RAYUWAR ASMAU CHAPTER 12
Da dare akai dinner inda yan mata sukai ankon wani pink material.
Amarya kuma ta saka golding kala, ango ma golding shadda ya saka.
Asama’u kuma ta saka Dark blue din material sosai tayi kyau.+
Sir Sabir ma Blue shadda ya saka sai ya fito shima kamar angon Asma’u.
Anci ansha an yi liki, duk wanda yaga Asma’u sai ta burge shi dan komai nata da banne ga kyau ga jikin yana dauka.
Samarin wajen sun yaba da ita. Sir Sabir kuwa sai kareta yake.
Sai da sukaje suna liki ne, kuma sai kuka taga ga Mami ga Yaa Buhari gata ammn ba Dady.
Sosai ta sa mutane da yawa kuka a wajen.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.
Inda washe gari aka dau amarya aka kai ta gidan mijin ta dake rijiyar zaki.
Gida ne katon gaske dan Dady ne ya gina masa shi.
haka nan an zubawa Zainab kaya sosai. Sai da angwaye suka je sanna suka taho Asma’u na zolayar Zainab
Gida su Asma’u suka tafi da su Maimuna da Maryam.
Aka bar amarya da ango su kadai a gida.
A gida ma wasu dayawa duk sun tafi dan daga Momy sai matar Uncle Abubakar da Uncle iliyasu da Mama binta da zasu tafi gobe.
Washe gari da safe Mami ita ta aikawa da amarya da ango kayan kari.
Su Asma’u kuwa suna tare da kawayen ta. Lokacin su Hafsat da Maimuna sun shirya kayan su zasu tafi.
Sosai Asma’u ta hada musu kayan biki har da turmin atamfa.
Har gun Mami ta raka su sukai mata sallama.
Mami ta ce, a sa driver ya kai su gida. Haka ai kai kuwa.
Driver sshi ya kai ko wacce har gida. Gidan ya rage daga Asma’u sai Maryam da Nusaiba da ta ce baza su tafi ba.
Sai karfe daya suka shirya suka tafi gidan Amarya.
Suna zuwa suka tadda Amarya a falo taci kwalliya, sai kamshi take fitar wa.
Tana ganin su ta taro Asma’u sai da suka zauna kuma sai ta bata fuska.
Kallon ta Asma’u tayi ta ce,
“Lafiya?”
“Wallahi sis baki kyauta ba wai sai yanxu ni nayi zuciya.”
Ta fada tana komawa gefen Maryam tana tambayar su ya gajiyar biki.
Dariya Maryam tai ta kalli Nusaiba ta ce,
“Yo ai ke zamuyi wa ya gajiya ko?”
Nusaiba ta ce,
“Lallai kam amman sai naga kamar ba ai komai ba.”
Dariya Asma’u tayi ta ce,
“To ku ina ruwan ku.”
Zainab ta ce,
“To waya fada muku sai kun gane anyi ko ba ai ba. Kowa da yanayin jikin sa haka nan wani yaji zafi wani bazai ji ba. Wani ya fitar da jini wani bai fitar wa. Wani tafiyar sa ta canja wani ba haka ba. Ke duk abinda zaku ji ana fadi ma wani vai san anayi ba. dan haka nidai baku jin baki na anan.”
STORY CONTINUES BELOW

Asma’u ta ce,
“Dadin mutum yayi karatun bangaren lafiya kenan duk da zaku san hakan ai.”
Maryam ta ce,
“Wai kuna so kuce duk abinda muke karantawa a littafi ba haka bane.”
Kai Zainab girgiza ta ce,
“Ba haka bane jiki jiki ne. Wani zai ji abinda yafi na littafi wani zaiyi zazzabi wani har da suma da dai sauran su.”
Kai Nusaiba ta gyada na gamsuwa da abinda taji.
Zainab ta ce
“Ku daure ku kai budurcin ku gidan mazajen ku dan ba darajar da takai wannan a idon mijin ku. Daga ranar da ya same ki a haka zaki ji dadin rayuwa aamman da ya samu akasin haka zaki gane kuranki.”
Maryam ta ce,
“Sis wa yakai mu. Inda muke jin labarin wacce takai budurcin ta yadda take samun jin dadi. Akasi da wanda bata kai ba wulakancin duniya ya kare akanta ba ma wacce ta zibar da mutuncin ta.”
Nusaiba ta ce,
“Shiyasa nifa Uncle Sabir yake burgeni. Ba ruwan sa bare har ya nuna yana son wani abu agun mace ko Sis.”
Ta fada tana kallon Asma’u.
Asma’u da jin ta sako Sabir duk jikin ta yai sanyi ta gyada mata kai ahankali.
Daga haka suka cigaba da hira har Maami ta aiki da abinci da rana.
Sai yamma suka tafi bayan sun gyare mata gidan.
Gida suka wuce suna shiga suka zauna falo ana hira da su Momy da Mami.
Sosai Mami ke jan su a jiki sai kace sun saba.
Haka suka raba dare suna hira har Maryam tai bacci ta bar Asma’u da Nusaiba.
Nusaiba ce ta kalli Asma’u ta ce,
“Sis dan Allah in tambaye ki?”
Asma’u ta kalle ta ta ce,
“Ina ji!”
Nusaiba ta ce
“Dan Allah ki fada min gaskiya.”
Murmushi Asma’u tayi ta ce,
“Karki damu!”
Shiru Nusaiba tayi kafin ta ce,
“Dan Allah mene tsakanin ku da Uncle Sabir.”
Murmushi Amsa’u tayi dan daman jikin ta ya bata tambayar da zatau mata kenan.
Kasa tayi da kai sannan ta dago ta ce,
“Malami nane, sai kuma yanzu da yake so na.”
Kai Nusaiba ta jinjina tai shiru. Murmushi Asma’u tayi ta ce,
“Ke fa?”
Ta tambaye ta ne dan bata san tana son Sabir ba.
Ajiyar zuciya Nusaiba ta sauke ta ce,
“Tin da na hadu dake naji kin kwanta min abu daya ne yasa na fara jin haushin ki shine ganin yadda Uncle Sabir ke miki. Gaskiya zan fada miki ni nake mutuwar son sa. Shi kam bai damu dani ba.”
Tayi shiru, sanna ta ci gaba da magana. Ta ce,
“Sis Mu biyu iyayen mu suka haifa nice auta dan haka duk son duniya suka daura mana. Maryam kawata ce, dan Mamanah da mamanta ma kawaye ne kamar yadda Dady na da nata ma abokai ne. Mun shaku da Maryam sosai, komai nawa ta sani nima haka. Dan ko zamu hutu tare muke zuwa daga family na har nata. Tin ina primary In muka zo hutu Uncle Sabir ke burgeni ke har na girma na fara son sa. Duk yadda nake dan nuna masa ina son sa baya gane wa. Sai ni kadai nake ta haukar son sa. Ina son Uncle Sabir kamar rai na. Ina kaunar sa, wallahi amman ke kina son sa?”
Nusaiba ta tambayi Asma’u. murmushi Asma’u tayi ta ce,
“Sir Sabir a matsayin wa na dauke shi. Ni malami na ne,”
Nan ta bata labarin haduwar su da labarin ta da Yaa Aslam ta karashe labarin tana kuka.
Sosai Nusaiba ta tausayawa Asma’u. Dan itama sai da tai kwalla dan itama tasan yadda so yake.
Hawaye Asma’u ta goge ta ce,
“Sir Sabir shike neman soyayya ta amman ni ba son sa nake ba. Amman nai miki alkawarin zan nusar da shi son da kike mas…..”
“A’ah……”
Nusiaba ta dakatar da ita.
“Karki so ma. Akan me a tinda yana son ki wallahi gara ya aure ki ina son farin cikin sa ko da zan kasance a cikin bakin ciki zan ji dadi in shi yana cikin farin ciki. Ki bari kawai Allah tabbatar da mafi alheri.”
Asma’u ta girgiza kai ta ce,
“Bazan taba iyawa ba. Bazan iya ba kina son sa sai na san yadda ya aure ki.”
Nusaiba ta ce,
“A’ah!”
Banza Asma’u tai mata ta shige bayi tai wnaka ta dauro alwala ta zo ta saka kayan bacci ta hau kan sallaya.
Tin Nusaiba na jiran ta idar suyi magana har bacci ya dauke ta.
Washe gari da safe kuma suka hau shirin tafiya.
Duk yadda taso su yi magana da Asma’u. Asma’u ki tayi.
Da kanta ta dauke su har gida bayan Mami ta basu kayan biki suma da turamen atamfofi.
Suna zuwa gida suka ci karo da Sabir shima zai fita.
Kai Asma’u ta dauke tai packing sannan ta fice tayi cikin gida da sauri.
Mamah ta sama a falo ta zauna a gefen ta suka gaisa. Suna cikin gaisawa su Maryam suka shigo.
Zama sukai gaba daya ana ta hira sai yamma sanna Asma’u ta koma gida.
A washe gari kuma Momy zata tafi. Ranar tin yamma suna tare da Momy.
Momy na tambayar ta aiki sannan tana son bugar cikin ta ko akwai wanda yace yana son ta.
Haka dai ta roke ta kan ta samu taje tai mata kwana biyu.
Asma’u ta amsa ne kawai badan zata je ba.
Har ga Allah tana son ganin Yaa Aslam sannan tana son ta san a halin da yake ciki.Washe gari Momy ta tafi. Haka gidan ya koma daga Mami sai Asma’u.
Yaa Buhari yana zuwa da safe da dare.
Ba abinda Asma’u ta sa a gaba sai aikin ta.
Zumunci kuwa sun kara kullawa da Nusaiba.
Yau tana zaune a garden tana sanye da wani Ash less dinkin doguwar riga.
Kanta ta yafa karamin bakin mayafi. tana zaune ta zubawa wata shuka ido. Ta lula can duniyar tunani.
Kamshin turaren sa da taji shi yasa ta juyo dan ganin wanene?
Sir Sabir ne, yake tsaye yana sakar mata murmushi.
Itama murmushin tayi. Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta.
Ido ya zuba mata, kasa tayi da kai, murmushi yayi ya ce,
“Baby nah!”
Shiru tayi, ya ce,
“Me yasa kike boyar min ne, bayan kinsan ganin ki shi zai samin sassauci a zuciya ta.”
Dagowa tayi idon ta jajir ta ce,
“Dan Allah Sir ka kyale ni kaima kaje wajen mai son ka.”
Kallon mamaki yake mata ya ce,
‘Me sona kuma? Wace mai so na?”
Mikewa tayi ta ce,
“Kai ma kasani ai, dan Allah Sir ka so Nusaiba!”
Ta fada tana tafiya. Mikewa Yayi yabi bayan ta.
Kafin ya karasa ta shiga mota ta tayar harta danna horn mai gadi ya bude mata gate.
Mota shima ya shiga yabi bayan ta. Gidan Zainab ta tafi. Sabir kuwa yana biye da ita a baya.
Tana shiga shima ya shiga. Da sauri ta fita a mota tayi cikin gidan.
Tana shiga taci karo da Zainab, kallon ta Zainab tayi ta ce,
“Lafiya?”
Ganin ta da tayi ta shigo a firgice, bata rufe baki ba Sabir ya shigo.
Murmushi tayi ta ce,
“Au ashe tare kuke?”
Ciki Asma’u tayi ta barsu a nan falo. Zama yayi yana kallon hanyar da Asma’u tayi.
Murmushi Zainab tayi duk da yanayin Asma’u ya bata tsoro.
Lemo da ruwa ta dauki masa. Bai sha ba sai magana da ya farai mata.
“Zainab ke kadai kika fi kusanci da Asma’u a kawayen ta dan Allah ki taimaka ki shawon kanta. Wallahi ina son Asma’u amman ita taki ta gane”
Murmushi jin Dadi zainab tayi ta ce,
“Kar ka damu zan sanar da ita.”
Kai ya girgiza ya ce,
“Na fada mata, amman taki ta fahimci irin son da nake mata ne”
“Ka barni da ita. Ina zuwa.”
Ta mike tayi
STORY CONTINUES BELOW

Tana daya daga cikin dakin da ta ce na ta ne.
Saboda shi karami ne kuma komai na ciki kalar ta ne.
Tana kwance akan kujera idon ta lumshe hawaye na zubo mata.
A ranta take cewa
‘Duk Yaa Aslam ne ya jawo mata. Yanzu ita bata da wani kwanciyar hankali. Daga wancan sai wancan. To wai ita tayaya zata auri Sir Sabir bayan tasan irin son da Nusaiba ke masa. Ai kamar ta zama azaluma ne “
Wata zuciyar ta ce,
‘To ai shi baya son ta. In kinso shi ba wani abu bane.”
Juyi tayi ta bude ido ta. Zainab ta gani tsaye akan ta.
Zaune ta mike ta ce,
“Ya dai?”
Kai ta girgiza ta zauna agefen ta. Ta ce,
“Lafiya naganki haka?”
“Uhnm Nida Sir Sabir ne!”
Ta fada mata duk abinda ke faruwa.
Zainab ma tana son Asma’u da Yaa Aslam to amman ba yadda zasu yi tinda shine ya nuna baya son ta.
Tinda haka ne gwara ta amshi Sabir din tinda shi yana son ta.
“Asma’u nima a gaskiya ina son ki da Yaa Aslam, but amman tinda haka ta faru ki yi hakuri ki rumgumi wanda yake son ki. Bance ki Yaa Aslam baya sonki ba, amman ki karbi Sir Sabir kuma ki yi istihara Allah zaba mafi alheri. Kiyi hakuri.”
Zainab ta dafa kafadar ta.
Dagowa tayi da idanun ta dake zubar da hawaye ta ce,
“Zainab kinsan so amman baki san zafin sa ba. Nusaiba na kaunar Sir tin tana yarinya take son sa. Tayaya xan raba wannan soyayyar da take masa. Ki tayani wannan abin ina son Sir ya fara son Nusaiba ni na hakura dashi. Ina tausayawa Sir saboda yana sona ni bana son sa, kuma ni ba kinsa nake ba, kawai dai Yaa Aslam nake so. Gwara ya auri wacce yake so zai fi jin dadin yasan yai aure da ya aure ni ni kuma zuciya ta na wani wajen ki duba magana ta Zainab nasan ke zaki fahimce ni.”
Ta fashe da kuka, jikin ta Xainab ta jata tana lallashin. Sai da tayi shiru sannan Ta ce,
“Zan sanar da shi amman ki daina kukan nan.”
Kai ta gyada. Mikewa Zainab tayi ta fita. Ta sanar dashi indai yana son Asma’u to sai dai ya hada da Nusaiba. Sosai hankalin sa ya tashi. Lallabashi tayi kan yaje yai tunani sannan ya tafi gida.
Wajen Asma’u Zainab ta koma. Kallon ta tayi ta ce,
“Sis nai miki shishigi fa”
Kallon ta Asma’u tayi ta ce,
“Name fa?”
“Nace indai yana son ya aure ki sai dai ya hada ke da Nusaiba.”
Shiru Asma’u tayi. Zainab ta ce,
“Kiyi hakuri in bakiji dadi ba.”
“Ba haka bane. Amman ba komai.”
“Yauwah dan Allah sis kina rage damuwa akan Yaa Aslam. Kina addu’a Allah ya yaye miki son sa.”
Dagowa Asma’u tayi ta kalle ta ta ce,
“Wallahi kullum sai nayi wannan addu’ar amman kamar bana yi son Yaa Aslam kara shiga ta yake. Kwanaa biyun nan ji nake kamar nai hauka dan son ganin sa da nake. Na rasa ya zanyi da son sa. Ina son Yaa Aslam kuma yana daga cikin wadan da ya koya min son sa haka.”
Ta fada hawaye na saukowa daga idon ta.
“To ya isa. Allah yasa haka shine mafi alheri”
Asma’u ta ce,
“Ameen!”
“Ina Mami?”
Zainab ta tambaya
“Uhmm Mami ta fita nima bata san nazo ba.”
Asma’u ta ce,
“Me kika dafa ne?”
“Taso muje ki gani.”
Ta mike ta kama hannun ta.
Dining sukayi suka zauna ta fara cin abinci.
Ranar har dare suna tare da yake Yaa Buhari bai dawo da wuri ba basu san har dare yayi ba.
Sai karfe goma sannan ya shigo, da ta ce, zata tafi kuma ya ce,
“Ba inda zata tinda Mami tasan tana gidan ta kwana kawai.”
Haka dole ta kwana agidan. Washe gari tare da Zainab sukai komai tai wanka ta shirya ta ce zata tafi.
Hanata tafiya yayi a lokacin ya ce, Ta bari sa tafi tare gaba dayan dan zainab ma zataje gaishe da Mami.
Haka ta zauna har karfe biyu sannan suka tafi gaba dayan su.
A gida suka yini sai dare suka koma gida.
Mami kuwa sai jan Zainab take ajiki bama da taga tana jin kunyar ta.
Ita ta fiso ta zama free da ita kamar yadda Asma’u take mata.
Tin daga lokacin ya zama na yar boye ke tsakanin Sir Sabir da Asma’u.
A office ta maida kanta busy yadda ko ya ganta ba damar magana saboda yadda take tare da patient din ta.
Haka a gida da ta shigo taga motar sa take komawa, in kuwa har ta shigo da sun gaisa take guduwa sama.
In waya ya kira ma baya samu dan yanzu sai tai kwana nawa ma wayar ta a kashe.
Sosai ya damu, dan yana son Asma’u yana kuma jin tausayin ta.
A haka sai da suka debe wajen wata uku suna yar buyar nan.
Kuma baya taba samun damar da zai ganta.
Sunyi bikin Maimuna inda aka kai ta gidan mijin ta dake sabuwar gandu.
Gida ne mai kyau kuma komai ya mata. Sosai Asma’u ta bata gudumawa mai yawa banda wasu abun da ta dauke mata.
Asma’u da Zainab ne dai sukai mata Babbar kawa.
Wanna karan ma sai da Maryam tazo, Nusaiba dai bata zo ba dan a lokacin basa kasar.
Anyi biki lafiya an kai amarya gidan ta.
Sosai Nazir ya amshi kaddarar Maimuna tinda daman yasan ba budurwa bace.
To shi ita yake so, dan haka ya daura aniyar zama da ita da dadi ba dadi.
Duk da Maimuna ba ruwan ta yanzu abinda ya ce, shi take yi.
Zaman lafiya suke sosai yake faranta mata shima take faranta masa.
Bangaren Sabir kuwa da abin ya ishe shi sai ya samu Yaa Buhari da batun yana son Asma’u.
Duk da Yaa Buhari yafi son Asma’u su daidai ta da Aslam amman bai sa shi rashin jin dadi ba.
Sosai yaji dadi dan shi yasan waye Sabir, Dan in Asma’u bata auri Yaa Aslam ba ta auri Sir Sabir ba komai.
Dan ya tabbata Sir Sabir ma zai kula masa da kanwar sa.
Daga nan kuwa Yaa Buhari ya tafi gida ya fadawa Mami.
Mami cewa tayi, a tambayi Asma’u aji daga bakin ta.
Yaa Buhari ya ce,
“Aah Mami in har aka ce sai anji daga bakin Asma’u to tabbas baza ta amince ba. Kinsan irin son da takewa Yaa Aslam.”
Shiru Mami tayi ta ce, zata tambayi Momy taji.
Momy ma sosai taji dadi dan daman ta yaba da hankalin Sabir sosai.
Itama cewa tayi a bari sai abin ya matso a fada mata sanin halin Asma’u zata ce A’ah
A bangaren Sabir kuwa yadda yayi zai hada Nusaiba da Asma’u dan yasan in ba haka ba Asma’u baza ta taba yadda ba.
Yasan ko ba komai Nusaiba mai son sa ce dan haka zai samu duk abinda yake nema a gun ta.
Amman yayi wa kansa alkawarin sai ya yayewa Asma’u halin kuncin da take ciki na rashin Yaa Aslam.
Ko bata son sa shi zai zame mata farin ciki. Farin cikin da zata manta da Aslam.
Nusaiba kuma ta fawalawa Allah komai. Addu’a da istihara take amman kullum son Sabir kara shigar ta yake.
Duk da haka suna waya da Asma’u dan sun zama kawaye.
A bangaren Zainab yanzu auren su wata bakwai yanzu tana da ciki wata hudu.
Bakuga yadda Asma’u ke ji da cikin nan ba.
Dan gidan ta koma da zama ma saboda taya ta aiki.
Komai yi mata take. In Asma’u ta zauna hira da cikin kuwa kwa rantse da mutum take hira.
Sosai Zainab ke kara lalashin ta akan zancen Sabir.
Duk da yanzu ya daina mata maganar amman tana lura ba wai hakura yayi da ita ba.
Yau tana gidan Yaa Buhari ake sa ranar bikin ta da Sabir, an sanya rana shekara daya, saboda so ake a hada bikin da na Nusaiba akai masa mata biyu a rana daya.
Ya sanar da su manufar sa tayin hakan kuma sun yadda dan sun san kafiyar Asma’u.
In ta ce,
“Eh!”
Ba wanda zai sa ta ce,
“A’ah!”
In kuwa aka matsa to za’a ga ba dai dai ba.
Duk da Momi bata so hakan ba. Amman ta yadda dan san halin yar tata.
Momy ma tazo komai anyi shi cikin kwanciyyar hankali.
Asma’u kuwa tana can bata san ana yi ba.
Duk da Zainab ta sani. Sai dai Asma’u kanji yawan faduwar gaba.
Momy ce zaune a falo tare sa Mami da Yaa Buhari.
Bayan sun gama tsara komai ne, Momy ta kalli Buhari ta ce,
“Buhari kun yi maganar Yayan ka da Mami kuwa.”
Dagowa yayi ya dan jima kafin ta ce,
“Wallahi Momy bamuyi ba. Kuma abin na raina kullum. Bama Asma’u da nake son sanar wa.”
Kai Momy ta girgiza ta ce,
“Kasan sai a shekaran jiya na fada yadda da ba haka matar Aslam ta bar shi ba. Kaga yadda take masa kuwa ta maida shi bawa fa, ba abinda yyake iya yi sai da izinin sa. Aslam duk ya rame.”
STORY CONTINUES BELOW

Tayi shiru ta ce,
“Jiya da na aika a kira min shi cewa tayi bazai zo ba, sai da ta shiga ciki yake bawa dan aiken hakuri kan ya bani hakuri tinda ta ce, bazai zo ba. Ni da ganin Aslam fa sai nai wata. Kudi kuwa account dinsa na hannun ta. Dan Allah Buhari yazamuyi Na fison muyi abu wanda baza mu.kaucewa Allah ba. Dan ni bana son bin malaman nan su fara juyawa mutun tunani da canfe canfen su.”
Kai Mami ta gyada ta ce,
“Innaillilahi wa inna illahir rajiun. Yanzu yadda ta maida Aslam din kenan. To Allah kai mana magani.”
“Ameen!”
Momy da Buhari suka amsa da.
Buhari na komawa gida ya samu Asma’u ya ce,
“Asma’u ina son magana da ke!”
Ganin da yadda yai mata maganar yasa ta san magana ce mai mahimmanci.
Kallon sa tayi ta ce,
“To ina ji.”
Tana komawa gefen sa. Kallon ta yayi, ya ce,
“Ina son ki sa a ranki duk abinda ya faru da bawa mukaddari ne Allah ya riga da ya tsara, sannan ina fatan duk abinda yya same ki zaki amsa hannu bibiyu”
Kai ta gyada ta ce,
“Insha Allahu.”
Ya ce,
“Magana zan miki guda biyu kuma kowa ce ina son ki amshi abinda zan fada miki.”
Sai da ta dago ta kalle shi sannan ta ce,
“Insha Allahu zzan dauka.”
Gyaran murya yayi sanann ya ce,
“Sabir!”
Jin suna da ya ambata yasa kirjin ta dukan uku. Ta dago da sauri.
Kai ya dauke ya ce,
“Sabir ya same ni da zance yana son ki. Dan haka mun ba shi dama dan nasan in take ce baza ki amshe sshi ba. Yau aka sa ranar bikin ku nn da wata shekara za ayi bikin ku insha Allahu.”
Kasa tayi da kai tana zubar da hawaye.
To ita dan ta dan ta auri Sir Sabir mene, tinda ta rasa wanda take so ma.
To amman fa ita Nusaiba take ji. Kuma bazata iya bujurewa maganar su Mami ba.
Tana son Yaa Aslam amman kenan ya zama dole ta hakura dashi. Tinda tasan ba yadda zai tana da aure ta so wani ba kuma.
Duk maganar da Yaa Buhari yacigaba da fadi ba ji take ba.
Sai da taji ya ambaci Yaa Aslam sannan hankalin ta ya dawo kansa.
“Tinda naje Abuja naga halin da yake ciki ba san ba haka matar sa ta bar shi ba. Sai kuma yau da Momy tazo take fadan halin da yake ciki. Asma’u mune kadai yan uwan Yaa aslam dole mu tsaya akan sa da addu’a sannan da wani abun da muka sani na tsarin jiki.”
Tinda ya fara magana take kuka har yanzu da ya kare abinda yake fadi
“Kar ki diba abinda yai miki ki ‘ki taya shi da addu’a kinsan Yaa Aslma ya so ki a baya to yanzu ma ki dauka kaddara kuce tasa kuka rabu “
Shiru tayi amman sai hawaye dake ambaliya a idon ta.
“Asma’u!”
Ya kira sunan ta.
Dagowa tayi da idanun ta da suka rine da hawaye sukai jajir da su.
“Mene na kuka? Sabir din ne bakya so?”
Kai ta girgiza
“To Yaa Aslam din baza ki taya da addu’a ba?”
Shima kai ta girgiza.
“To yi hakuri ki daina kuka kinji.”
Kai ta gyada masa.
Mikewa tayi jiki a sanyaye ta shiga dakin da take kwana.
Kayan ta ta fara hadawa tana cikin hadawa Zainab ta shigo.
Kallon ta ta tsaya ganin tana debo kaya daga cikin durowa zuwa cikin akwatin ta.
“Lafiya?”
Zainab ta tambaya.
“Tafiya zanyi. Sis yanzu a gida an daina so na mai sona a duniya mutum daya ne, kuma ya mutu wanda na dauka shima yana sona din ya daina, to Mami ma da Yaa Buhari sun daina. Wai har sun gaji dani zasu aurar dani ba tare da ina son sa ko an tambayen ra’ayi na ba. Zan bar muku gidan ku ina jin na tare muku wani abu shine yake son nai aure na bar muku gida. Zan tafi gida nasan can Mami baza ta koren ba dan nasan shi zai kai mata maganar Sir Sabir.”
STORY CONTINUES BELOW

Buhari da yana tsaye bakin kofa shima ya shigo. Ya ce,
“Ko daya kanwata. Bazan taba daina son ki ko gajiya da ke ba. Ki fuskance ni. Nasan dai ke ba yarinya bace karama kinsan komai. Bai kamata ace kin kai yanzu ba aure ba. kin gama karatu har kina aiki ai gwara kiyi aure tinda kin samu mai son ki. Kada ki manta da fa tini kina gidan ki wa yasani ma ko da ciki ko ‘da. Mutunci ‘ya mace gidan mijin ta fa.”
Fuska ta rufe saboda kunya. Yaa Buhari ya ce,
“Kiyi hakuri ki karbi zabin mu insha Allahu zaki ji dadi.”
Kai ta gyada. Ya ce,
“To ki mai da kayan.”
Kai ta make masa, ta ce,
“Ni dai gida.”
Murmushi yayi ya ce,
“Husnah daru.”
Kai ta gyada ta ce,
“Naji.”
Ya ce,
“Kya bari dai gobe ko?”
Kai ta girgiza masa. Duk yadda yaso ta zauna ki tayi.
Da zai matsa mata ma sai ta saka masa kuka.
Dole suka bar ta ta tafi ba dan sun so ba.
Tana zuwa gida ta shige dakin ta ta rufe.
Kwanciyya tayi ta rasa wane tunanin zatai tunanin aure da za ai mata ne ko tunanin halin da Yaa Aslam yake ciki ne.
Mikewa tayi ta fada bandaki alwala tayo ta fito ta dinga yin nafila.
Ta jima tana yi sannan ta dauko kur’ani ta karanta, addu’a tayi masa sosai.
Sannan ta zame agun bacci ya dauke ta.
Buhari ne ya fadawa Mami, Asma’u ta taho wannan yasa ta zo daki ta dduba.
A kwance ta same ta a kasa, idanun ta sun kumbura
Tabata Mami tayi ta bude idanun ta. Jajir suke sai kace gauta.
Mami ta ce,
“Tashi ki hau kan gado.”
Mikewa tayi ta hau kan gado. Fita Mami tayi ta kawo mata fura da ta dama.
Kawo mata tayi ta amsa ta sha. Mami na fita ta koma ta kwanta.
Bacci ne yaki zuwa wanna yasa ta mike tana ta addu’a.
*MS Indabawa*
*LABARIN RAYUWAR*
*Asma’u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer’s*
Dedicated to *My lovelly Mum*
Pagr *61-65*

Tin daga lokacin rayuwar Asma’u ta kara komawa shiru shiru, dan daga wajen aiki sai ibada da ta sa a gaba.
Addu’a kuwa kullum yi take Allah ya yayewa Yaa Aslam abinda yake damun sa.
Haka nan addu’a ta daya ce Allah ya zaba mata mafi alheri.
Duk ta rame, Mami ma ta rasa kanta.
Dan ko zaman falo ta daina kullum tana daki kan sallaya.
Wayar ta kuwa ta kashe ta gaba daya.
Duk yadda Sir Sabir yake son ganin ta ko kiran ta awaya ba dama
Dan sai ya yini a asibiti bai ganta ba.
In ma a gidan ne haka baya taba ganin ta.
Yau kamar kullum zaman dakin ya ishe ta gashi bata sallah.
Carbi ne a hannun ta, ta mike ta fita tayi garden.
Tana shan kwana Sir Sabir na shigowa. Hango ta da yayi yasa yabi vayan ta.
Tana zama shima ya karasa wajen ya zauna.
Kallon ssa tayi ta dan yi murmushi. Ta ce!
“Ina yini?”
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
“Wallahi kina wahalar dani.”
Shiru tayi ta kasa ce masa komai. Ya ce,
“Husnah kiyi hakuri wallahi tausayin ki nake ji shiyasa nayi duk abinda na aikata amman kiyi hakuri. Bayan nan kuma Nusaiba da kike magana akai na miki alkawarin tare za’a hada bikin ku.”
Dagowa tayi da sauri ya gyada mata kai, ya ce,
“Eh! Tare aka saka ranar ku.”
Kai tai kasa da shi. Tin daga lokacin bata kara magana ba.
Tana can tunani wai su biyu za’ai bikin su. A ranta ta ce,
‘To mene ni da ba son mijin nake ba.’
Duk maganar da yake mata ma ba ji take ba tana can duniyar tunani.
Haka har ta jiyo kiran sallah magariba.
Wannan yasa ta mike tana ce masa,
“Sai anjima.”
Kallon ta yayi ta shige cikin gida. Kai ya girgiza ya rasa ya zai yi ya shawo kan Asma’u.
Tana zuwa ciki ta kunna wayar da wajen sati biyu rabon da ta kunna.
Text din Nusaiba da Zainab da Maryam duk ta gani.
Na Nusaiba ta bude taga sakon akan sa ranar da akai musu ne.
Tsaki tayi najin wai Nusaiba na murna dan zasu auri Sabir tare.
Wayar ta kashe ta jefa ta gefe daya ta saka kuka.
Sai da tayi mai isar ta sanna ta mike ta shiga bayi ta wanke fuskar ta.
Haka rayuwar ta ta kasance, har Zainab ta haihu ta haifi dan ta na miji.
Sunan Dady aka saka masa, Asma’u na kiran sa da Dady. Su kuma suna kiran sa da Aiman.
Sosai Amsa’u ke son Aiman. Dan kullun sai taje ta ganshi.
Duk da, da ta ganshi take tafiya. Ko zainab yanzu ta kasa gane kan Asma’u.
Dan sai taje gidan daga gaisuwa shikenan.
A haka har lokacin bikin su ya rage wata biyu da Sabir.
Amman zan iya cewa ko sun hadu daga gaisuwa shikenan dan ko zai yi magana ba jin sa ma take ba.
Haka nan su Mami da Momy da Zainab suke ta shirye shiryen bikin. Banda ita da ko an tambaye ta abu bata bada asma.
STORY CONTINUES BELOW

Takanas Nusaiba tazo dan jin me dame zasu yi amman sam Asma’u hata bata amsa ba.
Sai gun Zainab taje suka tsara komai da ita.
Ranan tana zaune tana lalluben littafan isilamiyyar ta sai da lalubo wani littafi.
Littafin da ta dade tana neman dan anan ta rubuta wasu abubuwa ta.
Tana Budewa taga littafan addu’oin da Malamin su ke basu ne tana rubutawa a ciki.
Dubawa ta farayi sai ta gano wani rubutu da ta rubata
‘Karya sihiri’
Dubawa tayi ta ga abinda ta rubuta.
‘Ya hallata a karya sihiri amman ba ayi ta ko wacce hanya sai abinda ya shafi hadisi ba aje gun wani dan yin wani abu ba.
Da farko wanda akai wa ya jimanci karatum Alkur’ani, Amanarrasuli, Ayatul kursiyyu, Falaki, Nas, Ahad, Bakara,
sannan mutum zai samu habbatus sauda, da zam zam sai a karanta, fatiha, aciki ya shafe jikin sa.
Ya na karanta suratul mulki, jinnu, yusuf, sannan ya samu zam zam, zuma a karanta Wasafati a ciki ana sha. Da yadda Allah komai akai wa mutum zai warke.”
Tana gani ta mike da sauri dauki wayar ta.
Kunnawa tayi ta lalubi number Momy ta tura mata da yadda zata yi sannan ta koma ta zauna.
Tana zama sa ga kiran Sabir nan tsaki tayi ta ce,
“Daga kunna waya.”
Dauka tayi ta kara a kunnen ta, tai sallama cikin sanyin murya.
Amsawa yayi daga dayan bangare. Ya ce,
“Kina lafiya?”
Kai ta gyada, sai kuma ta tuna baya ganin ta, ta ce,
“Lafiya!”
Ya ce,
“Asma’u yanzu haka kike ganin rayuwa zata tafiyu, aure fa zamu yi amman kwata kwata kin kasa sakin jikin ki dani sauran fa wata daya. Dan Allah ki tausaya min.”
Tausayin sa ne ya kamata, ya ce,
“Wallahi Husnah nai miki alkawarin samar miki dukkan farin cikin ki ko da zai zame min bakin ciki. Ki yadda dani.”
Shiru tayi dan ta saba da irin wadan nan kalaman wajen Yaa Aslam. Amman yanzu ina kalaman sukai.
Taso ace Yaa Aslam ne ke kara fada mata wadan nan kalaman.
Sai dai kash ba shi bane, to tana fatan Allah yasa hakan.
Alkawarin rikan da ya dinga daukar mata sai take ganin kamar Yaa Aslam ne.
Wannan shi ya dan sasauta mata ta sauko saboda tausayin sa da take ji.
A haka ya roke ta, akan ta daina kashe wayar ta.
Sannan kuma yana son ta fada masa abubuwan da take bukata.
Ba laifi ta dan saki jiki sunyi waya amman fa duk sai dai in shi ya tambaye ta abu.
Suna gamawa ya kira Nusaiba ita ma suka dan gaisa.
A bangaren Aslam kuwa abin ba dadin ji, dan pretty ta zame masa karfen kafa.
Baya iya komai sai da cewar ta. Duk da sai tai wata nawa bata gari amman ko kala baya iya cce mata.
Sai dai in shi zai fita ta hana shi fita.
Yanzu ma tayi tafiyar da ta saba ne, shine ya samu damar zuwa gaida Momyn sa.
Yana zuwa Momy ta bashi hadin abinda Asma’u ta turo mata ya sha.
Sannan ta bashi sauran ta ce, yana amfani dasu
Sosai ta masa nasiha kan ya dage da addu’a da karatun Alkur’ani.
Shi sai a lokacin ma ya tuna da duk ya manta bayayi.
Mutumin da a da sai ya kwana a kan sallaya.
Kwana biyun da tayi bata nan sosai ya samu ya dawo hayyacin sa.
Dan Mami da ruwan da ta bashi ya kare take kara aika masa da wani.
Ba laifi kuma yana tashi yai sallah da addu’oin neman tsari.
Sai gashi ya fara dawo dai dai, duk yadda ya firgice yanzu ya dawo dai dai.
Dan kullum zai je gaishe da Momy, kuma Yanzu yana yawan tunanin ina Asma’un sa.
Sai da Pretty tai sati biyu sannan ta dawo.
Tana shigowa gida ta tadda baya nan. Nan ta tanadi masifar da zatai masa.
Sai wajen karfe goma ya baro gidan Momyn sa.
Yana shigo yai cikin gida. A falo ya same ta kafa daya kan daya.
Kallon ta yayi ya watsar yayi hanyar bangaren sa
“Mallam baka ganni bane?”
Ta tambaye sa
Banza yai mata dan shi bai zata da shi take bama.
Mikewa tayi ganin ya shige ba tare da ya dawo ba.
Bayan sa ta bi, ban san me ya faru ba sai ihun ta na jiyo ta fito daga dakin sa da gudu.
Zama tayi tana defe kunci saboda zafin marin da taji.
Kallon dakin tayi tana tunanin ayyan kuwa Aslam ne wannan.
Aslam har ya daga hannu ya mare ta. Sosai take jin jina Abin.
Shi kuwa wanka yayi yai alwala ya saka kayan baccin sa zama yayi yana mamakin har tayaya ya bari yarinyar nan ta raina shi haka.
Ya jima yana tunani sannan ya mike ya tada sallah.
Ya jima yana sallah sannan ya zauna yyana addu’a, maganin shi ya sha ya dauki al kur’ani yana karanta Suratul Bakara.
Tin da ya fara karantawa yaji kansa na juyawa amman bai dai na ba.
Haka ya cigaba da yi. Har ya daina jin abinda yake ji.
Sannan kuma ya kwannta. Abin mamaki da ya rufe idon sa sai yaga Asma’u,
Mikewa yayi ya dauko wayar sa number ta yai dailing amman a kashe hakura yayi ya koma ya kwanta.