RAUDHA CHAPTER 3

 RAUDHA CHAPTER 3

“Katabbatar sun nuna maka takardun motan su kafin su wuce”. Yafaɗa maganar yana kallon Jone fuska a ɗaure

+

“Ok sir”. Jone yafaɗa yana me sara masa

Juyawa yayi kawai yatafi cikin tafiyan sa na zaratan maza yabar wajen

Lumshe idanun ta tayi tana sake kwantar da kanta jikin kujeran, tana jin sanda Jone yake sake tambayan Ramcy numban wayan ta, kuma tana jin sanda yayi musu sallama har yana ce mata

“Baby baza ki buɗe idanun ki muyi ban kwana ba?”

Buɗe idanun kuwa tayi sai dai bata kalle sa ba tayi wa motan keey taja da wani irin Speed tabar wajen

Gaba ɗaya sojojin sake kallon motan sukayi suna jinjina ƙarfin hali irin na RAUDHA, tabbas ko basu faɗa ba akwai abinda tataka har take iya yin hakan agaban su

Shima ɗin idanun sa kawai yazuba ma motan cike da mamakin tantiranci irin na yarinyan da har take musu tsaurin ido, har motan taɓace ma ganin sa kafin yadena kallon hanyan. Ahankali yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana me lumshe idanun sa cike da tuno suffarta, murmushin sa me kyau yasaki yana ɗaukan wayan sa dake faman ƙara yakanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin.

          🌐🌐🌐

Har suka shiga cikin Kaduna babu wanda ke magana cikin su

Akaro na biyu RAUDHA tasake kallon Ramcy da har yanzu bata dawo dai-dai ba, juya kanta tayi kafin tasake maimaita tambayan da tayi mata

“Ramcy tunanin me kike yi ne ina tambayan ki ina muka dosa?”

Sai alokacin Ramcy tadawo hayyacin ta sosai, cikin jan numfashi tace “uhmm Besty wlh ban ji ba duk hankalina ya tashi da ganin wannan dogon mutumin me murɗaɗɗen jiki, nayi tunanin yau kashin mu ya bushe wlh, don nasan halin sojoji basu da mutunci ko kaɗan”.

Siririn tsaki RAUDHA taja batare da tace uffan ba taci gaba da sharara gudu

Ganin haka yasa Ramcy tasoma nuna mata inda zasu yi

A ƙofar wani madaidaicin gida suka tsaya, gidan me dakali ne da yasha suminti tare da sabon penti, koda gani ansan cewa gidan ana sha’ani sabida yanda mutane maza  da mata suka cika ƙofar gidan, da alamun dai wani wajen Za’a tafi don gefe ɗaya motoci ne sun fi biyar afake

Tunda motan tatsaya yawancin mutanen wajen sai idanuwan su yadawo wajajen

Sun ɗau lokaci kafin Ramcy tasoma fitowa, sai da tafito taleƙa da kanta tana kallon RAUDHA da bata da alamun fitowa tace

“My Besty don Allah fito mushiga kiyi haƙuri”.

Yamutsa fuska RAUDHA tayi tana sake kallon mutanen wajen ta cikin motan, cikin ƙare musu kallo da taɓara tace “kinsan bana Son mutane idan nafita kallona zasu riƙa yi”.

Dawowa ciki Ramcy tayi tace “Plz Mana Besty Ina ruwan ki dasu? Kar ma ki kalli kowa kinji?”.

Gyaɗa kanta tayi tana sake ware idanun ta tana kallon su, sai da ta ɗan ja lokaci kafin tabuɗe motan tafito bayan ta mayar da hulanta akai

Sai kawai gaba ɗaya mutanen wajen suka sanyo mata idanu suna kallon haɗaɗɗen yarinyan me cike da ban sha’awa a idanun duk me kallo, yarinya ƴar hutu da ji da kai

RAUDHA sai faman ɓata fuska take yi tatako zuwa wajen Ramcy tana ɗan lumshe idanun ta

Sai da Ramcy tariƙe hannun ta kafin suka nufo gidan

Ba maza ba har matan sakin baki da hanci kawai suka yi suna kallon ikon Allah, kuma akasarin su kallon arniya kawai suke mata sabida shigan dake jikin ta

Sai da suka zo gab shiga gidan ne, Amarya da har da ita ake kallon sannan ne tagane Ramcy ce ƴar uwanta, sai tadaka tsalle tanufo ta tana faɗin

“Rahma ke ce ashe?”

Ramcy da itama sai yanzu idanun ta suka kai kan Amarya Shatu sai tawashe baki tana sakin hannun RAUDHA suka rungume juna cike da farin ciki

“Wlh ban gane ki ba sai yanzu ashe kece?” Cewar Shatu bayan ta ɗago kanta tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta

Duk ƴan matan sai suka nufo wajen su don ba ma idanun su abinci wajen kyakkyawar matashiyar nan me kama da ƴan ƙetare

“Ni ce wlh kin gammu sai yanzu”.

Murmushi Shatu tayi tana kallon RAUDHA dake tsaye tana bin mutanen wajen da kallo sai kace taga abun ƙyama, sai faman yamutsa fuska take yi

“Wannan kuma daga ina sarkin jajibe-jajibe?”

Sai da Ramcy takalli RAUDHA kafin tamayar da idanun ta kan Shatu da tayi maganar tace “mu shiga ciki mana ko anan ne zaki tarbe mu?”.

Dariya Shatu tayi tana kallon sauran ƴan matan wajen tace “ku jira Ni yanzu zan dawo”.

Gyaɗa mata kai kawai sukayi domin har yanzu sun kasa magana tunda sun samu abincin kallo

Riƙo hannun RAUDHA Ramcy tasake yi suka bi bayan Shatu da tayi gaba abinta

Dama tuni mutanen wajen sun soma gulma suna raɗe-raɗin ita kuma wancan wacece? Sai dai babu me basu amsa haka suka ci gaba da gulman su, yayinda ƙawayen amarya kuma suke jiran tadawo tabasu amsa

Suna shiga cikin gidan matan dake faman aiki suka sanyo musu idanu

Ramcy bata kalli kowa ba bare tagaishe su don tasan basu gane ta ba, haka tabi bayan Shatu har ɗakin Maman su, suna shiga babu kowa sai Maman Shatu ɗin tare da wata dattijuwa

Idanu suka sanyo musu cike da mamaki

Maman Shatu tace “ke Shatu wannan kuma daga ina?” Tayi maganar tana nuna RAUDHA da tatsaya ƙeƙam abakin ƙofa

“Mama baki gane ta bane? Rahma ce da baƙuwar ta”.

Sai Maman da Dattijuwar suka mayar da idanun su kan Ramcy da har ta zauna ma

“Ƴar ƙwal uba kece da wannan shigan banzan Ramatu?” Cewar Dattijuwar tana kai hannun ta jikin Ramcy taɗaga mata duka

Matsawa gefe Ramcy tayi tana dariya tace “ƴar tsohuwa me ran ƙarfe har dake a bikin nan?”

Mama tace “Rahma wacece wannan wai da kika zo mana da ita me kama da ingozi?”

Ɓata fuska Ramcy tayi tace “wai menene haka don Allah ƙawata ce fa muka zo da ita biki”.

Gaba ɗaya sai suka kama baki har Shatu suna sake maida idanun su kan RAUDHA dake tsaye har yanzu, sai dai yanzu sosai ta ɓata fuskarta tana sake sakar musu lumsassun idanun ta, kafin kuma tajuya tafice abinta

“Kun gani ko don Allah menene ruwan ku da ita? haka ake amsan baƙuwa?” Cewar Ramcy tana miƙe wa tsaye dasauri tafita

Sai suka juyo da kallon ga junan su

Shatu tace “cabb ɗi wai har yanzu Rahma bata dena halin ta ba? Ni nasan wlh daga shige-shigen ta ne ta samo wannan arniyan, wai ƙawancen ma har da arniya”.

Sai taja tsaki tana nufan ƙofa batare da tabi takan Mama da tsohuwa dake surutu ba

A zaure Ramcy ta cinma RAUDHA tayi saurin riƙo ta

A fusace RAUDHA tajiyo tana kallon Ramcy da shanyayyun idanun ta tace “meye kika riƙe Ni?”

Cikin lallami Ramcy tace “don Allah kiyi haƙuri Besty basu san ko ke wacece bane, amma zanyi musu bayani yanzu kin ji?”

Gajeren tsaki RAUDHA taja batare da tace uffan ba

Roƙon ta Ramcy taci gaba da yi daƙyar tasauka, amma da sharaɗin baza ta kwana anan ba sai dai su tafi Hotel

Gyaɗa mata kai kawai Ramcy tayi cike da son kwantar mata da hankali

Shatu ce tafito itama tagan su anan tsaye, sai kawai tasaki murmushi tace

“Yanzu party zamu je Rahma, ki taho muje tunda ga motoci sun zo”.

Murmushi Ramcy tayi tace “to zamu zo daga baya, aina ake yi?”.

Faɗa mata address ɗin wajen tayi kafin tafice abinta

Riƙo hannun ta tayi zasu koma ciki amma RAUDHA tatirje alamun baza ta je ba, sai ita Ramcy ɗin ne takoma ciki don sanar musu da tafiyan ta

Tana shiga ɗakin taga mutanen wajen duk sun shiga ciki suna tambayan yarinyan da tafita

Anan ne ma suke sanin ashe Ramcy ce ɗayar

Tana shigowa duk suka yi mata caa aka suna faɗin “shine zata wuce su bata gaishe su ba?” Ita dai haƙuri tabasu kafin tayi ma Mama ƙarya akan zasu wuce wajen party amma ba lallai tadawo nan ba sai gobe, zasu sauka gidan yarinyan da suke tare da ita (tana nufin RAUDHA)

Bata jira ma abinda zasu ce ba tafito tasami RAUDHA tariƙe mata hannu suka fito cikin gidan

Yawancin mutanen wajen duk sun shige cikin mota, ko kallon sauran mutanen da suka banko musu ido basu yi ba suka shiga cikin motan RAUDHA taja suka bar wajen.

            🌐🌐🌐

Suna isa ɗan ƙaramin Hotel ɗin me ban sha’awa suka fito suka shiga ciki

Ramcy ce tayi musu booking ɗakin da zasu zauna, sai da tagama komi sannan suka nufi inda jerin ɗakunan suke, a upstairs ɗakin nasu yake

Bayan tabuɗe suka shiga

Direct Kan gadon RAUDHA tanufa tafaɗa tana ajiyan zuciya, lumshe idanun ta tayi tana jin zuciyarta babu daɗi, sosai ranta yasosu da yanda mutanen suke kiran ta da arniya

Zuwa Ramcy tayi tazauna gefen ta, shiru tayi naɗan wani lokaci kafin tace “Besty ko zamu je wajen partyn ne?”

Shiru babu amsa

Sai da tasake maimaita mata sannan ne RAUDHA tabuɗe idanun ta cike da ɓacin rai tace “Ni baza Ni ba”.

“Plz Besty kin San bazan iya tafiya in barki anan ba, sannan idan banje ba Shatu zata ji haushi tunda nazo mata biki ne kiyi haƙuri da abinda akayi miki, hakan bazai sake faruwa ba”.

Gajeren tsaki RAUDHA taja tana miƙe wa zaune taja jakan ta dake hannun Ramcy ɗin, taciro ƙwayoyin ta ta’afa a bakin ta don jin kanta ya soma ciwo sakamakon hayaniyan mutane

Can kamar baza ta sake cewa komi ba sai kuma tatashi tana ajiye Facing Cap ɗin ta saman gadon takalli Ramcy tace “tashi muje”.

Dasauri Ramcy tatashi tana murmusawa suka nufi ƙofa suka fice, Ramcy ɗin tarufe ƙofan suka sauka ƙasa, inda suka ajiye motan su suka nufa suka shiga RAUDHA tafiga motan suka bar haraban wajen._______📖A Hotel 🏨 ɗin da su Shatu suke yin party RAUDHA tatsaya, ɗan ƙaramin hotel ne me kyau da tsada, gaba ɗaya haraban wajen motoci ne manya-manya jibge, da gani kasan harkan da manyan mutane ake yi

Dama shi Mijin Shatu ɗin me kuɗi ne, don haka abokan sa duk yaran masu hannu da shuni ne kuma duk sun hallara wajen, partyn dama daga Ƴan mata sai samari ne

Fitowa suka yi cikin motan suka nufi ciki

Tunda suka doso bakin wajen Cool music ɗin da aka saka yaratsa kunnuwan RAUDHA, sosai taji wani sanyi da nishaɗi ya ziyarce ta duk da kuwa bata cikin Mood ɗin ta

Suna shiga sai idanun mutane da yawa yadawo kan su sai kallon RAUDHA ake yi wacce ita kuma ta kafe inda MC ke tsaye yana surutun sa da idanu

Sai da Ramcy tariƙo hannun ta suka shige wajen kujerun sannan ne tadawo da hankalin ta gare ta

Zama sukayi akan kujeran da babu kowa

Hankalin fa abokan ango gaba ɗaya ya koma kan RAUDHA tun sanda tashigo tatafi da duk wani nutsuwar su

Har wani daga cikin su dai sai da yaciri baki yayi ma ango magana “ko ya santa ne?” Shi kuwa yakaɗa kansa kamar ƙadangare yana murza baki yace

“A’a Niii..? wlh bansan taba, sai dai ko Babyna?”.

Shatu dake gefen sa tana jin duk abinda suke faɗa tace “nima haka yanda kuka ganta haka naganta..”

Maganar da MC yayi ne yadawo dasu daga surutun da suke yi

Sai suka tashi suka fita filin rawa inda MC yakira ango da amarya akan su zo su taka

Duk abokan tashi sukayi suka nufi yin musu manne, amma banda wanda yake tambayar Ango ɗin ko sun san RAUDHA ne

Hankalin sa gaba ɗaya yana ga su RAUDHA, sai daga baya ne shima yatashi yanufi fili yana sakar musu maƙudan kuɗi kamar wanda be san zafin sa ba

Yana gamawa kuwa yaratsa yafito cikin cunkuson ƴanmata da samarin da suka cuɗe waje ɗaya duk wai akan sun zo ma Ango da Amarya manne

Wajen su Ramcy yanufa dake zaune su basu tashi ba, sai ma RAUDHA da takifa kanta saman table sakamakon Ciwo da kanta ke mata, duk da sosai take son daurewa amma abin ya gagara dole takwantar da kanta don taji daɗi

Yana isowa yayi musu sallama idanun sa akan RAUDHA wacce ma batasan yana yi ba

Amsa masa sallaman Ramcy tayi tana kallon sa, ganin dai ba ita yake kallo ba sai itama taɗauke kai taci gaba da latsa wayan ta

Zama yayi sannan ne alokacin yadawo da idanun sa kan Ramcy ɗin yana murmusawa yace “ƴan mata sannun ku dai”.

“Yauwa sannu”. Ramcy tabashi amsa batare da tasake kallon sa ba

Numfashi yasaki yana ƙara mayar da idanun sa kan RAUDHA ɗin yace “amma wannan lafiyan ta ƙalau ana shagali tana kwance?”

Sai alakocin Ramcy tasake dawo da idanun ta kansa, kuma a lokacin ne tayi masa kallon ƙurilla

Kyakkyawar saurayi ne me ji da kyau da kuɗi, ko kaɗan baya da makusa, yana sanye cikin farar Gezna wanda akasarin abokan dama shi suka saka, sai ɗai-ɗai ku da suka sanya farar Shadda

“Lafiya lau”.

“Ok Allah yasa hakane, but don Allah ko zaki iya min magana da ita coz wurin ta nazo”.

Ramcy tace “ai tana jinka duk abinda zaka faɗa”.

Dafa table ɗin yayi yana ɗan bugawa yace “ƴan mata Plz ki tashi muyi magana”.

Ramcy da taɗau Juice tana sha ta’ajiye tana faɗin “me zai sa sai tatashi? Kawai kayi maganar ka mana ai kunne🦻 ke ji”.

“Kuma hakane fa”. Yafaɗa yana dariya

Sai kuma yasake mayar da idanun sa kan tulin gashin ta cike da sha’awa yace “Baby Ni dai har ga Allah kinyi min ne shiyasa nataho don na yaɗa manufa na akan ki, sunana Saifullah zan zo insan naki sunan?”

Shiru RAUDHA tayi bata da alamun tashi duk da tana jin sa

Ramcy kuwa ganin ya hau mata magiya sai takatse shi da faɗin “Besty bata da lafiya kayi haƙuri ka ƙyale ta haka nan”.

Bada son ransa ba yayi shiru but ya so yasake ganin baby face ɗin ta, amma babu yanda ya’iya sai yanemi Numban wayan ta wajen Ramcy

Ita kuma Ramcy tabashi nata kamar yanda tayi ma Sojan can

Miƙe wa yayi yayi musu sallama yakoma wajen abokan ango wanda tuni sun ƙosa yazo yabasu labarin RAUDHA don sun san wajen ta yatafi, duk da kuwa su ma suna son ace su ne suka samu gurbi a wajen ta

Ramcy magana tayi ma RAUDHA akan zata je wajen Shatu kafin tatashi tatafi, bata jima ba tadawo tace

“Besty tashi muje naga alamun wajen baya miki daɗi”.

Kamar jira take yi kuwa tamiƙe dafe da kanta tayi gaba Ramcy tabi bayan ta

Wani daga cikin abokan Angon da tun sanda yaƙyalla idanu akan RAUDHA yasusuce, yana ganin sun fita yamiƙe kamar yana waya shima yafice

Yana fita yasoma waige-waige ko zai hango su amma ko me kama da ƙeyan su be gani ba, sai motar da yagani tafice da gudun tsiya, sai da yaɗan ƙara duddubawa ko zai gansu kafin yayi tunanin ko su ne suka fita, sai yayi saurin shiga motar sa yatake musu baya, but ko me kalan motan su ma be gani ba a hanya amma haka yaci gaba da tafiya ko Allah zai sa yadace

Abinda be sani ba bata hanyan ma da suka bi yabi ba, domin suna soma tafiya RAUDHA tatsayar da motan, sosai kanta ke sara mata kamar zai rabe gida biyu, riƙe kan tayi da hannu ɗaya tana yarfe ɗaya hannun

“Lafiya Besty menene?” Ramcy tafaɗa cike da tashin hankali

Jujjuya kanta take yi kafin tace “kaina ke ciwo zafiii”.

Duk hankalin Ramcy ya tashi haka take ta mata sannu, daga baya tace “su je asibiti”

But ita RAUDHAN tagirgiza mata kai alamun a’a, sai tabuɗe Lockern cikin motan taciro Cocaine ɗin ta tasoma shaƙa wai ko zai sa taɗan ji dama-dama idan hankalin ta yagushe

Ramcy dai sai kallon ta take yi tana mata sannu

Tsawon mintuna 5 taɗauka idanun ta a lumshe kafin tayi ƙarfin halin kunna motan taci gaba da tafiya, but sai dai yanzu ɗin a hankali take tuƙa motar har sanda suka ƙarisa cikin hotel ɗin tayi parcking, fita tayi batare da takashe motan ba

Sai Ramcy ce tazagayo ta’amsa keey ɗin takashe kafin takulle motan suka nufi ciki, har sun shiga reception Ramcy tatuna basu ɗauko Jakan kayan su ba, sai tadubi RAUDHA dake riƙe da kanta tana faman haɗa hanya tace

“Besty jira Ni anan bari in ɗauko Mana Jakan mu”.

Gyaɗa mata kanta tayi, ita kuma tafice dasauri

Ci gaba da tafiya tayi tahaye benen, daƙyar take tafiyan saboda yanda Cocaine ɗin yasoma gusar mata da hankali, ahaka tahaura saman tadoshi ɗakin su, tana shan kwana taji tayi karo da mutum sai dai takasa ɗago kanta bare taga wanda tabuge, illa lafewa da tasake yi ajikin sa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin sa

Hannun sa biyu yasa yaɗago kanta yana kallon Beauty face ɗin ta da talumshe idanuwan ta, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne yaji ya ziyarce shi lokaci ɗaya

Sosai yagane ta tunda kayan ɗazu ne ajikin ta

Tabbas tun kallon farko da yayi mata yatabbatar da ita ɗin mara tarbiyya ce duk da har yanzu be tabbatar wa kansa ita musulma ce ko Christian ba, yanzu kuma gashi ya ganta cikin hotel kuma a buge hakan ya tabbatar masa da zargin sa, hakan yasaka kuma yaji mugun tsanar ta da haushin ta cikin ransa wanda be san dalili ba

RAUDHA buɗe kyawawan idanunta da a yanzu suka sauya kala tayi, tasauke cikin nasa idanun da yakafe ta dasu

Duk da gaban sa yayi mugun faɗuwa amma hakan be sa ya tattakura ya tunkuɗe ta ajikin sa ba

Da bango tabugu kafin tafaɗi yarab a ƙasa, tsananin azaban da yaziyarce ta batasan sanda taware idanun ta duk ka waje ba tana fashewa da kuka, ban yi zaton idanun ta sun kai girman hakan ba sai yau da tafiddo su waje tsaban taji azaba 😄

Kallon kallo kawai suke yi yayinda take gunjin kuka

Cike da takaicin ta yatamke fuska yana aika mata da banzan kallo yace “kin zata kowa irin ki ne mara tarbiyya ƴar ƙwaya Da zaki haɗa jikin ki da nawa? Wawiya kawai”. Yaja dogon tsaki yana tsallake ƙafafun ta yawuce dasauri-sauri cikin tafiyan sa na zaratan maza

Lumshe idanuwan ta tayi hawaye na kwaranya saman kuncin ta

Yau da tana da ƙarfi a jikin ta wlh da babu abinda zai hana ta cin collarn rigansa sai taga wanda yaɗaura wa Uwar sa aure

Tana nan zaune har sanda Ramcy tadawo, ganin RAUDHA a ƙasa ya ɗaga mata hankali, cikin sauri tace “Besty ya haka faɗi kika yi?”

Tatambaye ta tana ɗago ta a lokaci ɗaya

RAUDHA bata iya ce mata komi ba sabida tsananin tuƙuƙin da zuciyarta take mata da maganar da wannan mutumin yafaɗa mata da kuma abinda yayi mata, sabida tsaban baƙin ciki ma gaba ɗaya ta dena jin ciwon

Har sanda taɗaga ta sannan tariƙo ta suka ci gaba da tafiya

Suna shiga ɗakin RAUDHA taƙwace jikin ta tanufi kan gado tafaɗa kai tana lumshe idanuwan ta da har yanzu sun kasa dena fid da hawaye

Ramcy duk bata kula da hawayen da take yi ba, sai zama da tayi tana tambayan ta abinda zasu ci

Sai alokacin ne ma ita RAUDHAN tatuna rabon ta da abinci tun daren jiya, tunda koda Ramcy tazo gidan ta ita tatashe ta a barci, kuma bata ci komi ba suka taho, gashi yanzu har duhun magriba ya shiga bata sanya komi a bakin ta ba

Bata kula Ramcy ba itama kuma sai bata sake cewa komi ba, tasan halin ƙawarta ba ko yaushe take son magana ba sai idan taga dama koda zaka shekara kana mata maganan ne, ita ɗin ƴar ganin dama ce

Har aka kira isha’i RAUDHA bata motsa daga inda take ba

Ita kuma Ramcy tuni har tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallan da ake bin ta yau ɗin, sai da tagama ne tasake dawowa tatambayi RAUDHA abinda zasu ci

Sosai a yanzu take buƙatar abinda zata sanya a bakin ta koda kuwa bazai mata daɗi bane, sabida tsaban yunwan da a yanzu take ji, daƙyar ta’iya buɗe baki tace ma Ramcy ɗin “duk abinda taga yayi mata tace akawo”

Nan kuwa Ramcy taɗau wayan ɗakin tayi musu odan abinci sannan tazauna zaman jiran kawowa, babu jimawa taji ana Nocking taje tabuɗe ta’amso tadawo ta’ajiye akan table ɗin dake tsakiyar ɗakin

“Besty taso muci ga abincin an kawo”.

Shiru RAUDHA tayi, sai kuma daga baya tayunƙura tatashi duk jikin ta babu ƙwari, ga fuskarta a a ɗaure kamar bata taɓa yin walwala ba

Sai a lokacin ne Ramcy takula tatambaye ta

“Besty lafiya wai meke damun ki ko kan ne?”

Girgiza mata kai kawai tayi tamiƙe tadawo kusa da ita da take zaune saman sofa, bata yi magana ba har suka soma cin abincin

Bayan sun gama ne tamiƙe tanufi Toilet tayi wanka, tana fitowa wayan Ramcy yasoma ringing

Ɗaukan wayan tayi taduba sannan taɗago tana kallon RAUDHA tace “Sojan nan ne da nabashi Number yake kira’.

RAUDHA batace uffan ba sai buɗe Trollyn ta da tayi tana ciro kayan da zata saka

Har wayan tatsinke aka sake kira amma batace komi ba, ita kuma Ramcy bata amsa ba, sai da yayi 3missed call kafin yadena kira

A lokacin har RAUDHA tagama saka kayan ta na barci riga da wando Three qweater farare masu taushi sosai, sai time ɗin takalli Ramcy tace “ki cire layin ki sanja wani”.

Ramcy tasan me take nufi don haka tabuɗe wayan tacire layin tabar ɗaya simcard ɗin ciki, karyawa tayi tazubar sannan taci gaba da latsa wayan ta

Dama Numban ne kuma taba ma wanda suka haɗu a partyn Shatu

Kwanciya RAUDHA tayi tajuya bayan ta tana lumshe idanuwan ta

Itama Ramcy bata wani daɗe ba tazo takwanta nan da nan barci yafige ta

RAUDHA tana nan kwance amma barcin yakasa ɗaukan ta, takaicin Sojan da sukayi karo duk ya addabi zuciyarta, daƙyar tayi barci bayan ta haɗiye ƙwayoyin ta.Washe gari sai kusan ƙarfe 11:30am. Ramcy tasoma farkawa, sai da tashiga Toilet tayi alwala tafito sannan tasoma tashin RAUDHA but ko motsin kirki taƙi yi, haka ta haƙura taƙyale ta tayi sauri tagabatar da sallan asuba da basu yi ba, sannan taje tayi wanka, tana fitowa sannan ne RAUDHA tabuɗe idanun ta

+

Tana nan kwance har sanda Ramcy tasaka kayan ta sannan ne tatashi ahankali tashiga Toilet ɗin, wajen mintuna goma taɗauka tafito tana zama kan sofa, kwantar da kanta tayi tana lumshe idanun ta

Kamar jiya Ramcy ce tayi musu odan breakfast da zasu ci, bayan sun gama ne sannan ne RAUDHA tayi wanka tafito

Time ɗin ita kuma Ramcy ta sauya kayan ta zuwa wani jan yadi dack da ɗige-ɗigen fari ajiki, sai akayi zanen Flower da blue colour, ɗinkin doguwar riga ne fitet gown da yamatse ta sosai

Itama RAUDHA kayan ta taciro tasaka bayan ta shafa Lotions ajikin ta, batayi kwalliya ba sai Powder da tasaka a baby face ɗin ta

Tunda tagama shiryawa Ramcy take kallon ta, tana son tayi mata magana akan kayan amma tana tsoro don bata son yau ma mutane suriƙa mata kallon arniya

Riga ce tasaka irin na jiya, sai dai shi wannan maroon colour ne saɓanin na jiya baƙi ne, kuma wannan yafi Robber sosai gashi shara-shara ne, gaban rigan ma sosai yabuɗe har yafi na jiya, sannan ma be kai mata iya gwiwa ba, kai gwara ma na jiya sau dubu akan wannan

Har ta zauna tasoma saka Socks a ƙafan ta sai kuma taja tsaki tana miƙe wa tasoma cire kayan, sauyawa tayi da pencil ɗin wando ja da ƙaramar riga me ruwan zuma, sai tasaka top shima ja me kwalliyan Flower da stone, gashin ta ta tattare tasaka Ribom sannan tasaka Socks da Hill shoes me tudu white, sai tasanya Facing Cap white colour sai dai Robber ne wanda yakama mata kanta sosai

Ita RAUDHA tayi kwalliyan nan ne don fita yawo don ko kaɗan bata son komawa gidan bikin nan

Koda suka fita suna cikin mota anan Ramcy tace mata

“Besty mu leƙa gidan biki”.

Turo baki gaba RAUDHA tayi tace “Ni babu inda zani yau”.

“Please mana Besty don Allah muje yau babu abinda zai faru, kinga yau ne bikin dole zanje kuma bazan barki natafi Ni kaɗai ba”.

Daƙyar dai da suɗin goshi RAUDHA tayarda zataje, daga yawon su suka nufi gidan su Shatu, amma firr RAUDHA tace “baza ta fita daga motan ba” dole Ramcy taƙyale ta ita tashiga cikin gidan su Shatu ɗin

Wajen mintuna 20 taɗauka kafin tafito tanufi maƙotan su inda Shatu take taron ta

RAUDHA da tagaji da kallon mutane ta cikin Glasses gyara kujeran tayi takwanta tana lumshe idanun ta

Koda Ramcy tadawo batace mata komi ba taja motan suka tafi, wani restaurant suka je anan suka ci abinci suka koma Hotel ɗin da suka sauka

Tun da suka shiga RAUDHA tahaye gadon tasoma barci, ba ita tatashi ba sai magriba, har Ramcy ta fita ta dawo

Anan tayi wanka tasoma ramuwar sallan da ake bin ta, bayan ta idar suka ci abinci suka yi kallo sannan suka koma barci lokacin har 12:00pm na dare tayi.

The following day Ramcy ita kaɗai tafice tanufi gidan su Shatu, so take yi tayi musu sallama daga nan idan tadawo sai su wuce gida.

Koda tadawo RAUDHA cewa tayi ba yau zasu tafi ba, itama Ramcy bata wani damu ba tunda tasan Baban ta yayi tafiya kuma ba lokacin dawowar sa bane yanzu, idan ƴan gidan su ne zata kira su tasanar musu tana gidan su Umma.

     Tun daga ranan kuwa basu da aiki sai yawo cikin gari, su je nan wajen shaƙatawan su je nan, kullum cikin siyan kayan daɗi da maƙulashe suke yi, su ci wannan su sha wannan, har Club suke zuwa

Satin su ɗaya cif kafin su nufo hanyan Zaria, ko a hanya wannan karon basu haɗu da Sojoji ba, iyakan motar su da suka gani guda ɗaya a wajen.

   🌐🌐 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

           *FEW WEEKS*

Gobe ko jibi Daddyn RAUDHA yafaɗa mata zai dawo, shiyasa take ta farin ciki, taso yafaɗa mata Real time ɗin ne sabida taje tarbo shi amma yaƙi, shima yace be da tabbas ko zai dawo a ranan da yaɗiba mata.

Washe gari tana cikin barci Saude tashigo cikin ɗakin, ita tatashe ta tafaɗa mata Samuel yazo

Kamar an tsikare ta tamiƙe tafita da gudu

Samuel shine drevern Daddyn ta, tunda taganshi tasan Dad yau zai dawo

Lokacin da taƙarisa wajen sa yana kusa da motan da yazo, cikin fara’a take tambayan sa

“Samuel Daddy ya dawo ne?”.

“No Ma’am ya bani umarni ne in ɗauke ki zuwa can gidan”.

Bata ce komi ba tajuya dasauri, a Parlour tatarar da Saude tace mata su haɗa kayan su su koma can gidan, sannan ita tawuce ɗakin ta da gudu

Dama duk idan Daddy zai dawo gaba ɗaya ma’aikatan gidan suke komawa can tunda dama daga can ɗin ne suka zo, sai masu kula da gidan kawai ake bari.

Babu abinda taɗauka sai jakarta, takwashe duk ƙwayoyin ta tazuba a ciki, baza ta iya tsayawa tayi wanka anan ba idan taje can zatayi, daga ita sai riga da gajeren wando na barci tafito tana riƙe da waya a hannun ta, Numban Dad ɗinta take Kira Amma baya shiga, ahaka tafita tafaɗa cikin motan Samuel suka bar gidan

Babban katafaren gidan su suka nufa, suna zuwa gateman yabuɗe musu suka shige ciki

Wani katafaren mahaukacin mansion suka nufa wanda tsananin girman sa ya zarce na mai karatu, tun daga bakin Gate kusan tafiyar minti goma ne a mota kafin ka’isa inda aka shata wani ƙaton round about me matuƙar kyau da ƙawatuwa, da wasu irin manyan lanters masu Flower a jiki wanda ruwa ke ɓulɓulowa zuwa sama yana wani irin buɗe wa kamar zai zubo ƙasa sai yakoma ciki.

Haka suka zagaye round about ɗin suka wuce wani ƙaton gini dayake na securities ne da masu gadi haɗe da masu gyaran haraban wurin

Nan ɗin ma kusan tafiyan minti goma sukayi kafin suka isa ga ainihin gidan wanda tun daga nesa ƙayatuwar sa da tsantsan kyawun sa zai iya zautar da kai da baka taɓa gani ba

3 upstairs ne ginin kuma akwai lifter da zai kai ka duk inda kake so

A hawa na uku ɗakin RAUDHA yake, gaba ɗaya saman Glasses ne wanda idan kana wannan ɗakin zaka iya hango wancan ɗakin, but an saka cootens ako ina ta yanda baza ka iya ganin waje ba sai ka yaye labulen

Ɗakin RAUDHA babban Parlour ne da ɗakuna biyu da Toilet har da kichen aciki, akwai ɗakin games komi na more rayuwa akwai aciki, gefe ɗaya kuma ga kayan wasa irin su teddy’s da sauran su, duk Daddy yazuba Mata don ya mayar da ita ne tamkar yarinya ƙarama, babu abinda zata nema be mata ba

Tana shiga ɗakin ta inda babu komi aciki sai babban katafaren Royal bed tare da dogayen sif wanda yamamaye kafataren bangon gaba ɗaya, komi na ciki Sky Green

Ɗayan kuma ɗakin kujeru ne kawai da kayan kallo aciki, sai speaku 🔊 manya-manya da sauran abubuwa na ƙyale-ƙyale, duk abinda ke ciki pink and white colour

Kayan ta tacire tashiga cikin Toilet, cikin Jacuzzi tafaɗa bayan ta haɗa ruwa da kumfa, tayi mintuna goma aciki tana kwance kafin tasoma wanka, bata son ko kaɗan Daddyn ta yadawo bata gama shiryawa ba

Bayan ta fito ta gama shafa Lotions tazira kayan ta, riga ce off Shoulder me ruwan madara, sai guntun wandon shi iya cinya shima Milk ɗin, ɗaure gashin ta tayi tasaka Room Slippers pink colour me tuntu a sama

Fitowa ɗakin tayi sai dai bata hau lifter ba sai tabiyo takan bene, da gudu take taka kan Steps ɗin har tasauka ƙasa, a cikin kujera talume tana kallon katafaren t.v plasma dake aiki shi kaɗai

Babu kowa cikin tanƙamemen parlour’n sai ita kaɗai, girman parlour’n sai da yaɗauke set uku na kujeru daban-daban

Bata jima da zama ba tajiyo horn ɗin motoci, da gudu tatashi tafita, tun daga nesa tahango motoci kusan goma suna tahowa amma haka tanufi wajen da gudun ta tana farin ciki

Kafin ta’iso har motocin sunyi parcking mutane sun soma fitowa

Motoci biyar na bodyguard ɗin Daddy ne, sauran kuma na mutanen  sa ne tare da abokan sa da sukai mishi rakiya

Farin dattijon mutum ne yafito a motan tsakiyan wanda shi kaɗai ne fari tar kuma babba sosai, mutumin yana da tsananin kwarjini da cikan haiba, kallo ɗaya idan kayi masa zakaga tsantsan kamar da suke yi da RAUDHA, sai dai kuma bashi da maraba da Suhaib don shi yafi ɗauko sa sak kamar kaki yayi ya’ajiye

Da wani irin gudu tanufo mahaifin nata, duk yawan mutanen wajen tunda taƙilla idanu kansa bata ƙara waiwayan su ba

Tana isowa yamiƙa hannu yacafe ta a jikin sa, juyata kawai yake yi yana dariya cike da tsantsan ƙaunar ta, itama ɗin dariya take yi tana kiran

“Daddy.. Daddy..”

Duk wanda yagansu yasan akwai soyayya me ƙarfi a tsakanin su

Duk mutanen wajen kallon su kawai suke yi suna murmushi cike da sha’awan su

Sosai Daddy yaga Babyn nasa ta sauya masa, tayi rama sosai duk da yasan ita ɗin ba ma’abociyar cin abinci bane

Inda RAUDHA me tarbiyya ce be kamata tafito da wannan kayan agaban mutane ba, shima kuma Daddy ko kaɗan be damu da ganin ta ahaka ba bare har yaga tayi laifi

Tana jikin sa be sauke ta ba yakalli mutanen da murmushi a face ɗin sa yace

“Mu shiga ciki”.

Babu musu suka nufi cikin gidan gaba ɗayan su

A Parlour suka yada zango gaba ɗayan su

Daddy ajikin sa yaɗaura RAUDHA ko kunyan mutane baya ji, dayake yana rayuwan sa irin na turawa ne shiyasa be ji kunya ba, kuma ko kaɗan baya jin shakkar nuna tsantsan soyayyar da yake mata ako ina, bare kuma ya ɗauke ta ne tamkar yarinya ƴar shekara biyar, sosai yake tsananin tausayin ta kasancewar ta tashi cikin maraicin uwa, shiyasa duk wani abun da yakamata uwa tayi ma ƴarta shi ke yi ma RAUDHA

RAUDHA lafewa tayi ajikin sa tana kallon mutanen dake zaune ana gaggaisa wa, wasu daga cikin abokan shi sai tonan ta suke yi tana murmusawa amma batace komi ba

Ahaka dai sukai ta yin ma Daddy barka tare da nuna murnan su na samun nasara da yayi a kasuwancin sa

Masu aiki duk sun jibge musu Drinks a gaban su

Sun ɗan ɗauki kusan mintuna 20 kafin suyi masa sallama su tafi

Anan RAUDHA tasake matse shi tana faɗin “I miss You Daddyyyy?”

Har da ƙwallan ta

Shima sake Hugging ɗin ta yayi yana murmushi me bayyana haƙora yace “I miss You more than you Babyna”.

Ɗago kanta tayi tana kallon sa da dariya a fuskarta, sosai za’a gane farin ciki tsantsa da take ciki

“Daddy na..” Tafaɗa tana sake yin dariya bayan ta sake shigewa jikin sa

Daddy dariya yayi yace “Baby murna yayi miki yawa kin kasa magana ko”.

Still ɗago kanta tayi tana kallon sa, baki awashe tagyaɗa masa kai

A lokacin ne sauran ma’aikatan gidan suka soma shigowa suna kawo mishi gaisuwa har dasu Saude aciki

Amsa musu yake yi cikin fara’a wanda zaka gane ɗab’ian sa ne hakan

Sai da kowa yafita kafin yasake kallon RAUDHA, wannan karon ma da murmushi a face ɗin sa yace “to ya kike Babyna na same ki lafiya?”

“Eh Daddyna”.

Shafa kanta yayi yace “duk kin rame Sweetheart, kin yi ciwo ne baki faɗa min ba?”

Girgiza kanta tayi tana sake cusa hannun ta cikin nashi tace “Daddy ban yi ciwo ba kewar ka ne ya ramar dani”.

Dariya yayi sabida yanda tayi maganar

Itama sai tatayashi tana yi tana cino baki alamun zatayi fushi

Cikin dariyan yace “sorry Baby Kar ki ɓata rai, tashi muje ɗakina sai inyi wanka mu sake gaisawa ko?”.

Ɗaga ta yayi tana jikin sa wannan karon ma be sauke ta ba yanufi lifter yabuɗe yashig_______📖Bayan Daddy yayi wanka parlour’n sa suka zauna, anan an rigada an jera masa abinci a dainning, don haka tare suka soma ci da RAUDHA, suna yi suna hira yana tambayan ta matsalolin ta

+

Sai da aka kira sallan Asar kafin yamiƙe yafita bayan yayi alwala

Itama RAUDHA dasauri tashiga ɗakin ta na Part ɗin Daddy ɗin taɗauro alwala

Ko wani upstairs akwai ɗakin ta aciki, Dad ɗin ta yana hawa na biyu ne

Bayan an idar da Sallah koda yadawo mutanen anguwa yagani sun yi masa dafifi a ƙofar gida, a zummar sun zo tayasa murna but a baɗini maula suka zo yi, sun san Alhaji me kyauta ne bazai taɓa barin su haka ba

Ai kuwa bayan ya gaisa dasu faram-faram sai yashiga cikin gidan yakira bodyguard ɗin sa ɗaya yace ” yabiyo sa ya’amso musu saƙo”.

Kuɗi yabashi yace yaraba musu sai wasu daga cikin kayayyaki na masarufi da yasa a ɗibo daga store duk a rabar musu kar yalalace

Zama yayi a parlour’n sa RAUDHA na jikin sa sai zuba masa surutu take yi

Sosai RAUDHA take da miskilanci amma idan tazauna gaban mahaifin ta zakai tunanin ta haɗiye rediyo ne saboda yanda take zuba kamar ana ƙara mata sabbin batir

Koda aka kira wayan Daddy dake can cikin bedroom ɗin sa da gudu taje taɗauko masa, zama tayi gefen sa tana faɗin

“Daddy Yaya ne yakira ka”.

Amsan wayan yayi yana murmushi yakara a kunne da sallama a bakin sa

Daga can Suhaib amsawa yayi cikin jindaɗi sannan yagaishe shi

Ga duk kan alamu yanda suke wayan zaka san akwai shaƙuwa da junan su, anan Suhaib yake faɗa masa bazai samu zuwa ba sai jibi sabida aiki da sukai masa yawa

Daddy be wani damu ba yace masa yakula da kansa sosai Allah yakawo sa lafiya

RAUDHA ce ta’amsa wayan tana ta zuba masa shagwaɓa akan ita dai sai yazo, daƙyar ya rarrashe ta tahaƙura

Haka suka kasance a ranan cikin farin ciki, duk inda Daddy yake tana maƙale dashi, ƙarshe ma a part ɗin sa takwana.

Washe gari da wuri tatashi tayi wanka tashirya cikin biri da wando me hannun vest, sai dai bata saka wani riga aciki ba kamar yanda ake saka wa, blue colour ne na jeans, sai ta tufke gashin ta a tsakiyar kai da jelan

Tana fitowa ta tarar da Daddy zaune yana amsa call, shi lokacin ya daɗe da tashi ma har ya fita waje ya gaisa da baƙi, shigowan sa kenan yasoma waya da wani abokin kasuwancin sa

Zama tayi gefen sa har yagama sannan yakalle ta cikin so da ƙauna yace “My Baby kin tashi?”.

Gyaɗa masa kai tayi tana turo baki gaba

Murmushi yayi yashafa mata kai kana yace “oya tashi muje muyi breakfast tukuna sai ki faɗa min meke damun ki”.

Dasauri tatashi tariƙo hannun sa suka nufi kan dainning inda aka jera musu breakfast kala-kala

Akan cinyan sa ya’ajiye ta yahaɗa musu duk abinda suke buƙata, shi yadunga ciyar da ita har suka kammala sannan suka dawo parlour

Jan hannun ta yayi suka koma bedroom ɗin sa inda yanuna mata wasu manyan Trollys guda uku yace mata duk tsaraban ta ne, sannan yaƙara mata da sabuwar waya iPhone 11pro har da Lapton tare da keey ɗin mota, sai yanuna mata wani ƙaton computer me kamar t.v yace mata sai ta’ajiye a ɗakin games ɗin ta

Ihu kawai RAUDHA take yi tana murna, ɗarewa jikin sa tayi tai ta zuba msa peck a fuska kamar zata cinye sa

Shi kuwa sai dariya yake yi yana jindaɗin yanda take murna da annashuwa

Waya yakira, babu jimawa ɗaya daga cikin bodyguard ɗin sa yashigo yanuna masa computern yace masa yakai ɗakin games ɗin RAUDHA, dayike yasan komi na gidan tunda shine Amintaccen sa, haka yaɗauka yafice su kuma suka dawo Parlour

A ranan tare suka wuni ko fita be sake yi ba

Wajen 02:00pm. Ramcy tazo gidan taya Daddy murnan dawowa, har Part ɗin shi RAUDHA tajanyo ta tunda dama sun saba dashi, kuma shima ya ɗauke ta tamkar ƴar sa ne tunda RAUDHA tana son ta, duk abinda zai iya ma ƴarsa to itama zai mata

Har ƙasa tazuƙuna tagaishe shi, ya’amsa mata cikin fara’a yana ta tambayan ta mutanen gida, daga ƙarshe yace mata tatashi tazauna itama kan kujera, babu musu kuwa tatashi tazauna ɗin kamar yanda yabuƙata, sai suka soma hira gaba ɗaya su ukun cikin nishaɗi

Sai kusan magriba Ramcy tace zata tafi, Trolly ɗaya na tsaraba Daddy yabata, dama yayi ne don ita, itama RAUDHA sai da taƙara mata da wasu abubuwan, Ramcy tayi murna sosai kuma tayi ma Daddy godiya har sai da yace ya isa

Duk da yasaba bata kyauta amma na yau yafi na ko yaushe tunda wannan tafiyan wajen watanni uku yashafe kafin yadawo, kuma be saba yin hakan ba iyakan wata ɗaya ko zuwa kusan biyu yake yi

Drever yamayar da Ramcy har gida tare da tsaraban ta

Su ma sauran ma’aikatan gidan duk sun samu nasu tsaraban, duk wanda yake gidan kuwa ya shaida tunda an ba kowa, sun yi murna sosai tunda tsaraban ba kaɗan bane.

      Da dare suna zaune aka kira Daddy a waya, abokin kasuwancin sa ne yake shaida masa akwai matsala yayi gaggawan zuwa yanzu

Kayansu da sukayi oda a UK sun samu matsala, kuma ana buƙatar su nan da 24hours

Dole hankalin Daddy yatashi, anan yake faɗa ma RAUDHA zai koma China akwai matsala

Ai nan RAUDHA tasa mishi fitina, daƙyar ya rarrashe ta tahaƙura

Wanka yayi yasauya kayan sa zuwa farar tissue yai shigan sa na hausawa, dama Daddy be cika saka kayan turawa ba anan ɗin in ba can yaje ba, amma idan yana nan shigan hausawa yake yi na manyan kaya

Motoci biyar na bodyguard suka raka sa zuwa airport, har da RAUDHA sai da tabi shi sai kukan taɓara take mishi yana rarrashin ta

Sai da Flight ɗin su yaɗaga kafin suka dawo gida.

       Wajen ƙarfe 11:37pm. RAUDHA tana cikin tsaka da barci tatashi a firgice sakamakon harbin Bindiga da taji

Sosai ake harbi kamar za’a tarwatsa gidan

Nan da nan tafirgice tasaki kuka cike da tsananin tsoro, wani irin kifo wa tayi takai tabuga kanta da tyles, but bata damu ba tanufi ƙofar ɗakin tasaka keey jikin ta na wani irin kyarma kamar an saka ta a shock, zame wa ƙasa tayi tana ci gaba da sharɓan kuka, wani harbin da tasake ji kurkusa sai da tasaki fitsari tarufe bakin ta dasauri tana ƙwalalo idanu, tsaban tsoro ƙirjin ta kamar zai faso yafito, daƙyar tararrafa tanufi bakin gadon taɗau wayan ta tasoma kiran Numban Daddyn ta, sai dai baya shiga hakan yasa tasake ɓarke wa da kuka kamar ana tsuma ta, izuwa lokacin majina da hawaye ne suka haɗe sukai dame-dame a fuskar nata, yau dai ta sadakar mutuwa zatayi

Hannun ta na rawa tanemo Numban DPO ta danna masa kira, yana ɗauka tasoma faɗa masa abinda ke faruwa tana yi tana kuka

Ai kuwa nan da nan DPO da yaran sa suka nufo gidan

A can kuwa tsakar gidan sai karan batta ake yi tsakanin ɓarayin da suka shigo su wajen ashirin da bodyguard ɗin gidan, in banda musayar wuta babu abinda suke yi duk an ji ma wasu ciwo

Gaba ɗaya gidan ya hargitse kamar filin dambe, masu aiki duk sun nemi maɓuya, haka ma maƙota duk da basu san takamaiman inda ake harbin ba.

          RAUDHA tana gama waya da DPO Yayan ta takira tana kuka tana faɗin “Yaya don Allah kazo kaɗauke Ni zasu kashe Ni, wayyo Allah yaya na shiga uku shikenan zasu kashe Ni mutuwa zan yi…”

Sai tasaki kuka tana sharɓan majina

Hankalin Suhaib a matuƙar tashin hankali yake tambayan ta su wanene? Amma ina ta kasa ma magana sabida tsaban kuka

Sai da yayi ta faman rarrashin ta kafin daƙyar ta’iya mishi bayani

“Don Allah kiyi shiru kinji? Kiyi shiru my dear please, I promise you babu abunda zai same ki baza su kashe ki ba kinji… Sorry.. sorry My dear zuwa gobe insha Allahu zan zo..”

“A’a yaya kazo yau katafi dani don Allah zasu kashe ni”.

Suhaib kamar zai yi kuka yace “Dear baza su kashe ki ba yanzu bari in Kira Asp. Aryan yanzu zai zo kin ji ki kwantar da hankalin ki, ina zuwa zan sake kiran ki”.

Ɗif yakashe wayan

Sake maƙurewa tayi ajikin bango tana ci gaba da kukan ta cike da tsananin tsoro.

A waje kuwa har ƴan sanda 👮 sun zo kuma anyi nasaran kama wasu, wasu kuma sun gudu, a cikin bodyguard ɗin wasu duk sun samu harbi sannan an kashe mutane uku har lahira.

RAUDHA bata buɗe ƙofar ɗakin ta ba sai da taji muryan DPO, nan tasake haukace musu akan sai sun kira mata Daddyn ta, shi da kanshi DPO ɗin yakira sa amma wayan sa akashe, shaf sun manta a yanzu ɗin yana jirgi wayan sa baza ta shiga ba

A taƙaice dai aranan daƙyar suka rarrashe ta suka haɗa ta da ƴan sandan da zasu yi gadin ɗakin ta, kuma bata yarda ta kwana ita kaɗai ba sai da aka kira mata su Saude da sauran masu aiki, a waje kuma duk aka ƙara matakan tsaro

RAUDHA ƙiri-ƙiri ta kasa barci in banda firgita babu abinda take yi duk da kuwa ba ita kaɗai bace a ɗakin, kuma ta hana kowa barci dole su zauna gadin ta, aranan dai haka suka kwana gaba ɗayan su ido buɗe har Suhaib da ba ma agidan yake ba, koda yakira ta saka mishi rigima yayi kar yafara yakashe wayan, a haka takwana da waya a kunne tana jin motsin sa, shi kuma sai faman kwantar mata da hankali yake yi tunda tuni barci ya ƙaurace ma idanun sa, ko kaɗan bazai iya barci ƙanwar sa na can cikin firgici ba.

Ta tsorata sosai ita duk a ganin ta ɗauke ta suka zo yi tunda tasha jin ana ɗauke mutane akashe su, sosai take matuƙar tsoron ƴan kidnappers, bata so ko kaɗan taje hannun su._______📖Ƙarfe 07:30am. Yayi ma Suhaib a garin Zaria, lokacin da yashiga gidan RAUDHA maƙalƙale shi tayi tana ta kuka, daƙyar yararrashe ta tayi shiru sannan yace “taje tahaɗo kayan ta su tafi” babu musu kuwa tasaka Masu aiki suka haɗa mata kayan ta+

Duk ka gaba ɗaya duk wani abun buƙatun ta sai da Suhaib yasaka aka kwashe mata aka zuba a mota, mota biyu aka cika drevers sukai gaba dashi, su kuma sai suka biyo Flight suka nufi Abuja

Drevern sa yazo yaɗauke su a airport suka nufi gidan Suhaib ɗin dake Asokoro, babban gida ne me hawa biyu, sosai gidan yahaɗu matuƙa gashi an kashe kuɗi kamar baza’a mutu ba

Drever na yin parcking suka fito, Suhaib yariƙe mata hannu suka nufi cikin gidan, suna shiga parlour’n gidan

Matar sa Farida tafito daga ɗaki tana kallon su da murmushi a face ɗin ta, tana da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe

“Sannun ku da zuwa, maraba da ƙanwata”.

Suhaib ne kaɗai ya’amsa gaisuwar matar tasa yayinda RAUDHA kuma in banda kallon ta babu abinda take yi, har yanzu tana cike da tsoro sosai duk da kuwa sun bar garin

Zama Suhaib yayi yazaunar da ita kusa dashi

Ita kuma Farida sai tanufi Fridge taɗauko musu drinks tahaɗo da Cups ta’ajiye musu a gaban su kana tazauna tana cewa “My Husband kayi sauri da yawa”.

Suhaib dake kallon ta yace “to me zan zauna yi tunda na ɗauko ta? An gama gyara mata ɗakin saman?”

“Eh an gama, Allah yakyauta gaba to, mun gode Allah da babu abinda yafaru”.

Sai kuma tamayar da idanun ta kan RAUDHA tace “Baby babu magana?”

Sai lokacin RAUDHA tabuɗi baki tace “Sannu to”.

Gaba ɗaya sai da suka dara ganin yanda tayi maganar tana turo baki

Suhaib yace “tashi Baby in Kai ki ɗakin ki sai ki huta ko kafin akawo miki kayan ki?”.

Babu musu tamiƙe yariƙe mata hannu suka haura sama

Farida tabi su da kallon aranta tana mamakin irin ƙaunar da Mijin nata yake nuna ma ƙanwar sa

Ko kaɗan bata kishi da RAUDHA, hasali ma itama tana ƙaunar ta sosai tunda ta silan ta ne tasamu Suhaib ɗin, da fari ita take mahaukacin ƙaunar sa tun lokacin da yasoma aiki a Companin Daddyn sa, itama a lokacin tasamu aiki a Companin, sai tasoma shige masa suna mutunci batare dashi yasan son sa take yi ba

Duk wanda yake mu’amala da Suhaib dole ne yasan ƙaunar da yake ma ƙanwar sa, koda kuwa baka taɓa ganin ta bane labarin ta sai ya ishe ka, be da wani magana sai ta RAUDHA, hakan ne yasaka itama Farida tasoma nuna ƙaunar ta gare ta, duk da batasan RAUDHA ba amma sai tasoma tayasa ƙaunar ta, wannan dalilin ne Suhaib yasake sakin jiki da ita, domin sosai yake jin daɗin yanda take nuna ƙaunar ta ga ƙanwar sa, komi tasamu tace yakai ma RAUDHA, komi maganar ta RAUDHA, hakan yasaka soyayyar Farida tashiga ransa ainun tunda tana son ƙanwar sa, ita kanta Faridan tasan sabida RAUDHA yake son ta

Har Allah yasa daga ƙarshe suka yi aure, wajen shekara ɗaya da rabi kenan yanzu

RAUDHA sau biyu tataɓa zuwa gidan, sai dai har yanzu ta kasa sake jikin ta da Faridan duk da kuwa tana nuna mata kulawa da soyayya, sai dai ita akwai ta da rashin sabo idan har bada Daddy ko Suhaib ba bata son wani yashiga jikin ta, that’s why bata cika zuwa ba tunda shi Suhaib ɗin yana zuwa can.

      A halin yanzu Farida ta ajiye aikin ta, tun sanda tasamu ciki Suhaib yace mata sai dai ta’ajiye aikin ta rainan masa Yaron sa, dama can shi baya son Matar sa tariƙa aiki tunda suna da kuɗin da komi zai iya wadata ta dashi

Itama kuma bata yi musu ba ta’ajiye kamar yanda yake so ɗin, but duk wata yana bata albashi hakan yaƙara faranta mata sosai, kuma taji daɗin abun da yayi mata shiyasa bata damu yanzu tayi aiki ko kar tayi ba, tunda mijin ta na mata duk abinda take so..

Dafa kafaɗan ta yayi hakan yasa tadawo duniyar tunanin da talula tabi sa da ido

Murmushi yasakar mata yace “tunanin me kike yi haka har na dawo baki ji ni ba?”

Numfashi taja tace “babu komi Husband”.

“Ok to ki kula min da ƙanwata don Allah, idan tatashi kiyi mata duk abinda take so ki kula da ita plz sweetheart?”

Murmushi tayi tace kar ka damu insha Allahu bazan baka kunya ba Mijina”.

Kyakykyawar murmushin sa yayi mata yana shafa gefen kumatun ta yace “Thanks Sweetheart, yanzu ta kwanta ne kayan ta na kan hanya idan sun iso sai ki saka a shigar mata dashi ɗakin ta, Ni zan tafi office insha Allahu Nima bazan daɗe ba zan dawo”.

“To amma bakayi breakfast ba katafi yanzu kuma haka zaka tafi kenan baka yi ba?” Tayi maganar idanun ta cikin nasa

Suhaib yace “nayi late yanzu Sweetheart idan na je office zan yi kinji?”

Gyaɗa masa kai tayi

Shi kuma yayi mata kiss a lips ɗin ta sannan yasake shafa kumatun ta yace “sai na dawo Byeee ki kula da kanki”.

Murmushi tayi masa tare da addu’ar dawowa lafiya.

Sai da yabar parlour’n kafin tamiƙe daƙyar takoma ɗakin ta dake ƙasa.

         🌐🌐🌐

Kwana biyu da zuwan RAUDHA gidan sannan  Suhaib yasamu Numban Daddy ya shiga, lokacin suna zaune a parlour sai yatashi tsam yafice, sai da suka tattauna da Daddy ɗin kafin yadawo yamiƙa wa RAUDHA wayan

“My sweetheart ga Daddy zai yi magana dake?”

Wani irin tsalle tayi tararumi wayan tana ihu tasaka a kunne

“Daddyyyy”. Tafaɗa da ƙarfin da yasa Suhaib da Farida suka rufe kunnen su suna dariya

Dama koda yafita yin wayan batasan da Daddy yake yi ba

Daga can Daddy murmushi yayi cike da farin ciki yace “my Baby Kar ki fasa min dodon kunne mana”.

Kawai sai tasaki kukan shagwaɓa tana faɗin “Daddy nayi missing ɗin ka.. yaushe zaka zo kaɗauke Ni?”

“Sorry My Baby.. bazan dawo nan kusa ba coz akwai matsala da kayana suka samu dole zan zauna zuwa ɗan wani lokaci”.

Kuka tasoma mishi sosai tana bubbuga ƙafa tace “Daddy Allah Ni bazan koma can ba sai dai kazo kaɗauke Ni bazan iya zama Ni kaɗai ba”.

Daddy yace “my dear ai dama bance ki koma can ɗin ba, tunda kina gidan yayan ki zaki zauna har nadawo sai in zo in ɗauke ki ko?”

Ɗaga kai tayi takalli Suhaib dake kusa da ita, fuskarta sharkaf da hawaye tace “Daddy bana son nan..”

Riƙo hannun ta Suhaib yayi kafin yace “baki son wajena ko my sister? Kin fi son ki zauna acan kidnappers su kama ki su kashe ki..”

Tun kafin ma yaƙarisa maganar tasoma girgiza mishi kai

Daddy yace “my dear ki zauna a wajen yayanki zaki fi samun kulawa, kinga waɗannan mutanen da suka shiga gida na anyi bincike an gane ke suka zo ɗauka sabida suyi garkuwa dake, idan kika koma yanzu akwai matsala”.

Cikin zubar hawaye tace “to Daddy zan zauna bana so su kama Ni”.

“Yauwa my dear, kinga sai ki soma karatun ki anan tunda Yayan ki yace min an soma siyar da Admission uhmm?”

Shiru kawai tayi bata ce komi ba

Suhaib da har yanzu yana riƙe da hannun ta yasoma murza mata yatsu yana faɗin

“Daddy zata zauna anan ɗin insha Allahu zanna kula da ita babu abinda zai faru da ita”.

“Yauwa Suhaib ka kula min da ita sosai duk abinda take so kayi mata, idan nadawo zan zo har nan in ganki, and mutanen da suke neman ki acan ma baza su ƙara ganin ki ba bare su kama ki ko my dear?”.

“Eh Daddy”. Tafaɗa tana turo baki

Farida ita dai nata ido ne, kallon su kawai take yi cike da burgewa, tabbas duk wanda yazauna dasu zai san suna matuƙar ƙaunar ta, tana jinjina irin girman soyayyar da suke nuna mata, tana ta kallon su har sanda suka gama wayan ita kuma RAUDHA tamiƙe dasauri tanufi upstairs inda ɗakin ta yake

Tana shiga tafaɗa kan gado tana rufe idanunta, ko kaɗan bata jin daɗin zaman gidan, ta saba da can ta saba da rayuwanta ita kaɗai, a kwana biyun nan sosai take jin kewar can, ga matsanancin kewar Ramcy da take ji, ko babu komi baza ta so tarabu da ƙawarta ba shiyasa duk bata jindaɗi a zamanta na nan

Tashi zaune tayi taɗau wayan ta dake ajiye a bed side drower, tun sanda tazo takashe ta’ajiye bata sake ɗauka ba sai yanzu, kunnawa tayi tay dialling Numban Ramcy, sai da taɗauka sannan takoma takwanta

“My Besty Ina kika shiga nayi neman ki har na gaji?” Cewar Ramcy kamar zata yi kuka

Lumshe idanu RAUDHA tayi kafin tabuɗe tace “I miss You my Besty.. Ina Abuja?”

“Shine baki kira ni kin sanar min ba? Sannan kika kashe wayan ki, naje gidan ku but ba’a buɗe min ƙofa ba, kullum sai naje ko yau ma sai da naje amma banga kowa ba, meke faruwa ne?”

Abinda yafaru RAUDHA tasanar mata

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… Amma basu yi miki komi ba ko Besty?”

“Babu abinda sukai min ki kwantar da hankalin ki”.

Ajiyan zuciya Ramcy tasaki da ƙarfi wanda sai da yasa RAUDHA darawa tace

“Wannan ajiyan zuciya haka my Ramcy?”

“Hmm ai dole ne my Besty wlh bazan taɓa jindaɗi ba idan wani abu yasame ki, dole zan shiga tashin hankali sosai”.

Murmushi RAUDHA tayi cike da jindaɗi batare da tafurta komi ba

“To yanzu yaushe zaki dawo ko sai Daddy ya dawo garin?”

Girgiza kanta RAUDHA tayi fuskarta na nuna damuwa tace “Besty bazan dawo nan kusa ba sabida waɗanda suke son yin garkuwa dani suna nan ba’a kama su ba, dole zan zauna anan har sanda za’a yi solving matsalan”.

Shiru Ramcy tayi batace komi ba

Sai da RAUDHAN tasake mata magana kafin tace

“Shikenan Besty mun yi nisa?”

“Nima banji daɗi ba wlh, amma komi zai wuce ai zamu sake haɗu wa ba da jimawa ba, zan saka Ya Suhaib yakawo ni”.

Ramcy tace “nima idan nasami lokaci insha Allahu zan riƙa zuwa har nan Besty, muna nan tare ako ina ne, nisan gari bazai hana Ni zuwa gare ki ba”.

Murmushin jindaɗi RAUDHA tayi kafin tace “Thanks friend Allah yabar mu tare”.

“Ameen ameen My Besty, kinga aunty Nafeesa ta haihu ɗan babu rai?”

Cikin damuwa RAUDHA tace “oh yaushe kenan?”

“Jiya ne, dama cikin be isa haihuwa ba”.

“Eyya.. ki miƙa min gaisuwa ta gare ta kinji?”

“Insha Allahu zata ji Besty”.

Daga nan hira suka ɗan taɓa kaɗan kafin takashe wayan ta’ajiye

Tana nan kwance shiru kamar ruwa ya ci ta, sai kuma daga baya tamiƙe taɗauko HangBag ɗin ta wanda tazuba  ƙwayoyin ta

Tunda tazo gidan komi bata sha ba, shiyasa take jin ta daban

Kallon cikin jakar tayi, babu yawa duk ya kusa ƙare wa

Tsaki taja tana ajiye jakan, sai kuma taɗauka taciro tasoma afa ƙwayoyin, sannan kuma takoma takwanta tana lumshe idanun ta, ajiyan zuciya kawai take sauke wa har zuwa lokacin da ƙwayoyin suka soma mata aiki, gyara kwanciyarta tayi babu jimawa barci yayi awon gaba da ita, a lokacin ƙarfe 05:30pm.

Har bayan isha’i bata farka ba, don haka Farida tashigo ɗakin domin tatashe ta tunda ta shigo har sau biyu tana duba ta

A bakin gadon tatsaya tasaka hannu tana shafa baby face ɗin ta, ta jima tana ƙoƙarin tashin ta kafin tabuɗe idanun ta da suke a rine sosai, sake lumshe idanun tayi tana buɗe wa ahankali

Murmushi Farida tayi mata tace “ƙanwata wai barcin nan baya isan ki ne? Tunda kika zo babu abinda kike yi koda yaushe sai barci, ko kasa sai ya shafa miki lafiya ai”.

Kallon ta kawai RAUDHA take yi bata ce komi ba, sai dai a yanzu ɗin ta ɓata fuska

Still Farida murmushi tayi tasaka hannu tana janye jakar dake ajiye akan gadon tana faɗin “kiyi haƙuri kinji, naga Yakamata ki tashi kiyi sallah ne kici abinci tunda lokaci na ƙure wa”.

Kamar ance taleƙa cikin jakan sai taga ƙwayoyin ciki, duk da Farida ba wai tasan kayan maye bane amma taga an rubuta sunan shi ajiki, sai kawai tasaki baki tana kallon RAUDHA dake ƙoƙarin miƙewa zaune

Bata ce komi ba kuma taɗau jakan tamayar mata inda sauran suke sannan tafice

Ɗakin su takoma inda Suhaib ke zaune yana faman aiki a Lapton, zama tayi kusa dashi kan Two sitter tana kallon sa, cikin sanyin murya tace

“Dama RAUDHA tana shan kayan maye?”

Cakk yatsai da abinda yake yi yana ɗago wa yakafe ta da idanun sa masu matuƙar kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *