RAUDHA CHAPTER 1

 RAUDHA CHAPTER 1

__________📖 Alarm ɗin da tasaita ƙarfe 09:00pm. Yatashe ta daga barcin da take yi, a hankali tayaye bargon da tarufe jikin ta har kanta dashi tasoma miƙa tana hamma, ɗakin gaba ɗaya duhu ne don ba’a ganin komi, miƙewa zaune tayi ta jima ahaka har magagin barcin da take yi yasake ta kafin tazuro ƙafafun ta tasauko daga gadon tanufi wajen makunnin ɗakin takunna wuta, haske ne

yamamaye gaba ɗaya ɗakin da yatsaru iya tsaruwa, komi na ɗakin Sky Green ne, takowa tayi ta’isa gaban gadon tana sake zama, hannu tasanya tadafe goshin ta na tsawon mintuna 3 kafin tasoma tattare gashin kanta da yake abaje har zuwa kafaɗun ta taɗaure da jelan gashin, miƙewa tayi tasoma cire kayan barcin jikin ta sannan taɗaura towel tashige toilet, tana shiga tasakarwa kanta shower, sai da tadaɗe tana jiƙa ƙanta daga sama har ƙasa kafin tasoma wankan, acikin mintuna 15 tagama taɗauro showel tafito, a gaban dressing mirror tazauna tasoma tsane kanta, sai kuma taɗau handrayer tafara busar da gashin ta, tanayi tana lumshe manyan idanuwanta har sanda tagama tasoma shafa Expensive lotions ɗin ta, bayan ta gama powder kawai tasanya a kyakykyawar face ɗinta tashafa lipstick💄a ƙananun laɓɓan ta, kana tamiƙe tanufi Sif ɗin kayan ta tasoma zaɓo kayan da zata saka, riga ne ja me gajeren hannu tasaka ajikin ta wanda yatsaya mata iya cibiyan ta, sai tasaka dogon wando pencil da yayi matuƙar matseta yafito da halittan ta, Hill shoes tasaka red colour me igiya sannan takoma gaban madubi tasoma tattare gashinta tana sake gyarawa tare da shafa mayuka masu matuƙar saka gashi ƙyalli, sannan tafeshe jikinta da perfomer’s masu ƙamshin daɗi da sanyi, ƙaton Ribom tasaka green colour takama gashin sannan tanufi inda take rataye Wizy Bags ɗin ta taɗauko ɗaya tadawo gaban gadon ta tabuɗe drower takwashi kuɗi masu yawa tazuba a jakan, wayan ta dake ajiye saman drower ɗin taɗauka shima tasaka a jaka kafin taɗau car key tataka tafice, tana fitowa tasauka dawnstair, bata damu da duhun da yamamaye ko ina ba, haka tafice a parlour’n tanufi Compound ɗin gidan, motarta tabuɗe tashiga tafice a gidan da mugun gudu, kasancewar dare yasoma yi motoci sun soma ɗauke ƙafa haka tayi ta tsula gudu kamar zata tashi sama ko tsoro bata ji, wayan ta da yasoma ringing tamiƙa hannu taciro cikin jaka tana peacking call ɗin takara a kunne, kafin tayi magana Ramcy ta riga ta dacewa+

“Wai Babe kina Ina ne naji ki shiru har yanzu?”.

Cikin siririyan muryan ta me sanyi tace “ga ninan zuwa”.

“Ok sai kin zo”. Cewar Ramcy tana katse kiran

Ajiye wayan kawai tayi taƙara speed, tana tuƙin ne cike da gwaninta har Allah yasa takawo ƙofar gidan su Ramcy ƙawarta, Ramcy dake bakin ƙofar gidan su a tsaye tanufo motan tabuɗe tashige, ita kuma taja sukaci gaba da tafiya, kallon ta Ramcy tayi tana murmushi tace

“Kinyi kyau Babe”.

“Thanks”. Ta’amsa mata ataƙaice

Daga haka basu sake magana ba har suka iso gaban wani kyakkyawan Club, fitowa sukayi cikin motan bayan tayi parcking motan aciki, atare suka jera sukayi cikin Club ɗin

Sosai ciki yacika da mutane maza da mata kowa na harkan gaban shi, an saka music wasu na ta faman cashewa, suna shiga Direct RAUDHA wajen masu rawa tanufa tashige cikin su tasoma kaɗa jiki tana rawa me ban sha’awa, dama abinda ke kawo ta Club kenan RAWA, tana ƙaunar rawa a rayuwan ta, koda tana cikin damuwa ne idan har zataji kiɗa na tashi to fa sai zuciyarta tayi mata sanyi, haka tayi ta cashewa tana rausaya jiki kamar zata karye, dama ba wani auki ne da ita ba, ita kuwa Ramcy ba gwanar rawan bace, zuwa tayi tazauna cikin wasu maza tasoma kora sheesha tana yi tana kaɗa kai

RAUDHA rawa yayi rawa sai zuba ihu take yi tana dariya tana tiƙan rawa, sai da tagaji sosai kafin tayo wajen Ramcy tazauna tana waftan Sheeshan hannun ta tasoma sha tana fesarwa ta hanci ta baki cike da ƙwarewa, mazan wajen duk kallon ta suke yi suna dariya, yayinda ɗaya daga ciki yasoma mata kirari yana faman koɗa mata kai, ita kuwa sai faman bankan sheesha take yi tanayi tana shaƙan Coken, Ramcy tashi tayi tanufi wajen wani saurayi dake can zaune tare da ƴan mata, magana sukayi sannan yamiƙo mata wasu ƙwayoyi da bansan ko menene ba, amsa tayi tanufi wajen Receptionist tayi odan Juice tadawo, kallon ta kawai RAUDHA take yi har tazauna kana tamiƙa mata hannu, ita kuma tabata Cup ɗaya bayan da tasaka mata ƙwayoyin ciki, amsa kawai tayi tasoma korawa tana jin ta asama, zuwa lokacin tasoma kai ƙololuwan bugawa, don daƙyar take iya buɗe kyawawan idanuwanta tana kallon mutane, sai da tashanye gaba ɗaya tasaki Cup ɗin Ramcy tayi saurin tarewa

Lumshe idanu tasoma yi tana buɗewa daƙyar, cikin tsananin maye take cewa “ahh.. ahhm Rammmm.. Rammcyyyy ƙaro min..”

Bata iya ƙarisa maganar ba ma sai shiru tayi tana ci gaba da zuƙan Sheeshan tana fesarwa ta cikin hancin ta, Ramcy itama da tagama buguwa tashi tayi takoma tasake yin musu odan wani Juice ɗin tadawo, zuba musu ƙwayan tayi suka ci gaba da sha, yayinda su kuma mazan nan sai harkan gaban su suke yi, daga ƙarshe ma tashi sukayi ɗaya bayan ɗaya suna barin wajen, yayinda wasu suka wuce wajen ƴan matan su, wasu kuma sukayi gida don alokacin dare yayi sosai

RAUDHA buɗe manyan idanuwan ta da suka kaɗa sukayi jazur tayi tana kallon Ramcy tace “amm… Babe muje.. giii..gida, yauuu banjin zannn iya kaaaiiiii asuba”.

Gyaɗa kai kawai Ramcy tayi tana miƙe wa tsaye, taɗau jakan ta tana ƙoƙarin rataya wa, ita kuwa RAUDHA kasa miƙe wa tayi sai da tafi minti 3 azaune kafin tayunƙura tamiƙe, sai kuma takoma yarabb kamar wacce aka jefar

“Oshhhhhhh”. Tafaɗa tana riƙe kanta da yabugi kujera

Still sake miƙe wa tayi, har ta soma tafiya kuma sai tasake faɗi, dole Ramcy ne tariƙo ta suna tafiya suna layi har suka fice daga Club ɗin

“Babe anyaaa zzzaki iya tuƙi? Kar fa kije ki zubarrr damu?”

RAUDHA dake faman layi takai tadawo tana son buɗe mota but takasa, taɗago kanta tana kallon Ramcy daƙyar, lumshe idanu tayi tasake ware idanun sosai kan Ramcy kana tace

“Kin fini.. sanin.. abinda nake yi ne? Common shiiiiiga… Muje ma..na..”

