RAUDHA CHAPTER 10

RAUDHA CHAPTER 10

_______📖 Sun Isa Bayelsa wajen gabanin magriba, driver ya zo ya kwashe su ya nufi da su tanƙamemen gidan su, gidan flet ne me kyan gaske+

Suna shiga parlour’n matasan duk suka wuce ɗakunan su, inda Ammee ta nuna wa RAUDHA ɗakin da zata zauna, tana fita ta shiga Toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala, doguwar riga blue ta saka kafin ta gabatar da sallah

Bayan ta idar ta fito Parlour, babu kowa sai Ammee da itama zaman ta kenan

Tace, “ƙariko mana ɗiya ta”.

Taho wa tayi ta zauna a gefen ta

Ammee na murmushi tace, “kin ji sabon wuri, da fatan dai ya miki?”

Itama murmushin tayi tace, “Yayi min Ammee”.

“To Masha Allah haka nake so, bari in saka a kawo miki abinci ko kina jin yunwa”.

“A’a Ammee a bari sai anjima zan ci”.

Ammee tace, “to shikenan, kinga dai gidan mu ko. Nasan yanzu dare yayi ne shiyasa babu wanda zai zo sai zuwa gobe zaki ga ƴan uwa, Family House ɗin mu na nan baya ne, mutanen gidan duk ƙannin Uncle ne da matan su da ƴaƴan su, zuwa gobe insha Allahu sai mu je ku gaisa”.

“To Ammee”. RAUDHA tafaɗa tana murmushi.

    A lokacin su Faruk suka shigo da sallaman su

Amsa musu suka yi.

Zannurain sarkin tsokana yace, “Hajiya RAUDHA ga ki ga garin mu, to ya kika ji namu garin? Da fatan dai yayi miki zam-zam ko?”

Dariya tayi tace, “Bro Zannu ai komi zam-zam”. Har da mishi waigi da hannu 👍

Wannan karon dukan su suka yi dariyan

Abubakar yace, “ai sai kin gaji da yawo, Allah ya kai mu dai gobe, gaba ɗaya babu inda bazan zaga dake a garin namu ba”.

Ammee tace, “a’a babu inda ɗiya ta zata je gobe, hutu zata yi, idan ma yawon zaku fita sai dai zuwa jibi, yanzu ku tashi ku je ku ci abinci don ga yi can Asabe ta gama jera wa. Ina Uncle ɗin ku?”

“Yana wajen su Baba Iliya a waje”. Abubakar ya bata amsan hakan

Tashi suka yi su ukun zasu nufi kan dainning, har sun yi gaba sai Abubakar ya dawo yana cewa, “Friend ke fa? Baza ki taso mu ci abincin ba?”

Girgiza kanta tayi tace, “ba yanzu ba”.

“Cabb.. don Allah ke kuwa ba kya jin yunwa? Duk uwar daɗewan nan da muka sha a hanya?”

Hararan sa Ammee tayi tace, “dayake ance maka kowa ma irin ka ne, wuce ka tafi kai dai kaje kaci abincin ka”.

Turo baki yayi yayi gaba

Ita dai RAUDHA sai dariya take mishi

Ammee tace, “ƙyale shi ai halin sa sai shi in dai Abubakar ne”.

Daga nan hira suka ci gaba da yi. Inda Faruk shima ya dawo ya zauna kusa da su ana yi da shi

Sai da aka kira sallan isha’i kafin su wuce masallaci, su kuma RAUDHA da Ammee suka nufi ɗaki don gabatar da nasu.

           *WASHE GARI*

     Ƙarfe 11:30am RAUDHA ta tashi daga barci, wanka tayi ta shirya cikin riga da skert ƴan kanti, rigan me ruwan madara ne me gajeren hannu, sai kwalliya da akayi da jan zare aka saka Stones, sai kuma skert ɗin ja ne, daga ƙasan an zizara kalan ruwan madara, yana da faɗi skert ɗin sai tsagu ta baya, hula ta saka irin na saƙa me tuntu fari, an yi harafin *R* a gaban da jan zare, flet shoes ta zira a ƙafafun ta ta ɗauki wayan ta tafito Parlour.

      Ammee na zaune ita da wata matashiyar yarinya me kimanin shekaru 22, yarinyan tana da girman jiki da tsaho shiyasa idan ka ganta zaka yi zaton ta haura 25yrs.

       Hango ta da Ammee tayi nan da nan ta washe baki tana nuna mata kusa da ita “ta ƙariso”

Sai da ta gaishe ta kafin ta zauna tana kallon yarinyan da itama take kallon ta

Ammee tace, “ku gaisa mana Suhaima”.

Gaishe ta Suhaiman tayi. RAUDHA ta amsa tana murmushi

Ammee ta sake cewa, “ita ce ɗiyar Baba Iliya, Sauran duk sun zo sun tafi kina barci ban tashe ki ba”.

Murmushi kawai RAUDHA tayi

Sannan Ammee tace, “ta je tayi Breakfast in ya so Suhaima ta raka ta zuwa gidan ta gaishe su”.

Tashi tayi ta nufi wajen dainning, sai da ta gama karya wa kafin ta dawo tana tambayan Ammee su Abubakar

Ammee tace, “Abubakar ya shiga school, Zannurain kuma sun wuce wajen aiki da Uncle ɗin ku, shi ya hana Ni ma in tashe ki, yi maza ɗauko mayafin ki ku je ku dawo”.

Amsa mata tayi da, “to” sannan ta wuce ɗakin, bata jima ba ta dawo riƙe da ƙaramin mayafi a hannun ta baƙi, rataya shi a wuyan ta tayi suka fita da ita da Suhaima

A waje suka iske Faruk na waya, da hannu yayi musu alaman su jira sa. Yana gama wa ya kalle su yana murmushi yace, “sai ina kuma? Sarkin yawo an samu ƙawa ko har an soma jan ta?”

Dariya Suhaima tayi tace, “kai yaya Faruk kai kuma. Ammee ce fa tace in raka ta gidan mu”.

Ita dai RAUDHA murmushi tayi, sannan ta gaishe shi tana cewa, “kai baka je aikin ba?”

Idanun sa akan ta yana murmusawa yace, “ban je ba, sai zuwa anjima zan leƙa, ku mu je in raka ku”.

Tare suka jera suka nufi babban gidan nasu, sashi-sashi suka je da RAUDHA ta gaisa da mutanen gidan, sannan suka yaɗa zango sashin su Suhaima, sun jima suna hira kafin suka fito suka yo gida

RAUDHA anan waje ta bar Suhaima da Faruk suna magana ta shigo gida. Tana shiga ciki Ammee ta tambaye ta Suhaiman? Take sanar mata “tana waje ita da Faruk”.

Hira suka soma yi, can sai ga Suhaima ta shigo ta zauna aka ci gaba da yi da ita.

       Suhaima ita ce yarinyan da suke soyayya da Faruk, da tuni sun yi aure amma yace ba yanzu ba, wai karatu zai koma.

      Sosai RAUDHA take jin daɗin zaman ta a cikin wannan Familyn, kowa na son ta kuma yana nuna mata ƙauna. musamman ma kasancewar ta samu Suhaima, tunda ita mace ce tana jin daɗin zaman su tare, kullum suna yawo a cikin gari, idan basu fita da su Abubakar ba, to Suhaima zata ja ta su fita tare, har gidajen ƙawayen ta suke zuwa tare

Ana gobe zata tafi sai ga Rayyan ya dira gidan, lokacin Ammee ce kaɗai zaune a Parlour ya shigo, tace, “a’a kai kuma daga ina? Saukar yaushe?”

“Yanzu Ammee”. Yayi maganar yana zama

“To aikin kuma fa?”

Murmushi yayi yace, “kai Ammee kya bari mu gama gaisa wa ai ko?”

Taɓe baki tayi tace, “to”.

Dariya yayi yace, “Ammee kenan, wai to”.

Itama dariyan tayi tace, “to in ban ce to ba me kake so in CE?”

Murmushi kaɗai yayi sannan ya gaishe ta. ta amsa tana tambayan sa lafiyan sa da aikin nasa

“Alhmadulillah Ammee, ina mutanen gidan?”

“Ai gaba ɗaya ba sa nan, Ni kaɗai ce, yanzu ma Suhaima da RAUDHA suka fice”.

Numfashi yaja kafin ya miƙe yace, “bari in ci abinci Ammee, yunwa nake ji”.

Wuce wa yayi kan dainning, yaci abincin sannan ya wuce ɗakin sa, yayi wanka ya ɗauro alwala ya tafi masjid, kasancewar a time ɗin ana kiran sallan Azahar ne. Daga can sai ya wuce family House ɗin su don gaida su.

        Babu jima wa su RAUDHA suka dawo gidan, a gajiye suka shigo, sabida yawon da suka sha yau ɗin, Suhaima ma bata zauna ba tayi gidan su

     RAUDHA kuma ɗaki ta shige tayi wanka ta saka riga da skert Robber, light green colour, ta fito Parlour ta zauna akan dainning tana zuba abinci.

