RAYUWAR ASMAU CHAPTER 4

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 4

Washe gari kamar yadda ta tashi tin asuba ta tashi.+

Sallah tayi ta zauna tai karatun al kur’ani sannan ta janyo littafin ta ta kara dubawa ta jima tana duba littafin sannan ta mike ta sauka kasa. Mami ta dan kamawa abubuwa ssannan ta koma sama.

Wanka tayi ta shirya cikin wata maroon kalar doguwar riga mai dogon hannu.

Golding din takalmi da jaka ta dauka sai bakin hijab da ta saka iya kar sa kirji.

Ba karamin kyau tayi ba fuskar ta tayi fes a ciki.

Idonun ta sun kara gaske da girma girar nan tata a kwance luf luf. Leben ta sai kyallin man lebe yake.

Dakin Dady ta shiga suka karya sannan tai musu sallama ta fito ta tafi dakin Ya Buhari.

Yana zaune a gaban system ta same shi. Karasawa tayi ta ce,

“To su Yaya me ake aka tashi da sasafen nan.””

Bai kula ta ba. Dan durkusawa tayi ta gaishe shi. amsawa yayi yana dagowa ya kalle ta.

Baki ya tabe ya ce

“Baki kyau ba.”

Murmushi tayi ta ce,

“Kyan kaga nayi.”

“Ahakan?”

Kai ta gyada masa.

“Uhmm dauki abonki afirij.”

Ya fada yana nuno mata firij din.

Gun firij din tayi ta bude. Ice cteam ta gani a ciki dayawa. biyu ta dauka ta ce,

“Yaya in na dawo na dauki sauran.”

Kallon ta yayi ya ce.

“A dawo lafiya.”

Sannan ta fita. Dakin Mami taje tai mata sallama sannan ta sauka kasa.

Baba yana ganin ta ya taso yayi wajen motar ya fito da ita.

Sai da suka gaisa sannan ta bude gidan baya ta shiga.

Kiran Yaa Aslam ne ya shigo dauka tayi,

Bayan sun gaisa yake cewa “amman dai tana ckul ko?”

“Aah Yaya yanzu dai zan tafk.””

“Amman dai kinsan kin makara a yadda kika fadan kina da test ko?”

“Ah haba dai!”

“Eh man tara saura minti goma. Minti goma zai kai ki ckul ne.”

“Insha Allahu!”

“To Allah bada sa’a sai kin dawo ki turon pics din ki ina jira.”

Ta katse wayar selfie ta dauka ta tura masa sai anan taga ashe dai da gaske Yaa Aslam yake ta makara ta tabbata nan da minti goma da kyar zasu karasa.

Addu’a take Allah yasa kar ya shiga har sai ta shiga.

A hankali Baba ya dinga jan su har suka karasa makaranta.

Lokacin tara da minti goma. Da sauri ta fita daga motar.

Hango shi tayi yana nufar ajin cikin takun kasaita yake tafiya.

Yana sanye da golding kala shadda ya saka brow kalar takalmi da hannun sa rike da waya ya kara a kunne daga gani amsawa yake.

Ba kara min kyau yayi ba. Fatar sa ta kara kyau da sheki. Gashin kansa ya kwata luf luf dashi.

STORY CONTINUES BELOW

Ganin ya karasa ajin ma. yasa ta tsaya daga inda take hangen sa.

Waje ta samu ta zauna daga gefen ajin ta kifa kanta akan jakar ta ta fashe da kuka.

Ta dade tana kukan dan har karfe goma bata dago ba tana ta shesheka.

Karfe goma dot ya fito daga ajin rike, da takardu a hannun sa. Yana karasowa inda take akai kiran wayar sa.

Daukar wayar yayi, ya kara a kunnen sa yana kallon Asma’u da ta kifa kai.

A wajen ya tsaya ya amasa waya, tana jin yadda yake maganar a hankali amman ta kasa dagowa.

“Yanzu zan karasa office din kin karaso ne?”

Ya tambaya.

“Ok!”

Kawai ya ce ya kashe wayar.

Sai da ya kara kallon ta sannan ya bar wajen. yana barin wajen zainab ta karaso tana dago kanta.

“Kuka!”

zainab ta fada tana share mata hawaye.

“Ba dole nai kuka ba. Wannan course din kar ya jawon Matsala fa”

Ta fada tana kara fasa wani kukan.

“Haka ne, amma kinsan Sir Sabir yana da sauki kai da kin shigo zai iya barin ki.”

“Haba Zainab sau nawa nake makara yake kyale ni so kike a fara kawo wani zargin bayan kinsan baya bari a shigar masa aji duk wanda ya makara daya ga ya shiga juyawa yake.”

“Kinga bar wannan zancen kije gun sa, kawai ki baahi hakuri kiji me zai ce,

ya kara bada wani Assignment din ma in bai miki ba kinga kina da assignment balantana ma insha Allahu zai miki.”

“Uhmm fa Zainab kar naje yaki min. Ni dai wallahi na hakura”

“Dallah can tashi muje!”

ta kamo hannun ta suka nufi office din sa.

A bakin office din ta bar ta. Yauma kamar rannan ta dade tsaye a kofar amman ta kasa kwankwasa kofar

Cikin sanda ta dan kwankwasa. Izinin shiga ya bada. wata faduwar gaba ce ta sameta.

A hankali ta daura hannun ta akan kofa, ta murda ta budo. Nan ma ta dau minti biyu kafin ta tura ta shiga.

Tana shiga taji wani sanyi me ddi hade da kamshin turare na dukan ta.

Tsayawa tayi a gun kafin tayi sallama. wata yarinya dake gefen sa, tana bude masa fulas din abincin data kawo ta zuba mata ido.

Yarinyar zata yi shekara goma sha shida zuwa sha bakwai Kyakyawa ce suna kama da Sabir kamar kanwar sa.

‘Yar yayar sa ce tazo musu hutu shine Mamah ta aiko ta, ta kawo masa abinci dan tasan halin sa da kyar zai ci wani abu gashi ya fito bai karya ba.

Kallon Sabir yarinyar tayi ta daga masa kai.

Ya ce,

“Uhmm Maryam zo ki tafi nagode kar Mamah ta tafi ta barki.”

Maryam ta ce,

“Kai Uncle wallahi Mamah ta ce, in tabbatar da kaci tukkunna “

murmushi yayi wanda ya kara fitar da kyawun sa ya ce,

“Da yake, ni yaro ne ko. Ko ni yaro ne, ina uncle din ki zaki ce sai naci abinci ne, maza zo ki tafi kice naci kinji.”

Ya fada yana daukar dankalin da aka soya a cikin kwai da attaruhu da albasa yana ci.

Gefen kuma kunun gyada ne da yaji madara.

Jakar ta ta dauka ta ce,

“Allah Uncle haka zan ce baka ci ba.”

Tayi gefen Asma’u dake tsaye tana jin su.

“Sannu!”

Ta fada tana mika mata hannu.

Dagowa Asma’u tayi ta kalli yarinyar kamar su daya da Sabir.

Dan murmushi Asma’u tayi ta mika mata hannu ita ma suka gaisa.

Murmushi Maryam tayi ta ce,

“Sunana Maryam Suleiman ni ‘yar yayar Uncle Sabir ce.”

Kallon ta Asma’u tayi da idon ta da suka canja kala ta dan yi murmushi ta ce,

“Ni kuma Asma’u Suleiman!”

Maryam ta ce,

“Lah suna Baban mu daya amman wallahi Asma’u kin burge ni kawai naji ina sonki.”

Murmushi Asma’u tayi ta ce

“Nagode sosai.”

Sabir dake zaune yana cin dankali yana kallon su ya ce,

“To Maryam kije kar Mamah ta tafi ta barki dai Allah ke kadai zaki zauna a gida har magariba.”

Sakin hannun Asma’u tayi ta ce,

“Na tafi sai nazo gun ki wata rana.”

Murmushi Asma’u tayi ta daga hannu tana mata bye bye har ta fita.

Kai ta juyo ga sabir da ya zuba musu ido sai fitar da murmushi yake

Tana juyowa ya mai da kan sa ga abinda ke gaban sa.

Asma’u ta ce,

“Sir dan Allah ka taimaka min!”

“Dame fa?”

Ya fada yana cin dankalin sa cikin kwanciyyar hankali.

“Sir Test wallahi makara na yi shiyasa “

Bai dago ya kalle ta ba ya ce,

” *Husnah* wai ke kullun sai kin makara!”

Da sauri ta dago kanta jin sunan da ya ambata.

Ido suka hada wannan yasa tai saurin dauke kan ta.

“Ji idon ki me ya same shi? Kuka ko?”

Kai ta girgiza.

“To mene?”

“Ba komai.”

” *Husnah* baki ban amsa ba. Me yasa kike makara?”

Shiru ta karayi.

“Tin yaushe kike tashi?”

Ya tambaye ta.

Asma’u ta ce,

“Asuba!”

Kai ya jinjina ya ce,

“Me kike yi har kike makara?”

“Ba komai!”

“Ba komai amman kuma kike makara?”

Kai ta gyada.

“Ki fadan abinda kike in kika tashi tin asuba.”

Kasa tayi da kai ta ce,

“Mami nake dan tayawa aiki sai nai shirya. Kuma in nace bazan karya ba sai Dady ya zaunar dani sai naci. daga nan sai naje na tashi Yaya Buhari na gaishe shi na taho makaranta.”

Murmushi yayi jin yadda take maganar cikin shagwaba. ya ce,

“Ku nawa ne a gidan ku?”

“Daga Dady sai Mami, sai Yaya Buhari sai ni!”

Ta fada tana wasa da hannun ta.

“Kina da kanwa ko kani?”

Kai ta girgiza ta ce

“A’ah!”

Ya ce,

“No wonder ashe shiyasa kike shagwaba ko dan kece autah ko?”

Fuska ta dan bata tayi shiru. Ya ce,

“Eh mana. In ba haka ba menene na kuka dan baki shiga class ba.”

Shiru tayi ya ce,

“Dauko takarda.”

Tai saurin ajiye jakar ta tana daukar wata takarda.

Kujera ya nuna mata ya ce,

“Zauna!”

Ta zauna. question din ya karanto mata ta rubuta.

Abincin sa ya cigaba da ci cikin kwanciyyar hankali. Sai da ya gama ya koma cikin office din inda aka zuba masa wasu hadadun kujeru da kayan kallo.

TV ya kunna ya rage volume

TV ya kunna ya rage volume yana kallo yana kallon ta sai rubutu take. Cikin minti latalin ta gama ta mika masa. Ta ce
“Nagode!”
“Uhmm please ungo amson maltina a cafeteria.”
Kin amsar kudin tayi tace zata siyo masa.
Kai ya girgiza ya ce,
“A’ah nagode karbi ki siyon ki siyo kema.”
Amsa tayi ta fice ta bar jakar ta agun. Tana fita zainab ta taso ta ce,
“Ya akayi?”
Murmuahi tayi ta ce,
“Yayi min. Maltina zan siyo masa wai.”
Suka wuce cafteria suka siyo masa sanna suka dawo.
Sabir kuwa Asma’u na fita ya bita da kallo sannan ya lumshe ido.
A ransa ya na fadin.
“Allah ka dauran abinda zan iya dashi.”
Yana mamakin duk rashin son maganar sa inda ya zauna yana tai mata wadan nan tambayoyin.
Murmushi yayi tuno yadda take bashi amsar su.
Yana nan zaune yaji knocking din ta. Izini shiga ya bata ta shigo.
Tana shigowa ta mika masa maltinar sannan ta dauki jakar ta ta kara masa godiya ta juyo zata fita
” *Husnah* “
Ya kira sunan ta.
Juyowa tayi, table ya nuna mata ta dawo tayi wajen.
Kallon sa tayi ta ce,
“Me zan miko maka?”
Murmushi yayi ya ce,
“Dauki wannan fulas din kije kici.”
Kai ta girgiza ta ce,
“Nagode sir!”
Hararar ta yayi ya ce,
“Nace ki dauka ko?”
Da sauri ta dauki fulas din ta ce,
“Nagode!”
Ta fice da sauri. Murmushi yayi ya dauki maltinar ya fara sha yana lumshe ido.
Can ya mike ya dauki paper da tayi rubutu a jiki.
Rubutun ta mai kyau ya bayyana karantawa ya fara yi yaga duk tayi dai dai.
Lallai yarinyar tana da kokari da haka a assignment din ta ma tafi kowa marks.
Tana fita ta mikawa Zainab fulas din hannun ta. Amsa tayi ta ce,
“Wannan kuma fa?”
“Wallahi Sir ne wai dole sai na amsa.”
Budewa zainab tayi kamshi ya doki hancin su.
Anan suka tafi cafeteria suka siyo lemo suka wuce aji suka ci.
Fulas din Asma’u ta wanke ta ce,
“In zai tafi na mika masa.”
Anan take bata labarin Maryam yar gidan Antyn Sir Sabir.
Zainab ta ce,
“Kace yau kin hadu da yar uwa irin ki mai magana “
“Dallah ni ina da surutu ne.”
Dariya Zainab tayi ta ce,
“Ke zan tambaya. Allah yarinya jibi ki fito da wuri dan zai amshi assignment ba ruwana.”
“Insha Alah takwas ma na fito.”
“Alah yasa.”
“Ameen!”
Suna zaune da yamma bayan sun gama lecture tana jiran fitowarsa taga shiru shiru gashi har anzo daukar Zainab wannan yasa ta nufi office din shi.
STORY CONTINUES BELOW
Knocking tayi. Yana ciki a kwance ya kasa tashi ya tafi gida duk jikin sa ya mace.
Jin knocking din ya gane nata ne dan haka ya mike kawai ya dauki jakar sa da basket din da Maryam ta kawo masa abinci.
Kofar ya bude sukaci karo da juna baya tayi zata fada yai saurin riko ta ta dawo jikin sa.
Da sauri ya dago ta yana fadin.
“Sorry!”
Baya ta ja a hankali ta ce,
“Ba komai. Daman fulas din ka na kawo maka.”
basket din ya mika mata ya ce,
“Muje na saka a mota.”
Ya rufo office din ta biyo bayan shi. A hankali yake tafiyar itama tana biye dashi har suka karasa wajen motar.
Kujere me zaman banza ya bude ta ajiye masa fulas din tai masa godiya ta juya zata tafi,
” *Husnah* “
Ya kira sunan ta.
Juyowa tayi, ya ce,
“Kizo na rage miki hanya man.”
Kasa tayi da kanta ta ce,
“Lah sir nagode nasan anzo dauka ta ma.”
“Oh sai anjima!”
ya shiga mota
Hannu ta dan daga masa ta juya ta nufi gun drivern su.
Shiga tayi suka wuce a gida. Tin a mota suke waya da Yaa Aslam har ta karasa gida basu gama ba.
Ganin Mami a falo yasa ta tsinke wayar ta fada kan ta tana cewa
“Wash!!”
Mami ta ce,
“Ji zaki karya ni “
Murya Ta shagwabe ta ce,
“Mami na gaji.”
“Kije ki watsa ruwa ki dan kwanta ki huta kafin magariba.”
Mikewa tayi ta yi sama tana dailing number Ya Aslam.
Wayar suka cigaba dayi tana karasawa daki ta fada kan gado ta ce,
“Wash! Allah Yaa Aslam na gaji “
“Ayyah sannu baby na ko nazo nai miki tausa ne.”
Murmushi tayi ta ce,
“Da kuwa naji dadi.”
Murmushi yayi ya ce,
“To kwanta ki rufe idon ki.”
Kwanciyya tayi ta lumshe idon ta. ya ce,
“Yauwah bari a fara ta kafa ko?”
“Wallahi kamar kasan sun gaji kuwa.”
A hankali ya dinga cewa na miki nan na miki amcan kai ka zaci da gaske tausar yake mata.
Har akai magariba sannan sukai sallama ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta tada sallan.
Sai da tayi isha’i sannan ta mike ta nufi dakin Yaa buhari ta dauki ice cream sannan ta sauka kasa duk agajiye.
Dady ta sama a zaune gefen sa Mami sai Yaa buhari a can gefe. sannu da zuwa tai musu ta zauna gefen Dady tana cewa
“Dady wallahi yau na gaji da yawa.”
“Ayyah sannu Autar dady.”
“Yauwah!”
Dady ta mikawa ice cream din ta ce,
“Dady bismillah!”
Murmushi yayi ya ce
“Nagode!”
Muje to kuci abinci. Ta fada tana mikewa. Binta sukai ta zuba musu ita kuma taja gefe tana shan ice cream.
Yaa Buhari ya ce,
“Dady kaga ko shiyasa da bazan siyo mata ba dan nasan ba son cin abinci take ba.”
Dady ne ya kalle ta ya ce,
” *Husnah* ajiye kici abinci kinji.”
Ajiyewa tayi ta dan tsakuri abincin sannan ta ce ta koshi ta fara shan ice cream din ta.
Suna gamawa tayi sama dan yau a gajiye take.
Kwanciyya tayi ta jawo waya ta lalubo number sa.
Lokacin shima yana kwance aka katon gadon sa sai juyi yake ta kira sa.
Da sauri ya dauka ya ce,
“Baby na lafiya?”
“Uhmm lafiya lou! Yau na gaji shi yasa nazo na dan kwanta da wuri.”
Ya ce
“Nifa ince nasan I yanzu kina gun Dady.”
“Yau na baro Dady da wuri.”
Ya ce,
“To muyi hira.”
Shiru tayi ta ce,
“Ka kawo hirar to.”
Ido ya lumshe ya ce,
” *Husnah* ina bukatar muyi aure wallahi. Dan na fara kosawa zama ni kadai in dawo daga aiki bame min oyoyo bare ingan ki naji dadi.”
Murmushi Asma’u tayi. ya ce,
”Dani dake na shirya, aure kawai nake bukatar muyi. Kuma nasan ko yanzu nace ayi za ai mana”
Asma’u ta ce,
“Yayana ai lokaci ne.”
“Uhmm haka ne, *Husnah* kin jefon kifiya tazo ta soken a zuciya ta. Amman sam ban ji zafi ba ko haushi, saboda kin turan abu me dadi a cikin ta.”
Ido ta zaro tana dariya
“Nayi arangama dake a cikin rayuwa kin shige cikin jikina, munyi shakuwar da babu batun rabuwa, na kira ki mallaki na, haka nima na zamo nakine babu fargaba a cikin rai na. saboda nasan irin son da mukewa juna.”
Idon ta a lumshe ta fara magana tare da murmushi a kan fuskar ta,
“Nice mahadin ka sahibina. Har abadan dakai nake son rayuwa. Ko da rana ko cikin damuna zan tsaya ka ban gujewa dukkan ruwa. Na sanar dakai dukkan sirrika na. Babu wanda zaiji tinda ka adana. Kazama shalele na guna kaine dan lele. Hanyar mu daya ce zata bulle da mun shiga za’a kulle, dadi rayuwa da masoyi shakuwa aure burin ran mu kuma insha Allahu nan ba da jimawa ba zan zama mallakin ka ta har abada.”
Mikewa yayi daga kwancen da yake ya ce,
“Kalaman ki na kashe min jiki da haifar min da kasance tare dake.”
Amsa’u ta ce,
“Haka nima nake ji. Kamar yadda kake koren damuwa. kai ke kawar min da kishiruwa. Bani son muyi rabuwa. Na fison kasancewa dakai har abada. Wallahi yaa Aslam da kai kadai nake son rayuwa, son ka kadai nake so na mutu dashi. Wallahi in bakai mutuwa zan yi ko ban mutu ba zan zamo ina raye kamar gawa ne. kai ne rayuwa ta Yaa Aslam “
Ya ce,
“In bake ya zanyi. In babu ke nazama tarihi, abar batu na duniya. Gangar jiki ce ke duniya amman ruhina da ke zasu kasan ce. Nafi son mutuwa ta raba mu”
“Ban son maganar mutuwa ko rabuwar mu Yayanah.”
Ta fada muryar ta na canja wa.
“Yi hakuri.”
Ya fada.
Dan murmushi ta yi ta ce,
“Ba komai. In munyi aure zan kula da Yaya nah!”
Murmushi yayi ya ce,
“Wallahi akan ki bana bidar shauki, nasan komai wanda zaki iya. Yadda dake nayi auren mu in anyi zamu more rayuwa. Nasan zaki kula dani ki ban duk hakkina.”
Ido ta rufe da tafin hannun ta. wai kunya. Tayi shiru. Ya ce,
“Kina ji na?”
Kai ta gyada tayi shiru Ya gane me yasa tayi shiru dan haka ya ce,
“Wai kunyar nan fa tayi yawa. Ba damar nayi zancen aure. Bude naga idanun ki masu kyau da haske masu haskan zuciya ta.”
“Ya Aslam, Kai ne ka kasance abin anbato na a koda yaushe sai nayi tunanin ka. Dadi cikin kunnuwa na, zancen ka inkayi. ina son na kar kare rayuwa ta da kai. Ni gani nake sam babu wacce ta kaini dace, nice sarauniyar Mata.”
“Kin fi haka ma. in nace zan fadi yadda kike a cikin raina, watakila ki zata na haukace. son ki nasa naji ni a wata duniyar ta daban. Buri na kawai na gan mu tare a inuwa daya.”
“Allah nuna mana.”
“Ameen.”
Agogon dakin sa ya kalla ya ga har sha daya ta gota.
Dariya yayi ya ce
“Baby ina gajiyar ne?”
Murmushi tayi ta ce
“Yaya nah ya gusar min da ita.”
“Kinsan karfe nawa?”
Kai ta girgiza.
Ya ce,
“Karfe shada da miti ashirin da uku.”
“Kai tab hira dakai tafi komai dadi a guna da dauken hankali na wallahi.”
Murmushi yayi ya ce,
“To muje muyi alwala muzo mu kwanta.”
Ta mike shima ya mike suna dawowa sukai sallama kowa yayi addu’a ya kwanta.
Ranar alhamis da wuri ta gama komai ta shirya tayi dakin Dady.
Karfe takwas da arbain ta gama komai ta shiga dakin Yaya Buhari.
Gaisawa sukai kawai ta fita duk dan kar ta makara.
Shi kansa yau yasha mamakin ganin Asma’u bata tsaya jan magana ba.
Baba ma da ya gama shiryawa ita kawai yake jira tana shiga ya tada mota suka nufi makaranta.
Suna cikin tafiya motar ta tsaya. Fita Baba yayi Ya taba motar ya dawo amman shiru.
Sai da yafita sau uku ana hudun Asma’u ta ce,
“Baba me ya samu motar.”
Baba ya ce,
“Asma’u kinsan ance karfen nasara bai da tabbas motar nan lafiya muku fito amman kinga ta tsaya taki tashi.”
Fitowa tayi ta duba agogo tara saura minti biyar.
Waya Baba ya dauka ya kira mai gyara motocin gida ya fada masa inda yake
Kallon sa Asma’u tayi ta ce,
“Baba bari na hau napep dan na makara gashi zanyi submitting aasignment “
“To bari na tsayar miki da Napep din.’
“Aah Baba na gode.”
Ta fada tana dan matsawa.
Mamaki take ganin karfe tara amman ji yan makaranta sai zirga zirga suke bama maza yan makarantun gwamnati.
Duk Napep din da zai zo a cike yake zuwa.
Wata Mota ce ta tsaya a gaban ta. Matsawa Asma’u tayi.
Kara binta akai ta kuma matsawa. Fitowa yayi daga cikin motar.
Wani hadaden saurayi ne ya fito. Fari ne, yana sanye da Ash kalar shadda kafar sa da bakin takalmi haka hannun sa daure da bakin agogo.
Kansa bbabu hula sai gashi dake kwace luf luf. Yana da idanu, haka nan hancin sa dogone har baki.
Karasawa yayi gun ta cikin nutsuwa ya ce,
“Assalamu Alaikum.”
“Wa’aikulum salam!”
Ta fada tana dan matsawa daga wajen.
Kara bin ta yayi ya ce,
“En mata ina zaki?”
Ko kallon sa batai ba ta fara tsaida wani Napep.
Bai tsaya ba sakomakon cikar da yake.
“Naga kamar makaranta zaki kizo na rage miki hanya.”
Dagowa tayi ta watsa masa wani irin kallon sannan ta matsa wajen wani napep da ta tsayar.
Kallon ta yayi har ta shige ciki sannan yayi murmushi ya shiga motar sa ya tafi.
Tana zuwa ta tadda har an yi submitting ga wani malamin yana musu lacturrle.
Kuka ta saka. tana zaune har lecturer ya fito.
Ta shiga ajin ta kifa kanta a benci tana cigaba da kuka.
Zainab ta matso gun ta tana bata hakuri sai ga. sir Sabir nan.
A haka ya shigo har ya gama lecture Asma’u bata dago ba.
Sai da zai fita ya dan matso gefen ta ya ce yana son ganin ta. Sannan ya tafi.
STORY CONTINUES BELOW
Asma’u duk ta tsure dan tasan akan bai ga assignment din ta ba.
“Zainab Allah bazani ba ni nagaji da kullum complain wallahi.”
“Kiyi hakuri kije baki san me zai faru ba.”
Da haka Zainab ta lallabata ta tafi office din nashi.
Da sallama ta shiga bayan tai knocking an bata izinin shiga.
Kai daga kallon ta ma zaka san ta sha kuka dan idon ta yayi ja dashi.
Sir Sabir ne zaune a wata kujera sanye da Wata brown shadda. Gefen sa gayen da ta gani dazu a hanya ne yaso ya rage mata hanya.
Waya taji Sir sabir yana yi yana cewa,
“Ki nifa ban san ta ba a ranar nima na taba ganin ta.”
Shiru yayi sanna ya ce,
“Sai kinzo. In kuma na fita ne shikenan.”
Ya kashe wayar.
Kallon sa ya maida kanta ya ce,
“Mene?”
Kallon sa ta tsaya yi ta ce,
“Uhmm uhmm!”
Sai ku a tayi shiru. Fauwaz dake, gefen sa ya dago dan ganin da wa yake.
Ido ya zaro ya ce
“Kai kece?”
Kallon sa tayi ta dauke kai ta ce,
“Sir kace nazo.”
“Me yasa banga assignment dinki ba.”
Shiru tayi.
Sai da ya kara nanata tambayar sannan ta dago ta kalle shi
Fauwaz ne ya dago ya ce,
“Friend ita ce wacce nake baka labarin na hadu da ita fa dazu. Motar suce ta lalace,”
Hararar sa Sabir yayi ya kalle ta ya ce,
“Ke me yasa kullum kina da matsala ne, in tayi baki makara ba yau abu kaza ya faru me yasa ne *Husnah* “
Fauwaz ya ce,
“Haba aboki kayi hakuri man.”
Ya kalli Asma’u ya ce,
“Beauty mene matsalar ki yanzu?”
Banza tai masa tai kasa da kai idon ta na cikowa da kwalla dan ita da kai mata fada gara ka dake ta. Bata son fada a rayuwar ta yanzu zata fara kuka.
Kallon ta Sabir yayi ya ce,
“Mikon Assignment din naki kuma ki kara samun matsala na rashin submtting ko makara ki gani.”
Da sauri ta dauko ta mika masa. Ta ce,
“Nagode!”
Tayi hanyar fita da sauri Fauwaz ya mike zai bita Sabir yai saurin riko hannun sa.
kafin ta bude kofa aka bude. Maryam ce ta shigo cikin shigar ta mai kyau ta saka doguwar rigar atamfa a mata dinkin mai dogon hannu.
Mayafin ta dan yafa kai ba dan kwalli sai jaka dake kafadar ta.
Tana ganin Asma’u ta saka dariya ta ce
“lah Asma’u!”
Sai kuma ta kama hannun ta. Ta kalli Sabir ta ce,
“Uncle kace, baka santa ba a ranar ka taba ganin ta.”
Sai a lokacin Amsa’u ta tuno da statement din sa da ta shigo taji yana waya.
Kamo hannun ta tayi suka shigo office din ta ce,
“Ke nazo nema muyi sallama gobe zan koma garin mu gashi ban da number ki.”
Murmushi Amsa’u tayi wanda Fauwaz ya kasa dauke ido daga kallon ta.
Hannun Maryam ta kama suka fita kallo Fauwaz da Sabir suka bisu da shi.
Wajen Zainab suka karasa ta zauna sannan sukai musayar number sai hira ta balle.
Dan har lecture tare suka shiga suka fito sukaje sallah sannan suka je cafteria suka ci abinci.
Sai karfe biyar sannan suka rabu shima dan an tashi.
Har bakin office din Sabir suka rakata suna daga mata hannu sannan suka juya.
Sabir da ya zata ma ta tafi ta shiga ta zauna akan kujera ta ce,
“Wash! Wallahi Uncle na gaji haka nima zan sha fama in na fara karatu.”
Kallon ta yayi ya ce
“Daman baki tafi ba.”
Kai ta daga masa ta kalli Fauwaz ta ce,
“Uncle Fauwaz ya kake?”
“Ni ba ruwana da ke. Kin tafi kin barni.”
dariya tayi ta ce,
“Ayi hakuri wallahi Uncle Fauwaz. Asma’u ce ta burge ni na dawo amsar number ta kasan gobe zamu shige.”
Kai ya daga ya ce,
“Dan bani number na gani.”
“Tab ta ce, kar na bawa kowa wallahi.”
Sai lokacin Sabir ya ce,
“In ba kwana zamuyi ba mu tashi mu tafi dare na yi biyar da rabi fa.”
Mikewa yayi ya dauki jakar sa da basket ya mikawa Maryam Amsa tayi suka fito tana ta basu labarin Amsa’u in ka kalli Sabir zaka zaci ba jin ta yake ba amman gaba daya hankalin sa na ga ita yana jin abubuwan da take fada.
Da haka suka je gida haka tai ta bawa Mamah labarin Asma’u ranar dai har dare bata da magana sai Asma’u daga ta ce, tayi kaza sai ta ce tayi kaza.
Ta ce,
“Mamah baki ga ba yarinya karama ta na karanta medicine kuma a final year wallahi ta burge ni ga kokari da muka shiga lecture ita ke bada asma.”
Mamah ta ce,
“Sai ki koyi da ita to.”
“Ai insha Allahu Mamah kuma nayi ‘kawa.”
Shi dai yana zaune yana ji yana kara jin Asma’u na kara burge shi.
Asma’u ma da taje gida sai da ta bawa Mami labarin yarinyar.
Mami ta ce,
“Daman haka rayuwa take wani na son ka wani kuma kin ka yake yanzu dai ita kince daga haduwa Allah ya sa mata son ki. To Allah ya bar mu ga masoyan mu.”
“Ameen!”
Ta mike ta hau sama.
Yaya Aslam ne ya kira ta bayan sun gaisa yake tambayar ta makaranta ita ma take tambayar sa wajen aiki.
Soyayyar Asma’u da Aslam abin sha’awa ce da burge wa dan ba karamin son juna su suke ba kowa da son dan uwan sa son da basa son su taba rabuwa da junan su.
Kowa na kula da tarairayar juna. Ga shi soyayyar su mai tsabta da kyau suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *