RAYUWAR ASMAU CHAPTER 13
Haka canji ya dinga samuwa wajen Aslam. Dan har fita yake hana Munasha.+
Sosai ta shiga hankalin ta. Dan taga ya dawo Aslam din shi na farko.
Wanda kwarjinin sa ya dadu, shi wani lokacin Mamakin mai ya hada shi da Pretty yake yi
Haka zai je gun Mami yai ta cewa,
“Mami number Asma’u nake nema.”
Sai dai Mami ta dauke kai in ya ishe ta. Ta ce,
“Me zakai mata?”
“Mami ina son jin muryar ta ne, ina son sanin halin da take ciki.”
Dariya Mami take in ya fadi haka. Tace,
“Aslam sai yanzu kake son sanin halin da take ciki, a kalla shekara biyu rabon ku baka taba tunanin haka ba sai yanzu.”
Yana mamaki in Mami ta ce, sun shekara biyu basa tare dan shi gani yake kwana ki ne.
Ganin yadda Aslam ya daina sakar mata dan ba inda take zuwa ma. Kuma duk masu aikin nan ya rage su.
Gashi ya amshi kudin sa dake gun ta.
Wannan ya tada mata da hankali har ta dau aniyar koma wajen Bokan ta.
Shirye shirye tafiya ta fara ba tare da tasanar da shi ba.
Haka ta dauki hanyar nijar. Agidan kawar ta ta sauka daga nan ta nufi gun bokan ta.
Yana ganin ta ya fara dariya dan yasan aiki ya lalace yanzu kuma damar sa ce.
Da ta fada masa damuwar ta yayi dariya ya ce,
“In zaki yadda ki bar Aslam shine yafi miki alheri. Kizo gareni muyi rayuwa mai dadi.”
Zabura tayi jin abinda bokan yake fadi.
Mikewa tayi tana nuna shi da yatsa. Ta ce,
“Allah ya kiyaye min na aure ka. na aure ka nace na auri wa? Baka da hankali.”
Ta tofar da yawo tayi gaba. Dariya yayi ya ce,
“Dani kike zaki dawo da kafafun ki.’
Haka ta tafi aka rakata wanin wajen,
Malamin bai mata aiki ba sai da ya kusance ta.
Haka taa dawo gida da sa ran ganin canji ammn abinda Aslam yai mata ya kara tada mata da hankali.
Dan takardar saki ya mika mata. Har saki uku.
Sosai ta firgita. zatai masa magana ya zare mata ido yace ta tafi zai aiko mata da kayan ta.
Gida ta tafi tana kuka kai kace babar ta ce ta rasu.
Aslam kuwa ji yayi kamar an dauke masa duk wani nauyi akan sa.
Yanzu damuwar sa daya ita ce Asma’u.
Asibitin sa, da baya zuwa shi ya koma ya tada shi.
Sai da ya dai dai ta komai sannan ya fara shirin tafiya Kano.
STORY CONTINUES BELOW

Pretty kuwa Momah ta ce ta dinga kwantar mata da hankali kan zasu san abinda zasuyi ta koma gidan ta.
Sosai ta ji dadi. Haka ta koma karuwancin ta duk da ita ta fison tayi aure ta huta.
Duk wanda yazo mata ta ce ya fito baya kara dawowa.
Haka nan ko a cikin yan harkar su haka abin yake.
Ita auren kisan wuta take son tayi. Tunawa da bokan ta da tayi ta ce,
“Bazata gun sa ba tasan ba zai sake ta ba ko ya aure ta.”
Shikuwa bata san yana can yana shirye shiryen yadda zai shawo kanta ba.
Rannan tana kwance akan gado ta mike zunbur.
Mayafi ta saka ta fito sai tasha. Motar nigar ta shiga suna sauka tayi wajen Bokan ta.
Da kuka ta ke ce masa ya taimaka ya aure ta.
A haka dai ta zauna a gun sa suna rayuwa banza dan ba aure sukai ba.
Asma’u kuwa abu na kara rikice mata duk da tana son sa son Sabir a ranta amman kuma ita tana son Aslam fa.
Ga shi lokacin biki sai karatowa yake yanzu sauran sati biyu.
Yau tin da ta tashi take jin faduwar gaba amman ta rasa ko ta macece.
A haka tai wanka ta shirya ta tafi aiki.
A wajen aikin ma ba wani aiki tayi ba sai kwanciyya.
Tana tashi kuwa taiwa Mami waya ta tafi ganin Dady.
Gidan Yaa Buhari ta tafi can ta zauna tana tai wa Aiman wasa.
Yaro ya fara girma kyakyawa dashi. Dan farin Baban sa ya dauko.
Yau tin safe Aslam yayo wa kano linkaya.
Da wajen karfe biyu ma yana cikin kano.
Gidan su Asma’u ya wuce kai tsaye. Yana zuwa Mami ta tarbe shi kamar yadda suka saba.
Zama sukai suna hira, yana tambayar Buhari.
Mami take fada masa haihuwa yaron da akayi ma.
Sosai ya taya shi murna dan Aslam akwai son yara.
Shiru yayi kafin ya dago ya ce,
“Mami! Husnah fa.”
Murmuahi Mami tayi ta ce, ta tafi aiki daga can kuma tace zata gidan Buhari.”
Kai ya gyada ya ce,
“Mami daman akan Husnah nazo.”
Gyara zama Mami tayi ta ce,
“To ina ji.”
Kasa yayi da kai ya ce,
“Mami wallahi ban san ya akai har na auri Pretty ba bayan duk duniya ba wacce na tsana sama da ita, wallahi Mami bansan me ya raba ni da Asma’u ba, sai kawai tsintar kai na nayi da rasa ta. Mami ki taimake ni ki bawa Husnah hakuri ta zo muyi aure.”
Tinda ya fara magana Sabir da ya ke tsaye bakin kofa yake jin sa.
Juyawa yayi ya shiga motar sa yayi gidan Buhari.
Mami ganin hankalin sa ya tashi yasa ta ce,
“Kaga Aslam ka kwantar da hankalin ka, kasan komai mukadari ne, ni kai na zan so Asma’u ta aure ka. Amman in haka Allah ya tsara zan fi kowa murna, haka nan in akasin haka ne ma bazan yi bakin ciki ba tinda nasan kana tare da ita a matsayin dan uwa. Yanzu dai ka kwanar da hankalin ka kaji.”
Kai ya gyada. Mami ta kawo masa abinci ya ci sannan ya hau sama
Dakin Asma’u ya fara shiga, kamshin ta da ya missing shi ya fara sheka yana lumshe idanu.
Kan gadon ta ya fada yana shinshinar sa
Ya jima a Kwance sanna ya mike yana kurawa wani hoton ta kallo.
Ba karamin kyau tayi ba, ita da wani jariri.
Ga dukkan alama yasan ‘dan Buhari ne.
Murmushi yayi ya ce,
“Su Husnah da ‘da.”
Mikewa yayi ya fita ya sauka kasa. Mami ya sama ya ce,
“Mami A wanne gida Buhari yake?”
Mami ta ce,
“Can Rijiyar zaki ne!”
Kai ya gyada ya fita da yake yasan duk gidan jen su.
Can ya nufa kai tsaye da zumudin ganin Asma’u.
Asma’u da tinda tazo tana dakin ta da Dady dan har bacci sukai suka tashi sukai wanka.
Kwalliya tayi sosai wacce ta dade bata yi ba.
Haka ma tai wa Aiman kwalliya dan fita take son suyi.
Tana fita falo ta samu Sabir a zaune.
Dan murmushi tayi ta zauna daga nesa dashi.
Ta ce,
“Yaushe kazo?”
Ya ce,
“Maman Baby kenan tun dazu. Ina zaku kukai wannan kwalliya haka.”
Murmushi tayi ta ce,
“Unguwa zamu ni da Dady nah.”
Kallon ta yayi a ransa ya ce,
“Kar dai ace Aslam taiwa kwalliyar nan.”
Mikewa tayi ta shiga dakin Zainab bata nan.
Kitchen ta shiga, ta ce,
“Mumyn Dady mu xamu tafi unguwa.”
Juyawa Zainab tayi ta ce,
“Au daman zuwan da Sir yayi kenan.”
Hararar ta tayi ta ce,
“Ba tare zamu fita ba.”
Baki Zainab ta kama ta ce,
“Oh wai ke ki ta fita da yaro sai kace matar aure ai sai ya kashe miki kasuwa. Oh ko da yake an siyar daman.”
Dariya Asma’u tayi ta ce,
“Kinyi kidan ki kinyi rawar ki.”
“To a dawo lafiya. Kema nan da yan wattan ni dai zaki rike kanin Dady.”
Zainab ta fada tana dariya
“Allah ya isa sis ke kin fiya abu wallahi.”
Ta fita tana cewa.
“Ba za mu kawo miki tsara ba ba.”
Inda ta bar shi anan ta same shi.
“Sir sai mun dawo!”
Ta fada tana yin gaba.
Mikewa yayi ya ce,
“Nima gida zan tafi.”
Ta shiga mota ta saka Dady a abin zaman sa.
Sanan ta koma driving sit din ta. Ta zauna.
Taga ya leko, ya ce,
“Gobe zasu kawo lefe fa amarya ta.”
Murmushi ta dan yi ta ce,
“To Allah ya kaimu.”
“Ameen! Yau an kai na Nusaiba.”
Ta ce,
“Masha Allah Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya.”
“Ameen a dawo lafiya.”
Ya mike yana daga mata hannu.
Hannu itama ta daga masa ta tada motar ta fice.
Motar sa shima ya tada ya bi bayan ta.
Suna fita Aslam na shigowa gidan.
Parking mota yayi sannan ya kira Buhari.
Buhari da baya gida ya ce, Ya shiga zai sanar da Zainab.
Haka akai kuwa dan Zainab da kanta ta zo ta shiga dashi sai sannu da zuwa take masa.
Kan kace kabo an cika masa gaba da kaya sha da ci
Mamaki yake yadda take masa sai ya tuna Pretty yadda take ma abokan sa.
Har takai ta kawo ba mai zuwa gidan sa.
Zama tayi suna hira sama sama har Buhari ya dawo.
Da saurin sa ya kara sa gun sa yana masa barka da hanya.
Sai da suka gaisa yake tambayar sa ina Aiman.
Zainab ya tambaya Zainab ta ce, masa sun fita da Asma’u.
Sai a sannan Aslam ya ce,
“Buhari magana nazo muyi akan Husnah!”
Buhari ya ce,
“Ina ji.”
Aslam ya ce,
“Wallahi Bro duk abinda ya faru ban san taya akai suka faru ba. Wai ni na guji Husnah yarinyar da bana tunanin zan iya rayuwa in ba da ita ba.”
Kai ya dago ya kalli Buhari idon sa jajir ya ce,
“Ka taimaka ka shawon kan ta please.”
Kai Buhari ya jin jina ya ce,
“Yaa Aslam kafi karfi komai a gun mu. To amman Asma’u ma dai gobe za’a kawo laifen ta nan da sati biyu biki.”
A zabure ya mike, yana dafe kai da yaji yana masa lilo kamar zai fadi.
Buhari ne ya mike ya kama shi ya zaunar.
Kan sa ya jinjina da kujera, yana jin zuciyar sa kamar zata fashe.
Ya jima a haka sannan ya mike ya fice. Bin sa Buhari yayi yana kiran sa.
Amman ina bai ma san yana yi ba. Mota ya bude zai shiga Buhari yai saurin kamo shi.
Ciki ya maida shi dan ya fuskanci baya cikin haiyacin sa.
Daki ya kai shi ya ce ya kwanta. Tinda ya kwanta ya rasa me ke masa dadi.
Komai ya tsaya masa. Tayaya zai iya cigaba da rayuwa ba tare da Asma’u ba.
Kai ya tabbata itama Asma’u na son sa. Bari ta dawo yaji ta bakin ta.
Haka yai ta saka da warwara. Ji yake tamkar a mafarki duk abinda yake faruwa.
Wai shine zai rasa Asma’u anya kuwa.
Haka dai.
A bangaren Sabir kuwa Asma’u ya dinga bi dan yaga ina zata.
Gidan Maimuna yaga ta dosa. Shima duk da ta shiga sai da yai awanni sannan ya juya ya tafi.
Sai magariba sannan ta dawo gida.
Tana shiga kuma taji wata faduwar gaba.
Motar da bata sani ba ta gani. Kai ta dauke ta ce,
“Baki mukayi kenan.”
Aiman ta dauko tana tafe tana masa wasa har ta shiga falo.
A falo suka baje dan anan suka tadda Zainab a zaune.
Kallon Zainab tayi ta ce,
“Momah da son dinta kun dawo.”
“Mun dawon Momyn Dady ya gidan?”
“Lafiya.”
STORY CONTINUES BELOW

Mika mata Aiman tayi ta ce,
“Bashi ya sha ai yayi kokari madara fa nai ta bashi.”
Amsa shi Zainab tayi ta fara bashi Mama.
Asma’u ta ce,
“Naga mota a waje baki mukayi ne?”
Zainab bata kai ga bata amsa ba Yaa Buhari ya shigo da sallama.
Hannun sa rike da hannun Yaa Aslam.
Tana ganin ya Aslam ta daure fuska. Kirjin ta taji ya tsananta da bugu.
Aslam kuwa na ganin ta yayo gun ta.
Yaa Buhari ne ya kama hannun Zaninab suka shige daki suka bar su nan.
Ganin haka yasa Asma’u mikewa da sauri zata bi bayan su.
Hannun ta ya dango hakan ya hanata iya tafiya.
Bata jiyo ba kuma bata da alamar dawowa.
Janyo ta yayi ya dawo da ita ya zaunar akan kujera.
Kai ta dauke, Kallon ta yayi Ya ce,
“Innalillahi wainna illahir rajiun! Ni kuma haka tawa kaddarar take kenan, Allah ka bani ikon cinye ta.”
Jin dumi akan hannun ta yasa kallon hannayen ta.
Hawaye ne ka zuba daga idon Aslam yana diga akan hannun ta.
Sosai zuciyar ta ta raunana. Ta dago fuskar sa tana goge masa hawayen.
Kallon ta ya tsaya yi komai ta tuna kuma ta dauke hannun ta daga fuskar sa tana hade rai.
“Naji kuma na cancanci ko wane hukunci a gare ki. Amman dan Allah karki bari a raba mu. Na tabbata da ba son wanda zaki aura kike ba.”
Wani bakin ciki ne ya turnuke ta. Wato kar ta bari a raba su dan yaji zatai aure shine yazo ya hana aure ta tinda shi yaje can da matar sa ba.
“Husnah kice wani abu!”
Taji tsigar jikin ta ya tashi jin muryar sa da kiran sunan da shi da Dady ne kadai ke fadi sai yanzu da Sabir ke fada wata rana.
Hannun ta ya kama. Ita kuwa tana can zancen zuci.
Jin ya kama hannun ta yasa tai saurin mukewa tana zame hannayen ta.
Kallon sa take ido na zubar da hawaye ta ce,
“Kazo ka hanani aure wato ko? Kake cewa kar na bari a raba mu bana son wanda zan aura, wa ya fada maka haka. Waya fada maka. To in baka sani ba ka sani ina son wanda zan aura kuma ba wanda ya isa ya rabani da shi sai Alalh kuma bazan taba auren ka ba.”
Tayi daki da gudu ta saka key. Tinda ta fara magana yake jin wata juwa na dibar sa.
Tana shiga daki shima ya zube nan wajen sumame.
Sai da akai isha’i ne Buhari ya fito ya tadda shi a haka.
Da sauri ya dauke shi suka nufi asibiti da shi.
Emergency aka nufa dashi amman har karfe sha dayan dare sun kasa dawo dashi cikin haiyacin sa.
Mami ce ta kira Buhari ta ce, Aslam yana nan.
Eh yana nan. Ya fada mata amman bai ce suna asibiti ba dan kar ya tada mata dda hankali.
Ranar a asibiti ya kwana
Zainab Kuwa duk yadda take knocking kan Asma’u ta bude kofa taki bude wa.
Asma’u tana can tana kuka ta rasa kukan me take.
Kukan murna Yaa Aslam ya dawo gare ta zatai ko kukan ya dawo a kureren lokaci take.
Bazata taba cewa bazata aure Sabir dan Aslam ya dawo gare ta.
Mutum da ya juya mata baya a lokacin da tafi bukatar sa.
Kuka kuwa ranar ta sha shi dan kwana tayi tana zubar da hawaye.
Duk bugun kofar da ake tasan akan ta fito ne.
To baza ta taba fita taga Yaa Aslam ba ya fama mata ciwon da bai gama warkewa a zuciyar ta ba.
Aslam kuwa har safiya bai farfado ba.
Har Sabir ya karbi aiki ya duba shi anan ya gane wanene saboda Asibitin Asma’u Buhari ya kai shi.
STORY CONTINUES BELOW

Zainab kuwa da kan ta, ta kai musu abinci da kayan da zai amfani.
Haka ta koma gida tayi tayi da Asma’u ta bude kofa amman taki.
Haka Asma’u ta kara yini da kwana kuka daga sallah sai kuka sune aikin ta. Addu’a kuwa ba wacce batai ba Allah ya cire mata Aslam amman ina kamar addu’ar neman kara son sa take yi.
Yau kwana Aslam uku kenan bai farfado ba. wannan ya bawa Buhari tsoro ya bugawa Mami waya ya sanar da ita komai.
Sosai hankalin Mami ya tashi ta tawo asibitin.
Duk abun nan da ake Sabir ne tsaye kan Aslam.
Asma’u kuwa ta zama ta dakin dan sam ta daina fitowa duk yadda Zainab take damunta ta fito amman taki.
Yau kwanan Aslam hudu yau ne Mami ta sanar da Momy halin da ake ciki.
Momy bata ce komai ba sai fatan Allah ya abashi lafiya.
Dan tasan koma menen bazai rasa nasaba da Asma’u ba.
Shi lokacin da ya sata a duk wani hali na kunci da tashin hankali wa yasani.
Amman shi yazo zai tada wa yarinya da hankali.
Da cewa tayi ma a tura shi Abujan in abun ya ci tura.
Da yamma Sabir nakan sa, yaga naurar tafiya da numfashin sa tana harbawa da sauri da sauri.
Nan da nan ya kira sauran nurses cikin ikon Allah sai ga Aslam ya na magana.
Koda Sabir ya kara kunnen sa sai yaji yana fadin,
“Husnah Husanh dan Allah kar ki bari a raba mu. Wallahi ina kaunar ki. Husnah! Husnah! Mutuwa zan yi in har kika guje ni.”
Ya cigaba da ambatar sunan ta. wata nan nauyar ajiyar zuciya Sabir ya sauke.
Sai da yaga ya bude ido ya kira masa Buhari.
Buhari na ganin ya farka ya dinga murna.
Haka Mami ma. Buhari shi ya kai sa yai masa wanka ya dawo da shi ya bashi ruwan zafi ya sha.
Ruwa aka kara saka masa dan tinda ya kwanta aken kara masa.
Aslam kuwa gaba daya ya kasa mantawa da kalaman Asma’u.
Wai tana son Wanda zata aura.
Dole ya rabu da Asma’u ko da xai rasa ransa tinda da tace, tana son wanda zata aura,
Sabir da yake likitan sa yasan me yake damun sa.
Ciwon zuciya ne, sai jinin san da yai muguwar hawa.
Da bai samu wannan hutun ba tabbas zai iya tashi da mutuwar barin jiki.
Kuma ya tabbata har da son Asma’u a silar ciwon sa.
*Toh kunji fa wai Aslam zai hakura da Asma’u*
*MS INDABAWA*
*LABARIN RAYUWAR*
*Asma’u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer’s*
Dedicated to *My lovelly Mum*
*76-80*
*Na gaida ke sisto nah. Barrister Sadiya. Ina kaunar ki yar uwa. Allah ubangiji ya kara basira. Allah kawo miji na gari. Ameen*

Kun yadda. Kuma zai iya?
Yau tin safe Zainab ke bugawa Asma’u kofa amman ko mostin ta bata ji ba.
Abinda ya daga mata hankali kenan. Ta dau waya zata kira Buhari kenan sai taji shigowar sa.
Da sauri ta karasa wajen sa ta na ce masa
“Kaga Asma’u can kwana hudu taki bude daki yanzu na buga ma ko motsin ta bana ji.”+
Da sauri yayi cikin gidan kofar yake duka amman sam ko motsi.
Da gudu yayi dakin sa ya bude wata durowa ya dauko dayan key din
Fita yayi da sauri yana budewa yaga ta kwance akan sallaya tana fitar da numfashi a hankali.
Dago ta yayi yaga jkin ta duk a sake yake.
Da gudu ya dauke ta ya nufi mota da ita.
Asibiti yayi da ita da gudun gaske. kafin ya karasa ya kira Sabir ya fada masa gashi nan tare da Asma’u.
Yana karasa wa aka kawo gado aka dauke ta kai aka yi wani daki da ita.
Ruwa Sabir ya fara saka mata sannan ya fara duba mai ke damun ta.
Ya gano har da rashin cin abinci sannan kuma jinin ta ya hau.
Ya tabbata zuwan Aslam ne ya sata a wannan hali.
Shi kan sa yasan Asma’u na mugun son Aslam.
Dan ta sha fada masa. Sosai ya tausayawa mata dan ba karamin jin jiki take ba.
Aslam dake can kwance shima ya ce da Mami yana son ya koma gida.
Mami cewa tayi ya bari jikin sa ya kara kwari dan ko tafi sai da kyar yake taka kafar tashi.
Rigima ya sawa Mami dole shi sai ya tafi.
Da kyar ya bari ya kara kwana biyu, dan washe gari Buhari yana tafiya massalaci ya mike ya tafi gidan sa.
Motar sa ya dauka ya dau hanyar Abuja, duk da jikin sa ba kwari.
Tafiya yake yana tunanin halin da yake ciki.
Wai shine zai rasa Asma’u. Hawaye ne ke zuba a idon sa.
Dai dai zai shiga Abuja motar ya kwace daga hannun sa yayi cikin jeji.
Asma’u kuwa tana kwance. jiki dai yaki yayiyu.
Sam jiki ba samun sauki duk maganin da take sha.
A gaskiya tasan tana kaunar Aslam kauna kuwa ba ta taba dainawa.
Tana kwancen nan ba wanda take son ta gani inba Aslam ba.
Kuka kam ita kadai tai tayi. Ta tabbata a yanzu tai rashin Aslam ba a da ba.
Bikin ta da ya rage kwana biyar.
Ba dan taji sauki ba aka bata sallama sai dan bikin ta da ya karato.
Har gida aka kira akai mata maj lallai da gyaran kai.
Rama kuwa ta kara ramewa tayi fari da ita.
Ba abinda take iya ci. Da ta zauna ita kadai sai kuka.
Zainab duk tai rabon katin bikin nata.
Ita dai komai da akeyi nata ido ne.
A bangaren Aslam kuwa Buhari na dawowa bai ga Aslam ba ya tafi gida.
Motar sa yaga ya dauka nan da nan ya kira Momy ya sanar da ita Aslam ya taho.
Haka ma ya kira ya sanar da Mami. Addu’a Mami tai masa Allah yakai sa lafiya.
STORY CONTINUES BELOW

Momy kuwa tun karfe biyu take zuba idon ganin Aslam amman bata ganshi ba.
Hankalin ta ne ya tashi. Can kuma sai ga sshi an kira ta da wayar sa wai yana asibiti.
Asibitin taje a lokacin aka fito dashi daga emergency aka tafi dashi inda za’a bashi daki.
Gun su tayi aka basu daki sannan likita ya kira ta.
Bayanin abinda ya same shi yai mata cewar ya bugu ne sosai a bayan sa. Sai yan raunika da ya dan daddauje.
Takardar magunguna ya bata ta amsa ta tafi ta bayar aka siyo mata.
Lokacin da Momy ta buga waya tana fadawa Buhari abinda ya faru Suna tare da Sabir.
Sosai Sabir ya tausaya masa. Haka su ka rabu jikin Sabir a sanyaye.
Tunani kuwa har ya rasa wane iri zai yi.
A ransa kuwa cewa yake yanzu yana ji yana gani zai raba farin cikin mutun biyu.
Ya tabbata duk son juna su ke jefa su a halin da suke ciki.
In har ya auri Asma’u yasan ya raba ta da farin cikin ta kuma Aslam ma bai da sauran farin ciki.
Sai yanzu yake tunani anya da Aslam yana cikin haiyacin sa ya juyawa Asma’u baya
Gaskiya da kamar wuya. Dan ya gano irin son da yake mata zai iya rasa rayuwar sa.
Haka ya koma gida duk baida sukuni.
A bangaren Aslam ma yana farkawa ya farai wa Momy kukan wai dan Allah ta taimaka a bashi Asma’u.
Momy kam Mamaki ta dinga yi saboda sai da ta fada masa kar ya soma sawa ransa abinda ya riga da yai masa nisa.
Da bata bashi amsa ba haka ya dinga kuka sai kace karamin yaro.
Ganin numfashin sa na neman daukewa yasa ta ce, yayi hakuri za tai san yadda zatai.
Duk da haka bai samu sukuni ba. shi dai ba wacce yake son gani sai Asma’u.
Momy kam bata fadawa Mami abinda ya faru da Aslam ba.
Kuma sai da ta hori Buhari da shima kada ya sanar da ita.
Ita tunanin ta ma rashin zuwan ta bikin.
Sai Allah yasa kuma ana jibi kamu aka sallamo Aslam daga asibiti.
A gida ta barshi da Dady kan cewa jibi zata dawo.
Haka Momy ta tafi tana tausayawa dan ta.
Sai ta tuna lokacin da take cewa sai ya auri Asma’u amman yaki yac”e sai Preety zai aura amman shine har da suma gashi kuma yanzu ya dawo da son ta.
Bangaren Su Mommah pretty kuwa ba karamin tashin hankali Ta shiga ba.
Ganin Pretty har wata hudu ba ita ba labarin ta.
Gashi ko waya bata yi nan fa suka hau bada cigiyar ta.
Amman abin ko alamar nasara babu.
Wata kanwar Mommah ce ta ce, a dage da addu’a Allah bayyana ta
To An dauki wata ana ta addu’a da sadaka amman shiru.
Da farko Mommah ma cewa tayi ita bata ga abinda addu’ar keyi ba.
Kanwarta ce, ta ce, ai addu’a sai a hankali a cigaba da yi har Allah y amsa.
Haka aka kara kaimi wata rana kamar daga sama sai ga pretty ta dawo da yaro a baya.
Duk ta rame tayi baki sai wani wari take fitar wa.
Tana ganin Mommahn ta tasa kuka. Ta fada jikin ta.
Mommah ce ta daga ta tana toshe hanci,
“Daga ina?”
Ta tambaye ta. Pretty ta ce,
“Mommah ruwa.”
Ruwa ta dauko ta bata ta kai ta bangaren ta ta ce tai wanka.
Mommah ta rike ta ce, baza ta tafi ba dan tsoro take ji.
Zama Mommah tayi ta shiga bandaki tai wanka.
Tana fitowa tai wa dan ta wanka, Mommah ce tasa a kawo musu abinci.
Nan aka cika dakin da abinci kala kala. Tin da ta fara cin abinci take turashi kamar wacce aka ce za a kwace mata.
Mommah ce ta ce taci a hankali, amman ina haka yaron ta da bai fi wata biyu ba ta dinga cusa masa abinci.
Tana gamawa suka zube a falo sai bacci.
Ido Mommah ta zuba masu tana zubar da hawaye.
Ganin yadda tayi baki, ta rame, ga yaro ko a ina ta samo shi.
Bacci sosai tayi dan har akai magariba tana bacci.
Sai da Dady ya dawo suka shiiga da Mommah ce ta same ta tana zaune, tana bawa danta nono.
Tana ganin Dadyn ta ta mike. Dady ne ya karasa ya amshi yaron hannun ta.
Magana yai mata amman da ta bude baki zata bashi amsa dai ta kasa magana.
Har kuka tayi dan jin ta kasa magana. Dady na ganin haka ya samo malami yai masa bayani.
Addu’a aka kara mikewa da ita da rokan Allah.
Cikin hukuncin Allah sai ga Preety na magana.
Anan ne take fadawa Dady duk abinda tayi da raba Aslam da Asma’u da bin malaman da take.
Har da auren da sukai da boka wannan yaro kuma dan ta ne da boka,
Bata taba zaton zata kubce daga wajen boka ba.
Sai rana daya ta ganta ta samu hanya har ta fito.
Bara tayi sannan ta samu na mota. Da kyar wata motar koso tumakai ta dauko ta.
Acikin wajen da tunakrn suke ta zauna duk da wajen kashi da fitsarin su ne.
Da haka suka karaso har kano aka sauke ta.
Da kyar ta samu ta karaso Abuja. Take fada musu a kafa ta karaso gida.
Jikin ta kuwa yayi wani iri kamar konuwa ga kaikayi.
Asibiti Dady ya fara kkai ta amman ina abin ba na wasa bane.
Da aka basu wasu gwaje gwaje aka gano tana dauke da cutar kanjamau.
Dady sosai ya razana. Preety kuwa kuka ta dinga yi tana dana sanin abinda ya faru.
Haka suka koma gida bayan an basu ranar da zasu na zuwa ganin likita da amsar magani.
Sosai Pretty ta razana da rayuwar duniyar nan, Ganin yadda take da amman yanzu ji yadda ta koma.
Ji dan da take riki dan shege, kuma ma na boka wai.
Haka nan ita ce ke dauke da kanjamau, yanzu wa zai aure ta.
Lallai *Duniya abar tsoro*
Yau ta kama kamu Asma’u ansha lalle da gyaran kai.
Duk da a kwance take sosai dan yanzu haka ma wani irin ciwon kai da zazzabi ke damun ta.
Tana kwance Zainab ta shigo da mai kwalliya ta ce,
“Asma’u tashi mai kwalliyar tazo.”
Da kyar ta iya mikewa idon ta jajir ta shiga bayi. Kasa sakawa jikin ta ruwa tayi sboda sanyin da take ji.
Fitowa tayi ta saka kayan da zata amfani dasu. zama tayi aka farai mata kwalliya.
Yar kadan akai mata amman ba karamin kyau tayi ba.
Ana cikin mata dauri Nusaiba ta kira ta. Dagawa tayi murya a sanyaye ta ce,
“Amarya”
Dariya Nusaiba tayi ta ce,
“Amare dai. Ya kunyi kamun ne, nifa har na gama shiri fita kawai zanyi. Yanzu Uncle Sabir ya kira ni wai ya muka tsara dinner nace ai ni ke na barwa komai.”
“Uhmm kema dai. Ni ba wata dinner da zan yi. Yazo nan kawai.”
Nusaiba tace,
“Ke kin isa ma. Kinji ana jira na bari naje mayi waya anjima.”
Ta katse wayar. Kallo ta bi wayar da shi ta ce,
“Oh wai wannan ce kishiya ta. Ita sai murnar bikin take yi.”
Maryam ce ta kira ta. Ta ce,
“Anty kiyi hakuri sai gobe zan taho yau zan tsaya wajen kamun Nusaiba. Jibi wai za ai dinner.”
Asma’u tace,
“Nifa ba wata dinner da zanyi.”
Shiru Maryam tayi a ranta tana tunani ko Asma’u bata son a hada musu dinner su biyu ne.
Sallama sukai tayi wajen Momyn ta tana fada mata gwara kowa yayi event din sa kar a wani hada.
Haka kuwa akai dan Mamahn Sabir ma haka tace kowa yai nasa.
A wajen Kamu kuwa Asma’u sai rawar sanyi take ga ciwon kai.
Anyi hotuna da kawayen su da yan uwan Dady da Mami.
Inda kafin a tashi jikin Asma’u yayi zafi kamar wuta.
Nan da nan Momy tasa aka maida ita gida. Ciwo sosai ta kwanta.
Washe gari akai Monday’s even Amman Asma’u da kyar ta iya zuwa.
Asabar dinner amma ranar a kwance sosai Asma’u take dan har asibiti aka tafi da ita.
Riketa sukai suka bata gado ana mata karin ruwa. Dinner dai da ba ayi ba kenan.
Rannar lahadi da safe aka daura auren Asma’u duk da tana asibiti lokaci nayi taji wata faduwar gaba.
Kuka ta sawa Momy dake wajen ta.
Momy sai lallashi take yi. Ba wanda yazo asibiti a ranar sai Zainab.
Shima abinci ta kawo fuskar ta dauke da fara’a sai tsokanar Asma’u take wai ta kwanatr da hankalin ta ta samu abinda take so ta mike.
Kiran da Mami ke mata yasa ta mike ta tafi ba tare da ta cigaba da tsokanar Asma’u ba.
Asma’u kam zuciyar ta ta gama karaya ta rasa Yaa Aslam kenan.
Da dare aka sallamo su gida suka nufa dan gidan ma har ya rage jama’a.
STORY CONTINUES BELOW

Dakin ta aka kai ta. tana kwance akan gado duk ranta a bace.
Zainab ce ta shigo ta ajiye roba sai karamin towel a gefe. Saboda jikin ta yai zafi za a fan sa mata ruwa.
Kai ta dauke ta lumshe idon ta. can taji an bude dakin. A hanakli taji ana taciya har aka karaso bakkin gado.
Bata san waye ba dan haka ta kara gyara kwanciyya. Roba taji an dauka an tsoma towel a ciki.
Ji tayi an tada ta zaune, ana cire mata kayan dake jikin ta.
Karamin wandon dake jikin ta kawai aka bari. Ido ta kara lumshewa. Saboda bata son bude su fan yadda suke mata zafi.
Jin an soma goga mata towel ta ajiye wata uwar ajiyar zuciya.
Ji tayi ana ta goga mata ruwa a jikin.
Shiru tayi abu daya taji shine, an fi goga mata a kirjin ta. Duk da haka batai gigin bude ido ba.
Can kuma sai taji kamar kamshin Yaa Aslam amman kuma sai ta tuna baya garin ma.
jini shirun yai yawa yasa ta a bude idon ta a hankali. Waza ta gani?
Yaa Aslam ta gani durkushe a gaban ta.
Ido ta zaro ta mike da sauri. Murmushi ya saki.
Bandaki ta shiga da gudu tana dafe da kirjin ta.
Ta jima a bandakin tana kukan da ta rasa dalilin name ne.
Sannan kuma tana mamakin taya Yaa Aslam ya shigo har ya ke shafa mata ruwa.
Ta jima a bandakin tana kuka ita kadai dan har sai da taji Zainab ta shigo tana kiranta.
Fitowa tayi daure da towel tana rawar sanyi. Dan wani zazzabi ne ya kara ta yar mata.
Kayan bacci ta fito ta saka. Har ta kwanta Zainab ta ce, taje falo ana neman ta.
Hijab ta dauka ta saka ta mike ta fita a hankali kirjin tane bugawa.
Falo ta fito jiki a sanyaye dan wani zazzabi take kara ji. Kan ta kuwa kamar zai rabe gida biyu.
Ta shiga falo taga Mami da Momy sai Uncle Habu (kanin Dady) sai Yaa Buhari da Sir Sabir. Taji dadi da bata Aslam a dakin ba.
Dukkan su murmushi ne akan fuskar su sai hira suke.
Kirjin ta ne ya buga ta ce,
“Allah yasa ba cewa za’ai na fito mu tafi ba.”
Karasa wa falon tayi ta zauna a gefen Uncle Habu.
Mutanen dakin ta gaisar daya bayan daya sukai mata sannu.
Kasa tayi dakai. Uncle Habu ne yai gyaran murya ya ce,
“Alhamdulilah Asma’u yau Allah ya nuna mana ranar Auren ki. Muna fatan zaki zama mace ta gari a wajen mijin ta. Kafin nan Asma’u. Asma’u duk abinda ya faru gareki ki dauka taki kalar Kaddara ce.”
Yai shiru, sannan ya ce,
” Auren ki dai bai dauru da Sabir ba.”
Dagowa tai da sauri ta kalli Uncle Habu sannan ta kalli Sir Sabir.
Murmushi ya sakar mata. Uncle Habu yacigaba da magana,
“Yau a wajen daurin aure anzo daura auren ku Sabir ya dakatar ya ce, a daura auren ki da yayan ki Aslam.”
Nan ma da sauri Asma’u ta dago tana kallon Sabir tana girgiza kai.
Murmushi ya sakar mata, yana mai girgiza mata kai ganin hawaye na shirin fitowa daga idon ta.
Uncle ne ya cigaba da magana ya ce,
“Ko da na tambaya akan me za’a fasa da shi sai ya kawon dalilan sa kamar haka:- Sabir ya ce, Uncle ina son Asma’u amman nafi son samuwar farin cikin ta. dole na hakura da ita tunda suna son juna su ita da Yaa Aslam. Dan ciwon da Aslam ya kwanta ma akan tane, haka ma kema kina son sa.”
Kai Asma’u ta fara girgizawa, Uncle yace, haka
“Haka sabir yacigaba da bani dal’lan sa. Ya ce, Na yadda Yaa Aslam na son ta kuma in na aure ta mutum biyu zasu rasa farin cikin su. In ni na hakura ni kadai ne zan ji ba dadi kuma nima na lokaci ne tinda na samu wacce ke sona tsakani da Allah. Nagodewa Asma’u dan ita tai min wannan gatan bazan taba mantawa da ita ba. Ina son Asma’u amman na hakura da ita Allah bata zaman lafiya da mijin ta.”
Kukan da Asma’u take boyewa shine ya fito fili ta fashe da kuka.
Zainab da shigowar ta kenan ta karaso tana lallashin ta.
Uncle ya ce,
“Ki daina kuka ki godewa Allah. Ina miki fatan Alheri Allah ya baki zaman lafiya. Ina farin ciki yau burin Yaya Suleiman ya cika. To Allah ya tabbatar da alheri. Ki kula da mijin ki. Allah miki Albarka.”
Ya mike ya fita. Mikewa Momy da Mami sukai suka fita.
Haka ma Yaa Buhari ya mike ya fita, bin bayan sa Zainab tayi ya rage daga Asma’u sai Sabir.
Mikewa yayi ya karaso gefen ta. Ya ce,
“Haba Husunah mene na kuka. Ki godewa Allah da ya sa na gane irin son da Aslam yake miki na tabbata Aslam na kaunar ki fiye da yadda nake kaunar ki, akwai dalili mai karfi da ya hana shi auren ki a baya zai iya zama ko bayin kan sa bane.”
Dagowa tayi idon ta jajir kamar gauta ta ce,
“Ni na fada maka yanzu ina son sane, bana son sa. Bana son sa sam. meyasa zakai min haka Sir. Yaa Aslam ba sona yake ba. Mutumin da yaki ni me ya dawo dashi gare ni……”
Sai kuma ta fashe da kuka. Sabir ya ce,
“A’ah Asma’u kar zuciyar ki ta dauki Aslam da wannan tunanin ki yadda da Aslam. Aslam na son ki. Aslam na kaunar ki, ni na yadda kuma nasan zaki ji dadi da Aslam amman dan Allah ki daina cewa bakya son sa. Nasan kema kina son sa. Ki amshi kaddara da Alalh ya saukar akan ku. Baki san me gaba zai faru ba. Nagode miki Asma’u da kika zaba min abokiyar rayuwa. Yau an kawo min Nusaiba daki na kuma duk a dalilin ki nagode.”
Ya mike ya fita. Kallo ta bishi da shi. Kuka ne ya kwace mata ta kifa kanta a kan kujera tana ta sharar kwalla.
Da kyar ta mike tayi daki tana wani irin kuka. Kan ta kuwa ko ya ta motsa ji take kamar zai fashe dan azaba ko wuyanta bata son motsa shi.
A haka Zainab ta same ta ta zata ma bacci take.
Shirin kwanciyya tayi ta kwanta da danta. Can cikin dare Zazzabi ya tada Asma’u sai kuka take.
A daren suka kara tafiya asibiti ba shiri.