Bata rufe baki ba tayi taga-taga zata faɗi, har takusa kai ƙasa tayi saurin riƙo motan tana gyara tsayuwar ta, buɗe motan tayi tafaɗa ciki tana mata key, itama Ramcy shiga tayi sannan taja motan da gudun tsiya tafice haraban wajen, izuwa lokacin tsit kake ji a titi domin kuwa wajen ƙarfe 0300pm. Ne na dare, ahankali take jan motan sai dai yanda motan take yawo akan titin zakasan ba cikin hankali mamallakin motan take ba, idan tayi nan sai tayi nan, daƙyar take buɗe idanun ta tana kallon titin, har ƙofar gida tasauke Ramcy kafin sukayi sallama taja motan tayi gaba, tana isa tanƙamemen gidan su tadanna hon ɗin da gaba ɗaya layin gidajen sai anji, Me gadi da yake zaune yana jiran dawowarta yamiƙe dasauri yabuɗe mata, tashigo aguje kamar zatayi ciki dashi tanufi parcking space, parcking tayi tajanyo jakan ta tana ratayawa tabuɗe motan tafito, tafiya take yi tana tangaɗi har taƙarisa bakin ƙofar Main parlour tabuɗe tashiga, ahankali take takawa tana faman layi taje gaba tadawo baya har dai ta’isa steps tasoma takawa tana haurawa sama, tana hawa tashige ɗakin ta tanufi kan gado tafaɗa kai, ahaka barci yakwashe ta batare da tacire ko takalmin ƙafafun ta ba.

        Ba ita tatashi ba sai washe gari ƙarfe 01:30pm. Ahankali take buɗe kyawawan idanunta da suke ashanye koda yaushe, hannun ta duk ka biyun tasaka tariƙe kanta tana sake lumshe idanuwanta, ta ɗan jima ahaka kafin tacire hannun tana sake gyara kwanciyarta cike da tsananin gajiya, ko kaɗan barcin be ishe ta ba so take yi tasake komawa, sai dai ƙarar wayan ta shi yawartsakar da ita, hannu tasaka taciro cikin jakan ta tana kallon screan ɗin, MY DEAR DAD aka rubuta, peacking tayi tasaka a kunne still tana gyara kwanciyarta, daga ɗaya side ɗin Dad ɗin ta ne yasoma magana

“My Baby good morning”.

Lumshe idanu tayi tana buɗe wa kana ta’amsa mishi “morning Daddy”.

“Baby har yanzu baki tashi barcin bane?”

“Eh”. Tabashi amsa ataƙaice

“Ok Allah yasa bani natashe ki ba don bana son takura miki?”

Memakon ta’amsa mishi tambayan sai canza maganar tayi dacewa “Daddy yaushe zaka dawo ne I miss You More?”

“Sorry My Baby umm? very soon Zaki ganni”.

Cikin dashashshiyar muryan ta cike da shagwaɓa tace “Daddy kasaka mana azo a ɗauke ni nagaji da zama Ni kaɗai, komi babu daɗi”.

Daddy cikin lallami tare da ƙaunar ƴar tasa yace “sorry Babyna ai nace miki nakusa dawowa very soon zaki ganni, and kuma kinga kin kusa fara school bazai yiwu ki biyo ni ba”.

“Daddy to ba sai kasaka Ni school ɗin nan ba, dama bana son anan”.

Murmushi yayi yace “Sweetheart kinsan ba zama nake yi ba, bana son kiyi nesa Dani that’s why nafison kiyi karatun ki anan Nageria”.

Turo baki kawai tayi bata sake cewa komi ba, Daddy lallaɓa ta yai tayi don yasan fushi tayi, shi kuma baya son ne taje Abroad tasake lalacewa coz yasan ta ba tarbiyya ne ya’ishe ta ba, yanzu haka ma nema mata shiriya yake yi Allah yashirye ta don duk abinda take yi yana sane dashi, sai dai tsananin ƙaunar da yake mata bazai saka yayi mata faɗa ba

Muryan ta shi yadawo dashi gajeren tunanin sa

“Daddy I will call you back idan nayi Lunch”.

“Ok My Baby Baki buƙatar komi ko?”

Cikin nuna sangarta tace “Daddy katura min kuɗi zan fita Shopping yau”.

“Ok byee take Care”.

“Byeeee Daddy”.

Ajiye wayan tayi sannan tatashi tazauna tasoma cire Hill shoes ɗin ƙafanta, Ribom ɗin kanta dake yashe a ƙasa taɗauka taɗaure gashin ta sannan tamiƙe tanufi gaban plasma t.v dake ɗakin takunna, Remote taɗauka tasoma sauya Channels, a BOM t.v tabar shi sannan tasaka Volume gaba ɗaya, nan da nan ko’ina yaƙaraɗe da Music ɗin da akeyi kasancewar akwai irin manya-mayan speakers🔊 masu matuƙar ƙara da ɗaukan duma, Toilet tashige tana bin waƙar kamar ita take rerawa, Brosh kawai tayi tafito tanufi ƙofan fita tafice ƙafarta ko takalmi, Steps tasoma takawa da gudu-gudu don ita akwai son gudu, tana jinta kamar ƴar chali-cahli ce

lokacin da ta’isa tanƙamemen parlour’n tabuɗe muryan ta da yake adishe koda yaushe tamkar tana mura tasoma kiran masu aikin ta, kafin tarufe baki suka fito suka gurfana gaban ta

“Where is my lunch?”. Tatambaye su tana bin su da kallo da shanyayyun idanun ta

Saude wacce take kula da abincin ta tace “yanzu zan zuba a warmers in kawo dainning”.

“Ok ki kawo min ɗakina ne”.

“An gama ranki yadaɗe”. Saude tafaɗa sannan tajuya takoma kichen

Kallon Larai tayi tace “ke kuma je ki sanar da Idi yawanke min Motan Daddy yanzu”.

Cike da girmamawa Larai ta’amsa mata sannan tafice dasauri don isar da saƙon uwargijiyarta, ita kuma juyawa tayi tasoma taka steps ɗin da gudu takoma ɗakinta, tana shiga tanufi Drower tabuɗe taciro wasu Tables taciri ɗaya tasaka a bakin ta, Fridge tanufa tabuɗe taɗau Faro water takora dashi, kan sofa tanufa tana riƙe kanta tazauna dai-dai lokacin da Saude tashigo riƙe da farantin Silver ta’iso gabanta ta’ajiye kan Centre table dake gaban kujeran da yake guda ɗaya cikin ɗakin

“Ranki yadaɗe gashi”.

RAUDHA da tasoma hawa kan network ɗago shanyayyun idanunta tayi takalle ta kafin tayi mata alama da hannu tatafi, juyawa Saude tayi tanufi ƙofa, sai da tabuɗe ƙofar kafin tajuyo tana kallon RAUDHAN da har yanzu take riƙe da kanta, cikin ranta sosai take tausayin yarinyan kuma take  mata fatan shiriya, duk da wani lokacin bata da kirki idan har sukayi mata ba dai-dai ba haka zata zazzage musu tijara son ranta, but idan har zasu kiyaye ƙa’idan ta to babu abinda ke shiga tsakanin su don ita ɗin ba me son shiga rayuwan wasu bane idan be shafe ta ba

Saude ganin RAUDHA zata ɗago kai yasaka tayi saurin fita tana rufo ƙofan.

     Ahankali tasaka zara-zaran hannunta tabuɗe abincin, Jolof Raice ne da yaji meat and veggies a sama, ɗayan Coolar’n kuma da tabuɗe ferfesun kayan ciki ne, a plate tazuba tasoma ci, sosai taci abincin kasancewar batayi breakfast ba, bayan ta gama miƙe wa tayi tacire kayan jikin ta tashige toilet, ita kuma Saude lokacin tadawo takwashe kayan abincin tafitar dasu

