RAYUWAR ASMAU CHAPTER 14
lokaci kadan ta fita a haiyacin ta. Momy da Zainab suna waje ciki kuma likitoci ne akan ta.
Aslam kuwa yana gefe ya rasa abinda yake masa dadi.
Sam sam baya son ganin ta a irin wannan halin bama da ya dauko ta zazzabin da ke jikin ta yai zafi sosai.
Ruwa suka juna mata bayan sun mata allurai.
Bacci ne ya dauke ta amman da ka kalle ta zaka san ba baccin dadi bane.
Duk ta rame ta dada haske. Idon ta ya zurma.
Sosai Momy ke tausayawa Asma’u ita bata so ma canjin nan da akai ba.
Taso su bar ta wajen Sabir din ta samu sabon farin ciki.
Tabbas in har Asma’u bata son Aslam a yanzu ita ta dauki alkawarin sashi ya sake ta.
Aslam ma ya kasa zaune bare tsaye yana gefen gadon ta.
Da ka ce ya tafi gida ma cewa yayi shi zai kwana da ita.
Haka aka barshi a gun ta. Ranar bai kwanta ba kallon Asma’u ya tsaya yi sai kace sabuwar hallitta.
Yana son Asma’u yana kaunar ta yasan da bai same ta ba da yayi babbar asara.
Ba abinda zai ce da Sabir sai godiya dan yai masa abu da bazai taba mantawa da shi ba.
Haka suka kwana washe gari yana dawowa daga sallar asuba yaga ta farka.
Karasawa yayi da sauri yana kamata. Dago kanta da tayi taga shine yasa ta ture hannun sa tana watsa masa wani irin kallo.
Kallon mamaki ya tsaya yana mata. Kai ta dauke daga kallon sa ta zare ruwan dake shiga jikin ta.
Mikewa tayi sai tayo baya zata fadi. Da sauri ya tare ta ta fada jikin sa.
Kwantar da ita yayi ya shiga bayi ya hada mata ruwan wanka da na alwala.
Wajen ta yayo zai kamata ta aika masa da wani kallo.
Bai karasa ba bare ya taba ta. A hankali ta taka ta shiga bandaki.
Wanka tai tai alwala tai brush sannan ta fito.
Sallah tayi ta koma kan gadonta kwanta ta juya masa baya.
Haka suka cigaba da zama a dakin. Shi dan shakkar yai mata magana.
Har karfe takwas sai ga Zainab da Momy nan sun kawo msu abinci.
To sai a lokacin ya samu yaji muryar ta. Har da ganin murmushin ta mai kayatar da shi.
A lokacin in yai mata magana tana bashi amsa badan ransa yaso ba, sai dan a gaban Momy ne kawai.
Haka suka yi, Asma’u ce ta matsa su koma gida bata san zaman asibiti duk da a office tinda suke zaune.
Haka suka koma gida jikin ta ba kwari.
A ranar Zainab ta koma gidan ta. Momy ma ta fara shirin tafiya.
Da Mami ta ce, su tafi da Asma’u Momy ce ta ce Aah a barta ta kara samun karfin jikin ta.
Mami ma tana son zama da yar ta ko dan ta ga ya jikin ta zai kaya.
Haka Momy ta tafi amman Aslam ya ce ba inda zaije.
Asma’u na kwance a dakin aka budo kofar daki.
Mikewa tayi da sauri ganin Aslam ne. Fuska ta hade ta dauke kai.
STORY CONTINUES BELOW

Zama yayi a gefen gadon da take zaune.
Zai yi magana kenan ta daga masa hannu. Tace.,
“Dan Allah ka kyale ni. Ka barni kar ka kara min kalaman yaudarar da ka saba.”
“Haba Husnah nine mayaudari?”
Ya tambaye ta yana nuna kansa.
“Eh kai ne!”
Ta fada a harzuke.
Sannan ta ce,
“Kai ne Yaa Aslam ka azabtar da zuciya ta. Dan Allah ka barni na huta. Dan Allah,”
Ta mike zata shiga bayi kenan ya kamo hannun ta ta fado jikin sa,
Makale ya yayi da kirjin sa. Duk yadda taso ta zame daga rikon da yai mata ta kasa.
Fuskar ta yadago yana son hada ido da ita.
Gane abinda yake sonyi yasa tayi saurin lumshe idon ta.
Murmushi ya saki ya hade bakin su waje daya, tana kokarin gwace bakin ta ya kara janyo ta jikin sa.
Hannnun sa ya daura akan kirjin ta yana wasa da su.
Duk yadda taso ta kwance ya hanata taa har ta hakura sai dai hawaye dake ambaliyya a idon ta. Jikin ta kuwa in banda rawa ba abinda yake saboda tsabar tsoro.
Sai da yaji ya dawo nustuwar sa sannan ya zare bakin sa ya rumgime ta tsamm a jikin ta.
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa. Dago fuskar ta yayi yana lashe mata hawaye da harshen sa.
Cikin zafin nama ta kwace jikin ta da sauri tayi cikin bandaki.
Bandakin ya bi da kallo yana wani murmushi.
Bayan sati daya
Alhamdulilah jikin Asma’u yayi sauki sai abinda ba a rasa ba.
(Nace abinda ake nema ya samu. Dole a watsa ke.)
A cikin sati dayan nan kullun tana daki a rufe dan ita sam bata son Yaa Aslam yazo wajen ta.
A ranta tana son sa amman kuma da taga fuskarta sai ta tuna abin da yai mata da irin wahalar da ta sha.
Gashi dai ta auri burin ranta amman kuma kullun cikin damuwa take.
Mami na kula da yadda take rufe daki duk dan saboda Aslam.
Aslam kuwa kullum in ya taba kofar ta yaji a rufe sai dai ya girgiza kai kawai.
Yau ma kamar kullum tana daki kwance akan gado tana kallon pictures din Dady taji ana mata knocking.
Sanye take da dogon wando sai yar riga, kanta ba dankwali ta yi parking din kanta ya sauko har gadon bayanta.
Sai tashin kamshi take, duk da in ka kalli fuskar ta zaka san tana cikin damuwa hakan bai sa kyan ta bayyana ba.
Mikewa tayi ta bude dan ta zaci Mami ce, tana budewa sukai ido hudu dashi.
Yana tsaye sanya da farar shadda ya kara kyau jikin sa ya murmure.
Juyawa tayi zata koma ya janyo ta ta fada jikin sa.
Kamshin turaren sa ya doki hancin ta. Idon ta ta lumshe dan tana son kamshin Yaa Aslam.
Kanta ya kwantar a kirjin sa. Zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri sanadin jin ta da yayi a jikin ta.
Idon Asma’u a lumshe, Kamar an tsikare ta. Ta mike da sauri, tana hararar sa.
Murmushi yayi. Hannun ta ta kwace zata koma.
Ya ce,
“Haba Baby love, kizo kinyi baki a akasa.”
Ya fada yana kuyawa ya nufi sauka. Kallo ta bisa da shi ta saki tsaki ta shige daki.
After dress ta saka ta dan yafa mayafin ta sauka.
Tana daga stair ta hango Yaa Aslam gefen sa Sir Sabir suna magana.
Kai ta dauke sai kuma ta ga Nusaiba. Da sauri ta karasa saukowa tana murmushi.
A gefen Nusaiba ta zauna tana kamo hannun ta.
Murnushi Nusaiba tayi ta ce,
“Ah ai jiki yai sauki Sis.”
Murmushi tayi suka gaisa. Kallon Sir Sabir tayi ta dan dauke kai ta ce,
“Ina yini Sir?”
Murmushi yayi ya ce,
“Lpy Husnah! Ya jikin?”
Aslam ne ya ce,
“Jiki ya warke sai abinda ba a rasa ba.”
Suna zaune Mami ta shigo da alama ma daga unguwa take.
Gaisawa sukai ta haye sama. Mai aiki ta saka aka kawo musu lemo da ruwa.
Tinda ta sauko ya tsare ta da ido duk wani motsin ta akan idon sa yake.
In ta dago ta kalle shi sai ya kashe mata ido daya.
Da ta harare shi zai sakar mata murmushi.
Tana lura da Sir Sabir shima yadda suke yar kallo shi da Nusiaba.
Baki ta tabe, ta kama hannun Nusaiba sukai sama
A sama ma tsiya Nusaiba ta dinga mata kan gara ta tare tinda ttaji sauki.
Asma’u dai sai dai tai murmushi. Sun jima a gidan dan sai da sukai magariba sannan suka tafi.
Har bakin mota suka rakasu suna musu bankwana.
Nusaiba na rokar Aslam kan kafin su tafi ya kawo mata Asma’u.
Suna tafiya ta juya zata koma ciki. Da sauri Yaa Aslam ya kamo hannun ta.
Juyowa tayi ta dan harare shi. Murmushi yayi ya ja hannun ta sukai garden.
Inda suka saba zama ya zaunar da ita.
Ido ta lumshe tana tuna lokacin da sukai rayuwa a garden.
Rayuwar da bazata taba mantawa ba. Wata ajiyar zuciya ta saukar.
Aslam dake zaune yana kallon ta ya mike ya durkusa a gaban ta.”Kina Ina Fateema kibiya. A gaakiya ina yaba hankalin ki. Da kokarin ki. Allah ubangiji ya kara basira da zakin hannu ni Maryam ina son ki
Mikewa yayi ya durkusa a gaban ta. Hannun sa ya daura a kan cinyar ta
Da sauri ta bude idon ta. Kallon sa ta tsaya yi kamar yadda shima ya kasa dauke idon sa daga kallon ta.
Hannun ta ya kamo ya fara murzawa a hankali.
Ya kira sunan ta a hankali. Ya ce,
“Husnah ki yadda dani wallahi ina son ki. Duk abunda ya faru ki manta da shi.”+
Ido ta rufe dan ita ta kasa mantawa da abinda Yaa Aslam yai mata.
To wai mema tai masa da har ya guje ta bayan yasan bazata ta iya rayuwa ba shi ba.
Bayan yasan duk farin cikin ta yana gare sa.
Bayan yasan shine ruhinta. Shine sirin ta daga mahaifinta sai Mami sai Shi da Yaa Buhari sune kadai gatan ta.
Amman shine ya juya mata baya. Ko yasan halin da ta shiga.
Ko yasan irin jinyar da tasha. Ko yasan irin azabar da take sha a duk sanda lokacin kiran sa ko turo mata da sako yai bai turo mata ba.
Duk shekarun nan da suka wuce in dai zata kwanata bacci sai tai kuka. Dan ya riga da ya sabar mata shine mutun na karshe da yake saka ta bacci da kishoshin Annabawa da sahanabai.
Amman duk a lokaci daya ya rushe duk abinda ke tsakanin su.
Tabbas ya dawo gareta ne dan ya raina mata hankali.
Ina dayar matar tasa. Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.
Ya dawo gare ta ne dan yasan da shi kadai zata iya rayuwar aure.
Ya dawo gare ta ne dan yasan duk lagon da zai amshi zuciyar ta.
Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.
To yayi karya duk son da take masa baza taba sakar masa ba.
Inda da ya nuna baya sona nima yanzu na hakura da shi.
Zan zauna da koma waye amman banda da Yaa Aslam.
Bazan zauna dashi ba Yaa Aslam ya wahalar da ni.
Tana tuna irin hirar rakin su da yakan ce bazai taba rabuwa da ita ba.
A lokacin in ta kawo misalin abinda zai iya raba su har haushi yake ji.
Amman lokaci daya ya rabu da ita. Ta kan tina irin alkawarin da yake mata da irin son da yake mata to duk suna ina.
Lallai in ta kara yadda da Yaa Aslam zai kara yaudarar ta ne.
Tasan tana son Yaa Aslam amman zata danne zuciyar ta ta nuna masa ita yanzu ba son sa take ba.
Sai ta kwatar wa kanta yanci a gun sa.
Idon ta ta bude jajir da su. Aslam dake rike da hannun ta ya zuba mata ido ya kara bude idon sa ganin yadda idon ta ya kada yai jajir.
Kuka ta fashe masa da shi. Nan da nan ya hau lallashi amman sam taki yin shiru.
Sai da kyar ta yi shiru nan ma ta mike ta yi cikin gida tana sharar hawaye.
Mami dake falo ta ga wucewar ta. Kai kawai ta girgiza.
Dan tasan Asma’u na son Aslam. Tana lura da yadda take rufe daki kuma duk tasan akan sa ne.
To ai dai jikin ta yai sauki dan haka tazo su shirya su tafi dan ta fara tausayawa Aslam. Bama da tasan kafiyar ta.
Tana zaune Aslam ya shigo shima duk yanayin sa ya sauya.
Kallon sa Mami tayi ta ce,
“Ya dai?”
STORY CONTINUES BELOW

Kai ya dan sosa ya ce,
“Ba komai!”
Mami ta ce,
“Shikenan ka fara shirin tafiyar ku. Tinda jikin nata yai sauki nan da jibi sai ku tafi ko?”
“To Mami Allah kaimu.”
Ya fada yana mikewa.
Sama ya hau Mami ta bisa da kallo.
Asma’u ta shiga daki ta shiga bandaki ta watsa ruwa tai alwala.
Tana fitowa ta shafa mai tai salla. Tana kan sallaya Mami ta shiga dakin da sallama.
Dagowa tayi ta amsa tana gyara zama. Zama Mami tayi agefen gadon ta ta ce,
“Asma”u jikin ki yai sauki dan haka ki hada kayan ki nan da jibi sai ku tafi ko?”
Wata faduwar gaba ce ta zowa Asma’u dan har sai da ta dafe kirji jin kamar zai fadi.
Dagowa tayi ta ce,
“Mami Allah da saura na.”
Mami ta ce,
“Asma’u ba inda yafi dakin mijin ki dadi da gatan ki. Ki tafi ke karasa warke acan. Allah baki lafiya. Allah miki albarka.”
Kuka Asma’u ta saka ta ce,
“Mami bana son na tafi na barki. Mami na rasa Dady kema kada na rasa ki Mami ni a nan zan zauna.”
Murmushi Mami rayi ta ce,
“Haba Husnan Dady. Kinsan sai kwana yayi ake tafiya. Kuma kinsan Dadyn ki bai da wani buri da ya wuce ya ganki a gidan Yayan ki matsayin matar aure. To ki daure ko dan Dadyn ki ki zauna lafiya a gidan mijin ki. ni kuma ki kwantar da hankalin ki zan na zuwa ganin ki akai akai. Kuma ga Yaa Fati nan ma. Ki daina kuka in ba so kike hankali na ya tashi ba.”
Da sauri ta hau goge hawayen fuskar ta.
Bangaren Sabir da Nusaiba kuwa zaman lafiya suke sosai take kula da shi shima kuma so sai yake kula da ita.
Sai a yanzu yake jin son ta sosai a cikin jikin sa.
Perty kuwa tana can ta koma ga Allah yanzu Aslam take so ta gani ta roki gafarar sa
Tasan taci zalin Asma’u dan tasan soyayyar dake tsakanin su amman ta raba su.
Dole ta nemo Asma’u itama ta nemi gafarar ta
wannan dalilin ne yasa ta tafi kano dan neman inda Asma’u take.
Har gida Zainab ta zo jin Asma’u zata tafi.
Kayan gyaran jiki ta hado mata sosai, inda ta bata wasu ta ce ta tafi da su.
Haka ma Maimuna har gida tazo tai mata sallama.
Ana gobe zasu tafi suka je gidan Sabir. Gida ne mai kyau wanda aka zuba masa kayan more rayuwa kala kala.
Tinda suka je Nusiaba sai nan nan take da Asma’u duk Asma’u ta kasa sakin jiki saboda kallon da Aslam yake tsare ta dashi.
Shi yana mamakin Asma’u kamar ba ita ba.
Duk ta canja masa. Anya kuwa Asma’un sa ce wannan.
Shifa ko a gida baya ganin ta. Bare ya samu damar mata magana
To in ya ganta ma ya samu fuskar magana man.
Haka suka dan zauna sanna suka tafi gidan Mamah mahaifiyar Sabir.
Sosai Mamah tai mata nasihar zama da miji sanna ita ma ta hado mata kaya ta bata.
Gidan su Zainab suka je tayi wa mahaifiyar Zainab sallama.
Daga nan kuma suka koma gida
Duk tafiyar nan da suke kallo ne kawai nashi amman ya kasa koda mata magana.
A haka suka karasa gida ta debo kayan ta ta shige.
Sama ta hau ta ga Mami ta fito da akwati nan ta da na wajen Yaa Aslam da na wajen Sir Sabir da ya ce ya bar mata.
Zama Asma’u tayi ta ce,
“Mami na gaji. Sai kace ban saba fita ba.”
Mami ta dago ta kalle ta ce,
“Kinsan jikin naki ne. Ya kamata kije asibiti yau.”
STORY CONTINUES BELOW

“Eh sai anjima zan leka.”
Asma’u ta fada dai dai shigowar Sabir.
Mami ta kalle shi ta ce,
“Kaga masu dibar kaya a kasa ko?”
Kai ya gyada, Mami ta ce,
“Kaje kace su zo so dauki kayan an gama.”
Mikewa yayi ya fita. Mami ta ce,
“Tinda kince ke sai kayan Dady gasu can an saka miki su a mota.”
Murmushi Asma’u tayi ta ce
“Mami ba haka bane, kinga Dady dan kar ya daurawa kowa nauyi ya siyon kayan nan. Kuma kayan nan da kyan su, bayan haka masu tsada ne to me za a canja ayi dasu. Kuma naga su aje yayi Mami dan zaman duniya dai kawai wani ma neman wanda bai kai shi ba yake amman bai samu ba.”
“Haka ne! Kayan na da kyau masha Allah.”
Mami ta fada.
Suna zaune aka shigo aka kwashe duk kayan.
Sai a lokacin jikin Asma’u yai sanyi ganin da gaske dai tafiya zatai.
Daki ta mike ta shiga.
Daren ranar tare suka kwama da Mami tana tai mata nasiha akan aure. Asma’u ji take kmar tace ta fasa. Wwai da da bata da burin sai ta ganta a gidan Yaa aalma amman yanzu duk bata so
Washe gari da safe Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.
Tai wanka ta shirya cikin wata Farar atamfa wacce akai mata adon da ja da baki.
Simple make up tayi, ta saka jan mayafi da jan takalmi sai bakar jaka.
Sosai tayi kyau. Ba abinda tta dauka saboda komai nata an tafi mata dashi.
A falon sama ta samu Mami da Yaa Aslam wanda ya saka wata milk din shadda tai masa kyau.
Sai tashin kamshi yake yi. Yaa Buhari a gefen sa. Sai Zainab dake dakin Mami.
Gefen Mami tayi ta zauna. Yaa Buhari ya kalle ta ya ce,
“Ji ‘ya Malama tashi zakiyi dan yanzu zaku tafi.”
Baki ta turo ta dan harare shi. Daga kan da zatai sai taga Yaa Aslam ya zuba mata ido baki da hanci yana kallon ta.
Kai ta dauke ta kalli Mami ta ce,
“Mami ni kam in nace na fasa ai ya fasu ko?”
Kai Mami ta daga. Yaa Buhari yai dariya ya ce,
“Karya kike wallahi.”
Mami ta ce,
“Ku tashi ku tafi.”
Kwanciyya tayi akan kafar Mami. Zainab ta fito ta ce,
“A’ah me zan gani!”
Yaa Buhari ya ce,
“Eh man wallahi aka zan fitar da ke.”
Mikewa tayi ta fara zubar da hawaye. Murmushi Mami tayi ta ce,
“To mene na kuka. Haba Husnahn Dady ki daina kuka bayan ga Momyn ki can tana jiran zuwan ki.”
Kai tai kasa da shi amman hawaye ya kasa daina zuba.
Yaa Aslam kuwa kukan da take ji yake kamar yai me dan sam baya son kukan Asma’u.
Zainab ce ta kama ta ta ce,
“Haba Asma’u ki daina mana.”
Suka mike suka fita har da mami ta raka su compound sannan ta dawo.
Asma’u kuwa sai jikin ta ya kara sanyi na jin rabuwa dai zatai da gida
Sai da suka fita daga gida Aslam yaji Asma’u na kuka.
Motar yasa Buhari ya tsayar sannan ya koma gidan baya.
Jikin sa ya jata yana lalashi ta a hankali a hankali.
Sannu a hankali tayi shiru. Tana rasa dalilin da yasa in har tana tare da Yaa Aslan take jindadi a ranta. Ko taji ta samu relief.
A haka suka karasa airport ba tare da sun san anje ba. Har sai da su Yaa Buhari suka fita sannan yai musu knocking.
STORY CONTINUES BELOW

Dogowa sukai yai musu nuni da waje. Jikin ta ta kwace daga nashi ta fita da sauri.
Jakar ta ya dauka ya fita yana murmushi. Suna zuwa aka fara kiran su.
Ba jima ba suka tashi. Asma’u na hawaye dan sai Yaa Aslam ne ya tallabe ta yana lallashi har suka shiga jirgi.
A cikin jirgin ma jugum tayi tana kwance a kan kafadar sa.
Suna sauka har motar gida tazo daukar su.
Gida sukai. Asma’u duk sai taga gidan ya canja da ta jima bata je ba. Ba kamar da da ta samu hutu taje ba.
Amman yanzu a kalla tai shekara biyu zuwa uku ba tazo ba.
Suna fitowa Momy ta fito ta kama ta. Cikin gidan ta shige da ita aka bar Aslam da daukar jaka.
Sama ta nufa da ita tana. Dakin guda aka kai ta.
Ruwan wanka Momy ta hada mata sannan ta sauka.
Bandaki ta shiga. Kafin ta fito an jere mata kayan abinci.
Mai ta shafa ta saka wata bakar doguwar riga da ta gani akan gado.
Sallah tayi tana zaune akan sallaya ya shigo dakin.
Dagowa tayi ta kalle shi ta dauke kai. Sanye yake da wando three quarter daga alamu shima wankan yayi.
A gaban faranti da aka jero mata abinci ya zauna.
Ya ce,
“Bismillah”
Kai ta girgiza ta ce,
“Alhmdlh”
Murmushi yayi ya ce,
“Humm! Ai gwara ma kici domin nasan baki ci komai ba duk yinin yau ga idanunki duk sun kumbura saboda kuka”
Fuska ta bata ta ce,
“Wa kuma yace maka banci abunci ba”?
Kusa da ita ya matsa daf ya d’ora tsinin dogon hancinshi akan nata. Ajiyan zuciya ya sauke. Yana kallon ta ido cikin ido yace,
“Nasan Husnah d’ita fiye da yanda take zato. Idan tana fad’amin gaskiya ina ganewa idan kuma tana fad’amin karya ma ina ganewa. Dan haka kina sanin abinda zaki fada min. Oya So let’s eat, drink and…..”
Bai karasa fadar abinda xai fada ba ta ce,
“Me?”
Bai bata amsa ba sai kiss da yai mata a kumatu. Harshenta ta fito dashi a waje.
Ai kam Charaf Yaa Aslam yasashi a baki. D’an kokarin tureshi ta farayi ganin ya fara sarrafata yasa tai la’asar. Har cikin kwanyar kanta take jin kiss din da yakeyi mata. Sai daya gama da kanshi ya d’an ja da baya kad’an.
Kallon ta yayi da idon sa da sukai jajir ya ce,
“Now let’s eat”
Asma’u da jikin ta yai sanyi sosai tai kasa da Kanta ta dauki cokali ta fara cin abincin a hankali.
Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya bude dayan fulas din naman kazan ne a ciki. daukowa yyai ya mika mata. Amsa tayi tana ciki a hankali duk jikin ta a sake.
Lemo ya mik’a mata, cikin sanyin murya tace
“Na koshi.”
Cup d’in yai gefen bakin ta da shi. karba tayi ta kai bakin ta ta sha kad’an ta janye ta maida ta aje.
“Duka zaki shanye”
Yaa Aslam ya fad’a yana murmushi.
Hararar sa tayi ta ce,
“Haba dan Allah ni ina zan iya shanye wannan? Wallahi na koshi.”
Aslam yai murmushi ya ce,
“Kokartawa xakiyi ko in maki d’ore kamar yadda da nake miki.”
Kai ta dauke, tana hararra sa ta kasan ido.
Yau Kwata kwata sai take jin Yaa Aslam ya koma mata wani sabo daban. Ga shi tana kasa hana shi duk abinda yake mata.
Ba yanda ta iya illa ta sha kamar yanda yake so. Shima kai ya kafa yasha nashi. Tashi yayi ba tare dayace mata komai ba ya fara cire rigarshi. Idanu ta zubawa kirjinshi da kwanjunan hannunshi.
Murmushi Yaa Aslam yayi ya nufi wajen ta.
Duk’awa yayi da niyar daukar ta. Ta mike za tayi waje.
Kamota yayi ya dauketa ya direta kan gadon ya kura mata idanu. Cikin sanyin murya yace
“Kina sona Husnah?”
Banza tai masa kamar ba da ita yake ba.
Murmushi yayi, ya zura hannun shi ta cikin rigar ta yai kark’ashin bayanta.
Sannu a hankali ya fara d’age mata rigar jikin ta. Tana jinshi tai lamo kaman wadda batada rai. Kirjin ta sai dukkan uku uku yake
Tana son ta hana shi amman ta kasa.
Fuskan shi ya d’aura a kan nata ya fara gogo mata hancinshi. A hankali ya tallabota ya fara cire mata rigan. Tsotsan kunne ya fara yimata cikin natsuwa yana hura mata iska a ciki. Jin sanyin AC na ratsata ta ko ina na jikinta yasa ta farga batada riga.
Jawo Hijab din ta tayi ta rufe kirjinta. Ajiyan zuciya Aslan ya sauke. Kara matseta yayi da kirjinshi sosai. yana shafa bayanta a hankali hadi da mazaunanta.
Sanin zata iya guduwa a ko da yaushe yasa ya kara matsa ta a jikin sa.
Hannu ya d’ora akan gashin ta ya ‘dago fuskanta ya kaimata sumba a wuya, lips d’inshi ya tura cikin bakin ta a hankali ya fara tsotsawa yana zare bra dinta… Hannunshi ta rike gam. Chaan kuma ta saki ta zubawa sarautar Allah ido…
Tasan ita halak dinsa ce to amman kuma tana tuna abunda yai mata.
Tana can tunani taji ya fara wasa da ita sosai da sosai.
Sosai jikin ta ya fara rawa, Duk sun fita a cikin hayyacinsu daga ita har shi.
Hannun sa ta rike tana girgiza masa kanta. Ta ce
“Dan Allah ka daina Yaa Asl……”
“Shhhhhhhhhhh. Enough” ya fad’a yana k’ank’antar da murya chan k’asa ‘kasa.
Fuskantar ta juyar saboda ya matse ta ba damar tashi. ta fashe da wani irin kuka.
Kuka sosai takeyi. Ganin ya kasa shawo kanta yasa Aslam sakin ta yana maida numfashi yana ajiyan zuciya.
Da sauri ta mike ta saka kayan ta ta fice da sauri.
Yana kallon ta ya saki ajiyar zuciya ya gyara kwanciyya.
Tabbas yasan da duk abinda ya faru bai faru ba da yanzu yaga jinin sa a tare da Asma’u.
To amman ji yadda Asma’u ke gudun sa kamar dodo.
Asma’u da inda yaje gida suke tare kullum amman yanzu sai dai daga nesa.
Har gara yau ma ya samu damar zama kusa da ita har ya umarce abu tayi.
Yana son Asma’u so bana wasa ba. Amman ya rasa ta yadda zai nusar da ita ta yadda.
Asma’u na fita tayi dakin Momy, Momy na zaune suna waya da Mami tana fada musu sun sauka lafiya.
Asma’u na shiga ta ce,
“Ga ta nan ma.”
Ta mika mata wayar. Gaisawa sukai tai musu ya hanya.
Kan gadon Momy ta hau. Momy ta kalle ta ta ce,
“Kinci abincin ne?”
“Eh naci.”
Momy ta ce,
“Me kike bukata?”
“Ba komai!”
“To kwanta ki huta.”
Ta kwanta.
Yau kwanan su biyu a gidan Momy amman zai iya cewa rabon sa da Asma’u tin ranar da suka zo.
Kullum tana daki a rufe bata fitowa falo ko da fito da ta ji shi take komawa.
Ya zuba ido yaga Momy ta ce, su koma gidan su amman Momy tayi shiru.+
Haka ne yasa aka je aka share gidan a goge dan ya kagu ya tare.
Momy kuwa tana can tana shirya musu walima da za’ayi ne kafin su tare tinda ba wani biki akai ba.
Yau ya cire kunya ya ce zai fadawa Momy shi ta bashi Asma’u su tare.
Yana shigowa ya same ta akan kujera tana duba wasu takardu.
Yana zama ta mika masa wasu takardun. Amsa yayi yana dubawa.
Dagowa yayi yana kallon ta. Murmushi tai masa ta ce,
“Eh ai dole a hada maka walima Allah yayi Asma’u matar ka ce.”
Murmushi yayi ya koma gefen Momy ya kama hannun ta sai hawaye.
Kallon sa tayi ta girgiza masa kai. Ta ce,
“Mene na kuka?”
“Dole nai kuka Momy. Momy kina sona Allah ya biya miki bukatun Alheri Allah yasa ki kyakyawan karshe.”
“Ameen! Duk wannan addu’ar ta mece?”
“Momy kina sona da Asma’u kiga lokacin da nace bana son ta ke kika ce A’ah amman na ki sam. Wallahi Momy ban san me ya raba ni da Asma’u ba dan ban taba jin kin ta ba. Kullum da ita nake kwana nake tasho. Ina son Asma’u Momy.”
Asma’u da fitowar ta kenan taji yana maganar tai saurin komawa daki.
Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ga hawaye nan ta rasa hawayen me take yi.
Momy kuwa, hawayen sa ta share masa ta ce,
“Ai Allah zaka godewa da yada Asma’u taka ce, gashi har ka mallake ta.”
“Haka ne Momy ina gode masa a ko da yaushe. Kuma ina gode muku.”
Ya mike ya ce,
“Bari naje na fara rabo.”
Momy ta ce,
“A’ah sai na ji ta bakin ta tana son naka ne har yanzu ko aah.”
Dariya yayi Ya fice, yana cewa,
“Momy tsokana”
dariya Momy tayi dan a duniya tana son dan nan mata daya guda tilo. Duk farin cikin sa shi take fata.
Abinda ta dade bata gani a tare da shi ga shi yanzu ya dawo kullum farin ciki da annushuwa ne dauke a fuskar sa.
Tasan duk wannan bazai rasa nasaba da samun Asma’u da yayi bane.
Mikewa tayi ta yi sama. Dakin da Asma’u ta shiga.
A kwance ta same ta. Mikewa tayi tana gyara zama.
Zama tayi a gefen ta.
Ta ce,
“Asma’u kina son Aslam har yanxu ne?”
Shiru Asma’u tayi a aranta ta ce ko bana son Aslam ai ba zan taba fada miki ba Momy bare ina son sa.
Momy ta ce,
“Karkiji komai ki fada min.”
Kasa tayi da kai ta daga mata kai, murmushi Momy tayi, ta mika mata katin hannun ta.
Amsa tayi ta kalla. Murmushi tayi dan tasan Momy na son ta.
Dagowa tayi ta ce,
“Momy har wata hidima za’a kara.”
STORY CONTINUES BELOW

Kai Momy ta gyada ta ce,
“Auren da muka dade muna fata ba dole ba. Yau Allah ya nuna mana kowa yaxo ya taya ni farin ciki na hada ‘dana da ‘ya ta aure.”
Murmushi Asma’u tayi tai kasa da kai. Wai yanxu Momy sirikar tace.
Washe gari Aslam yai tafiya dan ya ce, shi zai je ya yo musu order kayan da zasu saka.
Tin ranar Asma’u bata kara ganin Aslam ba, kuma bata neme shi ba.
Shi kuwa yana can yana fama da rashin ta. Duk yadda yaso ya ji muryar ta baya samu, dan ko Momy ya kira ya ce a hada su da ta amsa bata magana wani lokacin ma kashewa take.
Murmushi yake dan shi, yasan yai wa Asma’u ba dai dai ba. Amman bari zai wanke laifin sa ne bari da su tare.
Cikin kwana biyu aka kara yiwa Asma’u gyara inda akai mata lalle da gyaran kai.
Sosai tayi kyau ta koma amaryar tata dai.
Yau ce ranar walimar da Momy ta hada a yau kuma zata tare a gidan ta.
Har su Zainab suna hanya, ita da Mami da Yaa Buhari.
Asma’u na ganin su ta rumgume su. Sai murmushi take.
Dakin ta ta ja Zainab tana dauke da Dadyn ta.
Tunda su zainab suka je take kallon ta ta ce,
“Ke Asma’u wannan kyan fa tin kafin ki tare ko dai har anyi wani abu ne.”
Duka Asma’u ta kai mata ta ce,
“Ai shi ba ruwan da.’
Dariya Zainab tayi ta ce,
“Ma gani dai.”
A ranar Yaa Aslam shima ya dira da kayan da ya taho masu da shi.
Yana ganin Buhari ya yi wajen sa, ya fe,
“Bro har kun zo.”
“Eh man kun taso mu.”
murmushi yayi ya ce,
“Wallahi Momy ce.”
Suka shiga ciki yana daukar akwatin hannun sa.
Dakin sa suka nufa shima.
Karfe hudu har an gamai mata kwalliya. Kyan da Asma’u tayi ba zai fadu ba.
Amman tayi kyau sosai. Ta saka wani Material Milk kala wanda akai mata ado da dark brown din material.
Ta dauki dark brown din takalmi da jaka, da mayafi.
Ta saka milk din fashion. Ruwan turare akai ma. Tayi kyau kamar ka sace ka gudu.
Kowa yayi kwalliyar sa cikin shiga mai kyau. Dan lokacin ma har Maryam ta zo ita ma.
Da yake a harabar gidan Momy za’ai har wajen ya cika da jama’a
Bangaren mata daban na maza ma daban.
Momy da kanta ta shiga dakin da aka shirya Asma’u ta kamo ta.
A falon da ta zaunar da ita. Aslam ta kira ya fito shima cikin wata milk shadda da akai mata aiki da dark brown din zare.
A takaice dai anko sukai kuma sosai sukai kyau.
Tinda ya fito ya daura idon sa akan Asma’u ya kasa daukewa.
Sai da Momy tai masa magana sannan ya kalle ta yana sosa keya.
Hannun Asma’u ta kama ta kamo hannun sa suka sauka kasa.
Mami dake zaune a kasa tana ganin su ita ma ta mike.
Momy da Mami su suka fitar da yayan su.
Har wajen zaman su suka kai su. Akai hotuna da kowa da kowa sannan aka ci aka koshi akai musu addu’ar zaman lafiya.
Duk wanda yaga Aslam da Asma’u yasan sun dace da juna. Dan suna kusan dibar kamanni da sai shi fari ne tas.
Ana kiran magariba aka tashi daga taron kowa yai cikin gida maza suka tafi massalaci dan da anyi isha’i za’a kai amarya gidan ta.
Suna shiga ta shige toilet dan yin alwala amman sai ta ga ba hali dan period din ta yazo.
Wanka kawai tayi ta fito. Momy ce ta shigo ta ce, tai sallah ga wani ruwan turare nan tai wanka dashi.
Da toh ta amsa mata kawai. Bayan mintina kadan Momy ta dawo dakin.
Ruwan wanka ta hada mata da wani hadin turare, mikewa Asma’u tayi tai wanka.
Tana fitowa Momy ta kawo mata garwashi da wani turaren ta turarre jikin ta.
Wani hadin humra Momy ta kawo mata da wata atamfa ruwan ganye da ruwan daurawa.
Simple make up akai mata. Aka saka mata alkebba Golding kala.
Momy tai mata ruwan turare sannan ta saukar da ita wajen kawayen ta da Mami.
Nasiha sukai mata da addu’ar zaman lafiya. Sannan mutum biyu daga kawayen Momy suka fito da ita.
Dakin Dady suka kai ta shima nasiha yai mata mai ratsa jiki.
Sosai Asma’u take kuka dan sai yanzu ta san tayi aure.
Daga nan suka tafi da ita gidan mijin ta. Sai Zainab dake can tana kintsa gidan.
Gida ne katon gaske dan harabar gidan kanta katuwa ce, banda bayan gidan.
Garden da swimming pool ne sai bishiyun kayan marmaru kala kala. Da lilo.
Harabar gidan an kawata ta da fulawoyi. Kofa daya ce zata sada ka da shiga cikin gida. Da ka shiga kuma zaka ga katon falo aka saka masa wasu royal furnitures Coffee kala da adon milk. Haka ma labulayen kofi da milk ne.
Daga gefen sa yar stair ce da wajen daining da kitchen. Kitchen din ta an cika mata da kayan amfani zamani.
An mata adon sa irin na, Island kitchen plan akai. Daga can bangaren kuma Toilet ne.
Sai kofofi biyu dake kallon juna. dayar tana dauke da falo, da bedroom guda biyu. Ko wanne an zuba masa kaya masu kyau da tsada. Daki daya akai masa adon pink dayan kuma aka zuba masasa irin kayan Babban falo. Kamar yadda falon ta ma adon pink din akai mata
Dayar kofar ma, yar barende ce wacce zata fito dakai harabar tsakar gidan. Sai bandaki da falo da dakin bacci.
Wannan shine bangaren mai gida Aslam, sai arabi’an cusin da aka saka masa red nd white. Haka ma bedroom din an zuba masa red an white kaya.
Kayan kallo da kayan electronic duk masu kyau da tsada aka zuba su
Gida sai sanyin AC da kamshin turaren wuta da yake.
Kowa ya je yaga gidan sai ya sanya albarka da addu’ar zamab lafiya.
Haka suka ajiye Asma’u a dakin ta, suka karai mata nasiha sannan suka mike suka tafi.
Zainab ce kadai a wajen ta, Asma’u kuwa har lokacin in banda kuka ba abinda take.
Jin kan ta take kamar zai fadi dan ciwo. Zainab ce ta zauna a gefen ta, ta kamo hannun ta.
Dagowa tayi da idon ta jajir sai ta fada jikin Zainab tana kuka.
Lallashin ta Zainab take tana cewa,
“Haba Sis mene na kukan? Dan Allah kiyi hakuri ki daina.”
Shiru Awma’u tayi tana ajiyar zuciya. Zainab bata dade ba Yaa Buhari yai mata waya ta fito su tafi dan ya ajiye Aslam.
Kara kimtsa ta tayi, sannan ta mike tana mata sallama.
Tana fita Aslam ya shigo bayan sun yi sallama da Zainab.
Kofa ya rufe ya shigo dakin da Asma’u take. A ciki ta amsa sallamar tana me dukar da kanta kasa.
A gefen gadon ya zauna. Fuskar ta ya yaye, yana kallon fusakar ta da tai jawur da ita.
Hannun sa ya saka ya janyo ta jikin sa, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke.
“Ina kaunar ki Asma’u ina kaunar ki Asma’u “
Ya fada cikin wata irin murya.
Lamo tayi a jikin sa, tana jin wani yanayi a jikin ta.
Zaunar da ita yayi ya mike ya fita. Kitchen ya shiga ya dauko plate da cups.
Shi ya zuba musu gasasusun kajin a plate ya dauko lemo ya zuba mata a cikin cup.
Mikewa yayi ya dauko ta ya zaunar da ita akan carpet.
Ganin baza ta ci ba yasa ya fara bata da kanshi. Ba dan ta so ba ta dinga ci.
Duk wannan abin da ake kanta akasa, yake sam taki yadda ta dago bare ya kalli fuskar ta.
Suna gamawa ya janyo ta jikin sa. yafara kissing din bakinta nan da nan kwalla tazubo a idonta, Alkebbar jikin ta ya zare mata nan yatsaya kallon surar jikinta yadda tafito acikin kayan data saka, kokarin cire mata
riga yafara, yana cirewa yaji jikinta dumi tun alokacin yagane period take nan yaji haushi yakamshi yau ya so ya sami Asma’un sa amma kuma babu dama mensuration ya bata masa shiri, romancing din ta ya fara yi da zafi da zafi, jan na fulaninta ya fara tareda bata zafafan kiss ako wanne lungu najikinta wanda sai da yakwashe fiyeda minti 25 asannan ne yafara kokarin zame skirt din jikinta da yake tagama jigata bata iya yunkurin hanashi ba amma fa ta fashe da wani wahalallen kuka.+
Haka ya hakura yafara wasa da kirjinta har na tsawon wani lokaci, sai da yadanji dama dama sannan yayi magana cikin narkakkiyar murya Ya ce
“yaushe zaki gama?”
Banza tayi dashi jin haka yasashi dora hannunsa akan mararta har tsawon minti biyar sannan ya dauke hannunsa. Murmushi kawai ya saki a ransa yace,
“Yau ta fara.”
cigaba da shasshafata Aslam yayi har yasamu nutsuwa yadda ya kamata sannan ya kyaleta yayi hugging dinta ajikinsa sai da ya danyi bacci ahaka sannan yatashi yana kallonta.
Asma’u kuwa duk abin da yake tana jin sa sai sanyi da jikin ta yayi.
Mikewa yayi ya tafi dakin sa. Wanka yayi yai sallah.
Shiryawa yayi ya feshe jikin sa da turaruka, sannan ya fito.
Asma’u Kuwa tana can kwance in da ya barta.
Tana nan kwance tanata kuka saboda radadin da dukiyar fulaninta suke yi mata.
Lallai tin yanxu ma wai, wannan inda abun akai ya zan ji kenan.
Jikin ta yai nauyi ma ta kasa tashi. Tana kwance tana zubar da hawaye.
Kofar dakin taji ya bude, kai ta dauke tai saurin jan bargo jikin ta.
Murmushi yayi ya matso wajen ta. Bargon yayaye, ya kura wa surar jikin ya ido.
Asma’u da idon ta ke a rufe, amman tana jin idon sa a kanta.
Daukar ta yayi gaba daya yai cikin toilet da ita.
Kafa ta fara winsilawa, dan ya sauke ta.
Bai saurare ta ba har ya zaunar da ita a kan wata kujera dake cikin toilet.
Ruwa ya hada mata ya saka ta a cikin. Wata ajiyar zuciya ta sauke, tai lakwam a cikin ruwan.
Shi da kansa ya cuda ta ya gama ya nado ta a towel.
Kayan bacci ya saka mata. Ya feshe ta da turarukan ta.
Kan gado ya kwantar da ita akan shima ya bi bayan ta.
STORY CONTINUES BELOW

Bargo ya ja mata, ya jata jikin sa ya rumgume ta.
Jijjiga ta ya dinga yi har tai bacci. Ya jima yana farin cikin samun Asma’un sa.
Yau dai gashi ga Asma’un sa. Yana godiya da Allah da ya bashi ita.
A haka shima bacci ya dauke shi.
Asubar fari Asma’u ta farka kamar yadda ta saba.
Jin ta a jikin Aslam kanekane ya hana ta zame jikin ta. Dan kar ta tada shi.
Ta jima tana kallon Aslam tana murmushi.
Can taga yai motsi, ido ta tai saurin rufewa, mikewa yai yana addu’ar tashi daga bacci.
Kwanciyya ya gyara mata ya shiga toilet ya watsa ruwa yai alwala ya fice.
Asma’u na jin fitar sa ta mike ita ma ta fada toilet tai wanka. Tana fitowa ta fada gado.
Sai karfe tara ta tashi. Dakin ta ya fara gyarawa, ta fita ta dan sharshare gida ta bade shi da turaren wuta.
Kitchen ta shiga ta daura ruwan zafi. A fulas ta zuba, ta fasa kwai ta soya ta wanke plate din.
Daki ta koma, tai wanka ta shirya cikin wani purple kala material mai adon yalo.
Sosai tayi kyau, simple make up tayi ta rufe kofar dakin ta ta shige bed room tai kwanciyyar ta.
Aslam yana dawowa ya tadda dakin a rufe, murmushi yayi yai bangaren sa.
Shima kwanciyya yayi. Wajen karfe sha daya Momy ta aiko musu da break fast din su.
Aslam aka kira, yaje ya amso. Dakin Asma’u ya kara tabawa ya yaji a rufe.
Daki ya koma yai wanka, ya shirya cikin wata Brown kalar shadda.
Sosai yai kyau. Fitowa yayi ya kara taba kofar dakin tata.
A rufe dai take har lokacin. Knocking dakin yayi, amman shiru.
Can ya kara knocking. Muryar ta yaji a hankali ta ce,
“Waye?”
Murmushi yayi a ransa ya ce,
“Waye kuma? Ah lallai Asma’u.”
“Nine?”
Ya fada mata.
“Menene?”
Ta tambaye shi.
“Ki fito ki karya.”
Ya fada.
“Ina zuwa!”
Ta bashi amsa.
Falo ya koma ya zauna sai da yai wajen awa sannan ta fito.
Daining area ta nufa ta hada masa abinda zai bukata.
Nata ta diba ta fara ci. Tasowa yayi ya zauna a gefen.
Kallon ta yayi ya ce,
“Baby na kin ta shi lafiya?”
Kai ta dago ta kalle shi da daradaran idanun ta.
“Lafiya!”
Ta fada a hankali, da ba dan yana kallon ta ba da bai san tayi magana ba.
Abincin yaja ya yana ci yana satar kallon ta.
Suna gamawa ta koma dakin ta ta saka key.
Kallo ta yini tana yi, haka ma da rana Momy ce ta hada masu abincin rana ta aika musu.
Shima sai da ya kira ta sannan ta fita suka ci.
Sai da sukai sati Momy na aika musu da abinci sannan ta kyale su.
Asma’u ita ta cigaba da musu girki. Duk aikin gidan da abinda ya hau kanta da ta tashi da safe take yin su ta gama.
Haka nan girki, shima zatayi ta jere masa ya fito ta gaishe shi daga haka bata bashi fuska bare ya kawo mata wata magana.
STORY CONTINUES BELOW

Bangaren sa ma da ya fita aiki zata je ta gyara shi, ta wanke masa under wears nashi ta goge ta turare dakin ta rufo.
Duk abinda tasan ya dace tana yin sa sai dai da dare yayi zata rufe kofar dakin ta.
Sosai Aslam yake mamakin Asma’u shi dai ya san tabbas Asma’u na son sa amman bai san dalilin yin hakan ba.
Wata zuciyar kan fada masa ko dai ta daina son sa ne amman sai ya karya ta.
Pretty kuwa taje kano sai da lokacin da ta samu gidan su Asma’u gidan ba kowa sun tafi Abuja.
Sai da ta kwana biyu basu dawo ba. Kullum sai taje. A kwanan na ukun ne ta samu Mami a gidam.
Iso akai mata Mami ta amshe ta hannu bibiyu, kamar ta santa.
Sosai Mami ta burge Pretty dan ita bata xata irin manyan matan na irin haka ba duba da yadda su sukai mu’amala lokacin da suna da arziki suke jin duniyar tasu ce.
Sai da Mami ta sa aka kawo mata lemo ta sha sannam ta dube ta ta ce,
“Sai dai ban gane ki ba?”
Pretty ta ce,
“Eh! Wajen Asma’u nazo.”
Mami ta jinjina kai ta ce,
“To gashi bata nan. Tayi aure.”
Pretty ta ce,
“Dan Allah Mama a ina take ina sson ganin ta na nemi gafarar ta.”
Mami ta kalle yarinyar taga ba alamar mugunta a tare da ita.
Mami ta ce,
“Tana Abuja acan take aure.”
Shiru Pretty tayi, can kuma ta ce,
“Mama ni ce matar Aslam dan yayar ki. Mama duk abinda ya faru tsakanin Aslam da Asma’u nice sila, ni na yi asirin da Aslam ya daina waiwayar Asma’u duk da bai daina son ta ba. Mama dan Allah ki taimaka ki tayani bawa Asma’u hakuri, nayi nadama dan naga sakayyar Alalh.”
Kuka sosai take har ta zube akasa. Mami ce ta karasa ta daga ta ta mayar ta zaunar akan kujera.
Hawayen fuskar ta ta goge mata ta ce,
“Hakika kin raba son da ya dade da kafuwa, son da ba’a taba zaton rabuwar sa ba. Asma’u tayi jinya sosai wace banyi zaton zata warke ba duk a dalilin rashin Aslam. Amman ba komai haka Allah ya kaddara kuma bawa baya wuce kaddarar sa. Allah yayi sai sun rabu kuma sun dawo sun yi auren dai. Zan taya ki rokar Asma’u duk da nasan Asma’u na da saukin kai. Insha Allahu zata yafe miki.”
Rumgume ta Pretty tayi tana godiya. Da zata tafi har kudi Mami ta bata.
Hakan zaman Asma’u da Aslam yaci gaba da kasancewa, ko kad’an bata sakar mishi fuska idan yazo inda take, amma tana masa duk kan abinda zai sa ta.
Haka nan girki duk wadan da tasan yana so tana masa, amma da ta jishi zata shige d’akinta,
Aslam ma gane hakan yasa wani lokacin baya dawowa gida ko in ya dawo yana bangaren sa, sai dai ya makala nauwara daukar bayani a babban falo kitchen da dakin ta. Wannan yasa ya daina neman takura mata.
Dan kullum yana ganin yadda take gudanar da rayuwar ta in baya gidan.
Ba karamin burge shi take ba. Bama yaga ta ci ado tana zaune kawai.
Ko kuma ta saka kanannun kaya, tai ta juyi ita kadai.
Wani lokacin ta kira gida da su Zaianb tai ta waya, haka zata kira Momy ma.
Wani lokacin kuma ya ganta tana kuka yakan rasa me yasata kuka.
Rayuwa dai kala kala kala take gudanar wa. Abinda yafi burge shi da ita, shine yawan ibadar ta.
Yana lura da yadda take dukufa wajen addu’a da nafufuli.
Wannan na dada masa son ta da kaunar ta.
Kallon rayuwar ta da yake yi, yasa ya daina takura mata da son damun ta. Sai dai yana ‘ko’kori wurin kyautata mata sosai da son nuna mata shi masoyinta ne na ha’ki’ka.
Yau watanta biyu kenan babu abinda ya canja tsakaninta da Aslam.
Tana zaune falon d’akinta ya shigo, bata san ma ya shigo ba tana can duniyar tunani, a fili ta furta,
“Allah sarki Dady na ka tafi ka barni cikin wannan duniyar mara dadi. Yanzu banda waji farin ciki.”
Aslam ya zauna daga nesa da ita ya ce,
“Ai ke kika ki barin farin cikin ya sameki.”
Kamar bazatace komai ba, sai kuma tace,
“Waya fada maka, ai farin ciki na nasan ya tafi kenan bazai taba dawo wa ba dan yanzu na rabu da duk masoya na. Kaga kuwa ina farin ciki.”
Yace
“Ni menene naki. Nima masoyin kine na gaskiya wanda ke da burin ganin farin cikin ki a ko da yaushe.”
Shiru ta mishi ba tace komi ba, Mikewa yayi yayo wajen ta. mikewa tayi da sauri zata fita a dakin.
Da sauri ya kamo hannun ta ya zaunar. ya ce,
“Haba Husnah ki tunanin zaman mu zaiyi a haka kuwa? Ina mijinki amma bazamu zauna wuri d’aya ba?”
Kasa tayi da kanta tana wasa da zoben hanun ta. Wanda shine ya bata.
Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Take tsigar jikin ta ta fara mikewa.
Magana ya ke mata cikin wata irin murya mai burkita mai sauraro.
“Husnah ki yadda dani wallahi son da nake miki ba abinda ya ragu a cikin sa.”
Ya fada yana shinsinar wuyan ta. Kamshin ta mai dadi da kwanatr masa da hankali ya shaka take hankalin sa ya fara tashi.
Bakin ta yai saurin cafka, yana tsotsa kamar wanda ya samu alawa.
Hannun sa ne ya gangara kan dukiyar fulanin ta. Wasa ya dinga yi da ita.
Jin yana son wuce guna da iri yasa ta sakar masa wani irin kuka.
“Ni dai Yaa Aslam ka kyale ni, wallahi nasan ba sona kake ba. Ka rabu da rayuwa ta dan Allah. Ka koma gun wacce kake so har ka aura. Ni nasan daman Sir ya gama cutata ne da ya bar maka ni. Baza ka taba ganin daraja ta ba.”
Ta fada yana kuka mai tsuma zuciya.
Kallon mamaki ya tsaya yi mata, kasa jurar jin kukanta yayi mai tsuma zuciya, duk ya rikice, ya rasa ya zaiyi, ya fara magana cikin sanyin murya.
“waya fad’a miki ina da wadda nakeso bayanke? Wlhy ke kad’ai nakeso Asma’u, ban ta’bason wata d’iya mace a rayuwa ta ba kamar yanda nake sonki, ke ma kin sani ban taba soyayya da wata bayan ke ba. ki bani dama in bayyana miki irin son da nake miki.”
Da ‘karfi tace
“baka so na Yaa Aslam, baka so na. Ka koma wajen matar ka da kake so, ni ka kyale ni, nasan dan kaji zan aure ne kazo to kaji dadi da ka raba ni da mai so na.”
Duk ya rikirkice, ya ce,
‘Wallahi banda burin ‘bata miki rai ‘kanwata, don Allah ki fahimceni, wallahi ina sonki, naayi miki alkawarin faranta miki har iyakar rayuwatah.”
Hannu biyu ta sanya ta rufe kunnenta tace
“Bana sonji Yaa Aslam don Allah ka ‘kyale zuciyatah ta huta hakanan, duk abinda zakamin don kasan ina sonka ne….”
Kasa karasa maganar tayi ta kifa kanta akan kujera taci gaba da shesshe’kar kuka.
Sosai yake jin kukanta a jikinshi, ya rasa yanda zai rarrasheta, hannu ya saka ya d’agota a jikinshi, da sauri ta fara ‘ko’korin zamewa, anma tsam ya rumgumeta a ‘kirjinshi sosai, har saida tayi ‘kara saboda ba ri’kon wasa ya mata ba,.
Kuka kawai take dan bata da wani ‘karfin da zata kwaci kanta.
Aslam kuwa idonshi lumshe, ko lallashinta ya kasayi, duk jikinta ya saki ta fara rage kukan, sun dad’e a haka, kafin ya sassauta mata ri’kon ta zame ta kwanta a hankali ta rufe idonta, shima mi’kewa yayi ya fita ya barta.
Sai da ya fita daga d’akin kuma ta fashe da kukan takaici, Aslam yaa riga ya gama da ita tunda ya gane mahaukacin son da take mishi, kuka take sosai a ranta tana addu’ar Allah ya rage mata son sa