     Ammee ce ta fito daga kichen tace mata, “ɗiya ta bari na shiga ɗaki na kwanta zuwa anjima, idan Uncle ɗin ku ya dawo ki tashe Ni”.

“To Ammee”. Ta amsa mata tana ƙoƙarin ɗaukar wayan ta dake ring

Abincin da ta saka a baki take tauna wa tana kallon wayan, number ne shiyasa bata yi peacking ba ta ajiye, taci gaba da cin abincin ta, sake kira akayi, sai da akayi mata Three missed calls kafin ta ɗaga tana kara wa a kunne.

      Daga can ɓangaren Zulain ne yayi sallama

   Ta amsa mishi tana tambayar “waye ne?”

Murmushi yayi yace, “Zulain ne Masoyin ki?”

Ɗan jim tayi don ta manta shi ma

Ya sake cewa, “har kin manta Ni Ko? Uhmmm”.

“Sorry i remember.. but aina ka samu Numba na shi ne abinda ya bani mamaki?”.

“Kin san duk wanda yake son abu, to samuwar hanyar da zai bi don mallakar shi ba abu bane me wahala, Sharif Ya samo min wajen yayan ki”.

“Eyya”. Tafaɗa tana kai abincin baki

“Uhmmm me kike ci haka babu tayi?”

Murmushi tayi tace, “ko zaka ci ne? Shinkafa ne. Duk da dai nasan ba iya cin ciman mu zaka yi ba?”

“Wa ya faɗa miki? Ai muna dafa wa acan”.

“Really”.

“Yes sweetie”.

Dariya kawai tayi taci gaba da cin abincin ta tana sauraron sa.

      A lokacin ne Ray ya shigo parlour’n, idanun sa a kanta ya faɗa yana ganin yanda take sakin murmushin ta me ƙara mata kyau, take yaja numfashi yana sake ƙare mata kallo. Ahankali ya soma takowa cikin parlour’n hannayen sa cikin aljihun wandon sa

    Motsin da taji kaɗan shi yasa ta waigo idanuwan ta suka faɗa kansa, tsayar da idanun ta kawai tayi tana kallon sa a ranta tana mamakin ganin shi ɗin

While shima idanun nasa akanta ne, ya nufo inda take, dai-dai ya ƙariso wajen take faɗin, “ok shikenan zan yi missing naka nima, shikenan ko?”

Daga can Zulain yace, “No ban yarda ba, don nace dai ki faɗa ne kika faɗa, amma Ni kaɗai ne nayi missing ɗin ki”.

Ray tuni ya runtse idanun sa saboda wani irin kishi da ya turniƙe shi, tuni zuciyar sa ta raya masa ba da Suhaib ko Daddy take waya ba. Buɗe ido yayi ya sauke a kanta, sai kuma ya ja kujera ya zauna yana ci gaba da tsare ta da ido

Haka kawai taji baza ta iya ci gaba da wayan a gaban sa ba yana kallon ta, don haka tayi wa Zulain sallama ta kashe wayan

Anan Ray ya sake tabbatar da ba su bane tunda ta kira sunan sa

Abincin ta taci gaba da ci batare da ta kula sa ba, sai tsinkayar muryan sa tayi yana cewa

“Meyasaka kika tsane Ni RAUDHA?”

Take ta ɗago manyan idanuwan ta ta sauke a kansa, kallon kallo suke wa juna ko wannen su zuciyar sa na saƙa masa abubuwa a game da ɗan uwan sa. Ganin kallon da yake mata yana saka ta jin wani iri, sai ta ɗauke nata idon tana mayar wa ga Plate ɗin abincin ta, sai dai tambayar da yayi mata yake kai kawo a ranta amma kuma bata da alamar tanka masa

“Why kika tsane Ni nace? Ko gaishe Ni ba kya son Yi a matsayi na na Yayan ki, why?”

Shiru tayi tana caccakan abincin da Spoon ɗin hannun ta, sai kuma ta miƙe tayi hanyar barin wajen

Take ya saka hannun sa ɗaya ya kamo nata, babu zato taji ya janyo ta zuwa jikin sa..

Waro lumsassun idanuwan ta tayi a kansa tana me mamakin abinda yayi mata. Cikin haushin sa tace, “meye haka?” Ta ƙare maganar tana son sauka daga jikin sa+

Be hana ta ba, don shima be san sanda ya janyo ta ɗin ba, kawai dai yabi umarnin zuciyar sa ne, so kawai yake yi yaji ta a jikin sa, be iya ce mata komi ba har ta juya ta bar wajen itama batare da ta sake furta masa komi ba

Ɗakin ta tawuce ta faɗa kan gado, a ranta sosai take mamakin abinda Ray yayi mata, tsaki taja tana birkita kwanciyar ta

“Ko meye ruwan sa dani ne wai? Ni fa na tsani takura a rayuwa ta”. Tafaɗa a fili tana sake jan wani dogon tsakin

Ko kaɗan ba ta son yanda zuciyar ta take damun ta da tunanin sa. Hannu ta saka ta janyo rigan ta tana shinshina, gaba ɗaya ƙamshin sa ya addabar mata hanci, miƙe wa tayi ta hau cire kayan a ranta tana mita, sauya wani kayan tayi ta koma tayi kwanciyar ta ta hau charting da Ƙalby ɗin ta.

      Da dare suna zaune gaba ɗaya a Parlour bayan sun gama cin abinci, Uncle yace da Rayyan “gobe kace zaka tafi ko?”

“Eh Uncle”.

“To sai ku wuce da ɗiya ta tunda itama goben zata tafi”.

“To Uncle”. Ray yace hakan cike da murna a zuciyar sa

Ita kuwa RAUDHA tamkar ma bata ji me ake cewa ba, Game suke buga wa ita da Abubakar

Sai da Uncle ya Kira sunan ta yana cewa, “ɗiya ta gobe zaku wuce tare da Captain, zuwa gobe insha Allahu zan baki kuɗi ku fita da Abubakar ki siya duk abinda kike so ko?”

Murmushi tayi tace, “Uncle ni ba sai ma na siya komi ba”.

“A’a kina nufin ki koma haka babu tsaraba?”

Ammee itama tace, “ai hakan ma bazai yiwu ba, nima zan ƙara miki da nawa, tunda naga ba kya son kayan ku na Hausawa, Ni dai su na siyo miki, da fatan dai zaki saka ko ɗiya ta?”

Murmushi RAUDHA tayi tace, “eh mana Ammee zan saka insha Allahu”.

“To shikenan, zuwa gobe za’a amso daga ɗinki, duk na rigada na bayar an ɗin ka miki”.

“Nagode Ammee sosai”.

“Ɗiya ta babu godiya a tsakanin mu, ai mu mun ji daɗin hutun nan da kika yi mana”.

Zannurain ya amshe zancen da faɗin, “da fatan dai zaki sake ziyartan mu? ba wai da kin tafi kin manta damu ba”.

Dariya tayi tace, “Ni ai ba don ku zan zo ba, don Uncle da Ammee zan sake zuwa, tunda ku ko tsaraban ma babu wanda yace zai bani a cikin ku”.

Gaba ɗaya suka yi dariya har Ray dake sauraron su yana latsa wayan sa

Faruk ne yace, “kar ki damu Lil Sister, mun miki tanadin tsaraba sai zuwa gobe kowa zai baki”.

Murmushi tayi tace, “Thanks Yaya Faruk”.

      A haka dai hiran nasu ta kasance, inda daga baya kowa ya wuce ɗakin sa don kwanciya

RAUDHA na tsaka da saka kayan barcin ta, taji ana mata Nocking a bakin ƙofa, tsayar da abinda take yi tayi tana kallon ƙofan, sai kuma taƙarisa saka doguwar rigan da sauri, don a tunanin ta Ammee ne taje ta buɗe mata, saɓanin tunanin ta sai taga Faruk ne, waro idanu tayi a kansa tace, “Yaya Faruk kai ne?”

“Eh Ni ne Ƙanwa ta”.

“To me kake buƙata?” Ta sake jeho masa tambayar

“Magana zamu yi Sister, amma na rasa hanyar da zan bi don sanar miki, yanzu kuma naga dacewar na faɗa miki tun yau tunda gobe zaki tafi”.

Murmushi tayi tace, “kai Yaya Faruk, to shigo mana”.

Ta matsa mishi a hanyar ya shiga, sannan ta mayar da ƙofan ta rufe.

Kan kujera ya zauna, itama ta zo ta zauna a gefen sa tace, “ina jin ka Yaya, wani magana ne zaka faɗa min har ka kasa sanar min sai a yanzu?”

Idanun sa a kanta yayi murmushi yace, “ba abu ne me sauƙi ba shiyasa na kasa sanar miki, sabida wlh kullum na tunkare ki da maganar sai inji nauyin faɗa, ina son ki RAUDHA! ina ƙaunar ki matuƙa”.

Waro ido tayi tana bin sa da kallo, sai kuma tayi dariya tace, “Yaya Faruk kenan, Allah ka bani dariya..”

“Sabida ban cancanci na so ki ba ko?” Ya katse ta da faɗan haka yana me tsare ta da ido

Sosai taji wani iri a kallon da yake mata, idanun sa iri ɗaya dana Ray, shiyasa ko kaɗan ba ta son suna kallon ta. kau da kai tayi tana cewa, “yanzu dai mu bar zancen nan Bro, dare yayi ina jin barci”. Ta ƙare maganar tana shirin tashi

Riƙe mata hannu yayi, hakan yasa ta dakata daga tafiyan da tayi ninya

“Please Sister, ki bani amsa ta don Allah, wlh ina ƙaunar ki, tun sanda muka zo gidan ku na kamu da soyayyar ki, na kasa sukuni gaba ɗaya sai yanzu da na samu na faɗa miki”.

Numfashi taja kafin ta juyo tana kallon sa tace, “meyasaka kake son yaudaran kanka ne Faruk? Kar ka manta Na san alaƙar ka da Suhaima”.

Cikin marairaice fuska yace, “Yanzu ke nake so ba ita ba, wlh ina matuƙar ƙaunar ki, ƙaunar da ban taɓa wa Suhaima ba, kin ga kuwa ke Yakamata in aura ba ita ba”.

“Kar ka ja maganar da tsaho, bazan so ka ba Yaya Faruk, ina da wanda nake ƙauna a halin yanzu”.

Zai yi magana ta katse sa da faɗin, “Please ka fita min a ɗaki ina jin barci”. Ta ƙare maganar tana janye hannun ta tabar wajen

Shiru yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya tashi ya nufi ƙofa, har ya buɗe zai fita kuma yaja ya tsaya, kallon ta yayi yace, “Bazan haƙura dake ba RAUDHA, zan bi duk ta hanyar da ya dace don mallakar ki”.

Juya wa yayi ya fice batare da ya jira jin ta bakin ta ba, wanda itama bata yi ninyan maganar ba.

        Da fitan sa suka ci karo da Ray da ya fito daga Parlour ɗauko ruwa a gora, mamaki ne ya kama Ray ganin inda ya fito, take wani irin faɗuwar gaba ya riske shi, cikin sauri yace da shi, “Kai daga ina ka fito?”

Shafa kansa Faruk yayi yana sunkuyar da kai

“Ba da kai nake magana ba? Daga ina ka fito? Yayi maganar cikin kakkausar murya cike da fushi

Sosai Faruk ya tsora ta da ganin yanayin nasa, cikin sauri yace, “Brother daga wajen RAUDHA na fito, lafiya?”

Mari ya wanke shi dashi, ya saka hannu ya finciki wuyan rigan sa, cikin tsananin fushi da har idanun sa sun kaɗa yace, “me kaje yi ciki? Me kuka yi?”

Mamaki sosai ya kama Faruk da abinda Yayan nasa yayi masa, wanda be taɓa tunanin haka a gare sa ba, idanun sa kawai yake kallo yana mamakin tsantsan kishin da ya hango a tattare dashi. Cikin sanyin murya yace, “babu kom..”

Be bari ya ƙarisa ba ya daka masa tsawan “ya bar gaban sa”

Da sauri Faruk ya wuce yayi hanyar ɗakin sa, yana me sake mamakin yayan nasa, “kar dai ace shima son ta yake yi?”

Ray kuwa na tsaye a wurin zuciyar sa na tafarfasa, sosai yake jin ƙuna a ransa, sabida abinda zuciyar sa ke raya masa, riƙe kansa dake sara masa yayi, sai kuma ya juya ya nufi ɗakin RAUDHA

Har ta kwanta taji an hankaɗo mata ƙofa, da sauri ta ɗago kai tana kallon Ray da ya nufo inda take, idanu kawai ta zuba masa tana kallon sa tamkar zaki

Gaban ta ya ja ya tsaya yana bin ta da kallo cike da tsantsan fushin da ya nuna a fuskar sa, cikin kaushin murya yace, “keee uban me ya shigo da Faruk cikin ɗakin nan?”

Mamaki maganar nasa ya bata, sai ta miƙe zaune don ta kalle sa da kyau, cikin taɓe baki tace, “kai kuma asuwa da zaka tambaye Ni abinda ya kawo sa?”

Sosai ransa ya sake ɓaci da maganar ta, cikin tsawa yace, “wato kina nan kina halin ki ko? Ke daƙiƙiyar ina ce da baza ki taɓa sauya wa ba? Wato iskancin naki ya tashi kan wasu ya koma kan ƙani na, ƙani na kike bi?”

Sosai RAUDHA tayi mutuwar zaune da jin zantukan sa, sai kawai tabi sa da ido domin ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi bare ta furta wani kalma, duk da kuwa laɓɓan ta sai motsi suke yi, sai dai baƙin cikin zantukan sa yasa ta kasa furta komi, kafe sa tayi da idanun ta ko ƙyafta su ba ta yi

Zai sake yin magana, sai yaji muryan Ammee daga bayan sa tana faɗin, “wai me ke faruwa ne? Menene haka Rayyan lafiyan ka ƙalau kuwa?”

Juyo wa yayi yana kallon ta da jajayen idanuwan sa, be ce komi ba kuma ya raɓa ta yabar ɗakin

Mamaki sosai ya kama Ammee da yanayin da ta gan sa, tabi shi da kallo tana aiyana abubuwa da dama a ranta, sai kuma ta juya ga RAUDHA dake zaune har yanzu ta kasa motsa wa, idanun ta na kafe a inda Ray ya bar wurin. muryan Ammee ya dawo da ita hayyacin ta, sai ta lumshe idanun ta hawaye na cika mata idanu

“Ɗiya ta wai lafiya? Menene ke faruwa? Me Rayyan ɗin ya zo yi wajen ki?”

Matse bakin ta tayi tana buɗe idanuwan ta da suka cika taf da hawaye, cikin rawan murya kamar zata yi kuka tace, “Ammee nima ban sani ba?”

“Baki sani ba kuma?” Ta sake tambayar ta da mamaki

Gyaɗa mata kai tayi don baza ta iya magana ba

Shiru Ammee tayi tana Kallon ta, sai kuma tace, “to meyasa zaki yi kuka Ɗiya ta? Wani abun ya faɗa miki ki sanar dani don Allah?”

Still sake girgiza mata kai tayi alamun babu komi

“Shikenan.. kwanta kiyi barci, zamu yi maganar dashi gobe”.

RAUDHA ba dai tace mata komi ba, ta kwanta tana rufe idanun ta

Itama Ammee juya wa tayi tabar ɗakin tana me rufo mata ƙofa.

Ammee na fita RAUDHA ta buɗe idanunta, sai ga hawaye shaaa sun soma zubo mata

“Ni yake nufin ƴar iska?” Tayi maganar a fili cike da ƙunan zuciya

Duk da ada ya faɗa mata waɗannan kalaman masu ɗaci, amma bata taɓa jin ɗaci da raɗaɗin su a zuciya ba sama dana yanzu, sabida a baya ko kaɗan bata san ciwon su ba, bata san zafin kalman iskanci ba, bata san ma meye ma’anar su ba, da ciwon da yake saka wa duk wanda aka kira sa dashi, alhanin kuma shi ba ya aikata wa

Hawayen ta kawai take share wa tana sake jin tsanan Ray a zuciyar ta, sosai tayi kwanan ƙunci a wannan ranan, don daƙyar barci ya ɗauke ta.

       *WASHE GARI*

    Zuwa la’asar sun gama shirin su, har airport su Zannurain suka rako su, inda jirgin su ya ɗaga.

    RAUDHA dai ta tafi cike da kewar ahalin gidan, sosai tayi shaƙuwa da su wanda bata taɓa yin makamancin sa ba a ƙanƙanin lokaci, tana zaune ne a gaban kujeran Ray, don wajen zaman su ma ba ɗaya bane, ta kwantar da kanta ta rufe idanu tana faman tunani a ranta.

    A airport ɗin Kaduna suka sauka, time ɗin ƙarfe 08:02pm. Ne na dare

Suna fito wa Ray yace mata, “ta biyo shi su shiga mota”.

Kasancewar an zo ɗaukar sa

Bata ce masa komi ba, taja Trolly ɗin ta tayi hanyar barin wajen

Ganin haka ya nufo ta da sauri ya sha gaban ta yana cewa, “ina zaki je kuma? Kin san dare yayi be kamata ki bi hanyar Zaria yanzu ba, tunda kin san doka ce ƙarfe 04:00pm ake rufe hanya, mu je gida na ki kwana, in yaso gobe a kai ki gida”.

Wani kallo ta sakar masa, cike da tsantsan takaici da haushin sa da ta kwana dashi tace, “Ka sani bazan taɓa neman taimako a gare ka ba, ko meye zai same Ni a hanyar nan, na gummaci na bi ta akan dai na je inda kake, Never”.

Ta juya taci gaba da tafiyar ta

Sakato yayi kawai yana bin ta da kallo har ta ɓace wa ganin sa.Tafiya miƙaƙƙa RAUDHA tayi, but bata sami abin hawa ba, duk da kuwa ga taxi nan suna ta yawo, da zaran tace musu “Zaria” sai su ce “baza su ba, an rigada an rufe hanya, ko sun je sojoji za su iya kama su, idan ma basu kama su ba, ƴan kidnapped za su iya ram da su, yanzu duniyar abun tsoro ne, an dena tafiyan dare”+

Memakon ta saduda sai taci gaba da tafiyan ta a titi, batare da ko tsoro ba, duk da kuwa hanyan ba wai babu ababen hawa bane, tamkar ma rana alokacin

Tana cikin tafiyan ne, motan da aka ɗauko Ray ta faka a gaban ta, taja ta tsaya don bata shaida motan ba, tana ganin ya fito ta ɗaure fuska tana me kawar da kai, har ta soma tafiya ya dakatar da ita ta hanyar shan gaban ta

Wayan sa ya miƙa mata fuskar shi shima babu walwala yace, “gashi Daddy Yana son magana dake”.

Kallon sa tayi still fuskarta a matuƙar ɗaure, tamkar ta share sai kuma ta amsa ganin ya sake ce mata “ta amsa”

Hannu tasa ta amshi wayan ta kara a kunne, cikin raunin murya tana shirin kuka tace, “Daddy”.

“My daughter meyasaka baza ki bi shi ki kwana a wajen sa ba? In yaso gobe ki dawo gida. kin san hanya babu kyau, yanzu kidnappers sun yi yawa, kuma kin san halin su yanzu sai su ɗauke ki”.

Silalo wa hawayen ta suka yi, cikin shashsheƙan kuka tace, “Daddy bazan iya bin sa ba, zan je hotel na kwana”.

“Hotel kuma Baby? please ki bi shi kinji, nasan Baby na yanzu ba ta min gardama tana jin magana ta, just ki bi shi, ba na son ki kwana a hotel sabida ɓata gari sun yi yawa, kina da mutuncin ki baza ki kwana a hotel ba, promise Zaki bi shi?”

Gyaɗa kanta tayi tana ci gaba da hawaye, sai kuma ta buɗe baki tace, “Zan bi shi”.

“Yauwa good girl, Allah ya miki albarka uhm? Ki kula da kan ki, i love You”.

“Me too Daddy”.

Ray dake tsaye a gaban ta, kallon ta kawai yake yi yana sauraron abunda take faɗa, sai dai ba ya jin me Daddy ke cewa, tuni ya faɗa kogin tunani wanda har be san sanda ta ida wayan ba, sai jin dogon tsakin da taja yayi. Waro idanu yayi yana kallon ta cikin ido, kasancewar itama ta kafa masa nata idanun tana mishi kallon tsana, wayan da take miƙa masa yabi da kallo, dai-dai da ta sakar mishi wayan zai faɗi, yayi saurin tare wa yana me bin ta da kallo da har ta wuce zuwa motan. Numfashi yaja batare da yace komi ba yabi bayan ta

Baya ta shiga ta zauna

Shi kuma ya shiga gaba kamar yanda yayi ɗazu, Drever’n yaja motan suka yi gaba, har suka kai babu wanda yayi ƙwaƙƙwaran motsi

Cikin Barrack ɗin sojoji gidan nasa yake, yawanci ginin gidajen duk iri ɗaya ne, gidan sa shi ne number 7.

    Drever’n yana parking Ray ya fito, RAUDHA kuwa bata fito ba sai da taga yayi gaba sannan ta fito tare da Trolly ɗin ta, Drever’n ya amsa ya haɗa dana Ray yabi bayan sa, itama sai ta taka tabi bayan su

Tana shiga parlour’n ta tsaya tana me ƙare wa ko ina kallo, ba wani karikitai bane me yawa a Parlour’n, daga kujeru sai Fridge da kayan kallo, sai wasu Flowers guda biyu da akayi ado dasu a gaban t.v’n, sai kuma hoton shi guda biyu manne a bango, ɗaya da kakin sojojin sa yayi matuƙar kyau, tamkar ka ɗauke sa ka saka a aljihu, ita kanta ya burge ta matuƙa, har ta ƙi ɗauke kai a hoton sai da ta gama ƙare masa kallo, sai kuma ɗayan yana duƙe tamkar yayi ruku’u yana dariya, farar riga ce a jikin sa sai wandon soja…

Maganar Ray ɗin ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka wajen ƙare wa hotunan kallo, sai ta zubo masa idanu cike da jin haushin kanta da ta tsaya tana kallon sa a hoto, don ta nuna masa ba burge ta yayi ba, sai ta taɓe baki ta furta, “ko kyau! Sai mugun hali”.

Ray ya ji ta sarai, sai yayi murmushi kawai yana yin gaba zai shige ɗaya daga cikin ƙofofin biyu da suke jere, sai da ya kusa shige wa sannan yace da ita, “ta shiga ɗaya ɗakin”

Taka wa tayi ta buɗe ƙofan ta shiga tare da Trolly ɗin ta da ta ɗauka a Parlour, babban ɗaki ne me Toilet a ciki, gado ne kawai da sip, sai lallausan carpet ɗin ƙasa, baya ga haka babu komi ciki. Kan gadon ta nufa ta zauna tana me zare veil ɗin da tayi rolling da shi a kanta, babu abinda take yi sai faman taɓe baki tana bin ko ina da kallo, tare da karkaɗa ƙafafun ta dake lilo ƙasan gadon

Kamar shuɗewar mintuna goma sai ta miƙe ta shiga Toilet, wanka ta soma yi ta ɗauro alwala, ta saka riga da wando masu taushi na barci, sannan ta ɗaura Robber White Hijab tayi Sallah, bayan ta idar ta koma kan gadon ta kwanta tana me zame hijabin daga jikin ta. Shiru tayi tana tunani a ranta, sosai take jin yunwa a wannan gaɓar, amma kuma ba shi ne damuwar ta ba, illa kewar Ƙalby ɗin ta da ya addabi jiki da ruhin ta, yau kwata-kwata ba su yi waya ba, tunda tun jiya rabon ta da shi, ga shi ko text be tura mata ba, ta hau social media Nan ma bata ga saƙon sa ba, duk da kuwa ta ga ya hau, kuma ta tura masa saƙo be buɗe ba, ta rasa meyasa yau yaƙi kula ta, har kiran sa tayi ya ƙi ɗauka, daga ƙarshe ma sai ya kashe wayan, ko kaɗan bata san laifin da tayi masa ba, duk da kuwa tana ji a jikin ta fushi yake yi da ita..

     Ajiyan zuciya ta sauke, kana ta janyo wayan nata ta sake kiran sa, wannan karon ya shiga, sai dai har ta gama ring be ɗaga ba, sake kira tayi, anan ne yayi peacking

Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sauke har tana lumshe idanu, sai ta kara a kunne kawai ta sakar masa kuka

Shiru Ray yayi a ɓangaren sa, yana me sauraron kukan nata dake shiga masa can cikin kunne, yana saukar masa da kasala, lumshe idanu yayi batare da yayi ƙoƙarin dakatar da ita ba, domin kuwa sosai sautin kukan nata yake masa daɗi

Ganin yayi banza da ita, sai ta ƙara Volume ɗin kukan nata, har da buga ƙafafu

Dariya ne ya so kufce masa, domin kuwa yana jiyo buga ƙafan da take yi akan gadon, danne dariyan sa yayi yace, “Sweetheart mene ne?”

Cikin kukan take cewa, “ba kai ne ba!”

“To me nayi uhm? Faɗa min inji?”

“Ka ƙi kula Ni yau gaba ɗaya, kuma yanzu na kira ka, but kana son share Ni har kaƙi rarrashi na”.

Murmushi me sauti yayi, cike da farin ciki a zuciyar sa yace, “I’m so sorry pretty uhm? Ki yafe wa Ƙalby bazai sake ba”.

“To sai ka faɗa min abinda nayi maka yau kaƙi kula Ni”. Tayi maganar cikin shagwaɓa

Lumshe idanuwan sa yayi, cikin sanyi yace, “Babe zaki kashe Ni da wannan shagwaɓar taki”.

Daɗi taji a zuciya, sai ta sake ɓare baki ta hau masa shagwaɓa

“Pretty idan na kama ki ko!” Sai ya cije bakin sa yana me jan numfashi sosai

Ita kuwa dariya ta ƙyalƙyale masa dashi tace, “to ka sanar dani meyasa ka ƙi kula Ni yau?”.

“Ina fushi dake ne sabida kin min laifi”.

Waro ido tayi, sai kuma ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, “to me nayi maka?”

“Kin yi min alƙawarin Ni kaɗai zaki so, Ni kaɗai zaki kula a matsayin wanda zaki aura, amma kuma kina kula wasu”.

Sosai wannan karon ta waro idanun ta waje, cikin mamakin sa tace, “ban gane ba Ƙalby, ya akayi kasan cewa ina kula wani?”

“Ok da gasken kenan kina kula su?” Yayi maganar cike da kishin da dole sai ka gane ran sa babu daɗi

Tayi saurin cewa, “no Ƙalby, na rigada nayi maka alƙawarin kai kaɗai zan so, kuma kai zan aura, har yanzu kuma ban karya alƙawarin ba, har yanzu kai ne kaɗai wanda nake kallo a matsayin miji na uban ƴaƴa na, kai kaɗai ne a zuciya ta, domin tuni narigada na baka kyautar ta,”.

Sosai Ray yaji daɗin zantukan ta, har yana jin wani irin sanyi sosai wanda tun jiya be ji irin sa ba, gyara zaman sa yayi daga kan kujeran da yake zaune, sannan yace, “Allah ko Baby na Ni kaɗai?”

Murmushi tayi tace, “kana tantama ne?”

“A’a na yarda dake ɗari bisa ɗari, I love You My pretty”.

“Me too dear, amma yaushe zamu ga juna, na ƙosa wlh”. Tayi maganar cikin shagwaɓa

“Pretty kenan! To ki saka mana rana”.

“Da gaske Ƙalby? Tafaɗa da farin ciki

“Da gaske Baby na, ai nima na ƙosa mu riƙa soyayyar fili ba na waya ba”.

“To shikenan, ka bari zuwa bayan bikin Besty na sai mu haɗu, sabida daga yau har Sunday ba na da time”.

Yace, “amma kiyi min alƙawari duk rintsi duk wuya baza ki taɓa rabuwa dani ba, Ina jin tsoro Pretty, Ina jin tsoron idan kin ganni ki ce ba kya so na, baza ki aure Ni ba, idan kuwa haka ta faru mutuwa zan yi”.

“Ƙalby wlh nayi maka alƙawari, duk rintsi duk wuya ina ƙaunar ka, bazan taɓa rabuwa da kai ba, nayi maka alƙawari zan aure ka”.

Murmushi yayi me sauti yace, “Nagode Baby na, Allah ya bar min ke”.

“Ameen ameen Ƙalby”. Itama tafaɗa tana dariya

Daga nan sun taɓa hira kaɗan kafin suka yi sallama, ajiye wayan tayi tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar kogin tunanin Ƙalby ɗin ta, murmushi kawai take zuba wa idanun ta a rufe

Numfashi taja kafin ta buɗe idanun tana ɗaura hannayen ta kan shafaffen cikin ta, sosai take jin yunwa don haka dole ta nemi abinci taci, tsaki taja tana tashi zaune tace, “bari inje wajen wancan mahaukacin sojan nace ya bani abinci, wlh yunwa nake ji bazan iya kwana a haka ba, dole ne ma yasan yanda zai yi dani…”

Bata ƙare maganar ba taji saukar muryan sa yana faɗan, “wato Ni ne mahaukaci ko?” Yayi maganar yana tsaye bakin ƙofa riƙe da handle ɗin, idanun sa a kanta

Waro ido tayi tana ɗan ja baya, mamaki ne ya kamata don bata ji motsin sa ba ko kaɗan har ta miƙe tana shirin fita

“Ki bar zaro min idanu ki amsa min tambaya na, Ni ne mahaukacin ko?”

Ɗaure fuska tayi tana me kawar da kanta, tare da kumbura baki, sai kuma ta taɓe shi tana me ɗage kafaɗa tace, “kafi kowa sani ai”.

Murmushi Ray ya saki yana me takowa cikin ɗakin sosai, ledan da ke hannun sa ya miƙo mata yana me faɗin, “zan ko nuna miki Ni mahaukacin gaske ne, na kula sabida ban ɗaukar mataki a kanki kike yi min duk abinda kika ga dama, komi dake bakin ki kina faɗa min batare da kin ji tsoro na ba, kin manta Ni Yayan ki ne, zan iya miki hukunci a duk sanda naga dama”.

Dogon tsaki taja cike da haushin maganar sa ta kalle sa tace, “waye kai? Ban san ka ba, kuma baka isa ka zama yaya na ba, idan ka isa kai kai ne, ka ɗauki mataki a kaina sannan zan tabbatar, ko kaɗan ba na jin tsoron ka domin kuwa baka kai matsayin ba, baka isa RAUDHA ta saka ka a cikin lissafin ta ba..”

Bata san sanda ya iso gare ta ba, sai ji kawai tayi ya murɗe mata baki, yana faɗin, “I will teach you a lesson now”.

Be bata damar ma magana ba ya saki ledan hannun sa ya janyo ta jikin sa, sai kawai ji tayi ya haɗe bakin su waje ɗaya

Wani irin zaro ido tayi waje, babu shiri ta haɗiye yawu cike da tsantsan tsoro da mamakin sa.Sosai Ray yake tsotson bakin ta tamkar ya samu Lolipop, ko kaɗan yaƙi bata damar da zata iya ƙwatan kanta, duk da kuwa kici-kicin da take yi domin gujewa abinda yake mata+

Sosai ta gaji dole ta ƙyale shi ta dena ƙoƙarin ƙwace kanta, sai kawai ta soma zubar da hawaye tana sauraron saƙon da yake bata, rufe ido kawai tayi zuciyar ta na ƙara cinkushe wa da tsanar sa

Ray sai da yaga ya kusa losing control ɗin sa, kafin yayi ƙarfin halin sakar mata bakin ta yana me ja baya a hankali cike da kasala

Kallon ta kawai yake yi yanda ta tsaya tana ta kwararan hawaye idanun ta arufe

“Daga yau ki sake yi min rashin kunya, tara ki nake yi dama, kuma duk zan fanshe, idan hakan ta sake faruwa a tsakanin mu, to ba iya nan zan tsaya ba, don dai Ni ina da tsoron Allah ne ba irin ki ba”.

Juya wa yayi ya wuce ƙofa zai fice

A lokacin ne ta buɗe jajayen idanuwan ta tana kallon sa, cikin ƙunan zuciya tace, “har abada bazan taɓa yafe maka ba, na matuƙar tsanar ka fiye da mutuwa ta, komi da komi dake tare da kai ba na ƙaunar sa, MAHAUKACI KAWAI”. Taƙare maganar cikin ɗaga murya, don ba kaɗan ba kalaman sa suka yi mata ciwo

Be ce mata komi ba, illa murmusawa da yayi ya buɗe ƙofan yana shirin fita

Hakan sai ya ƙara mata zafi a zuciya, domin so take yi ta ƙuntata masa kafin ya bar ɗakin, cikin tsanar sa tace, “Mutanen kirki ba sa nuna kansu, sai dai ayyukan su su bayyana su, kai ko kaɗan ba ka a cikin su, domin ayyukan ka tuni sun bayyana min kai tantirin ɗan iska ne, masu fake wa a cikin mutanen kirki, alhanin irin ku su ne ɓatattu”.

Sosai kausasan kalaman ta suka taɓa sa, juyo wa yayi yana kallon ta ido cikin ido, sun ɗau two minutes suna aika wa junan su kallo, kafin ya tako ahankali zuwa wajen ta, har yanzu kuma idanun su na a cikin juna, sai da ya tsaya gaban ta kafin yace, “kina bani mamaki RAUDHA, idan kina yin wani abu sai in ga tamkar baki da wayau, koda yake har yanzu ke yarinya ce, amma kuma ina me miki nasiha ki zama na gari a duk inda kike, har yanzu da sauran ki a cikin rayuwar nan, abu ɗaya yake hana Ni faɗa miki kalaman da zaki dauwama kina me dana-sani, dana-sanin rayuwar ki, amma kuma..”

Sai yayi murmushi yana fito da harshen sa waje, ya karkaɗa sa yana cewa, “amsa ɗaya nake so ki bani, ɗaya tak. Da Ni da ke ina son sanin waye ɗan iska?”.

Sai yayi dariya yace, “ba ma sai kin bani amsa ba shalele na, Ni ai ƙaramin ƙwaro ne a iskancin domin ban san komi ba, ke kuwa da, Kin dauwama ne a cikin ta tun kina ƙaramar ki, ga shi har yanzu kin kasa gane Allah ya faku bare ki tuba, ko ba ke ce na kama ki jiyan nan da ƙani na kuna abinda kika saba ba? To ki soma gyara kanki kafin ki ce zaki zagi wani”.

Juya wa kawai yayi ya bar ɗakin batare da ya jira cewar ta ba, yana fita ya zauna kan sofa a parlour, yana me ɗaura kansa jikin kujeran tare da lusmshe idanu

Allah ya sani shi kansa ya san yaji baƙin cikin kalaman nan da ya faɗa mata, amma ya zai yi? Yana son ne ya saka mata zafi a zuciya, ta yanda zata gyara halayen ta, domin idan taji raɗaɗin maganar sa wataƙil ta iya gyara wa, amma kuma yaga da alamu yana son ɓata rawan sa da tsalle, ko in CE ma tuni ya ɓata, kullum daɗa ƙara tsanar sa a zuciyar ta yake yi, shin ya zai kasance idan har ta gane shine masoyin ta taƙi shi? Yasan babu ta yanda za’a yi RAUDHA ta so shi, amma ya zai yi? Wani hanya zai bi don cire tsanar sa dake zuciyar ta, ya rasa ya zai yi, duk da kuwa sosai yake danne duk wani ɓacin rai da take ƙunsa masa, ya kasa ɗaukar mataki, idan da ace babu soyayyar ta a ransa, da tuni ya aikata mata abinda baza ta taɓa manta sa a rayuwar ta ba.

                    🔵🔵🔵

    Tun sanda ya soma maganar sa hawayen fuskar ta suka ci gaba da tsiyaya kamar an kunna famfo, yana fita ta fashe da kuka tana zame wa ƙasa anan, haɗa kai da gwiwa tayi ta soma rusa kuka cike da baƙin ciki a zuciyar ta, “shin me tayi wa bawan allan nan ne ya tsane ta? Meye alaƙar ta dashi ne da yake shiga rayuwar ta?” Babu abinda ke ƙona mata rai sai kallon ƴar iska da yake mata, kalman iskanci da yake jifan ta dashi, shi yafi komi ƙona mata rai

Ɗago kai tayi da fuskar ta yayi caɓe-caɓe da hawaye, cikin kuka tace, “I hate you RAYYAN! I hate you so much!”

Ta sake fashe wa da wani sabon kuka, ta jima a wajen a zaune tana ta faman kuka taƙi ta dena, dama RAUDHA ga taurin kai da naci. Ahaka ta kwana a zaune bata ko jirga ba, duk da uwar yunwar dake addabar ta, amma ta gummaci ta kwana a haka, da dai taci abinda ya kawo mata

Da asuba ta farka daga figaggen barcin da ya ɗauke ta, daƙyar ta iya ɗago kanta da ya riƙe yayi mata zafi, idanuwan ta kuwa sun yi luhu-luhu alamun tasha kuka da kuma rashin barci, gaba ɗaya fuskar ta yayi jazur tamkar tattasai

Miƙe wa tsaye tayi daƙyar, ƙafafuwan ta sun rigada sun yi tsami, dole ta kasa taka wa, ta daɗe tana yarfe ƙafafun kafin ta samu su yi mata dama-dama, ahankali ta taka ta wuce Toilet ta ɗauro alwala, sallah tayi da Hijab, sannan ta miƙe ta ɗauki veil ɗin ta da ta cire ta mayar

Baza ta iya sake yin wasu mintoci a gidan nan ba, ko kaɗan ta tsani komi da zai fito daga Ray, ba don jiya dare yayi ba, da adaren jiyan zata bar gidan, sai kuma ta yanke shawaran da asubahin nan zata bar masa gida

Tana gama rataya veil ɗin taja Trolly ɗin ta tafito Parlour, ƙofa tayi ta buɗe ta fice, dayake ya fita zuwa Masallaci kuma be dawo ba, har tabar haraban gidajen bata haɗu da kowa ba, tafiya sosai miƙaƙƙiya tayi har tafito bakin titi, zuwa lokacin daƙyar take iya ɗaga ƙafafun ta, amma haka ta daure take ta jan su har ta fice bakin titi, a lokacin gari ya fara haske sosai har ababen hawa sun soma wuce wa, nan ta tare keke napep tace “ya kai ta Kawo tasha ta hau mota”

Suna zuwa ta samu taxi ta shige, ita ce ta farko, amma dayake ta ƙosa ta bar wajen, kar ma ya biyo bayan ta, tace ma me motan “su tafi zata biya sa kuɗin” haka yaja suka bar tashan suka yo hanyar Zaria.

                🔵🔵🔵

     Sanda Ray ya tashi duba ta wajen ƙarfe 08:40am ne, koda yaga ba ta cikin ɗakin hankalin sa yayi matuƙar tashi, tunda yaga babu Trolly ɗin ta ya san tafiya tayi, nan ya biyo hanya ko zai ganta, amma Allah be sa ya ganta ba, dole ya ɗauki waya ya soma kiran ta, sai dai alokacin RAUDHA na cikin mota tana kallon wayan taƙi ɗauka, gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikin ta, ga barci dake damun ta shiyasa taƙi ɗauka

Sai da taga ya ƙi ya dena kiran, kafin tayi peacking tana ƙara wa a kunne

Sallama yayi mata. Ta amsa shi cikin dashashshiyar muryan ta da ya ƙara shige wa sosai sabida kukan da tasha

“My Pretty lafiya dai naji muryan ki ba ta fita, ina fata dai lafiya ba wani abu ne ya same ki ba?”

Sai da taja majina tana jingina bayan ta da jikin kujeran kafin tace, “lafiya”.

“Anya? ban yarda ba, but naji kamar ƙaran ababen hawa, ina zaki haka da sassafen nan?”

“Ƙalby gida zan je, kasan dama nace maka ina Kaduna ne”.

“Ok yanzu har kin hau mota ne, ko kuma Yayan naki zai kai ki?”

Gajeren tsaki taja tace, “wa yace maka yaya na ne shi? Allah ya kiyaye”.

Dariya ne ya so ƙwace masa, sai dai ya daure yayi murmushi yana cewa, “amma ai a matsayin Yayan ki yake, ko ba komi ma ya girme ki”.

“Ƙalby ka dena min maganar mutumin nan, idan ba so kake yi mu ɓata ba, raina a ɓace yake wlh”.

“I’m so sorry Pretty, Allah yasa dai ba shi ne ya ɓata miki rai ba?”

Cike da jin haushi tace, “shi ne mana, dama idan ba shi ne ba, waye ya isa ya ɓata min? wlh Ƙalby na matuƙar tsanar sa fiye da komi dake duniyar nan, da za’a bani bindiga wlh sai na harbe shi, babu wanda ya taɓa shiga rayuwa ta ya muzguna min irin sa, a kansa na soma kwana da baƙin ciki, kuma na tashi da shi, a kan shi nake zubar da hawaye a koda yaushe, bazan taɓa yafe masa ba”.

Sosai jikin Ray yayi sanyi ƙalau, muryan sa a sanyaye yace, “Why kika tsani bawan Allan nan haka? Ni naga tamkar gyara yake miki, mene ne aibun shi a ciki?”.

Lumshe ido tayi batare da tace komi ba

Sai da ya kira sunan ta sannan tace, “idan har kana so mu ci gaba da rayuwa a haka, kar ka sake min maganar sa, idan kuma ba haka ba”. Sai tayi shiru kawai batare da ta ƙarisa ba

Murmushi yayi me ciwo yace, “wato nima zaki tsane Ni Ko? Ke kenan babu wanda ya isa ya faɗa miki Gaskiya? Pretty ki bi duniyar nan a sannu, komi kika gani a..”

Ƙit tayi cancel ɗin kiran, sannan ta kashe wayan gaba ɗaya tana me ajiye wa saman cinyan ta, rufe idanuwan ta tayi. Bata sake motsi ba har sanda Drever’n ya sanar mata sun iso Zaria, sai anan ta buɗe ido ta faɗa masa inda zai kai ta.

    A bakin tanƙamemen gate ɗin gidan su ya faka, tayi masa maganar yayi horn

Horn ɗin yayi kamar yanda ta umarce shi

Me gadi ne ya leƙo, ganin taxi sai ya fito ya taho, har zai fara faɗan sa kamar yanda ya saba sai ya hangi RAUDHA dake zaune a baya, nan ya washe baki ya soma kwarara mata gaisuwa tare da maraba

Ɗaga masa kai kawai tayi, sannan tace masa, “ya buɗe musu ƙofa”

Da saurin sa kuwa ya koma ya buɗe, me Taxi yaja suka yi ciki

Dayake da tafiya sosai, shiyasa taƙi sauka tun daga wajen, har bakin ƙofan parlour’n gidan ya kai ta ya ajiye, sannan tafito ta miƙa masa 5k da ta zaro

Masu aiki biyu maza da suka hango ta, su suka ƙaraso suka yi mata sannu da zuwa, sannan ɗaya yaja mata Trolly ɗin ta suka yi ciki.

      A lokacin babu Daddy a gidan ya fita, tunda ta tambaya akace mata ba ya nan, sai ta wuce ɗakin ta , wanka ta soma yi ta hau yin breakfast da tasaka aka shirya mata, sai da taji ta ta ƙoshi sosai sannan ta zauna tana me jingina da kujeran ta lumshe idanun ta, bata sake motsa wa ba har wajen shuɗewar mintuna 20, lokacin sosai idanun ta suka rufe da barci, kan gado ta faɗa ta hau sheƙawa.

      Time ɗin da Daddy ya dawo, sannan tana barci, shiyasa be tashe ta ba har sanda ta farka don kanta, anan ne suka gaisa har yake tsokanar ta “ya ga ta sauya ne, duk tayi yaushi, ko dai tafiyan ne ya sata haka?”

Dariya tayi tace, “Daddy kenan, ai ba yau na saba tafiyan ba, kawai zaman mota ne daga Kaduna zuwa nan ya gajiyar dani”.

Shafa kanta yayi yana murmushi yace, “Daughter kin ganki ko? Akwai ragwanta wani lokacin, amma Captain ɗin ya kawo ki, ko saka wa yayi a kawo ki?”

Tana jin sunan sa ta sauya fuska tana ƙara lafe wa ajikin sa, kamar bata so tayi maganar tace, “Ya saka an kawo Ni ne”.

Domin tasan idan tace motan haya ta hau, ya dinga maganar kenan, ita kuma ta tsani duk wani magana da ta shafe sa a yanzu

Saurin ma sauya hiran tayi da maganar bikin Ramcy, haka suka ci gaba da hiran su, inda Daddy yake shawaran abinda Ya kamata yayi wa Ramcy ɗin a bikin

RAUDHA kuma ta bashi shawaran yayi mata kayan ɗaki

Yace, “ok babu damuwa, yanzu kuma zan buga waya a samo mata masu kyau koda a nan Nigeria ne, tunda naga yanzu su ma suna yin kaya masu kyau, zan kira mahaifin ta, idan za su yi mata sai su fasa su yi wani hidiman da kuɗin”.

“Yauwa Daddy, Amma Daddy a ƙoƙarta idan na waje zai samu ayi mata, ka ga yanzu ana fita Abroad sosai ba kamar watannin baya ba”.

“To my dear duk yanda kika ce ai, insha Allahu za’a samu ma kafin bikin”

Daga haka hiran suka ci gaba da yi, inda RAUDHA take ta mishi lissafin abubuwan da zasu kashe daga ita har Ramcy ɗin na hidiman biki, yace, “zai bata kuɗin”.

Washe gari RAUDHA ta haɗa Trollyn kayan ta ta wuce gidan su Ramcy, a ranan ma suka koma gidan RAUDHAN, ita da Ramcy da wasu tsirarun ƙawayen ta calss mate ɗin ta da suka zo mata biki, acan za su zauna ayi mata gyaran jiki da RAUDHA zata ɗau nauyi, da duk wasu shirye-shirye da ya kamata su yi
Duk a ranan ne dai me gyaran jikin ta iso aka soma wa Ramcy gyaran jiki, su kuma su RAUDHA da sauran ƙawayen su ne masu fita suyo abubuwan buƙata, duk a motan RAUDHA ake fita, duk da su ma ƴan matan ƴaƴan masu shi ne, wasu ma aciki da motan su suka zo, ga su suna da iyayi irin na gogaggun ƴan bokon nan ƴaƴan masu hannu da shuni, amma tunda suka ga RAUDHA sai suka raina kan su, ko wacce cikin su tana so ta shige mata
Ita kuwa ko kallo basu ishe ta ba, idan ma tana son yin abu, sai dai ta tambayi Ramcy, ita kuma Ramcy sai ta haɗa ta dasu su taimaka mata, shiyasa suke fita tare, ahaka har suka soma shige mata tana kula su, shima sai su ne suka tsulmo ta cikin zancen su
Itama RAUDHA har da ita akayi mata gyaran jikin kaɗan, ta ma ce ba ta so but Ramcy sai da tasaka akayi mata
Komi sun shirya agidan, inda suka koma gidan Aunty Nafeesa ana gobe bikin, don acan za su yi taron su na ƙawaye.
      Gidan su Ramcy ya cika maƙil da mutane, domin babu laifi suna da dangi sosai, musamman dangin Mahaifiyar ta, su ma sun zo da yawa, duk da ba Mahaifiyar a raye amma sun yi mata kara sosai, haka zalika Amaryar Baban su ma tayi gayya sosai, tunda ita a wurin ta ta riƙe su Ramcy tamkar ƴaƴan ta ne, sai kuma dangin Mahaifin ta, duk da su anan Zarian suke ma.
      Doctor Salman sunan Mijin da Ramcy zata aura, anan Zarian yake, a cikin samaru, babu laifi suna da hali sosai, don zan iya cewa ma, duk a cikin ƴan uwan sa ya fi su samun kuɗi, lokacin da Ramcy take zuwa A.B.U Zaria suka haɗu dashi, inda shi kuma ya je karantar wani course, kamar da wasa dai abun nasu, domin ita Ramcy taƙi ba shi damar yaga gidan su ma, a school kawai suke haɗuwa su gaisa, har ma sun rabu daga baya, tunda shi shekara ɗaya kacal yayi a lokacin. Sai kuma watarana kwatsam ya zo anguwan su wajen wani abokin sa, suka sake haɗuwa ita kuma ta fito gidan Aunty Nafeesa, anan yake faɗa wa abokin nasa “ita ce wacce ya so ta bashi dama taƙi” shine abokin yace “ai kuwa ga gidan su can idan kana so in Kai ka, ai Yayan ta Aboki na ne, Lawan”.
“Haba dai kana nufin Lawan Jaga?”
“Shi fa”. Abokin nasa ya sake tabbatar masa
Da wannan hiran nasu Salman yace, “ai kuwa zai sake dawowa, dama gida an matsa mishi ya fito da mata, shi kuma be shirya auren zumunci ba, kawai shi Ramcy ɗin ce tayi masa a yanzu, bari ya koma ya gwada sa’ar sa”.
Tunda Salman ya soma zuwa gidan su Ramcy, sai kuma ta ɗauki maganar nasa da muhimmanci, domin itama ba wai son sa ne ba ta Yi ba, kawai dai bata saba tsaya wa da samari bane, shiyasa tayi masa kora da hali
Ahaka soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su, a lokacin tana aji biyu ne a school ɗin ta, shine aka saka rana har sai da ta gama, kuma taƙi yarda ayi har sai da RAUDHA ta dawo, domin tace babu wanda ya isa yayi mata aure idan babu RAUDHA
Shi Baban ta ya san matsayin RAUDHA a wurin ta, shiyasa be damu ba, ya sanya musu ranan auren da yawa, ga shi yanzu har lokaci yayi.
      Washe gari asabar dubban jama’a suka shaida ɗaurin auren Rahma da Doc. Salman. Inda ya tara dubban jama’a sosai, har Suhaib ya zo mata tare da Farida.
    Su RAUDHA iyayen biki, sai cakare wa take yi, ta shiga wannan ta fita wannan ita da Amarya, yawancin kayan da suke saka wa ma iri ɗaya ne, tunda duk RAUDHA ta ɗinka musu
Kasancewar akwai partyn da za su yi, zuwa huɗu aka kai amarya ɗakin ta, gaskiya Ramcy tayi dacen muhalli, komi yaji, kuma ita kaɗai ce a gidan, duk da akwai fili na sauran ƴan uwan Salman ɗin, idan zasu yi auren su ma anan zasu zauna
Ɗakuna biyu ne da Parlour da kichen tare da Toilet, kuma duka an cika ko ina da kaya, musamman ma parlour’n ta da bedroom, kayan da Daddy ya siyan mata ne daga Dubai, kowa ya kalla sai yayi santin su, sosai suka yi kyau ga tsada
Tare da su RAUDHA aka taho kawo Ramcy, zuwa biyar da rabi har sun hallara inda za’a yi partyn, sosai wajen ya haɗu Masha Allah
Duk ƴan uwa sun taru, inda akayi ta yaba kyan da Amarya da ango suka sha, sun yi anko masha Allah, an fara gudanar da shagulgula cikin tsari, inda aka fara kiran Aminin Ango yazo ya bayar da tarihin Ango, riririri haka ya soma basu tarihin Ango suna ta shan dariya, dayake shi ɗin me yawan barkwanci ne, shiyasa yana ba da labarin ne yana saka wasa. Sai da yagama ya koma ya zauna
Inda aka ce Aminiyar amarya itama tazo ta ba da tarihin Amarya, aka kira RAUDHA, sai dai babu RAUDHA a wajen, ba ma ta iso wajen ba, tana can tare da Zulain shi ya tsayar da ita, tasha mamakin ganin sa a bikin, shine yake sanar mata “sun je gidan su ne, Daddyn ta yake sanar dasu suna biki, shine Sharif Ya rako shi nan ɗin tunda shi ya san kan gari” suna zuwa kuma basu sha wahala ba suka gano gidan
Tare suka taho wajen partyn a motan Sharif, tunda duk an watse tana tare dasu bata sani ba, daga tace ma Ramcy bari ta dawo
Suna zuwa a lokacin ne ake neman ta a hole ɗin, Ramcy sai leƙa kai take yi ta gano inda take amma ina bata ganta ba, sosai taji haushi jin M.C na sanarwan “idan babu ita a turo wata ta wakilce ta”
Waya ta ɗauka tana shirin kiran ta, sai gasu sun shigo su uku, RAUDHA na gefen Zulain suna taka wa a tare gunun sha’awa, kasancewar doguwar riga ce a jikin ta, har ƙasa yake jan mata, duk da ta saka Hill shoes, dole take amfani da hannun ta ɗaya wajen riƙe gefen rigan, hakan sai ya ba da wani style ɗin me ban sha’awa, ga shi rigan sosai yayi mata kyau ya ɗauki white skin ɗin ta, golden colour ne da ƙyalƙyalin kwalliya da kuma net da akayi amfani dashi, sai akayi mata light make-up a kyakykyawar fuskar ta da ya ƙara ƙawata fuskar
Masha Allah, kowa ya ɗaura idanun shi a kansu, ba ƙaramin tafiya da imanin jama’an wajen suka yi ba, daga ita har Zulain da ya sha kwalliyan sa cikin Suit farare, da baƙar rigan ciki, kasancewar suna tafiya ne a gaba Sharif na biye dasu a baya, sai kayi zaton su ɗin Ango da Amarya ne, sun yi kyau matuƙa, wasu ma daga cikin matasan har sun gane fuskar Zulain tunda ba ɓoyayye bane a TV. News, ana yawan saka shi idan har kai ma’abocin kallon labarai ne, dana American Dana Nigerian ma gaba ɗaya, to zaka iya sanin sa.
     RAUDHA jin ana kiran sunan ta, kai tsaye can ta wuce ta amshi abun maganar 🎤, tana murmushi ta soma ba da tarihin Ramcy da harshen turanci, duk da tana haɗa wa da larabci
Hakan sai ya sake birge mutane sosai, nan akayi ta mata tafi, sosai ta tafi da imanin duk wani saurayi me ji da kansa.
    Tana gama wa ta koma inda su Zulain suka zauna, hakan ya hana mutane da dama zuwa wajen ta, tunda sun ganta tare da saurayin ta.
     Ba’a tashi ba, su Zulain suka yi mata sallama suka tafi.
     Koda aka tashi a motan amarya da ango RAUDHA ta koma gida, duk da abokan ango suna ta mata tayin hawa motan su, amma ko kallo basu ishe ta ba, hakan yasa ma ta hau motan su Ramcy suka wuce gida.
    A can suka kwana da sauran ƙawayen, tunda dama al’adan su ne, ana kwanar wa Amarya, sai washe gari kowa ya watse, sanda RAUDHA zata tafi Ramcy tasha kuka, ta hana ta tafiya, RAUDHA me zata yi in ba dariya ba, ita abun ma dariya yake bata
Dama a lokacin akwai Salman sun zo da Abokin sa, su ma dariyan suka soma mata, sai daga baya da yaga da gaske dai kukan take yi taƙi barin RAUDHA ta tafi, shine ya zauna rarrashin ta, daƙyar ta yarda ta bar RAUDHA ta tafi
Abokin Salman ɗin shi ne ya dawo da ita gida, tunda Salman ɗin ne ya saka a dawo da ita
Tun a mota yake ta mata surutu, ita dai ko sauraren sa ba tayi, don ba ta son ma ta bashi ƙofan da zai iya ce mata yana son ta, saboda ta ga take-taken haka a wajen sa
Sabit ganin yanda ta nuna masa, shima sai ya kama kansa don yasan yarinyan ƴar zafi ce, yana kai ta suka yi sallama ta wuce gida, shi kuma yaja motan yabar gidan, duk da a ransa ba haka yaso ba.
🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵
       *AFTER ONE WEEK*
     Yau Sunday ranan da RAUDHA za su haɗu da Ray, sosai yau ta tashi cikin zumuɗi, tun jiya ta saka masu aikin ta suka yi mata irin su soye-soyen nan, cake🍰, cin-cin da su nama, duk ta saka aka soya mata, yau kuma ta sanya su suyi mata girke-girke kala-kala, sannan su shirya mata a ƙaramin parlour’n sama
Yau dama Daddy Yana da inda zai je, shiyasa tun safe ma ba ya gidan, duk da kuwa yasan da zuwan Ray ɗin, but yarigada yace wa RAUDHA tace masa ya jira sa, saboda yana so yayi masa maganar auren su ne, idan da gaske yake yi ya turo.
        Sai da ta tabbatar sun gama shirya mata komi yanda take so sannan ta baro parlour’n taje ɗakin ta ta shiga wanka, tana fito wa ta zauna a gaban mirror ta soma tsara kwalliya a kyakykyawar fuskar ta, tana yi tana lumshe lumsassun idanuwan ta fuskar ta cike da annuri, tunanin kawai yanda za su haɗu da Ƙalby ɗin ta take yi yau, har ta ƙosa mintocin da suka rage haɗuwar su suyi ta haɗu dashi
Light make-up tayi, amma bakin nan ya sha jan jambaki tamkar zai dubo sabida maiƙon sa, kayan ta ta saka, riga da skert na atamfa, yau ce rana ta farko a rayuwar ta da zata fara saka kayan Hausa wa, tun sanda Ammee ta ɗinko mata ta dawo dasu bata taɓa saka wa ba, ko a bikin Ramcy babu kayan hausawan da ta ɗinka musu daga ita har Ramcy ɗin
Ray da kansa ya ce mata “ta saka mishi yau domin yaga yanda kayan za su yi mata” shi dai a rayuwa yana son ya ganta sak da kayan Hausa wa tushen ta, hakan yasa itama a ranta taji tana ƙaunar sakawan sosai, ko domin ta burge sa
Atamfar ba wata me karikitai bane, gaba ɗayan ta me ruwan silver ne, sai akayi zane-zane a jikin ta ƙalilan da kalan fari da blue, wanda sosai ya ɗauki white skin ɗin ta, yayi mata mugun kyau, ga shi ɗinkin kamar dama an gwada ta, skert ɗin ya zauna mata ɗas a jikin ta, da akwai tsagu ta baya har zuwa kusa da gwiwar ta, sai rigan kuma me collar akayi mata da hannun link, amma wajen ƙirjin ta zuwa bayan ta duk net aka saka mata blue colour, sai hannun ma na net ne, illa wajen link ɗin da aka zizara atamfar, sannan collarn shima da atamfan akayi mata, rigan itama ta zauna mata ɗas gunun sha’awa, tare da fito mata da kyakykyawar ƙirar jikin ta
Sai dai matsalan kuma ta rasa yanda zata yi ta ɗaura ɗankwalin, ga shi tana son ta ɗaura ba ta son saka wani abu a kanta, dole ta ɗauki waya tayi kiran Saude, ita ta samu ta ɗaura mata me Steps ɗin nan, gashin ta ya zubo ta tsakiya, sai ta yafa farin gyale a gefen kafaɗan ta na dama, hohoho Fans thinks about yanda RAUDHAN ku tayi kyau, amma Ni idan na faɗa dole zan rage wani abu aradun Allah kuwa
Tana cikin zira Hill shoes ɗin ta ne, wayan ta ta soma ƙara, ta ɗauka tana murmushi don tasan ko waye ne
Sanar mata yayi ya iso, sai tace, “bari zata aiko a wuce da shi masaukin sa”.
Daga nan ta ajiye wayan, taci gaba da sanya takalmin, kasancewar me igiya ne, sai da ta gama sannan ta miƙe batare da ta ɗauki wayan nata ba ta fito daga ɗakin, Direct Block two ta wuce inda a nan ne aka sauke Ray
Da shigan ta ƙayataccen parlour’n dake ta faman tashin ƙamshi saboda gyaran da ya sha na musamman, sai ta hange sa can saman kujeru kansa a ƙasa yana latsa waya, yana sanye cikin ɗanyen shadda me ruwan ƙasa, da hulan sa zanna bukar
Sai da gaban ta yayi muguwar faɗuwa saboda kawai ganin sa da tayi, amma sai ta daure ta soma taka wa a hankali cikin tafiyan ta me tsananin burge duk mahalukin da ya gani
Abun mamaki! yawan kusantan ta da shi yawan jiyo daddaɗan ƙamshin turaren sa, wanda tuni ta rigada ta san waye mamallakin turaren, ko barci ta tashi idan har aka tambaye ta ƙamshin waye wannan? Zata buɗe baki tace na Rayyan ne, amma sai kuma bata damu ba, don ko kusa zuciyar ta bata taɓa kawo mata tunanin shi ɗin zata gani ba, shi ne wanda suke soyayya a waya ba.
     Ta iso tsakankanin kujerun inda sosai a wannan lokacin turaren nasa suka yi mata muguwar shiga hanci, a zuciyar ta tana me mamakin “me zai kawo sa nan bare har turaren sa ya cika wajen?” Sai kawai ta haɗa idanu dashi sakamakon ɗago kansa da yayi yana kallon ta
Wani irin zaro idanun ta waje tayi, ido cikin ido suke kallon juna, bakin ta na rawa tace, Kai!.. kai me kazo yi nan?”
.
+
_Hhhh to tambaye shi dai? Shin me zai faru? Ga RAUDHA ga Captain Rayyan sun haɗu?_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *