RAYUWAR ASMAU CHAPTER 2
Da wuri ta kamala abinda zasuyi ta shirya tayi wajen Dadyn ta.
Tare sukai break, sannan ta tafi. Da wuri ta shige ajin su.
Text din Ya Aslam ne ya shigo.
“Morning Pretty nah. Ya kike tin dazu nake son kiran ki. Nasan kina aiki. in kingama ki turon hoton ki. Sannan naje Lagos ne Dady ya aike ni. Ina bukatar addu’ar ki.”
Murmushi tayi ta maida masa da sakon.
“Na tashi lafiya Yaya nah. Kaima ina fatan kana lafiya. Ya hanya. Hotona yana can na tura maka yana jiran ka.”
Ta tura tana murmushi, Zee ce ta taba ta,
“Sis Lafiya kike ta zuba murmushi haka.”
“Lafiya lou wallahi. Kin karaso kenan.”
“Eh!”
Dai dai shigowar malamin su. Sai karfe sha biyu ya fita wani ya shigo yai musu awa daya sannan suka tafi sallah.
Suna fito wa suka shiga cafeteria suka siyo lemo da snack, a nan kofar hall din su suka zo suka zauna. Karkashin wata bishiya.
A jaka suka saka abincin su dan ba lokacin zasu ci ba, kawayen su ne suka karaso wajen su uku.
“Ah *Asmy* da Xee.”
Su ka fada suna dariya.
Murmushi sukai masu,
“Ya kuke!”
“Lafiya lou. Ya karatun.”
“Alhamdulilah.”
“Masha Allah!”
Suka zauna suna dan taba hira.
Sai karfe biyu suka koma aji dan daukar wani darasin.
Karfe hudu sun gama kowa yayi gida.
*WACECE ASMA’U HUSNAH*
*Asma’u* ‘ya ce ga Alhaji Suleiman. Alhaji suleiman dan kasuwa ne duk da yana da kwallin masters a hannun sa. Ya karanci fanin kasuwanci. amman yafi sha’awar kasuwan ci da aikin gwamnati.
Sai daga baya ne ya nemi aiki sannan yake hada kasuwanci da aikin nasa.
Alhaji Suleiman dan gidan Malam Haruna ne, Malam Haruna malami ne, kuma dan garin kano ne. Cikin garin Madobi.
Yana da matar sa daya Aisha, Allah ya azurta su da Ya’ya uku maza sai autar su mace.
Alhaji Suleiman shine babba da matar sa daya hajiya Amina. Ya’yan su biyu, Buhari da *Asma’u Husnah*
Sai Abubakar me bi masa, yana aiki a banki matarsa daya masa’uda, da ya’yan sa biyar duk maza.
Abubakar, Suleiman, Abdulhakim, sai yan biyu. Dukkan su sun girma kowa ya kama aiki. yana zaune anan katsina shima.
Ilyasu shima matar sa daya soja ne. Yana da ya’ya uku duk maza suna zaune a kaduna.
Muhammad, sai yan biyu shima. Shima dukkan su sun girma suna aiki.
STORY CONTINUES BELOW

Sai kanwar su kuma autar su Mariya wacce take aure a kaduna itama mijin ta soja ne. Ya’yan ta uku duk maza. Umar, Usman, Aliyu.
Amina Maman *Asma’u* ta kasance yar aminin Kakan *Asma’u* wato Baba Haruna.
Amina su biyu Allah ya bawa mahaifin ta Malam Isah da matar sa Hafsat. Da yayan su Fatima da Amina.
Yayar ta na auren minister of Agriculture wanda suke zaune a Abuja.
Aslam shi kadai ne danta. Wanda shi kuma yayi karatu a Kasar waje fanin asibiti wato medicine kwararen likitane.
Amina da Suleiman sunyi auren soyayya ne wamda har yanzu suke shan soyayyar su.
Zuri’ar ta kasance ba mace a cikin ta illa *Asma’u Husnah*
*Asma’u Husnah* ita kadai ce jika mace ga Haruna da Isah, wannan yasa dukkan family din suke son ta da kaunar ta.
Bama Aslam da yake da son yara. Dan da aka haifi *Asma’u* sai da kyar ya bar gidan shima dan makaranta ne.
Soyayyar ta dai da ita ya tashi. Sai kuma Allah yayi *Asma’u* irin yaran nan ne masu shiga rai.
Dukkan yan uwan ta son ta suke. Yarinya ce wacce tin da aka haife ta take da kyan ta duk da baka ce amman bakin ta me kyau ne su ake kira da black beauty.
Dan *Asma’u* komai Allah ya bata. Shekarar ta biyu aka sa ta a makaranta. Inda tana da shekara biyar tana nursery two.
Allah ya bata kokari duk da karancin shekarun ta inda aka dinga mata jumping din classes.
Shekarar ta takwas ta gama primary ta tafi secondary. Tana da shekara goma sha hudu tayi candy.
A lokacin Ta fara girma dan ta fara kirgar dangi. Kyawun ta ya dada fitowa.
Tana yin candy ta samu admission inda take karantar medicine yanzu haka Asibiti zasu tafi.
Tin tana primary ta sauke alkur’ani inda yanzu haka tana da haddar sa akai.
Kuma bata daina yi ba. tana kanyi dan duk juma’a take bawa Mamin ta haddar. Karatun ta baya hana ta haddar ta. Kamar yadda duk asabar da lahadi take zuwa isilamiyya da safe.
*Asma’u* yarinya ce me fara’a da barkwanci da son jama’a. Koma abin hannun ta be rufe mata ido ba.
Akwai tarbiyya dan duk yadda mutum ya girme ta zata bashi girman sa.
Akwai ta da son zumunci. A duniya tana son Dadyn ta kamar yadda shima duk duniya bai da wacce yake so irin ta.
Kullum bata da buri sai na ganinnta kyautata masa. Yan uwa kuwa kowa ya samu abin mata ko ya burgeshi sai ace *Asma’u!*
Kowa sha’awar ta yake. Tin tana karama tayi mugun sabo da Aslam wanda in yaxo shi ke rainon ta gaba daya.
Da anyi magana zaice *Asma’u* matar sa ce. Wannan yasa Dadyn *Asma’u* shaidawa zuri’ar su cewa ya bawa Aslam *Asma’u* ko yana da rai ko be da rai *Asma’u* ta Aslam ce.
Aslam yaji dadin wannan hadin da akayi musu. haka ma Dadyn sa da Momyn sa.
Inda sauran yan uwa masu son ta kowa ya janye kudurin sa yana sanya musu albarka
Sam *Asma’u* bata san anyi ba dan a lokacin tana da karancin shekara bata san anyi ba.
*ASLAM*
Aslam saurayi ne dan shekara talatin kuma kwararen likita. Yana da katon asibitin sa wanda Mahaifin sa ya gina masa.
Aslam yaro ne me farin jini, shima akwai fara’a da son yan uwan sa.
Yan mata da yawa na son sa amman shi sam bai basu fuska.
Dan yakan ce shi yana da *Husnah* sa kowa yasan sa da *Husnah*
Daga cikin yan matan nashi ne ya hadu da preety wacce ta nace masa kuma tai wa kanta alkawarin duk daren dadewa sai ta aure shi.
Aslam kyakyawa ne na karshe. Dan sai ka zata balarabe ne. wannan ya samo asali ne saboda, kakarsa dan yar libiya ce.
Fari ne dogo jikin sa a murde dashi. Idanun sa manya, da siririn hanci sa da pink lips din sa.
Duk jikin sa gashi ne kwance luf luf. Haka nan kansa suma ce cike a cikin ta. Wacce ita take karasawa ake ce masa balarabe.
Aslam na son *Asma’u* sosai dan bai hada son ta da komai. Duk abinda zai faranta mata yana mata sai dai in yaga ba dai dai bane.
Shi yake kara daura ta akan karatun ta dan ta waya zai mata bayanin duk abinda bata gane ba.
Haka fanin addini ma duk takan tambaye shi koma meye dan ya riga da ya sabar mata.
Dan ko wankan tsarki shi ya koyamata kafin ayi musu a isilamiyya.
Haka wasu hukunce hukuncen duk yana sanar da ita dan babu kunya tana daukar sa tamkar Ya Buhari.
Aslam shi ya hana a sanar da ita maganar bashi ita da akayi duk da yaga ta girma.
Ya fadawa Dady kan a bari ya janyo hankalin ta tukunna. Dan haka bai dade da sanar da ita kudurin sa akanta ba.
Lokacin da ya tare ta ba karamin nauyi abin yayi mata ba sai daga baya da kyar ta sanar masa ta amince.
Amman duk son da yake mata in tayi masa laifi sai ya mata fada haka in koyar karatu ne ya tashi zasu ajiye batun soyayya a gefe. ya koya mata kome inda ya kamata ya koya mata.
Haka in fanin soyayya ne ba a baya ba wajen fitar da duk abinda ke zuciyar sa ya fada mata
Yasha fada mata.
“Wallahi *Husnah* duk abinda nake fada miki wallahi daga cikin zuciyata yake ba koya ko kwafar na wasu nake ba. Abinda nake ji game dake, shi nake fada miki.”
Sosai yake mantar da ita duk damuwar ta da abinda yake damun ta ya faran ta mata.
*Asma’u* kanji duk duniya ba wanda ya kai ta wajen samun soyayya.
Kamar ko yaushe tin asuba da ta tashi bata koma ba, bare yau da tasan suna da Sir Sabir.
Da wuri ta sauka kasa ta gama duk abinda ya kamata tayi. Ta dawo dakin ta tayi wanka ta shafe jikin ta da mai.
Durowar ta ta bude, ta tsaya kallon ta tayi minti Biyar a wajen sannan ta samu ta zaro wata bakar doguwar riga.
Hannun rigar an masa irin dinkin babbar riga da wani yadin material me multicolour (Kaloli daban daban.) Sai gaban rigar da aka masa ado da stone (duwatsu) aka jere wasu manyan jajayen stone (duwatsu) guda takwas suma.
Dago rigar tayi tana kare mata kallo, Ya Aslam ne ya siyo mata da yaje dubai. Juya ta ta kara yi, sannan ta dire akan gado.
Wani jan skin tied ta dauko sai jar bra da pant, saka su tayi a jikin ta. Sannan ta dauko rigar ta saka ta daure ta, ta ciki.
Jan hijab ta dauka wanda iya kar shi saman kirjin ta. Wani jan sandal ta dauko tasaka a kafar ta.
Sai bakar jaka da ta zuba abin da take bukata. A kan gado ta ajiye jakar da wayar ta.
Dakin Dady ta nufa, sai da yasa ta ci abinci sannan ya barta ya tafito.
Jakar ta ta dauka, sannan wayar ta.
Sakon Ya Haidar ta gani, budewa tayi tana murmushi.
” *Assalamu Alaikum*
Da fatan Baby na ta tashi lafiya, yasu Mami da Dady da Buhari. Ina fatan duk kuna lafiya.
Daman zan fada miki ne ina kan hanyar Kaduna, ina bukatar addu’ar ki, in na isa zan kira dan nasan yanzu ba kya kusa.”
Murmushi tayi sannan ta nemi waje ta zauna.
Sakon fatan alheri da isa lafiya tayi masa sannan ta tura masa.
Ta jima tana tunani sannan ta tuna fa makaranta zata tafi.
Da gudu ta fita tayi dakin yayan ta. Bacci sa yake kamar kullum, gadon ta fada.
Da sauri ya mike,
“Ya Salam!’
Ya fada yana dafe kai. Murmushi ta saki,
“Ina kwana yayanah.”
Harara ya wulla mata, ya mike ya shige ban daki. Zama tayi jiran sa.
Wayar ta ce tayi kara, ta dauka.
” *Asma’u* tara saura minti goma dai.”
Ido ta zaro waje tana mikewa,
“Dan Allah da gaske,”
“Duba agogo ki gani.”
“Innalillahi wainna illahir rajiun. Gani nan gani nan.”
Ta fada tana nufar kofar ban dakin.
“Yayah! Yayah!”
Banza yayi mata. Kuka ta fashe masa dashi.
“Yayah!”
Ta fada cikin kukan. Shiru ya kara yi mata. Ya cigaba da cuda jikin sa.
Sai da ya gama sannan ya dauro shawul ya fito. Tana jikin kofar a tsaye.
Kallon ta yayi ya dauke kai ya fara goge jikin sa. Yana zama a gaban mudubi.
STORY CONTINUES BELOW

Karasawa wajen sa tayi da sauri, ta durkusa akan gwiwo yin ta tace,
“Yaya da Allah ka zo kakai ni makaranta na makara.”
Mai ya cigaba da shafawa. Kuka ta saka masa sosai.
“Rufe min baki.”
ya fada fuskar sa a bace.
“To Yaya dan Allah ka kaini makaranta.”
ta fada tana hade hannun ta gu daya.
“Ina Baba da yake kai ki makaranta.”
tace,
“Yaya na makara kuma Baba makara zamu yi dan baya gudu wallahi.”
“Ni ba inda zan kai ki.”
Kuka ta kuma saka masa.
“To ya isa tashi bari nasa kaya. Toh ta fada tana fita, dakin Mami ta ttafi dan mata sallama.
Kallo Mami ta bita dashi ganin idon ta yayi ja.
“Me yasami idon ki, kuma daman baki tafi ba.”
Asma’u ta ce,
“Yaya ne yasa ni kuka.”
Mami ta ce,
“Akan me?”
Tace,
“Na makara yaki yazo ya kai ni.”
“Kin je tsokana har kika makara ko.”
“A’ah!”
“Yanzu yana ina?”
“Shiryawa yake, yanzu zai zo ya kaini.”
“Ok jeki same shi.”
Juyawa tayi, sai gashi nan ya shigo, cikin blue (ruwan omo) din shadda wacce akai mata aiki da dark blue, (ruwan omo me turuwa) blue hula yasaka, da bakin takalmi sai bakin agogo a daure a tsintsiyar hannun sa.
Sosai yayi kyau, ya fito kamar wani tauraro, sai tashin kamshi yake.
Durkusawa yayi har kasa.
“Mami ina kwana. Da fatan an tashi lafiya?”
“Lafiya lou. Ya ka tashi.”
“Lafiya Alhamdulilah! “
“To jeka maza ka kaita makarantar daga nan ka wuce aiki zan aiki driver ya kawo maka abincin ka kaga ta makara.”
“To Mami sai na dawo.”
“Allah kiyaye hanya Allah muku Albarka.”
“Ameen!”
Ya mike ya fice, komowa *Asma’u* tayi ta rumgume Mami ta mata kiss (sumbatar) a kumatu.
Ta sake ta tana.
‘Bye bye Mami.”
“Bye Ayi karatu sosai banda kula kawayen banza.”
“Insha Allahu.”
Ta fada tana fita a guje tana mata bye bye da hannu.
Murmushi Mami tayi, dan *Asma’u* akwai ta da hankali ga nutsuwa, bar ta dai da tsokanar yayan ta amman komai nata cikin burgewa take yin sa.
Baka ce *Asma’u* Kamar yadda Dady yake baki, shi kuma Ya Buhari fari ne ya dauko Mami.
Amman komai na fuska da zubin jiki me kyau na Mami ne, dan Mami akwai diri hakan yasa ita ma *Asma’u* tana da diri me kyau.
Kamar yadda shi kuma Ya Buhari ya dauko zubin jikin dadi dan dogune, sannan jikin su a murde yake, suna da dan jiki dai dai gwargwado.
Bakin *Asma’u* bai mata muni ba sai kyau da ya kara mata. Dan Bakin ta me kyau ne, irin chocolate colour haka fatar ta take me kyau da taushi.
Kowa na sha’awar kalar fatar ta.
Kai ta jin jina.
“Allah bada sa’a.”
ta fada a fili tana yin dakin Dady.
Tana fita har ya shiga mota. Da gudu ta karasa ta bude gidan gaba ta shige.
Hanya suka dauka. Cikin minti ashirin sun karasa makaranta. Har kofar department ya dire ta sannan ya juya.
Tana karasawa kofar hall din su ta hange, sa a gaban aji.
Sanye yake da ruwan madarar shadda wacce akai masa dinkin riga wacce da kadan ta wuce gwiwa da dogon wando.
An masa aiki a jiki da dark brown (ruwan kasa) zare sai dark brown hula da takalmi dake kafar sa.
Ta jima tana kallon sa, Sai bayani yake zuba musu. Daga bisani ta buya daga gefe dan kar ya ganta.
Tinda ya mata kashe din kar ta matso masa kofar aaji muddin ta makara.
Tana daga taga tana jiyo muryar sa, me sanyi da dadin sauraro. Sai da taga ya kusan fitowa sannan tabar kofar hall din.
Ya fito ya tsaya a kofar ajin yana kallon ta, duk da ta bashi baya amman ya tabbata ita ce.
Ya jima yana kallon ta ko zata juyo amman ina ko juyowa batai ba kamar tasan yana wajen.
Wajen ya bari ya nufi Office din sa. Yana bawa wajen baya tana juyowa bayan sa ta tsaya kallo.
Kai ta girgiza ta juyar da kanta. Zainab ce ta karaso wajen.
“Sannun ki, kin kyauta.”
“Wallahi bansan lokaci ya tafi haka ba.”
“Haka dai kullum bayan kin gama tsokanar ki ko.”
“Ni yau ban tsokane sa ba.”
“Ke din kuwa.”
“Eh!”
Dariya zainab tayi,
“tashi ki rakani na siyo lemo dan Allah.”
Mikewa tayi suka nufi cafeteria. Sai da suka siyo lemo sannan suka dawo.
Wajen da suka saba zama nan suka zauna gefen hall (dakinn daukar darasi) din su karkashi wata bishiya.
Suna zama, sai ga kiran Ya Aslam nan.
“Assalamu Alaikum!”
“Wa’alaikum salam!”
“Love!”
“Na’am Yayana ya hanya?”
“Hanya lafiya gashi har nagama komai yanzu sai gida, shine nace bari na karaso naga Queen of my heart.”
“Wow! Amman kuwa da ka kyauta.”
“Gani nan shigowa ckul din.”
“Sai ka karaso.”
“Aha.”
Ta kashe tana murmushi.
“Waye zezo?”
Zainab ta tambaye ya.
“Ya Aslam ne.”
“Oh Allah kawo shi lafiya.”
“Ameen!”
Yan department din sune suka karaso wajen su uku. Hafsat, Amina da Khadija.
Bayan sun gaisa suka zauna. Hafsat sai hade fuska take Suna dan taba hira. Amman ita ta hade rai
Zainab ce ta ce,
” *Asma’u* wannan week end din zamu zo gidan ku, zamu kawo miki IV Fadila.”
“Eh daman ai ke bakya zuwa gidan mu sai da dalili wai ke kunya.”
Khadija ce, ta sa baki.
“Ke zuwa kike.”
Murmushi Zainab tayi.
“Yauwah tambayar min ita dai.”
Amina ce tace,
“Yo ke ina ruwan ki. Sun fi kusa kuma kowa yasan zee bata son zumunci.”
Dariya Zainab tayi,
“Ai ita tasan ina da zumunci tasan kuma me yasa yanzu na daina zuwa gidan su.”
Tsaki *Asma’u* tayi,
“Wai fa dan Yaya Buhari saurayin tane shine fa.”
Khadija tace
“To kunji dalilin ta ko.”
“Wannan ba dalili bane,”
Cewar Amina.
“Yauwah yar uwa.”
*Asma’u* ta fada tana wa Zee gwalo.
Zuwan wata katuwar mota shi yaja hankalin su banda *Asma’u* da tayi kasa da kai tana wasa da wayar ta.
*Morning yan uwa ya kk ya gd da iyalai.*Dukkan su hankalin su ne yayi kan motar, banda *Asma’u* da ta daukar da kan ta, tana wasa da wayar ta.+
Khadija ce ta fara magana, ta ce,
“Kai motar nan ta hadu amman.”
Amina tace,
“Ai daga duk kan alamu, ma na cikin ta zai fi haka hauduwa.”
“Gaskiya kan motar ba karya, ko wane dan gayun ne a ciki.”
Hafsat ta fada
“Ni kam ba ruwana da na ciki sai motar da ta burge ni.”
Zainab ta fada.
“Kai Allah bani irin motar na.”
Hafsat ta fada.
“Hassada kike yi tinda kika ce Allah baki irin ta sai dai kice Allah baki finta.”
Amina ta fada.
“Duk karya ne irin haka nan, dan kaga Abu ka roki Allah yabaka irin sa shine haka.”
Zainab ta fada tana tabo *Asma’u*
” *Asmy* kalli waccen motar amman tayi kyau wallahi.”
Kai ta dago ta kalli motar, ji tayi gaban ta ya fadi.
“Eh tayi kyau.”
Ta fada tana mikewa sakamakon kiranta da ake yi.
Can gefe ta koma jikin wata motar, ta dauki wayar.
“Hallo my beauty! (Kyakyawa)”
“Ya Aslam wannan ai tsokana ce.”
amsa ta amsa masa da muryar shagwaba.
“Wacce tsokana nayi.”
ya tambaya
“Wai beauty!”
ta bashi amsa.
“Oo Ke ba kyakyawar bace.”
Ya tambaya.
Ta ce,
“Gaskiya ni ba kyakyawa bace. Wannan ai sai kasa ayi min dariya.”
“Ba wanda zai miki dariya kinji, saboda kyan ki ba kowa ke da irin shi ba. Kina da wani kyau wanda kafin a samu mutum me irin sa ake dade wa. Ur skin is fresh with a beauty colour. (Fatar ki a murje, me kala me kyau).”
Ta ce,
“Uhmm please stop dis joking I beg you. (Dan Allah daina wannan tsokanar na roke ka.”
Murmushi yayi ya ce,
“Wallahi I am not joking, I am telling the true. (Ba tsokanar ki nake ba ina fadan gaskiya ta ne.)”
Baki ta turo ta ce,
“Naji ya isa, ka karaso ne,”
“Eh! Gani kina ina ne.”
Ta ce,
“Ina kofar department din mu,”
“Nima ina wajen.”
“Kai ya Aslam!”
ta fada.
“Da gaske ina wajen.”
“Ta ina.”
“Ina cikin wata Ash marsandi.”
“Oh na ganka. Ina ta bayan ka.”
“To kizo man.”
“A’ah Yaya please kai ka fito.”
“To gani nan.”
Baya ta juya masa.
Kofar motar ya bude, wani sanyi da kamshi me dadi ne ya fito.
Kafar sa ya ziro kasa. Safa ce da takalmi sau ciki bakake a kafar sa.
STORY CONTINUES BELOW

Daya ya diro sannan ya fito gaba dayan sa. Suit ce a jikin sa, ruwan kumkumadi.
Ya cire ta saman sai yar ciki da ya rage. Tin daga kafar sa na fara kallon sa inayin sama. har na karasa kirjin sa wanda yake a bude dashi na kirar cikaken namiji me jini a jiki wanda ya cika namiji.
Kan fuskar sa na gangara. Fuskar sa me kyau ce doguwa fari ne tas dashi, sai manyan idanu wadan da suke a lumshe, wanda ake ce musu (sexy eye)
Bakin shi dan karami ne, wanda yake da lebe me taushi gasu pink sai kwalli suke. Kansa cike yake da suma, kamar ta indiyawa.
Sai saje dake gefen fuskar sa, wanda ya kara fito masa da kyaun fuskar sa. Idon sa sanye da farin gilashi.
Masha Allah wannan gayen duk inda ake neman cikaken namiji me kyau da kwarjini ya kai ya ma wuce nan.
Yan mata da yawa kallon sa suka tsaya yi sai gulmar sa akeyi. Dan ya gama haduwa ba karya.
Waige waige ya farayi dan neman inda take, duk da ta juyar da kanta sai da ya gene ita ce. Dan duk jikin sa ya gama shaida masa, *Husnah* sa ce.
Cikin tafiyar kasaita da nuna kalama tare da nutsuwa yake tafiya.
Sannu a hankali har ya karasa gefen ta. Ta bayan ta ya zaro hannayen sa dake cikin alhiju ya rufe mata idanu.
Jin an rufe mata ido da hannu me laushi, ga kamshin turare dake tashi, tasan Ya Aslam ne.
Murmushi ta saki me sauti.
“Haba My Hero, ai nasan kai ne.”
Hannun sa ya janye ya maidasu kan kafadun ta ya juyo da ita.
Kasa magana yayi ya kure ta da idanu.
Ido ta kashe masa guda daya.
“Yah dai.”
Yawu ya hadiye tare da sauke ajiyar zuciya yana me sakin wani murmushi dake karawa fuskar sa kyau.
Wani kallon soyayya yake aika mata dashi.
Ba karamin kyau sukayi ba.
“Baby nah kinyi kyau fa.”
ya fada yana kara kallon ta.
“Zaka fara ko?”
Ta fada tana nuna masa wasu kujeru da aka gina su.
Zama yayi ita ma ta zauna.
“Sannu Yaya nah Ya hanya?”
ta tambaya cikin kulawa.
Ya ce,
“Hanya Alhamdulilah.”
“Sannu toh!”
“Yauwah! Naji dadin zuwa na dana ganki Sweetheart, kin kara kyau, ashe duk hoton da nake gani rage min kyaun ki yake yi.”
“Yayana kenan yasu Momy.”
ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.
“Suna lafiya.”
Ya fada yaba dago face din ta.
“Bari na karbo maka lemo.”
Ta mike.
Kamo hannun ta yayi ya ce,
“A’ah yanzu na gama cin abinci ga naku can ma a mota.”
Murmushi tayi,
“Kai Yayah.”
“Eh!”
“Zakaje gida ne.”
“A’ah! Daga nan zanyi gida.”
“Ok.”
“Ina sonki Baby nah.”
Murmushi tayi ta dukar da kanta.
“Baby kunyar nan taki tana dada miki kyau.”
Kai ta kuma dukar wa.
“Bari na wuce kar nayi dare. Tinda naga Baby nah ai nagodewa Allah.”
Murmushi tayi.
“To nagode.”
“Nike da godiya Baby nah “
Suka mike suka nufi motar. Dai dai karasowar Sir Sabir zai dauki motar sa.
Kallon juna suka yi, ya shige motar sa.
“Waye wancan.”
Juyawa tayi,
“Sir Sabir wani lecturern mune.”
STORY CONTINUES BELOW

“Kuna magana ne?”
Ya tambaya fuska a dan hade
Kai ta girgiza ta ce,
“A’ah!”
“Ina zee kuwa?”
Ya tambaya.
Kallon gun da suke tayi ta ce,
“Gata can bari na kira ta.”
Ta tafi wajen su Zee,
“Zee kizo inji Ya Aslam!”
Ta fada tana kamo hannun ta.
Wajen su suka karasa.
“A bamu waje ko?”
Ya fada yana kallon *Asma’u* baki ta tabe ta bar wajen. Dariya yayi, yace,
” *Husnah* rigima.”
Sannan ya dawo da hankalin sa kan Zee.
Bayan sun gaisa yake bata amanar *Asma’u* sannan sukayi sallama.
Wajen *Asma’u* yayi,
“Haba Baby na yanzu da Yayan naki kike fushi. Kiyi hakuri kinji.”
Shiru tayi masa. Murmushi yayi, ya koma gaban ta,
“Ko so kike na rumgume ki na rarashe ki.”
Ido ta zaro, tana girgiza kai. Ya jawo ta. Saurin janye hannu ta tayi. Tayi wajen motar sa.
Bayan ta ya bi, yana Murmushi ya shiga motar. Leda ya miko mata.
“Gashi ni zan tafi.”
Amsa tayi ta ce,
“To Allah kiyaye hanya.”
“Ameen nagode!”
Ta rufe masa kofar tana daga masa hannu. Tare da murmushi akan fuskar ta.
Sai da taga bata hango shi sannan ta koma wajen kawayen ta.
Ido suka bita dashi,
” *Asma’u* waye wancan.”
Hafsat ta tambaya fuskar ta a hade. Kallon ta *Asma’u* tayi sannan ta dauke kai.
Zainab ce, tace,
“Yayan ta ne.”
Khadija tace,
“Amman fa ya hadu. Wai meyasa ke kike baka ne.”
Amina ce, tace,
“To ko zaki canja mata halitar ta ne,”
Harara ta Khadija tayi,
“Ni na tambaye ta, ta wani haden rai da dauke kai.”
Hafsat ta fada, Mikewa *Asma’u* tayi ta kalle ta.
“kin tambayen an amsa miki ba shikenan ba. ko kin manta wa kike tambaya ne. *Asma’u* da batai miki komai bace kika dau gabar duniya kika daura mata, kin manta in nayi miki magana ko kallo na bakya yi shine kuma yanzu zaki zo kina tambaya ta. Kuma cikin isa sai kace ni yar kice. Ke bama zan fada ba. Kiyi abinda xakiyi.”
Ta fada tana kama hannu Zainab suka shige hall.
“Haba *Asma’u* me kenan kika yi ke da bakya fada.”
Kuka *Asma’u* ta fashe dashi,
“Ya zanyi kema kinsan dai Hafsat ta kaini bango ne. Duk makarantan nan ba wacce ta tsana kamar ni tin ina dauke kai sannan yanzu tazo tana min gadara. Akan abinda be kai ya kawo ba.”
“Ya isah toh mene na kukan!”
Ta fada tana jan ta jikin ta tana rarashin ta.
Ta jima tana addu’a cikin ranta sannan taji sanyi. Kan ta, ta dago ta kalli Zainab.
“Nagode besty.”
“Ba komai.”
kasa ta duka zata dauki jakar ta. Sai a lokacin ta tuna da abinda Ya Aslam ya kawo musu.
Murmushi tayi ta dauki ledar tana dubawa. Takeaway yayi musu, guda uku sai dayar ledar kuma kaji ne guda biyu a ciki da lemuka na jarka.
Raba su tayi gida biyu ta mikawa Zainab.
“Besty dan Allah mikawa su Amina kayan nan.”
Karba tayi tayi waje.
Su *Asma”u* na barin wajen, su Amina suka farayiwa Hafsat fada.
“Haba Hafsat, meyasa kike haka, yarinya bata tsare miki komai ba amman kin tsane ta gaskiya ki daina haka.”
Hafsa ta ce,
“Tayaya zakice bata taren komai ba, yarinyar da ta shigo ta same ni sannan tazo tafi ni kokari shine bata fini komai ba.”
Khadija ta ce,
“Yo dan tafiki kokari, ai kema dagewa ya kamata kiyi ba ki tsane ta ba.”
Khadija ta fada tana bata fuska.
“To ku dake ni mana.”
Hafsat ta fada.
“A’ah A’ah ba abin duka anan. Sai dai muyi miki addu’a Allah ganar dake.”
Dai dai nan wata daliba da tayi kaurin suna a makarantar ta karaso gun su
“Hae Babies.”
“Hae!”
Gefen Hafsat ta zauna.
“Dan Allah wa naga ta tsaya da yaron nan da yazo yanzu. Dan bayan ta na gani banga gaban ta ba.”
“Oh ai *Asma’u* Suleiman ce.”
Hafsat ta bata amsa.
“Wane department take,”
Suka fada mata tai musu godiya ta bar wajen
Zainab na fitowa Munasha na shiga Hall wajen *Asma’u* ta dosa kai tsaye,
Tana karasawa wajen, tace,
“Hae Bae!”
Murmushi *Asma’u* tayi.
“Sannu!”
“Yauwah! Uhmm daman nace wanda yazo din nan sunan sa nake son ji.”
Murmushi *Asma’u* tayi,
“Ya Aslam Sunan sa.”
“Ok toh nagode.”
Ta fada tana mikewa dai dai karasowar Zainab.
Kallo Zainab tabi ta dashi, ta karasa gun *Asma’u*
Fuskar ta a daure take tambayar ta.
“Me ya hada ki da waccan?”
Bin ta *Asma’u* tayi da kallo.
“Tambayata tayi.”
“Akan wa?”
“Ya Aslam mana.”
” *Asma’u* kin san wace wannan kuwa?”
ido Asma’u ta bude alamar tsoro. Ta girgiza kai ta ce,
“A’ah wace?”
“Toh! Ita ce wacce ake kira Munasha! Kinsan dai Munasha ita ce wacce ba abinda bata aikatawa, ki kula da ita dai.”
Ido *Asma’u* ta zaro, saboda tsoro.
“Wallahi ban sani ba.”
“Ki dai kula.”
“Insha Allahu.”
Daga nan suka fara cin abinci, suna gamawa aka fara taruwa a hall din. Gaba suka koma, sai ga lecturer su nan.
Sai karfe hudu ya fita, sallah sukayi suka shige library dan yin karatu.
“Sis Koyan lecture da Sir Sabir yayi muku yau.”
Asma’u ta fadawa zee
“Toh!”
Ta fada tana koya mata, sosai take ganewa. Sai karfe biyar da rabi sannan suka fito, lokacin har anzo dibar su.
Sallama sukayi, suka wuce.
Tana komawa gida ta tadda Mamin ta a falo.
Kanta ta haye,
“Mami na ya gida?”
“Lafiya Alhamdulilah, Ya makarantar?”
“Lafiya Mami.”
“Tashi kije kici abinci nasan baki ci komai ba.”
“Lah Mami naci Abinci. Mami kinga yau Ya Aslam ma yazo makarantar mu.”
Ta fada tana murmushi, fuska Mami ta dan hade, ta ce
“Wajen wa yaje?”
“Wucewa zai yi ya biyo.”
Asma’u ta bata amsa.
” *Asma’u* ban yadda ki kara bari ya same ki a makaranta ba, ke bashi ba koma waye kar ki kuma haduwa da wani namiji a makaranta.”
Fuska ta marairaice,
“Mami dan Allah kiyi hakuri, bazan kara ba.”
“Ba komai baki bata min ba. Amman kika kuma shi zai batan rai.”
“Kiyi hakuri insha Allahu bazan kuma ba.”
STORY CONTINUES BELOW

“Kar ki damu tashi kije ki rage kayan jikin ki.”
“Kin hakura toh!”
asma’u ta tambayi Mami.
Murmushi Mami tayi,
” *Asma’u* kenan. Na hakura, kinji.”
Murmushi tayi ta tashi ta haye sama.
Murmushi Mami ta kuma yi, tana girgiza kai, *Asma’u* sam bata son bacin ran iyayen ta ko ya tayi musu laifi zata daga hankalin ta, har sai taga sun hakura.
Ita kanta Mami tasan ba wani abu bane dan Aslam yaje makarantar ba, amman in har bata tsawa tar ba nan gaba zata iya bawa kowa damar yin haka.
kuma hakan baya da kyau.
Tana shiga dakin ta ta fara lalubar number sa. Bugu daya ya daga.
“Yayanah ya hanya?”
“Hanya lafiya Alhamdulilah na kusa karasawa.”
“Kai Yaya gudu kake yi ko?”
“So nake nayi sauri na karasa.”
“Dan Allah ka rage gudun nan.”
“To shikenan sai anjima.”
“Aha! Ka kula da kan ka.”
“Insha Allah!”
Ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya ne. Bandaki ta shiga tayi wanka sannan ta fito.
Kwalliya tayi me kyau, ta saka riga da siket yan kanti ruwan madara da dark brown.
Brown (Ruwan kasa) din hijab ta dauka ta saka sanna ta dauko jakar ta tana duba wa.
Tana gama dubawa ta mike ta hau kan sallaya, tana jan carbi. Kiran sallah da taji ya sanya ta mike ta tada sallah.
Tana idar wa ta janyo Alkur’anin ta, tana karantawa. sai da akayi sallah isha’i sannan ta mike tayo.
Tayi Isha’i sannan, ta mike tayi shafa’i da wuturi. Tana idar wa ta fara yin addu’a.
Wayar tace tayi kara dubawa tayi. Sakon Ya Aslam ne ya shigo.
*Baby nah, na sauka lafiya. Zan kira ki anjima.*
Murmushi tayi, ta mike tayi waje.
Tinda ya gansu a tsaye ya kasa sukuni sam ya kasa samun nustsuwa, waye wannan da yazo gun ta, sam shi abin damun sa yake.
Haka ranar ya gama, aiki duk jikin sa babu dadi, ransa a bace dan abin be masa dadi ba.
Haka ya tashi a aiki ya wuce gida.
Mamah na gani sa taji hankalin ta ya tashi, dan duk ya fita a haiyacin sa.
Gaishe ta yayi, ta amsa.
“Sabir lafiya kuwa?”
“Lafiya lou Mamah.”
Kallon sa tayi, tana me girgixa kan ta.
“Wai Sabir mecece ni a gunka.”
Kan sa ya dago, yana kallon ta.
“Eh! Tambayar ka nayi,”
“Mamah Mahaifiya tace ke.”
“Ka tabbata?.”
“Na tabbata Mamah.”
“Amman kuma me yasa in zurfin cikin naka ya tashi har ni da nake mahaifiyar ka, kake boye min.”
Kai ya sunkuyar,
“Mamah kiyi hakuri.”
“Ni kawai ka fada me ke damun ka.”
“Mamah ni ba abinda ke damuna aiki ne kawai.”
“Shikenan Sabir, tinda haka ka zaba ai shikenan. Nidai zan ta tayaka da addu’a Allah ya, yaye maka abinda ke damun ka.”
“Ameen! Mamah nagode Allah kara girma.”
“Ameen! Abincin fa zaka ci yanzu ko sai anjima?”
“Mamah ban dade daci ba, sai dai in anjima.”
“To shikenan.”
Ya mike yayi dakin sa.
Kanta ta girgiza tana jinjina zurfin cikin Sabir da ko ita, bazai fadawa damuwar sa ba.
Ta dauki a niyyar sashi a addu’a Allah ya yaye masa koma me ke damun sa.
Sabir dan gidan, Alhaji Marzuk ne, da matar sa firdausi, yana aiki a ma’aikatar lafiya ne dake jigawa.
Inda ita kuma matar sa ke aiki a ma’aikatar ilimi. yayan su uku. Biyu mata daya namiji.
Rukkaya ita ce babba wacce, tayi aure a Lagos ya’yan ta uku. Maza biyu daya mace Maryam
Sai me bi mata, Mufidda wacce take, aure a nan kano. Ya’yan ta biyu.
Sai Auta Sabir, wanda yake babban likita a nan asibitin Aminu kano. Yanzu haka an dauki contract ne inda yake lecturing.
Mahaifin Sabir na son Sabir haka ma maman sa da yan uwan sa. Basu da buri sai na suga yayi aure.
Mamah sa tayi, tayi yayi aure yace lokaci ne beyi ba. Ba kalar matan da bata kawo masa ba amman sam ko kallo bai isar sa.
Dan yanzu haka ta bashi lokaci indai bai yadda ba zata hada shi da koma waye.
Zaune suke, da kwalbar giya a gaban su. Wacece in ba Munasha da Bilkis ba.
Aminan juna wanda harkar su take iri daya kuma hali ma iri daya wannan ya kara hada aminan takar tasu.
“Munasha, Jibson ya kawo karar ki, wai kin ki ki bashi hadin kai.”
Fuska Munasha ta hade, tare da zukar tabar dake hannun ta.
“Bilkis Amman na fada miki, cewar tin ranar da na hadu da yaron nan duk kan bukata ta da sha’awa ta, ta koma kansa.”
“Amman dai nasan kina shan azaba dan kin saba da rayuwa da maza, yanzu nasan kina cikin tashin hankali.”
Idanun ta ta dago wadan da suke jijir dasu.
“Haka ne, amman zuciyata ta, tafi wajen wani can.”
“Ki daure kije gare shi ko kya samu nutsuwa.”
“Kina ganin beyi zuciya ba.”
“Tayya zaiyi zuciya dake bayan yasan matsayin ki da irin zumar da kike shayar dashi.”
Ido ta juya,
“Amman kice lalashi na kika yi.”
“Daman mana.”
“Ok jeki.”
Ta mike tayi benen wajen.
Kwabar da ke gaban ta ta dauka ta zuba giyar dake ciki a kofi.
Sha ta farayi, tana lumshe ido sai kace me shan wani abin dadi.
*Wacece Munasha*
Munasha, suna ta na ainihi Maimuna, mahaifin ta Malam Anas, Sai Mahifiyar su Sadiya. talakawane dan mahaifin ta itace yake siyar wa.
Basa dai taba rasa abinda zasu ci, haka nan sutura duk shekara yana dinka musu ita kala biyu ko daya.
Mahaifiyar ta aikato take yi a wani gida dake unguwar su, anan take samar musu yan kwancen kaya, da dan abinci.
Munasha, ta kasance me kwadayi da son abun duniya.
Duk kokarin da Mahaifin ta yayi mata, abu bata taba ganin ya mata sai rainuwa haka nan abinci, in anyi shima sai ta ga damar ci.
Ya sanya su a makarantar boko da arabi. Bokon dai dayaya aka gama ta. Hakan yasa tana yin candy ta fara bin maza.
Dan a duniya tana son ta ganta da kudi wannan yasa, ta fara bin maza. Ganin mahaifin ta zai hana ta fita yasa a cikin Yan iskan su, tasa wani yazo, a zuwan ya dauki nauyin karatun ta.
Mahaifin Munasha yaji dadi da wannan abin wannan yasa Munasha ta samu kafar fita. Dan wani lokacin ma haka tace ta koma hostel da zama.
Nan kuwa ba a hostel din da take in ba club ba sai, sai gidan samarin ta.
Munasha, ta zama babba a harkar karuwanci,KARASHEN LBRN Munasha*+
A cikin kawayen ta mutum daya ce ta arxiki. Wacce tun fara bin mazan ta take mata fada akan irin samarin da take kulawa.
Dan ke daga ganin samarin ma xaka san yan iska ne, bare in suna mu’amala suyi ta taba ta. Ko ace za’a tafa.
Ko in tana bukatar abu sai dai tace saurayi yayi mata.
Rashida yar gidan masu hali ce, dan sau tari takan bata kudi kashe wa. Sannan in an mata kaya kala uku zata dau daya ta bata.
Amman sam Maimuna bata godewa Allah. Ita burin ta tagan ta ta kula me kudi wanda zai na kashe mata kudi.
Bayan yawancin samarin yanzu basa yin abu dan Allah sai dai in zasu fansha.
Rashida takan mata fada.
“Haba Maimuna, yanzu da hankalin ki, kike kula wadan nan mazan.
Shin me yan mata memukeso muzamane, ina hankalin mu yake ina tunanin muyake ne, Shin iyayen mu me suka gaza yimana muke nema mudorawa kan mu akan hanyar da baza ta bulle da mu bane. Duk kokarin da Baba yake, amman kike son daurawa saurayi duk buqatar ki.
Haba yar uwata ashe kinyadda saurayinki xemiki abunda iyayenki baxasu yimiki, Maimuna ki nemo hankalinki da nutsuwar ki6oye son abun duniyarki badon komaiba sedan kitsira da martabarki taki ta ‘ya mace.
saurayi nagaskiya shine wanda yake sonki da aure baya neman komai daga gareki burinsa yaga kin tsira da mutuncinki.
Saurayi mayaudari shine Wanda yake miki hidima ba don Allah ba sedan kibashi gishiri yabaki manda.
Mace wadda akasanta da kunya, tarbiyya, mutunci, Jan aji, kamala, sanin yakamata, amman kin manta dacewa yanxu xamani yasanja wasu daga cikin samari sundena abu dan Allah sedan samun riba.
wallahi Maimuna, idan saurayi yafuskanci ke kinada kwadayi akwai matsala ta hanyar haka xesamu damar isar da qudurinsa, wallhi saurayi bashida abun duniyar daxe rudeki yaxubar miki da mutuncinki bashida abunda xemiki wanda iyayenki xasukasa.
Alokacin bakida damar hanashi duk abinda yanema domin shi kika fara mora. kinsan ko farce yata6a miki yacuceki dan Allah Mainuna ki kula.”
Duk lokacin da Rashida tai mata fada takan dauka.
Amman da ta hadu da yan harkar ta zata manta.
In kuma Rashida tai musu fada gaba dayan su, sai suce dan ita Rashida din yar masu Hali ce shi yasa bata san halin da suke ciki ba.
Tin asali Yayan Rashida ke son Maimuna, amman tafiyar sa karatu malesia, shi ya sa soyayar ta ja baya.
Duk da a cikin zuciyar sa bai da burin da ya wuce ya kamala karatu ya dawo ya tai maki rayuwar Maimuna da mahaifin ta ba.
Itama a zuciyar ta shi take so, dan Nasir namiji ne wanda ya amsa sunan namiji, ya hada komai kyau ilimi da gayu.
tinda ya tafi be dawo ba duk da suna waya amman karatu yana dauke hankalin sa. Ba dan baya son ta yafi bawa karatu lokacin sa ba. A’ah sai dan son da yake yaga ya kammala karatun sa ya fito da sakamako me kyau.
STORY CONTINUES BELOW

Maimuna kyakyawa ce ajin karshe, fara me kyaun sura. Amman duk ta zubar da mutuncin ta.
Har Kungiya ce, da ita wace take daukar yara ta kaisu wajen manyan Alhazai.
Wanda har a cikin makaranta ma, akwai wadan da suka daure mata gindi.
Yanzu haka Munasha ta zama kwarariya dan ta kama naira a hannu.
Yanzu haka da taga saurayi yayi mata zata san yadda zatayi ta ja hankalin sa.
Har wajen malamai take kai mutum a janyo mata hankalin sa. Munasha babbar yar duniya ce wcce idon ta ya gama budewa.
Ba kasar da bata fita.
A harkar karuwanci dai ta fita zakkah. Amman duk da haka, son Nasir na cikin ranta.
*-*-*-*-*-*-*-*-*
Kwance take a kan gadon ta, sanye take da hijab fuskar ta, tayi kyau da ita.
Sai futar da annuri take, allon wayar take kallo. Wannan yasa na mika kai dan ganin abinda take yi.
Aslam na gano kwance akan katon gadon sa, yana sanye da blue (ruwan omo) din T-shirt, da blue din wando, da alamar kayan bacci ne a jikin sa.
Magana ya ke fada mata kunne na kasa ina sauraro.
“Ke na bawa zuciyata *Asma’u*, ki adanata dan nasan zaki mata gata,”
Murmushi *Asma’u* keyi. Sanna tace,
“Hmm Ya Aslam. Gakiya kam zan kula maka da ita fiye da yadda zan kula da tawa.”
“Nima na sani. na baki ita ne saboda bana son kowa ya taba ta. Duk wanda zai shiga ke zaki bashi izinin shigar ta”
Murmushi tayi.
Ya cigaba da magana
“Dake na fiso muyi soyayya, sannan dake nafi son muyi rayuwa. Dan Banda kamar ki a duniya, wannan yasa na mallaka miki zuciya ta”
“Kai Ya Aslam!”
Ido ya kanne mata ya ce,
“Ke ta daban ce. Shi yasa kullum yabon ki nake. Ke nake son ki kasance a kusa dani. Dan kece kadai farin ciki na.”
Shiru *Asma’u* tayi tana sauraron sa, tare da lumshe idanun ta.
Kallon kyakyawar fuskar ta yake yi.
“Ke ce Taurruwa ta. ke kika hasken zuciyata. Kin kawar min da dukkan damuwa ta. Ban da bakin magana gare ki ban san irin godiya da zan miki ba. Ban san kuma me kike son na miki ba.”
Idon ta, *Asma’u* ta bude, ta kira sunan sa.
“Ya Aslam!”
Kallon ta yayi kafin ya amsa da
“Na’am Baby bag!”
Ta ce,
“Alkawari nake son karike min koman wuya kar mu rabu kaji.”
Murmushi yayi, ya gyara kwanciyar sa. Yana kara fuskan tar ta.
“Alkawari na rike miki kuma koman wuya bazan rabu dake ba kinji.”
“Nagode!”
Kallon ta yayi yana kashe mata idanu kamar me jin bacci.
Kasa tayi da kanta.
“Wallahi rabuwar mu abu ce me wuya dan mun zama hanta da jini. Ko ‘da da uwa.”
Dariya ta saka tana girgiza kanta. Shima dariyar yake.
“Wallahi da gaske nake. Na fada miki duk abinda kika ji na fada daga zuciyata yake. Abinda zuciya ta take ji kenan baki na ya furta miki.”
“Na yadda da kai Yayanah. a zuciya ban da kamar ka komai nawa ya zama naka. Amman dan Allah kar ka yadani ka kula da soyayya ta. Dan kai dai na aminta dakai kuma na yadda da kai. Mun shaku mun saba Ya Aslam abin da ya rage kawai auren mu ne.”
Ta fada yana rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta.
“Oo please kicire kunyar nan cigaba da narka min zuciya mana.”
Ido ta zaro
“tayaya zan cigaba da narka maka zuciya. Yanzu ya zanyi in na narka maka zuciya.”
“Sai muyi amfani da taki ko?”
“A’ah muyi amfani da taka dai.”
“To cigaba ina jinki.”
“Kai Ya Aslam”
Kunnen sa ya kama yace,
“Yana jira zai kaiwa zuciyar ki abinci taci.”
Dariya ta saki.
“Ya Aslam kenan!”
“Allah yunwa take ji fa.”
“Toh Zan kasance me share maka hawaye a duk lokacin da zasu zuba zan hana su zuba. Zan kyautata maka in faran ta maka.”
“Allah tabbatar mana da Alheri, sannan nikai na bazan taba barin ki kiyi kuka ba.”
“Nagode!”
“Ba godiya a tsakanin mu.”
Murmushi sukayi gaba dayan su.
“Tashi kije kiyi Alwala kizo kiyi addu’ar bacci.”
“Toh!”
Ta fada tana tashi. Ban daki taje tayo alwala.
Addu’a tayi, yana jin ta har ta gama.
Wayar ya kashe, sannan ya kirata. Kamar yadda ya saba yi mata kissa Annabawa haka ya farayo mata har bacci ya dauke ta.
Washe gari ya kama asabar dan haka tin da ta tashi da asuba tayi sallah.
Ta fara gyara dakin ta, tin daga karkashin gado har su durowar ta duk da ba datti amman sai da ta gyare ta goge ko ina.
Sannan ta fita madafin su (kitchen) ba kowa a ciki wannan ya tabbatar mata da Mami na can gyaran daki.
Dan duk karshen sati sai sun gyare gida ko ina da ina tsab.
Wake ta auna tayi waje dashi. Ban garen masu aiki tayi.
Baba Lami ta sama zaune. Gaishe ta tayi, sannan ta tambaya ko Lubabatu na nan.
Kiran ta Baba Lami tayi. Lubabatu na ganin *Asam’u* ta saki murmushi.
“Ina kwana?”
“Lafiya lou.”
“Dan Allah daman waken nan zaki surfa min saboda kar na makara zan je isilamiyya.”
“Bakomai kawo.”
Ta mika mata. Ta juya ta fita.
Kunun gyada ta dama musu, sannan ta hau gyaran kitchen din nasu.
Sai da tagama gyara sannan Lubabatu ta kawo mata markaden.
Kayan hadi ta zuba sannan ta fara soya kosai.
Kosan kuwa yayi kyau dashi ya tashi abin sha’awa.
Tana gamawa ta gyara falon su, sannan ta jere kayan karin nasu a inda suke cin abinci.
Kitchen din ta gyara ta wanke duk abinda ta bata.
Dakin ta ta koma tayi wanka sannan ta shirya cikin riga da siket yan kanti.
Sai ruwan tokar hijab da ta dau wanda yake a wanke a goge dashi.
Dakin Dady tayi, ta gaishe dashi sannan suka sauko kasa, Mami ce ta sauko da Ya Buhari, suka gaisa. Sannan suka fara karya wa.
Suna gamawa ta mike ta haye sama. Hijab din ta! Ta saka wanda yake har kasa. Sai nikaf da ta saka kafar ta da safa.
Jakar ta ta dauka, ta fito.
“Mami da Dady na tafi sai na dawo.”
“To a dawo lafiya Allah bada sa’a”
“Ameen!”