RAYUWAR ASMAU CHAPTER 3

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 3

._

________________________

Asma’u sai sha biyu da rabi ta dawo. a gajiye ta dawo ga rana.

Tana shigowa gida Mami ta tare tana

“oyoyo ‘yar ta”

Murmushi tayi ta karasa gun Mamin ta, ta zauna a gefen ta. ta ce,

“Mami sannu da gida!”

“Yauwah Asma’u ya makarantar?”

Asma’u ta ce,

“Lafiya Alhamdulillah!”

Mikewa tayi ta ce,

“Mami bari naje na watsa ruwa.”

“Toh!”

Tayi sama, tana shiga ta ajiye jakar ta, ta cire kayan ta ta sakale su ta shiga bandaki.

Ta jima tana watsa ruwa sai da taji sanyi sannan ta cuda jikin ta.

Tana fitowa ta saka wata doguwar riga mara hannu.

Hijab ta saka ta tada sallah. Sai da ta idar sannan ta shafa mai ta shafa hoda.

Wayar ta dake ta kara tin tana bandaki ta dauka.

Yaa Aslam ne dan haka da sauri ta dauki wayar ta kara akunnen ta.

Sai da yai sallama ta amsa sannan ya tambaye ta ya makaranta. Dan yanzu ya kira Mami ta ce yanzu ta dawo.

Da wayar a kunnen ta, ta sauka kasa dan samar abu me sanyi.

Ice cream ta dauko a firij din dake kitchen din su, sannan ta dawo falo inda Mami take.

Wayar ta kashe tana kallan Mami ta ce,

“Mami Zafi bai yiba wallahi.”

Mami ta ce,

“Ranar da kika kwaso ce kinsan sha biyu lokacin tafi budewa.”

Ice cream din ta fara sha tana lumshe ido har ta EMgama ta kwanta.

Ta ce,

“Mami bari na dan yi bacci kafin anjima dan nagaji.”

Mami ta ce,

“Ai gara kina huta wa.”

Cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ta. Mami na zaune a gefen ta, ta zuba mata ido.

Mami bata san saboda me ba. Amman Asma’u na yawan bata tausayi.

Yanzu da tana baccin ma kallon ta kawai take tana dada jin kaunar ‘yar tata.

Asma’u ba dai hazaka ba sam ina ta tashi tin safe sai goman dare zata kwata. In kuma ta tashi da asuba bata kara rintsawa ga karatun su mai wahala. Amman kuma komai nata yana tafiya dai dai. Sai dai wani lokacin in karatu ya sako ta a gaba har ramewa take yi dan ko lokacin cin abinci bata samu.

Kafin la’asar ta tashi tayi sallah sannan ta dawo falo ta zauna tana danyin chatting a wayar ta.

Tana zaune taji sallamar Zainab da gudu ta mike tana rungume ta.

“Ah lallai yau Zee ce a gidan namu.”

Hararar ta Zainab tayi ta ce,

“Ke dallah a gaban Mamin.”

Ta dan daura mata hannu akan leben ta.

“Mami na kitchen bari na kirata ku gaisa mu tafi sama zaki fi sakewa.”

STORY CONTINUES BELOW

Hanyar kitchen tayi tana kwadawa Mami kira. Mami ta fito ta ce,

“Lafiya?”

Asma’u ta ce,

“Mami, Zainab ce ta zo.”

“Allah sarki sannun ta da zuwa ina zuwa.”

Ta koma kitchen din ta rage gas sannan ta fito.

A falo ta same su. Zainab na ganin Mami ta sauka daga kan kujera tai kasa da kai tana gaishe da Mami cikin girma mawa. Mami na tambayar ta su Maman ta.

Sai da suka gaisa Mami ta koma kitchen sannan suka koma sama.

Suna zama yar aikin su Asma’u ta kawo mata ruwa da lemo hadi da snacks.

Suna hira tana ci har basu san magariba tayi ba sai kiran sallah da sukaji kawai.

Ido Zainab tayo waje dasu ta ce,

“Nashiga uku salar me?”

Dariya Asma’u tayi ta ce,

“Mene magariba ce.”

Duka takai mata ta ce,

“Shine kike min dariya ko?”

“Sorry ta tashi muyi sallah ko?”

Ta mike ta shige ban daki alwala tayi sannan ta fito ta tada sallah.

Asma’u ma bandaki ta shiga tayo alwala tai sallah.

Suna idar wa Zainab ta mike. Kallon ta Asma’u tayi ta ce,

“Ai kya bari dai kici abinci Yaya ya dawo mukai ki gida ko?”

“Rufan asiri dare ai sai ya karayi.”

Hararar ta Asma’u tayi ta ce,

“Da yake a jeji kike ko? To in na fadawa Momin taki ana zaki kwana fa.”

Dariya Zainab tayi ta dauki jakar ta ce,

“Ni tashi muje.”

“Allah sai kinci abinci.”

Ta fada tana fita daga dakin.

Kitchen ta shiga ta hado mata abincin da sukai.

Tuwon semo ne miyar agushi taji nama sai kamshi take.

Sai lemon ginger da Mami ta hada musu. Diba tayi a babban faranti tayi daki dashi.

A zaune ta tadda Zainab tana shiga Zainab ta amshi kayan ta dire ta fara zubawa dan tai sauri ta gama su tafi.

Sai da taci ta koshi sannan ta mike ta wanke hannu. Kiran sallah isha’i taji wannan yasa tana fitowa ta tada sallah. Tana idar wa kuwa ta mike tayi waje.

Asma’u tabi bayan ta tana cewa,

“Ai kya bari nayiwa Mami magana ko?”

Tsayawa tayi ta na kallon Asma’u, kallon ta Asma’u tayi ta ce,

“Ga kujera ki zauna man.”

Zama tayi ita kuma ta shige dakin Mami. Mami na zaune tayi kwalliya kamar yadda ta saba ta tarbar Dady.

“Mami zata tafi!”

“Au har ta fito.”

“Eh!”

Asma’u ta bata amsa.

Leda Mami ta nuna mata ta ce,

“Dauki wacan ki kai mata ki dauki dubu biyu, ki bata kisa Baba ya kai ku ki rakata.”

“To Mami Allah kara budi da girma.”

“Ameen muje nai mata sallama ko?”

Suka fita tare Asma’u rike da ledar kayan kwalliya a hannun ta.

Sai da Mami tai mata sallama tare da godiya, sannan suka fita tare da Asma’u.

Suna fita suka tadda Yaa Buhari ya dawo. Asma’u ta ce,

“Yauwah kinga Yaya ya kaiki ma ko?”

Banza Zainab tai mata har suka karasa gefen sa.

Murmushi yake sakarwa Zainab dan shi bai ma kula da wata Asma’u ba.

Asma’u dake gefe ta ce,

“Ah lallai soyayya!”

Duka ya kai mata. Tai sauri kaucewa. Tana dariya.

“Kaga Yaya muje ka kaimu dare nayi.”

Gaba yayi Zainab tabi bayan ta shi ya bude mata mazaunin ta gaba ta shiga.

Asma’u ta tsaya ta ce,

“Ai kuwa nima sai an bude min in ba haka ba bazan raka ku ba.”

Rankwashi Yai mata ya ce,

“In na bude me zai cijeni.”

“Babu!”

Asma’u ta fada tana zama a cikin motar.

Suna tafe suna hira suka bar Asma’u ganin haka yasa ta dauko waya ta kira Yaa Aslam.

Waya suke tana bashi labarin zuwan Zainab da abinda suke mata.

Hakuri ya bata ya ce,

“Dadin ta kema kina da wanda zaki hirar dashi ko?”

“Eh man.”

Daga nan suka dinga waya har aka zo gidan su Zainab.

Sai da Asma’u ta rakata gida ta gaida Momin ta sannan sukai sallama Momi na mata godiyar kayan da Mami ta bata.

A mota ma wayar ta taci gaba dayi tabar Yaa Buhari yana ta surutun sa shi kadai.

Sai da ta gama waya da take yai ta mita ta ce,

“Kaji Yaya kai lokacin da kukai min banza me nace nima ramawa zanyi.”

Dariya yayi ya ce,

“Wai wane wannan sirikin nawa ne?”

“Bazan fada ba.”

Dariya yayi ya ce

“kinsan dai dole na sani ko?”

“Naji lokacin ka sani.”

Daga haka suka cigaba da hirar su abin sha’awa har suka koma gida.

A falo suka tadda Dady suka masa sannu da zuwa sannan ssuka ci abinci.

Sannan kowa yayi daki sa dan yin bacci.

Kamar yadda ta saba haka tana kwanciyya Yaa Aslam ya kira.

Sai da sukai waya sannan sukai awala tai addu’a suka kwanta yana mata tarihin sahaban mazon Allah (SAW)

Yau kamar kullum tin asuba bata koma bacci ba sai da ta gama komai tayi wanka sannan ta shirya cikin jar doguwar riga mai dogon hannu. Sai bakin mayafi da ta yafa.+

Bakar jaka ta dauko ta ciro littafan ta ta zuba a ciki. Turare ta fesa ta dauki bakin cover shoe ta saka ta tafi dan yiwa Dady sallama.

Dady ya amsa yana kallon ta ya saki murmushi ya ce,

” *Husnah* kinyi kyau!”

Murmushi tayi ta zauna suka gaisa, anan yake fada mata ginin asibitin da ake mata ya kammalu dan haka zai je yayo order kayan da za’a zuba.

Asma’u baki yaki rufowa sai murmushi take tana ta godiya ga Dady.

Ba abinda Dady yake so kamar yaga ya farantawa iyalan sa.

Hannun ta ya kamo ya ce,

” *Husnah* ki kara gwazo ba abinda bazan miki ba in dai bai fi karfi na ba kome ne indai kina so zan miki.”

Murmushi tayi ta ce,

“Dady nagode!”

Abinci ta hada masa, kallon ta yayi nan da nan ta gane abinda yake nufi dan haka ta fara hada tea.

Agogo ta kalla taga har karfe takwas tayi. Yau za’ai submitting assignmenat din Sir Sabir gashi ya ce in takwas da rabi tayi monitor yakai masa.

Tana rasa dalilin da yake sata tana yawan makara.

Ba yadda zatai yiwa Dady haka ta zauna ta dinga cusa abinci har ta gama ta mike.

Kudi ya bata ta amsa tana godiya tai masa sallama ta yi dakin Yaa Buhari,

Yau taci sa’a ta same shi yana shiryawa. Murmushi tayi tana murna zai rage mata hanya. ta ce,

“Na Anty Zee barka da safiya!”

Kallon ta yayi ya ce,

“Barka kadai ya kika tashi?”

Ta ce,”

“Lafiya Alhamdulillah! Yaya dan Allah….”

Sai kuma tayi shiru

Kallon ta yayi ya ce,

“Dan Allah me?”

Kai ta dan sosa tace,

“Wallahi na makara gashi malamin mu ya ce Takwas muyi submitting din Assignment.”

“Ke kika sani!”

Ya fada yana taje kan sa.

Kallon sa tayi ta kalli agogon dake hannun ta. Ido ta zaro ta ce,

“Inna illahi wainna illahir rajiun!”

Ta fada tana fashewa da kuka.

Kuka take sosai, tana bubbuga kafa a kasa kai kayi zaton dukan ta akayi.

Kallon ta Buhari ya tsaya yi, dan inda sabo ya saba da halin Asma’u na shagwaba.

Sai da yaga da gaske dai take sannan ya mike ya kamo ta.

Kukan ta cigaba dayi shi dariya ma ta bashi.

Da wannan kukan da ta tsaya yi ta dauki kusan minti uku dama zuwa tayi Baba ya kai ta amman ta tsaya.

“Yi shiru yi shiru, shige muje!”

Ya fada yana daukar hular sa ya saka

STORY CONTINUES BELOW

Hannun ta ya kama sukai dakin Mami, gaisawa sukai ta tsaya kallon Asma’u ta ce,

“Wannan kuma fa?”

Ta fada tana nuna Asma’u. Dariyar Buhari ya danne ya ce,

“Shagwaba daga ta makara sai kuka.”

Mami ta ce,

“Ai Asma’u akwai wasa wallahi kasan Allah tin asuba bata komawa amman da ta gama taya ni aiki ta shiga wanka sai ta dauki kusan awa tana wanka bare shiryawa kuma tayaya baza ta makara ba.”

Murmushi Buhari yayi ya ce,

“Uhm Ai “Asma’un Dady sai Dadyn. Mami mun tafi sai mun dawo.”

Ya kama hannun ta suka fice Asma’u na dagowa Mami hannu.

Murmushi Mami tayi itama ta daga mata hannu. A ranta tana cewa,

“Asma’u kenan.”

A mota ma haka ta dinga a zalzala shi amman ina tin a gida takwas da rabin ma tayi.

Tana zuwa taga da malami a ajin a haka ta shiga ta zauna suka dinga amsar lecture.

Sai da malamin ya fita Zainab ta karaso gefen ta tana dafa ta.

Kallon ta Asma’u tayi fuskar ta dauke da damuwa. Ta ce,

“Kiyi hakuri ki tashi muje ki kai masa ki bashi hakuri.”

Baki Asma’u ta rike ta ce,

“zai amsa.”

Zainab ta ce,

“Insha Allahu.”

Agogon hannun ta Asma’u ta kalla ta ce,

“Sis kinga fa har sha daya.”

“Tashi muje insha Allahu zai amsa.”

Mikewa Asma’u tayi jiki a sanyaye suka nufi wajen office din malamai.

Suna zuwa gefen office din Zainab ta ce,

“Kije ki fito ina jiran ki.”

Fuska Asma’u ta bata zatai magana Zainab ta ce,

“Kiyi hakuri kisan dai malamai basa son rakiyar nan ko?”

Kai ta gyada ta tsaya ta kasa tafiya. Zainab ta ce,

“Haba Asma’u kije man.”

Kamar bazata je ba kuma sai ta fara tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Zainab na kallon ta tasan halin Asma’u zuwan ne bata sonyi. Take wannan tafiyar kamar me.

Murmushi tayi ta karasa karkashin wata bishiya ta zauna.

Asma’u kuwa ji take kamar ta juya gaban ta sai dukan uku uku yake a haka ta karasa har kofa office din da aka rubata *Sabir Marzuk*

A hankali tayi knocking wanda ita kanta ba dan ita tayi ba da bazata ji ba.

Sai da tayi irin knocking din nan sau uku sannan ta samu tayi da dan karfi.

Izinin shiga ya bayar. Handle din kofar ta murda a hankali ta bude.

Wani kamshin turare hade da sanyi me dadi taji yana tashi.

A hankali ta kutsa kai ciki tana yin sallama kamar bata so.

“Assalamu Alaikum!”

Dago kai yayi jin muryar ta. Kallon ta ya tsaya yi kafin yai saurin kawar da fuskar sa, ya amsa da

“Wa’alikum salam!”

Kai tayi kasa dashi ta kasa magana. Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu.

Shi kam kallon ta yake kawai yana mamakin ta.

Tsaki tayi a zuciyarta ta ce,

“To me zan ce?”

Da kyar ta iya dago kanta ta ce,

“Uhm uhmm Sir dan Allah ina neman taimakon ka ne?”

Kallon ta shima yayi ya ce,

“Ok!”

“Uhm Uhm!”

Sai kuma tayi shiru.

Murmshi yayi ya ce,

“Ki saki jikin ki me zan taimaka miki dashi.”

Yai maganar cikin harshen turanci.

Dan sanyi taji ji a ranta da bai mata rashin mutunci ba.

Dagowa tayi suka hada idon. Idon ta Cike Da kwalla kamar zatai kuka. kallon ta yayi yai saurin kawar da fuskar sa. ta ce,

“Sir Assignment nazo nai submitting”

Kallon ta ya tsaya yayi, yana mamakin ta, ‘wai Assingment tazo kawo wa.”

Asma’u ta ce,

“Sir Kayi hakuri na zo a makare ne.”

Ta fada murya na rawa. Hannu ya mika mata kawai.

Jakar ta tai saurin a jiyewa kan kujerar dake gaban table din sa.

Dauko takardar tai a cikin wani littafi ta mika masa.

Amsa yayi ya zubawa sunan ta ido.

*Asma’u Suleiman* rubutun ya kalla yaga kamar computer ce ta rubuta shi.

Sai da ya kai hannu ya shafa ssanan ya kara kallon sunan ya ce

” *Asma’u Husnah* “

Wata faduwar gaba Asma’u taji tai sauri dago idon ta.

Dan duk duniya a wadan da ta sani take rayuwa dasu mutum biyu ke kiran ta da *Husnah* ko su ce, *Asma’u Husnah* sai kuwa yanzu da taji shi ya ambata.

Sunan yai dadi da yadda ya kira ta sai taji kamar Yaa Aslan ne ya kira ta.

Kai kadai ta gyada masa, ya ce,

“Zaki iya tafiya.”

Jakar ta ta dauka, ta ce,

“Nagode!”

Ta juya a hankali ta bar office din.

Zainab na hango ta ta mike ta ce,

“Ya dai ya amsa.”

Kai kadai ta gyada mata ta ce,

“Muje kar malama safiya ta shiga.”

Suka kama hannu suka tafi.

Sai da aka tashi suka fito sukai sallah suka yi wajen Baba da yazo daukar ta.

Munasha ce ta karaso gun da sauri tta ce,

“Hae Babies!”

Da sauri suka juya. Amsa’u ce ta danyi murmushi ta ce,

“Sannu!”

Zainab kuma ta hade rai tana yin gefe.

“Baby an tashi ko ina Yayan ki?”

Amsa’u ta ce,

“Yana nan lafiya.”

Munasha ta ce,

“Dan Allah wane irin aiki yake yi ne?”

Asma’u ta ce,

“Likita ne!”

Ido Munasha ta bude ta ce,

“Wow kace gidan ku kwari ne, amman ya dace likita. in kinje ki gaishen dashi.”

“Zai ji insha Allah!”

Ta fada tana juyawa.

Munasha ta ce,

“Tnc bye!”

Ta juya kawar ta na bin bayan ta.

Zainab ce ta karaso ta ce,

“Ke baza ki daina kula ta ba ko?”

Fuska Asma’u ta marairaice ta ce

“Ya zanyi kina ganin dai ita ke kula ni.”

Kallon ta Zainab tayyi ta ce,

“Sai da safe.”

Ta shige motar gidan su. Kallon ta Asma’u tayi itama ta shige mota tana murmushi.

*Yan uwa dan Allah ina barar addu’a ku in kunyi sallah ku sani a addu’a Allah biya min bukatuna na alheri*

*Mutane da yawa na kira da min text na yadda suke jin dadin kasancewa dani nagode Allah ya bar kauna*

Fatan alheri ga dukkan yan uwa musulmai tare da murnar shiga cikin sabuwar shekara.

Tana zuwa gida ta shige tai wanka sannan ta dawo wajen mami dake falo.

Mami ta ce,
“Ya makaranta?”

“Mami makaranta lafiya Alhamdulilah!”
“Allah taimaka!”

“Ameen! Mami Dady bai dawo ba, me kika dafa.”

Mami ta ce,
“Shinkafa da miya.”

Mikewa Asma’u tayi ta dauki waya dan taji yanzu Dadyn ta zai dawo ko sai anjima.

Yana dauka ya ce,
” *Husnah* ya makarantar ne?”

Murmushi tayi ta ce,
“Dady har na dawo kuma Mami ta ce baka dawo ba yanzu zaka dawo ko sai aajima.”

Murmsuhi Dady yayi ya ce,
“Sai anjima.”

Ta ce,
“To Dady bari na kawo maka abinci kar ka ci na waje kaji.”

“To *Husnah* baki gaji ba.”
Kai ta girgiza ta ce,
“Ban gaji ba Dady.”

“Shikenan kisa Baba ya kawo ki sai kin zo.”

“To!”
Ta kashe wayar.

Kitchen ta shiga ta hada musu abinci a katon basket sannan ta dauko jug ta zuba lemon da mami ta hada.

Sai da ta gama hada komai sannan ta fito ta hau sama.

wanka tayi ta saka atampa dinkin riga da siket ta dauki hijab iya gwiwa ta saka.

Kasa ta sauko hannun ta rike da wayar ta.
Tana sauka ta ce,
“Mami sai na dawo!”

Mami ta ce,
“A dawo lafiya.”

Ta duko baske ta fita. Baba na gganin ta ya ttaso ya ce,
“Sai ina kuma?”

Ta ce,
“Wajen Dady.”

Ya ce,
“To muje!”

Yai gaba tabi bayan sa. Suka dau hanya. Basu dade ba suka karasa office din Dady.
Suna zuwa wani masinja yazo ya dauki basket din yayi offfice din Dady.

Tana shiga ta dauki kudi a wata loka a cikin office din ta mika masa.

Godiya ya dinga yi dai dai fitowar. dady daga toilet.

Karasawa tayi tana cewa,
“Dady sannu ya aiki?”

Dady ya ce,
” *Husnah* ke zanwa sannu kinje kinsha makaranta..”

Murmushi tayi ta ce,
“Dady yau ba gajiya kaga biyu mun gama komai.”

“To Alalh bada sa’a.
“Ameen Dady!”

Ta dauki basket din ta fara zuba masa abinci.

Sai da yaci ya koshi sannan ta ce,
“Dady bari naje wajen Yaya.”

“To a dawo lafiya.”
Ta fita.

Knocking tayi a office din sa amman shiru.

Tura kofar tayi kawai sai gannin shi tayi kwance ya lumshe ido yana amsa waya.

STORY CONTINUES BELOW

Dagowa yayi ya zubo mata ido, ta ce,
“Ina ta bugu yanzu da wani ne ya zo da sai dai ya koma.”

Hannu ya daura akan lips dinsa ya ce,
“shitt!”

“Naki nayi shiru.”
Ta fada tana dire masa fulas din a gaban sa tayi kan kujerar ssa ta office ta zuna.

Juyi yake yi akan kujerar tana murmushi a ranta ta ce,
“Wani lokacin tana nata office din tana duba mara sa lafiya.”

Dariya ta saki ta ce
“Yaya dan Allah kallo ni a office dina.”

Baki ya tabe ya ce,
“Ai ba kyau kikai ba.”

Dariya tayi ta ce,
“Kyan kaga nayi.’

Ta mike ta ce,
“Uhmm bari naje na taya Dady aiki.”

Ta fice ta koma office din Dady. Gyara masa ta hau yi ta gyara masa ko ina ta share sannan ta zauna.

Dady ya ce,
” *Husnah* kenan sarkin aiki mijin ki ya huta komai kin iya ga tsabta.”

Murmushi kawai tayi ya zaro wayar sa ya ce,
“Zo kiga kayan da aka turo sun miki naje na karbo ko wasu kike so.”

Ya fada yana dubo pics din. Matsowa tayi gefen sa ta zauna.

Mika mata yayi ta dinga kallon kayan ta ce,
“Masha Allah Dady sunyi.”

Dady ya ce,
“Kin tabbata.”

Kai ta gyada masa. Ya ce,
“Shikenan nan da sati biyu nake son tafiya. Da ba ckul da mun tafi tare.”

“Wallahi kuwa?”
Haka suka zauna Dady na aiki tana taya shi hira har karfe shida tayi.

Buhari ne ya shigo office din ya ce,
“Dady ni zan tafi sai kun taho.”

Dady ya ce,
“To muma fitowar zamuyi.”

Gefen Asma’u yayi ya mata rada. Hararar sa tayi ta mike.

“Dady muje””
Ta yi gefen sa.

Mikewa Dady yayi ta kamo hannun sa suka fito.

A hanya kafin su sauka sai sallama akewa Dady jama’a sai gaishe shi suke.

Dady mutum ne mai son jama’a da taimako kowa nasa ne.

Dady yana da mutane sosai dan duk wanda ya kawo.kuka sa sai ya taimaka masa.

Suna isa gida ana magariba dan haka parking kawai sukai suka yi alwala suka tafi masallaci.

Asma’u kuma ta yi cikin gida sama ita ma tayi tai alwala tai sallah ta zauna har akai isha.

Sanna ta sauko. Su Dady ta gani har sun shigo Mami na gefen sa.

Mikewa sukai suka hau sama Dady ya watsa ruwa ya saka jallabiyya sannann ya sauko suka ci abinci

Karfe Tara Asma’u tayiwa Dady sallama. sannan ta matsa gun Mami shima tai masa.

Wajen Yaya Buhari tayi, tana murmushi kafin ta karasa ya mike.

Kallon sa tayi ya ce
“Lafiya?”

Hararar ta yayi ya ce,
“Abu zanje na siyo.”

Kallon sa tayi ta ce
“Dan Allah Yaya ka tahon da ice cream dan Allah!”

Wajen Dady yayi ya duka ya ce zai fita yanzu zai dawo sannan ya kalli Mami ya ce,
“Mami me zan taho miki dashi?”

Mami ta ce,
“Ni ba komai a dawo lafiya.”

Ya juya zzai tafi Asma’u ta saki kuka. Da sauri ya juyo Dady ma ya mike da sauri.

Mami kuwa da tasan halin ta yasa ta dauke kai. shi wanda yai mata laifin yafi kowa son jin me akai mata.

Gun Dady tayi ta ce,
“Dady ba Yaya Buhari bane, nace ya siyon aabu yai min banza.”

Kai Dady ya dago ya kalle shi. Shi kuma ya ce,
“Haba kanwata ai naji wasa fa nake miki.”

Kai ta dago tana goge hawaye ta ce,
“Da gaske?”

Kai ya daga mata ta ce
“To a dawo lafiya. Ni sai da safe.”

Ta fada tana mikewa tayi ta ce,
“Dady Sai da Safe. Mami sai da safe.”

Suka ce,
“Allah tashe mu lafiya”
Ta nufi dakin ta.

Yaya Buhari kuwa ajiyar zuciya ya sauke, ya fita.

Mami ta ce,
“Allah Dadyn Asma’u ku kuke sa Asma’u kara sa ta gainin yarinya ce. Yarinyar nan fa girma take ji abinda tayi sai kace yar shekara biyar.”

Murmushi Dady yayi ya ce,
“To in ban kula da Asma’u ba da wa zan kula.”

Murmushi Mami tayi ta ce,
“Ai shikenan tai ta zama aa yarinyar kuwa “

Murmushi Dady yayi ya ce,
“In girman yayi zata girma ne amman yanzu nawa Asma’un take. Dan dai tayi nisa a karatu ne kike ganin girman ta amman waasu kamar ta ma suna secondary school.”

“Ai kai dai baza ka taba yadda ba “
Daga haka suka cigaba da hirar su.
Asma’u kuwa tana shiga daki tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin ta.

Kan gado ta kwanta tana daukar wayar ta. Missed call din sa ta gani. Ido ta bude ta tafi kiran ta.

Da sallama ya dauki wayar. Ido ta lumshe jin muryar sahibin ta.

Kwanciyya ta gyara sannan ta amsa sallamar tata.

“Baby na kina lafiya ya gida da makaranta?”
“Lafiya lou Yaya na, ya su Momy da wajen aiki?”

“Duk lafiya Alhamdulilah!”
“Masha Allah!”

” *Husnah* tin dazu nake kiran ki. zan zo wani aiki Kano nake son na fara fada miki.”

Da sauri ta mike ta ce,
“Yaya dan Allah da gaske?”

Kai ya gyada kamar yana ganin ta ya ce,
“Da gaske zan zo nayi wata daya ne.”

Murmushi tayi ta ce,
“Kai Alhamdulilah Allah kawo ka lafiya amman naji dadi wallahi. Yaushe zaka zo?”

“Eh nan da sati biyu zan taho.”
Murmushi tayi ta ce,
“Allah nuna mana.”

“Ameen!”
Ya amsa.

“Yauwah Yaya gobe zamu yi test ina son ka sani a addu’a.”
Murmushi yayi ya ce,

“To Allah bada sa’a amman dai ni bana jin ki *Husnah* yanzu ma kafin ki kwanta ki dan duba littafin kinji.”

“Insha Allahu da asuba ma zan kara dubawa.”
“Yauwah Allah bada sa’a!”

“Yanzu ki dauko littafin kiyi karatun awa daya zan kira ki anjima.”
“To!”

Ta kashe wayar. Mikewa tayi ta dauko jakar ta.

Test din Sir Sabir zasu yi gobe dan haka ta kuduri aniyar gobe da wuri zata fita.

Sai da ta gama karatun kamar yadda Yaa Aslam ya ce, tayi sannan ya kira ta.

Alwala yasa tayo ta shiga tayo tazo tai adduu’a ta kwanta.
Karfe sha biyu Mami ta leko dakin taga Asma’u kwance akan gado. Addu’a tai mata ta tofa masa sannan ta fice.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *