guguwar cuta zai kinkimo ya jeho mana cikin rayuwa dan duk sambatun da naji yanayi na yayi NADAMA ba yarda dasu zanyi ba dan haka nikam ba zan tsaya a mahalaka ba momy ku tashi mu tafi…” Wani ihu da ya amsa amo cikin dakin ne ya katse ma bunaya maganar ta Alhassan ne ya farka yana ihu cikin yanayi na firgici da razana yana sakin sambatu marasa kan gado da makama da gudu su alhaji sukayi kansa suna rinrike shi. fizge-fizge ya shiga yayi da juyi gadon da yake kai sai girgiza yake saboda karfin jinjiga da yake nan suka shiga Neman ma sa sauki wajan Allah suna tayi masa addu’o’a gabadaya yanayin sa yasauya ya koma abin tausayi da sawa mai kallon sa karayar zuciya inna mero momy gabadayan su kuka suka saka saboda tsabar tashin hankalin dasu gani karara dan Adam ba abakin komai yake wajan allah shi yasa ake so kullum mutum yakasance cikin bauta da rokon allah yayi wa dangin rai dakyau momy ke wannan tunani
Kusan mintina goma suka shafe a haka har likita ya aka kuma kira shima ganin da yayi wa alhassan a wannan lokacin yayi matukar tausaya masa ba kadan ba da kyar da taimakon du’a’in da su alhaji sukeyi Allah yataimaka jinjigar da yake ta lafa sai numfashi da yake fiddo wa a hankali idanuwansa sun canza launi sun koma jajir har da wani kore kore sukeyi abin ban tausayi da sanya kuka matuka
Bayan kowa ya zaunane likita ya dubi mahaifin alhassan da alhaji anas yace “ina ganin mai zai hana agwada na gargaji da taimakon addu’o’a domin wannan abin nasa ba na asibiti bane” alhaji ya gyada kai sannan yace”nima tunanin da nake kenan”
Kowa dai yayi na’am da wannan shawarar na agwada na gargajiya
Cikin wannan yanayin Alhassan ya fara dawowa hai yacin sa yashiga kokarin yin magana amma ya gagara sai nuni yake da hannu da sauri momy da inna mero sukayi wajan sa har rige rige sukeyi bayan sun isa wajan sa can kasar murya sukaji ya Shiga ambaton sunan bunayya dukkan su suka dubi juna sannan momy ta dubi alhaji cikin murya mai taushi tace “alhaji waccen wofin yarinyar fa yake kira” ta fadi tana nuna bunayya wacce a wannan lokacin ta gama tsurewa jikin ta kyarma kawai yake idanuwan ta duk sunyi zuru zuru cikin yanayi da tausayi alhaji ya kai duban sa ga bunayya ya girgiza kai sannan
Yace “ta so ki zo kin ji ‘ya ba abin da zai faru dake ki kaddara wannan abin dake faruwa jarrabi ne daga allah ya jarrabe mu dashi kin ji ki cire tsoro da shakka a zuciyarki ki kaddara komai ya samu bawa daga allah daure ki ta so ki zo wajan mijinki”
Ya karashe cikin sanyin murya mai cike da rarrashi hakan da bunayya tagani tashi ga girgiza kai hawaye na kwarai ya sabar fuskar ta cikin rawar murya mai son rushe wa da kuka
Tace “dady…” Da sauri ya daga mata hannu alamar tayi shiru yayi mata nuni da ta taso ta zo
Ba yarda ta iya haka ta kokarta ta mike cikin nuna jarumtaka zuci ta mike ta fara Jan kafa ta doshi wajan abban ta momy da ke kallon ta duk sai taji ‘yar ta ta taba ta tausayi matuka yanayin da ta ga ta koma cikin kankanin lokaci kamar wacce ta tashi daga cuta too dama ya lafiyar kura balle ace tayi gudawa.
Ta na isa kusa da abban ta ya rike mata hannun gagam suka isa wajan Alhassan kallo daya tayi masa ta kau da kai dan wani irin yanayi na tausayi ta ji ya tsikari zuciyar ta yanayin da taga kamannin sa ya sauya kamar ba Alhassan din ta ba dan gayu da son tsabta Sam baya son kazamin mutum ta nisa wasu guntayan hawaye suka zubo mata aran ta tace ‘ba ka muradin Kazanta amma zuciyarka na dauke da KAZAMIN BURI Wanda ya kai ka mahalaka…’
Amm ba tar sunan ta da taji anyi ya dawo da ita daga guntun tunanin da tashi ga alhassan ya kokarta cikin wahalalliyar murya ya ambace ta yana mai ya fito ta da hannu da ta iso gareshi.
Gaban ta taji ya buga ta juya ta dubi abban ta ya gyada mata kai alamar ta je tai saurin kallon momy amma ita ta kau da kai
Cikin yanayi na yanke tsammanin abin da zai faru ta isa ga Alhassan ta dan rangwafa sannan ta kokarta cikin muryar tausayi tace “sannu”
Kai kawai ya gyada mata sannan ya fara kokarin magana murya kasa kasa ba sosai ma take jiyo shi ba
“Ki yafe na San nayi matukar zaluntarki na cuci rayuwarki da duniyarki na ci amanarki na ha’ince ki duk akan wani ban zan kudiri na wa maras amfani a gareni zuciya ta debeni na aikata abin da na jayowa zuri’a ta da dangina abin allah wadai da tur na cuci kai na da iyaye na na cuce ki ke matata wacce ki ka bani yarda da duk amanarki na boye miki mugun hali na na zo miki da fuskar salihan ci kaico na kaico na da wannan rayuwa da na sayo wa kai na yanzu da wacce irin fuska zan kai leku da mahalicci na na San na aikata babban laifi wanda da wuya na samu yafi a gareku da ubangijina…” cikin wani irin hali ya fara tari mai dauke da jini ganin haka da bunayya tayi ya Sanya fidda idanuwa waje cikin tashin hankali ta ambaci sunan ‘Abba’ ganin da sukayi ta tsora ta ya sanya dady saurin rike ya mai ce mata “ki natsu ba abin da zai faru dake daure ki sauri mijin ki kiji abin da zai sanar dake..” Da sauri ta dubi dady tace ” abba dubi kagani aman jjni yake don allah a kira likita kar jinin sa ya kare mutuwa zai yi Abba”
Yace ” to yi shiru bari akira shi ya duba shi amma ki natsu bana so naga kina tayar da hankalin ki”
Nan dai alhaji yashiga rarrashinta da ban baki har tayi shiru sai ajiyar zuciya take ta juya ta dubi Alhassan Wanda a wannan lokacin tarin nasa ya lafa ya sake ya fitota cikin sanyi jiki ta isa gareshi nan ya cigaba da cewa “buruka da kudire kudire na daukar wa rayuwa amma duk ciki ba na abin yabo sai yanzu nake nadamar abin da nake aika tawa duk abin da ya faru wallahi ba a son rai na bane ba yarda zanyi an sanya min takunku Wanda yake zabi ya rage gareni mutuwa ko rayuwa jindadi..’Da sauri bunayya ta katse shi
“nifa ban fahimci abin da kake cewa ba ban San ina ka do sa ba”
Ta fadi cikin yanayi na rawar baki
Wata irin ajiyar zuciya yayi wacce sai da ta sanya shi kamar mai yin kurin yin amai haka da bunayya tagani ya sanya ta ta ja jikin ta gefe ta mai kallon shi fuskar ta cike da damuwa.
“Ba da son rai na na jefa kai na cikin wannan hali ba zuciya ce ta debe ni…”
“Kai kuma sai ka biye mata ko”
Muryar inna mero suka tsinkaya ta na fadin haka cikin yanayi ns damuwa
Momy ta dubi inna mero “don allah kiyi shiru inna mero duk abin bai kai ga haka ba”
Cikin yanayi na tsukewar fuska inna mero tace “haba me amfanin saka kai cikin halaka da hankslin mutum da tsuwar sa yabi wa son zuciya kaicon irin wannan hali na bakar zuciya irin taka Alhassan haba don allah ai wannan CUTAR KAI ne”
Tunda ta fara magana ba Wanda ya katse har takai aya wata uwar harara ta wurga wa Alhassan tare da Jan guntun tsaki
Bunayya dake tsaye ta dubeshi ido cikin ido tace” yanzu meye riba a cikin wannan matacciyar rayuwa da kayi menene abin yabo a ciki kawai dai ka kashe rayu ka dan ba rayuwar ka kadai ka kashe ba har da tawa da ma dangi baki daya dan na tabbata duk Wanda yaji irin abin da ka aikata duk masu Kaunarka sai sunyi allah wadai da kai har da ni kuma aciki” ta kareshe maganar cikin yanayi na son fashewa da kuka
A razane ya dubeta Bakin sa na karkarwa “Kin tsaneni bunayya ke ma ki na cikin wadanda suka juya min ba ya haba bunayya kar kiyi min haka…tabbas nasan nayi wa rayuwarki illa na cancanci ki yi min komai domin daukar fansa amma ki sani duk abin da na aika ta ba a son rai na bane sharrin zuciya ce mai tarwatsa rayuwar dan-adam Wanda ya ki yaki da zuciyarsa domin zam to wa hanya ma daidai ciya nasan nayi wa rayuwa illa matuka na cuci kai na na cuci rayuwa amma don allah bunayya ki yafe ni nayi NADAMA har zuciya ta”
Ya karashe maganar sa cikin yanayi na son rushe wa da kuka gabadaya dakin yayi tsit duk tausayin Alhassan ya dasu a zuciyoyinnsu
Haka su ka cigaba da zama har zuwa tsayin lokaci ba Wanda yasake tsinka wa sai alhaji anas da mahaifin Alhassan da suka koma gefe su magana kan wannan rikitaccen al”‘amarin..
*** **** ***
Tun da rukayya ta fice daga cikin asibitin cikin sanyi jiki zuciyar ta a cunkushe da al’amarin da ya caza mata kwanya haka ta Shiga motar ta ta fice daga cikin asibitin ran ta a jagule
Gida ta dosa ta na isa tayi wa mai gadi horn da gudu ya zo ya bude mata get din ta doshi cikin gidan da motar ta
Mai gadi na daga mata hannu amma ba ta bi ta kanshi hankalinta gabadaya yayi kan motocin da tagani zube a tsakar gidan nan ta fara tambayar kan ta da me ke faruwa kuma su wanene suka zo kodai Baki tayi haka taii tayi wa kan ta tambayoyi har ta samu gurin da tayi parking ta fito ta karewa motocin kallo gaban ta taji ya bada rasss alamu firgi ta da tsoro suka bayyana a fuskarta cikin azama ta doshi cikin falon gidan nan ma takalma tagani reras Bakin kofa nan gaban yasake faduwa tashi tambayar kan ta da meke faruwa mai ya kawo su dady gidan ta minti na biyu ta shafe tsaye a wajan sannan ta kokar ta Jan jiki ta doshi cikin falon Bakin ta dauke da sallama cikin yanayi na sanyi jiki.
Ba Wanda ya amsa sallamar illa idanuwa da taga kowa na falon ya zubo mata nan taji kafafuwan ta sun dau rawa musamman ganin da tayi wa fuskokin kowanne ba alamun fara’a. A sanyaye ta karasa cikin tsakiyar falon tana rarraba ido yarda kasan maras gaskiya cikin zukewar rashin Ku zari ta fara kokarin zama tare da Watso musu gaisuwar cikin ladabi+
Wani irin kallo ta ga momy tayi mata
Sannan tace “ina wayarki take?”
Ji kake kulululu.. Cikin rukayya ya juya har sai da ta ya mutse fuskan cikin yanayi na fargaba ta kure momy da kallo
Cikin haushi ta daka mata tsawa ” wai ba cewa nayi ki bani wayarki ba ko sai kin gama ganina tun da yau kika fara arbani San nan zaki bani”
A razane hannu na karkarwa ta banbaro jakar ta dake rataye aka fadarta ta zuge zip din nan ta zaro wayar ta mike mata cikin tsoro kamar wacce za a fizgo a kirba
Ba tare da momy tace mata komai ta kunna wayar haske ya bayyana a kan fuskar ta sannan ta Sanya hannu ta lanlatsewa kamar mai binciken wani Abu sakanni kadan ta juya ta dubi
Dady dake zaune shima fuskarsa a cinkushe ta mika masa wayar ba tare ya amsa ya Shiga kallon abin da take nuna masa nan da nan fuskarsa ta kara shan kunu a zafafe ya kai kallon sa ga rukayya wacce a wannan lokaci gabadaya ta gama yanke tsamman kan akwai abin da yake shirin faruwa babban kuma akan ita ta aikata laifi
Story continues below

“daga ina kika fito tun yaushe kika bar gidan nan?”
Furucin da dady ya tare ta dashi kenan Wanda yakara har gitse mata kwanya tashiga zargin kan ta da TUHUMA anya ba wani Abu bane yafaru nan zuciyar ta tuno mata da sabeer cikin azama tashiga karade falon da kallo ko zata gan shi ba shi ba dalilin sa nan gaban ta yakara tsinkewa anya bawa ta makarkashiyar ya shirya mata ba in ta tuna yar suka rabu lokacin da zata fita tabbas GADAR ZARE sabeer ya shirma ta kuma ta zurma ya hada ta da iyayen ta to laifin me tayi masa da har zai mata haka saboda tsabar bankada har da iyayen sa ya gayyato su na yi mata kallon hadarin kaji tabbas sabeer ya cika maras imani duk abin da yayi mata a baya bai isheshi ba sai ya sake kulla mata wani makircin duk abin da yake mata ba ta taba kai karar sa ba amma shi da yake butulu ne shi shine zai hada ta da iyaye tabbas yaci ka butulu maras tausayi kai namiji ma ya tabbata ba dan goyo bane namiji hankaka cikin baki bayan ka fari…
“Dake fa ake magana amma kin ba banza ajiyarmu” momy ta fadi cikin zafin rai Wanda yayi ssnadiyar katse mata tunaninnta
Da sauri ta dago kai ta dubi momy wacce fuskar ta a murtuke ba alamun wasa gareta ta kokarta cikin cinye magana tace “_gidan bunayya naje…”
“Ga kanwar uwarki ko”
Cewar dady ya tare ta cikin zafin rai shi ma
Nan rukayya ta kara shiga rudu tabbas ba karamin Abu bane ake tuhumar ta akai shin abin tambaya menene suka bincika cikin wayarta me su kagani kodai wani makircin na sabeer ne ya kulla mata tabbas ko me nene to ba karami bane
Cikin dakewar zuciya ta dubi momy
“Momy bunayya ce bata da lafiya shine naje to cikin kazamin yanayin da nasa meta ne ya cinye min lokaci har ban samu dawowa da wuri ba”
Momy ta dubeta asheke “wato bunayya ta fi mu a wajan ki ko mijinki shima bunayya ta fashi a wajan ki koh”
Wani irin kallo mai cike da tsoro rukayya tayi wa mahaifiyar ta tana mai girgiza kai
“Eh mana tafi a wajan ki ga zahiri kin nuna mana ba a Bakin komai muke a wajanki ba kin mai da mu banza duba kigani wani mai sanin darajar iyaye ne zai musu haka”
Ta turo mata wayar ta tana mai cilla mata harara rukayya cikin rawar jiki ta sanya hannunta na karkarwa ta amshi wayar idanuwan ta na akan iyayen ta
“Ba mu zaki kalla ba kin ji ko”
Dady ya fadi cikin tsawa da har zuka
Yanayin da yayi maganar ya girgiza rukayya har yasanya sakin wayar ta fadi kasa ba shi ta kai wa wayar raruma
Ta dire idanuwan ta akan fuskar wayar me za tagani habawa ai sai cikin ta yashiga kadawa ganin abin da tagani ta fara rawar murya ta son yin magana amma ina tagagara sai ta kafe wayar da ido kawai ta na kara dubawa tana mai kokonto akan abin da tagani anya ba mafarki take in kuwa da gaske ne taga ta kan ta ta shiga uku ‘Dady 30misscall-momyna60misscall sabeer 25misscall’
Haka tai ta na na ta abin da tagani cikin rawar murya mai son fashewa da kuka ta dago kan ta idanuwanta sun kada sunyi jajir tabbas ta San ba tayi musu adalci amma kuma ai ba ta San haka ya faruwa ba da gangan tayi musu haka ya kamata suyi mata UZURI ko dayake dole su ji zafi musamman in tayi lakari da irin kirar da sukayi mata amma bata dauka ba kuma wayarta a kunne tana hannunta amma ai bata San anyi kira ba saboda rudanin da tashiga
‘Yanzu mai yadace tayi’ ta shiga tambayar kan ta haka dai tai ta tunaninnika cikin yan sakan ni nan ta yanke hukunci kawai ta shiga basu hakuri ta nuna musu ba ta san sun yi mata kiran ba ga halin da take ciki a lokacin nan ta numfasa tare da Jan hanci idanuwan ta sun kada sunyi ja tabbas ita kan ta ba ta ji dadin hakan da ta faru ba.
“_momy don allah kuyi hakuri wallahi ba da gangan nayi haka ba lokacin hankali na ga badaya a tashe yake kuma wayar ta jaka duk na rude ban San kunyi kira ba kuyi min AFUWA…”
Cikin tsawa momy ta tare ta
“Dahalla malama rufe mana baki maras kunya ke har kina da Bakin magana to bari kiji in gaya miki duk abin da kike muna sane duk irin CIn kashin da rashin kyautatawa da kikewa mijinki duk mu Nada masani ya kuma kin kyauta kin cika ‘ya”
Ai rukayya ba ta San lokacin da ta zabura ba wata katangar tashin hankali ta ji ta ruguzo mata tashiga sallallami idanuwa warwaje ‘shikenan ta faru takaare’ ta fadi a zuciyarta dan ta San tabbas ta kade har ganyen ta tun da dady yaji abin da tayi to sunan sorry cikin rawar baki ta tara kukarin yin magana.
Ai bata kai ga furta abin da zata ce ba taji saukar mari Wanda yasanya har taurari sai da ta hango sunayi mata lale marhabin
“In kika sake ki furta wata kalma a nan wajan sai na karkaryaki maras mutunci yanzu ke ko kunya bakiji mijin ki marufin sirrin ki ke zargi zargi fa saboda ke baki da hankali na dauka komai na duniyar nan in kika ga yafaru mai dadi da rashin sa duk daga ikon allah” bunayya tai matukar jin Marin da mahaifinta yayi mata hannu biyu ta sa ta dafe kuncin ta idanuwan ta suka shiga zubda hawaye cikin tsananin tashin hankali tashiga duban iyayen na tana mai tambayar kan sirrin mijinta da akace ta fallasa shin menene laifin ta dan ta nuna bacin ranta akan abin da yayi mata shikenan ita ba ta da iko ko ‘yancin da zata kwatarwa kan ta to gaskiya da sake dole ta San matakin da zata dauka akan sabeer don taga abin nasa ba na karewa bane cutar ta kawai zai dunga yi yana gama ta da iyayenta suna ci mata mutunci akan abin da ba ita bace da laifi.
Girgiza kai tashiga yi bakin ciki hade da takaici suka cika mata zuciya ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mace
“Da yake bakin San darajar mijinki ba shine har kin samu iko da dama in zaki fita bashi da ikon hanaki saboda gaki ishasshiya ko” momy ta fadi cikin bacin rai mai tsanani
Bunayya dai rasa Bakin magana tayi gani take gabadaya angama cutar mata da rayuwa.
“Ina shi sabeer din yake?”dady ya dube ta tare da fadin haka
Cikin mamaki tashiga duban mahaifin nata dan ba ta San amsar da zata bashi ita dai ta San gida ta barshi to ina dalilin tambayarta in da yake.
“Da ke fa ake kin yi wa mutane shiru”.
Momy ta tare ta a zafafe.
“Ya kamata Ku sassauta ma ta haka don allah da me za taji ne duk kun hadu mata aka”.
Mahaifin sabeer ya fadi haka da bashi da niyar yin magana amma ganin da yayi suna kokarin firgita mata kwanya ya sanya shi tsinkawa.
Mahaifin bunayya yace “_alhaji wannan maras mutumcin bai kamata a rangwanta mata ba tun da ita ma ba ta San rangwami ba a rayuwarta”
“Duk da haka Ku bi ta a sannu duk wannan hargagin da kuke bashi zai kai Ku ga ci ba bai kamata ace kun tattauro laifin gabadaya kun daura mata shi ma sabeer din zai iya kasantuwa da nashi laifin aciki dan yayan yanzu ba shedarsu ake ba”
Duk sai suka yi shiru jin furucin mahaifin sabeer din
Alhaji ya dubi bunayya
” ina kika baro shi sabeer din?”
Cikin murya mai ciki da rashin jarumta bunayya ta dubi mahaifinta “Ban San ina yake ba hasali ma lokacin da zan fita a gida na bar sa”
Momy ta dubeta
“Kina nufin kice baki gan sa ba Baku hadu dashi ba?”
Rukayya ta girgiza kai alamun a’a
Momy ta gyada kai sannan tace
“_to ai bin ki yayi can inda kika je ya taho dake saboda kiran ki da ake tayi baki daga waya ba kusan mun shafe awa hudu a gidan nan Muna jiran ki ganin da mukayi shiru shine ya tafi can gidan bunayya din ya taho dake”
Rukayya tace “_nidai ban gan sa zai iya yuwa lokacin da mukaje baya gidan dan da naje nasame ta cikin mawuyacin hali kawai ssibiti muka nufa ba tare da nazauna ba kuma bayan an sallamemu ne wani tashin hankalin yasake kunno kai mijinta yasamu hatsari to shine mukaje aka dauko shi zuwa asibiti yanzu haka yana can an kwantar dashi”
Zantukan rukayya yayi matukar sanyayamusu jiki jin abin da yafaru
Momy da alhaji sukayi ajiyar numfashi
Mahaifin sabeer yace “allah shi kyauta ya kare gaba yanzu abin da za ayi Ku kira sabeer din Ku sanar dashi dawowar ta”
Haka kuwa akayi alhaji yashiga kokarin kiransa
Sai ga sallamarsa gabadaya suka amsa masa yanayin da yashigo falon duk jikin sa a mace ya samu guri ya zauna hade da dafe kai
Duk sai suka zuba masa ido cikin alamun son abin da yake dawainiya da zuciyarsa
Alhaji ya kokarta tambayarsa
Shiru yayi tare da ajiyar zuciya ya dubi rukayya da ke zaune can gefe duk ta wani hargitse da alamun kuka matayi
“Mijin bunayya fa ya rasu bayan fitowarki asibiti” sabeer ya fadi
Wani irin zillo rukayya tayi hade da dafe kirji idanuwa warwaje “ya rasu fa kace”
Ya gyada mata kai alamar eh
Ya dora dacewa “_bayan barin ki asibiti da ji mawa na isa bayan naje gidan bunayya ban sameki ba nan mai gadi yake sanar dani abin da ke faruwa ban yi kasa a gwuiwa ba na nufi asibiti da kuka je maganar gaskiya nayi matukar girgiza da halin da na tsinci Alhassan aciki har hawaye sai da na zubda masa saboda irin azabar wahala da naga ya na cikin ta”
Ya tsagai ta da magana tare da tsane gumin da ya tsantsafo masa ya dubi Rukayya cikin nuna alamun bacin rai
“Abin Bakin ciki abin tur!!abin ai allah wadai rukayya Ashe Alhassan dan kunyar asiri ne ba tare kowa na da masaniya ba…”
Ai ba bunayya ilahirin duk dangin rai dake cikin falon sai da katangar tashin hankali ta zubo musu gabadayan su suka shiga sallallami
Ita kuw ido ta zurawa sabeer tashi tariyo abin da yafaru acan bays Ashe dagaske ne maganar bunayya ba karya tayi ba mijinta dan kungiyar asiri ne kai innalillahi wa’ainna ilaihi raji’un abin da tashiga fadi kenan azuciyar cikin tashin hankali tausayin bunayya ya lullube ta ba ta San lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba ta dubi sabeer cikin matsanancin tashin hankali tace
“sabeer tabbas alhassan ya juye iyayen bunayya da ita kan ta ta bai bai saboda irin fuskar salihan ci Da yazo musu da ita..Ashe kwallon dan ta’adda ne abin takaicin Ashe sau biyar ta na damun ciki yana lashe wa yanzu haka ciki nashida ne a jikin ta yake Neman daukewa allah yayi nashi ikon”
Momy tace “amma dai Alhassan bai yi wa kansa adalci a rayuwa ba me kenan yayi kan shi ya cuta da dangin sa domin kuwa duk Wanda yaji wannan lamarin sai yayi allah wadai dashi amma bakomai yayi wakan sa allah ba azalumin ba wan sa bane…allah ya jikan sa”
Nan dai suka Shiga jaje na tashin hankali gabadaya abin da ya tarasu awajan sun manta dashi lamarin Alhassan ne kawai ke caza mu kwanya kowa sai fadin albarkacin Bakin sa yake
Rukayya iyakar matsuwa ta masu dan tako sa ta je ta tadda bunayya domin kuwa ji take kamar ita kayi wa wannan kashin rayuwar sai dai ba yarda ta iya haka ta yi shiru tare da hada tagumi duk sai taji duniyar ta fice mata arai ganin lamarin take kamar a mafarki kamar ba gaskeKusan awa guda suka shafe a haka cikin yanayi narashin dadi can alhaji ya kokarta ya dubi sabeer yace
“Yanzu haka suna ina”
“Ai sai da aka kammala komai sannan na taho yanzu haka gawar na gidan iyayen sa can DORAYI acan za ayi jana’izarsa”
Alhaji ya gyada kai yace “shikenan yanzu abin da yadace Ku tashi?” gabadayan su suka tashi jiki a sake in kazare rukayya Wanda tayi matukar matsuwa da taganta tare da bunayya domin zuciyar ta har yanzu ba ta gasgata abin da sabeer ya sanar da ita ba tana SHAKKA akai cikin wannan tunane tunane suka shiga mota guda duk kan su sabeer ke tuka su shima cikin yanayi na sanyin jiki
Cikin kankanin lokaci suka isa dorayi har kofar gidan su Alhassan yakai su yana kokarin yin parking al’umma na kokarin daukar gawar Alhassan domin kai shi gidan sa na gaskiya
Ganin haka da su alhaji su kayi
Alhaji ya dubi sabeer “kace mun zo adaidai yanzu abin da za ayi Ku su hajiya Ku shiga ciki bari mu Mara musu baya”
Haka kuwa akayi sabeer yayi parking su rukayya su ka fito su shiga cikin gidan su kuma nan sukayi alwala su ka bi bayan su zuwa makabarta.
Shigar su rukayya gidan yayi daidai da fitowar bunayya daga bayi hannunta rike da buta cikin yanayi na rashin dadi tayi musu sannu da zuwa kallo daya za kayi mata ta raunana maka zuciya saboda gabadaya ta zama abin tausayi ta kode ta jeme a lokaci da kamar wacce ta tashi daga cuta idanuwan nan nata sun kada sunyi jajir lokaci lokaci hawaye na zubo mata sai ta sa hannun ta ta dauke su
Rukayya cikin tsananin tausayi ta ce da ita “_bunayya Ashe abin da ya faru kenan..”
Bata ida rufe baki ba bunayya ta rushe da kuka mai tsuma zuciya nan hankalin mutanan dake tsakar gidan yayo kan ta kowa tausayinta yake ji saboda irin halin da take ciki
Hajiyar rukayya da mahaifiyar sabeer su ka shiga rarrashin ta har dakin inna mero su ka kai nan al’amari yasake rikicewa inna mero dake zaune sai faman sharar kwalla take tana ganin bunayya ta sake rushe wa da kuka nan daki ya hargitse da koke koke momy ita tai tayi musu nasiya da ban baki akan kuka ba nasu ba ne kamata yayi daidai wannan lokaci su shigayiwa mamaci addu’a, domin samun rahamar ubangiji.
Inna mero ta tsagaita da kuka sai Jan hanci take
Ta dubi momy tace “hajiyar rukayya lamarin nan ba na sauki bane dole duk wani mai imani yakokawa alhassan inna mero ta sake rushewa da kuka
Momy tashiga rarashinta da kyar aka samu tayi shiru
Haka dakin yakasance cikin rashin magana illa ajiyar zuciya kawai da zaka ji yana sauka rukayya da bunayya can uwar Dakar inna mero suka shige domin kuwa nan falon bazai zau nun musu ba
Rukayya ta dubi bunayya bayan ta dauke hawayen da suka gangaro mata
“Nayi matukar firgita da razana lokacin da sabeer ya zo min da zancen mutuwar Alhassan sai dai wani abin da ya sanya zuciya shakku abin da naji kin sanar dani Alhassan na aikatawa shi ssbeer yazo dashi gaban su momy ya fadi”.
Bunayya tayi wani murmushi mai ciwo matuka Wanda kuka ya fishin dadi ta ja hanci ta kure rukayya da idanuwa sannan tace cikin sanyin murya “ni kam ban yi Bakin ciki da mutuwar Alhassan ba dan mugun iri aka rage cikin doron duniyar nan in har irin su Alhassan na rayuwa to tabbas rayuwa za tai taka sance wa ciki bakin ciki da takaici…haushi na daya auren da nayi da Alhassan har yasanni shi nayiwa bakin ciki yanzu ya tafi ya barni da abin fade da kallon bsnza da mutane zasu ring an yi min bakincikina na biyu ta kabar da zanyi masa wallahi Alhassan ya cuce ni ya cuci rayuwa ya dasa min Bakin ciki a zuciya Wanda zai ta yaduwa har yakaini ga kushewa ba zan ya fe masa b…”.
Da sauri cikin azama rukayya takai hannun ta bakin bunayya cikin tashin hankali
“_meye haka bunayya kalau kike yanzu ke anaki rashin hankalin naki wannan abin da kike kokarin yi na la’antar mijinki shine daidai haba bunayya hakan bai dace ba komai ya aikata ai shi da ubangijin sa don allah ki daina irin wannan banzayen kalaman akan miji ki Sam basu kamace ki ba a matsayinki na musulma kuma mumina ki yarda da kaddara ki yarda wannan ita CE kaddararki da allah ya yi miki domin gwada imaninki “
Kuka bunayya tasaka wani kululun bakin ciki taji ya tokare mata zuciya
Iyakar tsana bunayya ta tsani alhassan azuciyar domin kuwa ya cuci rayuwar ta matuka ba ta zaton za ta iya yafe masa cutar da yayi mata cikin zubda hawaye “Ba ni kadai Alhassan yaka shewa rayuwa bani kadai yadasawa Bakin ciki a zuci ba bani kadai ce dangin rai da yashiga tashin hankali ba a sanadiyyar Alhassan kin ga kuwa Sam bai dace ace anyi masa fatan cigaba da rayuwa a duniyar nan ba”
Rukayya shiru tayi tana sauraron kalaman bunayya a yanayin da ta fuskanta lamarin na Alhassan ba karami bane tabbas lamari ya bace matuka har ya tunzura ta ya sanya take fadin kalamai munana akan sa amma kuma hakan Sam bai dace ba komai irin batawar da mutum yayi ma bai kamata ka maye gurbin abin da yayi maka da irin cutar da yayi maka ba bin sa zakayi da addua domin komawa hanya madaidaciya musamman shi Alhassan da tasa takara addua samun dacewa ya kamata ayi masa wajan allah
Dogon numfashin da bunayya ta ja ne yakatse rukayya daga zancen zucin da take ta dubeta cikin tsananin tausayi
“Don allah bunayya ki sassautawa zuciyarki ki fidda tsanar da kikayiwa mijin ki domin kuwa tasa takare yanzu ya rage shida ubangijin sa.
Gyada kai tayi tare da dauke hawayen da basu gajiya daga idanuwan ta
“Haba rukayya rai biyar sai kace ran kiyashi ai duk mai imani ba zai iya kashe kiyashi har biyar ba amma don allah ki jibi cutar da Alhassan yayi min ‘ya’yan biyar ya salwantar min da rayuwarsu haba haba don allah ki dubi lamarin nan da cuta babba a cikin ta amma ba komai don kan sa nasani allah ba azzalumin bawan sa bane zai bi wa Wanda aka cuta hakkin sa”
Cikin tsananin tausayi rukayya tace
“Don allah kiyi shiru ya isa haka kawai bishi da addua”
Wani kallo bunayya tabi ta dashi tare da girgiza kai wani wahalallan murmushi ya kunce mata ita kai ta San abin da take ji azuciyar ta na Bakin ciki da takaici yau ce takara NADAMAR auren Alhassan yau ne tayi da nasanin sanin Alhassan cikin duniyar ta da rayuwar ta kaicon wannan rayuwa ta takaici kaicon wannan bakar rana marashin dadi da armashi
Sallamar da akayi takatse musu shirun da sukayi momy ce ta shigo ta dubi su fuskar ba alamun wata fara’a tace “Ku taso ga su alhaji zaku gaisa” Cikin yanayi na sanyin jiki suka mike dukkan su momy na lura da yanayin da suke ciki ta girgiza kai tare da fice wa daga dakin sannan suka bi bayan ta suna isa falon su ka tadda su alhaji Duk sun hallara nan dai kowa yashiga yi ma rukayya gaisuwa da nasiha da kuma duk abin da yadace ban baki da hakuri haka sukai ta rareashin ta har zuwa wani lokaci sannan su alhaji sukayi musu sallama suka fice.
Sabeer da aka barshi karshen fita ya dubi bunayya cikin hali na tausawa
“_bunayya sai hakuri allah ya jikansa ya kyautata makwancin sa ke kuma allah ya baki hakurin rasa shi”
Kallo kawai ta bi shi dashi da tana da halin yin magana da tace ba ameen amma da yake ance ko ido bai ci ba ya San kima shiyasa ta hadiye takaicin ta
Tunda akayi rasuwar kullum rukayya gidan take wuni wajan bunayya ta rarrashin ta da ban baki domin ta sassauta tsanar da tayi wa mijin nata dan yarigaya ya koma ga mahaliccin sa.
Yau ma kamar kullum anyi sadakar uku ta Alhassan su momy da alhaji duk sun zo anyi addu’o’i ga mamaci domin samun rabauta bayan ankammlane bunayya na zaune ita da momynta da inna mero da kuma rukayya da sauran dangin kowa yayi shiru ba Wanda ke magana in ka zare bunayya da inna mero dake ta sharar kwalla kamar wacce aka ci kara bunayya ta mike tare da duban rukayya tace “_ta so don allah ina son magana dake”
Kowa ya bita da kallo cikin rashin fahimtar abin da tace ba Wanda ya tsinka rukayya ta mike suka fito daga cikin dakin can gefe guda suka samu lokacin mutane yan gaisuwa sun ragu
Bayan sun zauna bunayya ta dubi rukayya cikin Jan hanci tace
“Sabeer na nan ko ya koma gida ne?”
Cikin mamaki rukayya ta dube ta amma ba ta bari ta gani hakan ba ta mai da mata da amsa tare da tambaya
Murmushi bunayya tayi wasu ta wagar hawaye suka zubo mata ta dubi rukayya “ina bukatar ganin sa ne akwai maganar da nake so muyi dashi ne”
Ba tare da ta sake tambayar ta ba ta daga waya ta kira sabeer din aiko tayi sa a adaidai lokacin yana kokarin tafiya nan ta sanar dashi abin da ke Faruwa shiru yayi yana jujjuya maganar ‘wai bunyya ce ke kiran sa to lafiya me ya faru take neman ‘ lokaci da ya yaji gaban sa ya buga tsoro ya dan kamashi nan da nan yashiga amboton sunayen allah bayan ya gama nazarin ne ya ce da rukayya gashi nan zuwa ta amsa da to minti kadan yashigo can gefe ya hango su rukayya tayi masa nuni da ya karaso gabannsa ya cigaba da faduwa har ya isa ya dubi ruksyya
“Lafiya dai ko ake nema?”
Gyada kai tayi
“Ga mai Neman kanan ba ni bace”
Ta fadi cikin kokarin kau da fuska shi ma bai bi ta kan ta ba gabadaya ya tar kata hankalin sa izuwa bunayya bayan yan sakanni ya ja numfashi yace “me ke faruwa ne?”
Cikin kokarin ta ra hawayen da kekorin zubo mata ta dubi sabeer San ta juya ta kalli rukayya su duk sai suka zuba mata idanuwa tsayin lokaci bata tsinka ba su ma kuma basuyi mata magana ba dalilin hawayen dasu kaga yana zuba bai sai sun tambaye ta komai yedalili sun San bai wuce kan lamarin Alhassan.
Maganar da bunayya ta fara cikin rawar murya da son rushewa da kuka ita ta hankalto dasu daga zancen zucin da suke.
“Nasan rashin sani ne yasanya kuma ba kuyi min allah ya isa ba saboda adalilina kuka hadu da Alhassan”
Da sauri suka dubeta cikin son fahimtar abin da ta fadi ina ta dosa amma sun kasa sai kawai suka cigaba da bin ta da kallo.
Ta girgiza kai hawaye suka shiga zubo mata
“Nasani can baya har ma izuwa yanzu ba wata jituwa bace a tsakanin ku saboda lamarin da ya afku Wanda duk cikin ku ba wanda yasan inda gaskiyar take kawai lalube kuke cikin duhu musamman ma ke rukayya da kika di daukar abin da zafi”
Tayi shiru na yan sakanni sannan ta dora dacewa “rukayya nasani kina zargin mijinki da salwantar miki da ciki adalilin furucin da yayi miki na bai shirya haihuwa da wuri ba wannan kalaman nasa su sukayi tasiri a zuciyarki na kafa hujjar shine ya yi silar salwantar cikin da kike dashi ko ba haka ba ne ?
Ta fadi tana mai duban su duk su biyun Wanda a wannan lokaci duk sun gama shi ga wani Hali na rashin haiyaci rukayya gumi ne kawai ke keto mata ta ko ina ta shiga duban sabeer Wanda yayi kuri da idanuwa yana duban bunayya matukar shiga firgici yashiga yayi matukar mamskin jin wannan maganar daga bakib bunayya me take son CE masa tanaso tace tana da masaniya game da xubewar cikin rukayya in kuwa haka tabbas akwai babbar matsala.
Bunayya ta dubi rukayya tace
“Kin har baki manta ba ranar da kuka sami sabani da ssbeer kin zo gida na ko”
Kai kawai ta gyada mata cikin rashin haiyaci.
“To a wannan rana cikin ki ya fice daga jikin ki bayan kin bar gida na”
Wata irin zabuwa rukayya tayi tare da kure bunayya da ido shi kan sa ssbeer wani irin rashin natsuwa yaji ya ziyarce shi cikin matsanancin tashin hankali ya dubi bunayya.
“Me kike nufi kins nufin kice kin San dalilin zubewar cikin rukayya in kuwa kin sa to ya akayi kuma ya hakan ta faru har cikin ya zube.
Cikin kunar rai da takaici bunayya tace “Alhassan ne sila shine ya hallakarmu muku da GUDAN JININ ku shine yasan ya rashin jituwa a tsaksnin ku shine ya haifar da rashin kwanciyar hankali a tsakanin ku..”
Wata irin kara rukayya ts saki ta re da mikewa cikin zafin nama idanuwan ta suka shiga zubda hawaye gabadaya duniyar taji Rana juya mata
Wannan wani irin tashin hankali ne wannan wacce irin rana ce ta Bakin ciki da takaici
Abinda take ta fadi a zuciyar ta kenan sabeer kuwa hannu biyu yasanya ya na dafe kai saboda wani irin nauyi da yaji yayi masa kamar zai tarwatse gabadaya ji duniyar ta na juya masa yashiga ambaton sunan allah lokaci guda idanuwan sa suka kada sukayi jajir takaicin duniya duk ya cika masa zuciya .
“Da sani dole kuyi bakin ciki da wannan rana dole ne ku tsani Alhassan dan yayi matukar cutar rayuka ba kadan ba allah ne kai zai yi mana sakayya”.
Sabeer cikinzafinrai yace “ya isa hakan bunayya ba sai kin yi masa allah ya isa ba ai shi yanzu bashi da wata sauran rayuwa yanzu ya rage shi da ubangijinsa wannan ya rage tsakanin su dan haka nidai ba abin da zance dashi ba zan yi masa mugun fata ba Baki bunayya ta saki tana duban sabeer tai mamaki matuka da jin furucin sa tabbas yana da sauki hali ba tayi zaton lamarin zai zo da sauki haka ba tabbas ya cika nagari
Sabeer dake Jan hanci yasan ya hannu ya dauke gumin da yankaryo masa ya dubi rukayya dake tsaye kiman kamar bishiyar da aka dasa hawaye kawai ke zuba s fuskarta tsansnin tashin hankali ya bai yana karara s fuskarta
“Ki kokarta ki zauna mu fuskanci juna kar jiri ya sanya ki kije kasa”
Ba tace dashi komai ba illah idsnuwa da ta zuba masa ganin da sukayi bata da niyar zama bunayya ta miki ta rukota jiki a sanyaye ta zaunar da ita gabadaya jikin ta yasaki ba alamun karfi tayi shiru tana juya lamarin ganin abin take kamar ba gaske ba amma da alamun abin ns son tabbata yarda kwanyar ta da zuciyar ta suke gasgata mata lamarin tabbas maganar bunayya gaskiya dalili kuwa shine ranar da taje gidan ta ta tadda Alhassan a gidan har suka gaisa Ashe macuci ne bata sani mai dauke da fuskar salihanci
Ta numfasa tare da duban bunayya idanuwan ta na zubda hawaye.
“allah yana nan ba azzalumin bawansa bane amma allah nagani Alhassan ya cuci rayuwa matuka sai nace allah ya bi min hakki sabida yasanya ni zargin mijina ba tare da yana da laifi mun kasa zaman lafiya Duk a dalilin haka”
Tayi shiru saboda kukan da yaci karfin ta
Nan su ka Shiga rarrashinta da ban baki
Sabeer cikin son mai da komai ba komai na ya dubesu su dukkd biyun
“Yanzu abin da za ayi wannan maganar ta zama a iya mu a matsayin Sirri saboda ko min fadi ba ta yar da hsnkalin rayuka za ayi don haka mu rufe sirrin mu a nan nidai na yafe allah ya yafe mana baki daya”
Cikin sanyi jiki rukayya tace “shikenan ni nayi masa afuwa na yarda wannnan abin da ya faru yana cikin KADDARARMU allah ya sa mudace ya sa mufi karfin zuciyoyinmu”
Duk su ka amsa da ameen
Bunayya ta yi ajiyar numfashi mai karfi Wanda yasan yasu saurin dubanta murmushi tayi hawaye kuma na zuba
“Nagode da wannan halaccin da kukayi min ko ba komai Alhassan miji nane na rayudashi matsayin mijina amma kuma ban sani Ashe ba mai so na bane ni kadai nake son sa amma bakomai allah yajikan duk laifin da yayi min na yafe masa duniya da lahira allah ya sa mufi karfin zuciyoyin mu dan nasan tabbas zuciya ce Takai shi ma halaka”
Ssbeer yace “ai zuciya muguwar aba ce da kike ganin ta in har tafi karfin mutum shikenan rayuwarsa ta gurbata amma inkai mutum ne kafi karfin ta to komai zai zo maka da sauki cikin lamuran rayuwa”
Nan dai suka cigaba da hira da maganganu akan lamuran rayuwa da yarda take kasancewa mutum in ya biwa son zuciya
Lokaci kankani duk saber ya bi hanyoyin da suka dace har ya shafe duk wani ki da tsana da sukeyiwa Alhassan azuciyoyinsu
Sai gabani mangaruba ssannan su rukayya da ssbeer suka bar gidan+
Haka rayuwa tai ta guda cikin dadi rashin haka zuciyoyi dai gasunan jikin dan Adam suna ta aiki wani yafi karfin tasa wani kuma zuciyar tafi karfinsa allaha ya sa duk wani dangi rai yafi karfinzuciyarsa sa.BAYAN WATANNI TAKWAS
Rayuwa sai faman ta fiya take al’aamura sai faruwa suke dangin rai sai macewa suke sabbin rai suna wanzuwa a doran duniya
A wannan lokaci rayuwa dasuka shiga tsanani sun koma farinciki duk wani kunci da takaici ya bar duniyar su da rayuwarsu
Farinciki ya wanzu tsakanin ma’aurata rukayya da sabeer hankali ya kwanta kamar bawani Abu na rashin jituwa da ya taba shiga tsakanin su
Cikin wani yammaci rukayya zaune cikin kamfacecen falon ta mai cike da kayan more rayuwa hannunta rike da tuba ta na sha cikin dake jikinta dan wata shida yayi turtsetse dashi a gabanta tayi wani irin kyau na fitar hankali kallo daya zakai mata ka tabbatar farinciki da kwaniciyar hankali ya shigo rayuwarta
Kamar daga sama ta tsinkayi muryar mijin nata yana kwado sallama tana kokarin tashi ya shigo ta sauri yace “zauna zauna kar kiyi min asara haka kawai”
Baki ta turu masa cikin sigar shagwaba “habadai asarar mai zanyi maka”
Yayi dariya yayi mata nuni da cikin da ke jikin ta sannan yace ” yayana mana tagwaye”Idanuwa rukayya ta kwalalo masa baki sake.
Ya tuntsure da Dari ganin yarda tayi sai kace wata sakankiya .yakai hannusa zuwa la66a ta ya jasu
Ta saki kara “wayyo baki”.
Shi ma ya kwaikwayi yarda tayi duk suka tuntsure da dariya
Ta kaima sa dundu cikin sigar wasa
“Wallahi mugu ne kai”
“Ke ma ai muguwa ce”
Ta galla masa harara
Sannan tace “bunayya na gaisheka yanzu mukayi waya da ita wai Ashe cigaba da karatu za tayi a kasar saudiya domin zama cikakkiyar likitar mata”
Sabeer yace “allah sarki bunayya kice ba batun aure kuma kenan”
Rukayya tace “cabdijam bunayya ai gabadaya zancen aure ya sure mata arai ita fa tace ko za tayi aure ba yanzu ba “
Gyada kai yayi “da gaskiyar amma yadace ace tayi saboda kare mutuncinta da martabar gidansu haka shi zai fi cancanta”
Rukayya tayi dariya tace “to ustaz mai waazi za tayi ba sai anyi mata waazi ba.”
Ta na fadin haka ta janyo ledar da sabeer yashigo da ita tana mai cewa “me kuma muka samu”
“Bude kigane wa idanunki”
Ba tare da tasake cewa komai ba ta bude ledar tuba CE a cikin murmushi tayi taga abinda take so ta sake janyo dayar ledar ta bude littattafai ne aciki da sauri ta dubi sabeer “wadannan fa”
“Naki ne ke na sawa “
Ta tsuke fuska tashiga duban littattafsn sukai kala goma amma duk na koyar girki ne iri daban daban
Duban sa tayi fuska a tsuke
“Me zanyi da littatatfan Koyan girki”.
“Don ki koya “.
Ya fadi yana mai yin murmushi haka da tagani yasan ya tajin haushi duk ta kwase littattafan ta watsamasa dariyar da yake boye ta kunce masa nan ta fara alamun son yin kuka tana bunbuga kafa akasa
Ganin haka Da yayi yasan yi sauri n zuwa ya rike ya matse gam sai da tayi kara
“So kike ki salwantamin da bebyna”
“To bakai bane”
“Nayi me “.
Ya kwaikwayi yarda tayi magana cikinshagwaba duk suka tuntsure da dariya
Haka rayuwa tacigaba da guda cikin farin ciki da kwanciyar hankali ga maaurantar
Rukayya ta haifi yayanta biyu duk maza kyawawa. ..+
TAMMAT BI HAMDULLAH
Ina godiya ga Allah mai kowa mai komai da yabani ikon kammala wannan labari tsira da aminci su kara tabbata ga annabin farko kuma nakarshe
Ya bamu ladar abin alheri da muka aikata aciki ya yafe mana kura-kuran ciki