RAWANIN TSIYA CHAPTER 7 BY FADEELAH
ASALIN ABUBAKAR SADIQ BUNZA!+
Alhaji Muhammad Bunza asalin mutumin qaramar hukumar Bunza ne a Kebbi state. Yaran shi sun kasance su uku- Sa’ad wanda shine babba, Sai Mariya itace ta biyu sannan Abubakar wanda shine qarami.
Alhaji Muhammad a wannan lokacin ya kasance attajiri don haka ne yaran suka taso cikin gata da wadata.
Sunyi karatun boko da islamiyya mai zurfin gaske.
Sa’ad da Abubakar a turai suka yi karatun su na jami’a. Ita kuwa Mariya dayake mace ce sai tayi nata karatun a nan qasa Nigeria.
Sa’ad wanda a yanzu yara suke kira Big Daddy ya karanci Medicine a qasar Germany. A dalilin bala’in qoqarin shi a wannan lokacin ne babban asibitin Berlin suka bashi automatic appointment inda suka dauke shi a matsayin babban likita. Albashi mai yawa suke biyan shi.. Cikin shekaru shidda ya tara kudade masu yawan gaske. Wannan kudaden ne ya dinga turowa nan gida Nigeria inda aka fara gina mishi wani qaton asibiti a cikin garin Abuja. Dayake harka ce ta kudi, nan da nan aka gama gina asibitin.. aka zuba kayan aiki masu kyau da quality sannan aka dauki ma’aikata, likitoci da nurses first class har daga qasashen qetare. A lokacin da asibitin nashi ya zama ready to start operating ne yayi sallama da Berlin wanda suka yi yarjejeniya akan whenever they need his assistance zasu kira shi.. ya amince da hakan matuqar he is free. A yanzu haka dai Shine mamallakin shahararren asibitin nan da yake cikin garin Abuja mai suna Asokoro District Hospital.. Sa’ad yayi aure a lokacin da ya dawo Nigeria, ya auri matar shi mai suna Rahinatu (Mummy) wadda ta haifa mishi yara guda uku. Jameela, Yazeed da Hafsat
A dayan bangaren kuwa Mariya wadda a yanzu yara suke kira Mom tayi karatun ta a Usman danfodio Univerity inda ta karanci English. Dama tun tana qarama mahaifinta da aminin shi suka yi alqawarin hada yaran su aure (wato ita Mariya da yaron aminin mahaifinta Aminu) Faduwa ce ta zo daidai da zama domin kuwa ko dama Aminu (wanda a yanzu yara suke kiran shi da Dad) yana son Mariya don haka da kan shi ya nemi soyayyarta kuma ya samu. Aminu dai a qasar Ingila yayi karatu inda ya karanci Political science. Bayan ya kammala masters dinshi ne ya dawo gida inda ya fada siyasa. Sossai ake damawa da shi a harkar siyasa, Ba tare da bata lokaci ba kuwa aka yi bikin shi da Mariya tunda dama a lokacin itama ta gama karatun ta. Sun haifi yaran su guda biyu Nana Fatima da Faisal. Bayan shekaru da dama ana damawa da Aminu a harkar siyasa kwatsam sai ranan ya fito takarar gwamnan jihar Kebbi… dayake dai mutumin arziki ne kuma talakawa sun shaida irin qoqarin da yake yi aikuwa kamar wasa ya lashe zaben. Aminu dai sai da yayi shekaru takwas a matsayin gwamnan Kebbi state sannan ya sauka.. daga nan ne ya tattara iyalin shi suka koma Garin Abuja inda harkar siyasar tashi ta koma. Yanzu haka ya riqe muqami kala-kala a cikin gwamnati, har yanzu yana shanawa a cikin gwamnatin qasar nan.
Abubakar kamar yadda kuka sani a Stanford yayi karatunshi a qasar America inda ya karanci Petroleum Engineering. Shima din dai ko da ya gama kamfanin ExxonMobil ne suka bashi aiki.. it’s one of the biggest Oil & gas producing company a USA. Dayake Abubakar yana da qwalwa sossai ba qaramin amfani yayi musu ba haka shima ba qananan kudade suka dinga biyan shi ba.. Nan da nan yayi masifar kudi na fitar hankali.. a lokacin da ya nemi barin su ya dawo gida hana shi suka yi.. a tunanin su ma kudin da suke biyan shi ne basu ishe shi ba don haka suka ninka mishi. Mai karatu ba sai na yi maka bayanin irin kudaden da ake samu a bangaren mai ba, musamman a turai wanda in dollars suke biya. kafin a ce kwabo Abubakar ya zama billionaire. Dama tun kafin ya tafi turai karatu yana da budurwar shi mai suna Haleema.. asalin ta bafillatanar Adamawa state ce, aiki ne ya kai mahaifinta Kebbi state. Abubakar dai ganin ExxonMobil sun qi sakin shi ne yayi planning kawai ya dawo a daura mishi aure da Haleema sai ya dauke ta su koma can. A can din ta cigaba da karatu don kuwa dama bata gama ba. Sun zauna a America har tsawon shekaru Ashirin da biyu… tsakanin su da Nigeria sai dai hutu. Sun haifi yaran su guda biyu- Abubakar Sadiq da Asma’u. A lokacin da suka dawo qasar Nigeria ne suka yi settling a Abuja inda ya kafa Oil Producing company dinshi mai suna Bunza Oil & Gas wanda cikin qanqanin lokaci yayi fice ba a Nigeria ba har wasu qasashe na qetare. Kafin ace wani abu gaba daya Nigeria babu state din da bazaka gidajen man shi ba. Bayan ‘yan shekaru ne Alhaji Aminu (Dad) mijin Mariya (Mom) wanda yayi zurfi a siyasa yayi mishi hanya aka gabatar da sunan shi a wurin shugaban qasa wani lokacin da za’a nada sabbin ministoci. Kamar da wasa kuwa duk yayi passing interviews dinshi yayinda Senate suka yi approving musamman ganin achievement dinshi a qasar America. Nan da nan aka nada shi Minister of Petroleum na qasa wanda sai da yayi shekaru hudu sannan ya sauka a yayinda aka canza gwamnati. Shekara biyu da rabi da saukar shi ne suka yi accident shi da mai dakin shi akan hanyar su na dawowa daga airport bayan sunyi tafiya zuwa qasa mai tsarki don yin Umrah.. a sanadiyyar wannan hatsarin ne suka rasa rayukan su! Allah ya jiqan su da Rahama.. Ameen.
STORY CONTINUES BELOW
Haleema mahaifiyar Sadiq tana da qanwa mai suna Hauwa. Hauwa tana auren Nazif abu- Dawood, asalin shi balaraben qasar Egypt ne wanda aiki ya kawo shi qasar Nigeria (Kebbi state) anan ne ya hadu da Hauwa har suka qulla soyayya ta kai su ga yin aure. Basuyi shekaru biyu da yin aure bane suka koma Egypt inda ya samu appointment a embassy dinsu a can. Sun dade sossai da yin aure sannan suka samu haihuwa. Hanan ita kadai ce suka Haifa, daga ita basu qara samun haihuwa ba.
wannan kenan!!
☆☆☆☆☆☆☆☆
Asali dai family dinsu gaba daya kyawawa ne tun daga kakannin su. Musamman bangaren su Sadiq wanda suka dauko jinin fulanin Adamawa daga mahaifiyarsu da kuma bangaren Hanan da ta dauko jinin larabawa.
Mun sani cewar Sadiq da qanwar shi Asma’u a qasar America aka haife su don haka they are citizens of America by birth. Dayake mahaifiyar su ta cigaba da karatu a qasar America ko da ta haifi Sadiq wanda ya ci sunan mahaifin shi musamman ta dauko wata ‘yar uwarta daga can gida Adamawa wadda suka girma suna kiranta da ‘Naana’ a dalilin bata so tana barin shi a wurin masu aikin su turawa tunda dai tana zuwa school.
Naana dai qanwar mahaifiyar Haleema ce don haka kamar Uwa take a gareta. Zamu iya cewa Naana tana matsayin Kaka a wurin su Sadiq kenan. Asalin sunan ta Asma’u, tayi aure har guda biyu amma bata samu haihuwa ba, a dalilin haka ne auren nata yake mutuwa.. Gashi Allah ya jarabce ta da son yara, Ganin tayi aure har sau biyu tana rabuwa da mazan akan rashin haihuwa ne ta haqura ta rungumi qaddara. Da wannan ne Haleema mahaifiyar su Sadiq ta dauko ta.
Naana dai Allah ya jarabce ta da son Sadiq da Asma’u. Haleema dai haihuwar su kawai tayi amma duk wata dawainiyar su ita
ce.. Sossai suka shaqu da ita suma, suna bala’in sonta. Dayake mace ce ta gari ta bada gudummuwa sossai wurin tarbiyar su… a dalilin kyautatawar da take yi musu ne ya sanya aka yi mata takwara da Asma’u. Iyayen Sadiq har suka bar duniya suna yaba mata tare da yi mata fatan alkhairi..
Family dinsu sun taso suna qaunar junan su dukda ba kusa suke ba.. a kowanne hutu sukan yi family meeting a Nigeria gidan Big Daddy tunda shine babba.
Tun suna yara Hanan take bala’in son Sadiq, haka kawai yake birge ta. Sadiq bayada hayaniya ko alama sabanin sauran ‘yan uwan shi. Hanan ta zauna ta karanci halayen Sadiq gaba daya, tun tana matse mishi yana basarwa har dai shima ya saki jiki da ita.. a tsakanin su akwai tazarar shekaru bakwai amma hakan bai hana su zama very good friends ba.. A kowanne lokacin hutu it’s either Sadiq ya je Egypt yayi part of his hutu a can ko kuma Hanan ta je America tayi hutun ta a can. Distance was really never a barrier to their relationship.. idan basu tare kullum suna waya (voice and video call)
Yazeed ya girmi Faisal and Sadiq da shekara daya. Tsakanin Faisal da Sadiq kuwa wata biyar ne (Sadiq ya girmi Faisal).
Yanzu haka shekarun Yazeed talatin, su kuma Faisal da Sadiq suna da ashirin da tara.
Shi Yazeed kamar Daddyn shi Medicine ya karanta a qasar Germany shima, har India ya je yayi wasu courses wanda yanzu haka shima qwararren likita ne a shahararren asibitin mahaifin nashi wato Asokoro District Hospital. A yanzu haka shekara daya kenan da yayi aure, ya auri matar shi mai suna Nabeeha wadda ta kasance babbar Gynecologist a asibitin mahaifin shi and she is yet to conceive..
Shi dai Faisal tare suka yi karatu da Sadiq a Harvard inda shi Faisal ya karanci Accounting yayinda Sadiq ya karanci Business administration. Ko da suka gama masters dinsu, Bunza Oil & Gas suka fada. A yanzu haka da Sadiq yake part-time aiki a Bugaje industries, Faisal shi yake running Bunza Oil & Gas full time wanda from time to time ne Sadiq din yake zuwa..
‘Yan uwan su Mata Jameela, Hafsat da Nana Fatima duka sunyi auren su. Jameela tana zaune da mijinta a qasar Ingila, suna da yaran su guda uku- Aminatu, Aishatu da Ahmad.
STORY CONTINUES BELOW
Ita kuma Hafsat tana auren wani Babban Barrister a nan cikin garin Abuja. Yaranta biyu- Ibrahim da Aseeya.
Nana Fatima ma anan cikin garin Abuja tayi aure amma yanzu haka suna Dubai inda mijinta yake wani course na tsawon shekaru biyar.. saura musu shekaru biyu kenan su dawo. Yaran su biyu su ma- Zainab da Nafeesa.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Sadiq yayi 90% na rayuwar shi a qasar America domin kuwa ko bayan da iyayen shi suka dawo Nigeria shi a can aka bar shi.. sai da ya gama masters dinshi tare da Faisal ne suka dawo.
Suna dawowa kuwa sukayi service shine suka yi joining din Bunza Oil & Gas.
Sadiq da Asma’u dai duk arzikin su, duk matsayin mahaifin su a qasar basu wulaqanta mutane, basu da girman kai ko alama.. kai idan ba an gaya maka ba bazaka taba kawowa a ranka cewar ‘ya’yan one of the richest Businessmen na qasar Nigeria bane. They are so down to earth and it’s all thanks to irin tarbiyar da Iyayen su suka basu da wanda Naana ta dora musu a kai.
Kamar yadda na fadi muku Sadiq dai kyakyawa ne ajin farko. Gaba daya dangin su ya fi su kyau, daga matan har mazan. tun asalin shi ba mai yawan magana bane.. zai yi wuya a zauna ka ji muryar Sadiq. He speaks only when its necessary.. A duniyan nan mutum daya ce take sa shi yin magana- Hanan.
Gaba daya sirrin rayuwar shi babu wanda bata sani ba a dalilin muguwar shaquwar da suka yi.. Sadiq is a no-nonsense guy amma abin mamaki Hanan tana yin yadda ta ga dama shi.. Dangin su har mamaki suke yi yadda Hanan take dictating mishi abu kuma ya kasa tsallakewa. Hakan yana daga cikin abinda ya sanya suka yi tunanin lallai akwai soyayya a tsakanin su amma kuma to their greatest suprise both of them denied the fact. A bangaren Sadiq tabbas haka ne, babu soyayyar Hanan a zuciyar shi, soyayyar da yake yi mata irin ta ‘yan uwanta ce sabanin ita Hanan din wadda take yi mishi soyayya irin ta masoya..
Hanan kamar yadda kuka sani ta girma da son Sadiq amma unfortunately for her ba sonta yake ba.. a rayuwarta babu abinda take so irin soyayya.. tana girmama soyayya sossai. She doesn’t believe in marriage without Love, a cewarta there has to be mutual Love for a marriage to work… is it true???5
Sadiq dai a nashi bangaren Love is just a waste of time, baya da lokacin soyayya don kuwa bai ga amfanin ta ba.. to him arranged marriage will be the most easiest thing to do. Recently, Ya matsa mata ta aure shi saboda su Big Daddy sun fara yi mishi maganar aure.. ya matsa ma Hanan akan ta amince ta aure shi a dalilin ya san tana son shi dukda tana denying, ya nace mata akan ta aure shi a dalilin ya sani cewar ita kadai ce zai zauna da ita cikin sauqi ba tare da wani problem ba… but then, her response is always a NO!
☆☆☆☆☆☆☆☆
Sadiq dai tun da ya dawo Nigeria ya san amintar da take tsakanin Mahaifin shi da Alhaji Aliyu Bugaje (Paapa). A duk lokacin da ya ziyarci mahaifin shi yana kula da irin kusancin da yake tsakanin su.. Duk yadda ya kai ga zama busy even a lokacin da yake minister of petroleum, Idan har Alhaji Aliyu Bugaje ya ziyarce shi dole sai yayi squeezing time for him. there is no doubt cewar they were very good friends.. a wannan lokacin sun so su hada yaran nasu tunda basu san juna ba a dalilin karatu da suke yi a qasashen waje. Even though makaranta daya Hafeez yayi da Sadiq toh amma Sadiq din ya girme shi da shekaru shidda don haka sai da ma ya bar school din sannan Hafeez ya shiga. The few times da yakamata su hadu shine lokacin hutu and unfortunately idan Hanifa da Hafeez suka zo Nigeria, su kuma Sadiq da Asma’u might be out of the country on holiday or sun je Egypt gidan su Hanan… things like that kept happening and Allah bai yi sun hadu ba a wannan lokacin.
A lokacin da Iyayen Sadiq suka rasu kuwa Alhaji Aliyu Bugaje amongst so many others sun ba su Sadiq moral and financial support…
Its evident that basu buqatar Financial support din kowa domin kuwa duk wanda ya san tarin dukiyar da Alhaji Abubakar Muhammad Bunza ya bari ya sani cewar yaran shi sunyi rashi na iyayen nasu ne amma ba rashi na kudi ba domin kuwa sun tafi sun bar musu tarin dukiyar da har su mutu suna kashe kudaden bazasu taba qarewa ba.. gashi dangin su duk masu arziki don haka they lacked nothing (financially) a rayuwa.
STORY CONTINUES BELOW
Abokanen mahaifin nasu sun san da wannan, Sadiq yayi insisting akan su bari haka nan amma they don’t listen.. Yanzu haka Sadiq yana zaune sai dai ya ji alert na millions of naira daga friends din mahaifin nashi har daga USA. Tun abin yana damun shi har ya daina tunda ya kula ba dainawa zasu yi ba.. this alone shows how very great his Dad was when he was alive. Da bai yi zaman mutunci da mutane ba da babu wanda zai waiwaye su. Hakan ya sanya shima yake bala’in kyautata ma mutane.
Mai karatu, idan ka ga yawan kudaden da Sadiq yake zubar ma talakawa zaka riqe baki.. duk inda ya san ana buqatar taimako idan dai na kyautatawa Musulmi ne da addinin musulinci toh fa baya hesitating.. no matter the amount!
Dayake dai Sadiq a America yayi rayuwar shi, abokanen shi duk ‘yan can ne.. Don haka ko da ya dawo Nigeria his only friends are his Cousins Yazeed da Faisal sai kuma Hafeez wanda dukda ya girme shi he still considers him a friend and a younger brother!!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
A lokacin da iyayen nasu suka rasu Asma’u tana 100L a Nile University (a dalilin bala’in son iayayenta da take yi ne ya sa ta qi zama turai tayi karatu). Mutuwar iyayen su ya taba ta sossai.. Gaba daya kasa gane kanta akayi… ta girgiza sossai da shocking news na ras
uwar iyayen nata a lokaci daya.
Sai da tayi kwanciyar jinya na tsawon lokaci wanda har sai da aka hada da addu’o’i sossai sannan ta samu natsuwa..
Ko da aka samo kan Asma’u a wannan lokacin she already missed alot in school.. Dukda she was physically fine, da ka kalle ta zaka san emotionally she is not. A koda yaushe zaka ganta a dakin mahaifin nata ko kuma a na mahaifiyarta ta zauna tayi shiru.. Dukda Naana da Sadiq were always there for her, the environment wasn’t favorable.
Har shawara Big Daddy yayi da Sadiq akan suyi moving to one of other houses dinsu amma still, babu canji- Dama already sunyi turning down offer na komawa gidan Big Daddy din.. a cewar su they already have a Mother-figure (Naana) don haka they will be fine with her.
A qarshe dai Sadiq ya bada shawarar a fitar da ita daga qasar, just maybe zata samu relief.
Switzerland being Asma’u’s Favorite country ne ya sa Sadiq ya zabi a kai ta can din..
Nan da nan ya shirya musu ita da Naana. Dayake dai qasar Switzerland ba baquwar qasa bace a wurin Asma’u tunda duk hutu sai ta je, nan da nan tayi adapting.
Kamar yadda aka yi zato kuwa zaman ta can din yayi mata amfani.
Asma’u da Naana suna zaune a cikin wani lafiyayyen Mansion da Sadiq ya siya musu, ya sanya ta a best University da take qasar- University of Zurich. Duk wani abinda suke so suna samu in excess ma. In short, Asma’u tana rayuwa a qasar Switzerland tamkar sarauniya.. hatta yaran manyan attajiran qasar iyakar jin dadin da suke yi kenan.
Sadiq yakan je visiting dinsu twice a month depending on how less busy he is.
A yanzu haka da ya fara Zarya tsakanin Kano da Abuja (Bunza Oil & Gas da Bugaje Industries) ne baya samun zuwa.. Kamar yadda kuka ji kusan wata biyar kenan bai je ba wanda a kullum ita Asma’un tana cikin yi mishi qorafi.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Kamar yadda kuka sani dai Sadiq yana aiki a Bugaje industries ne a dalilin abinda ya faru a kamfanin.. Haka kun sani cewar ya zuba dukiya mai yawan gaske a cikin kamfanin don yayi restoring dinshi back to life. Yayi sparing 6 months of his time a kamfanin ne don kawai ya saita musu al’amura sannan ya tafi. He did all these a dalilin amintar da take tsakanin Paapa da mahaifin shi kafin ya rasu da kuma irin kyautatawar da shi Paapan yake yi musu even after his Dad passed away, most importantly he did it saboda Allah, sannan yayi ne saboda burin shi a rayuwa na son taimakon mutane.
A wannan halin ne Hanifa ta shigo rayuwar shi.. take yi mishi shirmenta kala-kala. Shirmen da yayi landing dinta a babban trouble.
Sadiq ya amince zai aureta ba don Mahaifinta yayi mishi maganar ba, infact he had already turned down the offer but Hanifa ta kwafsa ma kanta.. Kwafsawan da ya sanya a yanzu haka baya da wani burin da ya wuce ya gan ta a gidan shi a matsayin matar shi.. Simply for one reason- to teach her a lesson.3
Toh gashi kuma ya fadi ma Hanan maganar auren kuma ta hargitse- ta kwanta rashin lafiya.
Ga Hanifa kuma Paapa ya sanar da ita zai hada ta da Sadiq.. itama kuma ta hargitse- ta kwanta rashin lafiya.
Sadiq yayi Booking jirgi zuwa Egypt don duba Hanan even after knowing cewar Hanifa ma batada lafiya kuma ya sani sarai a dalilin shi ne.. he seemed happy jin cewar Hanifa batada lafiya sabanin Hanan wadda gaba daya ya hargitse a dalilin nata rashin lafiyar.NAZIF ABU-DAWOOD RESIDENCE
SHEIKH ZAYED CITY- CAIRO EGYPT+
Zaune take a kan gadon dakin ta yayinda ta jingina da headboard na gadon tana kallon shi.
Sadiq wanda yake zaune daf da ita yana riqe da bowl na Corn flakes a hannun shi da spoon yayinda shima yake kallonta.
Sadiq dai a jiya ya shiga jirgi zuwa Abuja.. wuraren qarfe shidda na safiyar yau din ne jirgin su ya tashi daga Abuja zuwa Cairo. dayake tafiyar awa hudu ce kacal, qarfe Goma sha daya saura ya shigo gidan su Hanan. A lokacin da ya iso Abbu baya nan, Umma dai bata yi mamakin ganin shi ba domin kuwa ko a jiya da suka yi waya ta sani sarai dukda tayi calming dinshi down ba zai taba haquri ba sai ya zo da kanshi. Sadiq ya tarar Umma tana ta masifa na yadda Hanan din ta qi cin abinci wanda daga nan ne ya lallaba Umma yayi taking charge yayinda tayi tafiyarta ta bar su…
“Please my sweet Hanan try and eat something… you know you slept on an empty stomach last night gashi yanzu ance any moment the doctor will come check on you.. if he finds out cewar baki ci komai ba allura zai yi miki kuma we both know how it will end..”3
turo baki ta dan yi sannan tace “toh na ji.. I will eat small”
Murmushi yayi sannan ya kai cokalin bakin ta yayinda ta bude ya sa mata.
“haka kawai kiyi ta sa ni ina surutu.. I swear you are the only one that makes me talk like a parrot”
Murmushi ta dan yi sannan tace “I am sorry Chocopie..”4
Haka dai Sadiq ya dinga bata Cirn flakes din a baki.. Idanuwa ta zuba mishi kamar kullum, Allah ya sani tana bala’in son Sadiq.. On top of everything kuma ga kyan shi da yake kashe ta.
Hanan dai tayi nisa a kallon Sadiq da bata ma san ta shanye Corn flakes din ba.
Shi kam da ya kula kamar bata san ta shanye din ba sai kawai ya dago empty spoon ya kai bakinta, ko da cokalin ya shiga bakinta sai ta ji wayam. Da sauri ta kalli cokalin sannan ta kalle shi ta ga ya fashe da dariya.
Turo baki tayi tana hararar shi tace “wulaqanta ni zaka yi???”
“No my sweet Hanan.. na ga kamar baki qoshi ba, ko zaki qara ne??” ya fada tare da kashe mata ido daya.
Murmushi tayi sannan tace “thank you for making me eat Chocopie”
“No thank my face instead..”
“what??”
“you were staring at my face all through, I caught you”
Murmushi tayi tace “toh ai kai ne kayi kyau dayawa Chocopie”
“huh.. not again” ya fada tare da ajiye bowl din a gefe ya gyara zama a kan gadon nata yace “tell me something”
“what”
“me ya faru?? why are you sick?? kar kiyi mun qarya”
Zuciyarta ce ta buga yayinda ta sa mishi idanuwa ba tare da ta san me zata ce mishi ba.
Me zata ce mishi toh?? cewar tana son shi?? cewa kar ya auri Hanifa ya aureta?? Soyayyar da take nema fa??3
STORY CONTINUES BELOW
“Oya oya oya, dont waste my time”
“and you? why did you come?”
“you dont answer a question with another question Hanan.. but zan amsa ki saboda ina buqatar amsar tambaya ta. I came to check on you.. Umma ta gaya mun baki da lafiya and I became worried. somehow ina ji kamar I have something to do with it and I want you to tell me.. me ke faruwa???”
Duqar da kai tayi yayinda take wasa da yatsun hannun ta.
Bata ankara ba ta ji hannun Sadiq a kan nata wanda ya sa zuciyarta ta buga yayinda jikinta yayi mugun sanyi.
“Baki so in auri Hanifa ko??”
Da sauri ta dago kai tana kallon shi yayinda wasu hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan ta.
Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude sannan yace “oooh shit Hanan.. meyasa baki fadi mun wannan ba?? Kin sani cewar ban taba qin yi miki wani abinda kike so ba, haka ban taba yin wani abinda na san baki so ba. Why this??”
Bubbuga hannunta yayi alamar lallashi sannan yace “Guess what, na fasa auren..”1
Da sauri ta riqe hannun shi tace “Please No, what makes you think cewar bana so ka auri Hanifa?? Yes I am a little sad because zaka samu sabuwar abokiyar shawara sannan I won’t be your fave anymore but hakan baya nufin cewar I am not happy for you.. On the contrary, I am very happy for you??”
“Okay fair enough.. but still kar ki manta aur
en na dan lokaci ne plus Hanifa can never be one of my faves because I hate her..”
Hanan wadda take kallon shi a ranta tace ‘Wait, is this suppose to make me happy??’
” …kamar yadda na fadi miki dai my offer still stands, idan kin canza mind I am available” ya fada kai tsaye in all seriousness.
Sakin hannun shi tayi sannan ta share hawayen fuskarta ta harare shi tace “…when I already have Hussain?? No Mr Sadiq, na fadi maka cewar Hussain zan aura.. he is a very nice, loving, caring, kind…”
“toh toh ya isa haka…”
Fashewa tayi da dariya tace “someone is jealous”
“yeah whatever..” ya fada tare da hararar ta as she continued to laugh at him.
“toh yanzu dai tell me, me ya sa baki da lafiya”
“Na shiga uku Chocopie, shikenan mutum bazai yi ciwo ba?? Allah ne ya saukar mun”
“aah yeah.. haka ne! toh Allah ya baki lafiya my sweet Hanan”
“Ameen Chocopie”
“Yaushe Hussain din naki zai zo?? I would love to meet him before I go back to Nigeria tomorrow.. na kwana biyu ban gan shi ba”
“well, Ya je Dubai but I am sure yanzu haka yana cikin jirgi.. he was worried da ya ji bani da lafiya”
“uhm.. toh dai duk damuwa da ke da yayi bai kai ni ba tunda na riga shi isowa” ya fada cikin tsokana.
Hararar shi tayi tace “hey Mr, ka riga shi jin rashin lafiyar ne don kuwa sai yau da safe ya ji.. again he had to put some things in place before coming… so?”
STORY CONTINUES BELOW
Girgiza kai yayi yace “toh masoyiyar Hussain, I rest my case. Yanzu tell me, me kike so? ina yake miki ciwo???”
“Ba ko’ina, kawai I am feeling weak ne”
“Ko zakiyi wanka??”
“Yes it’s a good idea.. ji nake yi kamar na kwana uku ban yi wanka ba wallahi”
Gani nayi ya miqe yace “bari in hada miki ruwan wankan toh.. I’ll just be back”
Bin shi tayi da kallo har ya shiga bathroom dinta yayinda na ga ta jingina kanta da headboard na gadon sannan ta rufe idanuwa tare da sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya.
Ko da ya hada mata ruwan wankan ya fito wayoyin shi ya kwashe sannan yace mata zai je ya dan kwanta yayi bacci saboda bai samu isashen bacci ba.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Da yamma wuraren qarfe biyar suna zaune a qaramin falon gidan…
Hussain wanda dawowar shi kenan daga Dubai ko gida bai je ba ya zo ganin Hanan. Tunda ya ji Hanan batada lafiya hankalin shi yayi mugun tashi.. Business deal din da ya je yi ma kasa gamawa yayi, dayake Allah ya taimaka tare da twin brother din shi suka je sai kawai ya bar mishi deal din shi kuma ya biyo next flight ya dawo.8
Ko da na kalli Hussain babu qarya kyakyawa ne.. Fari sol domin kuwa ya fi Hanan haske.. dukda a zaune yake na kula shi ba dogo bane sannan ba gajere bane. Asali mahaifin shi dan Nigeria ne, mahaifiyar shi ce ‘yar Egypt. Hussain is a software engineer, yana da kamfanin shi a nan qasar Egypt wanda yayi fice sossai.
Kayan ciye-ciye na hango masu yawan gaske a gefe wanda ya kawo mata.. kaya Kamar za’a zuba a shago.
“Habibty thank God you are okay, hankali na yayi mugun tashi da na ji baki da lafiya especially because I know that ke ba mai yawan ciwo bace.. what happened??”
Hanan wadda take murmushi tace “its nothing serious Habibi.. doctor yayi confirming cewa I am fine so please relax”
Masu aikin gidan ne guda biyu suka shigo falon cikin sallama riqe da tray na abubuwan motsa baki suka ajiye a gaban shi yayinda suka duqa har qasa suka gaishe shi… Daga nan kuma suka fara kwasar kayan ciye-ciyen da ya kawo ma Hanan suna shiga ciki da shi.
Hanan tana kallon su tace “Habibi wannan kayan fa sunyi yawa.. you shouldn’t have stressed yourself kai da dawowar ka kenan daga tafiya.. having you here alone and seeing you is more important”
“ssssshhh, I love you”
Kafin tayi magana ne suka jiyo muryar shi yana fadin “hmmmm, our Romeo has arrived”
Hanan wadda ta dago kai ta ga Sadiq tsaye yana kallonta harda kashe mata ido daya murmushi tayi tare da girgiza kai.
Hussain yana murmushi ya miqe tsaye yace “ashe Chocopie dinmu ya zo, it’s good to see you” ya miqa ma Sadiq hannu suka yi musabaha.3
“Good to see you too bro.. kwana dayawa, how have you been?” Sadiq ya fada yayinda suka zauna.
“Alhamdulillah.. ya mai jikin??”
Sadiq ya kalli Hanan wadda take kallon su tana murmushi yace “well if you ask me I’d tell you tayi faking ciwon ne don mu zo.. it’s like she needed some attention ne and she got…” bai qarasa magana ba Hanan ta zaro idanuwa tare da bude baki cike da mamaki.. da sauri ta dauki throw pillow ta jefa mishi cikin shagwaba tace “Haba Chocopie, dagaske fa bani da lafiya kuma ka sani”
STORY CONTINUES BELOW
Sadiq wanda ya cafke pillow din sai gani nayi ya miqa ma Hussain yana murmushi yace “I am just kidding my sweet Hanan, please dont cry”
Turo baki tayi tare da hararar shi wanda didn’t go unnoticed by both of them..
Sadiq ya kalli Hussain yace “mutumina zaka yi fama da shagwaba da kuka for no reason..”
Hussain yana dariya yace “ka manta harda masifa..”
“what???” ta fada tare da zaro idanuwa yayinda wayar Sadiq tayi ringing ya miqe yace “toh ni dai bari in gudu kar ta gwabje ni.. Gwara kai masoyi ne babu abinda zata yi maka, ni kuwa jikina ne zai gaya mun..”
Hussain dai dariya yake ta yi yayinda Hanan ta bi Sadiq da harara. Kashe mata ido daya yayi sannan ya amsa call dinshi ya fita.
“I like your Chocopie alot.. he is nice” Hussain ya fada4
Hanan wadda take murmushi tace “I like him too… very much”
“like or love??”
Da sauri ta kalli Hussain wanda shima ita yake kallo.
“uhm Habibi i have told you several times cewar i dont love..”
“Yeah kin fadi mun Habibty amma your eyes says otherwise.. the way you look at him is just so different plus kullum labarin ki nashi ne.. it’s obvious you have something for him”
“No, Habibi kai nake so dagaske.. Chocopie dan uwa na ne and besides, he is getting married..”
“whoa.. are you serious?? wacece wannan legend din da tayi capturing dinshi?”
Hanan dai fashewa tayi da dariya.
“ah toh dole in tambaya mana sanin halin shi.. kodayake ance dama irin su idan har suka fada tarkon so sun fi kowa yin zurfi..”
Hanan wadda take juya kalaman shi a ranta tace “if only you know cewar that’s not the case”
“toh ya maganar namu bikin?? yaushe zan turo a sa rana?”
Zuciyarta ce ta buga a dalilin tambayar da Hussain yayi mata. Ita fa a rayuwarta bata taba picturing kanta a matsayin matar wani ba banda Sadiq… Kenan her dream can never come true??
Qirqiro murmushi tayi tace “soon Habibi.. can’t wait to become yours”
murmushin jin dadi yayi yace “Allah ya nuna mana Habibty, I cant wait to have you too”
A haka dai suka cigaba da hirar su…
The thing is Hussain ya riga ya gane cewar Hanan tana bala’in son Sadiq, a lokacin da ya gano hakan ya so ya ja baya amma kuma irin hope din da ta bashi ya sanya ya gane lallai it’s a one sided thing, ya gane cewar Sadiq doesn’t feel thesame way about her and it’s the reason why she is holding on to him.. Ya sani cewar irin son da yake yi mata bata yi mishi irin shi amma hakan bai dame shi ba.. Sossai yake nuna mata soyayya wanda ita kuma take bala’in so.. she wants to feel loved and right now Hussain is giving her more than that..
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Wuraren qarfe takwa
s na dare suna zaune a dinning suna dinner yayinda suke hira.
STORY CONTINUES BELOW
“Yanzu Sadiq saboda dan zazzabin nan na Hanan shine ka baro komai ka zo Egypt??” Abbu ya fada yayinda yake kallon Sadiq yana murmushi.
Umma ce tace “hmmm.. ai nayi mamakin ganin shi. A jiya fa da muka yi magana a waya na sanar da shi cewar it’s nothing to be worried about amma ka gan shi nan”
Sadiq yana murmushi ya kalli Hanan wadda take zaune a gefen shi yace “ai bazaku gane bane.. idan har ban zo na duba ta ba bazan taba samun natsuwa ba”
Gani nayi ya riqo hannun Hanan yayinda ya cigaba da fadin “..she means a lot to me”
Hanan wadda ta matse hannun shi cikin nata ce tace “you mean alot to me too my chocopie”
Umma ce tayi gyaran murya tace “Ni kuwa Allah yasa amaryar nan taka mai fahimta ce don kuwa zata iya misunderstanding wannan relationship din naku”
Abbu ne yace “ai har yanzu na rasa yadda aka yi duk wannan kusancin nasu ace babu soyayya..”
Hanan ce tayi saurin kallon Umma wadda take kallonta itama..
“Abbu ai Hanan ce bata so ta aure ni” Sadiq ya fada
“toh an taba yin aure babu soyayya ne???”
“ofcourse Hanan.. do we need LOVE in order to live together??”
“Yes”
“toh ai kin ji tsiyar” Sadiq ya fada yana hararar ta yayinda su Abbu suke yi musu dariya.
“Kenan ita wadda zaka aura kana nufin babu soyayya a tsakanin ku??” Umma ta tambaye shi.
Gyaran murya yayi ya kalli Hanan sannan yace “akwai fahimtar juna Umma and I believe it’s what matters the most”
Hanan dai girgiza kai kawai tayi.. Allah ya sani idan da akwai abinda zata iya canzawa in Sadiq, it will definately be his point of view akan Soyayya!
“toh Allah ya sanya albarka”
“Ameen Umma”
“Yauwa na manta ma ban fadi maka ba, maganar zuwa neman aurenka.. mun yi magana a waya da Big Daddy dazu and munyi deciding zan je Nigeria in three weeks time sai mu je”
“it’s okay Abbu, duk lokacin da kuka shirya, there is no rush”
“a’a.. ai idan muka je neman auren kawai za’a sa rana don bana so a ja da nisa. Tun da Abban ka ya rasu nake yi maka addu’an samun mace ta gari kayi aure saboda considering your Status in Nigeria it’s very important for you to start a family..”7
Umma ce tace “gaskiya ne wannan… Allah ya nuna mana rai da lafiya”
Gaba daya suka amsa da ‘ameen’
Bayan sun gama cin abincin ne Abbu da Umma suka tashi yayinda suka bar Hanan da Sadiq.
“Chocopie yanzu dagaske gobe zaka tafi???”
“Yes Hanan, I need to start preparing my hand over notes a Bugaje industries”
“Please Chocopie ka bari sai jibi” ta fada cikin shagwaba
Kai tsaye yace “an gama My Sweet Hanan… whatever you want, you get”
Tana murmushi tace “Thank you Chocopie.. Gobe zamu je yawo??”
STORY CONTINUES BELOW
“Idan Hussain ya bada Go-ahead we will go”
Hararar shi tayi tace “Chocopie please stop..”
Yana dariya ne wayar shi tayi ringing.. Gani nayi ya kalli fuskar wayar sannan yace “its Hanifa’s Paapa..”
Amsa wayar yayi ya sanya ta a speakerphone..
“Assalamu alaikum.. ina wuni Sir”
A dayan bangaren ne Paapa yace “Lafiya lau Son.. Sorry dazu nayi missing call dinka..”
“uhm dama zan sanar da kai ne cewa nayi tafiya.. ina Egypt”
“toh fa.. hope all is well??”
“Yes Sir, dama cousin dina ce batada lafiya but she is fine now”
“Allah sarki.. Allah ya bata lafiya. Ai ga Baby nan ma batada lafiya tun jiya….”
“Subhanalillah.. Sir ko dai akan maganar auren ne? idan zai janyo mata matsala ko za’a janye ne??” Sadiq ya fada hoping Paapa zai ce a janye shima ya huta don kuwa a kullum idan ya tuna da decision din da yayi making na auren Hanifa gani yake yi kamar it’s not right…
“Not at all Son, the doctor said she is fine, babu wata matsala kar ka damu”
“Okay Sir, insha Allah idan na dawo zan zo in duba ta. Allah ya bata lafiya”
“Ameen Son.. Allah ya dawo da kai lafiya”
Bayan sun yi sallama ne na ga ya jefar da wayar yace “it gives me so much joy to hear that batada lafiya especially because I know saboda ni ne..”3
Hanan wadda ta cika da tausayin halin da Hanifa take ciki ce tace “Chocopie I swear ban san ka da irin wannan halin ba, ashe dama kai mugu ne??? how can someone’s illness give you joy??”
Murmushi yayi yace “point of correction Hanan, she is not just someone.. kin manta ko meye matsayin Hanifa a wurina??? kin manta abinda tayi mun da ya kawo mu wannan halin?”
“Ban manta ba Chocopie amma dai ka dan bi ta ahankali don wallahi har ta fara bani tausayi.. “4
Cike da mamaki ya kalle ta yace “tausayi??? after all she did to me?? Unbelievable” ya fada yayinda ya dauki glass cup na ruwa ya sha..
“I am sure by now she has started to regret dukkan abubuwan da tayi maka.. please I beg you dont be hard on her”
Murmushi yayi yace “it depends on how well she behaves my Hanan..”
“Ni kuwa ina ji a jikina wata rana da kai da ita zaku so juna sossai, I feel auren ku will last till forever..” ta fada cikin tsokana.
Wani irin kallo yayi mata yace “how can you even say this Hanan? Me??? fall in love with the stupid garl?? first off, babu soyayya a cikin al’amura na and secondly Hanifa zata zama Matana na dan lokaci ne.. so??”
A ranta ne tace ‘Rashin soyayya a al’amuranka is the only reason why I will never agree to become your wife Chocopie’3
Murmushi tayi tace “Hmmm… I swear irin ku ne idan kuka fada tarkon so, ciro ku zai yi wahala.. irinku ne fa kuke zurmawa kuyi dumu-dumu a ciki. Ni dai ina baka shawara ka bi ahankali, don kuwa Allah yana iya jarabtar ka da son Hanifa and you will have to take back all the horrible things you have said and done to her”1
“no way in hell that’s gonna happen” ya fada with so much confidence
Ni kuwa nace a’a Sadiq.. you might never know. Tohm…!!ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE
ASOKORO-ABUJA+
Zaune suke a danqararren main falon gidan wuraren qarfe takwas na dare suna hira.
Mai karatu tun da nake ban taba ganin tsarin falo mai kyan wannan ba.. Tun daga bangon falon, zuwa POP, zuwa floor da interior decor na falon abin kallo ne.. Dukda ban ga other parts of the house ba na tabbatar an kashe kudi masu yawan gaske wurin gina shi da kuma tsara shi.. abubuwa dayawa da nayi spotting a falon ban fahimci ko meye su ba. In taqaice muku zance dai everything is looking classy and elegant sannan most importantly ko ina tsab-tsab babu datti ko alama.. I am even guessing the house is new because it doesn’t look like ana wani zama a cikin shi..
Wani asirtaccen qamshi mai dadin gaske wanda ya gauraye da sanyin AC ne ya bada wani yanayi mai bala’in dadi.
Faisal yana zaune a kan kujera one-seater yayinda Yazeed yake kwance a kan 3-seater. Shi kuma Sadiq yana kwance a kan lallausar Chinese carpet din da ke tsakiyar falon.. ya tada kan shi da one of the beautiful and unique throw pillows na kujerun falon.
A jiya da daddare ne Sadiq ya dawo daga Egypt.. Kamar yadda yayi ma Hanan alqawari sun je yawo.. sunyi shopping sossai. Irin Shopping din da yayi mata kuwa kai kace a banza yake samun kudi ba neman su yake yi ba.. they had a great and memorable time together. Da zai tafi kuwa har kuka Hanan tayi knowing cewar the next time she will see him might be ranar bikin shi da Hanifa. Da lallashi suka rabu a airport.
< p>
Yanzu haka da ya dawo he decided to rest a nan Abuja kafin ya koma Kano gobe..
“I still can’t believe saboda dan zazzabi da Hanan tayi shine har ka je dubata a Egypt..” Faisal ya fada2
Yazeed yana hararar Sadiq yace “and again they tell us that ba soyayya suke yi ba.. I swear kun ma raina mana wayau”
Sadiq wanda yake latsa wayar shi ne yayi murmushi yace “rainin wayau kuma??? shin yanzu ba aure kuka ji zanyi ba???”
Faisal ya harare shi yace “eh haka muka ji kuma munyi mamaki.. but tell me something”
“what?”
“all the I love you that you guys keep telling each other duk a banza ne??”
Sadiq yana murmushi ya tashi zaune yace “ba a banza bane, Hanan is my favorite cousin sister and idan mun ce ma juna I love you ai it’s not a big deal… afterall ku ne kuka dauki kalmar da girma..”
“really??? toh gaya mana.. what does I love you mean to you???” Faisal ya tambaye shi yayinda duk suka sa mishi idanuwa.
Sadiq ya kalli Faisal sannan ya kalli Yazeed yace “to me it’s a way of showing benevolent concern for someone or their well-being.. so kun ga I care alot about Hanan don haka idan nace mata I love you it simply is because I care..”5
Faisal da Yazeed na ga sun kalli juna yayinda Yazeed yace “da kyau bature, wai kai zaka gwada mana kai haifaffen qasar America ne ko??”
Sadiq da Faisal suka fashe da dariya.
“toh bari ka ji.. when you say you love someone it also means you have a feeling of intense attraction towards that person”
Da sauri Sadiq yace “toh ni dai ba haka nake…”
Faisal ne ya daga mishi hannu yace “eh mun ji kai ba irin shi kake nufi da Hanan ba amma ka sani cewar ita irin shi take nufi da kai??”
Sadiq wanda yake murmushi ne yace “Na sani..”
STORY CONTINUES BELOW
“and??”
“and what??”
“and still baka tausaya mata ka aureta ba??”
“Hey, listen up guys, kun sani cewar I dont believe in love marriage but unfortunately Hanan so much believes in it, Na sani cewar Hanan tana sona irin wanda Yazeed ya fada and nima ina sonta amma ba irin shi ba.. You guys will not believe this, my marriage proposal is with Hanan a yanzu haka da muke magana.. a serious marriage proposal”
“what???” Yazeed da Faisal suka fada a tare wanda har Faisal ya zamo daga kujera ya koma ya zauna a qasa yana kallon Sadiq.
“Yes, ba tun yau ba nake roqon Hanan akan muyi aure amma ta qi.. na sani cewar babu abinda zai fi mun sauqi irin zaman aure da ita saboda we know eachother very well amma tayi emphasizing word dinnan LOVE”
“toh kai meye matsalar ka da soyayya???”
“A waste of time…” ya fada kai tsaye
“Hmmm.. I swear Sadiq ban taba ganin mutum irin ka ba a duniya.. Soyayya abu mai dadi ita ce baka so???” Yazeed ya fada yana mamaki2
Faisal ne yace “toh yanzu da kace marriage proposal dinka yana wurin Hanan, idan tace ta amince ya zaka yi??? fasa wannan din zaka yi??”
“Hey bro.. where is this interrogation coming from??? kun sa ina ta surutu.. am I safe?”
“Yes you are bro, a matsayin mu na ‘yan uwan ka muna so mu fahimce ka ne sossai because you are kinda complicated”
Sadiq wanda yake dariya yace “idan Hanan tayi accepting proposal dina zan fasa auren Hanifa.. it’s as simple as that”
“whoa..” Yazeed ya fada yana dariya yayinda ya cigaba da fadin “…Allah yasa ta amince bayan ka auri Hanifar sai itama ka auro ta su zama su biyu”
Faisal wanda shima yake kwasan dariya yace “wa ya ga mai stone heart da mata biyu… Cakwakiya international”4
Sadiq ma dariya yake yi a ranshi yana fadin ‘if only they know cewar Hanifa ba dadewa zata yi ba a gidan shi’
“One last question” Yazeed ya fada
“Ya salaam.. why did I even invite you guys to my house??”
“because we are the only friends you have and you can’t do without us” Faisal ya fada yayinda yayi mishi gwalo.
Girgiza kai Sadiq yayi yana murmushi yace “absolutely true but please let it be the last question because I am tired..”
“Toh Miskili..” Yazeed ya fada yayinda Faisal yake dariya yace “Ita wadda zaka aura yanzu na san itama ba sonta kake yi ba amma ita tana sonka?? ko dai abokin Abba (mahaifinta) ne kawai yake so ya hada ku??”
“the truth is we both don’t love each other.. it’s an arranged marriage and honestly it’s perfect for me..”
“hmmmm.. Na rantse da Allah ban taba coming accross mutum ba irin Sadiq” Faisal ya fada yana kallon Yazeed Confusedly.
“it will take a miracle for a lady to capture him, there is no doubt about that” Yazeed ya fada
“well, the most important thing is zaka yi aure and we are happy because a yadda social status dinka yake bai kamata ace you are still single ba.. presently fa you are one of the richest young multi-millionaires a qasar nan dukda baka so ana fadi.. your net worth is something else bro sannan ace baka da mata gaskiya bai yi ba” Faisal ya fada yana kallon Sadiq wanda ya dan bata rai.
Da alama dai baya son wannan maganar kamar yadda shi Faisal din ya fada
Wani young Chef ne na gani sanye cikin kayan chef dinshi farare sol ya shigo falon.. da ganin shi ka san professional Chef ne.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan ya gaida su Yazeed ne yace “Sir, the barbecue is ready.. should I serve it in the Galore or inside the house?”
“guys indoor or the Galore??” Sadiq ya tambayi ‘yan uwan nashi.
Faisal ne yace “I cant afford to miss the bright lights of the Galore at this time of the day bro… so please the Galore”
Yazeed yayi saurin fadin “I hope there is fish coz…”
“there is Sir” Chef din ya fada cikin ladabi.
“okay great”
“don’t worry Mr Doctor, ai na san baka cin nama sossai.. I got you covered” Sadiq wanda tuni ya miqe tsaye ya fada yayinda ya kalli chef din yace “The Galore it is Marwan… well done”
Chef din ya dan russuna tare da fadin “okay sir, thank you”
Su Yazeed suka miqe suka fita zuwa Barbecue Outdoor Galore na gidan.
Suna tafe na ji Faisal yana fadin “toh wai bro idan kayi aure zaka sallami Chefs din nan naka kenan???”
“definitely bro” Sadiq ya fada yayinda Yazeed yace “aikuwa zasu yi baqin ciki, amarya zatayi rendering dinsu unemployed”3
Faisal da Sadiq suka fashe da dariya.
Ni kuwa da nake biye da su nace babbar magana.. Hanifa ce zata dinga dafa abinci kenan.. toh ta iya ne????3
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Washegari!!
A yau ne Sadiq ya dawo Kano.. Ya biyo first flight going to Kano from Abuja. Wuraren qarfe tara na safe ne jirgin su ya sauka.. Dayake dama motar shi a nan Airport ya faka ta sai kawai ya dauko kayan shi ya shigo gari.
Straight Bugaje Industries ya wuce domin kuwa akwai meeting din da za’a yi wanda yayi ma Paapa alqawarin he will be there to attend.
Asali dai wani Babban deal ne kamfanin zai yi da wasu clients daga qasar Cameroon and it’s a huge deal.. As usual kuwa Sadiq yayi showcasing unique business strategies dinshi wanda sossai Clients din suka zama impressed.. Nan da nan suka yi doubling purchases din da suka yi niyyan yi wanda hakan yasa Paapa ya ji dadi sossai..
Ko da aka gama meeting din suka sallami clients din, Paapa ya dinga yi ma Sadiq godiya na yadda yake taimakon kamfanin tare da sanya mishi albarka wanda for him (Sadiq), albarkar da yake sa mishi is more important than any other thing.
Ko da Hafeez ya nuna ma Sadiq progress
report na abubuwan da aka yi lokacin da baya nan he was very much impressed.. Tabbas Hafeez yayi picking fiye da yadda ake tunani, there is no doubt the company will be in good hands!
A lokacin da aka tashi ne Sadiq yayi ma Paapa alqawarin zuwa duba jikin Hanifa. Actually he was hoping kafin ya dawo zai tarar har tayi resuming aiki wanda ba sai ya je duba ta ba kamar yadda yayi ma Paapan alqawari toh amma unfortunately for him da ya dawo an gaya mishi ta dauki sick leave na tsawon sati daya don haka kuma dole ne ya je ya duba ta din.
Wannan kenan!!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA
Wuraren qarfe takwas na dare Sadiq yana zaune a babban falon gidan tare da Hafeez da Mamy da Paapa suna hira..
Gani nayi Sadiq ya kalli agogo sannan yace “uhm.. ina marar lafiyar take mu gaisa? ko tayi bacci ne??” ya qarasa fadi hoping Allah yasa tayi baccin.
Mamy ce tace “anya?? bata yi bacci ba”
Paapa ne yace “Sai ki kai shi sashenta”
Mamy ta miqe tace “toh Paapa” ta kalli Sadiq tace “mu je in kai ka wurinta”
STORY CONTINUES BELOW
Kamar dai abin arziki Sadiq ya miqe har yana fadin “Bro mu je mana..”
Cikin low tone Hafeez yace “ah nooo.. I am sure this particular encounter between you two will be as devastating as a tornado so I wouldn’t want to witness it..”
Sadiq dai girgiza kai kawai yayi yana murmushi sannan ya bi bayan Mamy.
********************
Kwance take a kan Sofa na falonta yayinda take latsa wayarta tana cin chocolate..
Hanifa dai ko da ta kwanta rashin lafiya ta so Paapa yayi considering ya janye maganar auren ta da Sadiq amma unfortunately for her likita yace it’s nothing serious.. Tayi kuka har ta gaji, ta roqi Paapa har kalaman ban haqurin suka qare.. duk wata hanya da zata bi don ta hana wannan auren ta bi amma in vain.. tayi exhausting duk wata dabara da ta rage mata… presently she doesn’t even know what to do! abinda dai ta sani shine bazata taba bari ayi auren ta da Sadiq ba.
Da nayi zooming wayarta wasu designer English wears kala-kala na ga tana kallo.. they looked like they are from a new collection.
Sanye take cikin wani black palazzo trouser da wata ‘yar qaramar plain black T-shirt.. ko da na kalle ta sai na ga ta rame.. fuskarta fayau babu make up amma kuma tayi masifar kyau…. Black surely looks good on her. Ta daure gashin kanta a tsakiyar kai wanda ya sa tayi looking so cute kamar wata barbie.. Babu abinda yake tashi a falon sai lafiyayyen qamshinta wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadin gaske.
Hanifa dai asalinta ba ma’abociya kallo bace don haka ko kadan babu ruwanta da TV.. Gaba daya ma ta manta when last ta kunna TV na falonta don haka ko a yanzu TV a kashe take.. abinda kadai take amfani da shi shine home theatre, she connects it with her phone and dance to her music!
Wasu tulin empty ledojin Chocolates ne a kan side stool din da yake kusa da ita sannan a gefe kuma akwai wadanda bata bude ba.. this alone will tell you cewar Hanifa ma’abociya son Chocolates ce.
Mamy wadda ta shigo falon da Sadiq trailing behind her ce tace “Babyn Paapa kinyi baqo..”
Bata tsaya sauraron abinda Hanifa zata ce bane ta kalli Sadiq tace “have a seat”
“thank you Ma”
Hanifa wadda take kwance bata dago kai ba domin kuwa qamshin turaren shi da ta ji kawai ya sanar mata da ko waye tun ma kafin yayi magana..
Sadiq… her worst enemy at the moment!
Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta ji kamar zata mutu..
Bayan Mamy ta fita ne na ga Sadiq ya zauna akan kujerar da take fuskantar wadda Hanifa take kwance…
Wayar shi na ga yana latsawa ba tare da ya kalli Hanifa ba.. Hakan kuwa ya bata mata rai domin kuwa his presence is actually doing something weird to her gashi kuma hakan ya hana ta cigaba da abinda take yi..
Tsawon minti biyar Sadiq yana latsa wayar shi.. ko da na duba gani nayi yana replying wasu Mails ne don haka zan iya cewa basar da Hanifa da yayi is not intentional, toh amma kuma ai Mails din can wait abi??? well, I have no choice but to contradict myself on this.. Sadiq is actually doing this on purpose🤣
“Babyn Paapa, how are you feeling?? hope kin ji sauqi sossai?? Allah ya baki lafiya..” ta jiyo muryar shi kamar daga sama.
Cike da mamaki Hanifa ta dago kai tana kallon shi yayinda yake latsa wayarshi fuska a murtuke.. kai kace bai taba murmushi ba!
Banda don ta ji abinda yace da zata rantse ba da ita yake yi ba… Lallai Sadiq babban dan wulaqanci ne..
“…abinda kike tunanin zan ce miki kenan?? you think I am actually here to check on your well being??”
Ya dago kai ya kalle ta cikin ido yace “hell no.. kin fi kowa sanin cewar I dont care about you or what happens to you”
Kalaman Sadiq ne suka qara bata mata rai.. Gani nayi ta tashi zaune tana kallon shi.. irin kallon nan da idan an bata bindiga zata iya harbe shi
“I am sure you fell sick because of me and guess what?? it gives me plenty of joy… just wait until you come to my house and…”
Kafin ya qarasa maganar shi tace “Oh Mr Sadiq, I am so sorry for everything that I’ve done to you.. bazan qara yi maka laifi ba.. please kace ma Paapa a janye maganar auren nan because I am scared of you” ta qarasa fadi cikin qaramar murya yayinda fuskarta ta koma kalar tausayi
Mamakin da ya bayyana a fuskar Sadiq ne ya sanya ta yin murmushi tace “is that what you expect me to say to you?? hell no Mr Monster.. I am not sorry at all for what I did to you.. Just minutes ago, ina ta tunanin yadda zan hana auren nan but guess what, i am more than ready to become your wife. Ka shirya tarban bala’i a cikin gidan ka”2
Gani nayi ya girgiza kai yana murmushi ya miqe tsaye yace “Okay Mrs Bunza.. bring it on”
“Allah ya kiyaye in zama Mrs Bunza.. I will be in and out of your house before anyone could address me as that.. Monster” ta qarasa fadi da qarfi cikin bacin rai da masifa yadda zai ji domin kuwa shi har ya fita abinshi…