RAWANIN TSIYA CHAPTER 5 BY FADEELAH
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA+
A yau Sunday wanda ya kasance 30th September na shekarar..
Hanifa tana zaune a kan gadonta cikin Duvet wuraren qarfe goma da rabi na safe. Bata dade da ta farka daga bacci ba. Da alama dai sauka gadon ne ya gagareta.
Tun ranar juma’a da al’amarin nan ya faru take tunanin what next for her regarding Sadiq, she had so many options wanda tayi reducing to just 3- ta cigaba da wulaqanta shi har ya tafi, tayi resigning ko kuma ta cigaba da aikin amma a canza mata department.. bata tsayar da shawara ba amma tabbas cikin wadannan options din zata dauki daya!
Wayarta ce tayi qara alamun text message ya shigo.
Janyo wayar tayi sannan ta duba… Alert ne na salary.
Gani nayi tayi zaraf ta tashi zaune yayinda take qara kallon figures na salary dinta..
Ranta a matuqar bace na ga ta yaye Duvet din da ta rufa da shi tana fadin “ni za’a yi ma rashin mutunci??? saboda kudin shi ne ke circulating a kamfanin sai ya zabge mun salary?? toh wallahi bai isa ba..”
Gani nayi ta sauka daga kan gadon ta wuce ta fita tana ta masifa.. ko tsayawa ta dauki robe na rigar baccin nata bata yi ba.. daga ita sai gajerar sleeveless inner one din, gashinta all messy as usual idan ta tashi daga bacci.
Kai tsaye sashen Paapa ta nufa.
Ta tarar da shi kwance a kan 3-seater kujera riqe da remote yana kallon News a tashar Al-jazeera.
Yanayin yadda ya ga Hanifa kuwa ya tabbatar akwai matsala..
Gani nayi ya tashi zaune yayinda ta qaraso tace “Good morning Paapa”
“Good morning Baby.. zo ki zauna nan..” ya nuna mata space a gefen shi sannan ya cigaba da fadin “…ya na gan ki haka??? me ya faru kuma???”
Hanifa wadda ta zauna a gefen shi ce ta miqa mishi wayarta tare da fashewa da kuka tana fadin “Paapa ka ga anyi salary amma ji abinda aka tura mun.. ai ba haka aka rubuta za’a biya ni ba a offer letter.. this is like 50% off fa Paapa.. Sadiq ne yake nema ya wulaqanta ni saboda kudin shi ne… ni wallahi…”
“Baby sssshhhh, stop crying and listen to me. Kin tuna cewar an baki suspension har na sati biyu?? are you aware that idan an ba mutum suspension hakan yana nufin baza’a biya shi kudin adadin kwanakin da ya je suspension din ba?? its logical tunda you cant be paid for aikin da baki yi ba” Paapa ya fada yayinda yake riqe da hannunta.
“toh Paapa ni yanzu me wannan kudin zasu yi mun??? bazasuyi covering expenses dina ba na wannan watan.. Ko complete salary dina ma maneji zan yi balle 50% of it…”
“Zan tura miki kudi a account dinki… shikenan”
Tana share hawayenta ne ta matsa tare da rungume shi tace “nagode sossai Paapa, you are the only person I have in this world that care about me.. I am grateful for having you as my Paapa.. I love you so much my bestie”
Paapa wanda yake murmushi yace “I love you too my Baby”
Hanifa wadda tayi breaking hug din ce tace “toh Paapa wai for how long will this continue???”
“what??”
“this whole Sadiq thing.. Ka mayar mishi da kudin shi ya tafi ya bamu wuri for good, I swear even after this six months da zai yi ina mai tabbatar maka he will always come back to claim his money saboda na ga alama bayada kirki”
STORY CONTINUES BELOW
Paapa yana dariya yace “Sadiq is here to stay in our lives Baby.. he is practically my son tunda mahaifinshi was my very good friend.. Maganar biyan shi kudin shi kuwa bai taso ba don kamar yadda na fadi miki ya ba kamfanin kudin kyauta ne kuma banda abinki, ina na ga kudin da zan biya shi??? do you know the huge amount of money that he invested in the comapny?? not to mention debts din da yayi settling… Please Baby ki qyale shi ya huta haka nan”
turo baki tayi tace “toh shikenan Paapa..”2
Paapa dai murmushi yayi yana mamakin Hanifa.. he never thought cewar zata tsani Sadiq har haka.. shi kam da farko yayi tunanin they will get along especially ganin yanayin rayuwar Sadiq very simple..
“Yauwa lest I forget Paapa, anjima zan fita.. zan je shopping”
“hmmmm, Baby kullum shopping ba kya gajiya..”
Dariya tayi tare da fadin “Paapa bazaka gane bane”
“Ni kuwa na gane tunda you can’t save a single dime in your bank account” ya fada yana hararar ta.
Tana murmushi tace “zan fara saving kwanan nan”6
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Wuraren qarfe biyar na yamma Paapa da Hafeez suna zaune a babban falon gidan suna kallon news suna hira.
Mamy ce ta shigo riqe da tray mai dauke da bowls na fruit salad.
Hafeez ya miqe da sauri ya nufi wurinta ya karba yayinda Paapa yace “ke kam Mamy ba kya gajiya.. instead of ki ba maids su kawo, I see that you will never change” ya qarasa maganar yana murmushi.
Mamy wadda ta sakar ma Hafeez tray din ce tace “Paapa yana da kyau in dinga motsa jiki besides you know that I prefer doing these things by myself”
Hafeez ya ajiye tray din a kan side stool wanda yake kusa da Paapa yayinda ya dauki daya daga cikin qananan bowls din zai fara zuba mishi…
Wayar Paapa ce tayi ringing na ga ya duba.. sunan Hanifa ya gani.
Ji nayi yace “Baby hooo, I wonder what the complain will be yanzu”
aikuwa yana answering call din tun kafin yayi magana na ga ya zaro idanuwa yayinda ya miqe da sauri dafe da qirjin shi… hankali a matuqar tashe yace “what??? where is she???…”
Mamy da Hafeez suka mayar da hankulan su kan shi yayinda suka zuba mishi idanuwa babu ko qyaftawa..
Gani suka yi ya saki wayar ta fadi qasa yayinda ya fara fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..”
Mamy ce ta riqe shi tace “Paapa me ya faru??” Yayinda Hafeez yayi saurin daukar wayar ya sa a kunne yana sauraron mai magana on the other side of the call.
Mamy wadda take riqe da Paapa dai ji tayi yace “Hanifa…” daga nan kuma sai ya zame ya fadi akan kujera sumamme.2
Aikuwa nan da nan ta fara salati tana kuka yayinda Hafeez ya jefar da wayar hannun shi a rude ya dawo kan Paapa…
toh fa.. me ya faru kuma??
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
BRISTOL PALACE HOTEL
NASSARAWA-GRA
Kwance yake a kan three-seater kujera na lounge din deluxe suite dinshi. Mai karatu da ganin yanayin Suite din zaka amince ya ci kudin shi don kuwa babu wani abin more rayuwar dan Adam da babu a cikin shi… it’s more like a home!!
Ko ina na Suite din looking spotlessly clean kamar ba mutum bane yake zaune a ciki.. Wani lafiyayyen qamshi yake tashi wanda ya hadu da sanyin AC ya bayar da wani yanayi mai dadin gaske.
STORY CONTINUES BELOW
Babu qarya Sadiq yana more ma rayuwa yadda yakamata.
Riqe yake da I-pad dinshi yana
video call da wata farar yarinya kyakyawar gaske.. da ganin ta kuwa bata rasa dangantaka da larabawa domin kuwa tana kama da su.
“…I swear ka canza completely, ko kira na ka daina yi like before. Yanzu haka I am sure da ban kira ka ba you won’t call me” na jiyo tana fadi yayinda take turo mishi baki cikin shagwaba.
Yana murmushi yace “I tried calling you yesterday and network denied the call from going through.. besides it’s just yesterday that we didn’t speak fa, anyways i’m sorry my sweet Hanan”
itama murmushi tayi tace “its okay my chocopie, so tell me.. ya kake??”
“I’m good… Alhamdulillah”
“Something tells me kayi sabuwar budurwa, oya Spill. I’m sure ma saboda ita ne ka share ni” ta fada cike da tsokana.
Hararar ta yayi yace “babu wata budurwar da nayi.. ni har yanzu ke nake jira amma kina ta yi mun wulaqanci saboda wannan Hussain din naki”2
Fashewa tayi da dariya tace “Chocopie we both know that with the stone heart you’ve got, you are incapable of falling in love with any lady, kawai kana gani na a matsayin wadda zaka iya zama da ita cikin sauqi ne.. probably because I know you very well and I know what you like and dislike but the truth is that’s not what I want kuma ka sani.. I want LOVE and I am getting alot from Hussain”
“Meyasa kike fadin haka Hanan, dagaske ina son ki.. irin son da nake miki ma ya fi wanda Hussain din yake miki, Just Marry me and I will prove it to you..”4
“Prove it to me before the marriage”
Fashewa yayi da dariya yace “toh ai dai kin san I don’t know how to do that ko???”
“ashe kuwa baka son Hanan”
“ina sonta mana”
“Hanan does not like ugly broke asses kamar ka” ta fada yayinda tayi mishi gwalo.
Fashewa yayi da dariya yace “Ni??? ina matsayin dan uwan ki kike wulaqanta ni?? I swear idan baki bi ni ahankali ba sai nayi shige da fice na rusa abinda yake tsakanin ki da Hussain in ga tsiya..”1
Zaro idanuwa tayi tace “ah ah yi haquri, I dont want to be single and lonely like you”
A duniyan nan Hanan ita kadai ce macen da take sa Sadiq yayi ta magana har sai ya gaji.. Sadiq ba mai magana bane amma idan ka ji shi yana zuba bayani toh fa da Hanan ne. Hatta Naana da qanwar shi Asma’u baya zama suyi hira kamar haka..
“kar ki damu Insha Allah sai na riga ki yin aure”
“what??” ta fada tare da zaro idanuwa sannan ta cigaba da fadin “…don Allah kayi haquri.. kai da ko matar baka samu ba balle.. abeg ooo, I can’t wait that long please”
Fashewa yayi da dariya, yana shirin yin magana ne wayar shi tayi ringing.
Gani nayi ya kalli fuskar wayar ya ga sunan Hafeez….
“Hold on please, let me take this call”
“Go ahead Handsome, bari in cigaba da kallon kyakyawar fuskar ka while you are at it”
Girgiza kai yayi yana murmushi yace “when you just called me an Ugly broke ass?? sai kin biya coz it’s not for free”
Dariya tayi tare da yi mishi gwalo yayinda yayi answering call din Hafeez.
“Bro what’s up??”
Gani nayi ya tashi zaune da sauri hankali a tashe yace “what??? me ya faru???” daga nan kuma yayi shiru yana sauraren bayanin Hafeez sannan yace “Hanifa??? tana ina yanzu???”
STORY CONTINUES BELOW
Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude sannan yace “Ya Salam, I am on my way”
Yana kashe wayar ne ya jefar tare da kallon Hanan yace “babes I gotta go..”
“Me ya faru??? wacece Hanifa?? dont tell me she is…”
Miqewa yayi tsaye yace “No no no Hanan, it’s a long story.. bari in je in dawo and I promise to tell you everything”
“Okay toh shikenan.. take care”
“You too dear.. I love you”
“I love you too Chocopie”
☆☆☆☆☆☆☆☆
NASSARAWA HOSPITAL
KANO
Zaune suke a waiting room na dakin da aka kwantar da Paapa yayinda Mamy take ta kuka.. Hafeez kuma yana ba Sadiq labarin abinda ya faru.
Har lokacin da Sadiq ya iso likitocin sun hana kowa ganin shi.. da alama it’s kinda serious.
“…..wai she was in shoprite ne tana shopping shine accidentally suka yi karo da wani yaro, a yadda suka fada dai shine yake da laifi wanda he was about to apologize to her sai ta kwashe shi da mari a cikin mutane.. shine instantly yaron ya kira police suka tafi da ita.. the problem is yaron dan gidan Deputy Governor ne sannan ya ba DPO din da yake in charge strict warning akan kar a bada bail dinta don sai ta kwana a cell”9
“Subhanalillah.. yanzu kana nufin tana police station??” Sadiq ya tambaya cike da mamaki.2
“eh.. tana can. Actually bamu samu zuwa muka duba ta ba saboda halin da Paapa yake ciki.. we had to just rush him here sai kuma na kira ka”
Mamy cikin kuka tace “wallahi Hanifa bata jin magana, Yarinya baka iya hana ta yin abu ko ka sanya ta yi.. Kullum tana cikin wulaqanta mutane, yanzu ga irin abinda mugun halinta ya janyo ma mahifinta”
Sadiq ne yayi gyaran murya yace “relax Mamy, insha Allah he will be fine. Mu jira likitocin su fito mu ji abinda yake damun shi tukun”1
“Hanifa fa??” Hafeez ya tambaye shi.
Maganar gaskiya itace Sadiq ma ya goyi bayan lallai a bar Hanifa ta kwana a police station din domin kuwa it’s a good way to put some sense into her.. Gaba daya ya tsani yarinyar, infact he is very happy da hakan ya faru da ita.. the only problem is halin da mahaifin ta yake ciki, a dalilin haka dole ne ya san yadda zai yi ya sa a fiddo ta…
“Dont worry Hafeez, I will go get her but let’s wait and hear from the doctors first”
Bayan kusan minti talatin ne likitocin suka fito daga dakin Paapa. Gaba dayan su ne suka miqe suna tambayar abinda ke faruwa.
Dr. Mansoor wanda ya kasance family doctor dinsu ne ya gyara glasses din idanuwan shi yace “Ya akayi kuka bar Alhaji ya shiga irin wannan halin?? I thought we agreed akan kiyaye duk wani abinda zai tayar mishi da hankali.. Gashi yanzu haka jinin shi yayi mugun hawa”
Mamy wadda take kuka tace “kai Hanifa.. kai Hanifa..”
Sadiq ne yace “we are sorry doctor, what actually happened was beyond our control amma insha Allah zamu kiyaye gaba.. will he be okay??”
“eh toh for now he is stable kuma muna monitoring dinshi.. lets see what happens zuwa gobe”
“Zamu iya ganin shi???” Hafeez ya tambaya.
“No.. kuyi haquri zuwa gobe, yanzu dai kuyi qoqari ku yi reversing ko ma menene ya janyo mishi wannan matsalar so that idan ya farfado zuwa gobe he will feel good knowing that everything is fine”
Sadiq ne yace “Insha Allah, thank you doctor”
Bayan likitan ya tafi ne Sadiq ya kalli su Mamy yace “bari in je police station din, I think yakamata zuwa anjima Mamy ta koma gida kai Hafeez sai ka zauna, nima as soon as I’m done zan dawo sai mu kwana tare a nan din.. is it okay??”
STORY CONTINUES BELOW
Hafeez ne yayi saurin fadin “its okay” ya kalli Mamy wadda take qoqarin yin magana yace “kar ki damu, gobe da safe sai ki dawo tunda likita yace bazamu samu damar ganin shi ba sai zuwa goben”
Hakanan ba don ta so ba ta amince yayinda ta dinga yi ma Sadiq godiya tana sa mishi albarka.
☆☆☆☆☆☆☆
BOMPAI POLICE STATION
KANO
Zaune yake a ofis din DPO yayinda yake yi mishi bayanin case din Hanifa.
“wallahi ranka ya dade yarinyar tana da taurin kai ne don kuwa anyi da ita ta bashi haquri yadda al’amarin ba sai ya kai ga haka ba amma ta qi, instead ma zagin shi ta dinga yi shine yace a rufe ta a cell sai gobe a sake ta.. Yanzu haka
don bamu da yadda zamuyi amma da mun sake ta don kuwa tunda aka kawo ta take ta ihu tana masifa tana zagin mu.. duk ta cika mana kunnuwa” Ya dan yi shiru sannan yace “kana jiyo hayaniyar ta ko?”3
Tabbas tunda Sadiq ya shigo station din yake jin ihun mace cike da masifa .. kenan Hanifa ce?? Unbelievable!1
Murmushi Sadiq yayi yace “I understand DPO, dan bani few minutes.. let me make a call”
Lambar wayar PA dinshi na Bunza Oil & Gas yayi dialing..
Nan da nan yayi picking.. bayan sun gama gaisawa ne na ji yace “please patch me through to the Kano commissioner of Police, tell him its urgent”
DPO dai jin haka sai ya saki baki.. Babu shakka ya tabbatar yanzu Hanifa zata tafi gida.
A gaban shi aka hada Sadiq da CP yayinda yayi mishi bayanin abinda yake faruwa.. DPO wanda ya gane ko waye Sadiq a cikin bayanin da ya ji yayi sossai yayi mamaki don kuwa idan ba fadi aka yi ba bazai taba kawowa Sadiq babban mutum bane a qasar nan duk a dalilin simplicity dinshi.. 3
Nan da nan CP yace ma Sadiq ya ba DPO wayar.. aikuwa yana karba ya miqe tsaye cike da girmamawa ya buga qafa tare da yin salute yace “Sir”
Commissioner yace “release the girl right now and connect me with the deputy Governor afterwards”
“okay Sir” Ya fada.
******************
Tsaye take a cell din tana ta masifa.. duk ta bi tayi jajawur (abinka da farar mace).
DPO ne da Sadiq suka shigo wurin wanda tun daga nesa da ya hango ta a cikin cell din sai kawai ya fashe da dariya- the first time da Hanifa ta sa shi dariya.1
DPO shima yana dariya yace “wallahi ranka ya dade kuna qoqarin zama da irin yaran nan.. ni kam ko daura mun irin su aka yi a qafa sai na kwance na ruga a guje don kuwa zama da irin su, fitinarsu kawai na iya kashe ka”3
Sadiq wanda yake dariya bai ce komai ba..
Sergeants din da ke zaune a counter ne duk suka miqe cike da girmamawa yayinda suka biyo bayan su har gaban cell din Hanifa.
DPO yace “ku bude fitinaniyar yarinyar nan mu sallame ta a samu sauqi”
Da sauri Sergeant daya ya ruga don dauko key na cell dinta.
Hanifa wadda ta hango Sadiq tun kafin su qaraso wurinta ne ta cika da mamaki yayinda ta ji haushi sossai a dalilin ganin shi da tayi yana dariya.. wato he is happy ganinta a nan din kenan??? Right now he is the last person she expect to see… me yake yi a nan din??? instantly ta tuno wulaqancin da yayi mata na zabge mata salary da yayi.. aikuwa nan da nan ta qara cika fam.
Ranta a bace tace “Yanzu duk mutanen duniya a rasa wanda Paapa zai sa ya zo ya fitar da ni daga wannan wurin sai kai??? How can Paapa do this to me??”
DPO wanda ya cika da mamaki ne yace “ke shut up, Yanzu babban mutum kamar wannan kike wulaqantawa?? kin kuwa san qoqarin da yayi miki har kika samu aka sallame ki?? gaskiya baki da godiyar Allah..”
“Please leave me alone… kai baka ga dariya yake yi mun ba?? an gaya maka tsakani da Allah ya zo nan din??”
Tana kallon Sadiq a wulaqance tace “Ni kam gwara na zauna a nan da ace kai ne ka fitar da ni..”
Aikuwa Sergeant ya sa makulli zai bude kenan ta furta wannan kalaman.
Da sauri Sadiq yace “Dakata..”
Gaba dayan su suka kalle shi..
“didn’t you hear the lady?? tace gwara ta zauna anan da ace ni ne na fitar da ita don haka please respect her wish and let her stay here”1
Hanifa wadda hankalinta yayi mugun tashi ne ta zaro idanuwa tace “what??”
“Good night” ya fada yayinda ya juya abin shi.7
DPO ne ya bi bayan shi yayinda sergeant ya zare makulli shima ya juya abinshi.
Hanifa wadda jikinta yayi mugun sanyi kawai sai ta rushe da kuka yayinda na ji tana fadin “Sadiq ka zo ka sa a bude ni, wallahi sai na gaya ma Paapa ya kore ka.. Allah ya isa tsakani na da kai, mugu, You are a monster. I hate you..”
DPO wanda yake biye da Sadiq ne yace “don Allah ranka shi dade ka tafi da yarinyar nan, wallahi bazata bari mu zauna lafiya ba.. na san bata kyauta ba akan abinda tayi maka amma tunda kun saba da halinta ka taimaka.. “
Sadiq ya girgiza kai yace “Haquri zaka yi DPO, ku barta ta kwana a nan din, First thing tomorrow morning sai ku sake ta… Allah ya bamu alkhairi”
Haka DPO ya saki baki yana kallon Sadiq ya fita ya barsu da Hanifa…2
Hahahahaha.. I am laughing out loud!!8
Washegari!+
NASSARAWA HOSPITAL
KANO
Zaune yake a waiting room din wuraren qarfe Goma na safe.
Bai dade da dawowa daga gida ba inda yayi wanka yayi breakfast… A yanzu haka Hafeez shima ya koma gida don yayi wanka yayi breakfast sannan su dawo tare da Mamy.
Sadiq dai aiki yake yi a macbook dinshi- aikin Bunza Oil & Gas. A gefe kuma I-pad dinshi ce yayi setting yadda zata dinga ganin fuskar shi yayinda suke hira..
A jiya dai sai da Hanan ta nace mishi ya bata labarin abinda ke faruwa.. Sossai ta tausaya ma Hanifa jin ta kwana a cell, dukda ta fahimci bata jin magana but still.. Yanzu haka roqon shi take yi akan ya kira ya ji ko an sake ta
“Chocopie gaskiya baka da human feelings, yanzu fisabilillah ka bar ta a cell sauro suna ta cizon ta?? wallahi I didn’t sleep well jiya saboda tunanin halin da take ciki. Please call and confirm idan sunyi releasing dinta”
Yana dariya yace “sannu sarkin tausayi.. duk wulaqanta ni da tayi baki ga laifinta ba?? dagaske Hanan idan kika ga abinda yarinyar nan take yi zata baki haushi.. the sight of her alone disgusts me”3
“Allah sarki, qila yarinta ce”
“what??? Yarinta?? I am sure ke da ita age mates ne, haka kike yi?? even Mini-Me thats way younger than her tana irin wawancin da take yi ne? please stop it.. she lacks discipline ne kawai.. Mahaifinta ne ma yake bani tausayi and if not for him I swear sai tayi kwana uku a cikin cell dinnan sannan ta fito..”
“whoa.. Chocopie wallahi kai mugu ne, how comes after all these years yanzu nake ganin this side of you???” ta fada cike da mamaki.
Murmushi kawai yayi yace “Ni ba mugu bane, just accept my proposal and marry me..you will see. I am the most simplest and easy going guy you will find around..”
“Inaaa, ai Chocopie kai gaba daya a dictionary dinka babu soyayya, ni kuma ka ga kowanne page na dictionary dina soyayya ce. ai kai irinka kawai zaka nema, someone with a stone heart wadda zaku zauna without feelings for eachother at all don kuwa idan ka auri macen da ita take sonka amma kai baka sonta I swear sai baqin ciki ya kashe ta..”
Sadiq wanda yake murmushi yace “Ya salaam Hanan.. is there anything I can say in my defence??”
“I doubt” ta fada tana hararar shi.
Dr. Mansoor ne ya shigo da sauri with two nurses trailing behind him.
Sadiq ya miqe yana fadin “lafiya??”
Dr Mansoor yana murmushi yace “he is awake and he looks good.. bari in duba shi tukun, afterwards you can see him”
“Alhamdulillah” Sadiq ya fada yayinda likitan tare da nurses dinshi suka shiga.
Komawa yayi ya zauna sannan ya dauki I-pad din yace “he is awake.. thank God”
“Masha Allah.. toh yanzu can you confirm idan sun sake ta, I believe mahaifin nata zai so ya gan ta now that he is awake..”
Aikuwa tun kafin ta qarasa magana suka jiyo masifa..
Hanifa dai da safen nan aka yi releasing dinta. kiran driver tayi ya zo ya dauke ta. Tana dawowa gida ne ta ji abinda ya faru wanda a dalilin rudewa da tayi ta kasa jiran Mamy ta kammala hada breakfast su je asibitin tare.. instantly tana yin wanka ta garzayo!
STORY CONTINUES BELOW
Kashe ma Hanan ido daya yayi
sannan yace “speaking of the devil” yayinda ta kwashe da dariya tace “please hasko mun ita briefly in ganta kafin ka kashe.. don na san you are about to face the worst confrontation ever..”
Aikuwa kamar yadda Hanan ta buqata hakan yayi.. Briefly ya hasko Hanifa wadda ta qaraso wurin shi yayinda ya kalli screen na I-pad din yace “will talk later Hanan..”
Hanan wadda idanuwan ta suke wangale bata iya cewa komai ba… hakan ya tabbatar mishi da lallai akwai magana wanda ya tabbatar zasu yi ta anjima.
“Yanzu saboda mugunta da rashin imani ka sani cewar Paapa yana kwance a gadon asibiti tun jiya shine ka bar ni na kwana a cell… wallahi sai na gaya ma Paapa. Shi da yake yi maka kallon saint, he has to know that you are nothing less than a monster” ta fada tana kuka.3
Sadiq wanda ko kallon ta bai yi ba na ga ya koma kan Macbook dinshi without saying a word to her..
He didn’t acknowledge her presence yet again!!
Cike da bacin ran hakan tace “ina Paapa yake??”
Sanin bazai amsa ta bane ta juya zata shiga dakin Paapa yayinda tayi karo da Dr Mansoor yana fitowa tare da nurses dinshi.
“Doctor how is my Paapa??” ta tambaye shi da sauri.
Dr Mansoor wanda ya dan yi murmushi yace “calm down, he is fine…”
“can I see him??”
Dr Mansoor yace “Yes you can even though he requested to see Sadiq tunda mun zata shi kadai yake nan at the moment”
Ya kalli Sadiq yace “you can both go inside”
Gani nayi Sadiq ya rufe Mac book dinshi sannan ya miqe ya bi bayan Hanifa wadda tuni ta shige.
****************
Zaune yake a kan gadon yayinda idanuwan shi suke a rufe. Hanifa ce ta shigo a rude tana kuka ta qaraso wurin shi ta haye gadon zata rungume shi yayinda na ga ya dakatar da ita.
Gani nayi tayi pause yayinda hankalinta yake a tashe tana kallon Paapan nata wanda ko kallonta bai yi ba.. Babu shakka ran shi a bace yake, it’s the first time da yake yi mata haka… Hawaye ne suka cigaba da wanke mata fuska yayinda jikinta ya fara rawa…
“Paapa I am so sorry please forgive me…”
“Son” na ji ya fada harda sakin murmushi.
Sadiq wanda ya qaraso cike da girmamawa yace “Ya jikin ka Sir?”
“Alhamdulillah.. Dr Mansoor ya fadi mun you stayed with Hafeez all through the night.. nagode sossai. Allah ya saka da alkhairi”
Kafin ya amsa ne Hanifa ta kalli Sadiq sannan ta kalli Paapa tace “Paapa why are you thanking him for being a hypocrite?? ka san abinda yayi mun kuwa?? bari na yayi a police station na kwana sai yau na..”3
“Please just shut up.. na gaji da wannan halin banzan naki. Idan har Sadiq ya bar ki a station kin kwana its definitely because you did something wrong, didn’t you think of what would have happened da kika mari yaron deputy Governor?”
“But Paapa..”
“enough Hanifa” ya fada cikin tsawa.
Hanifa wadda hawaye suke bin fuskarta gani nayi ta zaro idanuwa tana kallon Paapan nata cike da mamaki.. yau wacce rana Paapa yayi mata tsawa a dalilin stranger.. what is going on??? does this really mean cewar Sadiq ya fi ta matsayi a wurin mahaifinta? does this mean abinda ya faru da ita bai damu Paapa ba??2
Qwanqwaso qofa aka yi… Mamy ce da Hafeez suka shigo riqe da kayan abinci a hannun su yayinda fuskar su tayi displaying tsananin murna da farin ciki.. da alama dai sun ji labari cewar Paapa ya farka.
STORY CONTINUES BELOW
“Alhamdulillah Paapa is awake” Hafeez ya fada yayinda Mamy ta qarasa kusa da shi tace “ya jikin naka???”
Yana murmushi yace “Alhamdulillah..”
Hanifa dai gani nayi ta tashi ta koma wata kujera a gefe ta zauna yayinda take ta share hawayenta.
Mamy wadda ta zauna a kusa da Paapa ne take shafa wuyan shi da fuskar shi tana tambayan shi yadda yake ji…
Sadiq da Hafeez kuwa excusing kansu suka yi sannan suka fita suka bar a confused Hanifa zaune tana share hawaye.
☆☆☆☆☆☆☆☆
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA
Zaune yake a cikin motar shi a parking lot na gidan wuraren qarfe takwas da rabi na dare yayinda ya amsa incoming call dinta.
A yau din da rana aka sallami Paapa a dalilin nace ma Dr Mansoor da yayi na ya sallame shi tunda dai he is feeling okay.
Likitan dai ya so ya ajiye Paapa for few days amma ya qi don haka ne ya sallame shi tare da alqawarin biyo shi har gida ya duba jikin nashi.
Paapa dai har suka bar asibitin bai yi ma Hanifa magana ba.. da alama dai ta bata mishi rai this time around. Sossai jikinta yayi sanyi saboda this is the first time da Paapa yayi fushi da ita.. Gaba daya ta zama confused ta rasa abin yi..
toh fa..
Yana answering call din ya ji ta fashe da dariya..
“what’s funny??” ya tambaye ta kai tsaye
“Hanifar ka… dukda briefly na gan ta na tabbatar bata jin magana. Da ganin idanuwan ta zaka gane fitinaniya ce. please tell me, ya kuka yi dazu? kar dai ignoring dinta kayi as usual?”
“what do you think??”
Hanan ta kwashe da dariya tace “dagaske Chocopie kai ne ainihin dan wulaqancin sannan sai ka ja gefe kace baka so a wulaqanta ka”
“Haka ma zaki ce Hanan??? wai yaushe kika lalace ne ban sani ba?? Gaba daya kin juya mun baya.. you of all people da kika fi kowa sani na amma kike fadin haka.. toh shikenan”
“Nooo, Chocopie yi haquri wasa nake yi..”
“Na haqura my sweet Hanan, ya zanyi da ke? kema kin san bazan taba iya yin fushi da ke ba..”
Murmushi tayi tace “thank you my Chocopie”
Fitowa yayi daga motar shi yayinda na ji yana fadin “yanzu dai I gotta go. Dazu aka sallami Paapan nata daga asibiti, I am at the house to check on him”
“Allah sarki, Allah ya bashi lafiya.. idan ka ga Hanifa ka ce mata fan dinta sends her regards all the way from Egypt..”
“Come down to Nigeria and deliver the message yourself”
Fashewa tayi da dariya.
A daidai lokacin da yayi ringing doorbell ne yace “dont forget to call me later”
“I will handsome.. I love you bye”
“love you too”
Yana kashe wayar ne Hafeez ya bude qofa.. da alama ma fita zai yi, Ganin Sadiq ne ya sanya suka koma tare yayinda suke ta magana.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Kwance yake a kan doguwar kujera riqe da remote yana kallon tashar CNN.
Bowl na fruit salad ne a kan centre table.. da alama dai ya sha ya ishe shi.
Hanifa ce tsugunne a gaban shi tana share hawayen fuskarta. Sanye take cikin kayan bacci na wandon three quarter da ‘yar qaramar T-shirt. Ta daure gashin kanta a tsakiyar kai.. she was looking so beautiful and cute dukda kukan da take yi.
STORY CONTINUES BELOW
“please Paapa kayi haquri.. you are the only friend I have, idan ka yi fushi da ni mutuwa zan yi, I promise to change…”
Hafeez ne yayi sallama yayinda Sadiq yake biye da shi.. shima cikin sallama ya shigo.
Paapa ne ya amsa sallamar su yayinda yayi murmushi yace “Son..”
Da sauri Hanifa ta juyo ta gan shi.. Sanye yake cikin wandon sweatpant baqi da polo T-shirt.. Gashin kanshi da na fuska sai qyalli suke yi yayinda duk ya cika falon da qamshin turaren shi mai dadi da sanyi… Sossai yayi kyau.
Hanifa dai Allah ya sani bata qaunar Sadiq amma the one thing she wish she could do till the end of her life is stare at him saboda bala’in kyan shi but unfortunately for her she can’t saboda dai Sadiq is nothing but an ‘enemy’ to her and ko alama bata
so ya kamata ma tana kallon shi..
“Ina wuni Sir”
“Lafiya lau Son.. Zo ka zauna” ya nuna mishi kujera.
Bayan ya zauna ne yace “Ya jikin ka? Hope dai ka ci abinci??”
“Alhamdulillah.. ba laifi gaskiya na dan ci again ga fruit salad na dora a kai” Paapa ya fada yana murmushi.
Shima Sadiq murmushi yayi yace “toh masha Allah..”
Hanifa wadda ta cika da qunci kasa motsi tayi daga inda take..
Muryar Paapa ta ji yace “tashi ki je ki kawo mishi abin motsa baki..”
Zaro idanuwa tayi tace “Paapa ni???”
Sadiq wanda ya kalli Hanifa for the first time da ya shigo ne ya cika da mamaki.. tambayar shi ma take yi?? mahaifinta ya aike ta sannan tayi questioning dinshi?? this is unbelievable.. Shi kam da farko ma ya so yace he is okay amma ganin haka sai ya fasa yayinda ya zuba ma sarautar Allah ido.
Wannan al’amari a wurin Hafeez dai ba sabo bane.. ya sani sarai abinda ya fi wannan ma Hanifa zata yi.
“Bazaki je bane???”
“Paapa I thought masu aiki ne zasu kawo kuma ma fa..”4
“What is wrong with you??? ba yanzu kike yi mun alqawari cewar you will change ba? kenan qarya kike yi mun?? kenan you will never change?? tashi ki tafi ki bani wuri..” ya fada cikin fada
“Paapa please kayi haq..”
“Hanifa I said get out..” ya fada cikin tsawa.
Fashewa tayi da sabon kuka ta miqe jiki a sanyaye ta fita yayinda Sadiq ya bi ta da kallo cike da mamaki..
Hafeez ne ya miqe tare da fadin “bari in kawo maka abin motsa baki bro..”
“No please, I am okay Hafeez”
Hafeez wanda still yana tsaye yace “okay toh.. ni bari in je inyi aski.. dama I was about going out ne.. hope zan dawo in same ka??”
Sadiq ya duba agogon shi yace “I am not sure gaskiya..”
“Okay toh idan dai ban same ka ba good night kenan?”
“Yeah bro..” Sadiq ya fada tare da miqa mishi hannu suka yi musabaha.
Paapa dai sossai yake jin dadin yadda Hafeez da Sadiq suka saba da juna. how he wish Hanifa ta kwantar da hankalinta sunyi zaman mutunci.. atleast ko don irin abin alkahirin da yayi ma kamfanin shi ai yayi deserving respect and gratitude from her.. if not for Sadiq da yanzu kudin kashewa wannan sai sunyi mata tsaye..
“Paapa sai na dawo” Hafeez ya fada.
“Sai ka dawo Hafeez”
Bayan Hafeez ya fita ne Paapa yayi gyaran murya yace “Hafeez ya bani labarin abinda Hanifa tayi maka a police station, things that you refused to tell me.. Please kayi haquri”
STORY CONTINUES BELOW
“No please Sir, ni yakamata in baka haquri da na bar maka ita ta kwana a station, I am really sorry…wani lokaci I just react without thinking twice ne..” Sadiq ya fada.
Murmushi Paapa yayi yace “ai kayi daidai abinda kayi mata.. if only she has a big brother like you na tabbatar she would have being a different person.. dukda Asma’u bata tare da kai a kullum I am sure kayi instilling good values in her. Yanzu haka ina blaming kaina for what Hanifa has become today…”
Daga nan Paapa ya fara ba Sadiq labarin tun lokacin da aka haifi Hanifa da yadda ta taso har zuwa yanzu..
“…..Banyi tunanin soyayyar da nake nuna mata zata sanya ta girma da irin wannan munanan halayen ba.. the thing is Mamy tayi qoqarin ganar da ni irin halayen da Hanifa take displaying and I always dismiss the case saboda ni ban ga tana yi ba.. I always thought irin ‘yan qananan maganganun nan ne na step-mother and step-daughter amma a cikin ‘yan kwanakin nan ne na fara tabbatar da maganar Mamy. Dukkanin abubuwan da take yi maka zuwa wulaqanta ma’aikatan da suke qarqashin ta a ofis da gida.. gashi kuma iya shegen nata har ya kai ta mari dan deputy Governor wanda ya janyo mata shiga Cell.. a dalilin Hanifa ciwo na ya tashi har sai da na kwana asibiti. I am even confused as to where to start from.. Kafin ka shigo roqo na take yi akan in yafe mata akan abinda ta aikata but a gaban ka ta qara kwafsawa.. it means she would never change kenan??”
Sossai Paapa ya bashi tausayi.. he understands perfectly well why Hanifa is the way she is…
Gyaran murya yayi yace “Zata daina Sir, tana buqatar strict discipline ne kawai and i am sure she will be just fine, kayi haquri”
“shiyasa nake so in roqi wata alfarma daga wurinka…”1
Zuciyar Sadiq ce ta buga yayinda ya zama confused for no reason.. haka kawai sai ya ji he doesn’t like where this is going..2
“…Over these past weeks, I have watched your relationship with Baby closely kuma na fahimci cewar kai kadai ne zaka iya taka mata birki akan abubuwan da take yi.. I know I am asking you alot, but idan ba zai zama maka takura ba i want you to take her away from me and make her a better person for me then you can send her back”
Cike da mamaki hade da rashin fahimta Sadiq yace “Sir??? ban gane ba..”
Murmushi Paapa yayi yace “abinda nake nufi shine zan aura maka Baby ka tafi da ita ka hora mun ita.. I want you to be her disciplinary master, idan ta gyara hali sai ka sallameta ta dawo gida. I can’t give her to you haka nan tunda mace ce kuma ba muharramar ka bace but idan da aure a tsakanin ku babu matsala..”8
Wata muguwar zufa ce ta karyo ma Sadiq dukda sanyin AC sa take ratsawa a falon..4
“…Na san zaka yi mamakin jin hakan daga bakina ko?? maybe kana tunanin zan mayar da ‘ya ta bazawara da kai na.. trust me, na zauna nayi nazari sossai na fahimci lallai idan har Baby bata canza irin wannan halin da take displaying ba ko zaman gidan miji gagarar ta zai yi.. Since you told me you are not in a relationship nayi tunanin it won’t be a problem afterall na dan lokaci ne..”
Sadiq dai gaba daya qwalwar shi ma ta daina tunani mai kyau.. infact ta tsaya ne wuri daya..
“it’s just a request Son, please idan bazaka iya ba it’s totally fine”
A yadda Paapa yayi magana Sadiq ya fahimci cewar bala’in son da yake yi ma Hanifa ne ya sa bazai taba iya hora ta ba.. again tunda har yake da niyyan bada auren ta don kawai a hora ta toh lallai ya gaji da halinta… But does it even make sense???3
One thing is Sadiq yana masifar ganin girman Paapa because Abban shi kafin ya rasu speaks highly of him plus ya nuna mishi cewar aminin shi ne na qwarai.. Paapa is one amongst others that kept in touch even after his dad passed away.. shiyasa lokacin da kamfanin shi yayi sinking yayi mamakin yadda bai gaya mishi halin da yake ciki ba and he had to find out through a newspaper.. Babu abinda ba zai iya yi mishi ba a rayuwa amma auren Hanifa?? yarinyar da ya tsana fiye da kowacce mace a fadin duniyan nan?? Nah…..