Minti 15 yaɗauke ta kafin tafito, doguwar riga tazira sannan tasaka Hijab tasoma gabatar da sallan asuba kafin tayi azahar, dama haka take yi koda yaushe, wani lokacin ma gaba ɗaya haɗe su take yi da dare tayi su, akwai ta da son wasa da ibada duk da ba wani addini tasani ba, but ko ta tara su idan tatashi sai tahaɗe tayi, tana idarwa ko tsayawa addu’a batayi ba tamiƙe tasoma tuɓe rigan, towel taɗaura tanufi gaban mirror tazauna tasoma shafa Lotions tana bin music ɗin dake tashi cikin t.v at the same tana kaɗa jikinta tana rawa, Light makeup tayi tamiƙe tanufi gaban sif ɗin kayan ta tazaɓo kayan da zata saka tazube kan gado, komawa tayi tazauna a bakin gadon taɗau wayan ta tana latsawa, ta ɗan jima kafin tamiƙe tasanya kayan, ƙaramar riga ce White wanda tatsaya mata iya cibiya, don idan har zata ɗaga hannun ta ko tayi motsi me ƙarfi ana hango cibiyanta, sai tasaka wandon rigan Robber iya gwiwarta shima fari, gaba ɗaya santalelen ƙaurin ƙafanta a waje yake, zama tayi tasoma zira socks white da yakawo mata har kusa da wandon ta sannan tasaka Hill shoes Black me igiya, miƙewa tayi takoma gaban mirror tasake gyara gashinta da yake baƙi siɗik taɗaure da Black Ribom sannan tafeshe jikinta da Parfomers masu shegen ƙamshi, miƙewa tayi tana wani jujjuya wa tana sake kallon kanta a mirror, sosai tayi matuƙar kyau kamar wata baturiya, dama ita irin shigan Turawa ke burge ta kuma shi ɗin take yi, ko kaɗan bata ta’ammali da kayan Hausa don haka farat ɗaya idan kaganta baza ka taɓa tunanin ta haɗa hanya da Hausawa ba coz babu ta inda take kama dasu, sai da tagama jujjuya jikin ta kafin taje tazaro Wizy Bag ɗin ta tare da ɗaukan wayan ta tafice batare da tayafa komi ba, haka tabar ɗakin ko T.v bata kashe ba, sai dai idan Larai me aikin ta tazo gyara ɗakin itace zata kashe mata.Packing space tanufa tabuɗe motan tashiga but sai dai bata shigar da ƙafafunta ciki ba, Lockern cikin motan tabuɗe taciro wani farin Robber tabuɗe, Coken ne aciki sai tazuba a tafin hannun ta tana shaƙa, sosai tashaƙa don sai da taji ta kan network kafin tajinginar da kanta tana lumshe idanu, as usual tana son taji ta kan network that’s why bata rabo da shan kayan maye, abin ma har yabi jininta, kana kallon idanunta da kuma yanda take yawan lumshe su zakasan ita ɗin ƴar ƙwaya ce, sai da taɗau kamar minti 5 kafin tashigar da ƙafafuwan ta tarufe murfin, key tayi wa motan tafige ta tayi bakin Gate, oready dama Gateman yarigada ya buɗe mata Gate don yasan halin ta bata da jimirin jira, tana fita tahau kan titi kasancewar gidan nasu a bakin titi yake, da wani irin speed take Jan motan Wanda idan kagani kasan Drever’n ciki ba ƙalau take ba, duk inda tawuce sai an kalle ta, haka take over taking Cars tana wuce wa babu ruwan ta

+

A cikin minti 15 ta iso wani supper market, cikin haraban tayi packing sai da tayi kusan mintuna goma tana zaune abunta kafin tabuɗe tafito, cikin wani irin tafiya tare da ficchi take takawa tadoshi cikin supper market ɗin, duk wanda ke haraban wajen sai da yaɗaga kai yana kallon ta, ita kuwa batasan ma suna yi ba, tafiya kawai take yi tana wani irin karairaya tare da lumshe idanu tamkar bata ganin gaban ta

Just 10minute taɗauka aciki before tafito riƙe da Ledoji a hannun ta tatunkari motan ta

“Woww wow Nazee ji wata zazzafan Babe sai kace ita tatsara kanta”.

Nazee da yake ƙoƙarin rufe ƙofar mota yajuyo yana kallon RAUDHA, sai kuma yaɗauke kai yana kallon Abokin nasa da ninyan yayi magana but sai shi yariga sa dacewa

“Kai wlh sai naje wajen ta don bazan bari tasuɓuce min ba, kutttt wannan irin su ai muke so Young Killer Babe”.

Har ya soma tafiya Nazee yajawo shi baya

“Kai rufawa kanka asiri wlh, kai baka san ko ƴar wanene ba ko?”

Saddeq dake kallon sa yace “ƴar wanene to? Kaga da Allah sake Ni kar  tatafi”. Yaƙarike maganar yana fizge rigan sa tare da kallon motan RAUDHA da har tasoma tafiya

Nazee saurin cewa yayi “wlh yarinyan M. makamashi ne, gwara ma kadawo kafin ka kwashi wulaƙanci a wajen ta”.

Cak Sadeeq yatsaya yana kallon Nazee yace “Haba dai kana nufin Alh. Mustapha Makamashi?”

“Wlh kuwa itace”. Nazee yasake tabbatar masa

Rufe baki Sadeeq yayi yace “kai wlh nayi tunanin ko irin Babes ɗina ne, wai kana nufin yanzu wannan musulma ce? Ikon Allah lallai kam huuuuu..”

Kasa ma ƙarisa maganar yayi yana sake bin hanyan da kallo da tuni RAUDHA taɓace a wajen, sai kuma yajuyo yana kallon Nazee yace “wlh nayi tunanin ko Christian CE kasan Ni dasu nafi harka coz waɗannan ƴaƴan musulman babu abinda suka iya sai girman kan tsiya”.

Dariya Nazee yafashe dashi kafin yasoma tafiya yana cewa “kai dalla muyi abinda yakawo mu Ni kaga tafiyana”.

Bayan sa Sadeeq yabi yana cewa “Guy Amma fa ta haɗu, duk sanda nasake ganin ta sai nayi mata magana Yasin”.

         🌐🌐🌐

WUTA kawai take ba ma Motan har ta’isa gida, wani irin hon take dannawa kamar zata tashi sama, dasauri Gateman yabuɗe mata tashigo aguje tanufi Compound ɗin gidan, anan tayi packing tafito takwashi kayan ta tanufi cikin gida, tana buɗe ƙofan parlour’n suka haɗa idanu dashi, tsaye yake ya sanya hannayen sa cikin aljihun wandon sa yana kallon ta, wani irin ƙara tasaki tazubar da ledojin dake hannun ta tanufe shi aguje, tana isowa wajen sa yacafe ta yasoma juyata tana dariya, shima ɗin dariyan yake yi yana faman wulwula ta sai kace ya ɗauki ƙaramar yarinya, sai da yadaɗe yana faman jujjuya ta acikin parlour’n sannan ya’ajiye ta a ƙasa tabiyo jikin sa suka faɗa saman sofa suna ɓaɓɓaka dariya tare da sakin nishi, sake maƙalƙale shi tayi cike da tsananin murna tace

“I’m so surprise Yaya yaushe kadawo?”

Hannun sa yasaka yana shafa fuskarta cikin murmushi yace “Yesterday Baby, mun dawo gaba ɗaya kenan fa”.

Wani irin tsalle tadaka ajikin sa cikin ihun murna tace “dagaske Yaya?”

Still Murmushi yasaki yace “Yes my dear”.

“But anan gidan zaku zauna ko?” Tasake tambayan sa cike da zumuɗi

Girgiza mata kai yayi yana taɓe baki yace “No muna Abuja fa”.

Hannun sa still dake yawo saman fuskarta tayi saurin cafke yatsan sa da baki tana gantsara masa cizo cike da mugunta, ihu yasaki yana janye hannun yace

“Oshhhhhhh Babe Zaki kashe Ni ne da zafi fa?”

Turo bakin ta tayi tana tashi ajikin sa tace “Yaya meyasaka sai acan zaku zauna?”

“Sorry Baby kinsan can nake aiki dole acan ɗin zan zauna, kinga shiyasaka ma nazo naɗauke ki mu koma can tunda nasan zakiyi fushi dani”.

Cikin dashashshiyar muryan ta tace “No Yaya bazan je ba”.

“Why dear?’ yatambaye ta yana kallon ta

“Ni bana son can nafison Nan”.

Riƙo hannun ta yayi still yana kallon ta yace “yanzu Baby kinfi son kizauna anan ke kaɗai? Why baza ki bini mu tafi tare ba? Idan Daddy yadawo I promise you zan dawo dake kinji?”

Juya kanta tasoma yi cike da shagwaɓa tace “Nooo Yaya bazan je ba”.

Kallon ta kawai yake yi cike da tsananin ƙaunar ta da tausayin ta, yasan halin ta idan takafe a abu to dole sai dai kaƙyale ta, be ce komi ba illa sake mata hannu da yayi yasoma tunani, miƙewa ita kuma tayi tana cewa

“Yaya kaci wani abu?”

Bata jira amsar sa ba kuma tasoma kwaɗa ma ƴan aikin ta jira, kankace me sun fito sun gurfana gabanta

“Uban me kuke yi aciki da bazaku Bama Yayana abinci ba?” Tafaɗa cikin ɗaga murya da baya fita, at the same time kuma tana riƙe da ƙugu tana kallon su

Kafin su buɗe baki suyi mata magana Suhaib ya riga su dacewa “come down Baby sun tarbe Ni mana har naci abinci”.

Hakan yasaka tasauke hannun ta a ƙugu tajuyo tana kallon sa yasakar mata murmushi, takowa tayi tazauna kusa dashi, sai Suhaib ne yabasu umarnin tafiya don ita bata sake bi takan su ba, daga nan hira suka soma yi har lokacin sallan asar yayi sannan yatashi yayi alwala a Toilet ɗin dake parlour yafice masjid

Ita kuma wajen kayan ta da tazubar tanufa takwashe tanufi ɗakin ta, tana shiga ta’ajiye kayan tafaɗa Toilet tasoma wanka, har Suhaib yadawo yashigo ɗakin nata but tana cikin Toilet bata fito ba, don haka yajuya yakoma parlour.

.

_______📖Tana fitowa tashirya cikin ƙananan kaya farar Vest da farar wando Three qweater, komi bata shafa a fuskarta ba tafice dasauri, da gudu take taka matattaƙalan benen har ta’isa cikin parlour’n taƙarisa wajen Suhaib dake zaune yana kallo, Bin ta da kallo yayi har tazauna kusa dashi kana yace+

“Kinyi sallah dai ko don nasan halin ki?”

Ɗan ware manyan idanuwanta tayi tana ɗauke kai tace “eh yaya”.

Be ce komi ba yamayar da kansa kan kallon sa, ita kuma jingina tayi da jikin sa tana kallon, MBC Action yake kallo ana wrestling🤼, miƙe wa kuma tayi tanufi wajen Fridge taɗauko Apple guda ɗaya tadawo tazauna tana ci idanunta na kan t.v, Suhaib kallon ta yayi sannan yamiƙa hannu ya’amsa Apple ɗin yakai baki yagutsira yamiƙa mata, can wrestling yayi nisa RAUDHA tasoma ihu tana kiran sunan Jonecena ganin yana shirin cin Kevin Owne (KO), shi kuwa Suhaib kallon kawai yake yi abinsa, can da tadame sa yajuyo yana kallon ta yaga tsaban ihu bata ma san tayar da raguwan Apple ɗin ba, ɗauka yayi yasoma ci kafin yace

“Baby kiyi ahankali Mana karki kashe min dodon kunne”.

Bata ma san yana yi ba, daga ƙarshe ma gaban t.v ɗin takoma kamar zata shige cikin plasma ɗin, Suhaib sai faman ƙorafin tana kare masa yake yi but taƙi tashi, lokacin da Jonesina yaci kuwa wani irin ihu tasaki tamiƙe tsaye tana tsalle cike da murna, sai kuma tasheƙo wajen Suhaib tana cewa

“Kagani Yaya yaci dama nasan shi zai ci, ina son mutumin nan wlh, kai kuma kafison KO yaci ko?”.

Suhaib yace “no nima ai Jonesina ne masoyina”.

“A’a Yaya kai dai kafaɗa gaskiya”.

Dariya Suhaib yayi yana jan hancin ta yace “wato ƙarya nake miki ko? Kin fiye son kanki da yawa Baby”.

Dariya itama tayi tana shigewa jikin sa tace “sorry yaya bazan sake ba”.

“Ok”.

Daga haka hira suka ci gaba dayi suna ci gaba da kallon su, har sanda aka kira Magriba kafin Suhaib yatashi yatafi masjid, ita kuwa RAUDHA tana nan zaune taci gaba da kallon ta batare da ta damu taje tayi sallan ba ita

Sai da akayi isha’i kafin Suhaib yadawo, lokacin tuni Saude ta gama deener ta jera saman dainnig, don haka yana dawowa kan dainning ɗin suka hau suka ci abinci sannan suka dawo parlour suka dasa hira, sai wajen ƙarfe 10:00pm. Sannan Suhaib yace “su je su kwanta”.

Tana shiga ɗakin ta taji ringing ɗin wayan ta, ƙarisawa tayi tazauna a bakin gado tana ɗaukan wayan, ganin sunan Ramcy yasaka tayi peacking call ɗin, daga can side ɗin Ramcy tace

“Hello Babe yakike?”.

“Lafiya”.

“Nayi ta kiran wayan ki bakiyi peacking ba, lafiya dai ko?”

Sai da takwanta kan gadon kafin tabata amsa da cewa “ƙalau bana kusa ne?”

Ramcy tace “ok yau zamuje Club?”

“No bcoz Yayana yazo sai dai idan ya tafi kuma”.

“Ok na gane, sai munyi waya kenan?”

RAUDHA tace “ok byeee”.

Daga haka aje wayan tayi tatashi tashige toilet, bata jima ba tafito tanufi ƙofan ɗakinta tasaka keey, wajen Fridge taje tabuɗe da makulli tana duba Wine🍷 ɗin da zata sha, ga sunan kala-kala aciki irin su Champagne, Whiskey, Vodka, Beer 🍺, but bakasafai tafi amfani dasu ba don tafi son ƙwayoyi, ko kuma irin su Cocaine da Codeine su tafi amfani dasu, ɗaukan Champagne tayi kwalba biyu ta’isa kan sofa tazauna, sai kuma tatashi takunna t.v tasanya music tare da ƙure ƙara taɗauko Cup takoma tazauna, waƙar take bi tana zuba Champagne ɗin acikin Cup, sai da tacika Cup ɗin damm sannan tasoma sha tana yi tana sake zubawa idan yaƙare

Acan kuwa ɗakin Suhaib yana kwance yana jin kiɗan da RAUDHA tasaka, shiru kawai yayi yana sauraron Music ɗin yana tunanin halin ƙanwar tasa, kuma yasan halin ta duk abinda tace zatayi babu wanda ya’isa yahana ta koda Daddy ne kuwa, idan har ba itace tabar abun don kanta ba, Allah ya ɗaura mata taurin kan tsiya babu wanda ya’isa yasauya mata ra’ayi, tun farko haka tatashi duk abinda take so shi take yi that’s why yanzu ta fi ƙarfin su sai dai su zuba mata idanu tare da nema mata shiriya, and kuma basa ƙaunar laifin ta bare suga fushin ta, suna matuƙar son ta fiye da tunanin me karatu, kar ma ace Daddy yaji, wannan dalilin ne yasaka RAUDHA tasangarce take yin duk abinda ranta ke so

Sai da tashanye gaba ɗaya kwalba biyun da taɗauko, alokacin tuni hankalin ta baya jikinta ta gama buguwa, a wajen barci yaɗauke ta batare da tasani ba, sai ƙarfe 11:30am. Sannan tafarka, shima ɗin Saude ne tazo take ta mata nocking bisa umarnin Suhaib, daƙyar ta’iya buɗe idanuwan ta tana buɗe wa suna rufewa sabida har alokacin giyar da tasha be sake taba, hannu biyu tasanya tariƙe kanta, ta daɗe ahaka kafin tatashi zaune idanuwanta a rufe, ɗaura kanta tayi saman gwiwowin ta still idanun ta arufe tana son komawa barcin, wajen mintuna 30 Saude tasake dawowa tabuga mata ƙofa tana cewa

“Ranki Yadaɗe yallaɓoi na jiran ki ne?”

Buɗe idanuwan ta da sukayi ja tayi tana ɗago kanta, bata amsa ma Saude ba illa miƙe wa da tayi tafaɗa Toilet, tana shiga tasakarwa kanta Shower ko cire kayan batayi ba, ta jima ahaka tana jiƙa kanta da jikin ta kafin tayi wanka tafito, Lotions kawai tashafa sannan tasaka ƴar yaloluwar baƙar riga me dogon hannu da iyakacin ta ƙwaurin ƙafafuwan ta, sai da takwashe kwalban champagne ɗin tasaka a Fridge sannan tarufe da keey kana tasaka Room Slippers tafice

ahankali take taka Steps ɗin benen don har alokacin ba wai giyar ya sake ta bane, idanuwanta da suka kumbure sai faman lumshe su take yi kamar wacce bata iya ganin gaban ta, ahaka taƙarisa kan dainning table inda Suhaib yake zaune har ya gaji da jiran ta ya soma breakfast ɗin sa, zama tayi kan kujeran dake Facing ɗin nasa sannan cikin siririyan muryan ta da kamar tana yin Mura koda yaushe tace

“Good Morning Yaya”.

Suhaib da yaɗago kai yana kallon ta yana taunan arish, ƙare mata kallo kawai yake yi har yacinye sannan ya’amsa mata

“Morning dear, how’s your night?”

“Fine”. Tafaɗa tana gyara gashinta dake  rufe mata idanu don bata saka Ribom ba

Shi da kansa yazuba mata breakfast ɗin yatura mata gabanta tasoma ci, ɗaukan tissue yayi yashare bakinsa yana miƙe wa yanufi cikin parlour’n, zama yayi yaɗau wayan sa yana neman layin matar sa

RAUDHA tunda taduƙar da kanta tana tsakalan abincin bata sake ɗago kai ba har sanda tagama tatashi tadawo kusa da Suhaib tazauna, a time ɗin kallo yake yi itama sai tayi joining ɗin sa bayan ta kwantar da kanta a jikin sa

“Yaya How many days before you go?” Tatambaye sa tana ɗago kai takalle sa

Idanunsa akan t.v yabata amsa

“Yau”.

“Yau kuma Yaya? Why baza ka bari sai kayi one week ba? Gaskiya bana son katafi”. Tafaɗa tana ɗauke kai akansa tare da turo baki

Lokacin ne yajuyo yana kallon ta yace “kema kinsan ina da iyali bazan zauna anan in tare ba, kuma nace ki bini kinƙi ya kikeso in miki?”

Kallon sa tayi sai kawai hawaye suka soma zubo mata, hakan ba ƙaramin ɗaga wa Suhaib hankali yayi ba ganin hawaye a idanun tilon ƙanwar sa, cikin sauri yajawo ta jikin sa yasoma rarrashinta

“Why are you crying my dear? Please stop it”.

Ita kuma har sake matso wasu hawayen take yi da hannu, cikin sangarta tasoma cewa “um um ni bazan Dena ba sai idan kace baza ka tafi ba”.

Suhaib yace “haba Baby kinsan fa tomorrow Monday Ina da office kinga bazai yiwu in zauna anan ba, but i promise sai dare zan tafi kuma zan fita dake muje yawo tare kinji?”

Daƙyar dai da daɗin baki sannan yasamu tahaƙura

“To tashi kije ki shirya mu tafi”.

“To Yaya”.

Tatashi dasauri tahaura sama da gudun ta, Suhaib da yabi ta da kallo girgiza kai kawai yayi cikin zuciyarsa yana jinjina hali irin na RAUDHA, sai kuma yasaki murmushi yatashi shima yanufi upstairs zuwa ɗakin sa

Wando pencil tasaka robber fari ƙal, sai tasaka jan riga wanda yatsaya mata iya cinyan ta, gashinta kawai takama da Ribom sannan tasanya hill shoes fari me igiya, tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba, fitowa parlour tayi nan ta tarar da Suhaib shima yayi shiga na ƙananan kaya sun matuƙar fito da kyawun sa, tana isowa kusa dashi yakalle ta cikin cool voice yace

“Baby meyasaka kikeson fita kanki abuɗe ne?”

Ɓata fuska tayi batace komi ba, don ita ko acikin kayan ta idan ba Hijabin Sallah ba to ko gyale bata dashi, kuma haka tatashi tun farko take yawon ta ko ina

“Please je ki saka Veil kinji?” Yayi maganar cike da rarrashi

Sai da tatura baki kafin tajuya takoma ɗakinta taɗauko Facing Cap Red colour, a hannu tataho dashi ta ƙi tasaka, sai da tadawo sannan ya’amsa shi da kansa yasaka mata, har da juya mata shi gefe in style sannan suka fice, motar sa suka hau suka bar gidan.

Yawo sosai sukayi har yamma suna can kafin daga ƙarshe suka wuce Shopping yayi mata siyayyan duk abinda zata buƙata da wanda take so, ka ma daga kan suturu kayan makeup dasu Chaculates, buskit e.t.c sannan suka dawo gida

Ƙarfe 80:30pm. Drever yakai Suhaib Airport yahau girgi yakoma Abuja.

Ƙarfe 90:30pm. Na dare RAUDHA tagama shirin ta cikin ƙananan kaya kamar yanda tasaba, Black Jeans da yellow ɗin riga me hannun vest tasaka, gaban rigan anyi zanen heart❤️ da stune masu ƙyalƙyali, sai tagyara gashinta tasaka Ribom baƙi tafeshe jikin ta da turare masu ƙamshi da ɗaukan hankali, Hill shoes tasaka me igiya shima baƙi sannan taɗau Wizy back ɗin ta da car keeys tafice, tana shiga motan tabata wuta tayi bakin Gate, nan da nan Gate man yawangale mata ƙofa tafice+

Cikin tuƙin ta na ganganci ta’isa ƙofar gidan su Ramcy acikin ɗan mintunan da basu gaza 8 ba, tana tsai da motan tasoma danna hon kamar zata tashi garin sabida ƙara, da gudu Ramcy tafito tashige motan taja sukayi gaba, yau kam sun ɗan taɓa hira ba kamar ko yaushe ba, don ita RAUDHA ba kasafai tafiye son surutu ba

Suna isa Club ɗin da suka saba zuwa suka fito sukayi ciki, dama ɗabi’ar RAUDHA kenan duk idan tazo club sai ta tiƙa rawa son ranta sannan ne zata nemi wajen zama, haka ma takasance yau tana shiga tafaɗa cikin masu rawa tasoma girgiza jiki, rawa take yi na ban sha’awa da burgewa, sosai taƙware a rawa wanda ko gasan rawan akaje ita zata cinye, ko wani irin waƙa irin rawan sa take yi

Acan gefe kuwa wani matashin saurayi ne zaune yana faman kurɓan Whiskey Yana kallon ta, murmushi kawai yake zubawa sabida tsananin burgeshin da tayi, har yana tunanin yanda zai je wajen  yarinyan tashigo hannun sa, yana nan zaune yana faman kallon ta har yagama kurɓe na cikin Cup ɗin hannun sa kafin yatashi yadoshi wajen, babu zato babu tsammani RAUDHA tana cikin tiƙan rawan ta tana ihun murna taji hannu a kwankwason ta abinda be taɓa faruwa da ita ba, dasauri tajuyo tana kallon saurayin dake gabanta yana faman doka mata murmushi, kafin tasake wani motsi ya riƙo mata hannaye yana faɗin

“Wow Babe you look so cute, kin matuƙar burge Ni fa”.

Saurin janye hannun  ta tayi tana me buga masa wani banzan kallo batare da tace uffan ba taci gaba da rawan ta, shi kuma memakon yaƙyale ta sai zuwa yayi yasake riƙo ta tare da janyo ta jikin sa gaba ɗaya yana cewa

“Common Baby muyi tare mana”.

Wannan karon ma ƙwace jikin ta tayi but batayi wata-wata ba tatsinka masa mari, dasauri yariƙe kuncin sa yana kallon ta da tsananin mamaki, ita ma ɗin kallon sa take yi da kyawawan idanuwan ta fuskarta aɗaure, kaɗa masa hannu kawai tayi alaman gargaɗi sannan taci gaba da rawan ta batare da tasake bi takan sa ba, shi kuwa cikin haushi yake kallon mutanen wajen duk da basu lura da abinda ke faruwa ba, azuciye yanufe ta yadanƙo gashin ta zai wanka mata mari Abokin sa da yake ganin komi yayi saurin damƙe hannun, kallon abokin nasa yayi shi kuma yagirgiza masa kai alamun kar ya’aikata, ita kuwa RAUDHA zafin riƙe mata kan da yayi ne yasanya ta sake taska masa mari cike da tsananin jin haushi

“Whattt..” yafaɗa da ƙarfi idanuwan sa kamar zasu faɗo ƙasa yana ƙoƙarin fizge hannun sa cikin tsawa yace

“Please Deeni kasake Ni in kakkarya yarinyan nan kana ganin abinda tayi min”.

Wanda aka kira da Deeni sake riƙe sa ƙam yayi yana basa haƙuri har alokacin kuma ya ƙi sakar mata gashi, RAUDHA kuwa azaba ya ishe ta sabida yanda yake ƙara jan mata, tayi saurin saka hannu tana son fizge gashin ta but ta kasa

sai alokacin su Ramcy dake zaune can nesa suka soma lura da abinda ke faruwa, dasauri tataho ganin da RAUDHA ake yi, itama tana zuwa tasoma janye gashin RAUDHAN amma duk sun kasa ƙwacewa, da yawa mutanen wajen duk sun taru a wajen ana basa haƙuri bcoz yawancin su sun san ita ƴar wanene, wannan dalilin ne yasaka ma babu wanda ke kula su idan sun zo suke cin karen su babu babbaka

Jawad fa yaƙi sakin gashin RAUDHA adole sai ya rama marin da tayi masa, sai fitina yake yi yana son ƙwace ɗayan hannun sa da Deeni yariƙe

Cikin tsananin ƙulewa RAUDHA tace “dan ubanka kasakar min gashina idan ba uwarka tashuka min ba”.

Har wani rawa jikin Jawad yake yi sabida tsananin ɓacin rai da irin zagin da tayi masa, wani irin ƙarfi da yazo masa take yahankaɗe Deeni yafuzgo ta yasoma naushin ta, nan da nan matasan wurin suka rufar masa suka riƙe sa ana son ƙwace RAUDHA, a time ɗin har ya farfasa mata hanci da baki sai zuban jini suke yi, hakan ya ɗaga ma RAUDHA hankali sosai tafashe da kuka tana jin wani baƙin ciki na turnuƙe ta, daƙyar aka ƙwace ta a hannun sa Ramcy tayi saurin riƙe ta tana duba inda yafasa mata duk hankalin ta atashe, furzo da jinin bakin ta RAUDHA tayi tana ɗago shanyayyun idanuwan ta da suka gama rinewa sabida tsaban wahala tana kallon Jawad wanda ake ta faman riƙe wa har yanzu be huce ba, bata iya cewa komi ba illa fizge jikin ta da tayi daga riƙon da Ramcy tayi mata tabi hanyan fita da mugun gudu tafice, motan ta tashige ko jiran Ramcy batayi ba tabata wuta tabar haraban Club ɗin, sosai take gudu akan kwalta kamar zata tashi sama sabida tsaban baƙin ciki, tana yi tana share jinin dake zuban mata da bayan hannu, Allah ne kawai yakaita gida da babu abinda zai saka batayi hatsari ba, tana zuwa bakin Gate ɗin tabugi Gate ɗin da motan kamar mara hankali, hon take dannawa akai-akai ɗaya kan ɗaya

shi kuwa Gateman sosai yatsorata da yanda aka bugi Gate ɗin, Bama shi kaɗai ba har ta sauran masu aikin gidan sai da sukayo wajen da gudu don suga meke faruwa, dasauri me gadin yabuɗe ƙaramin ƙofa yana leƙawa don be yi tunanin RAUDHA bace tunda bata taɓa yin hakan ba, ganin motan ta yayi saurin komawa yaja mata gate ɗin, ba don Allah ya tsare sa ba da tuni tataka kansa ta wuce sai yayi wuf yakauce, haka sauran masu aikin ma suka dare da mugun gudu ganin yanda tayi kansu suka bata hanya, ko kashe motan batayi ba bare tayi parcking me kyau tafito tanufi cikin gidan da gudu, Direct ɗakinta tashige tafaɗa kan gado tana kuka, sosai ranta yaɓaci har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshinta sabida mugun ɓacin rai, wani irin ƙara tasaki tana miƙewa tasoma wargaza duk abinda ke ɗakin tana yi tana ihu, abunka da taɓararriya abun kuka baya mata kaɗan

Saude da Larai da suka fito daga ɗakin su sukayi cirko-cirko a parlour suna kallon saman suna me jiyo ihun da RAUDHA take yi

Saude tace “yau fa an taɓo Hajiyan mu Allah yasa dai lafiya?”

“Hmm bana tunanin lafiya gaskiya, Yakamata muje mu dubo ta”. Cewar Larai tana kallon Saude

Ita kuma zaro idanu waje tayi tace “ke ki rufa mana asiri, muje tahuce akan mu kenan ko? Kinga gwara mu lallaɓa mukoma ciki muyi gumm hakan shi zai fi mana alkhairi don wlh yau ba ƙalau take ba yarinyan nan”.

Larai tace “maganar ki dutse fa, Ni fa har na soma barci ƙarar buga gate ɗin da tayi yatashe Ni, wlh na tsorata nayi tunanin ɓarayi ne”.

Dariya Saude tasheƙe dashi tana cewa “kai Larai kin cika tsoro wlh”.

“To ai tsoro halas ne, wanga buga ƙofa aradun Allah kiris yarage natsure”.

Saude in banda dariya babu abunda take mata, itama ɗin dariyan take yi suka nufi ɗakin su suna maida maganar

Gaba ɗaya sai da tagama hargitsa ɗakin kafin tanufi Fridge tajido Wine🍷 tazauna nan ƙasa tasoma kwankwaɗa, sha take yi amma hawaye na kwaranya a idanuwan ta, kawai hango yanda Jawad Yakamata yadunga naushin ta a fuska take yi, abinda ba’a taɓa mata ba koda a mafarki, don ita tunda tataso babu wanda yataɓa ɗaukan hannu yabuge ta a iya tsawon rayuwan ta sai shi, sosai take zub da hawaye duk jinin hancin ta da bakinta da suka fashe ya haɗe da ruwan hawayen ta sun yi mata caɓe-caɓe a face, kuma bata damu ba illa kwankwaɗan giyar da take yi, batasan sanda tashanye kwalba biyar ba don bata cikin hankalin ta, kuma hakan be taɓa faruwa ba don iyakacin ta kwalba biyu-uku bata wuce haka, anan tazube takwanta tana kwarara amai kamar zata zubo da hanjin cikin ta, daga ƙarshe barci ne yakwashe ta bayan ta gama surutan ta

_______📖Hasken ranan da yashigo ta windon ɗakinta ne yabugi kyakykyawar fuskarta da yakumbura yayi jazur, hakan yasaka tasoma motsa lumsassun idanuwan ta tana son buɗe wa, daƙyar ta’iya buɗe su sai kuma tamayar tarufe tana me saka hannaye biyu takama kanta sakamakon mugun sara mata da yake yi, ta ɗau tsawon mintuna 10 kafin tasake yunƙurin buɗe idanun, sosai suka sauya kala sukayi ja har wani yalo-yalo suke yi sabida tsaban rinewa, ahankali tasoma motsa jikin ta tana bin ɗakin da kallo, nan taganta  cikin aman da tayi tai dame-dame aciki, fuskarta kuma gaba ɗaya ya bushe da jini, abun da yafaru da ita jiya ne yadawo mata ƙwaƙwalwa tayi saurin runtse idanu tana jin zuciyar ta na tafarfasa, batasan iya lokacin da taɗauka ahaka ba kafin tasoma yunƙurin tashi, daƙyar take iya motsawa sakamakon tsamin da jikinta yayi mata sabida kwanciyar da tayi a ƙasa wanda bata saba hakan ba, miƙewa tayi tashige Toilet takunna shower tatsaya ruwan na dukan ta batare da ta cire kayan jikinta ba, lumshe idanuwan ta tayi tana ɗago kanta ruwan na dukan innocent face ɗin ta, sai da tayi kusan mintuna 15 kafin tacire kayan jikinta tayi wanka tafito ɗaure da towel, gaban gadon ta tanufa tazauna tare da ɗaukan jakanta tazaro wayanta tasoma dubawa, 20missed Call taga an mata, duk na Dad ɗinta ne sai kuma na Ramcy tare da Suhaib, miƙewa tayi riƙe da wayan a hannu tafito cikin ɗakin, ahankali take taka Steps ɗin benen tana saukowa, gab da zata isa ƙasa Larai tafito daga ɗakin su, tana ganin ta dasauri taduƙa tana gaishe ta, fuskar RAUDHA babu walwala tabi ta da kallo kana tace+

“Kishiga ɗakina ki gyara min”.

“To Hajiya”. Cewar Larai tana sake rissina mata

Direct ita kuma RAUDHA cikin parlour’n tanufa tashige cikin luntsuma-luntsuman kujeran tazauna, wayanta tasoma latsawa takira Dad ɗin ta, ringing ɗaya yaɗauka cike da matuƙar damuwa a muryan sa yace

“Sweetheart Ina kika shige ne nayi ta kiran ki baki anwer ba? Lafiya dai ko?”

Cikin muryan ta da yasake dishewa sabida kwanan tyles da tayi tace “Daddy lafiya lau ban tashi daga barci bane”.

Ajiyan zuciya me ƙarfi Daddy yasaki kana yace “har naji daɗi nayi tunanin ko babu lafiya ne gaba ɗaya hankalina ya tashi”.

Shafa kanta kawai tayi bata iya cewa komi ba

“But me yasami muryan ki naji baya fita sosai?”

Shanyayyun idanun ta tasake warewa tana jan hanci cike da jin zafi tace “Daddy a ƙasa na kwana”.

“Subhanallah.. Why dear? Kinsan bana Son wani ciwo yakamaki fa”.

Nan ma shiru tayi don bata son yawan magana sabida zafin da laɓɓan ta ke mata, ga kuma hancin ta dake zugi

Daddy yasake cewa “Sweetheart bari zan kira doctor Sadeeq sai yaduba ki don nasan mura ne yakama ki”.

“A’a Daddy bana so”.

Daddy be sake matsa mata ba don yasan halinta sai ce mata yayi “zai sake kiran ta yanzu yana aiki a office ne” daga haka sukayi sallama ta’ajiye wayan takwanta

Tana nan kwance idanuwan ta a lumshe Larai tadawo tasanar mata “ta gama” hakan yasaka tatashi tanufi ɗakin nata tashirya cikin gajeren wando yellow da yatsaya mata iya cinya, wata ƴar yaloluwar farar Vest tasaka tafaɗa kan gado batare da ta shafa koda Lotions bane a jikin ta sabida ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin nata, har alokacin giyar da tasha be gama sakin ta gaba ɗaya ba don daƙyar take iya buɗe lumsassun manyan idanuwan ta, hannu tasanya tana shafa laɓɓan ta zuwa wajen hancin ta tana runtse idanu, ba wani ciwo taji ba kawai haɓo ne amma yanda take nuna rakin ta zakayi tunanin dagaske ɗin ciwo yaji mata, tana nan kwance Saude tashigo tasanar mata “Ramcy tana jiran ta a parlour” bata ɗago kai ba tace da ita

“Kice tashigo”.

Juyawa Saude tayi tafice taje tasanar wa Ramcy saƙon ta, sai gata taturo ƙofan tashigo idanunta akan RAUDHA da har yanzu take kwance idanunta a rufe, wajen gadon tanufa tazauna agefe tana ci gaba da kallonta tace

“Besty lafiya meke damun ki?” Tayi maganar ne cike da kulawa

Shiru RAUDHA tayi kuma bata buɗe idanu ba bare takalle ta, Ramcy bata damu ba don tasan halin ƙawar tata sai sake cewa tayi

“Nayi ta kiran wayanki baki ɗauka ba shine nataho in duba ki, duk abinda yafaru adaren jiya ya ɗaga min hankali sosai”.

Tana ajiye maganar ta RAUDHA tabuɗe kumburarrun idanunta da har yanzu suke a rine takalli Ramcy, fuskarta babu ko ɗigon fara’a hakan yasaka hankalin Ramcy yasake tashi, cike da son rarrashin ta tace

“Don Allah kiyi haƙuri da abinda yafaru karki saka damuwa acikin ranki, duk abinda yafaru yarigada ya wuce bana Son Inga..”

“Wanene shi?” Cewar RAUDHA tana katse mata maganarta da faɗan hakan

Shiru Ramcy tayi tana kallon ta, itama ɗin idanun ta akanta suke tana jiran amsar ta

“Bansan shi ba Gaskiya don baƙo ne awajen”.

Shiru ne yagibta a tsakanin su naɗan wani lokaci kafin RAUDHA tatashi zaune tana kawar da kanta daga kallon Ramcy ɗin tace

“Ina son ki binciko min ko shi wanene, ina son insan komi daga gare shi”.

Sai tajuyo da kallon ta ga Ramcy taci gaba da faɗin

“Dole zan ɗau fansar abinda yayi min bazan taɓa yafe masa ba, zan nuna masa nafi ƙarfin sa, ki tabbatar kin binciko shi ɗin waye na baki nan da kwana biyu”.

Daga haka tamiƙe tashige Toilet tabar Ramcy anan tana Bin ta da kallo.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

    Alh. El.Mustapha Makamashi wani hamshaƙin me kuɗin gaske ne wanda duk faɗin garin Kaduna da kewaye babu wanda be san shi ba, babban ɗan Siyasa ne da yayi ƙaurin suna ako ina, ya riƙe muƙamai iri da kala har zuwa matakin gwamna, alokacin da yanemi takarar gwamnan Kaduna Allah be sa yaci ba sakamakon juyin mulki da akayi masa, wannan yasaka yafita siyasa gaba ɗaya yakoma harkan kasuwanci tsundum, Asalinsa Bazazzage ne kuma anan Zaria yake zaune, iyayen sa sun daɗe da rasuwa a hannun kawun sa yataso, shima Kawun nasa yanzu haka ya daɗe da rasuwa, yana da gidajen man fetur sun fi biyar agari mabanbanta acikin Nigeria, kuma yana da Companin haɗa auduga agarin Abuja wanda Suhaib ne ke kula dashi, Allah ya albarkace sa da yara biyu rak Suhaib da RAUDHA, tun RAUDHA na ƴar shekara biyar a duniya Allah ya’amshi ran mahaifiyar su, kuma har alokacin Daddy yaƙi aure sabida ƙaunar da yake ma Matarsa.

Babban Katafaren gidan Alh. M. Makamashi yana cikin K.R.G. ne, gidan da RAUDHA kuma ke zaune mallakin ta ne da Daddyn ta yamallaka mata, dawowarta gidan kuma ya samo  asali ne saboda tafiye-tafiyen da Dad ɗin ta yake yi don mutum ne da ba mazauni ba, idan yadawo shine take komawa babban katafaren gidan su acewarta tana jin tsoron gidan.

              ”’RAUDHA”’

Duk yanda zan fasalta muku yanda take ta wuce nan, yarinya ce sangartacciya da iyayenta suka ɓata ta da gata tun tana tsunman goyo, sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, basa son kukan ta bare fushin ta, hakan yasaka tataso babu ƙwaɓa take yin duk abinda taso, tun tana ƴar shekara 15 tasoma harkan shaye-shaye kuma hakan ya faro asali ne daga ƙawayen ta na school, ita ɗin yarinya ce me son rayuwan ƴanci don haka take yin duk abinda taso akuma lokacin da taso babu me hana ta, daga mahaifin ta har Yayanta suna matuƙar ƙaunar ta fiye da kansu, haɗuwar su da Ramcy tun fara zuwan ta Club ne, ita yarinya ce me son rawa don haka take zuwa sabida nishaɗin ta, anan suka haɗu da Ramcy har tasu tazo ɗaya

Ramcy ƴar talakawa ne amma suna da rufin asiri sosai, itama gangararriya ce sosai agidan su, haɗuwan su da RAUDHA kuma sai abun yaƙara yin yawa, a kayan maye babu abinda basu sha

Dad da Suhaib sun daɗe da sanin halin da RAUDHA take ciki sai dai har yanzu sun kasa hana ta abinda take yi sai fatan shiriya da suke mata, kuma hakan yana faruwa ne saboda basa ƙaunar su ɓata mata.

     RAUDHA irin yarinyan nan ne masu bala’in taurin kan tsiya, idan har tace zatayi abu to babu wanda ya’isa yahana ta, idan kuma tace bazata yi ba babu wanda ya’isa yasata tayi, ko kaɗan bata damu da rayuwan kowa ba rayuwanta kawai tasani duk wanda yataka ta to tana ƙoƙarin ɗaukan mataki, bata da sabo ko kaɗan idan har bada mahaifinta ko Ƴayanta ba, har ta da saurayi taƙi yarda tayi sabida a rayuwanta ko kaɗan babu tsarin soyayya, babu namijin da yataɓa burge ta bare har tashiga sabgan sa, ita dai ƙyale ta da harkan shaye-shaye anan tafi auki

Yanzu shekaran ta 19years ne, kyakkyawa ce na gaban kwatance, bata da ƙiban jiki sai dai kuma bata da rama ko kaɗan, kai da ka ganta kasan ita ɗin ƴar hutu ce da jindaɗi, skin ɗin ta fari ne me haɗe da sirkin ja, idanuwanta manya masu gazar-gazar ɗin gashi, haka ma gashin giranta me yawan gaske ne har yana haɗewa, sosai take da kufan gashi ajikinta ko ta ina, kallo ɗaya idan kayi mata baza ka so kaɗauke idanunka akanta ba coz haɗuwarta da tsananin kyawun ta, abu mafi burgewa atattare da ita shine muryan ta, idan tana magana har baza ka so tadena ba yanda muryan ta yake fita ɗan siriri kuma kamar tana mura, hakan na ɗaukan hankalin mutune sosai

Yanzu haka ta gama scondary school🏫 ɗinta tana jiran Admission taci gaba da karatun ta, sosai take da ƙoƙari a makaranta don bata wasa da karatun ta, wannan yasa duk rashin jinta Malamai suna ƙaunarta sosai, kuma ƙoƙarin nata yajawo mata farin jini har take yin duk abinda taso a school ɗin batare da ko harara ta samu ba, sannan kuma ansan matsayin mahaifin ta hakan yasaka da wanda ke sonta don Allah da wanda ke sonta ba don Allah ba duk suna tare da ita.

._______📖 *THE FOLLOWING DAY*

Tashinta kenan daga barcin da tasha tun daren jiya har ƙarfe 02:00pm. Na yau tana sheƙa barci, wanda hakan ko kaɗan baya damunta daɗewan ta tana barci, kuma hakan na faruwa ne idan tabugu takwanta bata iya tashi sai tai ta sheƙa barci kamar za’a sake mata wani daren, ahankali tamiƙe daga kan gadon ta tanufi Toilet tana murza idanun ta, wanka tayi tafito ɗaure da towel ajikin ta, direct gaban dressing mirror tanufa tazauna kan stool tasoma shafa Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi da tsada, bayan ta gama tamiƙe batare da tasake shafa komi ba tanufi Sif ɗin kayan ta taciro, ƴar shimi tasaka Milk colour da ɗan ƙaramin wandon sa shima Milk taɗau wayan ta tafito, ƙafafun ta babu takalmi haka take taka Steps ɗin benen tana saukowa at the same time tana latsa wayan ta, kan kujerun parlour’n tanufa tashige cikin one sitter tana ɗaura ƙafafuwan ta kan Centre table, latsa wayanta take yi tana girgiza ƙafafu, can taɗago kai tana kwaɗa wa Saude kira, kamar tana jira sai gata tafito ta gurfana gabanta+

“Miƙo min Malt”.

Tashi tayi tanufi wajen Fridge tabuɗe taɗauko Mata Maltina takawo mata, bata amsa ba kuma bata ɗago kai daga latsa wayan da take yi ba

“Ranki yadaɗe gashi”.

“Buɗe”. Tafaɗa ataƙaice

Buɗewa tayi tamiƙo mata tasanya hannu ta’amsa, ita kuma tatashi tawuce

Tana nan zaune tana kurɓan Maltinan ahankali tana Chatting wayan ta yasoma ringing, kallon screan ɗin wayan take yi tana ci gaba da kurɓan Maltinan, peacking call ɗin tayi takanga a kunne, daga can Ramcy tace

“Besty komi ya kammala, yanzu haka ina da labarin Saurayin nan”.

“Ok ki taho ina jiran ki”.

Bata jira cewarta ba takatse wayan tana ci gaba da Chatting ɗin ta

Mintuna 20 sai ga Ramcy ta shigo, zama tayi tana kallon RAUDHA da taɗago kai tasauke shanyayyun idanuwan ta akanta, tasan tana jiran tabata bayanan ne hakan yasaka tasoma sanar mata

“Sunan sa

Jawad Abdullahi yana zaune a Tudun wada, sana’ar sa shine harkan zane kuma shagon sa yana bakin titin gidan su ne, anan koda yaushe za’a iya samun shi, sannan shi ɗaya ne ɗa agidan su kuma shi ke ɗaukan  nauyin..”

Tsai da ita tayi da faɗin “wannan bayanin be shafe Ni ba tunda kin gano inda yake”.

Sauke ƙafafuwan ta tayi daga kan Centre table ɗin tamiƙe tsaye tana kai komo a tsakankanin wajen, Ramcy kuma sai kallon ta take yi kamar wata baƙuwa agare ta, tasan halin RAUDHA sosai yanzu haka mugun abu take shiryawa aranta, tasan tunda tayi ninyan ɗaukan fansa babu wanda zai iya hanata That’s why tayi shiru da bakin ta tana jiran taga abinda zata aiwatar

Riƙe ƙugunta tayi da hannayen ta tana sauke manyan idanuwanta da suka sake ƙanƙancewa akan Ramcy ɗin, cije laɓɓanta tayi cike da tsananin ɓacin rai tace “Ramcy ina zan samu Ƴan daba?”

Ramcy zaro idanuwanta waje tayi tana kallon RAUDHA da lokaci ɗaya tarikiɗe babu ko ɗigon rahma a fuskarta, idanun ta sunyi jazur haka ma fuskarta yayi ja tamkar tattasai, haɗiye yawu Ramcy tayi don ita akwai ta da tsoro, cikin tashin hankali tace

“Me kike shirin aikatawa ne Besty? Kar kuma daga baya asamu..”

“Ban tambaye ki wannan ba, ki sanar dani inda zan samu ƴan daba”.

Cike da sanyin murya Ramcy tace “sai dai anemo su tunda kina buƙata”.

Murmushi me kyau RAUDHA tasaki tana wani lumshe idanuwa tana buɗewa, kana kuma takoma tazauna tana harɗe ƙafafu tace “good My Besty”.

Daga haka tayi shiru tana jingina kanta da kujera talumshe lumsassun idanun ta tana jan numfashi, shiru ne yagibta a tsakanin su ita dai Ramcy idanuwanta na kan ta sai dai tunanin abinda take shirin aikatawa take yi da abinda zai biyo baya

“Bana Son in ganki cikin damuwa ƙawata ki saki ranki”. Cewar RAUDHA da tabuɗe idanu tana kallon Ramcy tana me yalwata Innocent face ɗin ta da murmushi

Tasan da cewa tana son Ramcy sosai aranta, haka kawai jinin su yahaɗu shiyasa taɗauke ta tamkar wata ƴar uwanta batare da taji ƙyamarta a matsayin ita ɗin ƴar talaka bace, tayi friends daban-daban ƴaƴan masu kuɗi irin ta amma duk ta watsar dasu duk a dalilin rashin son takura wa kanta, a cewar ta yawan tara friends trouble ne agare ta, tafi son rayuwa ita kaɗai hakan yafi mata daɗi tunda a haka tatashi

Ramcy dai bata iya cewa komi ba sai miƙewa da tayi tana shirin tafiya tace “Besty Ni zan tafi”.

Miƙewa itama RAUDHA tayi tana nufan hanyan dainning tace “kizo muci abinci sai ki tafi”.

Babu musu Ramcy tabi bayan ta suka zauna a dainning table ɗin, tun ɗazu Saude tagama abincin tajera kuma RAUDHAN na kallo taƙi zuwa taci sai yanzu da taga dama, ita dama cin abincin ta sai taga dama ne, don watarana ma bata ci gaba ɗaya sai dai Saude tazo taɗauke shi yanda ta’ajiye, in kuwa zataci baya wuce sau ɗaya a rana ko biyu, kayan ƙwalan da maƙulashe shine abinda take so, shiyasa bata rabo dasu Chaculates, buskit e.t.c

Ramcy tayi saving ɗin su suka soma cin abincin, babu wanda ke magana cikin su har sanda suka gama, RAUDHA tasoma tashi tana share bakinta da tissue tawuce cikin parlour, ita kuwa Ramcy sai da tacika cikin ta tayi nak kafin tamiƙe tataho wajen ta tana cewa

“To zan tafi Besty”.

“Ok”. Ta’amsa mata ataƙaice tana latsa wayanta

Hanyan ƙofa tanufa tafice cikin parlour’n

Tana fita itama tatashi tanufi ɗakin ta, Direct gaban drower tanufa tabuɗe taciri tables tawatsa abaki takoma kan gado takwanta tana tsotso, wayanta ta’ajiye tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana tunani aranta, ta ɗau tsawon lokaci ahaka kafin tabuɗe idanunta da ayanzu suka juye zuwa Red, Remote taɗauka dake kan drower daga kwancen takunna t.v, Bom t.v tasaka da ake waƙa tana me ƙure Volume, tuni ko ina ya game da ƙarar music ɗin, kwanciyar ta tagyara tana me rufe idanuwanta cike da kasala, ahaka har barci yasure ta.

     Sai bayan magriba tafarka, daƙyar tatashi tana sakin hamma tanufi Toilet, wanke fuskarta tayi tafito tafaɗa kan kujera, lumsassun idon ta take ta sake lumshewa tana yamutsa fuska, gaba ɗaya jikin ta ciwo yake mata musamman ma kanta, riƙe kan tayi da hannu tana jan siririn tsaki tamiƙe taɗau Remote takashe plasman, wayan ta dake ringing taɗauka ganin sunan Ramcy, nan Ramcy take tambayan ta “yau zasuje Club ne?” RAUDHA tace “baza su je ba”. Daga haka takashe wayan ta’ajiye, ita dama tana da zuciya idan har tayi fushi da abu to ta barsa kenan har abada, tuni ta cire ran komawa Club ɗin sai dai su nemi wani kuma

Miƙewa tayi tashige Toilet taɗauro alwala tafito, zama tayi tasoma lissafin sallan da ake bin ta na wajen kwana biyu kenan, sai da tagama lissafin ta sannan tamiƙe taɗau Hijabin sallanta tazumbula har ƙasa tasoma gabatarwa, gaba ɗaya sai da talissafo sallan nan kafin tasallame, bata tsaya wani yin addu’a ba tamiƙe tasauya kaya zuwa na barci tahaye kan gado tarufe jikinta da bargo taɗau wayan ta tasoma chatting, sai da taraba dare kafin takwanta.

Washe gari ƙarfe 11:30am. Tatashi, wanka tayi tasaka ɗan guntun wando iya cinyan ta baƙi me baza a ƙasan, sannan tasaka have-Vest ɗin wandon shima baƙi, Ash colour ɗin Jarket mara nauyi taɗaura asaman have-Vest ɗin wanda yatsaya mata iya setting wandon, tafeshe jikinta da turare tare da ɗaure gashinta da jelan a tsakiyar kai, tasaka Room Slippers taɗau wayan ta tafito parlour, directly kan dainning table tanufa taja kujera tazauna, Tea cup tahaɗa me zafi tasoma sipping tana faman latsa waya

Wajen mintuna 30 tana nan zaune kafin taɗago kanta tana ƙwala kiran masu aiki cikin dashashshiyar muryan ta, shiru babu wanda yafito don haka tamaida kanta taci gaba da danna wayan ta, sai da tagama abinda take yi sannan tamiƙe tadoshi hanyan ɗakin su Saude, tana zuwa tahankaɗa ƙofan tashige.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *